Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

๏ปฟ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ
*'YA'YANAH*
*{jarinah}*
๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ





*NAH*
*frauxeeyah s madakeeh*
(Autar kainuwa)


```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI, TARE DA NADAMA ME TSANANI.```




*NOT FOR SALE*



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*
Wednesday.
*01/01/2020*
___________________________________



*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
_____________________________________

*_Alhamdulillahi rabbil'alamin....dukkan godiya ta tabbata ga allah madaukakin sarki, wanda da ikonsa ne komai yake faruwa._*
*_Aminci tare da rahma su tabbata ga shugaban halitta, annabi muhammad (S.A.W).da alayensa da sahabbansa._*



*TSOKACI*
```Wannan littafi nawa k'irk'irar ren labarine, banyi dan cin zarafin wani ko wata ba, duk wacce yai dai-dai da halayyar ta ko suna toh tamin afuwa a rashin sanine... Ban yarda wani ko wata su jiya min labariba.```



๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ

*~Wallahi wani al'khairin idan akayi makashi yafi gaban kai godiya kai tsaye, sai dai kace sauran masoyanka su tayaka mik'a godiyarka๐Ÿ‘‡๐Ÿผ๐Ÿ‘‡๐Ÿผ~*

_Sister Zubaidah_
Da
_Broth Husaini 80k_


*littafinnan tun daga farkon shi har k'arshe sadaukar wane a gareku.*

*~Ina godiya sosai akan dumbin al'khairinku gareni, allaha ya saka muku da mafificin al'khairin sa, allah ya kareku daga dukkan sharri, allah ya kareku daga sharrin mahassada da makiya allahumma ameen๐Ÿ‘๐Ÿผ๐Ÿ‘๐Ÿผ~*




*DA SUNAN ALLAH ME RAHMA ME JIN K'AI*



*SABO WUSE*



๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *1&5*

*tudun wada*

"""Misalin karfe biyar da rabi na yamma, zaune suke suna fira cikin kwanciyar hankali da annushuwa, abinci ne a gaban dayan yanaci cikin farin ciki, kawai sai ganin yai an dauke kwanon abincin, yana dago kanshi yaga abba a gabansa yana ta faman huci.
Sauk'owa yai daga kan kujerar da yake, " yana fadin abbah ina wuni"...



Abbah "yace saurara malam, wai kai wanne irin mutum ne"?.
Banace kar na sake ganin ka a gidana ba?... "Wato har da abincin gidana kakeci", ba laifin ka bane, juyawa yai yace ni dai bansan halin wa kika kwasoba wallahi dan ni dai ba hali na bane, wuce ki bani waje.


_sai lokacin naga fuskar yarinyar kamar tayi kuka ta shiga gida tana waigo wa._



Sai lokacin ne saurayin yasamu damar yin magana, "yace abbah dan allah kar ka rabamu da nabeelah, na rok'eka abbah."๐Ÿ‘๐Ÿผ,
Juya baya abbah yayi yana cewa da me zaka iya rike tah? Bai barshi yayi magana ba yaci gaba da cewa " ko so kake na sai da akuya ta ta dawo tana ci min danga," toh bazai yiwu ba wallahi, kaga kyaykkyawar yarinya duk ka hure mata kunne toh bari kaji, *'YA'YANAH* 'yan hutune ba wacce zanwa auren wahala. yana gama fadar haka ya wuce ciki yana ta faman sababi.




Tashi saurayin yayi daga tsugunnon da yayi, kamar zaiyi kuka haka ya fito ya tafi gida.


Abbah yana shiga gida ya fara fada, wata mata naga ta fito tana fadin a'a al'haji lafiya kai dawa?.
Abbah "yace ni da yarinyar nan mana, na rasa a wajen wa ta dauko kafiya da taurin kai na rabata da yaron nan amma batajin magana, yanzu kuma har abincin gidana ake bashi ban saniba, kuma nasan da saninki take komai.
Kallon nabeelah tayi sannan tace waye yazo wajenki.?


Wanda aka kira da nabeelah tace mama al'ameen nefah, abbah " yace al'ameen din ni nake da ikon ciyar dashi, ai shi ya kamata ya kawo min a matsayina na wanda yakeso na zama sirikin sa.


_nikam nace lallai abbah kana ruwa๐Ÿ˜†๐Ÿ™Š_



ยฐยฐยฐmamah "tace haba al'haji dan allah ka dinga siyawa kanka mutunci a wajen yaron nan, sirikin kane fah amma sai da ka amso abincin nan.
Abbah yace dama ai na dade dasani ke kikesa yarinyar nan take biyewa yaron nan, amma zan gani ai nine mai ba da auren ko, yana gama fadar haka ya wuce dakinsa.



_nikam nace toh abbah allah yasa ka gane gaskiya tun kafin lokaci ya kure maka๐Ÿคญ๐Ÿ‘๐Ÿผ_


๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*BAUCHIN YAKUBU*

""" 'yan mata ne guda biyu zaune a kan gado kowacce da waya a hannun ta kirar *iPhone 11+* kowacce tana danna wayar tana smile... ga dukkan alamu chatting sukeyi, domin suna cikin nishadi.


Kofar dakin aka turo sai naga duk sun boye wayoyin sun dauki littafi kamar suna karatu.




*Muje zuwa guys yanzu wasan zai faraโ˜บโ˜บ*





*JUST FOLLOW ME*





_more comments_
_more typing_





*comments*
*share*
*vote*


๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ
*'YA'YANAH*
*{jarinah}*
๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ




*NAH*
*frauxeeyah s madakeeh*
(Autar kainuwa)




```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI, TARE DA NADAMA ME TSANANI.```





*NOT FOR SALE*




*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

Saturday
*04/01/2020*
____________________
________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________


*SADAUKARWA GA*

_Sister Zubaidah_
Da
_Broth Husaini 80k_




*DA SUNAN ALLAH MAI RAHMA MAI JIN KAI*




๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *5to10*





*โฐ โ˜ ุฃุฐูƒุงุฑ ุงู„ุตุจุงุญ ูˆุงู„ู…ุณุงุกโ›…*

*zikirin safiya da maraice*
๐ŸŒค๐ŸŒค๐ŸŒค๐ŸŒค๐ŸŒค

*ุงุนูˆุฐ ุจุงู„ู„ู‡ ู…ู† ุงู„ุดูŠุทุงู† ุงู„ุฑุฌูŠู…*

*ุงู„ู„ู‡ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ู‡ูˆ ุงู„ุญูŠ ุงู„ู‚ูŠูˆู… ู„ุง ุชุฃุฎุฐู‡ ุณู†ุฉ ูˆู„ุง ู†ูˆู… ู„ู‡ ู…ุง ููŠ ุงู„ุณู…ูˆุงุช ูˆู…ุง ููŠ ุงู„ุฃุฑุถ ู…ู† ุฐุง ุงู„ุฐูŠ ูŠุดูุน ุนู†ุฏู‡ ุฅู„ุง ุจุฅุฐู†ู‡ ูŠุนู„ู… ู…ุง ุจูŠู† ุฃูŠุฏูŠู‡ู… ูˆู…ุง ุฎู„ูู‡ู… ูˆู„ุง ูŠุญูŠุทูˆู† ุจุดูŠุก ู…ู† ุนู„ู…ู‡ ุฅู„ุง ุจู…ุง ุดุงุก ูˆุณุน ูƒุฑุณูŠู‡ ุงู„ุณู…ูˆุงุช ูˆุงู„ุฃุฑุถ ูˆู„ุง ูŠุคูˆุฏู‡ ุญูุธู‡ู…ุง ูˆู‡ูˆ ุงู„ุนู„ูŠ ุงู„ุนุธูŠู…*

โ„โ„โ„

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

*ู‚ู„ ู‡ูˆ ุงู„ู„ู‡ ุฃุญุฏ(ูก)* *ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุตู…ุฏ(ูข)* *ู„ู… ูŠู„ุฏ ูˆู„ู… ูŠูˆู„ุฏ(ูฃ)* *ูˆู„ู… ูŠูƒู† ู„ู‡ ูƒููˆุง ุฃุญุฏ(ูค)*

โ„โ„โ„

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

*ู‚ู„ ุฃุนูˆุฐ ุจุฑุจ ุงู„ูู„ู‚(ูก)* *ู…ู† ุดุฑ ู…ุง ุฎู„ู‚(ูข) *ูˆู…ู† ุดุฑ ุบุงุณู‚ ุฅุฐุง ูˆู‚ุจ(ูฃ)* *ูˆู…ู† ุดุฑ ุงู„ู†ูุงุซุงุช ููŠ ุงู„ุนู‚ุฏ(ูค)* *ูˆู…ู† ุดุฑ ุญุงุณุฏ ุฅุฐุง ุญุณุฏ(ูฅ)*

โ„โ„โ„

*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

*ู‚ู„ ุฃุนูˆุฐ ุจุฑุจ ุงู„ู†ุงุณ(ูก)* *ู…ู„ูƒ ุงู„ู†ุงุณ(ูข)* *ุฅู„ู‡ ุงู„ู†ุงุณ(ูฃ)* *ู…ู† ุดุฑ ุงู„ูˆุณูˆุงุณ ุงู„ุฎู†ุงุณ(ูค)* *ุงู„ุฐูŠ ูŠูˆุณูˆุณ ููŠ ุตุฏูˆุฑ ุงู„ู†ุงุณ(ูฅ)* *ู…ู† ุงู„ุฌู†ุฉ ูˆ ุงู„ู†ุงุณ(ูฆ)*

*ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช*


๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *5to10*

"""Wani babban mutum na gani ya shigo dakin da fara'arsa, jinai sun hada baki sunce "daddy barka da dare."
Wanda aka kira da daddy ya fad'ad'a murmishin sa yana fadin a'a twins ana ta karatu ko, sukace eh wallahi daddy kasan mun kusa exam ne, daddy yace "toh masha allah, allah ya taimaka ayi ta karatu sosai," sukace toh daddy.



Juyawa yai yana fadin toh ni na shiga daki, sai da safen Ku, ku tabbata kun rufe kofa kafin ku kwanta, sukace toh daddy bye.
Yana fita suka dauko wayoyinsu suka ci gaba da charting dinsu.


Dayar ce naji tace"haseenah wallahi aure nake so amma sam daddy ya kasa fahimta bansan wacce irin rayuwa yakeso muyi baโ˜น
Wadda aka kira da haseenah tace ni kaina nafi buk'atar auren tunda ai zamu iya hada karatu da auren, amma bansan wanne irin girma daddy yakeson muyi ba, *25yrs* ace bamu girmaba sai yaushe.


*_hmmm readers nasan kun k'osa kusan suwaye wad'annan 'yanmatan da kuma daddy, toh karku damu muje zuwa a sannu zan warware muku komai insha allah_*




๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
_______________

"""A dakinma abbah kasa zama yayi, yanata tunanin yadda nabeelah takeson lalata mishi *dogon burin sa,* wanda yai shekara da shekaru yana jiran shi,yasan dai bashi da matsala da safna da husna....
Yana ta tunani baisan lokacin da mamah ta shigo ba, sai da ta dafashi sannan ya dago kanshi yana kallon ta, a hankali mamah tace nazo ne muyi magana ta fahimta ni da kai,
Sai da yaja dogon numfashi sannan ya zauna yace" ina sauraronki".



Zama tayi itama sannan ta fara magana...
"Al'haji zuwa yanzu ya dace ace ka sauke wannan tsatstsauran ra'ayin naka kabar 'ya'yan nan su kawo mijin da suke son ya zama abokin rayuwar su da kansu, idan yaso sai kai binkice akan shi, idan ya hada abubuwan da shari'a ta addini tace, to falillahil hamdu, kaga saimu sawa abin al'barka,idan kuma ta kawo idan kuma suka kawo akasin haka sai mu zaunar dasu muyi musu nasiha sannan mu sake basu dama.



Kaga dai ai *al'ameen* ai yarone me ilimi da biyayya, sannan ga tarbiya, idan ya auri yarinyar nan mu kammu zamuyi alfahari da hakan anan gaba......
Hannu abbah ya daga wa mamah, sannan yace "nifah bazan taba kai 'ya'yana gidan daza susha wuya ba, a k'arshe na dawo ciyar dasu,toh wacce riba na samu kenan?



Numfashi mamah ta sauke sannan ta fara magana, al'haji wallahi ina tsorace maka ranar da zaka zo kana da nasani a lokacin da bazai amfane kaba, kasan mazon allah (s.a.w) yace: *_duk mutumin da allah ya bashi 'ya'ya mata guda uku, ya tarbiyantar dasu har ya aurar dasu, toh allah zai sashi a aljannah"_* sai wata mata tace "ya rasulillah ko biyu ne", *_sai manzon allah yace " ko da biyu ne"._*
Kaga kenan babu ribar da tafi wannan.


Abbah bai sake magana ba ya fice yabar mamah a zaune.





*JUST FOLLOW ME*




_more comments_
_more typing_





*COMMENTS*
*SHARE*
*VOTE*



๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ
*'YA'YANAH*
*{jarinah}*
๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ




*NAH*
*frauxeeyah s madakeeh*
(Autar kainuwa)




```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI, TARE DA NADAMA ME TSANANI.```




*NOT FOR SALE*



_more comments๐Ÿ˜_
_more typing๐Ÿ˜_



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*


Tuesday
*14/01/2020* ____________________________________


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
____________________________________



S๊™ฒย ย ย ย A๊™ฒย ย ย ย D๊™ฒย ย ย ย A๊™ฒย ย ย ย U๊™ฒย ย ย ย K๊™ฒย ย ย ย A๊™ฒย ย ย ย R๊™ฒย ย ย ย W๊™ฒย ย ย ย A๊™ฒย ย ย ย  G๊™ฒย ย ย ย A๊™ฒย ย ย ย 

๊œฑษช๊œฑแด›แด‡ส€ แดขแดœส™แด€ษชแด…แด€สœ
๐Ÿ…ฐ๐Ÿ…ฝ๐Ÿ…ณ
ส™ส€แดแด›สœ สœแดœ๊œฑแด€ษชษดษช 80แด‹




๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *10to15*


ุงุฐูƒุงุฑ ุงู„ุตุจุงุญ ูˆุงู„ู…ุณุงุก
*Addu'ar safiya da maraice*


๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุฃุตุจุญู†ุง ูˆุฃุตุจุญ ุงู„ู…ู„ูƒ ู„ู„ู‡ุŒ ูˆุงู„ุญู…ุฏ ู„ู„ู‡ุŒ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡ ูˆุญุฏู‡ ู„ุง ุดุฑูŠูƒ ู„ู‡ุŒ ู„ู‡ ุงู„ู…ู„ูƒ ูˆู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏ ูˆู‡ูˆ ุนู„ู‰ ูƒู„ ุดูŠุก ู‚ุฏูŠุฑุŒ ุฑุจ ุฃุณุฃู„ูƒ ุฎูŠุฑ ู…ุง ููŠ ู‡ุฐุง ุงู„ูŠูˆู… ูˆุฎูŠุฑ ู…ุง ุจุนุฏู‡ุŒ ูˆุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุดุฑ ู…ุง ููŠ ู‡ุฐุง ุงู„ูŠูˆู… ูˆุดุฑ ู…ุง ุจุนุฏู‡ุŒ ุฑุจ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุงู„ูƒุณู„ ูˆุณูˆุก ุงู„ูƒุจุฑุŒ ุฑุจ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุนุฐุงุจ ููŠ ุงู„ู†ุงุฑ ูˆุนุฐุงุจ ููŠ ุงู„ู‚ุจุฑ*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุจูƒ ุฃุตุจุญู†ุงุŒ ูˆุจูƒ ุฃู…ุณูŠู†ุงุŒ ูˆุจูƒ ู†ุญูŠุงุŒ ูˆุจูƒ ู†ู…ูˆุช ูˆุฅู„ูŠูƒ ุงู„ู†ุดูˆุฑ*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุฃู†ุช ุฑุจูŠ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุชุŒ ุฎู„ู‚ุชู†ูŠ ูˆุฃู†ุง ุนุจุฏูƒุŒ ูˆุฃู†ุง ุนู„ู‰ ุนู‡ุฏูƒ ูˆูˆุนุฏูƒ ู…ุง ุงุณุชุทุนุชุŒ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุดุฑ ู…ุง ุตู†ุนุชุŒ ุฃุจูˆุก ู„ูƒ ุจู†ุนู…ุชูƒ ุนู„ูŠุŒ ูˆุฃุจูˆุก ุจุฐู†ุจูŠ ูุงุบูุฑ ู„ูŠ ูุฅู†ู‡ ู„ุง ูŠุบูุฑ ุงู„ุฐู†ูˆุจ ุฅู„ุง ุฃู†ุช*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุตุจุญุช ุฃุดู‡ุฏูƒุŒ ูˆุฃุดู‡ุฏ ุญู…ู„ุฉ ุนุฑุดูƒุŒ ูˆู…ู„ุงุฆูƒุชูƒุŒ ูˆุฌู…ูŠุน ุฎู„ู‚ูƒุŒ ุฃู†ูƒ ุฃู†ุช ุงู„ู„ู‡ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุช ูˆุญุฏูƒ ู„ุง ุดุฑูŠูƒ ู„ูƒุŒ ูˆุฃู† ู…ุญู…ุฏุง ุนุจุฏูƒ ูˆุฑุณูˆู„ูƒ.*
- ุฃุฑุจุน ู…ุฑุงุช
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ู…ุง ุฃุตุจุญ ุจูŠ ู…ู† ู†ุนู…ุฉ ุฃูˆ ุจุฃุญุฏ ู…ู† ุฎู„ู‚ูƒ ูู…ู†ูƒ ูˆุญุฏูƒ ู„ุง ุดุฑูŠูƒ ู„ูƒุŒ ูู„ูƒ ุงู„ุญู…ุฏ ูˆู„ูƒ ุงู„ุดูƒุฑ*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุนุงูู†ูŠ ููŠ ุจุฏู†ูŠุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุนุงูู†ูŠ ููŠ ุณู…ุนูŠุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุนุงูู†ูŠ ููŠ ุจุตุฑูŠุŒ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุช. ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุงู„ูƒูุฑุŒ ูˆุงู„ูู‚ุฑุŒ ูˆุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุนุฐุงุจ ุงู„ู‚ุจุฑุŒ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุช*
- ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช -
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุญุณุจูŠ ุงู„ู„ู‡ ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ู‡ูˆ ุนู„ูŠู‡ ุชูˆูƒู„ุช ูˆู‡ูˆ ุฑุจ ุงู„ุนุฑุด ุงู„ุนุธูŠู…*
- ุณุจุน ู…ุฑุงุช -
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุณุฃู„ูƒ ุงู„ุนููˆ ูˆุงู„ุนุงููŠุฉ ููŠ ุงู„ุฏู†ูŠุง ูˆุงู„ุขุฎุฑุฉุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุณุฃู„ูƒ ุงู„ุนููˆ ูˆุงู„ุนุงููŠุฉ ููŠ ุฏูŠู†ูŠ ูˆุฏู†ูŠุงูŠ ูˆุฃู‡ู„ูŠุŒ ูˆู…ุงู„ูŠุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุงุณุชุฑ ุนูˆุฑุงุชูŠุŒ ูˆุขู…ู† ุฑูˆุนุงุชูŠุŒ ุงู„ู„ู‡ู… ุงุญูุธู†ูŠ ู…ู† ุจูŠู† ูŠุฏูŠุŒ ูˆู…ู† ุฎู„ููŠุŒ ูˆุนู† ูŠู…ูŠู†ูŠุŒ ูˆุนู† ุดู…ุงู„ูŠุŒ ูˆู…ู† ููˆู‚ูŠุŒ ูˆุฃุนูˆุฐ ุจุนุธู…ุชูƒ ุฃู† ุฃุบุชุงู„ ู…ู† ุชุญุชูŠ*
๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
*ุงู„ู„ู‡ู… ุนุงู„ู… ุงู„ุบูŠุจ ูˆุงู„ุดู‡ุงุฏุฉ ูุงุทุฑ ุงู„ุณู…ูˆุงุช ูˆุงู„ุฃุฑุถุŒ ุฑุจ ูƒู„ ุดูŠุก ูˆู…ู„ูŠูƒู‡ุŒ ุฃุดู‡ุฏ ุฃู† ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุฃู†ุชุŒ ุฃุนูˆุฐ ุจูƒ ู…ู† ุดุฑ ู†ูุณูŠุŒ ูˆู…ู† ุดุฑ ุงู„ุดูŠุทุงู† ูˆุดุฑูƒู‡ุŒ ูˆุฃู† ุฃู‚ุชุฑู ุนู„ู‰ ู†ูุณูŠ ุณูˆุกุงุŒ ุฃูˆ ุฃุฌุฑู‡ ุฅู„ู‰ ู…ุณู„ู….*




๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *10to15*


"""""Tunda abbah ya fita mamah tana zaune tanata tunanin ko abbah ya dauki shawarar ta, addu'a ta fara a zuci tana fatan allah yasa mijin ta ya gane gaskiya tun kafin ranar nadama tazo mishi.



""" Abbah yana fitowa ya ga safna da saurayinta suna fira, sai ya kara gyara tafiyar sa๐Ÿ˜†


_su abbah anga me maiko๐Ÿ˜๐Ÿ™Š๐Ÿƒโ€โ™€_

K'arasawa yai yamusu sallama.
Amsawa sukai cikin farin ciki, suka gaidashi, ya amsa da zai wuce mutumin ya ehbo kudi baiko k'irgasu ba ya mik'awa abbah, cikin farin ciki abbah yasa hannu ya karba yanata godiya kamar zai zauna mishi.


Abbah ya na tafe sai magana yakeyi shi kadai, "banda yarinya ta dauko irin halin uwar ta me zatayi da wannan talakan da ko sisinsa baci zatai ba" barinta zanyi tunda taji ta gani taje ta aure shin dad'in abinma ba ita kadai na haifa ba.



"" lokacin da saurayin safna zai tafi itama ya bata kudi sannan sukai sallama.



Tana shiga gida ta b'oye kudin dan tasan da mama tagani zata hauta da fadan me yasa ta karb'a, abbah kadai take nunawa sannan ta bashi wani abu a ciki.



Abbah yana dawowa gida "yace wa nabeelah tace wa al'ameen ya turo iyayensa".

Ba nabeelah kadai ba har da mama sai da tayi mamakin furicin na abbah, tunani mama ta fara yi kodai yaji nasihar da tayi masa ne.
Itakam nabeelah da to ta amsa sannan ta tashi ta koma daki, tana shiga daki ta dauki waya ta kira al'ameen, bayan sun gaisa tace "albishirin ka".

Al'ameen yace "goro fari k'atoto".

Nabeelah tace "abba ya amince muyi aure ni da kai, yace ma ka turo magabatan ka".
Al'ameen najin haka ya fadi yai *sujud shukur*(sujjadar godiya ga allah), nabeelah ta kira sunan sa a hankali "my one kayi shiru", ko bakayi murna bane? Al'ameen yace baby ina fara gode wa allah ne domin shine ya kawo mana komai cikin sauki, gaskiya baby naji dadi sosai allah ya tabbatar mana da al'khairi.

Nabeelah tace "ameen my"

Al'ameen yace toh baby zan shiga na sanar da umma tun yanzu, dan kinsan hausawa sunce _da wur-wuri ake kama fara,_ sai nazo anjima bye.


Murmishi nabeelah tayi sannan ta ajiye wayar, dama wayar safna take dauka idan zasuyi wayar ko ta mama.





```MUJE ZUWA MY GUY'S๐Ÿ˜ ```





*JUST FOLLOW ME*




_no comments_
_no typing_




*_comments_*
*_share_*
*_vote_*

๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ

*'YA'YANAH*
*(jarinah)*
๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ




*NAH*
fauziyyah s madaki
*{autar kainuwa}*




```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI TARE DA NADAMA ME TSANANI```




*THIS BOOK IS NOT FOR SALE๐Ÿ˜˜*



_more comments_
_more typing_



*VOTE ME ON WATTPAD*
*_fauxeey201*



*ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฑุญู…ู† ุงู„ุฑุญูŠู…*

Thursday
*30/01/2020* *____________________________________*


*๐ŸŒˆKAINUWA WRITERSโœ๐Ÿผ ASSOCIATION*๐Ÿค๐Ÿป
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



โ• Sโ•ฃโ• Aโ•ฃโ• Dโ•ฃโ• Aโ•ฃโ• Uโ•ฃโ• Kโ•ฃโ• Aโ•ฃโ• Rโ•ฃโ• Wโ•ฃโ• Aโ•ฃ โ• Gโ•ฃโ• Aโ•ฃ

*Sister zubaidah*
๐Ÿ…๐Ÿ…๐Ÿ…“
*Broth Hussain 80K*





๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *15to 20*



ุงุฐูƒุงุฑ ุงู„ุตุจุงุญ ูˆุงู„ู…ุณุงุก
*zikirin safiya da maraice*

๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุจุณู… ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุฐูŠ ู„ุง ูŠุถุฑ ู…ุน ุงุณู…ู‡ ุดูŠุกููŠ ุงู„ุงุฑุถ ูˆู„ุงููŠ ุงู„ุณู…ุงุก ูˆู‡ูˆ ุงู„ุณู…ูŠุน ุงู„ุนู„ูŠู…))*
ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุฑุถูŠุช ุจุงู„ู„ู‡ ุฑุจุงุŒูˆุจุง ู„ุฅุณู„ุงู… ุฏูŠู†ุงุŒูˆุจู…ุญู…ุฏ (ุตู„ู„ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…)ู†ุจูŠุง))*
ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ูŠุงุญูŠ ูŠุง ู‚ูŠูˆู… ุจุฑุญู…ุชูƒ ุฃุณุชุบูŠุซุŒุฃุตู„ุญ ู„ูŠ ุดุฃู†ูŠ ูƒู„ู‡ุŒูˆู„ุงุชูƒู„ู†ูŠ ุฅู„ู‰ ู†ูุณูŠ ุทุฑูุฉุนูŠู†))*
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุฃุตุจุญู†ุงูˆุฃุตุจุญ ุงู„ู…ู„ูƒ ู„ู„ู‡ ุฑุจ ุงู„ุนุงู„ู…ูŠู†ุŒุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุณุฃู„ูƒ ุฎูŠุฑู‡ุฐุง ุงู„ูŠูˆู…:ูุชุญู‡ุŒูˆู†ุตุฑู‡ุŒูˆ ู†ูˆุฑู‡ุŒูˆ ุจุฑูƒู„ุชู‡ุŒูˆ ู‡ุฏุงู‡ุŒูˆ ุฃุนูˆุฐุจูƒ ู…ู† ุดุฑู…ุง ููŠู‡ ูˆุดุฑ ู…ุง ุจุนุฏู‡))*
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุฃุตุจุญู†ุง ุนู„ู‰ ูุทุฑุฉ ุงู„ุฅุณู„ุงู…ุŒูˆ ุนู„ู‰ ูƒู„ู…ุฉุงู„ุฅุฎู„ุงุตุŒูˆ ุนู„ู‰ ุฏูŠู† ู†ุจูŠู†ุงู…ุญู…ุฏ(ุตู„ู‰ ุงู„ู„ู‡ ุนู„ูŠู‡ ูˆุณู„ู…)ุŒูˆ ุนู„ู‰ ู…ู„ุฉุฃุจูŠู†ุง ุฅุจุฑุงู‡ูŠู…ุŒ ุญู†ูŠูุง ู…ุณู„ู…ุงูˆู…ุงูƒุงู† ู…ู† ุงู„ู…ุณุฑูƒูŠู†))*
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุณุจุญุงู† ุงู„ู„ู‡ ูˆุจุญู…ุฏู‡))*
ู…ุงุนุฉ ู…ุฑุฉ.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ู„ุงุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡ ูˆุญุฏู‡ ู„ุงุดุฑูŠูƒ ู„ู‡ุŒู„ู‡ ุงู„ู…ู„ูƒุŒูˆ ู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏุŒูˆ ู‡ูˆุนู„ู‰ ูƒู„ ุดูŠุกู‚ุฏูŠุฑ))*
ุนุดุฑ ู…ุฑุงุชุŒ ุฃูˆ -ู…ุฑุฉูˆุงุญุฏุฉุนู†ุฏุงู„ูƒุณู„.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ู„ุง ุฅู„ู‡ ุฅู„ุง ุงู„ู„ู‡ุŒ ูˆุญุฏู‡ ู„ุง ุดุฑูŠูƒ ู„ู‡ุŒ ู„ู‡ ุงู„ู…ู„ูƒ ูˆู„ู‡ ุงู„ุญู…ุฏุŒูˆ ู‡ูˆุนู„ู‰ ูƒู„ ุดูŠุกู‚ุฏูŠุฑ))*
ู…ุงุนุฉู…ุฑุฉ ุฅุฐุง ุฃุตุจุญ.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุณุจุญุงู† ุงู„ู„ู‡ ูˆุจุญู…ุฏู‡ุŒุนุฏุฏุฎู„ู‚ู‡ุŒูˆ ุฑุถุงู†ูุณู‡ุŒ ูˆ ุฒู†ุฉ ุนุฑุดู‡ ุฒู…ุฏุงุฏูƒู„ู…ุงุชู‡))*
ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช ุฅุฐุงุฃุตุจุญ.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุงู„ู„ู‡ู… ุฅู†ูŠ ุฃุณุฃู„ูƒ ุนู„ู…ุงู†ุงูุนุงุŒูˆ ุฑุฒู‚ุงุทูŠุจุงุŒูˆ ุนู…ู„ุงู…ุชู‚ุจู„ุง))*
ุฅุฐุง ุฅุตุจุญ.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุฃุณุชุบูุฑ ุงู„ู„ู‡ ูˆ ุฃุชูˆุจ ุฅู„ูŠู‡))*
ู…ุงุนุฉ ู…ุฑุฉ ููŠ ุงู„ูŠูˆู….
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุฃุนูˆุฐ ุจูƒู„ู…ุงุช ุงู„ู„ู‡ ุงู„ุชุงู…ุงุช ู…ู† ุดุฑ ู…ุง ุฎู„ู‚))*
ุซู„ุงุซ ู…ุฑุงุช ุฅุฐุง ุฃู…ุณู‰.
๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ ๐ŸŒบ
*((ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ู†ุจูŠู†ุง ู…ุญู…ุฏ))*
ุนุดุฑ ู…ุฑุงุช.




๐Ÿ…๐Ÿ…ž: *15to20*

Al'ameen yana shiga gidan su, ya sami umma tana wanke-wanke kujera yaja ya zauna dauke da murmishi a fuskar sa, kallonsa umma tayi tace "me sunan manya" _da yake haka take kiransa_ yau kyautar me kasamu ne kake farin ciki haka? Ko kasamu labarin aikin da kake nemane?.
Dariya sosai al'ameen yayi yace "duk baki chanka ba umma, kyautar da akamin duk tafi abin da kika lissafo, kyauta ce da babu wanda ya isa ya ba da ita sai allah,
Umma tace "zaka fadamin na taya ka farin cikin ko sai ka gama jamin rai"! Da sauri al'ameen yace "ni na isa umma, kyautar dan mutum akayimin, kinga kwa ai yafi samun aikin", cikin rashin fahimta umma tace wanne irin kyautar mutum kuma kai da ba aure ba ya zakayi da yaron? Murmishi al'ameen yayi sannan yace toh umma bari dai nayi miki dallah-dallah, baban su *nabeelah* ya amince na tura magabatana ayi maganar auren mu.



Da sauri umma ta dago tana kallon d'an nata cikin tashin hankali ta fara magana "me sunan manya dan allah ka dawo hayyacin ka kada soyayya tasa ka zautu dan allah kabar wa allah komai idan yarinyar nan rabon kace zaka aure ta, amma bazanso ka jefa rayuwar ka cikin wani haliba ku biyu allah ya bani, kuma na yiwa mahaifin ku al'k'awarin kula da duk wata damuwar ku, ka taimaka ka tayani cika al'k'awarin."
Numfashi al'ameen ya sauke sannan ya fara magana, umma nifah lafiya ta k'alau kuma a cikin hankalina nake magana, da gaske nake abban nabeelah ya buk'aci ganin wakilai na, numfashi umma ta sauke, sannan tace toh allah yasa al'khairi ne dan gaskiya hankalina bai kwanta da saukowar mutumin nan daga kan ra'ayin sa ba lokaci guda, kuma yasan har yanzu baka da kudin da zai hada zuri'a da kai.
Al'ameen yace ni dai umma ki tamin addu'a tunda babu abin da ya gagari ubangiji, umma tace wannan haka yake, bari na gama gyaran gida sai naje na samu kawunka muyi maganar, godiya al'ameen yayi mata sannan ya fita zuciyar sa cike da farin ciki.
Da kallo umma ta bishi tana saka mishi al'barka har ya fita, sannan taci gaba da wanke-wanken ta.



~*************~
A bangaren nabeelah tana ajiye wayar safna ta shigo dakin zama tayi sannan ta fara magana, "shawara nake son baki a matsayina na 'yar uwarki"! Tasowa nabeelah tayi ta dawo kusa da 'yar uwar tata sannan tace ina saurarenki aunty safna, hannun ta safna ta kama sannan tace "a matsayina na 'yar uwarki ya dace na fada miki gaskiya, sannan nayi k'ok'arin kareki daga aikin da nasani da kuma nadama, dan muddin kika yarda kika *auri al'ameen* toh fah saikinyi da nasani da nadama dan babu abin da zaki samu a auren nasa sai tsiya da talauci, toh tun wuri ki farka daga naunauyan baccin da ya daukeki da kuma giyar soyayya da take dibanki.



Cikin firgici da tsananin mamaki nabeelah ke kallon 'yar uwar tata. sannan tace nagode, amma inason kisan cewa babu abin da zai hanani auren al'ameen sai dai idan dama allah ya rubuta shi din ba mijina bane, ko kuma idan allah ya dauki ran daya daga cikinmu kafin cikar burinmu, sannan aunty safna inason kisan cewa kece ya kamata ki farka daga naunauyan bacci ba niba, ki kuma dawo da hankalinki zuwa jikinki idan da hali har makaranta ki koma, dan naga kwakwalwar ki bata nuna miki dai-dai domin ni *talaka da me kudi* duk daya na daukesu, kuma na yarda da cewa allah yana tare da bawansa matuk'ar bawannan baiyi gaggawa ba sannan nasan allah yana azirta bawa alokacin da yaso idan yaso zai iya azirta al'ameen, daga k'arshe inason kisan cewa badan kyau ko kudi nakeson *al'ameen* a'a dan nasabarsa da addininsa nake sonshi.


Hannun safna ta kama sannan tace aunty safna inason kisan cewa,
_manzo allah (s.a.w)_ yace *""ana auran mace dan abubuwa huduโด 1dan kyanta 2dukiyarta 3nasabarta 4addininta. Sai manzon allah yace ka auri ma'abociyar addini zaka samu nutsuwa, hannunka zai albarka""*
Toh kinga kenan aunty safna shima mijin haka akeso ya kasance kuma soyayyar da aka ginata akan gaskiya bata taba lalacewa, sau da dama zakiga soyayyar da aka ginata akan wani abu ko akasa karya a cikinta bata dadewa sannan idan anyi aure saikiga ana samun matsala sosai, kinga kenan shima yana ba da babbar gudun mawa a *rayuwar auren mu* new book insha allah๐Ÿ˜๐Ÿ˜†๐Ÿƒโ€โ™€, dan haka dan allah aunty safna kicire tunanin nan a ranki, shiru sukayi dukkan su ko wacce da irin tunanin da takeyi a ranta.



Tashi safna tayi ta koma falo ta zauna tana tunanin maganganun 'yar uwar tata, tasan duk abin da nabeelah ta fada mata gaskiya ne toh amma ita gaskiya bazata iya rayuwar talauci ba, dan gaskiya tanason mijin da zata aura ya kasance me kudi wanda duk sati zasu dinga barin k'asar domin yawon bude ido sannan tanason ta dinga hawa manyan motoci kamar yadda abban su yake musu fatan samu.


```Hmmmm nikam nace safna kina ruwa tsumdum๐Ÿ˜๐Ÿ˜```




๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ๐ŸŒบ
_______________
*BAUCHIN YAKUBU*

""Sai lokacin da ya gani da idonsa auren mukeso sannan zai san *25yrs ba 15yrs* bane, saurin kallonta haseenah tayi, tace kamar ya?
Mubeenat tace kamar yadda nake fada miki inason aure, ko kadan babu san karatu a raina kamar aure, haseenah tace toh me zai hana muje mu samu hajiya babba mu fada mata, kallonta mubeenat tayi tace kinsan me kike fada kuwa? Toh idan baki saniba yau kisani hajiya babba itace ja gaba wajen dagewar sai munyi karatu.
Haseenah tace ya ilahi wannan wacce irin rayuwa su daddy sukeson muyi ne๐Ÿ˜•








*_MUJE ZUWA GUYS๐Ÿ˜_*











```JUST FOLLOW ME```



๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ๐Ÿ‘ญ

*'YA'YANAH*


Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment