Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

son tsotse jininka"
Alhji Munir ya zaro ido, yana son yi mata fad'a ya kasa saboda wani kwarjini da tayi masa, Kuma yana gudun kar tak'i sanar dashi komai akan rayuwarta, yaga kamar Babu abinda ta sani na game da jin dad'i, dalilin da yasa ya gano hakan shine, ya kawo mata abincin da yara suke murna idan suka ganshi Amma ita ta ture, ga waya da duk wani yaro ya Santa Amma tana neman lalata masa, ya kamo hannunta tare da tura gashin kanta wanda yake tashin tsami cikin d'ankwali, ya kalli k'afarta da ta kasance duk faso, yace "muje in siya miki silifas"
"Meye wannan?"
Hinde ta tambaya tana zuba masa idanuwa"
Alhji Munir yace "takalmi" ya nuna kafarsa yace mata "Amma ba irin nawa ba"
Kasancewar an sallamesu suka wuce hannunshi ana Hinde, d'ayan hannun Kuma ya rik'e magani.
Tana hango motarsa ta zame hannunta a nashi kafin ta k'arasa da gudu ta ture motar da k'afa, a tunaninta motar zata fad'i sai taga ko motsi batayi ba,
Alhj Munir ya girgiza Kai yana dariya.
Hannunta ya rik'e yasa ta a gaban mota shima ya shiga, ya had'e fuska alamar Babu Wasa yace "idan kika sake ta6a wani abu anan wlhi zan dakeki"
Batasan duka dole ta nutsu.
Alhj Munir yace "inane gidanku waye sunan mahaifinki?"
Duk da yarintarta wayonta yana nan saboda a zurfin tunani sai tafi wani Mai yawan shekarun ma,
Hinde ta fashe da kuka sakamakon tunowa da idan ta koma gidannan mahaifinta zai kasheta, Kuma burinta na fitar da mahaifiyarta bazai ta6a cika ba muddin ta koma wannan gidan, a tak'aice ma batasan halin da mahaifinta yake ciki ba.
Alhj Munir yace "kibani amsa in samu in mayar dake gida lokaci ya k'uremin kinga ana kiran sallahr la'asar"
Hinde ta share hawaye kafin tace "ni bani da iyaye, kawai tsintar kaina nayi a inda ka ajiyeni dan Allah ka taimaka min ko gidan masu aiki ka kaini in dinga samun kudi ina cin abinci"
Alhj Munir ya tsorata, shima ya fara tunanin anya ba aljana bace, duba da yawan gashin kanta gashi bak'i kamar na doki Kuma Babu alamar k'arashi akayi, farcenta kuwa dogo kamar ba'a a ta6a yankewa ba, Alhj Munir yace "y'an mata sauka ko nawa ne zan baki dan Allah ki saukarmin a mota karki cutar dani"
Abin ya bawa Hinde dariya, tunda taga yana jin tsoronta Kuma yake ganin kamar ita ba mutum bace , ta lank'washe hannayenta kamar kuturuwa ta zame hular kanta, cikin wata iriyar murya tace "dama inrinku muke nema, tun wuri ka kaini gidanku idan ba haka ba wlhi sai na juyar damu a cikin wannan motar, kuma kai zaka mutu ba niba"
Alhji Munir ya fara fitsari a wando cikin tsananin tsoro yace "dan...dan Allah kiyi hak'uri duk inda kikeso zan kaiki amman Banda gidana"
Hinde ta turje ita dole sai gidansa,
Alhj Munir shima ya dinga yi mata magiya amma Sam tak'i amincewa da ya kaita gidan iyayenta,
KD
K'arfe 9:pm na dare, Abu Uzaifa yayi parking motarshi a gurin ajiye motoci, Rashida na jinsa ta fara murmishi tana cewa "Munipa dadynki ya dawo"
Munipa tayi tsalle tana dariya, abin mamaki, Abu Uzaifa ya shigo da murmishi ya rungume Hajiya Rashida bai nuna mata komai ba, sai wani shauk'i ma da yakeji, yace "Munipa yau banzo d'aukarki ba ko?"
Munipa ta shagwa6a fuska tare da cewa "dady ai driver ya d'aukoni"
Hajiya Rashida tayi masa sannu da dawowa tare da tayashi rage kayan jikinsa suka wuce dinning dukkansu a tare sukaci abinci, Munipa tana kan k'afar Abu Uzaifa, bayan sun kammala an d'an jima abu Uzaifa yace "Amma wannan k'awar taki mahaukaciya ce ko?"
"Meya faru wani abun tayi maka?"
Rashida ta watsa masa tambayoyi,
"Babu komai amma last kar in sake ganinki da ita wlhi idan ta sake shigowa gidannan a bakin auranki"
Abu Uzaifa ya fad'a ranshi a 6ace,
Hajiya Rashida tayi dana sanin tambayarsa da tayi saboda wad'annan kakkausan kalaman daya gaya mata sun jefata cikin rud'u.
Washe gari, sam bayajin fita aiki, kiran ma'aikatan gurin aikin nasu yayi yace "su gudanar da komai yau yana gida"
Kasancewar yau Monday driver ne yakai Munipa makaranta shikuma yana nan gurin Rashida,
Kwance suke a kyakkyawan bed Wanda ya dad'a K'awata d'akin, Rashida na kwance a k'irjinsa tace "uhm meyasa kake cewa idan har ta sake zuwa sai dai ka sakeni, tunda nake dakai kalamar saki bata ta6a shiga tsakaninmu ba sai yau?"
Tana rufe baki Kiran Hajiya Indo ya shigo, Abu Uzaifa yasa k'arar magana,
Hajiya Indo ta mak'ale murya kafin tace "Mosoyina ya ake ciki?"
Cikin tsananin kishi Hajiya Rashida ta fizge wayar tace "wawuya dak'ik'iya girman kyauye mara hankali butulu, mijina kika koma bi iyee?"
"Ke Kuma wacece da zaki yimin magana da wayar saurayina?"
Da sauri Rashida ta mik'a masa wayar tare da fashewa da kuka tana cewa "wlhi Allah sai naje har k'auyen nasu nayi mata illa batasan tayi gangancin shiga gonata ba, batasan waye Rashida ba?"
Abu Uzaifa ya rungumeta yana cewa "haba komai ya wuce mana, tunda dai ban amsa ba"
Cikin zafin rai ta dawo kansa, "wane irin baka amsa ba, wayasani ma ko ankusa auran naku kanaso ka zamo munafiki?"
Kalmar daya tsana a rayuwarsa kenan, cikin zafin zuciya ya wanka mata mari yana huci kamar wani zaki.
K'AUYE
Biki ya rage saura kwana uku, hankalin Inna meramu inyayi dubu ya tashi ta rasa inda zatasa kanta, tayi tsubbace-tsubbacen abin har yanzu tana ganin kamar bata samu galaba akai ba, tana zaune a tsakar gida kan dakalin k'ofar d'akinta Hajara k'awarta ta shigo, jikinta har kyarma yake saboda tsabar munafurci, Inna meramu na ganinta tace "Allah yasa da abin alkairi kikazo, tunda naga kin kwaso sauri nasan akwai magana a bakinki"
Hajara tacire mayafin dake rataye a kafad'ar ta kafin tace "can naga Y'arki Mai mashin ya wuce da ita su biyu harda Hajiya Indo me k'afar yawo"
Inna meramu ta mik'e cike da ruwan masifa tace "da gaske kikeyi ko wasa?"
"Zanyi miki karya ne? ki tambayi mijinki shine ya samo musu Mai mashin"
Inna meramu ta rangad'a salati tare da d'aukar mayafi tabar Hajara a gurin ta fice ko takalmi babu,
Tayi neman duniya Allah besa zata had'u da malam Junaidu ba, kowa ta tambaya sai yace mata rabonshi da ganin malam Junaidu tun safe, hankalinta ya tashi lissafi ya kwance mata ta rasa makama ta rasa inda zatasa kanta, babban tashin hankalinta idan Usaini ya dawo zai iya nakasata duk da tsufanta bazai duba komai ba.
Ganin Inna meramu ta fice yasa Hajara fitowa itama ta dawo gida tana cashewa da rawa, tace "saura muga inda Usaini zai ladabtar da Inna Meramu saboda mugun San kud'i inake ina had'a zuri'a da gidan duhu, acan gonar bayan gari ta hango malam Junaidu ya rafka tagumi yana kuka cikin masifa ta tafi da gudu tana ta tsallake kinyar masara saura biyu ta isa gareshi ya....
Saboda Allah da Kuma masoyana nace..
Littafin WAKE ƊAYA is not free paid book ne,
Akwai wad'anda suka fara tura 500 d'insu da farko zan saku a Vip.
Nayi rangwame da nace 500 yanzu duk meso zai iya bin wad'annan tsarukan saboda masu maganar yayi musu tsada.
Normal 300
VIP 600
Special 1k
Ga matakan da za'abi domin biyan kud'in
Account number 3175689751 Zainab Habibu first Bank
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Katin mtn da Vtu ta wannan number 08163626370
Shedar biya ta wannan number 08141799224
Y'an Niger zaku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224
Mom Islam
*WAKE ƊAYA💍*
MomIslam

_True life story_

*Arewabook Momislam11*


Page 8

Malam Junaidu ya mik'e a zabure kafin yace "wlhi kina karasowa nan a bakin auranki"

"Kutumar uba!! ni zaka tozarta a bainan nasi?"

Malam Junaidu yace "Allah ya taimakeki ai babu mutane wlhi na gaji da zama dake, tunda muke tare talauci yayimin katutu dafa har kansila na nema"

Inna meramu ta fashe da kuka kafin tace "Bismillah Wanda be fasa saki naba ya raina.."
"Kul karki sake ki zageni shasha Sha marar tarbiya"
Ya juya yabar gurin tana tsaye tana d'ura masa.zagi.

IBADAN WAGA DUHU.

Gidane babba wanda ya amsa sunansa, da safe mutanen gidan duk suna nan, da zarar Rana tayi kuwa ko wacce zata kama gabanta, a gidan ko wacce da sana'ar da takeyi, mata uku ne a gidan duk basu da miji daga wacce tazo daga  Lagos sai wacce tazo daga sauran k'asashen yarbawar, matar farko Mai suna Iyabo tanayin Amala da alale
Ita Kuma ta kusa da d'akinta sunanta Iya Sadiya tanayin Ganda da sakwara, d'ayar sunanta Eleha tanayin shinkafa da Miya sai soyayyar doya da kunun aya da kunun zak'i, duk cikinsu Eleha ce mai yarinya Amira tanada shekaru goma ashirin 20yrs, Amina kyakkyawa ce ga son gayu bata harkar talaka, ko saurayi ne yazo inhar ya sake mata bakin aljihu to zata dinga nan nan dashi kamar ta goyashi, haka itama uwar ba k'aramin son kud'i ne da ita ba, kwatsam wata rana Amira taje tallar kunun zak'i da kinun aya Sasa, sukayi arba da wani Wanda zai yi shekaru 50yrs da farko tayi masa kallon wulakanci, da taga ya fitoda kud'ad'e sai tayi murmishi tare da cewa "Alhji a kawo kunun ne?"
Wanda ta Kira da Alhjin yace "eh a kawo nayi tunanin bazaki kulani bane"
Amira tace "Haba ai ban isa ba"
Ta mik'a masa kunu yasha ya lumshe ido, ga mamakinta sai taga ya k'irgo 5k ya Mik'a mata tare da cewa "da zaki amince dani da mun k'ulla alak'ar juna"
Amira tayi masa farr da idanu kafin tace "mezai hana"
Yana ganin bata fahimceshi ba yasa yace "ma'ana ki dinga zuwa inda nake kina debemin kewa"
Amira ta zaro ido kafin tace "duk son kud'ina Ina tsoron zina a yarenmu hukunci ake yiwa mutum, baka gayamin sunanka ba"
Mutumin yace "sunana Usaini mi mazaunin Kaduna ne ma'ana birnin Kaduna"
Amira tace "wow, ina son rayuwa a Kd"
"Zaki aureni?"
Usaini yace yana mata murmishi,
Amira tad'anyi Jim kafin tace "zanyi shawara"
Usaini yace "yau nake shirin komawa gida ina fatan zaki ajiye soyayyata a ranki?"
"Kabani numberka sai mu dinga gaisawa"
Usaini yayi shiru ya Kuma yace "ki aro mana biro sai ki rubuta"
Amira tace "in aro biro Kuma in rubuta?"
Wayancewa yayi da cewa "sai na jiki"
Ganin bai kar6i number ba Kuma bece komai ba ya wuce, ya sata fara zargin Anya wannan mutumin yanada lafiya kuwa?"
Sana'ar Usaini fashi da makami a babbar hanya, wannan sana'ar ta zame masa sirri duk iya bin k'wa-k'waf d'inka sai dai mutum yayi ya bari saboda Babu ta inda baya neman taimako haka shida kansa malamin kansa ne"
K'AUYE
Gidan duhu
Zuwa yamma Yara sun hallara a tsakar gida ko wanne da kwanon abinci a hannunsa yana jira a d'ibo a zuba masa,
Iyami ta kalli jerin yaran tace "rabona da ganin Hinde tun safe ko Babu lafiya ne?"
Gaban Hauwa ya bada dummm ta fara k'irk'iro k'aryar da zata dace da gaskiya, wlhi nima dai nayi shiru ne ai na d'auka tana d'akin Ladidi ne?"
Ladidi ta dafe k'irji kafin tace "ni!! wayewar garin yau ko lek'owa d'akina batayi ba"
Nanfa aka shiga salati ana mamaki tare da lek'a kowanne lungu da sak'o na gidan amma shiru babu alamunta,
Hauwa ta fashe da kuka tana cewa "ina yarinyar nan taje?"
Iyami tace "wayasani ko kin turata waje ta gano muku kayan duniya?"
Ladidi tace "kull iyami wannan wace irin magana ne? inda tanason turata waje meyasa tun tuni bata turata ba sai yanzu ki gyara maganarki"
Hauwa dai kuka take, ga gabanta daya tsananta fad'uwa ta runtse idonta yayinda hawaye suke ambaliya a fuskarta,
A haka dukkansu suka wuni jiki a janyaye tare da tararrabin idan shugaban ya dawo wane irin hukunci zai d'auka akansu,
Acan gidan Hajiya Indo, ta rasa makamarta, gashi Hanan tanayi mata bak'incikin samun kud'i tak'i nutsuwa tayi aiki,
A ranar da ta dawo da yamma suka nufi Tasha sai Kano, sai wajen shabiyun dare suka isa, a hakan ma motar tayi gudu sosai, lambar y'ar uwarta ta kirawo wato, Salima, cikin sa'a ta shiga, Saliman tana d'agawa Hajiya Indo tace "gamu a Kano idan Sunusi yana nan yazo ya d'aukemu"
Salima tace "wlhi mashin d'inma inaga Mai shi ya kar6i abinsa, dayake kinsan kar6a-kar6a sukeyi"
Hajiya Indo tayi tsaki cikin d'aga murya Hajiya tace "aikin banza ki zauna kiyita hawalar da kanki sai kace shine autan maza"
Sunusi dake saurarar duk abinda Indo take cewa, ya kashe wayar kafin yace "to kinji abinda y'ar uwarki tace "ni bazanje d'aukota ba wlhi sai dai ta kwana a hanya"
Salima ta hade hannnayenta biyu tana had'ashi da Allah, Amma Ina sam yak'i saurar ta sai ma ya juya baya yaci gaba da baccinsa,
Indo da Hanan suna tsaye a tashar mota sai uban masifa takeyi,
"Nifa nak'i jinin iskanci, yanzu haka ma ya taho a ru6a66en mashin d'in shiyasa mukaji shiru, da Mai mota ne ai da yanzu ya iso, ina nan ina gidan k'ank'ara?"
Hanan tace "ni wallahi bacci nakeji"
Hajiya Indo ta rufe ta da ruwan bala'i tare da cewa "barin zamo katifa ki kwanta a kaina jinki?"
Hanan ta zaro ido lafin tace "Allah ya baki haƙuri"
Can anjima Indo ta kalli agogon wayarta taga k'arfe 2:am na dare, cikin firgici tace "ciro mana tsumman zaninki mu shimfid'a nimafa na fara jin baccin"
Hanan tayi dariya tare da cewa "me mashin d'in har yanzu yak'i tahowa"
"To in ya taho ma ubanki zeyi miki?"
'Allah ya baki hak'uri"
Hanan ta fad'a tare da kwanciya a tsumman zaninta ragowar kayan tayi pilo dashi,
A wahale sukayi bacci Wanda baccin ma iya Hanan d'ince ta samu tayi ita kuwa Indo tunaninta ya Kasu kashi-kashi musamman ma da Abu Uzaifa ya tona mata asiri a gurin matarsa, yanzu komai nata ya rushe tana son zuwa gurin malamin garinsu abin ya gagareta saboda isashen kud'i da bata dashi.
Har akayi Kiran sallahr asbha a kunnenta, ta tashi Hanan sukayi sallah kafin tace ,zasu hau mashin su wuce gidan wata k'awarta wacce takeda tabbacin zata bawa Hanan din aiki,
"Jirani Ina zuwa"
Hajiya Indo tacewa Hanan, ta barta a gurin, abin mamaki har gari yayi haske Hajiya Indo bata dawo ba, suko masu motoci harkar gabansu sukeyi, tun Hanan d'in na zaune guri d'aya harta kasa jurewa ta dinga kaiwa da komowa ko zataga Hajiya Indo amma shiru,
Hanan ta tsuguna a gurin ta rusa ihu tana cewa "na shiga uku Indo ta tafi ta barni"
Wani d'an mai aiki a tashar ya daka mata tsawa, tare da cewa "sai kace k'aramar yarinya ki jirata mana"
Shima yazo yabar gurin a motoci sai tafiya sukeyi, wani Mai mota da  zashi Zamfara  ya duba agogon hannunsa yace "k'arfe d'aya" gaskiya Kuna mun iskanci nariga Shamsu zuwa fa Amma kuka cika masa mota ni kuka barni,
Hanan ta zaro ido tare da d'aukar jakar kayanta tayi bakin titi,
Tana tsaye a gurin masu adai-daita sahu sunata wucewa, har ta fara tunanin idan ta tare mai adai-daita ina zatace mishi, Alhalin ita bata san ko Ina a Kano ba haka Kuma bata ta6a zuwa ba tana dai jin sunan garin a bakin mutanen kauyensu da suke zuwa wata kasuwa sarin kaya,
Jikinta yayi laushi sosai hankalinta ya mugun tashi ko wacce mota tazo wucewa takeyi, ga k'oshin ruwa daya dameta ga yunwa,
Yanke shawarar tayita tafiya tayi, hakan ko tayi tana ta bin gefen titi a hankali da buhun kayanta a kanta, idan ta gaji ta huta idan ta huta taci gaba da tafiya, kwatsam ta tsaya a gaban wata mota dake shirin tashi, Motar fara ce tass mai kyau da tsada, musamnan ma idan ka hango mutanen da suke cikin motar mace d'aya zatayi shekaru 57yrs sai wani saurayi fari kyakkyawa fuskarsa a had'e ko alamun fara'a Babu"
Matar cikin motar tayiwa hanan Alama da hannu tace "kee.!"
Hanan ta juyo sai Kuma ta fashe da kuka,
Matar ta bud'e murfin mota kafin tace "zonan y'ata"
Hanan ta matso jikin matar, tana sheshek'ar kuka,
Matar  tace "meyasa kiketa kuka ko bara kikazo yi?"
Hanan ta yanke shawarar tace batada iyaye tunda taga Malam Junaidu yanzu ya dena sonta shikenan tayi rayuwarta ita kad'ai,
"Bansan inda kowa nawa yake ba, anan gurin nake zama koda yaushe"
Ajmal ya zaro ido kafin yace "wlhi Ummi ki kiyayi sharri irinna yarannan kinga mu tafi wlhi"
Ummin ta dakatar dashi tare da son gasgata abinda Hanan d'in ta fad'a, Ummi tace "ki gayamin gaskiya tare da sunanki"
Sunanan Hanan wata matace ta barni a tashar mota kuma bansan sunan garinmu ba"
Ajmal yace "Ummi wannan yarinyar fa karki d'auka k'aramar yarinya ce, wlhi babbace zatayi shekaru sha Uku"
Har yanzu dai Ummin bata kulashi ba, tace "oya shiga mu tafi zaki zauna dani?"
Hanan abin nema ya samu tana murna wacce bata nunata a fili ba ta shiga suka wuce caranci,
Sunyi tafiya mai d'an nisa ba wai sosai ba, Ajmal yasha kwana suka shiga anguwar, yana zuwa gaban wani tangamemen get bak'i yasha fenti ya danna horn, cikin k'an-k'anin lokaci aka bud'e masa suka shiga ciki, yanayin parking Ummi ta fito ta kamo hannun Hanan itama ta fito, gidane babba wanda yakeda kyau, tsayawa misalta kyawun gidan zai iya zame mana 6ata lokaci, Ajmal ya shigo hannunsa rik'e da rigar sanyi kasancewar garin na damina, ta gefen ido ya kalli Hanan da take ta wurga k'afa akan kujera sai Kuma ya shige ciki yana kiran Adnan,
HINDE
Tunda ta fara sauya wa Alhj Munir tunani ya za6i ya kaita  gidan wani malami acan garinsu da sunan gidansa zai kaita, saboda ayi masa tsakani da aljanun,
Tunda Hinde taga ya juya yabi doguwar hanyar da mahaifiyarta ta bata labari tafara murna, ta d'auki alwashin ta hanyar bin Alhji Munir inhar akwai masu biwa mutane hak'k'insu tabbas sai takai k'arar mahaifinta bayan nan sai tasa an rushe gidan duhu, amma tayaya zatayi hakan bayan bata da kowa?"
Tafiyar kawai Alhji Munir yakeyi Amma a zahiri tsoro ya cika ziciyarshi, gashi ya jik'e gurin da yake zaune da fitsari, sunyi tafiya mai nisan gaske kafin suka shigo garin Jos, yayi parking motarshi a farar gada, yace "zan je duba wani mutumi kizo muje?"
Hinde tace "kalan idan na fita ka gudu ko? to wlhi Babu inda zanje kafarka k'afata
Banyi editing ba.
Littafin Wake d'aya na kud'i ne akan sassaukan farashi, a jiya nayi rangwame ga wad'anda suka biya kafin mu shiga paid nace su bada 300 daga lokacin da muka gama free pages ya koma 500  a 10 free page zai k'are  08141799224

# Love
# Romantic
# Funny

Mom Islam
*WAKE ƊAYA💍*
MomIslam

_True life story_

*Arewabook Momislam11*


K'arshen Free pages

Page 9

Bata fito ba, har yayi nisa tana cikin motar sai ta6e-ta6e take yi masa, batayi aune ba tayiwa motar key garin rawar kai, mota ta fara tafiya da Hinde babu tsayawa, Hinde na ganin haka ta tsala ihu ta lek'a ta window tana cewa "dan darajar iyayenku ku tsayar da wannan abin, nifa bansan inda abin ze kaini ba"

Saura kad'an motar ta shige shagon wani mutumi, mutane da yawa suka cika gurin tare da taimakon tsayar da motar,
Alhji Munir ya iso hankali a tashe ya kalli cukowar mutanen dake tsaye a gurin yayi musu sannan yace "lafiya kuwa?"
Wani daga cikinsu yace "inafa lafiya y'arka zata hallaka mutane" Hinde ta zaro ido kafin tace "kai meye a kanka?"
Mai maganar yace "hula ce mana ko bayan ita nasa wani abu ne?"
Hinde tasa dariya tare da cewa "mutane basayin kyau wlhi rayuwar gidanmu tafi komai birgewa illar rashin yawo ne kawai"
Da sauri Alhji Munir ya kalleta kamar meson gano wani abun, sai Kuma yayi musu godiya ya shiga motar ba tare daya tanka mata ba suka wuce cikin garin Jos, suna tafe yana tunanin inda ze kaita,
"Gidan Affan"
Alhj Munir ya fad'a a fili"
Hinde da tsoro ya cikata ta rasa inda zatasa kanta saboda tsoro shiyasa tayi kamar ruwa ya cinyeta,
A Bauchi road yayi parking motarsa, gaban wani had'ad'd'en gida, mai d'auke da get biyu, daga yamma akwai d'aya sai hanyar shigowa ta kudu shima akwai d'aya, Alhji Munir yace "muje"
Hinde tak'i fitowa, har sai daya daka mata tsawa sannan ta fito jikinta na rawa, duk rawar da jikinta yakeyi bai hanata shafa jikin get d'inba tana shinshinawa, nanma sai dayayi mata magana sannan ta taho da gudu,
Hinde bata ta6a rudewa ba sai dataga tsarin gidan kasancewar tunda take Babu wani abin k'yle-k'yale da ta ta6a gani sai da ta fito waje, Alhji Munir ya rik'e hannunta suka k'arasa ciki, suna shiga parlon ta wani zabga uban ihu Wanda yasa Affan dake can d'akinsa na saman bene sai da yaji ihunta,
Alhji Munir yace "lafiya kuwa?"
Hinde ta nuna mutanen dake wulk'awa a TV tace "wlhi Kuna zaune da mutuwa baku sani ba"
Alhji Munir ya tsorata kafin yace "ban gane ba Hinde?"

Hinde ta mik'e da sauri ta tsaya cak akan kujera mai zaman mutum biyu kafin tace "laushi kamar kar in bar gidannan"

Wani saurayi yazo wucewa jikinsa sanye da blue d'in Kaya, da alamu uniform ne na ma'aikatan gidan"
Ya durk'usa har k'asa ya gaishe da Alhji Munir kafin yace "y'an mata sannu"
Hinde ta kwaikwayi maganarsa itama tace "y'an yata shannu"
Abin yaso bawa Alhji Munir dariya, sai ya gimtse yace "please kacewa Affan Abban Dogon agogo yazo"
Saurayin da keta bin Hinde da kallo ya wuce samma tare da isar da sak'onsa,
Wata budurwa ta shigo tana sanye da madai-dacin hijabi ta durk'usa ta gaishe da Alhji Munir kafin ta ajiye tran fruits d'in dake hannunta ta juya,

Hinde ta duro daga kan kujera tare da mik'a hannu ta d'auki mangoro tace "munada bishiyar mangoro a gidanmu Amma wannan yayi girma da yawa"
Ta kalli lemu da abarba da kankana da gwanda tace "wad'annan bansan ko meye ba, kai idan ka sani d'an gayamin"
Alhji Munir ya waiga baiga Wanda akace masa kai d'inba sai yace "au wai dani kike?"
Hinde ta ta6e baki kafin tace "to da dawa nake?"
A hankali yake sakkowa daga matattakalar benen, saurayi ne kyakkyawa fari yana d'auke da dogon hanci bakinsa madai-daici amma bashi da wani tsayi can yanada shi babu laifi, yana sanye da milk d'in riga, wandon jikinsa kuwa black ne mai kyau sai zubunan da suka wadata yatsun hannunsa zobunan sunkai guda uku, hannunsa na d'aure da tsadadden agogo mai jikin silba shima yayi kyau, kafarsa na sanye da takalmi silifas wanda ake Kira da d'an madina,
A hankali ya iso gurin Alhji Munir kafin ya nemi guri ya zauna sannan ya ce" Alhji Ina wuni ya jama'a"
Alhji Munir yace "lafiya Lau tun tuni nake jiran fitowarka amma shiru?"
Affan ya sosa kansa kafin yace "am sorry Alhji bacci nakeyi shiyasa"
"Ina Hajiya Amina?"
Alhji Munir ya tambaya kai tsaye,
"Tana part d'inta"
Alhji Munir ya mik'e kafin yace "au na d'auka ai a guri d'aya kuke?"
Affan yace "a'a dama tun tuni tana can sai dai tana shigowa nan kullum"
Alhji Munir yace "to Bari muje can d'in"
Yana rik'e da hannun Hinde data zubawa Affan ido tak'i kawarwa, janta da taji anyi ne yasata cewa "ammafa Alhji ka iya bak'inciki, Baabata tacemin a Aljannah akwai samari to wlhi naga d'aya, inba sa'a bama gidan Aljannah muka shigo"
Alhji Munir yayi murmishi,
A k'ofar parlon Hajiya Amina ya tsaya tare dayin sallama, Hajiya Amina ta amsa tana daga ciki a zaune kan kujera y'ar aikinta na mammatsa mata k'afa, Alhji Munir ya k'arasa cikin fara'a yace "Hajiya badai ciwon k'afar bane ya tashi?"
Hajiya Amina ta d'ago kanta tare da sakin murmishi tace "laahh Kaine a gidan namu?"
Alhji Munir yace "wlhi nine Ina wuni"
Hajiya Amina tace "lafiya Lau ya k'ok'ari?"
Alhji Munir yace "lafiya Lau na kawo miki bakuwa ne"
Hajiya Amina da son mutane tace "aikuwa inhar hakan ta kasance zanyi murna dama shekaran jiya y'an aikin namu suka tafi gida anyiwa mutum Uku aure kaga daga ni sai Ladidi can kuma gurin Affan Aisha ce"
Alhji Munir yayi hamdala saboda yasan idan yakai Hinde gidansa sai matarsa tayi Mata dukan tsiya, duk da dai yaje gurin malami dazu yace masa mutum ce ba aljana ba"
Alhji Munir yace to ai gatanan Hajiya na baki wuk'a na baki nama yarinyar yayar matata ne shine nace barin kawota"
Dama Hinde gurin zama take nema shiyasa da Alhj Munir yayi wannan k'aryar ko magana batayi ba.
Anan gurin Hajiya Amina yaci abinci shinkafa da Miya da aka kawo masa yasha ruwa yayi Mata sallama ya wuce.
Zuwa dare an kammala abinci an kunna engine haske ya gauraye d'akunan, Hinde ta mik'e tana tsalle"
Hajiya Amina tace "y'ata ki nutsu mana"
Hinde ta zaune tare da kallon mutanen da suka fara motsi a TV tace "Hajiya dan girman Allah ki fitomin da ko mutum daya ne mu gaisa"
A inda Hinde tayi maganar sai ta bawa hajiyar dariya,
Ladidi dake cin taliya tace "ke basa fitowa kallonsu kawai akeyi"
Hinde ta ta6e baki kafin tace "Hajiya Wai hakane?"
"Eh hakane jeki d'auki abinci kici naga kamar ba'ayi Kiran sallah ba"
Jikin Hinde na rawa ta d'auko abincin dake cikin

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment