Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ο»ΏMAJNOON
Complet
Mr smiles
Ebook creator: Shuraih Usman
@http://fb.com/hausaebooks
[10/20, 10:33 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJ'NUN*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

1 and 2
Via *OHW*
_A love story_πŸ’
*BISMILLAH*

" MAHAUKACI !! MAHAUKACI!!! " Shine sunan da dandazon yara kekiransa yana tafiya suna binsa a baya
Wasu daga cikin yaran dake biyarsa har rigarsa sukeja

Matashin saurayine mai kimanin shekaru 30, gashin kansa duk ya kudun dune,
Launin fatarsa ya chanza saboda dattin dake jikinsa rigarsa duk ta yage,
Farine amma saboda tsabar datti har farin yafara dishewa, fatar jikinsa dukta jeme saboda zafin rana hakama tufafin dake jikinsa, amma hakan bai hana kyan fuskarsa fita ba, kyankywane duk da cikin sigar hauka yake**
Tafiya yakeyi yaran kuwa sai binsa sukeyi suna masa ihu, wani lokaci idan yagaji da ihun yakan dan juyo yabi yaran da gudu sai su zura da gudu..

Hakadai yaci gaba da tafiya, idan yaga bola a gefen titi yakan tsaya yayi tsince2 sa kafin yaci gaba da tafiya,

Wata waka naji yaran sun fara masa suna cewa "ga maj nun uban tanbele, ga maj nun uban tanbele " shikuwa sai dukawa kasa yakeyi yana tsintar ledojin pure water, yana kwasar rawa ga alama wakar tanai masa dadi..

*** *** ***
A hankali take taku kamar batason taka kasa, matashiyar budurwace yar shekaru 20 cikin shigar kamala tufafin hausawa atamfa da zani sai kuma katon hijab data saka har kasa.
Hannnun rike da 'Yar karamar kula ta abinci...
Dai dai kwanar wani layi ta kunnu kai Tun daga nesa ta hangi yara sunai masa waka, "Ga maj nun uban tanbele"
Wani zarr taji jikinta yadauka, dasauri takarasa gurin duk ta watse yaran sannan ta dubesa ta saukar da murya tace "haba ! Haba meye haka katsaya yara suna mai maka waka kana rawa" sai tayi shiru tana kallonsa kafin yadago kai ya kallesa, sannan tace "ko so kake na fasa aurenka kane ?"

Maj nun yayi saurin girgiza mata kai "a a nadaina " yana gama fada yayi sauri yazauna ya langwabe kansa

Murmushi tayi tadawo kusa dashi tazauna ta mika masa kular datazo dashi "ga abincika maza ka cinye kabani kular na wuce gida, tun kafin Abbana yadawo "

Da karfi ya firgi kular yana kokarin budewa, da kyar yasamu ya iya budewa shinkaface da namomi akai, karkade hannunsa kawai yayi ya fara aikawa cikinsa sako.

Kura masa ido tayi tana kallosa cike da tausayi, bata ankaraba tafara hawaye, wani iri takeji a zuciyarta akansa, tarasa sanin ko meye wata zuciyar tace mata sona wata zuciyar kuwa tace mata tausayine... ita kanta takasa baya kanta amsa, *so ne ko tausayi*
Tana zaune tana tunani harya kammala canye abinci ya miko mata kula "ungo" maganarsa tafitar da ita daga duniya tunanin datake ciki, tadan zabura kadan, sannan ta kirkiri murmushi tace "harka cinye " yace "eh " yana wasa da tsunmar rigarsa,
Mikewa tsaye tayi shima ya tashi ta dubesa tayi murmushi tace "nizan wuce gida sai nazo da dadare"

Maj nun ya hada kansa da kafada yace "nibanason kitafi kitsaya, muyi fira " yakarasa maganar yana gunguni
Dariya tayi kafin tace " to shikenan idan nazo dadare zamuyi firar yanzudai zan wuce gida"
"Tohm.. toh yaushe zamuyi aure" maj nun yafada yana cizon rigarsa

Murmushi tayi tana kalloso tace "gobe "

Tsalle yayi yana ihu cike dajindadi yace "idan mukayi aure a jirgi zan daukeki nakaiki india"

Dariya tayi sosai, saida taga yafara kuluwa sannan ta tsayar da dariyarta tace "tohm shikenan nidai na tafi sai anjima" tana gama fada ta fice tabar gurin, saida tayi nisa kan dashu saikuma tatuna da maganar daya fada takara saka dariya.. sai kace itama haukar takee
Saita fara tafiya ta juyo ta kalle sa tagansa sai tsalle yake wani irin mugun tausayinsa takeji,
Hakadai taci gaba da tafiya cike da tausayin maj nun daidai kwatar layinsu ta hangi wata bakar mota da karfi taja da baya gabanta ya fadi sosai "innalillahi wa inna ilaihin raju un " itace kalmar data subuce daga bakinta..


Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:33 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

3 and 4
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Tayi rau rau da ido kamar zatayi kuka, nan ta fara salati harta samu na tsuwa tadan wani lokaci sai kuma taci gaba da tafiya

Takai dap da Motar taji ankira sunan " *Rumaisa* !!!" Gabanta yafadi ko juyowa batayiba taci gaba da tafiyar ta ..

Da sauri yafito daga cikin motarsa ya tari gabanta sukayi ido hudu, ya marairaice fuska kmar zainyi kuka yace "haba rumaisa meyasa bakijin tausayin zuciyatane, plx kitsaya ki saurareni dan Allah koda na minti biyune "

Hawaye sunka cinciko a idon rumaisa, a duk lokacin data gansa wani irin bakin ciki takeji ya ziyarci zuciyarta,

Muryarta tafarasa rawa kalilan abu zai iya sakata kuka, bude bakinta kuwa sai kuka "wai menai maka kake bibiyana kahanani jindadin rayuwata dan Allah ka fita harkata"

*Fahad* yayi shiru yana sauraron kukanta, zuciyarsa na masa kuna, kwata2 bayason ganin kukan rumaisa, idan tana kuka shima jiyakeyi kamar zai tayata, muryarsa na rawa yace " sonki nake rumaisa zuciya ta tsunduma a cikin kogin sonki, iduwana basa muradin ganin kowa saike, a koda yaushe kece a mafarkina, plx rumaisa dan Allah kisoni"

Hawayenta ta share ta sakar masa wani irin tsaki tace " ko kai kadaine namiji a duniya bazan sokaba, daidai da dakika daya bantabajin ina sonkaba" kafita daga harkata, kabano hanya na wuce " tanakarasa maganar tana kokarin turesa, shikuwa sai binta yake a duk gefen dataje yana fadan plx rumaisa,

Da taga bayada niyar bata hanya taturesa ta wuce,

A karo na biyu yakara shiga gabanta yana fadan plx rumaisa, wlh ke kadaice a raina, nayi miki alkawarin zan chanza halina idan har kika amince da soyayya ta, kiduba fa kigani wannan ma kadai ai kinyi jahadii...

Bata jira yakarasa kalmarsa ta jahadi ba ta wanka masa wawan mari tas kakeji kafin tace "bana son, kuma natsani ganinka " takarasa maganar tahuci ta zagaya ta gefensa ta fice..

Tsayi yayi a guri daya sai kace bushanshiyar bishiya
Dafe gefen kumatunsa yayi yana mai jin zogin marin da rumaisa tai masa,

Hartayi masa nisa kadan yak'wala mata kira tajuyo ya saukar da hannunsa akan kuncesa ya share hawayensa yace " bazan iya hakura dakeba, domin kece muradina, tunda nabiki ta laluma amma kinki aminta dani dan haka yau zan saceki"

Yana gama fadan hakan yajuya ya shiga motarsa yabar unguwar

"Mahaukaci" rumaisa tafada fuskarta a ya tsune sannan taja Tsaki taci gaba da tafiyarta harta isa bakin gidan su gabanta faduwa yake akan maganar daya fada mata nacewa nasaiya saceta...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:33 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

5 and 6
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Tana isa kofar gidansu tatura kofar tashiga a harabar gidan taga motar abbanta a gefe yayi parking, cak ta tsaya guri daya, gabanta yayi mummunan faduwa, bugun zuciyarta yakara karfi, duk tsoro yakamata, domin tasan dacewa da suci karo da Abba akan maganar majnoon to gwanda ta fada rijiya zaifi mata sauki, da kyar ta iya taka kafafunta takarasa bakin kofar falo,

A hankali take tura kofar falo tashiga tare dayin sallama, jin sallamarta yasa ya mike tsaye yana jiran shigowarta..

A tsaye ta samesa fuskarsa a murtuke😑

Sau daya tadaga kai suka hada ido da sauri ta sauke kanta kasa, sum sum take tafiya kamar ba lanka ajikinta, gabanta sai faduwa yake tanufi dakinta...

RUMAISA!! Cikin hargowa yakira sunanta saida ta kusan faduwa akan tsoro

Hawaye suka soma zubo mata a hankali takarsa gurinsa, tas tas yadauketa da mari biyu kyawawa saida tasaki kara tayi baya tadafa kan kujera,

Da gudu umma tafito daga dakinta cikin baccinta tajiyo karar mari,

Alhaji lafiya" itace kalmar da umma take fada tana kokarin karasowa gurinsu, rumaisa najin muryarta ta tamike da gudu ta rungumeta tana kuka, cike da masifa yafara mata magana "bana hanaki zuwa gurin majnoon dinnan ba, wato kin maida maganata maganar banza, nizaki mayar karamin mutum, wannan shine karo na biyar kenan danayi miki a kansa amma kinki jih, to wlh kisani yau kinyi kuma kinkai karshe, gobe gaben nan zan daura miki aure da *faisal*, tunda nalura dacewa bakida hankali, meye abinso acikin mahaukaci, shashashar yarinya"

Rumaisa takara fashewa da kuka jin yakira sunan faisal, kuma da furucinsa na cewa gobe zai daura mata, batajin zata iya rayuwa da wani da namiji a duniyar nan idan ba majnoon bane, tana manne a jikin umma tafito ta gurkusa a gaban abba tana kuka ta rike masa kafa " dan Allah abba kayi hkr wlh banason faisal"

A fusace abba ya dukar da kansa kasa yana kallonta yace "idan bakya sonsa idan na aura masa ke ki kashesa" yana gama fada ya firgi kafarsa yabar falon yanufi dakinsa..

Durkusawa tayi kasan cafet tana kuka sosai, a lokacin umma takaraso gurinta fuskarta ba annuri tadafata tabaya " rumaisa"
Dasauri tatashi ta rungume umma tana kuka tace "umma nashiga ukku, abba zaimun aure da faisal, kuma wlh umma bana sonsa" .....

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com







[10/20, 10:33 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

9 and 10
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Da sauri abba yakarasa bakin kofar dakin yana dukan kofar dakin akan ta bude, amma taki bude wa, sai kukanta yakeji,

Saida yayi mata barazana dacewa idan bata budeba yanzu zaije ya dauko sepia key yabude dakin kuma idan yabude zaiyi mummunar saba mata

Sannam tatashi tazo tabude kofar, jikinta na rawa, ta shunkuyar da kanta kasa,

Abba yashigo dakin ransa a bace yake kallonta " wlh idan kika fita a gidan nan bada saninaba, banyafe miki ba, kuma wlh zan iya tsine miki, akan wannan *Majnoon* din, kehar kin isa nahaifeki kuma kikibin umurnina" da sauri rumaisa tadago kanta a lokacin har hawaye sun fara ambaliya akan fuskarta, tana kallon abba takara fashe da kuka "kayi hakuri abba bazan jeba wlh bazan je dan Allah karka tsinemun" da sauri ta ajiye kolar dake hannunta takarasa bakin gado ta kwanta sannan tadago kai tana dube abba, muryarta na sarkewa saboda kuka tana cewa "kagani abba na kwanta wlh ba inda zanje yanzuma zanyi bacci, sannan ta hada hannayenta guda biyu tace "Dan allah abba karka tsinemin" takarasa maganar tana kuka, sannan ta noke kanta cikin filo,

Abba yana huci yace " nidai na fada miki karkibar gidan nan bada saninaba" yana gama fada yajuya yafita yabar dakin

Kuka take sosai zuciyarta har wani zafi take edonta duk sun kunbura, yazatayi da soyayyar majnoon datake sabuwar fill a cikin zuciyarta.. haka dai taci kukanta har aka kira sallar isha sannan tatashi taje tayi alwala, tazo ta dora sallah, bayan tagama sallar tafara kwararo adu a, saida tayi hawaye kafin takarasa adu' ar, tana kammala adu'ar sannan tanade sallaya ta takoma saman gado ta kwanta zuciyarta cike da tunanin majnoon komai zaici yau cikin darenan, a dai dai lokacin hawaye suka sauko kan kumatunta, koda tagama tunaninsa hawaye sharkaf a fuskarta, a hankali take fitar da sautin kukanta, tarasa gane wane irin sone takeyiwa mahaukacin nan,

Sai a lokacin tatuna da bata rufe kofar dakin taba, da kyar ta iya tashe taje ta rufe dakin sannan tadawo tayi shirin bacci sannan takara komawa kwance, tana cikin tunaninsa bacci ya kwasheta...

*2:39am Na dare*
Majnoon yana kwance a gefen layin wata unguwa mai mota yabiyo layin, ga alama mai motar nan yayi mankas da giya tun daga nesa yake masa hoh amma Majnoon yaki ko motsawa dominshi baccinsa yayi nisah, mai motar na karasa wurinsa yatakashi ya wuce ....

*Majnoon* ta furta Da karfi rumaisa ta farka daga mummunan mafarkin datake, da salati a bikinta, kuka yasoma zo mata, tayi jim tana tunani mafarkin, karde ace hakan tafaru da Majnoon, saitaji tanason ganin Majnoon a yanzu amma kuma saita tuna da maganar abbanta, hawaye suka sauko kan fuskarta a hankali ta sulale takoma kwance, tundaga lokacin bata kara komawa bacci ba sai sake2 take a zuciyarta..

*Asuba tagari*
Bayan Rumaisa tayi sallar asubah tashiga bandaki tayi wanka sannan tafito har a lokacin bata dawo normal domin gaggar jikinta ce kawai a tare da ita amma zuciyarsa zakatakaf tana gurin tunanin Majnoon,

Bayan taga shirinta tadauko littafanta tanufi dakin abba, zaune tasame saman kujera, nan ta durkusa har kasa ta gaidashi sannan tace "abba kayi hakuri da abinda yafaru jiya, kabani izini na fita, zanje makaranta"

Abba yadago kai ya kalleta har yanzu fushi yake da ita yayi jim, sannan yace " ai fita kije makaranta yazama dole nabarki kije amma kisani bazan barki kitafi ke kadaiba zansa driver yakaiki, domin banason wata alaka takara hadaki da waccen mahaukacin, wai shin meyake dashi da sauran maza basa dashi, yaja nunfashi kafin yace " kuma maganar aurenki munyi magana da abban faisal yace na kara masa kwana biyu domin yanason yayi shirya2 amma badan hakan ba da yau dinnan zan daura miki aure, yasa hannu yaciro kudi ya mika mata yace "kije waje kicewa drive yakaiki makaranta kuma idan aka tashi yaje ya daukoki"

Koda ta dago kanta idonta sunyi ja sosai takarbi kudin sannan tatashi tafita...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:34 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴
_The mad man_

_Author_:- *MR, SMILES*πŸ˜ƒ

11 and 12
Via *OHW*
_A love story_πŸ’

Tana zuwa tasanar da baba driver cewa abba yace yakaita makaranta, ba musu bb driver ya shiga mota suka lula makarantar,

Yana ajiyeta a harabar makarantar ya juya, tun a cikin mota ta sanar dashi cewa idan suka tashi zata kirasa yazo yamaidata" tohm kawai yace,

Bayan bayar makarantar Rumaisa tayi tsaye tana kallon makaranta kafin tad'aga kafarta tafara tafiya cike da yanga take tafiya harta karasa cikin aji, ganin kawayenta yasa takirkiri murmushi nan dai tadan waye fuska suka gaisa kafin malami yashigo a fara lecture,

1:30pm na rana Suka karasa lectures dinsu baki daya, kowa yafito nan tayi saida safe da kawayenta sannan tafito waje takira bb driver, bada jimawaba kuwa saigashi yakaraso..

Shiga motar tayi suka dauki hanyar gida,
Rumaisa ta dube bb driver tace "baba dan Allah inaso naje nan layin kusa da namu wurin wata zanje" bb driver yace "tohm shikenan ba matsala"

Bata kara maganaba saida suka kusa karasawa kusa dayin sannan tafara nuna masa hanya, dai dai inda tasan majnoon yana zama ta tsyar da bb driver sannan tafito tana dubinsa amma bata ganshi, danmm taji gabanta yafadi..

Mafarkin datayi jiya akansa shiya fado mata a zuciya gabanta yayi mummunar faduwa, hawaye suka cicciko mata edo, a zuciyarta take fadan kar dai ace abinda tayi mafarki yazamo gaskiya,

Shiru tayi tana kallon gurin kafin tajuya
A hankali take kokarin juyawa, ta gefen edonta tasoma hangosa yana d'aga mata hannu, da dasauri ta juyo batasan lokacin data kasance cikin murmushiba, da gudu yake zuwa gurinta, yana karasa yaja birki saida kura tatashi, yana cizon rigarsa yace " ke kuwa shine jiya baki zoba koh, saida nayita kuka"

Rumaisa tayi kuru da ido tana kallonsa cike da tausayi, tabbas taga alamun hakan a idonsa domin gasunan duk sun kunbura nunfashi taja kafin tace "kaci abinci yau" ya girgiza mata kai, alamar a a

Tayi shiru tana kallonsa tace "jiya dadarefa " haka yakarasa girgiza mata kai a a"

Wani irin kallon tamasa saida hawayen dake cikin Edonta suka zubo, da sauri tashare sannan takasa hannunta cikin jakarta ta ciri kudi har zata bashi sai kuma ta makale hannu tace "nabaka kudi zaka iya sayen abinci da kanka"

Ya girgiza mata kai yana Murmushi yace "eh zan iya, idan naje wurin talatuwa mai abince sainace tabani, nikuwa saina mika mata kudi"

Rumaisa tayi murmushi tace yawwa, gashi kaje kasiya " tamika masa kudin,

Karbar kudin yayi yana wasa dasu yace sannan yadago kai yana kallon rumaisa yace "kinsan wani abu, Rumaisa tace "a a saika fada "

Ya sunkuyar da kai yace " jiya ina bacci wata mota tatashi takani"

Dam taji gabanta yafadi, mafarkinta yafara dawo mata a kwakwalwa da sauri tace "amma dai bata taka kabandai koh"

Ya girgiza mata kai yace " eh, yana gama fadan haka sai kuma yayi shiru yana wasa da kudin dake hannunsa,

Rumaisa tace "kaje kasiye abincin nizan wuce nakoma gida"

Majnoon ya tsuke fuska bayason tatafi yace " yanzu yaushe zaki dawo" rumaisa tace " sai gobe irin wannan lokacin"

Majnoon ya kalleta saikuma ya sunkuyar dakai yace " bazakizo dadare "

Rumaisa tayi ajiyar zuciya tace "bazan zoba Majnoon domin abbana yahanamun zuwa gurinka "

Dasauri Majnoon yadago kansa yana kallonta yace " abba baya sonane"

Rumaisa ta girgiza masa kai tana murmushi tace " yana sonka mana, kaida zaka aure 'yarsa mezai hana yasoka, tana kallonsa tace " kodai ka fasa aure nane"

Da sauri majnoon ya Girgiza kai yana dariya yace "a a, ina sonki sosai" yana gama fada ya sunkuyar da kansa kasa yana wasa da yatsunsa, shi ala dole yaji kunya,

Yanayinsa yabawa rumaisa dariya,

Baba driver yana a mota sai mamaki yake me rumaisa takeyi a gurin mahaukaci gashi yaganta sai Murmushi take, ta mirror motar ya hangi wata mota a bayansa wadda tayi sanadiyar sakashi firgita fiye da kima, bakinsa na rawa ya iya furta "alhaji"

Da sauri yafito daga cikin motar, yana kiran rumaisa, domin tayi sauri tazo sutafi, tana juyowa yayi daidai da lokacin da abbanta yafito daga cikin motarsa, sukayi edo hudu ko kashe motar bai tsaya yiba, yanufi gurinsu,

Rumaisa kuwa tuni tayi mutuwar tsaye,

Fuskarsa ba annuri kwata kwata, yakarasa gurinsu, kafin yayi magana saida yadauke Majnoon da wani irin wawan mari, rumaisa ta kanne edonta domin bazata iya ganin ana duka Majnoon ba, a dai dai lokacin Hawaye suka sauko kan kuma tunta,
Kafin ta bude idonta itama taji saukari mari tas tas, saida ta ja da baya kamar zata fadi,

Yana dafe da kumatunsa Ganin an mari rumaisa yasa yayi ihu cikin sigarsa ta marasa hankali yayi kan abban rumaisa ya kamo kwalar rigarsa, ya ware hannu zai mazga masa mari rumaisa tayi saurin rike hannunsa tana kuka tace " karka maresa abba nane "
A hankali Majnoon yasaki wuyan abba yana huci,

Abba kuwa gabaki daya ya tsorata, ganin yadda majnoon ya damkesa, indai baibar gurinsaba to komai zai faruwa,

Majnoon ya rike hannun rumaisa, wannan shine karo na farko dataji majnoon yataba jikinta, wani zar taji, ta lumshe ido, tayi mamakin jin hannunsa da laushi,

Abban rumaisa yagyara rigarsa yana huci yace "sakarmun 'ya"

Uffan Majnoon baice dashiba, rumaisa kuwa kuka kawai take, tana fana dan Allah abba kayi hkr wallahi bazan sakeba,

Da karfi da yaji abban rumaisa yashiga Firgar rumaisa daga hannun Majnoon shikuwa Majnoon yariketa gam saikace abarsa,

Nan take mutane suka taru a gurin, da kyar aka iya b'amb'are rumaisa daga hannun Majnoon, mutane suka rirrikesa..

Abba rumaisa ya fincikota tana kuka, yanunawa majnoon yatsa yace "kaiiii dani kakee sa insa" sannan yayi kalci yaja hannun Rumaisa dakarfi yanufi mota da ita,

Janta yake amma tana juyowa tana kallon Majnoon, wanda mutum sama da biyar duk sun rirrikesa,

Rumaisa kuka take sosai,

Abba na karasa bakin mota ya bude kofar motar ya jefata a ciki, sannan ya zagaya ya shiga motar yabar unguwar.

Baba drive duk ya tsorata,
tsoro yakeji kar ya rasa aikinsa...

Facebook page:- Abdul-mr, smiles novel's

Website:_www.abduljega.blogspot.com
[10/20, 10:35 PM] β€ͺ+234 905 395 7618‬: _Title:-_ *MAJNOON*😴


2 Comments On MAJNOON
avatar
hafsat-muhammad-5

11 months ago

Reply

Amazing

avatar
hafsat-muhammad-5

11 months ago

Reply

Amazing

Please Login or Register in order to submit comment