Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shikenan Allah ya kaimu goben"
"Please akwai wata tambayar ma"
Ya zuba mata ido yace "ina jinki"
"Meyasa bazaka dinga hutawa Weekend ba"
Abu Uzaifa yayi murmishi yace "zan huta wataran".

Ya kalli Munipa da tuntuni tayi bacci yace "Munipa iyayen surutu anyi bacci"
Washe gari.
Ranar ta kama asabar, an tashi da sanyi mai shiga jiki, tun bayan sallahar asbha da sukayi basu fito ba, suna rungume da juna cikin blanket, Hajiya Indo na taja bargo tanason azo a tasheta, taji shiru, dole ta sakko tana sababin cewa "dan asara baccin sukeyi har yanzu basu san gari ya waye bane?"
Bayan ta fito daga toilet ta kalli agogon dake manne a bangon ɗakin tace "ƙarfe takwas a fa? na shiga uku, amma mutanen gidannan sun zama shegu suka barini na dingayin baccin asara?"
Tana idarda sallah taje gaban dress mirror taja wata madai-daiciyar kujera ta buɗe lotion ta shafa tana lumshe ido, tace "har naga irin murmurewar da zanyi inhar na shigo wannan gidan, ku kalla fa ɗakin saukar baƙi ne akayi masa wannan aikin asarar Kamar basu san darajar kuɗi ba"
ta ɗauki hoda ta shafa ta sanya janbaki pink, sai gashi ta fito rass da ita kamar mutuniyar birni,
Ƙarfe 9:11am Hajiya Rashida ta shigo ɗakin da Hajiya Indo ta kwana, lokacin ta gama kwalliya harta kwanta,
Tana jin shigowar Hajiya Rashidan taƙi koda motsi ne, saboda tana daga kwance wani azababben kishi ne ya kamata, a zuciyarta tace "yanzu haka sunyi abin dan wlhi bazasu kasa yiba sun barni a gantale"
Hajiya Rashida tace "Indo ki tashi an kammala karin kumallo idan muka je gidan Ƙanwar Ummana sai kidawo mu tafi, kokuma Abu Uzaifa ya wuce damu idan an dace sai ki wuce tasha, a zuciyar Hajiya Indo farinciki kamar ta rungume Rashida haka takeji, a hankali ta sakko tare da ƙanƙance ido irin na mai baccin safe tace "to shikenan babu damuwa mungode da ɗawainiya, samun irinku a duniyar nan wallahi sai an tona"
Hajiya Rashida tace "harda zan kawo miki ruwan zafi ashe har kinyi wanka?"
"Eh nayi kinsan ni da ruwan sanyi nake wanka shiyasa"
A zahiri kuma kwas-kwarima tayi.
Lokacin da Hajiya Indo ta fito Abu Uzaifa ya koma ɗaki, domin yasa Uniform ɗin gurin aikinsu,
Hajiya Indo anzo dinning an ruɗe saboda abinci data gani kamar banza, kuloli uku ne a jere a gurin masu masifar kyau, ɗaya cike da soyayyan nama ɗaya kuma farfesun kifi ɗayar tuwon shinkafa ne fari ƙal miyar da miyar shuwaka taji busashen kifi da naman kaza, Hajiya Indo ta wato ido kafin tace "waɗan can kayan basur ne ga inda zanci in ƙoshi kuma in yaga kaza"
Indo ta fara ci kamar an aiko ta, sai data cinye malmala huɗu tasha ruwa, ta ɗibi soyayyan naman ta tura a breziya taci farfesun kifin tunda shidai baze ɓoyu ba, ta karƙaɗe zaninta, ta dawo ɗaki, tunani ta fara yi tace "kamar naga gwangwanin madara akan teburin nan fa, anya bazan koma ba ina kuma ci dan idan natafi bansan larabar dawowata ba"
Tana tsaka da tunani Hajiya Rashida ta shigo tace "to na shirya kizo mu tafi"
Hajiya Rashida na fita Hajiya Indo ta tura ledar data haɗa soyayyan nama da soyayyar taliya guri ɗaya ta jefa cikin haka kana ta zuge zip ɗin ta kuma zuwa gaban mudubi ta kalli fuskarta tayi waje, a parlo ta tarar da Hajiya Rashida a tsaye tana jiranta, Hjya Indo na zuwa suka wuce parking space, Hajiya Rashida ta shiga gaba, Indo ta buɗe baya, ta rufe ƙofar tana cewa "Alhaji ina kwana"
Abu Uzaifa yace "lafiya lau" daga haka sukaci gaba da tafiya.
Suna isowa gidan hajiyar yayi yayi, parking a ƙofar gida suka fito suka buɗe get ɗin gidan tare da ƙarawa ciki,
Sallama sukayi, hajiyar ta amsa da wlkslm tare da basu umarnin ƙarasowa, suna shiga suka zube kan kujera, bayan sun gaisa Hanan na zaune gaban T.V tace "Baaba Indo nidai bazan koma ba a gidannan zan zauna"
Ba maganar Hanan ɗin takeso jiba shiyasa bata ce da ita komai ba.
Hajiya tace "Rashida an sami gidan aiki ammafa matar tanada tsanani kuma yara basa shekara a gurinta wata huɗu zasuyi ta tura su wani gurin aikin"
Rashida ta kalli Hajiya Indo da hankalinta ya kwanta yanzu saboda damuwarta kuɗi ne bawai wahalar da Hanan ɗin zata sha ba,
Hajiya Indo tace "Alhmdulilah ai komai yayi dai-dai in har kin yarda da ita Hajiya babu damuwa"
Hajiyar tace "ƙawata ce tun muna yara amma tanada faɗa, ga wannan dubu ɗari ne tace a baku"
Jikin Hajiya Indo na rawa ta durƙusa ta ƙarɓa, Hajiya tace "aciki dubu hamsin shine na aiki shikuma ragowar hamsin ɗin na kaya ne da zava siyawa yarinyar saboda batasan ƙazanta"
Hajiya Indo tace "ai shikenan komai yayi zan barwa Hajiya Rashida kuɗin wannan sai in kaiwa iyayenta"
Daganan tayi musu sallama tare da yiwa Hanan faɗa akan kintsuwa ta kuma karɓi lambar hajiyar Rashida ta rakata bakin mota sukayi sallama, Abu Uzaifa dake jiranta tun ɗazi harya ƙosa.
"Kayi haƙuri Alhaji na kanata jirana"
Abu Uzaifa yace "babu komai"
Tana shiga yatada mota, suna cikin tafiya ta fara karanto izaja'a nasrullahi sai da tayi ƙafa bakwai kafin tace "Allah ina roƙonka kasa duk abinda nacewa wannan bawan naka ya amince"
Duk a zuciyarta take wannan maganar har suka kusa zuwa tasha, tace "Alhaji dan Allah ko zaka bani lambarka in dinga jin labarin Hanan? na mance ban ɗauki lambar hajiyar ba"
Abu Uzaifa yace "ok babu damuwa kawo wayar insa miki"
Ta miƙa masa wayar tata wace ta gaji da gararin duniya me botir tace "ga ta"
Sai da ya shiga cikin tashar kawo sannan yayi parking ɗin motar yasa number tasa kafin yace "to Allah ya tsare ga dubu biyu babu yawa"
Hajiya Indo tayi masa godiya kafin tace "Alhaji badan kar kace nayi munafurci ba wlhi dana gaya maka wata magana"
Abu Uzaifa yace "babu komai ina jinki"
Hajiya Indo ta sosa gefen fuskarta kafin tace "dama naji labarin ance Hajiya Rashida tasi gidaje har uku tana kan gina na huɗu shine nace in gaya maka tare da yi muku Allah ya sanya alkairi naji ance wai Munipa ma ba ƴarka bace wai ta wani mutumi ne mai kuɗi, wlhi ban riƙe sunansa ba"
A gigice Abu Uzaifa ya kalli Indo kana yace "wace hujja kikeda ita da zata bani damar amincewa da maganarki"
Hajiya Indo tace "ɗazu ka kaimu gidan wata Hajiya wace Hanan take gurinta, sun barmu a parlo suka shige ciki, nikuma dason jin gulma nabisu na laɓe a bakin ƙofa inajin lissafin da sukeyi har Rashida na cewa wai baban Munipa yafika iya kwanciyar aure, wai kai sai kace ba ɗan boko ba"
Abu Uzaifa ya jinjina kai tare da cewa "tabbas Nagode sosai Allah ya faranta miki dama wannan ƙanwar maman nata babu abinda bazata sanyata yiba, tunda nayi saving numberki zamuyi magana, ga dubu biyar ki ƙara akan nada Nagode wlhi zancenki gaskiya ne, nima nafara lura da hakan".
Har gurin mota ya rakata sai da yaga tafiyarsa kafin shima ya wuce office yana aiki a market ɗinsa kasancewar ƙa'idar gurin duk wani ma,aikaci sai yasa uniform na manyan ma'aikatan daban haka na ƙananu, sunan super market ɗinsa (MURASH SUPER MARKET) meaning Munipa da farkon sunan matarsa Rashida, babban super market ne wanda duk wani ɗan Nigeria inhar yana fita to yasan da zamanta, labarin super market ɗin bai tsaya anan ba har ƙasar Turai ya zagaya.
Hajiya Indo na tafe a mota zuciyarta rass tanajin saura kaɗan ta samu Abu Uzaifa tama fara tunanin ai ta sameshi an gama.
Acan ɓangaren Hajiya Rashida ta tafi da Hanan kasuwa ta siya mata kaya ƴan kanti masu kyau da sauƙin kudi, tare da hijabai da takalmi harda man shafawa maisa laushin fata, daga nan suka wuce gidan Hajiya Anti, haka ake kiranta, bayan sun gaisa Hajiya Rashida tace "dama na kawo yarinyar ne da kuka yi magana da Hajiya jiya"
Hajiya anti tace "to nasha Allah"
Daganan Hajiya Rashida ta dawo gida tabar Hanan anan gidan.
Hajiya anti zatayi shekaru arba'in a duniya tanada yara uku Apnan da khairat sai namijin Sadik bayaji ko kaɗan ga neman tsokana.
Sosai Hanan tayi murna da zuwanta gidan saboda kayan wasa na yara da tagani ga su mota ta wasa da mashin manya na hawa harda ƴar bebi ƙatuwar wace ake saka mata batir kai abubuwan wasa dai ba'a magana.
Wata dattijuwar mata ta shigo lokacin Hajiya anti tabar parlon tace "ke sunanki Hanan ko?"
Hanan tace "eh"
Tsohuwar tace "taso muje kisa inufom ɗin aiki irin na namu"
Hanan ta maƙale kafaɗa tare da cewa "ni ki ƙyaleni zan ɗana mota"
"Wlhi Gara ki rungumi tiransafoma daki taɓa kayan Hajiya anti"
Hanan zatayi magana Hajiya anti ta shigo...



08141799224
*WAKE ƊAYA💍*
MomIslam

_True life story_


*Arewabook@momislam11*


🆓 Page 6

Cike da ruwan bala'i Hajiya anti ta iso gurin kafin yace " me kikeyi anan?"
Tsohuwar tace "na kawo mata kayan aiki tasa tace in tsaya ta gama"
Hajiya anti ta finciko Hanan kafin tace "ke sa idonki a nawa"
Hanan ta kalli Hajiya anti ba tare da taji tsoro ba tace "Hajiya wannan zaro idon da kikeyi walhi kinyi muni sosai ga fuskarki tayi kamar ta birin wasa"
A gigice Hajiya anti tayo kan Hanan tana huci,
Hakan yayi dai-dai da shigowar Nasim, cikin d'aga murya yace "momy meya faru?"
Ran Hajiya anty a dagule tace "wannan yarinyar fitsararta yayi yawa da alamu bata da kunya ni take zagi?"
Hanan tace "Hajiya kiyi hak'uri nifa bansan zakiji haushi ba, daga an gaya miki gaskiya sai ki wani dinga yiwa mutane fad'a?"
Cikin zafin rai Nasim ya taho ya wanka mata mari tare da cewa "zaki iya gayawa uwarki haka?"
"Uwa!!!"
Hanan ta ambata hawaye na ambaliya a fuskarta,
Sai Kuma ta sake cewa "da uwata tana raye Babu Wanda ya isa ya kawoni aiki, rashin uwa shine yasa nazo wannan garin"
Jikin Nasim yayi matuk'ar sanyi, sosai yayi nadamar abinda ya aikata musamman dayaga Hanan d'in tana kuka ga hawaye wani na bin wani.
Itako Hajiya anti Babu ko d'igon nadama a tare da ita tace "ka fita da ita zuwa filin horo na baya ka horata ka Kuma nuna mata aiyukan da suka zame mata wajibi idan bazata iya ba a Kira wace ta kawota ta koma da ita"
Hanan ta kurawa Hajiya anti ido, kamar Mai nazarin wani abu sai tace "ku y'an binni Kuna ganin Allah yayi muku kud'i to wlhi ku kiyayi ranar da Allah zai kar6a akan wulakanta Dan Adam da kukeyi"
Hajiya anti tayi kukan kura ta damk'o wuyan Hanan tana cewa "dan ubanki me kika taka a duniya kike gayamin wad'anan gur6atattun kalaman ko ubanki ya ta6a rik'e wani mukami ne?"
Zuciyar Hajiya anti na tafarfasa tace "Nasim fice da yarinyar nan daga gidannan wlhi zata zamemin musifa Dan naga so takeyi taja mana bala'i"
Jikin Nasim a sanyaye yace "d'auko jakar kayanki"
"Au tausayinta kakeji?, Bazata d'auka ba, nice na siya mata komai babu abinda tazo dashi Wanda ba ni na siya mata ba, dan haka ka wucemin da ita ko k'afafunta bana so in sake gani"
Nasim ya kama hannun Hanan suka fita zuwa parking space,
Nasim matashin yaro ne, saurayi wanda bai wuce 28yrs yaron Hajiya anti ne na fari, ba wani kyakkyawa bane asali ma ince Hanan ta fishi kyau, yanada tsayi ammafa gayu da tsafta sun gyarashi, koba komai bazamu kirashi da mummuna ba,
Nasim yace "shiga mota"
Hanan ta shiga suka wuce,
Sunyi tafiya mai nisa Nasim ya kalleta kafin yace "meyasa baki da kunya?"
Hanan tace "meyasa kake tambayata?"
"Saboda kin yiwa mahaifiyarta rashin kunya"
"Tak'i barina inyi Wasa shiyasa nake yi mata wa'azi"
"Kan uba, shekararki nawa da zaki yiwa mahaifiyata wa'azi bayan kinsan ta haifi wacce ta fiki?"
Hanan tace "ina zaka kaini dan Allah?"
Nasim yayi parking a gefen hanya kafin yace "inane garinku can zan mayar dake"
Hanan ta fara tsalle kafin tace "can jahar Kaduna a anguwar me gishiri Saminaka can ciki"
Nasim ya duba lokaci kafin yace "okay gaskiya sai dai in kaiki tashar mota ki hau ta haya, akwai nisa bazan iya zuwa ba, kai tsaye ya wuce da ita tashar mota aka sanyata a motar Saminaka lokacin da suka isa saura mutum biyu mota ta cika, tana zaune a motar wata tazo ta shiga, Nasim ya k'urawa Hanan ido,
Me gurasa ta kawo talla da me awara, Hanan tace "d'an gayu siyamin gurasa da awara yunwa nakeji"
A inda tayi maganar sai ta bashi dariya saboda turo baki takeyi, yace a bata ko wanne na ɗari yaje ya siyo mata viju ya bata, tana Sha tace "wlhi akwai yauk'i kumafa akwai dad'i ga sanyi mai sanyaya zuciya"

Ta6e baki Nasim yayi kafin yace "zan wuce na bada kud'in motarki ga dubu uku kibawa iyayenki"
Hanan tayi masa godiya ya tafi.
K'AUYE••
K'arfe biyar na yamma Inna meramu ta fito cike da masifa ta samu malam Junaidu dake d'inke rigarsa da allura tace "malam ina Hanan tayi ne?"
Malam Junaidu yace "nima rabona da ganinta tun safe data fice bansan Kuma inda tayi ba"
"Anya malam Babu sa hannunka a 6atan Hanan kuwa, bazance ta 6ata ba kodai ta tafi yawon data saba ne, abinda kukemin ya isheni meyasa kakeson tozartani ne, nayi abin siyarwa Dan in samu ta fita mun dashi ko Samira na siya mata Amma shine kace ta gudu ko?"
Bai ma kalleta ba bare ya nuna yaji maganar da takeyi,
Sallamar da sukaji ne yasa ta shigewa d'aki da gudu tana cewa "dan Allah kace bana nan"
Malam na ganinta yace "haba Gaje ya zaki shigo mana gida ko sallama Babu ?"
"Malam Ina ganin girmanka meyasa kake goyon bayanta bayan kasan bashi Mero ta daukarmin yakai na wata guda har yanzu k'eya kaji sak'on baya"
Malam Junaidu ya ciro wata kod'ad'iyar d'ari biyar ta yamutse wacce ita kenan masa ya mik'a mata kafin yace "shikenan na biya ko?"
"Eh kabiya sai Allah ya sake had'amu a gaba"
Malam Junaidu yace "wlhi ba Amin ba"
Gaje ta fice, sai ga wani yaro ya shigo wai "ana sallama da Inna meramu"
Malam Junaidu yace "waye"
Yaron yace "yayan Usaini Mai gidan duhu me"
Inna meramu na daga d'aki gudawa ta kamata, ta fito da uban gudu tayi band'aki tana cewa malam "biyoni da buta"
Malam Junaidu yace "kace tana zuwa"
Yaro ya tafi,
Inna meramu ta fito zani a hannu tace "malam nace ka biyoni da buta saboda k'n jini shine kak'i mik'omin ko?"
"Idan kin gama ki je ana kiranki k'ila ranar auran zaku saka"
Ciki Inna meramu ya sake rikicewa har wani k'ugi yakeyi k'uuuuuu,
Ta dawo gurin malam Junaidu jiki a mace tace "to meyasa malam bazaka fita ba kasandai wannan abin duk k'aruwarmu ce ko?"
"K'aruwarki dai Ni babu ruwana idan kika cutar da marainiya Allah ne zai hukuntaki tunda ke akan kud'i Babu abinda bazaki ita yiba"
Malam na rufe baki tace "naji tunda shedar da kayimin kenan idan Kuma yarinyar ta dangwalo mana arzik'i wlhi kayi kuka da kanka da ko sisi ba baka zanyi b"
Ta fice a sunkuye,
Bayan sun gaisa da yayun Usaini sukace sunzo akan a gaya musu ranar da akasa saboda zasu shiryo kayan akwati,
Inna meramu tace "nifa da nasa sati biyu ne, a lokacin ma da akasa yau saura kwana biyar, gashi yarinyar dai ba'a ganta ba, Amma kuci gaba da shiri Ina nan Ina aiki akai wlhi sai ta auri d'an uwanku, ai iri na Usaini abin alfahari ne ga duk wata y'a mace"
Sukayi mata godiya tare da mik'a mata dubu biyu suka wuce.
"Inna meramu ta dawo zuciyarta fesss ta rangad'a gud'a a gaban malam Junaidu tace "d'an mutum mai rana oh Allah sarki gashi nayi fitar dubu biyu"
Allah sarki malam Junaidu kallonta kawai yake a tunaninsa sai Hanan ta samu miji zata dawo garesu,
Gidan duhu••
Yau kwanan Usaini biyu da tafiya, a yaune Hinde ta shirya barin gidan ba tare da kowa ya sani ba, abinda zai bawa mai karatu mamaki shine, da Hinde ta yiwa Hauwa sallama tace "ki koma kawai karki nuna kin ganni ko labarin kinsan inda nake.
Hide ta bige kwad'on da Usaini yasa a k'odarsa kasancewar kwad'on bawai me kyau bane, tana shiga d'akin taji wani bala'in zaki kamar ta shiga cikin garwashi, abin mamaki gidan sama a d'akin ta dinga haurawa tana cigaba da tafiya Amma har yanzu bata iso k'ofar da zata sadata da waje ba, tana tafiya gurin yana sake yi mata nisa, bata sare ba taci gaba da tafiya har ta iso wata k'ofa wacce daga ita sai k'ofar gida, Hinde ta bangaji k'ofar, k'ofar ta bud'e ta fito, a tsorace take kallon gari, kasancewar hasken da garin yayi, gashi sai ganin mutane sukeyi takeyi sunata kaiwa da kawowa,
Acan 6angaren Hanan kuwa ta iso har ta Sami wani Mai mota zai kawota nan cikin anguwar tasu, motarsu ta biyo ta anguwarsu hinde kasancewar duk hanya ne,
Hinde na tsaye a jikin wani shago kafarta Babu takalmi gata kyakkyawa, tana ganin mota na tahowa taje da gudu ta d'auka abin Wasa ne, mota ta bigeta jini ya fara kwaranya daga hancinta,
Magidancin ya fito da gudu yana cewa "innalilahi wa inna ilaihir raji'un wannan yarinyar waye?"
Hanan ta fito da gudu kafin tace "gaskiya tunda nake ban ta6a ganinta ba wlhi".
Tashi d'aya mutane suka cika gari kowa yace be santa ba,
A haka Hanan ta ku6uce ta kama hanyar gida.
Baba Mero na dawowa "D'aki ta d'auki wata k'warya mai zurfi ta fara kiran Hanaaaaan... ki dawo gida ina neemanki "
Acan 6angaren Hanan kuwa harta matsu ta ganta a gida saboda wani d'oki da takeyi musamman ma taga Inna meramu ta mance da shafin malam Junaidu"
Kai tsaye Hanan ta wuce gidan Hajiya Indo, farko tayi sallama jin an amsa acan ciki yasata k'arasawa cikin gidan, Hajiya Indo ta fito tana cewa "muryar wa..."
Da sauri ta katse zancen da cewa "ke wace irin shegiya ce, In kashe kud'ina in kaiki aikatau din shine zaki gudo?"
Hanan tace "wlhi hajiyarnan batada kirki bakiga inda take yimin masifa ba kamar batasan darajar mutane ba" Hajiya Indo tace "Ina ruwanki da sanin darajar mutum ko ubanki ake zagi kullum kedai ba abaki kud'in aiki ba?"
Hanan tace "wlhi bazan zauna ana zagina ba nifa ba dole bane"
Hajiya Indo ta harareta kafin tace "gashi zanyi aure acan kina neman jawa kanki matsala, to wlhi ansa bikinki da Usaini mai gidan duhu saura kwana biyar"
Hanan ta fad'i a gurin ko numfashi batayi.

Cikin gaggawa aka wuce da Hinde asibitin cikin gari, aka fara bata kulawar ta musamman, Babu Wanda ya biyosu dan kowa cewa yakeyi bai Santa ba, gata wata irin yarinya gashinta har gadon baya yakai kwankwasonta, ga kyau kamar maiyya, kowa ya tsorata da ita, shidai tunda shine ya bigeta bai ji tsoron komai ba, bayan tafiyar mai motar wani Wanda ta tsaya a kusa da shagonsa yace "inaganin fa wannan mutumin kamar me gidan Mai d'innan da ake yawan zancensa a radio, dalilin da yasa na ganeshi kuwa, saboda muryarsa da naji ga hoton ana bada mai a k'aramar motarnan"
Ban suka fara tantama, wani yace "k'ila da mun nuna mun santa ya cika mana aljihu da kud'i, dattijon cikinsu yace "wayasani ma ko aljana ce, kafarta ko takalmi Babu, banga ma kunnenta da alamun an Huda ba"
Dukkansu suka tsorata da lamarin har suka fara cewa "Allah yasa wannan Alhjin ba gamo yayi ba wlhi da bazamuji dad'i ba saboda cewa za'adingayi a garinmu"
"Dalla can, tunda bazasu rabawa talakawa kud'i ba ai gara yaje ya kashe a gurin magani"
K'arfe shida na yamma Hinde ta farka, tana cewa "zansha fate..wayo zansha fate.."
Alhji Munir yace "y'ata ki kwantar da hankalinki barinje in siyo miki abinci kici"
Ya fita ya barta a kwance a gadon asibiti sai kale kalle takeyi, dayake ta samu sauki ta mik'e taje gurin abin kunna wuta tanata Wasa dashi, idan taga wuta ta d'auke sai tasa dariya ta kunna,
Hajiya Indo••
Cikin azama ta d'ibo ruwa a randar kasa ta watsawa Hanan, lokacin ta kira Abu Uzaifa tace masa yarinyar data kawo ta dawo yazo ya d'auketa ko ta bashi lambar masu tashar mota a mayar da ita, Dan batada kud'i, beyi mata musu ba yace to"
Hajiya Indo ta danna lambar malam Junaidu, yana ganin lambarta ya fice da sauri a gidan, yaje bayan gidansu ya ra6e, daga can 6angaren Hajiya Indo tace "gafa Hanan ta dawo tana gidana"
Malam Junaidu ya zube a gurin tare da sharce zufar data karyo masa yace....
Ayimin afuwa banyi posting jiya ba inata gyaran Facebook account d'ina ne

Littafin wake d'aya na kud'i ne akan farashi mai sauk'i zaku sameshi a ₦500 special ₦1000 siyan nagiri maida kuɗi gida, karku mance da rikita rikitar da littafin ya kunsa, gashi dai Hinde ta fito ina zata dosa, za'a mayar da Hanan kuwa?
Free pages yana iya k'arewa a koda wane lokaci.
Account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Katin mtn da Vtu ta wannan number 08163626370
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Y'an Niger zaku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
Mom Islam
*WAKE ƊAYA💍*
MomIslam

_True life story_


*Arewabook@momislam11*


🆓 Page 7

"Dan girman Allah karki bari ta dawo gida, Indo muguwar mata ce zata iya yin komai akan taga Hanan tayi aure a gidan duhu"
A inda yayi maganar ya ba Hajiya Indo tausayi, tace "insha Allah Junaidu hakan ma bazata faru ba, gobe zan mayar da ita kokuma in kaita Kano tunda tsakaninmu akawai nisa, da garaje bazata ji marmarin dawowa ba"
"Yauwa Indo nagode Allah yayi miki albarka"
Cewar malam Junaidu da har yanzu yana durk'ushe jikinsa na karkarwa,
Hanan da yanzu ta farfad'o ta kalli Indo sai Kuma ta fashe da kuka,
"Hanan meya faru ko kinason komawa gida ne?"
Hajiya Indo ta fad'a tana kallon yanayin Hanan d'in,
Cikin muryar kuka Hanan tace "nidai inason zuwa gurin Inna Meramu har ji nakeyi kamar in rufe ido idan na bud'e in ganni a gurinta"
Gaban Hajiya Indo ya buga rass ta fara tunanin inhar Inna meramu taji labarin Hanan tana gurinta to Babu makawa sai ta tozartata ko tayi mata asiri tabi duniya tunda Babu tsoron Allah a tare da ita,
A fili tace "ki kwantar da hankalinki nifa banasan inga kinje gidan duhu saboda wlhi inhar kika shiga wannan gidan kinyi sallama da shak'ar iskar waje sai mutuwa, saboda ba'a fita a gidan"
"Eh naji inaso"
Sosai Hajiya Indo ta sake tabbatarwa da maganar Hanan da takeyi ba yin kanta bane, saboda duk da yarintarta idan akace mata zatayi aure a gidan duhu har zagin mutane takeyi yau ita da kanta take cewa tanaso?,
Acan 6angaren Alhji Munir kuwa yanzu ya dawo da k'atuwar leda bak'a mai d'auke da soyayyan k'wai da dankalin turawa sai tea a sabon cup da bread Mai yanka-yanka,
Da sallama ya k'araso d'akin ya sameta ta haye saman gadon tana ta tsalle kamar ba itace mai jinyar ba, ga kanta nad'e da bandeji, ya ajiye ledar tare da kamo hannunta yace "zo kici abinci"
Da sauri Hinde ta nutsu,
Alhji Munir ya fito da soyayyan k'wai da dankalin harda shayin da bredi ya ajiye a saman ledar kafin yace "bismillah"
Jikinta na rawa ta d'auki kofin shayin a tunaninta kunu ne, tana Sha ta fesar tare da d'aukar wainar k'awai takai bakinta, lomar farko shima ta fito dashi tare da fashewa da kuka tace "fate nakeso ko tuwo ni bazanci wannan ba, saboda tunda nake ban ta6a ganinsu ba"
Alhji Munir ya zuba mata ido kafin yace "to kici dankali"
Cikin sa'a taci shima d'in ba sosai ba ta ture gefe tana jin zuciyarta na tashi, abinka da ba saba ci tayi ba.
Wayarsa ta fara Ring, a hankali yasa hannunsa a aljihu ya ciro wayar, Hinde ta k'ura masa ido tanason taga abinda zeyi da wayar, sai taga ya kara a kunnensa yana cewa "wlhi na bige yarinya ce gashi na rasa iyayenta inaga zamu koma k'auyennne ayi cigiyar danginta"
Hinde ta duro a gado tare da fincikar wayar hannunsa, tana ta kallo tana dariya tace "wannan abin magana yakeyi?"
"Eh mana yanzu aka kirani"
Ta Kuma kwashewa da dariya tace "Naga har haske yake kawowa sake kunnawa in gani".
Alhji Munir ya kunna mata kallon yaran larabawa da suke spelling din ABCD suna wak'a, yana fita ta ajiye wayar a k'asa tayi tsalle ta fad'a kan wayar tana cewa "kodai mayu ne, ga wasu fararen Abu sai kace aljanun k'arshen duniya"
Alhji Munir ya shigo da saurinsa ya ganta ta mimmik'e k'afafuwa a k'asa, cikin fara'a yace "tashi muje"
Tana mik'ewa yaga screen d'in wayarsa ya tsatsage gashi ko haske Babu, jikinsa na rawa yakai hannu ya d'auko wayar, ya danna ta kawo Amma ciki yayi Zane"
Ya kalli Hinde dake dariya a tunaninta tayi abin arzik'i tace "Baba na gyara maka zaman mutanen dake

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment