Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

.💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa_.

_story and writing_

By


*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*GODIYA TA TABBATA GA ALLAH MA DAUKAKIN SARKI TSIRADA AMINCIN ALLAH SUKARA TABBATA GA FIYAYYEN HALITTA ANNABI MUHAMMAD SALLAHU ALAIHI WA SALLAM*


*ALLAH NAGODE MAKA DA KASAKE BANI IKON RUBUTO WANAN TAKAITACCEN LABARI ALLAH KASA ZAMU AMFANA DA DARUSSAN DA SUKE CIKI AMEEN YA ALLAH*

*WANAN LITTAFI K'RK'IRA NE BANYISHI DAN WANI KO WATA BA INYAZO DAI DAI DA LABARINKI/LABARINKA, TO HASA SHENE KAWAI*👌.


*DUBUN GODIYA GA UWA TAGARI MAGANIN KUKANMU WATO SHUGABA ADILA (ANTY HAUWA MAMAN USAWAN) KEDIN TA DABANCE A CIKIN MUTANE 👌*.


*BAZAN GAJI DA MIK'A GODIYATA GA (DOCTOR MARYAM IBRAHEEM) BA SABODE KECE SILA😭*


*GODIYA A GAREKU WRITERS NA (AREWA WRITERS ASSOCIATION) FATAN ALLAH YAKARA HADE KAWUNANMU BAKI DAYA*


*INA TAYA KUNGIYAR MU ' MURNAR CIKA SHEKARA ALLAH YASA SHEKARA MAI ZUWA IDAN MUNADA RAI DA LAFIYA TAFI HAKA ' AMEN YA ALLAH*.



*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*


PAGE *ONE AND TWO*


_____Wata kyakyawar budurwa na hango sanye da , riga da zani kod'ad'u , da 'alamu sunji jiki sosai , amma kasancewar wanan budurwa kyakyawa, yasa ko yagaggun kaya tasa baya yimata muni , budurwar zatakai shekara goma sha biyar , tafiya takeyi cikin yanga da iya taku, duk a ganinta kaf cikin k'auyen (ZANKANA) itace wayayya, tunda ta doso gurin wasu samari suna shan rake, naji suna cewa saike Duduwa , 6ata rai tayi kana tace "wallahi duk wanda yakuma fad'amin wanan sunan saiyayi dana sani , cikin tsiwa take maganar, wani matashin saurayi ne ya taso yazo kusada ita yace " saike kyakyawa , washe hak'ora tayi tana dariya tace"yauwa Yasir ai kai kafisu mutunci,


Suna tafiya suna hira, har suka zo daidai k'ofar gidan su Duduwa , gidane mai zagaye da galan galan saboda bazaka kira gidan masu kud'iba saidai ace talakawa , bayan sunyi sallam da Yasir ta shige gida, tasami Umman ta 'tana tuk'a tuwo , yamutsa fuska tayi kana tace" waike Umma bakya gajiya da cin tuwo ? kullum tuwo ,wallahi ni nagaji cikin masifa take maganar , Umman ta da ko kallonta batayi ba tacigaba da tuk'a tuwon ta , Duduwa ce ta wuce d'akinta daya kasance mai katifar yayi ,ta janyo wata leda data mak'ale a mararta ,dan tasan hardai Umma ta ganta da ledar to saitayi mata nasiha , awara ce da yaji cikin farar leda , tanaci tana karkad'a k'afa tana mita, Umma ce ta k'wala mata kira ,seda tad'au lokaci sanan ta 'amsa , bayan ta goge hannunta ta fice zuwa gurin kiran Umman,


Tana zuwa Umma tace" ga tuwonki nan , kamar zata fasa ihu tace " ba yanzu zanciba sai zuwa anjima, tsayawa kallonta Umma tayi , tana tunanin girman kai 'irinna Duduwa, bayan Umma tagama tattare kwanukan abincin data zuba ta koma d'aki, bata ko kalli gurinda Duduwa ta tsaya ba , bayan sallahr isha'i , yaro yazo yana sallama , Umma ce ta amsa sallamar tare da cewa , waye? yaron yana daga k'ofar gida yace" Duduwa ake kira , kafin yaron ya k'arasa fad'ar sunanta ta fito cikin masifa Umma na tsaye tace" dan uwarka wacece Duduwar ? rik'e baki Umma tayi tana kallon ikon Allah tace" inkin gama masifar saiki tambayi waye mai kirannaki, bayan ta gallawa yaron harara tace"wai' injiwa ? yaron da tsoro ya kamashi yace " inji Yasir ne, da fara'a d'auke a fuskarta tace kace ina zuwa,



Bayan yaron ya fice, Umma ta dubi Duduwa tace"nidai nasihata dake shine kirik'e mutuncinki , wlh ke y'a mace ce mai rauni , tunda Umma tafara nasihar Duduwa ta had'e rai tace"Umma kullum kekenan fad'a kuma kinsan ' niba k'aramar yarinya bace, sanin halinta da Umma tayi yasata komawa d'aki , ita kuwa Duduwa kwaskwarima tayi tayi kwaliya tasa kayan sallanta ta fice zuwa gurin Yasir , tunda ta doso yajiyo k'amshin turarenta yafara fad'in, maraba da kyakyawa saike y'ammata murmushi takeyi tana sunkuyar da kai ,ammafa tak'i bud'e baki wai, saboda kar janbakin ya goge , bayan sund'an ta6a hirane yayi mata sallam , ganin bai mik'o mata komai ba yasata 6ata rai , shikuwa saboda tsokana yazagayo yace"kawo hannunki , a hanzarce ta mik'o , ganin wainar k'awai ce a leda tahau dariya , daganan sukayi sallama cikin farinciki,


Washe gari da safe , bayan Duduwa tayi sallah tazo gaida Umma , bayan sun gaisa ne Umma tace" maza tashi ki had'a wanke_wanke kiyi mana saboda yau inason zuwa anguwa ,da har ta6ata rai , amma jin Umma tace zataje anguwa yasata fara'a ta mik'e da sauri dandanan ta gama , lokacin Umma tagama shiri , dari hud'u ta bata kud'in cefanen abincin rana , tace "kafin ta dawo tasamu tagama , aikuwa Duduwa jiki na rawa tace" Umma insha Allah zan kammala kafin kidawo , Umma tayimata sallama ta wuce unguwa,


Duduwa na kwance tun k'arfe tara na safe har shad'aya na rana tana bacci , k'arar dabbobin gidansu ne ya tayar da ita daga baccin, gyalenta ta d'auke da kud'in da Umma ta bata ta nufi shagon mai saida kayan shayi , bredi d'an nera d'ari ta siyo sai madara ta hamsin sai k'wai na d'ari takuma siyo maggi na goma tasiyo indomie ta ragowar canjin , tana tafiya ne sukaci karo da wani saurayin dake kusada gidan su yace"ah kyakyawa ina zuwa ? naga kamar kayan dad'i kika siyo mana , tana dariya tace"Abdul yunwace ta isheni shine nazo siyan kayan shayi , Abdul daketa lek'en ledar yace"to sammin burodin inci ,mak'ale kafad'a tayi tana dariya,

Tunda ta koma gida tafara had'a wuta bayan ta d'ora shayin ta had'a takuma d'ora indomie , bayan ta kammalla girkin ta d'auko plet d'inda tasiyo a kasuwa , a cewarta bazata dinga cin abinci a kwano mai tsatsa ba , bayan ta d'ibarwa Umma tata ta shige d'aki da sauran tanaci hankalinta kwance , bayan tagama ci taji bata k'oshiba , komawa tayi kwanonda
tazubawa, Umma ta d'ebo kad'an tarugo da gudu taje ta wanke kwanukan duka ....✍️✍️✍️


*TABBAS ALK'ALAMI ✍️YAFI TAKOBI🤺*.


_Alk'alamin mom islam✍️._


*Please share 🤝*
*Comments*
*vote*✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 3_4


___Umma na dawo wa tasamu ankai mata abinci a kwano k'ato , ganin haka tafara sawa Duduwa albarka , Duduwa na ganin haka tafara mur mushi, bayan Umma ta bud'e kwanon 'ne taga indomie da k'awai a k'arshen kwano , zaro ido Umma tayi kana ta dubi Duduwa tace" wato fad'an danake yimiki baya shigarki kenan? kina y'ar talaka amma kin d'auki buri kin d'orawa kanki , kuka Duduwa ta k'a k'alo tana bawa Umma hak'uri ,

Suna cikin haka ne sai ga sallamar dillaliya nan , Duduwa najin muryar ta aikuwa ta rugo a guje tana oyoyo hajiyar mu ,
da fara'a dillaliya ta tari Duduwa tana cewa zuwan danayi yau gurinki nazo ,

Washe baki Duduwa tayi tace "wallahi dama ina nemanki 'ido rufe sekuma gaki , dillaliya ce tace" to mu k'arasa ciki , cikin fara'a suka k'arasa d'akin Umma ,

Bayan sun gaisa da Umma ne dillaliya take gayawa Umma maganar zuwan Duduwa birni ya taso , farinciki ne ya lulu6e Umma tace " alhamdulilah haka akeso ,

Dillaliya ce tace" kinga gidan da Duduwa zata sauka sunbada kud'i dubu hamsin , zaro ido Duduwa tayi kana tace " har anfara biyana kud'in ' ne tunkafin infara zuwa?

Dariya dillaliya tayi kana tace " a'a sunce dai za'a siya miki kayan sawa masu kyau , dakuma hijabai da gyalu luka suma masu kyau,

Tsalle Duduwa tayi tana dariya , Umma dake gefe tace"nidai nasihata kullum itace ki kulada mutuncin ki , insha Allah Duduwa ta amsa , bayan dillaliya tabawa Umma kud'in , Umma tak'i amsa tace"Duduwa ta shirya suje kasuwa suyi siyayya , tunda tafiyar gobe ce ,

A yaudai farincikin da Duduwa take ciki baya fad'uwa saboda yau ko rashin kunya bata yiwa Umma ba , nan tafara had'a kayanta tana kyautar wa saboda duk sun kod'e ,

Shirin zuwa kasuwa tayi , bayan sunje ne dillaliya ta za6o mata wasu riga da skirt na kanti masu kyau sunkai kala goma , sai atamfa kala biyar sannan pants da bra sukuma rabin dozin tasiya mata yadin hijab suka tsaya aka d'inka da takalmi masu kyau , tunda suka dawo gida bakin Duduwa yak'i rufuwa saboda ita burinta taganta cikin kayan ba zuwa birni yin aikin ba ,

Umma naganin kayan ta yaba dasu sannan tace" wa Duduwa ta kula sosai kar tabi maya daran samari , wasu hawaye ne masu zafi suka zubo a fuskar Duduwa , Umma na ganin hakan tasan ba k'aramin abu bane yake sata kuka , bayan tagama kukanne ta d'auki buta domin yin alwala ,Umma ma tashi tayi zuwa yin alwala ,

Washe gari misalin k'arfe takwas na safe sukajiyo sallamar dillaliya ,da cikin sanyin jiki Duduwa da Umma suka amsa sallamar ,bayan sungama shirye shiryen da zasuyi , tayi sallama da umman ta suka d'auki hanyar zuwa Abuja ,

Da isar su gidan dillaliya tayi nocking , mai gadi ne yazo ya duba , yana ganin dillaliya ya washe baki yace "barka dazuwa hajiya , goro dillaliya tabashi , yanata yimata godiya , ita dai Duduwa na biye da dillaliya , saboda duk inda tasa k'afa nan Duduwa take sawa,

Da isar su gidan wata kya kya kyawar mata fara sol, da 'a shekaru zatakai shekara hamsin a duniya , amma inkaga yanayin jikinta bazaka gane yawan shekarun ta ba , tunda suka iso cikin parlorn matar take yimusu sannu da zuwa , gaisawa suka farayi Duduwa ma ta gai sheta ,matar tace" what's is your name my daughter , jin wanan bahagon yaren yasa Duduwa mik'ewa tace "Hajiya zanyi kashi ......✍️✍️✍️

_mom Islam ce_✍️.


*Please share*🤝
*Comments*
*Vote*✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 5_6

__Matar ce tace" bari azo a nuna miki bathroom d'in , Duduwa najin ance bedroom tasa ihu , Matar da ake kira da Hajiya tace" lafiya kuwa daughter ? cikin kuka Duduwa tace" Hajiya kiyi hak'uri karki sa 'a maidani garin mu , cikin rashin fahim ta Hajiya tace" ban gane ba , Duduwa ce tak'ara share hawayen ta kana takuma duban Hajiya tace" kalma biyu zunyimin zafi , na farko kince min (bi dreba)🤣 yanzu kuma kince (buta) ni wallahi Hajiya ko wankin duka y'an gidannan ne zanyi akan a maidani garin mu , dariya ce taso ku6u cewa Hajiya , tace" yo daughter banda abinki , daughter yana nufin yarinya kokuma y'a , shikuma bathroom gurin wanka ne , OK Duduwa tace" kana ta waske tace ai nasani Hajiya kawai 'inason jin 'naku yaren 'ne,

Dillaliya ce tayiwa Hajiya sallama tayiwa Duduwa nasiha ,kana ta wuce garinsu ,

Da tafiyar dillaliya Hajiya ta nunawa Duduwa ai yukan dazata dingayi , kamar su gyaran d'aki dakuma gyara d'akunan y'an matan gidan saikuma zuwa super market siyayya,

Hak'ik'a Duduwa tayi murna saboda babu aiki mai wahala , godiya tayiwa Hajiya kana ta nufi kitchen saboda cikin ta yana kukan yunwa,

Tana zuwa ta samu Nanny d'in tana farfesun kaji , lashe baki Duduwa tayi kana tafara magana a cikin ranta tana cewa , inama nice aka bari a d'akin girkin 'nan da wallahi saina ci na k'oshi zankai musu sauran amma yanzuma bata 6aci ba,

Ganin hankalin y'ar aikin yakoma gurin aikin ta yasa Duduwa kwad'a sallama , amsawa tayi ba tare data d'ago kai ba saboda tana san kammala aikin cikin 'nutsuwa,

Duduwa ce ta k'arasa kitchen d'in cikin taku sai k'amshi take zubawa mai aikin da take sanye da rigar aiki tace "sannu Duduwa da zuwa, cikin fushi Duduwa ta galla mata wata uwar harara ...

Kana tace" as from today my name is Nancy..

Wani kallo y'ar aikin tayi mata kana tace to inma zagina kikayi keda Allah🤙,


Haka dai suka k'are kamar zasuyi fad'a haka Duduwa tabar kitchen d'in a zuciye ,


Washe gari bayan tayi sallahr asbah , taje ta gaida Hajiya bayan sun gaisa Hajiya take gaya mata anjima ita da su Humaira wato yaranta zasuje shopping ,wani tsalle ta daka kana tafara jerowa Hajiya godiya,

D'akin ta 'ta nufa ta shiga wanka bayan ta fito daga wankan'ne tazo gaban mirror d'in d'akin da yazama nata tafara tsara kwaliya saboda ko gidan makeup sun shafa mata lafiya,


Wani riga da wando ,da rigar iya guiwa wandon kuma tsukakke , wayo kuzo kuga Nancy ,

Kar ince Duduwa ta fasamin baki🤫,

Kunsan fa ba mu muna bace kuma ko batayi kwaliya ba tanada kyau to inaga tayi kwaliyar ,

Tunda ta fito daga d'akin ta take yanga tana wata kalar tafiya kamar mai tsoron k'asa ,

Ganin y'an matan gidan a parlor suna jiran ta yasata k'ara sowa da sauri tana cewa( ai sorry sit ,wata dariya suka sa , d'ayar mai suna Humaira itace babbar su tace "ba haka zakice ba cewa zakiyi ,am sorry sis ,

Godiya tayiwa anty Humaira kana suka d'auki hanyar parking spice, ganin motar dazasu hau sukayi an wanke ta , Duduwa cikin bahagon turancin ta 'tace....✍️✍️✍️.


_Mom Islam ce_✍️✍️

*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 7_8


"Tace very support🤣 anty Humaira da tagaji dayi mata gyara tace" please Nancy kidin ga daurewa kina k'yale turancin nan saboda , a gaban classmate d'inmu zaki bamu kunya , cikin k'awrewa Duduwa tace" au anty Humaira yanzu babu gyaran kenen, cikin takaici anty Humaira tace" cewa zakiyi very surprise , tsalle ta buga kana suka shige mota , da Isar su wani katafaren super market , kayane kala kala babu wanda babu , kuma duka gurin babu kayan talaka , suna shiga Duduwa ta sauya taku su Anty Humaira ko basu lura da ita ba , tana cikin takun 'nata ne taji wani hansom yace hey Lady , cikin firgici ta juyo tana k'aremai kallo , farine sosai kamar balarabe , gashin kanshi kamar na larabawa , idanuwan shi kuwa lumsa sune gasu bak'ak'e ,sai dogon hancin daya k'ara fito da ainihin kyaun shi , ganin ta tsareshi da ido yasa shi cewa are you ok k'ak'alo murmushi tayi ganin turancin ma bai 'iyaba , cikin zuciyar ta tace" mugu wai 'inci wanan uban kwaliyar yacemin LADI , shikuwa wanan saurayi ganin bata kulashi ba yasashi cewa dan Allah kya kyawa kiyi magana , wani farinciki taji kana tace " am barka da rana daganan tayi shiru , zaiyi magana ya hango su anty Humaira sun k'araso suna cewa Nancy kizo mu wuce , saurayin 'nne yace"please sister kibari muyi magana koda ta 5mins ce , murmushi anty Humaira tayi ,kana tace bari muje mota , Nancy saikin taho , mak'ale murya Duduwa tayi tace tom ,





Bayan sun anty Humaira su tafi saurayin yake cewa , dafarko dai sunana Khalil ni haifafen Abuja ne , kefa ? farr, tayi da ido kana tace"amm my name is Nancy , can kuma sai tayi shiru tace"nima haifafiyar Abuja ce kaga babbar antyna can , fad'ad'a fara'arsa yayi , yana ganin yasami matar aure, musayar number sukayi , saboda Hajiya tasiya mata waya , bayan sunyi musayar number ,yayi mata sallama ya wuce tana d'agamai hannu , tunda ta shiga motar , Khadija da kausar suke hara rarta , ko kulasu batayi ba ta shige mota ,


Ban sun koma gida sungama siyayyar dama su anty Humaira ta rako , tunda ta shige d'akinta domin rage kaya ta watsa ruwa,


Tana cikin cire kayanne taji wayar ta na ruri d'auka tayi kana tayi k'asa da muryar ta ,

Cikin sa sanyar murya yace "beauty gobe zantafi India , saboda hutun mu ya k'are kuma jigin safe zanbi please ki kulamin da kanki 'kuka tafara / nikuwa nace🤔Duduwa d'azu fa kuka had'u amma har kinshiga kogin love🤦‍♀️,



Cikin kuka tafara magana tana cewa " wallahi da su momy basuce mu dawo ba , bai gane mai take nufi ba yace " ban gane ba , cikin sha shek'ar kuka tace "satinmu biyu da dawowar mu daga India 🤣,


Cikin farin ciki yace" dama kuna zuwa ne ? ,


Eh tace Khalil yace"to yaushe zaku dawo ?jimm tayi kana tace"gaskiya sai su momy sun shirya....✍️✍️✍️.


Wayo anty Duduwa 🤭am sorry anty Nancy🤙.


Kuyi hakuri please page d'in babu yawa , kumin adu'a kuma ku had'a da Nancy saboda 🏃‍♀️.

_Mom Islam ce_

*Please share* 🤝
*Comments*
*Vote*✔️

💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.

________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]


https://www.youtube.com/channel/UCXPmzqpUDDjUfBUkYwadf4w

_*Ku danna mana subscribe kana da kararrawar sanarwa mu gode.*_
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 9_10


Daga nan sukayi sallama , tayimai Allah ya tsare , washe gari suna d'aki suna kallo dama bata da wani film daya wuce Indian film saboda sunan garin, data keso ne, duk wani yare ko turanci yana zama daram , wata safiya ce Hajiya ta tashi da matsa nancin zazza6i , kowa na cikin gidan jikin shi yayi sanyi , ganin ciwon bana wasa bane sukayi da ita ,Diza hospital dake maraba , saboda sun rud'e shiya sa,


Suna shiga cikin hospital d'in suka ci karo da Doctor Maryam ,wato matashiyar budurwar nan wace a shekaru zatakai 20 years a duniya,
Cikin azama tayo sauri tana tambayar su anty Humaira maiya sami marar lafiyar bakin anty Humaira na kar karwa tace" Doctor Maryam Wallahi bamu san mai yasami Hajiya ba , dafa kafad'arta Doctor Maryam tayi kana tace" ki kwantar da hankalin ki 'insha Allah zamuyi ' iya bakin k'okarin mu , anty Humaira ce tayiwa doctor Maryam godiya kana suka shige emergency room da Hajiya ,
suna shiga doctors biyu suka had'u a kanta wato da fitacciyar likitar nan wace kowa yasanta da adalci bata da walak'nci ita ce doctor (Anty HAUWA) ana kiran ta da (Maman Uswan),



Tunda suka rufu akan Hajiya basu d'ago ba aiki sukeyi cikin k'wa rewa da nuna adlci ,


Bayan sun shafe minti hamsin suna aikin abu d'aya ganin jikin Hajiya ya tsanan ta yasa aka kirawo anty Humaira da sauran suka shigo , tunda suka shigo Hajiya take kallon su tana hawaye tace "idan ,na mutu karku zauna a gidan da muke ciki dan Allah , ku koma gurin uncle d'inku , cikin kuka Humaira tace " Hajiya to Nancy fa yaza tayi ? Hajiya na hawaye tace.....✍️✍️✍️.


Kuyi hakuri da wanan zani anguwa please🤙.

_Mom Islam ce_✍️


*please share*🤝
*Comments*
Vote✔️
💖🌷NANCY Y'AR K'ARYA💖🌷.

_labari mai d'auke da nishad'i tareda fad'a karwa._


_story and writing_

By

*ZAINAB HABIB*
{MOM ISLAM}.
________________________________


*AREWA WRITER'S ASSOCIATION*
_________________________________
*💦{Arewa ginshiƙin al'ummah}💦*
_________________________________
https://www.facebook.com/104534761033461/posts
[email protected]

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHEEM*

PAGE 11_12

____ Hajiya ce tace" akwai wasu kud'a d'e da take bina sunkai , dubi d'ari uku , zaro ido Duduwa tayi, saboda har tafara tunanin kalar gidan dazata siya bayan an biya ta kud'inta,


Hajiya ce tafara wani 'irin tari kana wani , miyau _wato yau mai kumfa yafara biyo baya , tana gamawa rai yayi halin sa, kowa na hospital d'in saida ya tausaya mata bare yaran da Hajiya tabari , wani 'ihu Duduwa ta kurma tana cewa, na shiga uku bani da gata sai Allah, ganin kukan 'nata yayi yawa ne yasa doctors d'in sukayi waje da ita,




Anty Humaira ce tadin ga kiran waya tana gayawa y'an uwa rasuwar Hajiya , hak'ika mutuwar ta ta6a kowa saboda Hajiya bata da son duniya ,


😭Allah kasa muyi k'ya k'yawan k'arshe amen 🤲.



Bayan rasuwar Hajiya da kwana biyu, y'an uwan Hajiya suka ce zasu tafi da su Humaira garin su,
Duduwa bata gama tabbatar da , rasuwar Hajiya ba sai lokacin da wani dattijo wato d'an uwan Hajiya ya kira ta, yana cema ta yanzu kulle gida zasuyi saboda , umarnin Hajiya zasu bi,

Wasu hawaye ne masu zafin gaske suka zubo mata , duk da kud'in da take ganin kamar inta samu zata warke , amma yanzu jikin ta yayi sanyi sosai,

Washe gari ta tattara kayan ta tana neman gidan haya , cikin ikon Allah tasamu wani mutumi da yake kusa da gidan su yana dashi a can wata anguwa ta' talakawa ana kiran anguwar Riga y'ar kasuwa ,


Tambayar shi kud'in hayar tayi , cemata yayi dubu hamsin shekara d'aya , bayan sunje gidan tagani tace" mai yama ta uzuri saboda ba'a bata kud'in taba , cikin 'nuna rashin yarda yace" sai dai tabari 'in aka biyata sai ta koma ,


Gidan da mutumin ya kaita gidane mai kyau ma'ana 'akwai siminti kuma akwai bayi a ciki ga kitchen a waje bayi a d'aki ,

Mata biyu ne a cikin gidan kuma duk zasu girme ta d'aya tana da miji d'ayar kuma karatu ne ya kawo ta saboda bazata iya zaman hostel ba,

A yau ne akayi bakwai d'in Hajiya, an sallami Duduwa kud'in da Hajiya ta buk'ata 'a bata, alhamdulilah uncle yabata dubu d'ari uku da hamsin , kuka Duduwa takeyi sosai saboda 'a ganin ta sunyi mata hallacci,


*Wayoo kud'i 😫 Anty Nancy bani aron two thousands🤨*


Bayan sun su Anty Humaira sun k'ara bata kaya sabba bi dakuma gyale da hijab , sosai suka yiwa

Please Login or Register in order to submit comment