Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ne Sarki ya ce in su na biye da shi za su iya zama fada, in kuwa ba haka ba ya na mai d’aure su har sai hakin masarauta ya cimma ruwa, dan babu damar korar su daga fada su na amintattun Hadiman sarki, surrin fada babu wanda ba su sani. Da wannan su ka ja bakin su su ka yi shiru, su na mai Allah wadar da wanda ya bawa Sarki wanga shawara, dan kuwa Sarki idanu ya rufe madafa kawai ya ke nima, ya kuma sami bahaguwar madafa mai wuyar 6ullewa sai dai fa Allah shi kyauta da aikin dana sani.


Bintu na gyaran gadon Gimbiya Binta, ita kuma Gimbiyar na daga kishingid’e bisa tin tin ana mata danna. Sai ga Jakadiya ta shigo jiki na rawa daga gani kasan da magana a bakin ta. Bayi na ta gaishe ta, haka ma Bintu wacce tun shigowar Jakadiya ta ga ta kafe ta ido. Jakadiya na mai duban Bintu ta ce "ko da ban sani ba ke an Bintu’’

Gaban Bintu ne ya fad’i yayinda ta zube k’asa ta na mai fad’in ‘’Allah ya huci zuciyar Jadiya, Bintu na ke ba ki 6ata ba’’
Kallan ta ta ke cikin nazari, kafin ta juya ta dubi Gimbiya Binta, gudun kar sauran bayi su gane sakon da za ta fad'wa Gimbiya, sai cewa ta yi
‘’ta kan kwaba, ta kan kan ta, ta kan akwati mai taya, sai sid’if ta fad’a, sai sid’if na d’auka’’

Jin haka Gimbiya Binta ta saki k'awataccen murmushi, dama abun da ta ke jira kenan, kana ta ce
"zannuwa ishirin sun yi kad’an, aradu na k’ara mi ki goma har da kallabi goma’’
Jin haka Jakadiya ta rangwad’a gud'a ta na mai fad’in ‘’yaro wake tab'a mai uwa? Ba zai ci ba kayan kasuwa, sai ni Hindu jikar Baba Kilishi Jikar Nana, godiya na ke Gimbiya’’
Kana ta kai kallan ta ga Bintu ta ce "biyo ni yarinya’’

Gaba Bintu na fad’uwa duk dai ba ta fahimci zancen na Gimbiya da Jakadiya ba, ta bi bayan Jakadiya. Ganin haka wata Baiwa mai kaiwa Yerima Nuhu duk wani labari na game da lamarin Bintu ita ma ta ja kafar ta zuwa neman Yarima Nuhu, dan kuwa dai ita ma ba ta gamsu da wannan lamari ba.

Bintu na tafe bayan Jakadiya, ganin in da su ka dosa gaban ta sai faduwa ya ke, musammam da ta ga sun doshi turakar Sarki gadan gadan. Nan su ka tadda Sarki tare da Waziri da Hadimai, bayan su babu wani mahalik’i da ke wajan face amintaccen bawan sarki wanda ake kira Nahana. A bakin kofar turaka Bintu ta kasa d’aga k’afa ta shiga dan tsoro da kwarjini, tun da aka haife ta ko harabar wajan ba ta tab’a shiga ba, bare ace turakar sarki, ga ta ga sarki. Sai da Jakadiya ta d’an jawo ta, na mai mai mata shune da baki ta shiga.

Ganin ta gaban Sarki tuni ta zube k'asa ta na mai kwasar gaisuwa. Yau ga Bintu ga Sarki da waziri har da Hadimai, ko shakka babu dole k'awarta Cangwai ta ji wannan labarin.

Sarki zaune ya hakimce cikin rawani, ya dubi Jakadiya ya ce ‘’ba mu tarihin wanga d’iya’’

Zama Jakadiya ta gyara, kafin ta ce ‘’Allah ya ja daran Babban bijimi, wanga d’iya sunan marigayiya Baba Kilishi ta ci, hakan tsirar haihuwar ta da Gimbiya k’arama kwana d’ai ta, tare su ka tasa da Gimbiya k’ara, dad'in dad’awa makarantar su d’aya, bambacin su d’aya, wanga dai baiwa ce, kuma d’yar bayi, diya ce gun uwar bayi da kuma wannan bawa da ake kira Bala, eh Mahuta ba ,aradu ma kuwa’’

Waziri ya dubi Jakadiya ce ‘’ai fad'uwa ya zo daidai da zama, uban ta shi an babban bawa nai, ya ta ke da suna?’’

‘’Fatima, amma Bintu aka ce mata, kamar yanda ake kiran Gimbiya k'arama Binta’’ ta bashi amsa a takaice. Ita dai Bintu ta na nan kai durkushe daga can gefe amma daga tsakiya da ke ba shakka turakar ba dai girma ba, na gaske ma kuwa. Ko kwakkwaran motsi ba ta iyawa, bare ta d’an d’aga ido gudun kar ta had’a ido da Sarki, dan karshen kwarjini ya mata a yau da ta ke ga ta gashi.

‘’Fatima’’ muryar Sarki ta ji ya daki kunnan, tuni ta k’ara nutsuwa ta na mai rusunar da kai kamar wacce za ta shige k’ark’ashin k’asa. Ba mafarki ta ke ba, sarki da kan sa ya kira sunan ta, ina ma Cangwai ta na nan ta gani da idon ta, dan Idan ta ba ta labari sai ta ce k’arya ta yi.....tunanin da ta ke cikin ran ta kenan, jin Sarki ya ce
‘’a matsayin ki na baiwa a gare mu, shin akwai umarnin da za mu ba ki ki bi?’’
Bintu ta yi saurin duk’ar da kai ta ce "tir da bawan da bai bin maganar uban gidan sa, zan bi umarnin Mai martaba, ko da kuwa hakan zai zama sanadin rasa rai na, kwankwatsi ma kuwa’’

Kwalla na kad’ai Hadiman nan biyu ba su zibdawa Bintu ba, shi kuwa Waziri kai ya shiga kad’awa cike da gamsuwa, bare Jakadiya da ta ke ji kamar ta sab’a Bintu a baya tai ta rawa, Allah dai ya kawo mata tsuntsu daga sama gashesshe. Sarki na mai nazarin Bintu na wani d’an lokaci, daga bisani ya ce za ta iya tafiya. Ta na mai godiya ba tare da ta san abun da ake kullawaba ta fita.

Bayan tafiyar ta Sarki ya ce ya gamsu da komai na ta, amma ya na so Jakadiya ta sa ido kan ta na wani d'an lokaci kafin su gama zartar da hukunci. Da haka da haka har su ka wuce zaman fada.

Da yammacin ranar gaba d’aya walwalar Gimbiya K’amariyya ya dawo. Bintu na zaune gaban ta tana yanke mata farce wayar gida da ke aje d’akin ta ya fara k’ara. Cikin farin ciki ta d’aga, ganin haka Bintu ta tashi da niyar ba ta waje, amma Gimbiya K’amariyya ta d’aga mata hannu alamar ta yi zaman ta.

Maganar da Gimbiya ke fad’awa Yarima Barde ne ya bawa Bintu mamaki, ji ta yi ta na fad’in ‘’Takawa dai ya yanke hukumcin aurar da kauna ta Binta ga Mai Martaba Sarki na Fabarusa...’’

Gaba d’aya jikin Bintu yayi sanyi, cikin ran ta tausayin Gimbiya Binta ta ne ya kama ta, har fad’i ta ke
"Allah sarki Gimbiya ta ceto rayuwar ‘yar uwar ta, yanzu na gane dalilin maganar da sarki ya min, wato ina d'aya daga cikin bayin da za’a tura tare da Gimbiya Binta, kaiconi Bintu karatun mu kuma shikenan’’

Tausayin Gimbiya da ita kan ta shi ya gajiyar da ita ranar, ta kasa ta6uka komai har dare yayi ta koma gida.

Suna cin abinci da Inna, yau sun sami sauran biski daga gidan Sarki. Baba ya shigo babu sallama sai surutai ya ke kamar mahaukaci saban kamu, fad’i ya ke
‘’ta na ina ne wai ma?’’ ganin su a tsakar gida ya ja ya tsaya ya na mai fad’in
'’yo to ashe ku nan kusa ma’’

Inna ta yi kasake kafin ta ce ‘’Hallo Malam Lifiya? Yau ko sallamar babu?’’
‘’sallamar kenan ai uwar matar sarkin Fabarusa’’ cewar Baba ya na mai duban Bintu da sai saka lomar biski ta ke, hannu baka hannu kwarya. Inna na murmushin jin maganar Baba, ta ce ‘’Malam yau kuma raha a ke ji?’’

Cikin jadadawa Baba ya ce ‘’yo to wani raha bayan yanzu waziri ke sheda min, nan da d’an kwanaki za a tura a tsaida ranar bikin Gimbiya Bintu’’ ya k’arasa maganar ya na mai washe baki wanda daga Inna har Bintu sun kasa gane manufar dariyar ta sa.

Inna ce ta ce ‘’ayyo, Gimbiya Binta ko? Ai yanzu haka maganar da mu ke kenan, Wallahi yanzu ta ke sheda min’’

Baba na mai duban Bintu ya kai mata dak’uwa ‘’ungo nan yar jakar uba!’’ baki cike da biski Bintu ta tsaya ta na duban Baba. Ganin haka Inna ta ce "Allah sarki, aradu ba munahinci ta yi ba, hira ce ta kawo maganar....’’

Cikin k’ulewa Baba ya ce ‘’yo to na gaji da wannan rashin fahimta ta ki Yagana, gide ina nuna mi ki annabi hallo ki na runtse ido, wannan(ya nuna Bintu da yatsa) ita za a amrar ga Sarki Abdulrahman na Fabarusa a matsayin d’iyar Sarki....’’ tuni Bintu ta kwarai, ta wanke Inna da biskin bakin ta tsabagen tari.



🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.



©Khadija Sidi.....✍🏼


1⃣7⃣




Inna na mai rafka salati gami da dafe k’irji ta ce
‘’lahaila haillallahu mahammada rasulilahi! Bintu kuma Malam? Me ya had’a Bintu da masarautar Fabarusa saboda Allah da manzan sa? Yo to da haka a d’au wuk’a a da6a mana sai mu san kashe mu ake son yi da hujja!’’

Baba na mai nuna Bintu da d’an yatsa wacce ta ke hawaye d’aya na bin d’aya ya ce
‘’ga ta ga ki nan dai shegen biko’’

Kuka Inna ta sa yayinda ta rungumo Bintu ta na fad’in
‘’bar kuka Bintu, bar kuka d’iyar arziki, addua shi ya kamata mu yi, innalillahi wainna ilaihiraji’un’’

Ganin haka Baba ya sa kai ya fice ya na mai fad’in
‘’kwa dai k’araci munahuncin ku, bakin alk’alami ya bushe’’

Ranar sam Bintu ba ta sami bacci ba, kwana ta yi ta na kuka. Shi kan shi yayan ta Habibu ya tausayawa Bintu, zai ji dad’in zama yayan matar sarki, amma kasancewar auren hatsari ne ya sa shi girgiza da juyayin abun.

Washagari da ciwan mara Bintu ta tashi, kasancewa al’adar ta ta sake dawowa, ga kuncin zuci da ya addabi rayuwar ta ya sa gaba d’aya ta fita daga hayyacin ta. Ji ta ke dama motar bayi sun tafi sun bar ta a makaranta, in ya so Aisar ya tafi da ita ta huta da wannan rayuwa mara ‘yanci. In kuwa ta tuna shikenan fa ba ita ba komawa makaranta, ita da Aisar sai dai ta hange shi a akwaitin talabijin idan Allah ya sa an nuna shi sai ta k’ara saka wani kukan har da shasshek’a. Ko damar shiga babban gida ba ta samu ba, haka kuma daga Gimbiya K’amariyya har Gimbiya Binta babu wanda ya bi ta kan ta. Musamma Gimbiya da buri ya cika.

Ranar sarki ya tara iyalen sa a turaka bayan Jakadiya ta tabbatar ma sa da inganci da ilimin Bintu akan sarauta kasencewar ta tashi gidan sarauta, wanda su ke da yak’inin lamarin da aka k’ulla zai daidaita ba tare da an sami akasi ba.

Zaune suke gaban Sarki, Hajja Kilishi ce zaune ta 6arin dama, kusa da ita Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ne zaune. Sai Uwar fada da kuma Inna Salti, kusa da ita autan ta Yarima Nadir ne zaune daga 6arin hagu. Gaban su kuma ‘ya’yan Sarki ne maza, ciki har da babban d’an sa, dokajin Sa’ayra sa wato Yarima Inuwa, kusa da shi Yarima Nuhu ne. Sai kuma daga can gefe Yarima Hassan da Yarima Hussaini, Yarima Hamza, Yarima Abdallah da kuma Yarima Ahmadu su ka yi na su dairar.

Jin batun na Sarki, idan aka d’auke Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta da dama ita ta kulla k’ulalliyar babu wanda be girgiza ba. Yarima Inuwa ne ya duk'ar da kai kana ya ce
‘’Allah shi ja da ran Sarki, shin an zatar da hukunci ne ko kuwa ana buk'atar shawara daga iyalan Mai Martaba?’’

Sarki na mai duban sa ya ce
‘’mun gama yanke hukunci, amma jin ta bakin ku ba laifi ba ne’’

Jin haka sai Yarima ya ce
‘’Allah shi kyautata lamarin Babban biji, komai ku ka zartar daidai ya ke, ina ga zai fi kyau a duba lamarin nan saboda gaba, ran Mai Martaba ya dad’e’’

‘’Allah ya ja zamanin Takawa, ni ma dai hakan zance, dan kuwa gaban ya fi baya yawa, muddin ba za mu iya yin yanda su ka tambaya ba, zai fi kyau a yi watsi da maganar gaba d’aya in ya so sai mu nemi taimako wani wajan daban ko kuwa a amra masa K’amariyya yanda ya buk’ata’’

Inna Salti ce ta ara ta yafa, dan kuwa kusan ta fi kowa jin d’acin maganar cikin matan Sarki, hakan ya sa ta kasa yin shiru. Tun da ta fara maganar Gimbiya K’amariyya da Gimbiya Binta ke hararar ta ta wutsiyar ido. Shi kuwa Yarima Nuhu tun da aka fara maganar ya ke son furta abun da ke ran sa, jin Yarima Inuwa tare da Inna Salti sun share masa fage be yi k’asa a gwuiwa ba ya ce

‘’Ran ka shi dad’e, ka gafarce ni, amma ni a nawa wautar wannan lamari ba shi ne mafita ba, shin ya za mu yi a warware wannan sak’ar idan har aka kulla? Menene makomar wannan baiwa idan Allah ya sa Masarautar Fabarusa su ka gano wannan lamarin? Menene mazaunin wannan Masarauta ta mu? Shin gaba ake san kawarwa ko kuwa wata gabar ake san kullawa? Wannan tunani ya sa na yarda da Inna Salti, mu yi yanda Masarautar Fabarusa ta buk’ata ba tare da wani sark’akk’iya ba, ko kuwa zai fi kawai mu hakura da batun gaba d’aya in ya so mu nemi taimako a wata Masarautar ko ma Gwamnatin tarayya duk da dai shugaban k’asa be da lafiya, da lafiya ya ke na san da ba a kai ga haka ba, kuma ba za a rasa wanda zai duba wanga lamari ba’’

Ko da Yarima Nuhu ya dasa aya, Gimbiya Binta ji ta yi kamar ta kurma ihu, ita kuwa Gimbiya K’amariyya har ta fara kwalla ganin Yarima Nuhu na neman dawo da gaba baya. Shiru ya biyo baya. Har sun fitar da rai da k'ara jin maganar Sarki, daga bisani ya numfasa ya na mai duban Hajja Kilishi ya ce

‘’wani shawara za mu ji daga gare ki? Shin kin amince mu aurar da d’iyar mu ga abokan gaba ko kuwa mu sake neman taimako wanda hakan jinkiri ne wanda ya ke barazana ga rayukan talakawan mu?’’

Hajja Kilishi na mai nusar da kai cike da kissa ta ce
‘’lafiya toya matsafa, lafiya waliyin Allah, lafiya baya goya marayu, lafiya adali! Hukuncin ka daida ta Saka Takura, mun ji mun kuma amince’’

Sarki na mai nuna jin dad’i da batun Hajja Kilishi, haka ya bi sauran iyalan sa kowa na fad’in na shi albarkacin bakin. Duk da Sarki ya san Su Inna Salti, Yarima Inuwa da Yarima Nuhu sun fi gaskiya, sai ya bi san ran sa tare da kafa hujjar an rinjaye su, dan haka maganar ta tsaya. Da wannan su ka watse kowa da abun da ya ke sak’awa cikin ran sa. Musammam Yarima Nuhu wanda ba tun yau ya ke da k’udirin mallakar Bintu ba, ko da kuwa a matsayin sad’aka ce, tin da wata baiwa ta kawo masu tsirkun abun da ta ji Gimbiya Binta da Jakadiya su na kullawa ya kasa sukuni. Ya had’a goma na arziki ya nemi amintacciyar baiwar sa, ya ce ta kaiwa Jakadiya, wato na sharan fage kenan kafin ya je mata da buk'atar sa.

Su Gimbiya kuwa ko da su ka koma na su 6angaran mamakin yanda Yarima Inuwa, Nuhu da Inna Salti su ka nuna k’iyayyar su k’iri k’iri ta hanyar k’in amincewa da wannan lamarin, a nasu tun da su ne su ke ciki d’aya su ya fi dacewa ace sun yi na’am da lamarin, amma ga mamakin su waccan da su ke kira yan bakin gida su ne su ka fi nuna kauna gare su.

Yarema Nuhu kuwa kai tsaye 6angaran sa ya nufa rai 6ace, babban takaicin sa shi ne a rasa baiwar da za a sa cikin wannan hatsari sai Bintun shi ta arziki, Bintu da ya dad’e ya na saka buri akan ta, gaskiya dole ya san yanda zai yi wannan maganar a rusa ta. Bakin kofa ya ci karo da Baiwar da ya tura gun Jakadiya, hannun ta nik’i nik’i da kayan da ya bata ta kaiwa Jakadiya. Da ganin sa ta zube k’asa ta na mai gaishe shi. Cike da mamaki ya ce
‘’ba ki kai mata sak’on ba ne?’’

Kai duk’e Baiwa ta ce
‘’Allah shi taimaki Yarima, Uwar baka ta sake hali, da na kalle ta sai dak'uwa ta min, kasan Jakadiya gara ce, ga tsiya ga rana, tsiyar ta ya fi ranar ta yawa’’

Jin haka ya gane me ya faru, ma’ana dai Jakadiya ta yi tsiyar ta, ta kuma k'i kar6ar tsarabar sa wanda hakan ya na nufin ba zai sami kowani taimako daga gare ta ba. Cikin zafin rai Yarima ya ce ‘’kya iya tafiya da kayan’’
Sannan ya tsallake ta ya shige ciki ya na mai bugo k’ofar. Yayinda baiwa ta had’e kaya ta yi gaba, Allah ya kashe ya bata.

A wuni guda Bintu ta rame ta lalace kamar wacce ta shekara ta na ciwo. Da Baba ya dawo da daddare ya ke sheda mu su an fa aika Fabarusa, zance ya tabbata nan da wata d’aya za a amrawa Sark’i Abdulrahman aure da Binta d’iyar Sarki Sule na Sa’ayrasa. Inna na mai d’aure fuska ta ce
‘’yo to tun da ba da Bintu aka ce ba ai can da su gada, ni dai d’iya ta ba sunan ta Binta ba, Bintu an sunan ta, haka kuma ba d’iyar sarki ba ce d’iya ta ce’’

Baba na mai duban ta ya saki murmushin takaici, kana ya ce
‘’ke kuma d’iyar wacece? Ko in ce ke wacece a Masarautar nan da ga ke har d’iyar ta ki?’’
Inna ta yi shiru, ganin haka Baba ya k'ara
'’shirun da ki ka yi ya tabbatar min da kin tuna ashefa ku bayi ne, dan haka ba ku da ‘yanci, ki ma godewa Allah da ya sa amrar da ita ya ce zai yi ba bada ita zai yi sadaka ko sad’aka ba, gide ke dai kin cika butulu. Toh ki saurare ni da kyau gobenan za a zo a tafi da Bintu ga babban gida, hallo dangin ki d’aya ba a yarda kin shedawa ba, yo to ina bayi ina wasu dangi ma in ban da ba'a"

Kuka Inna ta saka ta na fad’in ‘’wannan zalinci da ke shirin aikata min da wanga yarinya Allah shi isar mana’’
Ciki Baba ya shige kafin ya lek’o da kan sa ta assabari ya furta ‘’je ki tari Magajin Gabasawa ki sheda masa, yo to ba ni na kar zoman ba, rataya aka bani’’
Ita kuwa Bintu da ke jiyo su daga d'aki zuciya ne kad'ai ba ta had'iya ba, tunani ta ke ina ma Aisar ya na kusa ya kawo ma ta d'oki yanda ya [truncated by WhatsApp]®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣8⃣



Kamar dai yanda Baba ya ce, da sassafe sai ga Jakadiya da amintaccin bayin Hajja Kilishi sun dokowa Inna sammako. Dan takaici Inna d’auke kan ta yi dan kuwa ta kasa bud’e baki ta ce da Bintu ta fito ta bisu.

Tun da Bintu ta ji sallamar su ta shige bayan kofa ta yi zaman ta, duk da ta ji buk’atar Jakadiya amma k’yememe ta k’i fitowa. Ana haka Baba ya fito ya rufe Inna da fad’a
‘’Magajin Gabasawan za ki yi wa musu ko kuwa Jakadiya? Iye Yagana? Gide ban san tsaurin idanu fa! Yo to yau ko ke Magajin Gabasawa ya ce zai aura sauki zan yi bare ma wanga d’iya, aikin banza aikin hofi! Ta na ina wai? Gide Bintu hito ki bi su in ba haka ba ina make ke! kwankwatsi ma kuwa!’’

Jakadiya na murmushi ta ce
"Mahuta bi su a hankali, ai tsakanin uwa da d’iya sai Allah bare kuma ace za a raba su rana a tsaka, bi su a sannu Mahuta, in ban da ke da abin ki Uwar bayi wanga lamari ai alheri ne aka yiwa d’iyar ki, wanga abu abin san barka?’’

Idan Inna ta tanka ko shakka babu dutse ma ya tanka, ganin haka Baba ya wuce su izuwa d’akin Bintu, ya tadda ita bayan kofa ta had’a zufa da hawaye. Fad’a ya hauta da shi, ta in da ya ke shiga ba ta nan ya ke fita ba. Amma kyememe Bintu ta k’i motsawa bare ta fito. Aikuwa da Baba ya fusata sai ya hauta da zagi, jin haka Inna ta shige d’akin da sauri dan ta san daga nan kuma abun da zai biyu baya.

Ilekuwa shigar ta kenan ta ga Baba ya d’aga hannu ya na shirin kaiwa Bintu bugu, nan da nan ta shiga tsakani, ta ce
‘’haba Malam! Ai ka ji tsoran Allah abin ga ai sai yayi yawa maye da hauka!’’

Nan fad’an Baba ya koma kan Inna, ai lalle Inna ke d’aurewa Bintu, dan haka zai fita ya dawo, in dan ya dawo ya ga Bintu gidan nan sai na lahira ya fita jin dad’i. Dan masifa da bambami ko sallama be yiwa su Jakadiya ba ya sa kai ya fice ya na kumfar baki.

Bayan fitar sa Inna ta ja hannun Bintu su ka fito tsakar gida. Inna na mai duban ta ta ce
‘’Bintu idan har ni na haife ki, toh na baki umarni ki bi su ku tahi Babban gida’’

Bintu na jin haka ta zube k’asa, hannayen ta biyu ta sa ta ruk’o k’afar Inna ta na fad’in
‘’Inna na tuba, Inna ki gafarce ni, Inna ki min afuwa, Inna kar ki ce na bisu, Inna kar ki yarda a raba ni da ke, kwankwatsi na dena 6ata mi ki rai, idan na k’ara aratta kashe ni’’

Inna na mai janye k’afafun ta daga ruk’on da Bintu ta yi mata ta ce
‘’na yafe ki duk da ba ki ta6a sa6a min ba, ke d’iya ce ta gari, dan haka ki sa Allah a ran ki shi ne kad’ai ka iya mi ki, tashi ki bisu, Allah shi fisshe ki alkairi...’’

Ta na gama fad’ar haka ta shige ciki ta na hawaye. Nan fa Bintu kuka har da birgima. Su Jakadiya su na nan suna gani sarautar Allah duk da dai su ma kukan na Bintu ya so ya d’an ta6a su.

Habibu ne ya shigo, ganin abin da ke faruwa ya shiga rarrashin Bintu, har ya samu ta yi shiru. Ya ce da su Jakadiya su yi gaba gasu nan biye da su, bara ya had’o kayan Bintu. Jakadiya ta ce ah ah ba a bukata, ita d’in ta kad’ai ake buk’ata.

Gaba su ka yi, hannun Bintu ruk’e da na Habibu, su na tafe ya na bata baki da nasiha har su ka isa kofar Babban gida. Nan ma Bintu ta ce ba ta san zance ba, Habibu be isa ya koma ya bar ta gun su Jakadiya ba. Jakadiya ta fusata ta hau Bintu da fad’a

‘’yau ina ganin walele gi6in takwaru! Gaskiya ne komai girman d’an mara kabo be isa aure ba! 'Yar tusa wacce ba ta san arziki ba! Ki na baiwa d’iyar bayi har kya wa mutane kwawarniya shiga rumbun k’ore, yo to sai ki ma Babban Bijimi musu da kwarnato in ya so a tsire ki ma ga me asara!’’

Bakin Bintu na rawa, ta saki hannun Habibu, wanda d’acin maganar Jadiya ya sa shi juyawa da sauri dan gudun kar ya maida mata ya jawowa Bintu da ma gidan su baki d’aya, ya na jiyo Jakadiya na masife Bintu yayinda ta ke hankad’a kafad’ar ta zuwa ciki, babu yanda zai yi haka ya tafi ba tare da ya sake ko waiwaye ba.


'Dakin Jakadiya aka aje Bintu, nan ta sha kukan ta, ta k’oshi dan kan ta ta yi shiru sai ajiyar zuci kawai.

Jakadiya ta shigo kana ta ce ta saka mayafi ki biyo ta, Babban bijimi na jiran zuwan su. Kallabin ta ta ware ta yafa bisa kan ta, babu musu dan kuwa taji tsoran maganar Jakadiya na za a tsire ta, ta bi bayan Jakadiya ba su zame koina ba sai turakar sarki.

In da Jakadiya ta tsaya daga waje, Bintu ta shiga daga ciki. Nan ta tadda sauran ilayan Sarki. Gimbiya Binta ba ta fasa

1 Comments On BINTU DIYAR BAYI CE 1
avatar
aminu-1-2

10 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment