Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

watsawa Bintu kallan wuk’anci ba, ita kuwa Inna Salti tsabar tausayin Bintu ne cikin ran ta. Yarima Nuhu kuwa Allah kad'ai ya san tashin hankalin da ya shiga, musammam yanzu da ya ga Bintu gaban Sarki, babu makawa ya na ji yana gani Bintu za ta si6ice ma sa. Tin shigowar ta ya sa saka idanu akan ta, k’irik’iri be damu da ba shi kad’ai ne ba, bare ya damu da fassarar da za a iya masa. Ita kan ta Gimbiya Binta ta lura da irin kallan da ya kewa Bintu, har zunguran K'amariyya ta yi dan ita ma ta ganewa idon ta, bare kuma su Hajja Kilishi har da murmushin mugunta, dan kuwa ta k’i jinin Yarima Nuhu.


🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


©Khadija Sidi.....✍🏼

1⃣9⃣



Muryar Bintu a shak’e tsabar kukan da ta yi ta kai gaisuwar ta ga Sarki. Hankali kwance, idan Sarki ya lura da sauyin yanayin da aka samu game da Bintu tsakanin ranar da ta fara zuwa gareshi da kuma zuwanta a yau, bai nuna ba don kuwa ko a jikinsa ya amsa, kafin ya k’ara da
‘’Masarautar mu na godiya ga wanga d’iya ta arziki, kasancewarki baiwa, mun baki ‘yanci, mun ‘yanta ki a yau kin tashi daga baiwa kin zama d’iya mai ‘yanci...’’

A firgice Gimbiya Binta ta kai kallonta ga Sarki ta na mai fiddo ido waje dan kuwa ba ta yi zato ba, kar dai danasani za ta yi, abun da ya fara zuwa zuciyarta kenan yayinda gaban ta ke dukan uku uku. Haka ma kowa na wajan ke kallan Bintu, wacce ta rasa me za ta yi, murna za ta yi na samin ‘yancin rayuwar ta bayan shekara goma sha biyar ta na baiwa, ko kuwa kuka za ta yi ta tashi daga baiwa, amma iyayenta na nan a bayi, tabbas ta tabbata d’iyar bayi. Hawaye ne d’aya bayan d’aya ke gangarowa daga idanun ta, murya na kakkarwa ta ke fad’in ‘’Godiya na ke ranka shi dad’e, godiya na ke Allah shi ja da ran Sarki, Alkhairin Allah ya tabbata a gare Mai Martaba’’

Yarima Nadir da ke jikin Inna Salti ne ya ce " Inna Salti me ya sa Bintu ta ke kuka?"
Hannun Inna Salti bisa le6enta ta amsa da
"Shhhh"
Wato ya yi shiru, shirun ko yayi.Yarima Nuhu wanda shi kansa ya rasa shin wai me ya ke ji a lokacin ji yayi kamar ya isa ga Bintu ya sa hannu ya share mata hawayen idanunta, ji ya ke kamar ya rok’i Sarki a bar ma sa Bintu, ko da kuwa shi ne abu na k’arshe da zai tambaya gun Sarki ya amsa masa. Yau ga Bintun arziki an zama ‘yantacciya, wannan fa shi ake kira ga k’oshi fa ga kuma kwanan yunwa.

Sarki bai gushe ba ya k’ara da ‘’Nan da mako hud'u za mu amra miki aure ga Masarautar Fabarusa, da an amra za a ba mu bashin da mu ka buk'ata, hallo tarewar ki can sai nan da mako hud'u kan nan kin sami shiri mai kyau. Ba mu amince ba sai da mu ka tabbatar de ke baiwa ce mai tarbiya, dattako da kuma sirri,kasancewar kin iya zama da d’iyar mu lamun lahiya ba tare da ta ta6a kawo mana kukan ki gare mu ba’’

Gimbiya Binta aka zagayar da kwayan ido ta cikin mayafi, cikin ranta fad’i ta ke ‘’Yo to ba girin girin ba d'iyar bayi, ta mai......’’

Jin Sarki ya ce ‘’Hajja Kilishi ga wanga d’iya za ta dawo gare ki ina fatan ke da Jakadiya za ku sa ta hanya, cikin surri ku koyar da ita dabarun Masarauta duk dai yanda Jakadiya ta sheda mana yarinyar dama mai sani ce, mu na so duk kan nan ku sani ba mu yarda ko da wasa wani ya k’ara kiran wannan d’iyar arziki da baiwa ba, haka kuma ban amince a yi mata yanda ake yiwa bayi ba, ku sani wanga d’iya d’iyar mu ce, dan haka a daraja ta’’

Gimbiya ta cije le6e, ita dai kam wannan lamari ba ya mata dad’i, ya Takawa ya ke san mata sakiyar da ba ruwa ne, ko da yake ma ita ina ruwan ta k’arshen ta ajali ne ke kiran Bintu, dan kuwa girman Masarautar Fabarusa ko jinin saraki sai sun shirya zaman ta bare baiwar da za ta je a matsayin Gimbiya, tun da dai ta ci nasarar sa min Aisar, ga shi Gimbiya K’amariyya ta sami Barde ai hutatai. Abunda ta ke jaddadawa zuciyar ta da ta ke nemen fashewa tsabagen bakin cikin kalaman Sarki kenan, bilhakki danasani ta fara, dan kuwa ba ta yi zato ba.

‘’Za mu mayar da d’iyarmu Binta kasar Nigeria, in da za ta je can ta cigaba da karatu kan mu biya bashi ga Masarautar Fabarusa komai ya warware........’’

Gimbiya Binta ba ta san sanda ta tashi tsaye a zabure ba, ta na mai girgiza kai. Nan kallo ya koma gare ta har sai da Yarima Inuwa ya daka mata tsawa ya na mai fad’in
‘’Gide kin manta gaban wa ki ke ne! ko ma ki zauna kar ki mana sakarci a nan’’

Gimbiya K’amariyya ce ta jawo hannunta, yayinda ta koma ta zauna a gajiye, tuni idanunta su ka kawo ruwa, ba ta san sanda ta furta.
‘’Tuba na ke Takawa, Allah ya ja da ran Sarki a min rangwame tuba na ke kar a bari na yi nisa da Mai Martaba’’

‘’Ko kuwa dai ba kya so kiya nisa da Aisar Gaddafi Nur ba’’ Fad’in Gimbiya K’amariyya kenan wacce ke rike da hannun kanwarta ta, cike da tausayi ta ke dubanta, dan kuwa ita kad’ai ta san zafin da ta ji jin za a raba ta da masoyinta Barde, yau kuma gashi ‘yar uwarta na shirin rasa na ta masoyinta sakamakon taimakonta da ta yi. Kana ta kada baki ta ce
"Allah shi ja da ran Sarki, dan Allah a duba lamarin nan, Binta har yanzu yarinya ce, za ta cutu muddin ta yi nisa da mu.’’

Yarima Nuhu na dubansu, bakinshi kunshe da murmushin mugunta ya ce
'’Kar ki fad’awa Takawa wanga yashashen zance haka K’amariyya, idan har wanga d’iya( ya nuna Bintu da yatsa) za ta iya taran aradu da ka ta shiga Masarauta mai girma a cikin badda kama, duk da k’aranci shekarunta, ban ga dalilin da zai sa Binta ba za ta iya zuwa wata k’asar ba domin rufawa masarautar ta asiri ba, yo to menene nan da makwafta Nigeria, ai Nigeria da Nijar d’aita, ko kuwa ki na nufin za a aurar da Bintu matsayin Binta ne kuma jama’a na ganin Binta a k’asar nan, dole sai ta tafi’’
Ya k’arasa magana ya na mai duban Gimbiya Binta da ta ke kuka bilhakki.


🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


©Khadija Sidi.....✍🏼

2⃣0⃣


‘’Nuhu ya yi gaskiya, kamar yanda wanga d’iyar arziki ta mana biyayya, mu na fatan ke ma haka za ki kasance me biyayya a gare mu, saboda haka sai ki zauna da shirin ki na bulaguro nan da mako hud'u, komai za a yi jiyo shi cikin surru, kar ku yarda da kowa sai amintaccun bayin ku. Mun yi magana, Mun sallame ku’’
Cewar Sarki kenan ya na mai kawar da kai daga kallan Gimbiya Binta gudun kar ta karya masa zuciya, dan kuwa shi dai yaransa su an rauninsa.


Komawarsu d’aki nan Gimbiya K'amariyya ta ga kuka da daru gun Gimbiya Binta, ba shiri Inna Salti da Hajja Kilishi su ka sallami bayin da ke cikin 6angaran gudun yad’uwar maganar. Wanda kuma su ka riga su ka ga halin da Gimbiya Binta ke ciki, Jakadiya ce ta tara su, cikin hikima ta mu su kashedin ko da wasa kar su yarda a ji halin da Gimbiya Binta ta shiga jin Mai martaba ya ba da amran ta ga Sarkin Fabarusa, duk wanda aka ji a bakin sa sai dai uwar sa ta haifi wani. Ai kuwa dai ba su fasa yad’awa ba, ta yanda Allah ya so ma maganar Jakadiya su ke yad’awa ba asalin zancen gaskiya ba.

Dakyar aka samu Gimbiya Binta ta sarara da kukan da ta ke, ita sam ta manta da azanci a maimakon ita za a aurar da Bintu, kasancewar haka ita ma sai an 6oyeta na wani d’an lokaci. Gashi Mai martaba ya ‘yan ta Bintu, wacce ta ke baiwar ta tin tale tale. Bauhaushe dai yayi gaskiya, in za ka gida ramin mugunta, ka gina shi gajere.

Da yamma Bintu na zaune d’aki tare da Hajja Kilishi, ilimin zaman fada ta ke ta koya mata, amma ita sam hankalin ta ma ba ya wajan dan haka ba wani ganewa ta ke ba. Zuba ido ta ke ko za ta ga Innar ta, amma babu Inna baba alamar ta. Hajja Kilishi ta ce da Bintu ta lek’a falo ta ce da d'aya daga cikin bayin ta maza su je 6angaransu Gimbiya K’amariyya su k’ar6o ma Bintu sak’o.

Ko da Bintu ta fito, ta bayin sai kai kawo su ke cikin hidimansu, sai ta kasa tsaida d’aya ta aika, duk da dai yanzu ba cikin sahun su ta ke ba inji Sarki, ita har yanzu ba ta ji wani canji ba, dan haka yanda su ke haka ta d'auki kanta, sutarar jikinta ma kayan bayin Sa'ayrasa ne wanda dama shi ne a jikinta tun safe da su Jakadiya su ka zo tafiya da ita. Hakan ya sa ta yanke hukuncin zuwa da kanta 6angaren. Ta na sa k’afa cikin falon ta yi ido biyu da Gimbiya Binta, wacce fitowar ta daga d’akin K'amariyya kenan, idanun nan sun yi jajur.

Ganinta Bintu ji ta yi kamar ta koma a guje, ile kuwa bud’ar bakin Gimbiya Binta sai cewa ta yi
'’Ke har kin isa ki nuna fuskarki gabana dan ubanki! Ya ki nan munafuka!’’

Jikin Bintu na rawa ta k’arasa gaban Gimbiya ta na mai zubewa a k’asa ta ce
‘’Kimin rai, tuba na ke Gimbiya’’

‘’A gidan ubanwa ki ke tuba! Oho wato Takawa ya ce kin zama daidai da kowa shi ya sa ki ka zo gwada kafad'a da sa’annin ki ko? Shu’uma daina rawar k’afa, kwalla ba amre ba ne! ki na cikin hatsari muddin Masarautar Fabarusa su ka san ke fa baiwa ce kuma d’iyar bayi, zamanki a Masarautar na d’an wani lokaci ne har sai mun cika burinmu, na farko shi ne na gama makaranta na kuma amri masoyi na Aisar, na biyu Didi ta amri burin ranta, wato Barde, na uku Mai Martaba ya biya bashi ba tare da an yi amfani da farin cikin iyalinsa ba, ke kuwa Allah kad’ai ya san ya rayuwar ki za ta kasance, hallo tsire ki Sarki Abdulraman zai sa a yi idan ya gano mak’aryaciya ya ke amre.....’’

‘’Ku kuwa Masarautar mak’aryata su ka bashi amren ta ba.....’’
Yarima Nuhu ne ya katse ta, da sauri ta juya ta kai kallonta gare shi, ashe ya shigo ba ta sani ba. Ya na jingine jikin bango daga bakin k'ofa, hannunsa sarke bisa k’irjinsa. Sanye ya ke cikin shud’ayan kaya, ya d’aura farar falmaran akai. Bai gushe ba ya k’ara.
‘’Ina tunanin halin da ki ke ciki ya sa ni tattaki dan zuwa na ganki, ba shakka garau ki ke tun da gashi kin sa d’iyar arziki gaba ki na mata yashasshen zance irin na marasa tunani, shin kin manta wanga d’iya ba baiwa ba ce?’’

Yanda ya ga ta cuna baki ya sa shi fad’in
‘’Dakyau, yanzu ina ga kin tuna, dan haka na miki uziri, amma daga yanzu ba na fatan sake tuna miki, hallo za ki kula.'’

Ya mayar da kallonsa ga Bintu,
"Bintun arziki tashi ki yi tafiyar ki, gide kar ki sake tsugunnawa haka gaban kowa, tabbas akwai aiki ja gaban Jakadiya muddin za ki kasance mata ga Sarkin Fabarusa dole ki wuce raini, ke ba baiwa bace, kar ki ta6a mantawa da wannan.’’

Da saurin ta ta tashi, ta na mai godiya ga Yarima Nuhu, ta bi ta gaban Gimbiya Binta, ta zo gaban Yarima Nuhu sannan ta fice ba tare da ta damu da ta k’arbo sakon na ta gun Gimbiya K’amariyya ba.

Ganin yanda ta ke tafiya ba Yarima Nuhu ba, hatta Gimbiya Binta sai da ta bita da ido, ba ta san sanda ta je tsaki ba ta ce
‘’Mtsw! Ka ga yanda ta ke tafiya d’iyar bayi sai shegen tak’ama da isa.'’

Ciki Yarima Nuhu ya shigo sosai, yayinda ya sami kujera ya zauna ya na mai murmushi ya ke duban k'anwar ta sa sannan ya ce
'’Halittarta ce haka’’
Da sauri Gimbiya ta dawo da kallonta gareshi, cikin rashin fahimta ta ce ‘’Na’am?’’

‘’Ko ba Bintu ba? Tak’ama da isa ba ta gada ba, amma Allah ya mata shi a halittar ta, kin ga baiwar Ubangiji ko? Ba ki ga tsayinta da dirinta ba ne? Su kad’ai sun isa nuna tak’ama, shi yasa na ke mai bakin cikin rasa ta da zan yi ta sanadiyar san rai irin na k’auna ta.’’

Kamar mai shirin yin kuka Gimbiya Binta ta furta ‘’Yarima......Bintu d’iyar bayi ce!’’

Ya na mai had’e rai ya ce ‘’Hakanan k'auna ce ta na ke kuma rainon san ta cikin raina tun kafin na mallaki hankalina, ina jin ta har jinin jiki na duk da kuwa ita d’iyar bayi ce, ni kuma d’an saraki, ki sani na san da duk wani tukgun da ki ka kulla ke da K’amariyya tare da d’aurin gindin Jakadiya! Har ki na da bakin kuka dan ance za ki bar k’asa? Da da ki ke gina ramin muguntar ba ki san za ki iya wad’awa ba?’’

Kuka Gimbiya Binta ta sa, hawaye d'aya na bin d’aya ta ce
‘’Ina soyayya da k’auna ta jini da amintaka? Ni fa ‘yar uwar ka ce jini d'aya, za ka za6i d’iyar bayi akan yar uwarka? Ka ce da ni wasa ka ke, ba ka san wanga d'iyar bayi.’’

Tashi tsaye ya yi, ya na mai danna idanunsa cikin nata ya ce
‘’Ni abinda ya ke ban takaici kenan, jini na ta san ta iya had’a tuggu haka? Kin san abun da ki ke shirin saka babban mutum kamar Takawa ya aikata kuwa? Kin san girman laifin kuwa? Ina mai gargad’inki, muddin ki na so mu shirya ki gaggauta kunce wannan sak’ar da ki ka kulla tun kan ya k’ure miki’’
Ya juya zai fita, har ya kai k’ofa Gimbiya Binta ta k’ara kiran sunan sa ‘’Yarima....’’

A hankali ya juyo ya na dubanta, idanunsa sun kad’a sun yi jajur. Gimbiya Binta na mai hawaye ta sake furta ‘’Bintu d’iyar bayi ce......’’

‘’Ita na ke kauna kanwata, idan har ki na so na da farin ciki kar ki ja min asarar Bintu ta ta arziki’’ Ya na gama magana ya fice, ya bar Gimbiya Binta ta na mai bin bayansa da kallo.

🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE




2⃣1⃣



Khadija Sidi......✍🏼



Duniya ta yiwa Gimbiya Binta zafi, ba ta san sanda ta durkushe kasa ta na mai sakin kuka mai tsanani. Gimbiya K’amariyya ce ta fito hannun ta ruk’e da sakon Bintu, gani Gimbiya Binta cikin tashin hankali ya sa ta sakin sak’on na Bintu bisa kujera, ta k'arasa gare ta da sauri ta na mai waige waige cikin fargaban sharrin masu tsirku. d’ago ta yi ta na fad’in
‘’haba ‘yar uwa, ba yanzu mu ka gama rarrashin ki ba, me yayi zafi Binta shi ba wuta ba? Maza tashi mu yi ciki kar bayi su gani su sami abin yad’awa’’

Kanta ta d’aura bisa kafad’ar Gimbiya K’amariyya ta na mai fad’in
‘’na shiga uku Didi, duniya na neman juya min baya, hatta d’an uwa na ya fi kaunar d’iyar bayi akai na ni da na ke cikin umman sa’’

Gimbiya K’amariyya na mai buga bayan Gimbiya Binta a hankali cikin rarrashi, ta ja ta su ka yi ciki. Sai da su ka shiga d’akin Gimbiya K'amariyya, ta sallami baiwar da ke cikin d’akin sannan ta zaunar da Gimbiya Binta bisa gado ta nemi ba'asi akan tsakanin Yarima Nuhu da Bintu. Nan Gimbiya ta fad’a mata yanda ta kasance tsakanin ta da Yarima Nuhu, jin haka ba ta yi mamaki ba, sai ma tsaki da ta ja ta ce
‘’shiga shigila gand’e ma shiga rawar takai! Har kya ma damu da Yarima Nuhu, in dai wajan shiga shirgin da ba na shi ba ne in aka gan shi kowa ya shafa fatiha, ya manta ba kauna ba, ciki d’aya su ka hito da Bintu! kar ki wani damu, zancen komawar ki k'asar Nigeria kuwa InshaAllahu zance ne, kuma in dai Aisar ne ya ma zama na ki an gama’’

Gimbiya Binta na mai kwantar da kan ta bisa gwiwar Gimbiya K’amariyya ta ce
‘’ina godiya Didi, dan Allah kar ki bari Takawa ya raba ni da farin cikin rai na’’
Ta na shafa kan ta ta ce
‘’in dai wannan ne kar ki damu, bayan auren d’iyar bayi na miki alk'awarin shedawa Hajja Kilishi lamarin ki da Aisar, sai a san yanda za a bullowa lamarin, ko?’’


Ta k’arasa maganar ne ta na mai d'ago fuskar yar uwar ta ta, cike da farinciki Gimbiya Binta ta tsinci kan ta ta na mai washe hakora, ashe dai da rabo. Haka dai su ka cigaba da hirar su cikin kwanciyar hankali har Gimbiya Binta ta mance da maganar Yarima Nuhu bare ma ya dame ta.

Bintu kuwa ko da ta samu ta ganta d'akin Hajja Kilishi, nan ta yi zaune abun ta, da Hajja Kilishi ta tambayi sak’on na ta, sai cewa ta yi ba ta ga Gimbiya K’amariyya ba. Hajja na k'orafin dama ba ta ce Bintu ta je da kan ta ba, ta sake aika wata baiwar ta karb’o sak’on, sannan ta bawa Jakadiya da ta zo tafiya da Bintu.
Sak’onni ne na kayan gyra jiki wanda ya had’a da su dilka, halawa, kalta, kurkum dadai duk sauran kayan gyaran jiki wanda musammam Hajja Kilishi ta sa aka mata sautin su daga Agadez.

A daren ranar Bintu ta fara shiga hannu, mai gyaran jiki na yi, mai koya mata kissa da dabarun zaman fada na yi, mai mata jawabi yanda sabuwar rayuwar ta za ta kasance na yi. Telar babban gida ma ba a barta a baya ba, haka ta yi tattaki ta zo ta gwada Bintu tare da tafiya da damin siturun da Hajja Kilishi ta zab’arwa Bintu. Hatta gashin Bintu da Marry ta yanke sai da Jakadiya ta saita almakashi ta daidaitasu, ta na mai tambayar ya aka yi gashi rabi dogo rabi gajere. A lalle sai an wayar da Bintu ta fito fes kamar d’iyar saraki. Ita kuwa Bintu ba ta fasa kuka da kewar Innar ta ba.


🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪
®
✏📖
​FIKRA WRITER'S ASSOCIATION​

🐪🐫BINTU 'DIYAR BAYI CE!
🐪🐪🐫🐪
🐪🐫🐪🐫🐪🐫
🐪🐫🐪🐫🐪🐫🐪



GARGA'DI

KUNGIYA MAI SUNA A SAMA, BATA YARDA WANI KO WATA YA MAYAR DA DUK WANI LABARI MAI 'DAUKE TAMBARIN SUNAN TA IZUWA DOCUMENT BA, YIN HAKA KARYA DOKA NE, WANDA HAKAN KA IYA JAWO YANKEWAR LABARIN. DAN ALLAH MU KIYAYE.


©Khadija Sidi.....✍🏼


2⃣2⃣


Daga ranar zuwa washagari sai ga Bintu an fara wasai. Washagari da safe, Bintu da Jakadiya tare su ka zauna karin kumallo, cin abinci ma sai Jakadiya ta koya mata dan kar ta je ta bada su a masarautar abokan gaba. Abinci ne kala kala na alfarma irin na gidan saraki, kai ka ce ba fari ake a masarautar ba. Bintu na gani Innar ta ce ta fad’o mata a rai, ba makawa ta san yanzu ta na nan ta na fama da hatsi da dusa, amma ita nan ga abinci har da na b’arna a gaban ta.

Da kyar ta iya cin kad’an daga abinci, hakan ma sai da Jakadiya ta sab’ar ma ta, ta na mai tuhumar ta da tsabar mugunta ne ya sa Bintu k'in cin abinci, dan a ganta ramammiya ta sa ace tsabar yunwar da ke addabar Masarautar su ne, ko kuwa cutar yunwa ya kama ta.

Kan wannan jaraba na Jakadiya ne ya sa ta bi yanda Jakadiya ta ce, ta na mai gwada mata yanda za ta yi haka har dai ta ta6a wanda za ta iya, a dole Jakadiya ta hakura ta rabu da ita.

***** ******
Sai da ya rage saura sati guda auren Bintu sannan Innar ta ta yarda ta zo wajan Jakadiya ganin Bintu, hakan ma sai da Jakadiya ta matsa tukunna. Ganin yanda Bintu ta canza ta yi wasai fatar ta har shek’I ya ke, duk da dai ta yi wani irin rama sai da ta ji dad’i. Sun dad’e suna hira, nan ta ke sheda mata sarki ya ‘yan ta ta. Sam Inna ba ta yi wani murna ba, a fad’an ta da hatsarin da aka jefa d’iyar ta har gwara a bar ta d’iyar bayi har abada. Da Inna ta zo tafiya da kyar Bintu ta sake ta, nan fa taita sana'ar ta ta, wato kuka babu kuma mai rarrashin ta bare ace mata ya isa.

Bayin da aka amince da su, wanda su aka yarda su shiga wajan Jakadiya kuwa kishi su ke da Bintu, musammam da su ka ji ashe ita ce za a aurawa sarki ba Binta ba, ga gyara da hidima da ake mata sai kace wata d’iyar saraki. Baiwa ta zama ‘yan tacciya. Da yawan su kan ce kukan munafurci Bintu ta ke, wasu kuwa fad’i suke ina ma su an Bintu, da kakarsu ta yanke sak’a.

Babban gida kuwa Gimbiya Binta Hajja Kilishi ta sa a gaba ta na mata gyaran jikin bogi, a lalle ayi basaja gudun ‘yan tsirku na fada. Amma a zahirin gaskiya Sarki ya sa a duba makaranta mai kyau da tsada k’asar Nigeria domin mayar da ita can. Har ila yau daga Gimbiya Binta har K'amariyya ba su fasa k’ulle k’ulle da shige da fice ba dan neman yanda za a yi Takawa ya sauya shawara, amma dai abin ya ci tira. Har kar gaban ta ya sa ko ta kan Bintu ba ta bi, bare ta sa ta a idanun ta.

Haka ma Yarima Nuhu, wanda ya rame a ‘yan kwanaki kad’an tsabagen fargaba auren Bintu da ke gabatowa bilhakki. Gashi gaba d’aya an 6oye Bintu cikin fada, raban da ya sa ta a ido tun randa ya zo ya tadda ita da Gimbiya Binta ta na mata cin kashi, duk yanda zai yi ya gan ta yayi amma babu Bintu babu alamar Bintu. Daga bisani ya yanke hukuncin tarar aradu da daka, bayan sun dawo daga shawagi, ko sauka daga dokin sa be yi ba, yayi tattaki zuwa wajan Jakadiya da buk’atar sa na ganin Bintu

Kan ya k’arasa ga 6angaran na ta su ka yi kaci6us a hanya, ta fito za ta turakar sarki. Ganin ta yayi saurin jan linzamin dokin domin tsayawa, har sai da dokin ya fara dara da nagarta (tsalle da rawa) cikin yanayin tada kura, Yarima Nuhu na mai damk’e linzamin gudun kar ya ji shi k’asa ya shiga k’ok’arin tsayar da dokin. Jakadiya na mai d’aga hannun ta na dama da ta d’unkule sama ta ce

‘’kiwo sannu Yarima, ba sake ba manko, kamazuru abokin dabara, amincin ka ya fi ga linzaminka’’
(ta na fahimtar da Yarima Nuhu ya nutsu, hankalin sa ya tafi kan linzamin dokin kada ya kada Shie’’

Ko da ta ga dokin ya tsaya, sai ta sa kai za ta yi gaba, Yarima ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar fad’in
‘’ba ki ji ba Jakadiya, wannan zuwan na ki ne’’
Jin haka Jakadiya ta ja ta tsaya, ta na bashi amsa da

‘’anya kuwa ba na ce ah ah ga Yarima ba yayinda na ke kan hanyar da zata sada ni da Babban Bijimi ba?’’

Da sauri Yarima Nuhu ya sauko daga bisa dokin, ya na mai jan linzamin dokin ya dawo daga gefan Jakadiya, wani irin iska mai zafi da k’asa ke busawa duk da dadai la’asar ce sakaliya.

‘’wa ya isa tsayar da Jakadiya a

1 Comments On BINTU DIYAR BAYI CE 1
avatar
aminu-1-2

10 months ago

Reply

Thank you

Please Login or Register in order to submit comment