Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

*(jarinah)*
👭👭👭👭




*NAH*
fauziyyah s madaki
*{autar kainuwa}*




```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI TARE DA NADAMA ME TSANANI```




*THIS BOOK IS NOT FOR SALE😘*



_more comments_
_more typing_





*بسم الله الرحمن الرحيم*




Wednesday
*05/02/2020*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

*dedicated this page to you munaya, love you my dear🥰😘💞💕*

╠S╣╠A╣╠D╣╠A╣╠U╣╠K╣╠A╣╠R╣╠W╣╠A╣ ╠G╣╠A╣

*Sister zubaidah*
🅐🅝🅓
*Broth Hussain 80K*



🅝🅞: *20 to 25*

*🙏🏼دعاءصلاةالاستخارة🙏🏼*


((قال جابر بن عبدالله رضى الله عنهما: كان رسول الله صلى الله عليه وسلم،يعلمناالاستخارةفي الأمور كلهاكمايعلمنا السورةمن القرآن، يقول: *((إذا هم أحدكوبالأمر فليركع ركعتين من غيرالفريضة،ثم ليقل:”اللهم إني أستخيرك بعلمك، وأستقدرك بقدرتك، وأسألك من فضلك العظيم، فإنك تقدر ولاأقدر، وتعلم ولا أعلم، وأنت علام الغيوب، اللهم إن كنت تعلم أن هذا الأمر----ويسمي حاجته----خيرلي في ديني ومعاشي وعاقبةأمري---- أو قال:عاجله وآجله----فاقدره لي ويسره لي،ثم بارك لي فيه،وإن كنت تعلم أن هذا الأمر شر لي في ديني ومعاشي وعاقبة أمري---- أو قال: عاجله وآجله----فاصرفه عني، واصرفني عنه، واقدرلي الخيرحيث كان، ثم أرضني به))*


وماندم من استخار الخالق، وشاور المخلوقين المومنين، وتثبت في أمره، فقد قال سبحانه: *{وشاورهم في ٱلأمى فإذا عزمت فتوكل على الله}* آل عمران:١٥٩.

*FASSARA*

*Addu'ar sallar istihara (neman zab'in allah idan mutum zai aikata wani abu).*

```jabir ibn abdullah, allah ya yarda da shi da mahaifinsa, yace: manzon allah, tsira da amincin allah su tabbata a gare shi, ya kasance yana koya mana yin istihara(neman zab'in allah) a cikin dukkan al'amura kamar yadda yake koya mana sura daga cikin al'k'ur-ani, yakan ce: "idan d'ayanku yayi niyyar yin wani al'amari to yayi sallah raka'a biyu,``` *ba ta farillah ba,* ```sannan yace: "ya allah! Ina neman zab'inka domin iliminka,kuma ina neman kabani iko domin ikonka, kuma ina rok'on ka daga falalarka mai girma; domin kaine mai iko, ni kuwa bani da iko, kuma kai ne masani, ni kuwa ban sani ba, kuma kai ne masanin abubuwan fake. Ya allah! Idan ka san cewa wannan al'amari``` *sai ka ambaci b'uk'atar taka* ```al'khairi ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da kuma k'arshen al'amarina``` *a wata ruwayar* ```da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - ka k'addara mini shi, kuma ka sauk'ak'e mini shi, sannan ka al'barkaceni a cikin sa. Kuma idan ka san wannan al'amari sharri ne gare ni a cikin addinina, da rayuwata, da k'arshen al'amarina -``` *a wata ruwayar* ```da magaggaucin al'amarina da majinkircinsa- ka kawar da shi daga gare ni, kuma ka kawar da ni daga gare shi, kuma ka k'addara min al'khairin a duk inda yake, kuma ka sanya ni in yarda da shi." ```


*duk wanda ya nemi zab'in mahalicci, kuma ya yi shawara da talikai muminai, kuma yayi azama a cikin lamarinsa, to ba zai yi nadama ba, domin allah madaukakin sarki yace: ("KUMA KA SHAWARCE SU CIKIN LAMARINKA, IDAN KUMA KA K'UDIRI ANIYA, TO KA DOGARA GA ALLAH ".)* _surah: ali-imran, aya:159_
____________________



🅝🅞: 2⃣0⃣

2⃣5⃣





"""Mubeenat tace rayuwar k'unci da takura mana, kafin haseenah tayi magana sai ga wata mata ta shigo dakin bakin ta dauke da sallama, amsawa suke sannan suka fara gaisheta, bayan ta amsa tace "kunata karatunne najiku shiru?.
Shagwa'be fuska mubeenat tayi zata fara magana, katse ta matar tayi tare da cewa yimin shiru kimsan banason k'orafe-k'orafenki, 'yar uwarki ta hak'ura amma ke har yanzu kin kasa gane halin daddyn ku na magana daya, shiru mubeenat tayi sai kuma ta fara hawaye tana fadin, yanzu mommy idan bakitsaya kin saurare ni, kinji matsala ta ba, toh wazai saurareni bare har ya bani shawarar da zataimin amfani.? Please mommy ki saurareni dan allah, ta hada hannayenta alamar rok'o👏🏼.


Juyowa matar tayi sai kuma 'yar tata ta bata tausayi zama tayi tana kallon 'ya'yan nata cike da so da k'auna, sannan tace "ina sauraron ki," sunkuyar da kanta mubeenat tayi, ta fara magana a hankali mommy wai meyasa daddy bayason mu kula samari ne, kuma me yasa yake musu korar kare idan sun zo? Bata bari ta ba ta amsa ba taci ga ba da cewa mommy ina tsoron abin da daddy yakeyi wallahi kar nan gaba azo ana zaginsa, kina ganin abin da yayiwa saif ranar nan, ni ina ganin mommy lokaci yayi da ya kamata daddy yasan soyayya baza ta hana karatu ba kamar yadda zaman aure baya hana karatu, amma wallahi hukuncin sa yanason ya shafi k'ima da martabar gidan nan.


Numfashi mommy ta sauke tana tunanin abin da mubeenat ta fada akwai k'amshin gaskiya a ciki, toh amma ita kanta bata san burin mijin nata akan 'ya'yan nasu ba, domin dai tasan yana da kudin da za'a iya sashi a sahun gaba-gaba na masu kudin bauchin, kuma ita kanta bata son abun da yakewa duk wani saurayi da yazo wajen yaran,
Kallon su mubeenat tayi tace "hak'uri zakuyi dan nasan yana da dalilin yin haka toh sai kuyi hak'uri har zuwa lokacin da allah zai sa ya sauko daga kan ra'ayin sa", sannan kuci gaba da kare mutuncin kanku da martabar wannan gida.

Sai lokacin ne haseenah tayi magana, tace insha allah mommy zamu kula.
Mommyn tace "toh allah yayi muku al'barka ya kareku daga dukkan abin k'i"

Suka amsa da ameen ya rabbi mommy.
Tashi tayi ta fito daga dakin ta tafi dakinta.



*WAI SHIN WAYE DADDY*

Asalin sunan sa *Ibrahim sani muh'd* dan asalin garin funakaye bajoga ne dake jihar gombe ne, su uku ne a wajen iyayen su, shine babba sai kuma k'aninsa alhaji lawan sai k'anwar su safiyyah, tun tashinsu babu abin da suka sani sai kiwo da tallen nono, ana haka har aka bude wata makarantar yaki da jahilci, allah yasa babansu ya amince da k'ar akasa k'anwarsu safiyyah.


Da yake safiyyah yarinya ce me basira sosai take mai da hankali wajen karatun, idan ta dawo gida kuma sai ta dauki tallan nono ta tafi, da dare idan sun fito dandali sai su koma gefe da k'anwar tasu safiyyah ta dinga koya musu karatun da akayi musu.

Bayan wani lokaci sai abokin malan sani ya bashi shawarar yasa yaran sa maza a makaranta ita kuma mace yayi mata aure tun kafin 'yan garin su fara cewa safiyyah ta girma a gida ta rasa mijin aure, da farko malam sani bai amin ce ba sai da yayi tunanin yadda akewa duk yarinyar da ta wuce shekara 12 batayi aure ba, dan har fita ma gagarar ta takeyi, hakan ne yasa malam sani saurin amincewa da shawarar aminin nasa jauro.
Bayan sati biyu malam sani ya samu safiyyah wacce suke kira da *ADDAH* _domin sunan yayar malam sanin taci_ yace addah dama zan shaida miki ne na cireki a makaranta,
Cikin tashin hankali tace "baffa dan allah kabarni na gama, uncle mai kyau yace zamu birni mu zana jarabawa kuma yace idan nayi kokari zai biyamin kudi da yawa naje birni nayi karatu," zama malam sani ya gyara sannan yace kinsan dai ruganar da yarinya ta wuce shekara sha biyu 12 za'a fara nunata batayi aure ba ko ki duba yarinyar can lamindo yanda ba dama ta fito yara zasu bita sunayi mata wak'a, yanzu shekarar ki goma danma allah ya baki jiki me kyau so kike kema a fara numaki mukuma adinga zaginmu?
Safiyyah tace toh ai baffa malamin mu yace mana kada muyi aure dan tsoron kar a takura mana, domin shi aure lokaci ne, kaga kenan baffa zan iya karatuna har zuwa lokacin da zan samu mijin auren sai na daina zuwa.



"""Shiru malam sani yayi ya tunanin ta inda zai billowa addan domin kuwa yasan ta da kafiya akan abin da takeso, chan dai ya nisa yace adda kiyi abin da nace miki, yana fadar haka ya fice a gidan, itama daki ta koma tasa kuka domin tun da yace haka tasan ya gama magana kenan.


Bayan sati biyu su iro da lawandi suka fara zuwa makaranta da akayi musu interview ba laifi sundanyi kokari dan haka akasasu a primary 6.

Bayan sati biyu safiyyah ta takura kanta da kuka amma malam sani yayi biris da ita, duk saurayin da yazo sai tak'i zuwa idan kuma baffan nasu yana gida sai ta fito ta yiwa mutum tas ta koma, tun abin na damun mahaifiyar su har ta zuba mata ido sai dai tana yi mata addu'a,.
Wata rana safiyyah ta dawo daga tallan nono ta hadu da malamin su, yana ganin ta yayi 'boyayyar ajiyar zuciya yace "safia dama kinanan kika daina zuwa makaranta? Me makon ta bashi amsa sai kuma ta fashe mishi da kuka, sosai hankalinsa ya tashi yace no safiyyah karkimin haka fad'amin me yafaru? Cikin kuka ta sanar mishi da yadda sukayi da baffa, cikin tashin hankali yace "yanzu yaushene bikin naki"? Tura baki tayi sannan tace nifah banason kowa😕
'Boyayyar ajiyar zuciya yayi sannan yace kar ki damu safiyyah zakiyi karatu sosai har sai kin zama doctor, cikin farin ciki tace da gaske uncle me kyau, sai da yayi dariya sosai sannan yace da gaske safiyyah me kyau, rufe idon ta tayi,
Kallon ta yayi yace kije gida zanzo na sami baffan namu, tace toh.


Tun da ya koma masaukin sa yake ta tunanin yadda zaiyi baban safiyyah ya barta tayi karatu, ya dade yana tunani amma bai samo mafita ba dole ya tashi yai alolar magrib ya tafi wajen da aka ware a matsayin masallaci.
Bayan an idar da sallah yana zaune yana azkar sai ya hango malam sani zai fita, tashi yayi da sauri ya k'arasa suka gaisa bayan sun gaisa yace baffa dama inason ka bani lokaci zanzo gida mu tattauna wata magana, malam sani yace toh ba damuwa muje yanzu, nan suka k'arasa malam sani ya shiga gida ya dauko tabarma suka zauna, sai da suka k'ara gaisawa sannan ya fara magana "sunana nuraddeen jamil ni haifaffen cikin garin gombe ne kuma anan na girma har na gama degree na aka turoni garin nan bautar k'asa, nine malamin ajin su safiyyah naga ta daina zuwa shine dazu muka hadu tace ancireta, shine nazo na rok'i alfarma dan allah baffa ka barta ta koma makaranta".
Numfasawa baffa yayi sannan yace: yaro bawai nak'i ta taka ba amma bari kaji...nan ya fad'a mishi komai akan rugar tasu, nuraddeen bai iya magana ba kawai sai yayiwa baffa sallama ya koma masauk'insa cike da sak'e-sak'e a ransa.




_JUST FOLLOW ME_



*MUJE ZUWA MY GUYS YANZU WASAN ZAI FARA😍🥰😘*




*duk wacce ta keson shiga group din 'ya'yanah jarina tamin magana ta wannan number👉🏽08064413906 idan kinsan bazaki comments ba, dan allah karki shigo*




_comments_
_vote and share_




*following me on wattpad and vote🙏🏼🙏🏼🙏🏼*






_COMMENTS_
_VOTE_
_SHARE_

👭👭👭👭

*'YA'YANAH*
*(jarinah)*
👭👭👭👭




*NAH*

*FAUZIYYAH S MADAKI*
*{autar kainuwa}*



*editing by shatuu❤*
(jakadiyar kainuwa)

```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI TARE DA NADAMA ME TSANANI```




*THIS BOOK IS NOT FOR SALE😘*



_more comments_
_more typing_



*following me on wattpad and vote.*
*_name: fauxeey201_*




*بسم الله الرحمن الرحيم*


Friday
*07/02/2020* *____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



*╠S╣╠A╣╠D╣╠A╣╠U╣╠K╣╠A╣╠R╣╠W╣╠A╣ ╠G╣╠A╣*

*Sister zubaidah*
🅐🅝🅓
*Broth Hussain 80K*



🅝🅞: *25 to 30*






*😴 أذكار الاستيقاظ من النوم*😴


*😴ADDU'O'IN TASHI DAGA BACCI😴*



*"الحَمْدُ لله الذِي أَحْيَانَا بَعْدَ مَا أَمَاتَنَا وَإِلَيْهِ النُّشُور"*

```Dukkan yabo ya tabbata ga allah wanda ya rayar da mu bayan ya dauki rayukanmu, kuma zuwa gare shi tashi yake.```



*Annabi, tsira da amincin allah su tabbata a gare shi, yace: Wanda ya farka da daddare ya ce:👇🏼*
*لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللّهُ وَحْـدَهُ لاَ شَـرِيكَ لَهُ، لَهُ الْمُلْـكُ وَلَهُ الْحَمْـدُ، وَهُوَ عَلَى كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرٌ، سُـبْحَانَ اللهِ، وَالْحَمْـدُ ِللهِ ، وَلاَ إِلَهَ إِلاَّ اللهُ وَاللهُ أكْبَرْ، وَلاَ حَوْلَ وَلاَ قُوّّةَ إِلاَّ بِاللَّهِ الْعَلِيِّ الْعَظِيمِ. رَبِّ اغْفِرْ لِي.*

```"Babu abin bautawa da gaskiya sai allah, shi ka'dai, babu abokin tarayya a gare shi; mulki da yabo nasa ne, kuma shi mai iko ne akan komai.```
```Tsarki ya tabbata ga allah, kuma dukkan yabo ya tabbata ga allah, babu abin bautawa da gaskiya sai allah, kuma allah shi ne mafi girma, kuma babu dabara babu k'arfi sai na allah, mad'akaki, mai girma. Ya ubangijina! Ka gafarta mini."```

_Wanda ya fad'i wannan za'a gafarta masa, idan kuma ya yi addu'a za'a amsa masa, idan kuma ya tashi ya yi alwala, ya yi sallah za'a kar 'bi sallarsa._



*"الحَمْدُ لله الذِي عَافَانِي في جَسَدِي، ورَدَّ عَلَيَّ رُوحِي، وأَذِنَ لي بِذِكْرهِ"*

```"Dukkan yabo ya tabbata ga allah, wanda ya ba ni lafiya a jikina, kuma ya dawo mini da raina, kuma ya ba ni iznin ambatonsa".```



*إِنَّ فِي خَلْقِ السَّمَاوَاتِ وَالأَرْضِ وَاختلْفِ اللَّيْلِ وَالنَّهَارِ لآيَتٍ لِّأُوْلِي الألْبَبِ(١٩٠) الَّذِينَ يَذْكُرُونَ اللّهَ قِيماً وَقُعُوداً وَعَلَىَ جُنُوبِهِمْ وَيَتَفَكَّرُونَ فِي خَلْقِ السََّموَتِ وَالأَرْضِ رَبَّنَا مَا خَلَقْتَ هَذا بَطِلاً سُبْحَنَكَ فَقِنَا عَذَابَ النَّارِ(١٩١) رَبَّنَا إِنَّكَ مَن تُدْخِلِ النَّارَ فَقَدْ أَخْزَيْتَهُ وَمَا لِلظَّلِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ (١٩٢)رَّبَّنَا إِنَّنَا سَمِعْنَا مُنَادِياً يُنَادِي لِلإِيمَنِ أَنْ ءامِنُواْ بِرَبِّكُمْ فامَنَّا رَبَّنَا فَاغْفِرْ لَنَا ذُنُوبَنَا وَكَفِّرْ عَنَّا سَيِّئَاتِنَا وَتَوَفَّنَا مَعَ الأبْرَار(١٩٣) رَبَّنَا وَآتِنَا مَا وَعَدتَّنَا عَلَى رُسُلِكَ وَلاَ تُخْزِنَا يَوْمَ الْقِيَمَةِ إِنَّكَ لاَ تُخْلِفُ الْمِيعَادَ (١٩٤) فَاسْتَجَابَ لَهُمْ رَبُّهُمْ أَنِّى لاَ أُضِيعُ عَمَلَ عَامِلٍ مِّنكُم مِّن ذَكَرٍ أَوْ أنثى بَعْضُكُم مِّن بَعْضٍ فَالَّذِينَ هَاجَرُواْ وَأُخْرِجُواْ مِن دِيَرِهِمْ وَأُوذُواْ فِى سَبِيلِى وَقَتَلُواْ وَقُتِلُواْ لأُكَفِّرَنَّ عَنْهُمْ سَيِّئَاتِهِمْ وَلأُدْخِلَنَّهُمْ جَنَّتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الأَنْهَرُ ثَوَاباً مِّن عِندِ اللّهِ وَاللّهُ عِندَهُ حُسْنُ الثَّوَابِ (١٩٥)لاَ يَغُرَّنَّكَ تَقَلُّبُ الَّذِينَ كَفَرُواْ فِي الْبِلَدِ (١٩٦)مَتَعٌ قَلِيلٌ ثُمَّ مَأْوَىهُمْ جَهَنَّمُ وَبِئْسَ الْمِهَادُ (١٩٧)لَكِنِ الَّذِينَ اتَّقَوْاْ رَبَّهُمْ لَهُمْ جَنَّتٌ تَجْرِى مِن تَحْتِهَا الأَنْهَرُ خَلِدِينَ فِيهَا نُزُلاً مِّنْ عِندِ اللّهِ وَمَا عِندَ اللّهِ خَيْرٌ لِّلأَبْرَارِ (١٩٨) وَإِنَّ مِنْ أَهْلِ الْكِتَبِ لَمَن يُؤْمِنُ بِاللّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْكُمْ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْهِمْ خَشِعِينَ لِلّهِ لاَ يَشْتَرُونَ بِآيَتِ اللّهِ ثَمَناً قَلِيلاً أُوْلَـئِكَ لَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ إِنَّ اللّهَ سَرِيعُ الْحِسَابِ (١٩٩) يأيُّهَا الَّذِينَ آمَنُواْ اصْبِرُواْ وَصَابِرُواْ وَرَابِطُواْ وَاتَّقُواْ اللّهَ لَعَلَّكُمْ تُفْلحون.*

```"Hak'ik'a a cikin halittar sammai da k'assai, da sa'bawar dare da rana, lallai akwai ayoyi ga ma'abota hankula. (Su ne) wad'anda suke ambaton allah a tsaye da kuma a zaune da kuma a kishingid'e, suke kuma tunani a kan halittar sammai da k'assai (suna cewa): "Ya ubangijinmu!! Ba ka halicci wannan abu a banza ba. Tsarki ya tabbata gare ka, ka kiyashe mu azabar wuta. Ya ubangijinmu!! Hak'ik'a kai, duk wanda ka shigar da shi wuta, babu shakka ka kunyata shi. Azzalumai kuwa ba su da wasu mataimaka. Ya ubangijinmu!! Hak'ik'a mu, mun ji mai kira yana kira zuwa ga imani, cewa: "ku yi imani da ubangijinku". Sai muka yi imani. To, ya ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu, ka kuma kankare mana miyagun aiyukanmu, ka kuma kar'bi rayukanmu tare da mutane na gari. Ya ubangijinmu! Ka ba mu abin da ka yi mana alk'awari da shi a kan harshen manzanninka, kada kuma ka kunyata mu ranar alk'iyama. Hak'ik'a kai ba ka sa'ba alk'awari". Sai ubangijinsu ya amsa musu (cewa): "Hak'ik'a ni ba zan tozarta aikin wani mai aiki ba daga cikinku, namiji ko mace; sashinku daga sashi yake. To, wadanda suka yi hijira, aka kuma fitar da su daga gidajensu, aka cuce su saboda Ni, suka kuma yi yak'i, kuma aka kashe su, lallai zan kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lallai zan shigar da su aljannatai wad'anda k'oramu suke gudana ta k'ark'ashinsu; (wannan) sakamako ne daga allah. Allah kuwa a wurinsa kyakkyawan sakamako yake. Kada kai-koman wad'anda suka kafirta a cikin garuruwa ta rud'e ka. Jin dad'i ne d'an k'ank'ani; sannan sakamakonsu wutar jahannama ce, tir da wannan makwanta. Amma wad'anda suka ji tsoron ubangijinsu, suna da aljannatai wad'anda k'oramu suke gudana ta k'ark'ashinsu, masu dawwama a cikinsu; wannan liyafa ce daga wajen allah; abin da kuwa ya zo daga wajen allah shi ya fi ga managarta. Kuma hak'ik'a akwai daga ma'abota littafi wanda yake yin imani da allah da abin da aka saukar zuwa gare ku, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu k'ank'an da kai ga allah, ba sa musanya ayoyin allah da d'an tamani k'ank'ani. Wad'ancan suna da ladansu a wurin ubangijinsu. Hak'ik'a allah mai hanzarta hisabi ne. Ya ku wad'anda suka yi imani! Ku yi hakuri, kuma ku rinjayi kafirai a cikin hak'uri, kuma ku yi zaman dako, kuma ku ji tsoron allah ko kwa rabauta.``` Sarah: ali-imran, aya: 190 zuwa k'arshen surar.

___________________



🅝🅞: 2⃣5⃣

3⃣0⃣




"""Tun lokacin da nuraddeen ya koma d'akinsa yake tunanin yadda zai 'billowa al'amarin, haka ya raba dare yana ta tunani, amma bai samo mafita ba, domin dai yasan baffa ba zai dauki 'yar sa ya bayar da ita ga mutumin da bai sanshi ba, da haka ya yi addu'ar bacci ya kwanta.


Bayan kwana biyu da uncle Nura ya rasa mafita, shi kuma yana tausayin safiyyah tare da k'aunar ta, sai kawai ya hada kayan shi ya koma gombe, bayan ya huta ya sami mahaifiyarsa da maganar safiyyarh, bai 'boye mata komai ba, ya sanar da ita da k'udirin sa na auren safiyyarh.
Da farko tak'i amincewa, sai da yayi ta rok'onta tare da nuna mata taimako za suyi, sannan tace:
" Na amince, amma da sharadin sai dai ta zauna a wajena"

Nuraddeen yace

" Dama wallahi ummi wajenki za ta zauna, tunda ga salma ita ma kamar salman take."

Ummi tace:

"Toh bari Alhajinku ya dawo za muyi maganar dashi"

Godiya yayi ma ta sannan ya koma part d'in sa.

Lokacin da alhajin ya dawo bayan yaci abinci, ya huta, ummi ta zo mishi da maganar d'an nasu, yadda su kayi da nuran ta fad'a mishi; da yake mutum ne mai sauk'in kai, bai musa ba, fatan alkhairi ya yi musu tare da addu'a.



""""Bayan sati biyu, Alhaji Jamilu da k'aninsa Alhaji Abdallah sai abokin sa Allhaji Aminu, suka shirya bisa jagorancin Nurraddeen, suka tafi funakaye bajoga, daga can ma akwai tafiya me d'an nisa kafin a je *wuri kesa*, sosai su ka samu tarba, alola su kayi dan lokacin har azahar ta gota, bayan sun idar da sallar, sai suka samu an kawo mu su lafiyayyen kindirmo (nono), sunji dad'i sosai da tarbar da suka samu, bayan sun gama ne suka buk'aci ganin baffa da 'yan uwansa, gaisawa su kayi cikin mutunta juna, sannan alhaji aminu ya fad'i buk'atar su ta son had'a zuri'a da su.
Da farko baffa ya k'i amince wa, har sai da sarkin wuri kesa ya sa baki, sannan baffa ya amince, nan dai suka ba da komai na neman aure, har da sadaki, sannan su kayi sallama akan nan da sati biyu za'a daura auren.



"""A 'bangaren safiyyarh kam ba tasan me yake faruwa ba 'yan uwanta dai su ilu sun sa ni amma baffa ya ce kar su fad'a ma ta; ita dai safiyyarh kawai ta ga baffan nata ya dai na cewa sai ta fita idan samari sun zo wajen ta, ba kamar da ba, nan ta fara murnar za ta koma makaranta, amma kuma yanzu bata ganin uncle mai kyau.


Bayan su Alhaji sun dawo, ya bawa ummi labarin komai, nan ummi ta fara kiran duk wanda ya dace a sanarwa da maganar bikin.


Bayan sati d'aya, ya rage biki saura kwana bakwai, ta kowanne 'bangare shiri ake yi, duk da ba wani taro ummi za tayi ba; amma ba laifi har 'yan uwa sun fara zuwa.
Ango kam yasha tsiya wajen abokan sa, wai kyau ya bi, dole suje su ga wannan big girl din da ta sace zuciyar shi.


_nikam na ce k'waila dai🙊😆😝_



"""A yau ne mutane da dama suka sheda daurin auren *Nuraddeen Jamil* da amaryar sa *safiyyarh sani* a bisa sadaki mafi daraja,😍 sosai rugar ta kesa ta cika ansha kindirmo (nono) sosai, sai dai fatan allah ya ba su zaman lafiya.


Bayan an watse ya rage sai ango da abokan sa, nan suka shiga suka gaida iyayen amarya, sun so ganin amarya amma aka hana, dole suka hak'ura akan ai za su ganta idan ankawo ta😆.


""Da daddare mahaifiyar safiyyarh ta zaunar da ita, tana ma ta nasiha, " adda ina so ki nutsu sannan kiyi hakuri da sabuwar rayuwar da ki ka shiga domin duk wacce tai aure ta shiga sabuwar rayuwa ne, zaki koma wajen da ba ki da kowa sai mijinki, za ki fara rayuwa da mutanen da ba ki saniba, amma da sannu za ki saba idan kinyi hakuri", sosai ta yi mata nasiha, haka ma baffa ya yi mata, tare da samata albarka.
Sosai safiyyarh ta ke kuka, da fargabar waye mijin? Bata da me bata amsa dan haka ta hak'ura ta kwanta.



Washe gari aka kawo motoci guda biyu na daukar amarya, haka suka cika motocin, sai cikin garin gombe; a part d'in nuraddeen aka sauke amaryar, bayan 'yan kawo amarya sun huta sunci abinci aka mai da su, tare da yi mu su alkhairi mai yawa.


Bayan tafiyar su abokan nuraddeen suka rakoshi, part d'in ummi ya kaisu suka gaisa sannan suka fito, suna fitowa yace toh na sallameku sai da safe.
Hada baki sukai suna fad'in *durun uwa(salatin arna)*🙊😆 wallahi sai mun ganta, d'an iska kawai🤣🤣🤣

Da gudu ya wuce ya kulle k'ofar yana fad'in idan ta girma kwa ganta amma yanzu nasan zagi zansha a wajen ku.
Sai da ya saita nutsuwarsa sannan ya shiga dakin da sallama, bakajin komai a dakin sai shashshek'ar kukan ta, k'ara sawa yayi da sauri ya d'ago ta yana tambayar ta lafiya?
Cikin kuka tace shikenan uncle sun rusamin mafarkina, a'a safiyyarh zakiyi karatu insha allah, kinsan waye mijin naki?
Kai ta girgiza alamar,

A'a

Kafin yayi magana wayarsa ta fara k'ara dauka yayi, ummi ce, tace ka kawomin 'yata, kafin yayi magana ta yanke wayarta. Murmishi yayi sannan,
Yace: tashi na kaiki wajen ummin ki, har ya juya, tace uncle me kyau, juyowa yayi yace safiyyarh me kyau.
Tura baki tayi tace baka fad'amin ba, yace me? Waye mijin, au kinason sanin sa?

Eh tace a tak'aice, yace "uhm kawai dai kisa a ranki auren ba saki domin yafi na zobe, da haka suka k'araso part din ummi.

Satin safiyyarh biyu a gidan ta fara zuwa makaranta, j.s one aka sa su tare da salma, sosai ummi ta ke k'aunar safiyyarh a ranta, kuma ba ta nuna ban-banci tsakanin ita da salma, haka ma salman tana k'aunar safiyyarh, Lamar Da ma sun dade da sanin juna.


Watan safiyyarh uku a gidan Nuraddeen ya gama bautar k'asar shi (n y n c) ya fara shirye-shiryen tafiya k'aro karatu.



*Muje zuwa my guys, haryanzu muna cikin labarin mu, masu tambaya ina abba kar ku damu mu hadu a next page.😍😍*






*_JUST FOLLOW ME_*






*Maison shiga group din 'YA'YANAH JARINA👉🏽08064413906 idan kinsan bazaki comments ba karki shigo, pls female only*


_Comments_
_Vote n share_

👭👭👭👭

*ƳAƳANAH*
*(jarinah)*
👭👭👭👭




*NAH*

FAUZIYYA SALEH MADAKI
*{autar kainuwa}*





```LABARINE DA YAKE TATTARE DA KWADAYI, SON ZUCIYA, DOGON BURI TARE DA NADAMA ME TSANANI```





*THIS BOOK IS NOT FOR SALE😘*




_more comments_
_more typing_



*Following me on wattpad and vote.*
*Name: fauxeey201*


*بسم الله الرحمن الرحيم*



Friday.
*14/02/2020*
*____________________________________*


*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*



*╠S╣╠A╣╠D╣╠A╣╠U╣╠K╣╠A╣╠R╣╠W╣╠A╣ ╠G╣╠A╣*

*Sister zubaidah*
🅐🅝🅓
*Broth Hussain 80K*




🅝🅞: *30 to 35*


*(( أذكـــــــار الــنـــــوم ))*



*أعوذ بالله من الشيطان الرجيم*
*🌙 بســـــم الله الرحـــمن الرحـــيم 🌔*

*{اللَّهُ لَا إِلَٰهَ إِلَّا هُوَ الْحَيُّ الْقَيُّومُ ۚ لَا تَأْخُذُهُ سِنَةٌ وَلَا نَوْمٌ ۚ لَّهُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۗ مَن ذَا الَّذِي يَشْفَعُ عِندَهُ إِلَّا بِإِذْنِهِ ۚ يَعْلَمُ مَا بَيْنَ أَيْدِيهِمْ وَمَا خَلْفَهُمْ ۖ وَلَا يُحِيطُونَ بِشَيْءٍ مِّنْ عِلْمِهِ إِلَّا بِمَا شَاءَ ۚ وَسِعَ كُرْسِيُّهُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۖ وَلَا يَئُودُهُ حِفْظُهُمَا ۚ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْعَظِيمُ}*
📚 صحيح البخاري

🌺 🌺 🌺 🌺 🌺

*بســـــم الله الرحـــمن الرحـــيم*

*{آمَنَ الرَّسُولُ

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment