Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kuma muryar sa

Ganin da Yar Mahaukaciya tayi Fati na neman faduwa ya sa ta saka dayar kafar tata da ba kunshi ta ce" Sis kina ji na aljanu ne fa


Fati tayi firgigit ta ce" maiye na aljanun?


Yar Mahaukaciya ta nuna mata kunshin tana wani zuru zuru da idanuwa tamkar zasu fado kasa

Mubasshir ya saki Hanun nata ya mike yana fadin ki fadawa Hajiya na fice sai tomorrow insha Allah


Yar Mahaukaciya ta gyada masa kai ba tare da ta amsa ba dan kuwa jira take ya FITA ta wanke kunshin nan , ya ce na aljanu ne kar taje su tashe ta tsakar dare KO su sace ta


Yana FITA Fati ta juyo da sauri uwa Wace aka kuna ta ce" hadade kakarfa , fari mai dogon hanci mai tarin suma , mai manyan idanu , dogo, mai karancin fara'a, mai aji , mai ,,,,,......,,,, cikin Sauri Yar Mahaukaciya ta ce" please ya isa haka malama ki mike ki wanke min wanan abin tun kafin su halaka ni



Fati ta ce" sanan ya fiki kyau da zazakar murya


Yar Mahaukaciya ta ja tsaki ta ce " shin zaki dawo duniyar mutane ki manta ta aljanin nan ki wanke min abin nan KO sai ransu ya bace?



Sai a lokacin Fati ta bada hankalinta kan Yar Mahaukaciya ai kuwa ta bushe da dariya ganin yanda take zufa ance mata kunshinta na aljanu ne ,

Da kyar ta samu ta lalabata suka ci gaba da zana kunshin suna dan labarin su







Yana fitowa suka hadu da Idriss ya dawo daga daukan bakin Hajiya Marhaba ,


Mubasshir yayi murmushi ganin yanda yake hada rai wai ya biyo rana yace" sai abokin ango


Idriss ya turo baki ya ce" kai ni fa yayan Sahla ne tohm


Mubasshir yayi dariya ya ce" ni kuwa yayanka ba , tunda ni yayan Rahman Hajiya ne


Idriss sai da yayi wani tsam ya tuna ramatunsa ya dafe kai ya ce " oh my god ina kokarin gyara auren wasu zan bata neman nawa auren ,


Mubasshir ya kale shi ya ce " ban gane ba


Idriss ya juya kai ya ce" idan na daidaita komai zaka gane abokina sai an jima zan shigo gidan ,

Ya juya da Sauri ya nufi bangaran Hajiya yana fargabar haduwarsu






Mubasshir ya daga kafada ya nufi motarsa duk da wani bangaran na zuciyarsa na yi masa hudubar ya bi bayan Idriss , wani bangaran kuwa ya ce " kaje kayi mai? Ba abinda ya shafeka da abinda baidameka ba








Anya kuwa???🤔🤔🤔 muje zuwa










[29/9 06:48] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




27


Lolz sis na samu sakonki na gode da soyayarki gareni Allah ya jibanci lamuranki sanan ya raya mai sunana love u irin da yawa din nan













Ci gaban labarin

Tunda garin Allah ya waye ba abinda kake ji duk gidan redion da ka kamo sai sanarwar daurin auren AA nera, haka talabijin KO Wace tasha sai suna yada labarin daurin auren nan a karfe goma na safiyar Asabar , haka masu sayar da jaridu sai buga na abin shirye shiryen da ake na bikin , sosai komai ya kankama lokacin daurin aure kawai ake jira



Cikin gidansu Mubasshir ba masakar tsinke , kowace ka hango sai kaga ta kusanta ta gyasa ta kwaliya kala daban daban baki ta KO ina ,

Dakin Hajiya Fadimatu na shiga inda abin mamaki na tarar da Mubasshir saman salaya Haka mahaifiyarsa sai jan carbi take da doguwar bakar abayarta da hijabinta har kasa , shi kuwa da farar jalabiyarsa mai dogon wando , gaba dayansu sun dukufa sai jan carbi suke , sai da karfe takwas tayi sanan naga sun yi adu'a sun shafa,


Mubasshir ya taso ya tsuguna gaban mahaifiyarsa ya ce " Maman Mubasshir ina kwana, kin tashi lafiya? Ya gajiya,



Hajiya Fadimatu ta dora hanunta na dama saman kansa ta ce " Lafiya lau Dan gidan Fadimatu , Allah ya yi maka albarka, ya sanya albarka a auren nan naka dan nabiyin rahamati


Mubasshir ya kuma sada kansa bai ce komai ba ,

Tayi murmushi ta mike tana fadin ka konta kayi bacinka domin ka san bazamu dauki al'adar nan ba , sai an daura auren ka fito kaji?


Mubasshir ya ce " an gama maman Mubasshir

Ya mike ya haye gadon mahaifiyarsa ya konta da niyar hutawa, ita kuwa ta shige dakinta mai kayanta ta shiga kintsawa .








Karfe goma na safiyar Asabar kofar gidansu Sahla kai kace idi ne ake ba masakar tsinke ta ko'ina taron jama'a ne ke kai kawo ka rantse da Allah ka ce wani dan yaki ne za'ayi irin yanda jami'an tsaro ke kai kawo a wajen

Cikin lasifika na tsinto daurin auren *MUBASSHIR MUBARACK da SAHLA ILYIAS* bisa sadaki naira dubu hamsin dan samun albarkar aure , sai barka ake ana musabaha


Cikin gida

Hajiya Marhaba ta mike tsaye ta ce " what? Dubu hamsin? Kudin sadakin yata? Bazai yiwu ba


Kawarta dake zaune kusa da ita ta ce " dubu hamsin uwa auren yar jeji? KO dai ba Mubasshir AA da ake fada bane?


Hajiya Marhaba ta juyo ta ce" ai idanuwanki sun Nuna miki lefenta dan Haka karkiyi kokarin yin gaba da zancen, shi kuwa Elhaj ai zai shigo ne ya sameni dan wly sai ya kara min bazai yiwu na karbi dubu hamsin nayi yaya da su?

Haka tayi ta mitarta gaban kowa ba abinda ya sha mata kai ,


Bangaren Sahla tunda aka daura aure take buga number Mubasshir aman a kashe wata irin murna take cikinta wai a yau ita Sahla zata amsa sunan Sahla Mubasshir AA tap ta zama babar mace Kenan dan kuwa KO First lady ,

Tabota Alisha tayi ,

Sahla tahi firgigit tana kalonta


Alisha ta bushe da dariya ta ce " angon namu yaki zuwa KO lafiya?


Sahla ta ce" kinsan shi da jama'a nasan bai samu hanyar shigowa ba
Suna tsaka da maganar wata kawarta Nusaiba ta shigo ta ce" bby wai kinsan kudin sadakinki dubu hamsin ne?


Sahla ta ce" kutumar ubancen dubu hansin fa ? Ta rarumo wayarta ta danawa mahaifiyarta kira

Tana dagawa ta ce" hello mom wani irin dubu hansin? KO auren da freind dina ya yi kudin sadakin yarinyar dubu dari biyu ya kai


Hajiya Marhaba ta ce" bby kontar da hankalinki dadynki zai shigo ne yanzu ya ce ya kawo kudin dubu dari uku ne so ki kontar da hankalinki ki fadawa kawayenki ga abinda ya bada



Hakan kuwa akayi ta dage tana fadin ai ga abinda ya bayar ( daga baya ba)


Bacinsa yake sha hankali konce tamkar ba ango ba har sai da karfe 12 tayi Hajiya Fadimatu ta hayo saman dakin ta tashe shi


Da adu'ar farkawa daga baci ya farka yana kokarin zama


Hajiya fadimatu ta ce" bacin ya isa haka, Idriss sun dade da zuwa , ka tashi dan ka shirya ka je ka gaisar da kakannin yarinyar da iyayenta sanan kaje musu da intis zata shirya amarya


Mubsshir ya Mike yayi bayi dan cika umarnin mahaifiyarsa












Sowie kadan ne 😁😘😘😘
[2/10 09:44] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




28

Wani ma yayi rawa balatana dan makadi, sisterna rabin jikina , ke din ta daban ce , wanan babin gaba daya naki ne Madame Abdul Kader *Maman Imran* love u so much











Labari

Ya dade yana wanka dan saboda sai da ya shiga ruwan zapi sosai ya wanke harda kansa ya dauro banban towel ya fito , yana fitowa ya ga Maman sa ta ajiye masa kayan da zai saka da komai saman bed

A nitse ya zauna ya busar da gashin kansa uwa na mace dan santsi da shekin baki ,ya dauki mayukan gashi ya shafa
Shi da kansa yake nanade kansa ya saka macaji ya daidaita shi yana jin haushin saurin taruwar gashin kansa kawai sai ya aske ya huta, kuma sai ya fito


Cikin nutsuwa yayi shirinsa ya gama ya dauko kayan , yana dagawa yaga manyan kaya ne gari da yar ciki da hula sun sha wani mahaukacin zubi a jikinsu hular kanta wani irin aiki ne aka yi mata sosai ta hadu , abinka da mai son manyan kaya , yayi murmushi a fili ya ce " Maman Mubasshir Kenan



Su Idriss na suna ta labari suna dariya su uku daidai suma sun sha manyan kayan su sai anuri suke abinka da ranar fito na fito

Mubasshir ya sauko cikin takun kasaita tamkar dan Sarki daidai da takalmin kafarsa na shadar nan ne haka agogonsa mai zubi ya sha hularsa , yana ganin su ya saki murmushi


Nura ya ce " waouh , waouh , waouh , wata miyar sai a makota , wai dan Allah kaine kuwa?


Mubasshir ya Mika musu hanu daya bayan daya suna gaisawa sanan cikin murmushi ya ce " angoncewa ce



Idriss ya sha kunu ya ce " kai kasan gaban manya fa kake


Mubasshir ya ce " meye manya? Yana wata yatsina


Ramadan ya ce " ya ilahi sirikinka ne fa


Mubasshir ya mike yana fadin " kunga mu yanzu mun zama masu iyali ku tashi mu nufi gidan iyayena na gaisar da kakata sai iyayen matata a al'adar chadi


Suka Mike suna murmushi , fitowarsu keda wuya wanan mawakiyar ta larabawa ta kwasa sai koda Mubasshir take , dago kansa da zai yi ya hango gimbiya Mubinah yar gidan sarkin Makah cikin shiga ta alfarma ta zuba zinari da wani mahaukacin lesh fari gata fara sai daukan ido take ,

Suna fitowa ta mike ta nufo Mubasshir Wanda sai da gabansa ya fadi a ransa ya ce " ya akayi mai martaba ya BArTA ta biyo su mai girma Barhan?

Tana isowa ta rungume shi irin gaisuwar larabawan nan sanan daidai kunan sa ta rada masa " na zo na raka mijina gidan amaryarsa da tayi min shigar wuri kafin na shigo



Mubasshir ya dan saketa ya lakaci habarta yayi murmushi sanan ya juya wajen iyayensa yayi Saurin tsugunawa yana gaisar da su


Hajiya ta taso ta kama hanunsa ta daidaita masa hularsa ta ce " Alhamdulilah yarona ya girma , Allah ya kade baki ( kunsan larabawa suna mugun gudun baki shi yasa daga sunyi magana sai kaji sun ce Masha Allah , 😁 )


Haka sukayi ta saka masa Albarka sanan suka juya inda wasu motoci kwaya hudu a jere farare tas sai sheki suke , yau yau aka fitar da su da ka gani ka san an cashi kudi a nan ,

Karar tafiyar doki naji na waiga wani ne ya taho da dokina biyu yana jaye da su da irin runfar nan ana jaye da su , sai karar kacaukacau suke sun mahaukacin sha ado na zinari sai kara suke


Mubasshir ya juya ya sauke idanuwansa saman Mubinah dan kuwa ya san wanan aikinta ne ya gala mata harara dan ta sani sarai ya tsani hawa doki KO a can su biyu suke hawa KO da ita KO da wani a gefen sa ,

Tayi murmushi cikin harshen larabci ta ce" kar a yada al'ada ka sani sarai da a can ka yarda kayi aurenka da sai ka zaga gari a saman doki dan haka ya sa na shirya wanan KO ba komai ka girmama al'adar mai martaba uba a wajenka



Da haushi haushi ya taka ya hau itama aka kama mata ta dare tamkar itace amaryar ,motocin nan suka saka su a tsakiya , mai girma Barhan ya karaso ya rufa masa alkyaba aka cire masa hular aka rufa masa ta alkyabar nan dan kuwa haka al'adarsu take


Cikin nutsuwa suka kama hanyar gidan su Sahla



Hajiya Hawau ta sha dinkinta na shada ta hade harda kafa daurin dan kwalinta sun malaya manyan tabarmi a tsakar gidansu da kawayenta tsofafi sai labari ake ana shan fura mai cukui sai kanshi take ga dadi abinka da tsohuwar da ta san darajar baki duk Wanda ya shigo Yar Mahaukaciya da kawarta Fati sai su zuba furar a cikin kwarya da ludayi su Mika masa , suma sun sha dinkinsu na shada duk da ba wata kwaliya suka yi ba dalilin ainkin da suke yi


Suna tsaka da shan dariyarsu suka jiyo karar ganga da kuma muryar mace tana ta ISO da larabci tana wakarta , ga Wanda ya iya ya san dan gata ake wakewa ga Wanda bai iya ba kuwa sai dai ya gyada kai dan dadin wakar


Fati ta kama hanun Yar Mahaukaciya ta ce" kawata ai angwaye ne



Yar mahaukaciya ta ce" mai ya kawo angwaye nan kuma a yanzu?


Fati ta ce " oho o mu dai mu shirya tarban su


Hajiya Hawau ta fado kincin din ta ce" Ramatutu ai ga Dan Aljannah nan ya ISO da tawagarsa kinga wa'incan kwaryoyin masu zane su za'a dauko a zuba musu furar , aman ai ke kinsan yanda ake dama ta dan Aljannah dan haka a dauko duka cukuii din da nonon a dame musu yi maza yar Aljannah


Yar Magaukaciya tayi murmushi Ganin irin yanda Hajiya ta rikice ta ce " Hajiya ai na dame ta tun dazu Idriss ya ce a aa zuwan su duk da nayi zaton ko wasa yake mun dai dame kuma yanda kike sonta , aman ciki zasu shigo kinga baza a bar Dan Aljannahn ki a wajeba KO?


Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Allah yayi miki Albarka bara na sauke su a baban falon , ku kuwa ku jera furar ku kawo musu
Ta juya tana kara daure dunkunkumin dan kwalin da ta dunkuma


Yar Mahaukaciya haka kawai ta tsinci kanta da tsoron hada ido da Dan Aljannah a wanan ranar , mutun a ranar da ba ta aurensa ba ma yana mugun daukan ido bare a yau?


Fati ta ce" Malama Hajiya garin kidima har kofina take ambato 😁



Yar Mahaukaciya ta ce" Dole Hajiya ta rikice dan kuwa dan gatanta ne


Haka suka dauko kwaryoyin suka kara darwaye su , gasu kananuwa masu shegen kyau da ludayinsu masu kyan gaske suka jere a saman wani baban faranti na silba mai shekin gaske , sanan suka ringa zuba furar nan suna saka ludayin a ciki , sai da suka gama

Yar Mahaukaciya ta ce " plz my kawali ki dauko na Dan Aljannah dan Allah



Fati ta zaro ido ta ce " mai kike nufi da hakan? Yayanki ne fa kuma kin sani sarai kar na fita na zubar garin kalonsa


Yar Mahaukaciya ta san sarai zata aika hakan yasa ta dauko wani farantin dan madaidaici ta zuba furar a wata kwaryar mai murfi sanan ta dauko ludayi ta dora a gefe ta dauko mushoir ( hankici ) sabo fil fari kar ta dora shima a gefe ta gyara komai

Fati dake kalonta ta ce" gaskiya al'adar Hajiyar gidan nan na mugun birgeni , koman ta daban ne sanan ta koyawa yar Jikanlen ta


Yar Mahaukaciya tayi dariya tana dora farantin Dan aljannah a gefen sauran furar ta ce " kama mu tafi malama kar suyi tafiyarsu



Suka kamo suka fito suna tafiya cikin nutsuwarsu suna fitowa kanshin ya daki hancinsu daga fatin Har Yar Mahaukaciya suka dago suka zubawa bakin dakin kalo

Idriss da dan Aljannah sun saka Hajiya a tsakiya ita kuwa sai washe hakora take daga gefe guda kuwa Mubinnah ce sai fifitu ake yi mata ta sha kyau har ta gaji, sai su Ramadan da Nurah a wata kujerar abin gwanin ban sha'awa


Fati ta juyo ta kali Yar Mahaukaciya Wace itama kamar ta fadi dan yanayin Mubasshir ya kidimata harda Idriss abin ya mugun haduwa kawai sai taji eh lale tana iya yin soyaya da shi dan kuwa ya mugun birgeta a yau

Fati kuwa ta kidime ta haukace ta ce" kawata kina ganin zinaria ce fa a jikinsu dan Allah ki duba ki ga irin yanda AA ya zama uwa Kwaï dan daukan ido



Yar Mahaukaciya cikin rada ta ce " ki nutsu mu basu juya tun kafin na kife a nan


Su duka suka dan saki murmushi sanan sukayi salama

Hajiya Hawau ta dago kanta ta amsa haka sauran jama'ar wajen

Cikin nutsuwa su Yar Mahaukaciya suka ajiye wanan farantin a saman table din dake ajiye a tsakar dakin sanan suka shiga dauka suna mikawa mutanen dakin , har sai sun duka har kasa su Mika musu hakan ba karamin birge hajiya Hawau da kuma su idriss yayi ba






🙆🏿
[2/10 09:47] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




29






Fati ta dauko ta nufi Mubinnah tana isowa ta dan risina ta Mika mata da Sauri mai yi mata fifitar nan zata karba Mubasshir ya daka mata tsawa " cikin harshen larabci ya ce" idan anzo waje ana anfani da al'adar su ce sanan nan gidan sirikai na kuma iyayena ne dan haka kar a kawo min batanci kin gane ?


Da sauri ta risina tana fadin Allah ya huci ran Dan Gattahn Mai Martaba mafi soyuwa ga gimbiya Mubinnah


Mubinnah duk da bata ji dadin yanda ya sacewa kuyangarta gwuiwa aman bacin ransa yafi komai daga mata hankali hakan yasa ta mika hanu ta karbin wanan kwabin da bata san KO na menene ba ta dan gyara zamanta tana shawara da zuciyarta shin zata sha ne KO aa


Su dai KO a ransu , Yar Mahaukaciya ta dauko farantin Mubasshir har a lokacin bata gama yi masa kalo ba tayi niyar bazata yarda tayi masa kalon kurula ba ,

A nitse ta nufi wajen da tafi jin kanshin sa , itama Fati ta dauko na Idriss ta nufe shi


Yar Mahaukaciya na isawa ta tsuguna har Kasa ta dago hanayenta ta mikawa Mubasshir dan farantin mai kyan gaske


Mubasshir ya zuba mata ido dan gashinta daga gaba ya dan leko kadan sanan bakinta sai sheki yake na mai mai maski da ta dan goga ,

Maganar idriss ya dawo da shi inda yake fadin" Malan kaga Karka wahalarmin da mata mana ka karba plz karka rama a kanta


Firgogit yayi dan kuwa ya fada wata duniyar tinani ya Mika hanunsa wajen karba sai da hanayensu suka gogi juna , ita kuwa Allah Allah take ta bar wajen dan jikinta har karkarwa yake jin baranbaramar da Idriss ya afka mata a gaban Hajiya harda bakin kunya sai ma da taji Muryar Ramadan na fadin" au kace kaima taka a gidan take , gaskiya kunyi mana wayo , wanan wayo har ina ? Gaskiya muma a san yanda za'ayi da mu


Da Sauri Yar Mahaukaciya ta janye hanunta ta Mike da gudu tayi dakinta tana haki


Mubasshir da Idriss gaba dayansu da ido suka bita , Mubasshir yayi dan daman bai rike hanunta ba , ji irin yanda take gudu ana kalonta ( inada tambaya , ina ruwanka hon)


Shi kuwa Idriss wata irin faduwar gaba ce ta ziyarce shi ta haka kawai a ransa ya ce " wai a nan a cikin zulumbuwar riga take lale akoy aiki a gabana ( to kaji 😏 )


Hajiya ta katse dan shirun da ya gilma ta hanyar fadin " tayi maka kyau idrissu , nace tayi maka kyau ka firgita min ya


Yayi murmushi ya ce " haba kakus ya zamu zo ki hada mû da fura ?


Ta ce " to dan nema ita ce da ni ehe 😏


Mubasshir ya ce " kyale shi hajiyata ni kadai na san darajar wanan dan haka kowama kar ya sha idan yana so



Haka sukayi ta barkoncinsu har dai Sahla ta gaji da Kiran mamanta tana fadan sun shiga wajen tsohuwar nan sun makale kar ayi mata abinda ba shi ba


Sahla ta ce " mom kiyi Kiran Yaya Idriss plz

Hakan kuwa akayi ta dana kiransa daidai zasu shigo falon nata ,

Salamarsu ta saka ta katse kiran jama'ar dakin na amsawa


Marokiyar ta rangada guda ta kwashi kirari da kuma isowar angon auta wato Sahla


Cikin nutsuwa suka tsuguna gaba dayansu kasa suka shiga gaisar da Su Hajiya Marhaba da kawayenta

Hajiya Marhaba murna kamar mai ,
Suna tsaka da gaisawa wayarta ta fara ringin

Ta dauka sai taga sunan bokanta ne inda ta rubuta hajiya bokatu ,

Tayi murmushi ta Mike ta dan matsa kadan ta daga


Daga dayan bangaran ya ce " na gama aikinki na aikawa mijinki yanzu yanzu zai aikata abinda na saka shi tunda kince kina so a cikin jama'a yanda kowa zai ganta a rana yanda ba Wanda zai so ta rabe shi KO?

Hajiya Sahla ta ce " kwarai kuwa boka yanzu ne daidai dan kuwa gaba dayan mutanen da nake so su ganta a tozarce suna wajen nan so kawai ayi aiki na cika


Boka ya ce " karfa ki manta kudin ki mai yawa ne


Ta ce " kar ka manta aikinka mai kyau ne idan har yayi kyau din ai kuwa abinda zaka samu har sai ya fi wanan


Ya bushe da wata mahaukaciyar dariya ya e " to bunsura sai na jiki , ya datse Kiran









To fa , kaka kara kaka , shin waye za'a tozarta a cikin mutane? Waye za'a wulakanta har ma kowa ya gujeta? 🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀🤷🏿‍♀ taku har kulun yar mutan Niger 😘😘😘😘
[9/10 10:01] Sajida: 🇳🇪Belles écrivaines du Niger



*'YAR 👧🏻*

*MAHAUKACIYA👹*

*_Na SAJIDA_*




30

*Jiki Alhamdulilah sisters na gode da adu'ar ku gareni love u*













Cikin takunta tamkar ba ita ce ta gama wayar ba ta juyo ta zauna , tana zama idanuwanta suka sauka kan Mubinnah Wace ita har ga Allah da farko bata ganta ba , gabanta taji ya fadi abinka da mai sakin magana idan ta raya mata ta kali Mubasshir wanda ya kagauta su tashi su bar dakin irin yanda matan nan kowace ta zuba musu ido ga uban surutu an cika su da shi ga wasu hotuna uwa Wanda aka gayace su gidan TV shi kam duk a takure yake


Hajiya Marhaba ta ce" Mubasshir wanan fa? Ban Santa ba


Mubasshir ya kara sada kansa kasa dan kuwa KO bai dago ba ya san da Wace ake magana


Idriss ya kaleta ya ce" Mom Wanan fa itace Mubinnah daya daga cikin yayan sarki


Hajiya Marhabah ta ce" wani sarkin?


Idriss ya ce" na Makkah mana mom


Hajiya Marhaba ta washe hakora ta shiga yiwa Mubinnah barka da zuwa jama'ar dakin ma haka , sanan kasa kasa sai surutu suke suna tambayar Kenan harda iyalan sarkin sun zo? Gaskiya Hajiya Marhaba ita tayi dace ,


Wani irin ihu suka jiyo , gaba dayansu suka yi tsit , suka kuma jiyo wani ihun da Sauri suka Mike Idriss ya ce " a nan ne


Mubasshirr ya kama hanyar fita shi da Idriss inda matan suka yi cirko cirko suna raraba ido dan kuwa kowanen su tsoron FITA yake ayi ba shi



Suna fitowa suke jin ihun daga wajen bangaren Hajiya Hawau ne Harda Alamar koke koke

Idriss ya sha gaban Mubasshir ya ce cikin haki" Malan dakata , mu fara Kiran yan sanda kafin mu shiga cikin gidan nan wa ya san Abinda ke faruwa a ciki, idan

Please Login or Register in order to submit comment