Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
    _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

    
            

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM DASUNAN ALLAH ME RAHMA ME JINKAI INAFATAN ALLAH YA TEMAKENI YABANI IKON RUBUTA WANNAN LABARI DANA DAKKO BA AKAN WANI KO WATABA KAGAGGEN LABARINE INAFATAN ALLAH UBANGIJI YABANI IKON YINSA CIKIN AMINCI KUBIYONI DAN KUGA IRIN SALON DAYAZO DASHI*


'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA NAMTARY UMMYN ABBA ALLAH YA JiKANKI YASA MUTUWA TAZAMO HUTU A GAREKI, ALLAH YABA8 MIJINKI DA YARANKI DA DUK WANNI MAKUSANTANKI HAKURI DA JURINYAR RASHINKI😭🙏🏻'''


Page 1-2



Yanzun ta samu ta gama azakar tana son ta koma baccin safe koda na minti goma ne, amman ina hayaniya mutanan gidan su ba zasu barta tayi wanann bacci ba gashi tana jin kanta nayi mata ciwo rabon ta da bacci tun jiya karfe ukun dare da ta tashi sallahr dare..

"Ohni Rumaisa, har sai yaushe mutanan gidan nan zasu san ba kyau shiga hakin mutum, mtsssss ina anfani ace gida baya yin shiru har sai in kowa ya kwanta sannan zaka ji gidan shiru, sai ka Aku haba, ni dai abun ya fara damuna wallahi."

"Aaha Rumaisa ke da wa Kuma,  naji kina ta maganganun? "Mama nida mutanan gidan nan mana, "To Rumaisa in ba hakuri mai za muyi, ai matsalar *GIDAN HAYA* kenan, yanzun fa fada ake da Lami da Halimai, wai Lami taga Halimai tana dibar mata abinci, Kuma ita abincin mijinta ta ajiye ma nashi,  kinji asalin fadan."

"Kai gaskiya Halimai bata da hali Mama,daga ita har mijinta, ni shiyasa bani son zaman tsakar  gidan nan, duk wata gulma daga jikinsu take fitowa, daga Halimain har ita Lami din, yau dai tasu ta hada su shiyasa aka jisu a cikin gidan nan."

"To ya zamu yi Rumaisa ai sai hakuri, shiyasa Babanki shima baya san yaga muna zama cikinsu, yace halinsu bai ye mashi ba."....cewa Rumaisa tayi."ai Mama basu da hali ko daya, sun sama kowa ido a gidan nan, bayan gidan nan gidan mutane ne, daki goma ne a cikin gidan Kuma kowane daki akwai Wanda suke zaune cikin su, ai dole ko wace gulma a unguwar nan ta fito daga gidan nan."

"Gidan nan Mama kinga sana'a akeyi kala kala, da masu kitso da masu kunshi da masu wankau, harda dai basu yin abinci sai dawa ba dole ayi gulma ba a gidan nan."

Itada Mama bata ce komai ba, tana tunanin halin yan gidan nasu.

Niko nace ai *GIDAN HAYAR* kenan Mama, tana cikin tinanin taji Rumaisa na yi mata magana.

"Yauwa Mama yau da wuri zani tafi gidan aiki na, saboda ina son nadawo da wuri na wuce Isilamiya, bari ma na tashi kawai na shiga wanka, Mama zo ki duba man kar wani ya shigo man ina cikin wanka kinsan dabi'ar gidan nan ce, bayan mutun yasa ba shi daya ke da gida ba."... Cewa Mama tayi."Yo ko kai daya ke da gida ai kace akwai kowa in ba kowa sannan kashiga, balle wannan gida ba naka ba *GIDAN* *HAYA*, ai Rumaisa hakuri zamuyi da halin yan gidan nan, tashi mu tatafi ki samu ki shiga kina fitowa nima na shiga, daman Babanki Shi tunda asuba yake wankashi."..."To Mama."

Haka su Rumaisa suka tashi, suka fita tsakar gidan, suka ebi ruwa a rijiya sannan suka kama hanyar kewaye, amman kafin su ida shiga Lami ta taso wai ta rigasu niyar shiga zuwa tayi ta nemo buta, haka su Rumaisa suka kyaleta basu kulata ba, ita ko Lami taso su biye mata suyi fada tunda uwar safiya sai kace suma kalar tane..

Bayan Lami ta  fito, Rumaisa ta fara shiga sannan Mama ta shiga suna gama wa suka koma dakinsu Rumaisa ta shirya cikin wata yar atamfarta tasa hijab dinta ta kama hanyar zuwa gidan aikinta..

"Assalama Alaikum."

"Amin wa'alaikumus Sallama."... "Aunty ina kwana."! ?..."Lafiya lau Rumaisa, Antashi lafiya."!?..."Lafiya lau Alhmdulh.".."ya Mamarki take."!?.."Duk suna lafiya Aunty."..."To Alhmdulh, Amman yau Rumaisa kin zo da wuri.".... "eh Aunty inason nagama da wuri zanyi wanki sanann na wuce Isilamiya."..."ok Allah sarki, Allah ya taimaka."..."Amin Aunty."

Nan dai Rumaisa ta fara yin moping din main parlour, sannan tayi na dakin Hajiya Maryam, ta wuce ta gyara kitchen, sai tayi wanke wanke, tana gama wa, ta taya Hajiya Maryam sauwar abincin rana,suka jerashi a dining sannan Hajiya ta sawa Rumaisa nasa ta, tayi mata godia ta wuce gida, tana jin dadin aiki gidan Hajiya Maryam, dan ita Hajiya mutun ce mai mutunci bata da wulakanta Dan  Adam, duk dukiyar mijinta da yake da ita  haka baisa ta ji warin tallkaba...

"Sallama Alama Alaikum, Sannunku da hutawa mutanan gidan nan."... Cewar Rumaisa da dawowarta kenan daga gidan aiki.

Ai Lami cewa tayi."ahaiye mun de mungode Allah bamu zuwa gidajen mutane zalamar Abinci, ko Hindatu."?.... Itaam Hindatu cikin wulakanci ta fara dariya tana cewa"aiko dai Lami, yo Allah ya bamu wadatar zuci,  mai zamuyi gidan wasu kwakwa, Halimai."?.... Ta jefa ma Halimai tambayar taba dariya raini, itama Halimai cewa tayi."Uhmmm kedai tayani gani Hindatu wai shine aka kira da *ANKI CIN BIRI* , *ANCI DILA* , hahahaha, yo ni  Halimai Allah ya sawaka man da zuwa kwakwa gidan mutane, ai na gwanma ce na kwana banci komai ba."... Ta karasa maganar itama tana kallon Rumaisa tana dariya.

Cewa Rumaisa tayi cikin ɓacin rai."Eh ai shiyasa naji ku yau da safe kuna fada a kan abinci, nagode ma Allah ni *Rumaisa* da nike zuwa kwakwa gidan mutane, Alhmdulh tunda bani satar abun wani, kin ga ko da *MUGUWAR RAWA,* *GWAMMA KIN* *TASHI* "

"Kam ubancan, ubawa kike gayama magana haka"? Cikin kukuwa da ɓacin rai tace."Wanda ya tsargu da kashi baki ji masu karin magana na cewa *IYA GANI, IYA KYALEWA,BA* dan haka in dan zaku yi abun ku karda ku sake ku sanyo ni, domin ni ba kyaleku zanyi ba kunji nagayama maku, baku iya komai ba sai *ZAMAN* *BANZA* da *SA* *IDO* aikin kenan an dai ji kunya wallahi."

"Ke Rumaisa, wai maiye haka?  bana ce maki karda na sake jin kin biye ma su ba?  kuna cece kace, sai kace wasu abokanki?  baki san dai kiga bakina yayi shiru ko."!?... Cikin firgici tace."Aah Mama ba haka bane, amman dan Allah kiyi hakuri ba zan Kuma ba."... Cewa Mama tayi."bani zaki ba hakuri ba su zaki ba hakuri, su da kika dage kina ta gaya masu magana san rainki sai kace wasu kawayenki, ai ko ba komai sun girmaiki, maza basu hakuri kafin raina ya baci."

"Su Lami dan Allah kuyi hakuri ba zan Kuma ba.".... Cikin fada Lami tace."da hakurin ya mutu sarakar nawa kika bada? fitsaraira marar kunya kawai."... ita dai Rumaisa bata ce komai ba ta shiga warta daki ta barsu tsakar gida sunata aikin jaraba..

"Rumaisa."... "naam Mama."... "daga yau itace rana ta karshe da zan maki magana a kan fadan da kike da su Halimai, taya zaki tsaya kina biye masu? Kuma kin san sarai mutanan nan ba wani tunani ga resu ba?  dan da kowa ma fada suke tunda suke yi da mazajensu dan haka daga yau kar na sake ji.".. "insha Allah Mama bazaki sake ji ba, bari na tashi nayi Wannnan wanki kafin lokacin Isilamiya yayi."

"To shikenan Allah yayi maki albarka, ya baki miji na gari."... "Amin Mama."

Bayan Rumaisa ta gama yin wanki, ta shirya ta wucewarta Isilamiya tana dawo wa ta tadda Mama tana aikin Tuwan dare, nan ta cire hijab taje ta kama ma Mama aiki, suna gama tuwo da miya, suka diba suka bama mutanan gidan sannan suka kwashe tuwansu suka ajiye a daki, suna jiran Baban Rumaisa ya dawo suci abincin, da yake tare suke cin abinci dare, bayan ya dawo suka ci abinci sukayi sallah kowa ya kwanta yayi bacci....




*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Vote
And
Like
Pls


🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
           _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

            

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar
da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________________

      

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

'''NASADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA NAMTARY UMMYN ABBA ALLAH YA JiKANKI YASA MUTUWA TAZAMO HUTU A GAREKI, ALLAH YABA MIJINKI DA YARANKI DA DUK WANNI MAKUSANTANKI HAKURI DA JURINYAR RASHINKI😭🙏🏻'''



Page_3-4

"Rumaisa.".. "Naam Baba, ina kwana."?  "lafiya lau, kin tashi lafiya"? "Lafiya lau Baba, "yauwa da man magana nike so nayi dake, jiya Mamanki ta gaya man yanda ki kayi fada da mutanan gidan, to daga yau karki yarda na sake ji, Kuma ba tarbiyar da muka baki ba kenan, bani son naga karami Yana raina na gaba da shi kinji."?cewa tayi. "Eh Baba, naji." cewa yayi."To Allah yayi maki albarka." "Amin Baba."
"To Maman Rumaisa ni zan wuce neman kudi, da akwai abunda kuke bukata."?  Cewa tayi."Eh ba sauran magi ya kare yau."murmushi Baban Rumaisa yayi sannan yace."Shi Kadai ya kare babu komai."? Cewa itama tayi tana murmushi. "Eh Shi kadai ya kare gaskiya."cewa yayi."To ga wata Naira dari biyu nan kun sawo magin, ni na wuce sai na dawo."ansa tayi tana cewa. "To angode, adawo lfy."cikin jindadi yace."Allah yasa, Amin."
"Mama bari nasamu na dan kwanta kafin gari ya ida yin haske."cewa Mama tayi. "Aah tashi dai mutashi mu shiga wanka, kafin mutanan gidan su tashi bacci."cewa tayi. "To shikenan Mama, na tashi mu wuce ko."?.. "to daman Babanki ya jawo mana ruwan wankan har dafa mana Shi yayi mu tafi kar ma ya huce."
Rumaisa ta fara shiga wankan tana fitowa ta tsarema Mama itama ta shiga, suna fitowa suka yi wanke wankensu duk abunda suka san nasune sai da suka kaudashi, suka kai shi daki, suka kulle dakinsu suka yi kwanciyarsu suna basu tashi ba sai karfe 9 na safe, Rumaisa ta shirya ta tafi gidan aiki...
Sallama Alaikum, Aunty ina kwna? Kin gani yau Kuma sai yanzun."cewa Hajiya Maryam tayi."aiko dai yanzun Fadila ta gama tambayar ki, zaki raka ta wai kunshi, ta gaji da jiranki, sai Yayansu yayi dropping din ta ya wuce wajen aiki."cewa tayi."ayya banji dadi ba, ai da na raka ko mike kafafu nayi tunda yau babu Isilamiya yau, ai shiyasa ban zo da wuri ba."
"Nikom nace Rumaisa yaushe zan baki waka kiyi man awara, kinsan Fadil yana bala'in san awara, gashi yau na ida soya mashi ta cikin freeze, nasan gobe dan Ubanshi sai munyi fada da Shi in yaji babu awarar.".. Murmushi tayi sannan tace."Shi dai Yaya Fadil yana son awara naga Alama, bakomai Aunty bari na ida aiki yanzun naje nayi maki ita zuwa anjima nagama insha Allah."
"Bani takura maki ba dai ko Rumaisa."?...cewa tayi."haba Aunty wata kallar takura, ai kifi karfin komai a guna.".. "To nagode Rumaisa, bari na tashi ya dibo wankan kafin ki gama."cewa tayi."To Aunty a fito lafiya."..  "Allah yasa."
Bayan Rumaisa ta gama yin aikin gida, ta ansa waken ta wuce gida, tana mamakin yanda Fadil yake da halinshi, shide haka Allah yayo Shi cewa tayi."ni Rumaisa ai tunda nike ban taba ganin dariyarshi ba, gaskiya Fadila tana hakuri da Allah ya hada ta da Yaya mai halin Fadil ace mutum baya dariya kullum fuskar shi tamau sai kace an aiko mashi da sakon mutuwa."haka ta kama maganar ta cikin zuciya har ta isa gida, dan tayi alkwarin baza ta sake yi masu sallama ba, in ba dai su Maman A'i ta iske ba a tsakar gidan wannan zata yi mata sallama har ta gaidata domin Maman A'i mace mai hankali da wayau...
Dawowar Rumaisa gida kenan tace."Mama ga aiki awara nan zamu sake yi ma Aunty Maryam." murmushi Mama tayi tace."A'a to bari na fito daman zaman banza nike yi bani da abun yi."nan fa Mama ta fito cikin some minute suka tsinke wankan, nan Rumaisa tasa hijab takai markade, tana dawowa suka daura sanwar awararsu, suna fira da Maman A'i, nan Hindatu ta fito tana yi masu wannan kallo sanann tace."Allah ka rabamu da matatsiyar zuciya, in ba rashin zuciya ba, mutane sai dan banzar kwakwa, in ba kwakwa ba ace duk sanda za'ayi awara kuke yinta dan ku samu na dare."
Maman A'i tace."Ai Hindatu kasan ance *NEMAN NA KAI,*  *HALAK NE,* dan haka ba ruwanki da lamarinsu, ya ka mata ku chanza hali, haba Hindatu mutanan nan basu tsarema ku komai ba amman duk kunbi ku sa masu ido, Kuma ku ke da abun da ido."ɗaga ma Maman A'i hannu Hindatu tayi tana cewa."dakata malama, au ashe yar iya Andawo?  yanzun za'a fara yin shigar sugula, inba shigar sugula ba wa ya saki cikin wannan maganar yar'nema."? Cewa Maman A'i tayi."Ban sani ba sai naji bugu sannan."Maman Rumaisa ce ta fara ba Maman A'i hakuri dan taga ranta ya fara ɓaci yanzun zata biye masu suyi fada cewa tayi."Dan Allah Maman A'i kiyi hakuri, karda ki biye mata, duka duka maiye duniyar, da za'abiye Anita bata lokaci gurin fada, kinga ma awarar ta kusa yi muna gama soyawa sai mu shiga daki ba shikenan ba." cikin raina da jin zafi da hassada Hindatu tace."da ya fi maku ma kwakwata banza da ku."Maman A'i tace."ke dai kije ji da shi, mundai yi gaba sai dai a bimu da ido."
"Maman A'i dan Allah kibar biye masu, mutanan nan ba hankali ne dasu ba." Cewa Maman A'i tayi."wallahi Maman Rumaisa, indai su kayi bisa idona sai na yi magana, yo ina dalili mutane ba ku hada miji ba, amman sunbi sun sa maka ido suna kishi dakai, ai wannan kishi ne da hassada, haka zasu kare a wulakance, mu Kuma insha Allah yanzun muka fara yin gaba, dan munyi masu nisa fidtinkau, dan ba yabon kai ba baki daya gidan nan mazajenmu sunfi sauran nasu, ai Alhmdulh ko nan aka tsaya."cewa Maman Rumaisa tayi."Allah yasa dai mu dace, "Amin Maman Rumaisa...
Bayan sun gama yin awarar, Rumaisa taje ta kaima Hajiya Maryam, nan suka dan yi hira sannan tayi mata sallama ta dawo gida direct dakinsu ta wuce, daman tsakar gidan su Lami ya iske suna zaman banza, zaman gulma...
"Rumaisa har kin dawo? "Eh Mama wallahi yau duk na gaji sosai, "ai dole, tashi kici abinci ba sai kin tsaya jiran Babanki ba, "To Mama." bayan ta gama cin abinci ta samu ta kwanta cikin bacci taji ana fada da mijin Halimai da na Lami, suna ta fada sai kace yara kanana,  wai abunda ya hada su, shi mijin Lami yace ma mijin Halimai yayi ma Halimai tsakani da matarshi dan ya lura ita take koya ma Lami zaman gulma da kirbibi, shi kuma mijin Halimai yace suna koya ma juna dai, dan matarshi ba ma gulmaciya bace, da kyal da jibin koshi su Baban Rumaisa suka raba wanann bala'i...
"Na boni ni Rumaisa, wai har sai yaushe mutanan gidan zasuyi hankali."Rumaisa tace tana mamaki dan  tunda suka zaune a gidan nan bata taba ganin rana ta zo ta koma ba, ba'ayi fada a cikin gidan ba sai kace antara karnika a cikin gida, haba Allah ya sawaka ya yaye masu wannan masifar da ke damunsu....


*Tabbas naga ruwan comments dinku sosai, sai kash abunda baiyi man dadi ba😩, sansanin yar'mutan kankia, bakuyi comments ba, haka real jameey fans  one and two comments dinku yayi man kadan gsky😏, Mudun baku gyara ba zan daina yi maku posting 🤷🏻‍♀️😂*


*Yar'mutan kankia ce❣️*
Share
Comment
Vote
And
Like
Pls

🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭
   A GIDAN HAYA
🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭🏭

_STORY AND WRITING_ _BY_
           _Jameelah jameey_
*Yar'mutan kankia ce ❣️*

*🌍MANAZARTA*
*WRITERS ASSOCIATION📚🖊*
      *M. W. A*

'''Kungiya d'aya tamkar da dubu.Masu Nazari da Aiki da Ilimi, Burin 'kungiyar a ko da yaushe shine ta fad'akar ta kuma Nishad'antar da masoyan ta.🤙🏻'''
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
___________________________________

     

*BISSIMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

Page_5-6

Washe gari, bayan su Rumaisa da Mama sun gama wakansu da wanke×2,suka dumama tuwan da ya rage masu sukayi kalaci bayan sun gama yin kalacin, Rumaisa taje dakin Maman A'i tayi mata karin karatu ita da A'i, bayan ta gama yi masu ta wuce gidan aiki..
"Sallama Alaikum, "Amin w'alaikumus sallam, Rumaisar Mama har anshigo kenan."?..."Eh wallahi Fadila Allah ya yarda, jiya Aunty ta  ce man kin jirani zani raka ki gun kunshi."cewa Fadila tayi."Eh wallahi, ashe ma mota ta bata da mai, sai da na shiga na kuna tace bata san wannnan ba sai dai Yaya Fadil yayi drooping din na, karki so kiga kallar wulakacin da nasha jiya kawata, Allah yaso ki ba baki biyo ni ba inajin yanda kike da saurin fushi sai kinyi kuka."cewa Rumaisa tayi cikin mamaki."Ke ko wannan wani irin wulakanci ne?da har zaisa mutum kuka? "wai zan shigar mai da datti cikin mota, duk kuwa wankan da nayi amman Yayi Fadil cewa yayi datti ke gareni kiji fa kallar wannan wulakancin da cin fuska?  kuma ba'a fita motar sai yayi 15min ta kashe ta, sannan zaka bude ka fita, ai na gaya maki na manta shap da wannan roles din nashi yana tsaya wa na kama marfin mota zani fita, kinga wata kallar tsawa da ya maka mani, wallahi bansan Lokacin da nayi Ihu ba, kuma dan nayi Ihu wai nasa mashi ciwon kai, ke dai wallahi ina tausayin matar Yaya Fadil."cewa Rumaisa tayi."Ha haha haha!  gaskiya Fadila sannu kiyi kokari, ai in nice da tuni munyi ta ba dadi, kin san Allah ni bani san tsawa ko ya take, ni fa lokacin damuna bani yin motsin kirki saboda bala'in tsoran tsawa nike, balle wannan Yayan naki ni ko dariya ban taba ganin yayi ba, maganar fatar baki bani fatan ta hadani da shi, shiyasa nagode ma Allah banda dakinshi nike gyarawa."cewa Fadila tayi."To ai shi Yaya Fadil koni baya cika san ina shigar mai room ba, balle yan aiki."...  "To ai muma yan aiki an hutar damu ko Fadila."? Cewar Rumaisa tana murmushi, itama Fadila cewa tayi."Aiko dai, shiyasa yake gyara wajen shi, in kinga part din Yaya Fadil sai ki rantsa kice dakin amarya ne, saboda tsatarshi."Cewa Rumaisa tayi."yajii dadi, niko inason mutun mai tsata sosai."Umma tace ta fito zata wajen aiki ta gansu suna ta aikin surutu tace."Kuna nan kunata abun surutun naku ko."? "Aah Umma, kawai dai ina gaisawa da kawata."cewa tayi."ai Fadila kinsan nasan gaisawarku ke da Rumaisa sai kuyi awa daya kuna ta zuba, da anyi maku magana sai kuce wai gaisawa kuke."Rumaisa tace tana murmushi. "Aunty ayi hakuri yanzun zamu tashi insha Allah."Umma tace."Allah yasa, ni na wuce office Fadila keda Rumaisa kuyi mana lunch."... "To Umma mai zamu dafa."? Umma tace."Ku yi komai yayi, amman ku san kunyi abunda Fadil yake ci karda kuyi abunda baya ci, yazo yaita yima mutane bakin rai.".. "to shikenan Aunty,  insha Allah."
"Kawata, bari nayi sauri na ida wanann moping din sai mu daura sauwar ko."? Fadila tace."Eh Rumaisar Mama, amman bari na taya ki ko munyi sauri mu gama, kafin Yaya Fadil ya shigo."
Kallon ta Rumaisa tayi sannan tace. "Fadilar Yaya Fadil, godia nike yar'umma.".... bayan sun gama yin aikin gidan baki daya nan fa suka shiga kitchen suka fara tunanin mai zasu dafa at the end Rumaisa tace tunda suna da garin dawa mai zai hana suyi tuwan dawa miyar danyar kubewa taji Nama da manya shanu, nan fa Fadila ta Amince, daya ke ita manyar tuwo ce, shap ta manta da Yaya Fadil dinta baya son tuwo, balle ma tuwan dawa..
Nan ko Rumaisa ta zage tayi tuwan dawa mai kyau, wanda kallo daya zaka yi mashi sai ka sake kallon shi tsabar kyaun da yayi, nan suka kulleshi a leda, sannan Fadila ta gurza kubewa ita kuma Rumaisa ta hada miya bayan ta gama hada miya nan take gidan ya gauraye da kamshi take yawun Fadila ya fara tsinkewa, tana ta yaba Rumaisa wurin iya gorki, ai suna cikin magana suka ji ana cewa."Ummana yau mai kike dafa mana cikin gidan nan mai dadi kamshi haka."? Fadila ce tace."Laaaa ga Yaya Fadil, oyoyo Yaya Fadil, ai ba Umma bace take yin girki yau ba."wani kallo yayi mata sannan yace."wacece take yin girkin nasan dai ke ba iya girki kika yi mai kamshi har haka ba."? Cikin shagwaɓa tace."haba Yaya  Fadil maiyasa zaka ce haka, bayan ni na gurza kubewar da akayi miya."murmushi yayi ma kanwar tashi sannan yace."to naji duk ba wannann na tambayeki ba wace ke yin wannan abun mai kamshi har haka."? Cikin jindadi Fadila tace tana kama hannunshi tace."Eh Rumaisa ce."zaro ido yayi gami da fisge hannunshi daga nata yana cewa."What? Wacece Rumaisa kuma."?cikin mamaki Fadila tace."haba Yaya Fadil kina nufin baka san Rumaisa ba sabuwar yar aikin gidan."? ɗaga mata hannu yayi yana mai wurga mata harara yace."Hey yaushe na zamo abokin wasan ki? Ya ina yi maki question kema kina yi man naki Fadila?  in nasan ta na tambayeki."? Ta tsora da yanda ya chanza mata lokaci guda cewa tayi."Aah hakane kuma Ya×2 Fadil, to Rumaisa yar'aikin gidan nan ce, kuma kawata ce."kallonta yayi yana mata kallon taji kunya bata iya girki ba yace."ita Umma tana ina."?cikin gajiya da question din Yayan nata tace."ai kasan ta hospital dinta ko? ko kamanta yau Monday? Tana zuwa taga patient dinta na musaman."cewa yayi "ok I forget about it , Allah abincin yayi dadi, ita Umma tasan ba ko wane abinci nike ci ba, shine taba yar yarinya tayi, salan tayi mana jaqwalgwalo."ya fadi yana ma Fadila kallon banza, dan yaji haushi sosai da ya tadda Umma bata nan.
Rumaisa ce ta fara gwalama Fadila kira."Fadila! Fadila×2,wai ina kika shigeni
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment