Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

haka sauran yan ajinsu banda princesses Wace gaba daya wani irin haushi ya turnuke ta na ganin kanwar AA ta dawo




Zaune yake cikin office dinsa , wayar sa ta dau kukan neman agaji , wanan Kiran na biyar ne hakan ya sa ya mika hanu ya daga


Daga dayan bangaren akayi salama

Mubasshir ya amsa yana fadin ya akayi ne kabir?


Kabir ya ce " Elhaj daman yau naga Hajiya ta dawo makaranta aman dalilin kokarinta aka canza mata aji aka mayar da ita ajin wanan saurayin dan gidan minister dake sonta , nayi nayi a maido ta sun kiya sun ce wajen yafi dacewa da ita , ni kuma sunki maida ni can din shine yasa nace bara na fada maka a san yanda za'ayi


Mubasshir ya ce " What? Shi din wanene shi? Dan ubansa na minister shine zai sota ?


Kabir ya ce " ayi Hakuri Elhaj yanzu haka ina zaune ina hangenta a ajin , shi kuwa ya dawo da kujerar sa kusanta sanan yau bata saka likaf ba


Ai Mubasshir bai san sanda ya kashe Kiran ba ya mike ya kwashi makulan motarsa ya nufi kofa KO sanar da su baiyi ba inda zai nufa


Tafe yake yana nanata Mubasshir Yar Amana ce a wajenka dan haka Dole kayi takatsantsan da al'amuran ta , bazai yiwu kana ji kana gani wani dan iska ya kara lalata mata tarbiya bayan ta titi daman da ta samu, Dole ka kawo canji a rayuwarta ka fada mata karta yarda ta kula KO wani saurayi kai zaka sama mata miji idan har bata iya zama sai da namijin a kusanta ( to kaji fa Mubasshir haka ta fada maka)

Haka yayi tayiwa kansa zance tamkar sabon kamu har ya iso makarantar su Yar Mahaukaciya


Masu tsaron kofar Makarantar kansu sunyi mamakin ganin AA da kansa a makarantar gashi ba wani abu ake ba balatana suyi tinanin an gayato shi ne , KO kanwar tasa dake makarantar ce ba lafiya KO wani Abin? Haka dai suka bude masa ya nufi ciki


Yana isa ya tsayar da motarsa ya fito cikin shigarsa ta alfarma ya nufi office din director din fuskarsa da glass na rana baki ,


Yana isa sau daya ya konkwasa

Director din ya amsa da com in


Mubasshir AA ya tura ya shiga yana kokarin zare gilas din idonsa


Director ya Mike da Sauri yana fadin "kai kai kai yau baki ne damu haka?


Mubasshir ya kale shi ya ce " Asalamu alaikum, i'm sorry director kafin mu gaisa ka fito ka fito min da sisterna daga ajin da aka kaita


Director ya kale shi ya ce" AA ni kasan na san mahaifinka kafin ya rasu , Nasan kai daya ya malaka, kuma mahaifiyarka bata kara aure ba , to taya ta zama kanwarka? Ni fa abin nan na daure min kai kuma kaga dokar makarantar nan fa AA ku da kanku kuka dorata bai dace daga kanku a samu wata matsalar ba fa


Jikin Mubasshir yayi sanyi tabas ya taka doka har biyu a wanan makarantar , ta farko ya saka an karbi Rahma ba tare da takardar haihuwarta ba , a zuwan dan kawai kwakwaluwarta ta bude sai na biyu ya kawo Wanda zai kula da dukan abinda take aikatawa a cikin makarantar a matsayin dalibi shima an yarje masa, to idan yaci gaba da haka za'a samu tangardar dokar


Director ya katse masa tinaninsa ya ce " Aman fa kayi hakuri AA daman dan a dan daidaita al'amarin ne dan ganin komai ya tafi daidai


She is my wife


Director ya zaro ido yana kalon AA dake tsaye yana dan kakauda kai yana nadamar abinda bakinsa ya fada wata karyar Kenan , director ya ce " what?


Mubasshir ya dan duko ya dora hanayensa biyu saman table din ya ce " *yes , She Is My WIFE* director shi yasa kaga inai maka kwana kwana, dan ajin da zatayi ba matan aure ni kuwa da nan na yarda na san baza'a samu malaman banza a nan ba


Director ya ce " Kai masha Allah , ai da tunda wuri ka fada min haka ai da ba'a soma hadata bama da mazan dan haka muje a maiyar da ita wancen ajin


Mubasshir ya fito daidai an fidosu cin abincin rana nan fa kalo ya koma sama shaho ya dau giwa duk sai masu kalon AA a jarida da kuma TV sukayi arba da shi a fili


Yar Mahaukaciya da Kawarta Fati sun fito suna tafiya da niyar dosar wajen cin abinci suka ji ana yi musu magana


Fati ta fara juyawa tayi arba da AA da director sun nufo su ,ai bata san lokacin da ta furta masha Allah irin kyan da yayi mata a fuskarta ta juyo da Yar Mahaukaciya tana Fadin wayo AA ne


Kalon kalo suka yiwa juna inda yana isowa ya ciro nikaf daga aljihunsa ya Mika mata


Cikin rawar hanu ta mika hanunta zata karba inda garin karkarwar ya kufce ya fadin ,nima na ajiye wayar dan caji😘😘😘😘😘😘😘😘
[9/11 16:55] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







50


Mamyna my blood sister *Mariam maman Imran love u*

Mamyna *Khadija ni ma ina sonki irin da yawa din nan*

Jinjina gareki sis *Muneera* ina yinki sosai



A tare suka duka da niyar dauko nikaf din da ya fadi , sai dai ya rigayeta dora hanunsa a sama hakan yasa ta kasa karasa nata hanun sanan ta kasa dagowa


A nitse ya dago fuskarsa cikin sa'a kuwa suka hada ido hudu da shi da sauri ta sada kanta suka kuma mikewa a tare ,

Kara matsawa yayi kusanta ya gyara nikaf din sai gani tayi yana nufo fuskarta da niyar ya daura mata

Abin mamaki KO motsi kasawa tayi ya kama ya daura mata nikaf din a fuskarta , abinda tunda yake bai taba ba domin yana dage mata nikaf din suka kuma yin ido hudu da yayi saurin lumshe idanuwansa wa'inda tini suka fara karbar sakonnin idanuwan *Yar Mahaukaciya*


Cikin mutuwar jiki ya ce " mu tafi Maman Mubasshir na kiranki


Yar Mahaukaciya ta zaro ido ta ce " Lafiyarta? Mai ya samu Maman Rahma? Bata jin dadi ne?


Mubasshir ya zuba mata ido irin yanda ta rikice take maimaita masa tambayar dake nufin abu daya a karo uku, wai kuma shi ya ce mata *Maman Mubasshir* ita kuwa tace masa wani *Maman Rahma*

Tabo hanunsa da tayi ne ya tunatar da shi fa ya shiga tinani , firgigit yayi yana fadin " No lafiyarta lau tana dai kiranki


Yar Mahaukaciya ta juya tayi salama da Fati kawarta suka juya suka shiga mota ya kama hanya ya harbata titi


Tafe yake yana tinani kala daban daban a zuciyarsa , haka bangaren Yar Mahaukaciya domin taga ba hanyar zuwa gida ya kama ba , aman bazata iya yi masa tambayar inda zai kaita ba , ta yarda da shi


Sun kusan minti arba'in a hanyar sanan suka iso wata babar unguwa Wace da gani ka san wanan unguwa ta manya ce, zama ta gyara ta kara buda idanuwanta tana karewa wanan unguwa kalo a ranta ta ce " Kai Lagos da abin mamaki take



Tsayuwar motar ne ya fargar da ita ta zubawa kofar gidan da suka tsaya ido , har wani kara murza idanuwanta take



Cikin dakakiyar Murya ya ce" fito


Yar Mahaukaciya gabanta ya fadi ta kali Gabas da yama , kudu da arewa ba kowa irin unguwar nan ce ta yan gayu KO ihu kayi iya kai zai tsaya , ta kuma kalon kasa taga ba kasa bace ta ajiye wata nanauyar ajiyar zuciya a ranta tace" Maman Rahma baga irinta ba , yanzu KO wani abin ya sameni a wajen nan ai bazan iya guduwa dan kuwa wanan takalman da kika sakani sakawa yayi min nauyi


*Wai bazaki fito ba?* Mubasshir ya maimaita fuskarsa a daure


Gaba daya jikinta bari yake , haka ta kokarta ta fito tana Jan kafa ta bi bayansa domin bai shiga gidan da mota ba ,


Kofa kanta sai da suka shiga uku a ta hudun ce ya dora hanunsa kana ta bude , itadai binsa take kawai bata ce komai ba har suka ISO wani banban waje mai kyan gaske , sai a nan ta fara ganin mutane kuma abin mamaki harda tsofafi



Wata tsohuwa ta hango tana kokarin tashi sai dai kusanta ta zubar da ruwa ga yanayin wajen shi kansa santsin ne da shi , ga santsin ruwan , Ai bata san lokacin da ta shige gaban AA Mubasshir dake tafiyar kasaita ta nufi wanan tsohuwa da gudu ta tarota gaba daya ta rungumota a jikinta tana fadin " Mama dan tsaya na taimaka miki karki fadi


Cikin ikon Allah tsohuwar bata kai kasa ba Yar Mahaukaciya ta kamata ta canza mata wajen zaman ta ciro dan kwalin kayan makarantarta ta gogewa tsohuwar nan hanu da baki sanan ta kakabe mata jikinta ta kara gyara mata zamanta


Tunda ta shige gabansa da gudu ya tsaya yana kalon KO itama irin na Shalan ne wato taji tsoron tsofafin mutane koma yace kyankyami


Abinda ya gani ne ya saka shi maida hankalinsa a kanta , mamakinta bai gama gushewa ba sai da yaga tana gogewa gogo fuskarta harda majina , ya kara maida hankalinsa ganin sai labari take bata ita kuwa ta dage sai dariya take baki ba hakori , ji yayi gaba daya zuciyarsa tayi sanyi , wata nutsuwa ta sauko masa a cikin ransa Wace ya rasa ta maicece , wani farin cikin ganin gogo na dariya ya sakashi shima yin dariyar sanan ya matsa kusan su ya dan tsuguna yana kalonsu cike da sha'awar yanayinsu



Yar Mahaukaciya gaba daya ta ma manta da shi tana kokarin ganin gogo ta daina yi mata labarin akoy aljana a cikin gidan ,,

Juyowa tayi a hankali tana nuni da hanunta tana fadin kinga Gogo gidan nan ba wata aljana sanan koda akoy aljanar akoy adu'ar da mamana ta koya min idan kinyita to fa aljanar nan zata kone , ido hudu suka kuma yi da Mubasshir dake kalonsu a tsugune domin sam bata san yazo gurin ba


Hadiye maganarta tayi tana kokarin daura nikaf dinta dan gudun baiwa gogo tsoro har cire shi tayi


Mubasshir ya Mike a hankali yana fadin mu tafi ya nufi hanyar fita itama ta kama nikaf din ta daura sanan ta biyo bayansa




Tafe suke a mota yana yi mata gargadi KO nace kashedi kan ta kiyaye harkar maza , ta fita a harkar maza ta cire maza daga ranta


Yar Mahaukaciya ta dago kanta ta kale shi


Ya ce " Yes ki cire maza a ranki , idan har mazan ne kin damu da su har haka kawai ki fitar da miji guda aman fa na hane ki da zance na hane ki da sauraron maza a titi ba ruwanki da mazan makarantar ku


Ta kuma kalonsa a ranta ta ce" to mai yake nufi da na saka maza a raina? Kuma na fitar da miji aman ya hanani kula su to ta yaya zasu soni ma a haka?


Mubasshir ya ce" Malama ki kali gabanki gindaya miki sharuda ne nake dan gudun gobe kiyama Allah ya tambayeni kan amanar da aka bani domin ni din nan ni ne tamkar *Mahaifi* a wajen ki a yanzu dan ni nake da ikon aurar da ke dan haka ki kiyaye bana son na kuma yi miki magana kan harkar Maza ( Toh fa kaji ikon Allah , sai Baba Mubasshir )


Har suka iso yana haikar baki Wanda ta gaji ta kontar da kanta jikin madubin motar cikin ikon Allah baci yayi awon gaba da ita




Suna isowa Wace Maman Mubasshir ta saka ta zo takanas tun daga maroco dan siyan kayan dakin Yar Mahaukaciya da kuma gama shiryata ta fito daga cikin falon ita da wata mata a kusanta Wace ta dan darata da tsayi ga wani irin fari da gareta idanuwanta da farin glas


Har bakin motar ta rakosu sanan tayi nuni da motar Mubasshir Wanda ya fito ya nufesu dan su gaisa


Yana isa ya dan risina dan duk da bata wani tsufa ba ya san zata haife shi hakan yasa ya risina ya gaishe su


Hajiya Fadimatu ta ce " yawa dan Fadimatu kaga Hafsat matar da ta hadawa yar gidan Mr President dakinta , tazo Nigeria ne na nemeta nima


Mubasshir ya ce" Masha Allah Maman Mubasshir , sanan ya ci gaba da fadin" yarinyarki tayi min baci a mota bara na dauko sakona na koma office ,


Yana gama fada ya juya ya nufi cikin falon inda Hajiya Fadimatu tayiwa su Hajiya *Rafi'at* salama kan sai tayi mata dabara ta zaba sai ta sanarwa *Hafsat* ta nufi motar *AA* dan ta tashe da yarinyarta su kuwa suka shiga wuleliyar motarsu suka kama hanyar tafiya.







Wai shin wacece *Hafsat da Hajiya Rafi'at?*


I don't kwnow , LV u asosai
[13/11 16:42] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







51


Cikin nutsuwa ta mika hanunta tana tashin Yar Mahaukaciya Wace tayi nisa cikin bacinta na gajiyar fadan AA Wanda bata san abinda tayi masa ba


Firgigit ta farka da adu'ar tashi daga baci a bakinta tana fadin " kayi hakuri

Hajiya Fadimatu ta zaro ido ta ce " Yayi hakuri? Mai yayi miki yarinyata?


Yar Mahaukaciya ta saki ajiyar zuciya Sanan tayi murmushi ta ce " Mamana Ashe mun karaso , bacine ya dauke ni nayi zaton Yaya ne ke tashina,



Hajiya Fadimatu ta ce " eyah, lafiya yau aka sauko da wuri haka?



Yar Mahaukaciya ta ce " no bamu sauka ba , yaya ne yace kina son ganina



Hajiya Fadimatu tayi jim , itadai tasan bata tura shi ba aman kuma bazata karyata shi ba gudun kar ta raina shi KO zuwa gaba hakan yasa ta share tana fadin " fito mu tafi ki huta kafin yama tayi yata



Daidai sun fito shima ya fito ya karasa yayiwa mahaifiyarsa salama ya juya akalar motarsa dan komawa office


Yana isa secretariar sa ta tarbe shi da dumbin takardu ta fara zano masa jama'ar da suka zo baya nan da sakon'nin da aka badar , tana tsaka da zanawa ya ce " Mariam kije gida ki huta



Mariam ta zaro ido cike da mamaki tana kalon bayansa da ya juya ya shige office dinsa domin tunda suke ba'a taba tashi kasa da karfe biyar ba , don kuwa AA akoy son aiki sai gashi yau tun kafin shi ya tafi ita ya salameta kuma da alama lafiyarsa lau , tayi ajiyar zuciya a fili ta ce" alhamdulilah ni ma sai naje na kula da gidana da wuri yau





Bayan shigarsa da kamar minti ashirin sai ga Abdul abokinsa yayan Sahla ya shigo office din da salama


Mubasshir ya dago kansa yana amsa salamarsa sanan ya sauke kafafuwansa ya Mika masa hanu sukayi musabaha



Abdul ya nemi waje ya zauna yana mai ajiyar zuciya


AA ya kare karantarsa ya lura duk ransa a jagule yake ya ce" freind yaya dai?



Abdul ya kale shi cikin yanayin tausayi ya ce" Hajiya ta koreni na koma ta kuma korata da kyar na samu ta yafe min aman tace kawai na manta da yarinyar nan domin tayi min nisa, ni na kasa gane wani irin nisa tayi min indai ba auren wani tayi ba KO mutuwa tayi bata duniyar? Nayi nayi ta fada min inda yarinyar nan take aman fafur Hajiya ta kiya taki ta saurareni please freind ka saka baki wly ni ban san mai nayi mata ba



Mubasshir ya yatsina fuska yana matukar mamakin Abdul kan mace ne yake kokarin yin kuka? Ya ce" wai wace kake nufi?



Abdul ya nisa ya ce" *Rahma* nake nufi freind , kuma da ta wani takarkare take hanani sanin inda hasken idaniyata take ta manta ta sanadiyata ta santa ne????




Mubasshir ya gyara zama ya ce" oh yarinyar nan , Au bata gidan? Toh ban gane ta sanadiyarka ta Santa ba , shin ba ka fada min cewar jikar Hajiyar bace?????
[13/11 17:44] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







52

Abdul ya dago kansa ya dubi Mubasshir ya tuna eh fa ga abinda suka fadawa Mubasshir aman gaskiya shi zai fada masa gaskiyar zancen KO ya kama masa Hajiya ta fada masa inda Ta boye masa Rahmarsa , cikin alamar dan jin kunya ya ce " No ba jikarta bace, hasalima bata hada komai da ita ba , ranar da na fara yin tiyata a rasun nan ranar da bazan taba mantawa da ita ba a ranan na hadu da ita , sanan a ranar hajiya ta ganta , yaron da ya rasun danta ne ,,,..............''''''''''''',,,,,,,,,,,,,nan ya kwashe duka yanda akayi har daukanta da sukayi shi da Hajiya Hawau ya fadawa Mubasshir Wanda yake sauraronsa kamar ana kara yi masa bita ne kan abinda aka karanta masa



Mubasshir ya ce " kuma haka kuka dauki yarinyar da baku san KO wacece ba , wada ta shigo maka asibiti da yaro jiki a farfashe? Shin idan fa wata muguwa ce KO sato dan tayi?


Abdul ya kawar da kansa ya ce" she is innocent, tabas Rahma ba muguwa bace, sanan kamila ce, kuma nitsatsiya ce, domin da muguwa ce a zaman mu da ita da KO ta yaya sai halinta ya fito



Mubasshir ya kuma jefo masa tambayar " kana sonta ne?


Abdul ya gyara zama yace" ina sonta tamkar yar uwata ta jini, ina jinta a jinin jikina,


Mubasshir ya ce" ya akayi ka gane cewar kana sonta? Mai kake ji har ka gane cewar sonta ne kake?


Abdul ya dago ya kuma kalon Mubasshir Wanda daman shi yake kalo, da alamar mamakin tambayoyinsa ya ce" kafi kowa sani domin kai har kayi aure KO?



Mubasshir ya koma ya jongina da kujerar da yake zaune ya lumshe idanuwansa ya ce" kafi kowa sanin KO auren mai nayi,kafi kowa sanin amintaka ta ci karfina har na kasa yin musu da abinda ya zamto tamkar a cikin duhu nake, ya kuma dago kansa ya ce " freind tell me dan Allah mai ake ji? May be na dade da fara son matata rashin sanin inda so din soyaya ya nufa ya hana ni ganewa



Abdul ya ja ajiyar zuciya ya ce" tabas kai namiji ne mai kokari, jarumta, na yarda da jarumtar ka , sanan na gode da abinda kayi domin ni, nima Allah ya bani ikon yi maka abin alkhairi , ya nisa ya dora da cewa" idan kaga abin sonka kafin ka furta masa kalmar so zakana ji gabanka na faduwa, koya ka nisanta da shi burinka ka dawo ka gansa, koda mumuna ne tofa zaka Ganshi ba Wanda ya kaishi kyau, da zarar kun hada idanuwa sai gabanka ya fadi, baka gajiya da kalonsa, ka tsani wani ya rabe sa balatana namiji, ka tsani wani ya kale shi, ka tsani....



Cikin Sauri Mubasshir ya furta wait wait wait yana daga hanunsa sanan dayan hanun yana laluba gashin kansa ya mike da sauri ya debi ruwa ya rufe ido ya shanye tas sanan ya ajiye kofin ya juyo yana kalon Abdul Wanda yayi tsamanin KO kwaruwa yayi ya ce" aman ai idan amanarka ne ma kana iya jin irin haka KO?



Abdul ya ce" koda kanwarka ce bazaka ji irin hakan ba , ina tsaka da zana maka ka katse ni , naci gaba ne?


Mubasshir ya shiga girgiza kai uwa karamin yaro ya ce" No barshi haka is OK



Abdul ya ce" gaba daya abinda na zana maka ba Wanda bana ji a tatare da yarinyarnan , dan haka ya hade hanayensa ya ce" ka taimakeni ka taya ni ta fada min inda take




Mubasshir ya rintse idanuwansa ya bude ya ce" zanyi kiranka zanje na ganta karka damu



Abdul ya taso cikin jin dadi ya rungume Mubasshir yana yi masa godiya sanan yayi masa salama ya fita


Yana tafiya Mubasshir ya shiga zaro ido tamkar sabon kamu ya fada saman kujera jagob ya tatara gashin kansa ya cakula ya rufe ido yana furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une , inalilahi wa'ina ilaihi raj'une , ya buga hanunsa saman table ji kake taratsatsa domin kolba ce ta fashe

Zumbur ya kuma mikewa ya dauki ky din motarsa hanunsa na digar jini aman bai damu ba ya fito ya shiga motarsa ma'aikatan sai kalonsa suke kowa na mamakinsa aman ba Wanda ya nufe shi dan ba fuskar hakan ,


Tuki yake na ganganci kansa ba hula sanan ba Babar rigarsa a jikinsa farar Riga ce kawa ta ciki, sai dogon wandonsa na shada , idanuwansa sunyi jajajir haka fuskarsa a murtuke , bai san inda zai nufa ba hasalima burin sa ya ganta a gabansa ya kali fuskarta sanan ya furta mata cewar shi fa sam baya sonta yana kokarin kare mutuncinta ne ,


Wani irin burki ya taka aman ina sai da ya bigi Babar motar da ta kwaso kaya take gabansa ji kake piiiiiiiiit karar oda inda kansa ya fada , jama'a duk suka fifito hanu a saman kai suna furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une

Da Sauri direban babar motar ya taka birki duk suka firfito suka nufe shi





Zaune suke suna cin abinci wayar dakin ta dauki kara , haka kawai ta ji gabanta ya fadi ta mike da Sauri ta nufi wayar ta daga , sakin wayar tayi sanan ta tafi luuu zata fadi tana fadin inalilahi wa'ina ilaihi raj'une


Da Gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana fadin mama lafiya??????????????????????????????????????????????????????????????????











😱😱😱😱😱😱
[16/11 09:07] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*







53
Da gudu Yar Mahaukaciya ta tareta tana faman fadin " Mama lafiya? Aman ina sai da suka kai kasa dan kuwa karfin ba daya ba, cikin Sauri ta rarumo wayar ta kanga a kunanta tayi salama


Daga dayan bangaran likitar take shaida mata anga numberta da kuma ta gida a cikin wani litafi a motarsa yana asibitin Jarumai aman bai ji ciwo sosai ba


Yar Mahaukaciya cikin sarkewar harshe ta ce" wa .....wane yayi hatsarin?"


Matar ta ce" *AA MUBASHIR* "



Yar Mahaukaciya ta furta inalilahi wa'ina ilaihi raj'une sanan ta FITA da sauri tayi Kiran direban gidan kafin ya fitar da motar ta haye sama ta dauko hijabin Hajiya Fadimatu da nata sanan ta sauko cikin gudu gudu ta tsuguna kusan Hajiya Fadimatu ta ce" Mamana yaya bai ji ciwo sosai ba , please ki tashi mu tafi wajensa plz mamana"


Hajiya Fadimatu da sai a lokacin ta dawo daga sumar tsoratar da tayi na jin gidan jininta a asibiti ta mike da kyar ta zura hijabin suka fito suka kama hanyar asibitin




Suna isa aka kaisu dakin da aka kontar da shi cikin girmamawa


Tsayuwa tayi tana kalonsa tana tofa masa adu'a tana yiwa Allah godiya da hatsarin nasa bai zo da tsanani ba , waigowa tayi ta kali doctern ta ce" docter bacin nan na lafiya ne?"


Docter ya ce" eh ma'am alurar baci muka yi masa dan ya huta domin da alama tinani yayi masa yawa dan kuwa shi kadai ya zo ya bigi motar sanan an duba motar lafiyarta lau, kuma shi ba shan wani abin maye yayi ba, ba earpice a kunan sa, kuma kwakwaluwarsa lafiyarta lau kawai dai cikin biyu ne KO wani abin ya taba masa

Please Login or Register in order to submit comment