Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shuraih 99% ne].
Can na hango wata katuwar rumfan sai da kayan mar mari iri iri kamar su tuffa lemon tsami dana
zaki kala kala, akwai dabino da inibi kala kala da sauran yayan itatuwa ,yawuna ya guda don haka
na dauko jakata na rataya na doshi rumfar "ina kuma zaka" direban ya tambayeni " zan sayo kayan
marmari a wancan rumfar" na maida masau
.

Nayi sallama a kofar rumfar wata balarabiya sanye da dogon siket har kasa ta sanya riga mai dogon
hannu ta yafa mayafi kato ya rufe tun daga kanta zuwa kaurinta tana fara'a ta tareni "ahlan
wasahlan" tayi min nuni dana shigo ciki"marhababika ya akhi"
Ta nuna min kujera na zauna ina shiga kanshin yayan itatuwa suka bigi hancina sha'awa ta
motsa ,kanshin ni'ima na kayayyakin marmari ya kaure rumfar
.[kar ku manta dai kuna tare da shuraih 99% ne]
Cikin fara'a ta tambayeni sunana da kasar dana fito na gaya mata ni dan najeriya ne sai kawai cikin
sauri ta bani ruwan sha ta jinjina min "nayi farin ciki da ganinka saboda dan uwana yana kasuwanci
acan " ta fada cikin larabci
.
Sannan ta dauko jakar saye syae ta cika mini da kayan marmari ina kokarin ciro kudi na biyata ta
riken hannu tace "kyauta na baka dan uwa na, saboda ina son musulmin Nageriya "
Na gode mata na gaigaisa da sauran mutanen da ke rumfar na fito kofar rumfar ta biyoni "ina ne
masaukinka kwana nawa zaka yi " na bude baki zan bata amsa kenan sai wata kara mai karfi da
fashewa ta abku, wuta da hayaki a lokaci guda suka watsu cikin sauri na saki ledar da ke hannunsa
na watsar da jakata na rumbace ta muka zube a kasa , nayi haka don gudun kada tararratsin bomb ya
same ta
.
TOH FA DAN JARIDA YA FADA HATSARI
Daga shuraih usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 4
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Daga kowacce kusurwar kasuwar sai mutane ne ke runtumawa a guje , daga nan kuma sai harbi da
bindigogi masu sarrafa kansu ya biyo baya abin da yakara yamutsa gun kasuwar ta yamutse ,
.
Hayaki ya turnuke sama kura ta tashi hargowa ta cika ko'ina mutane da gudu suna tsallake
rumfunansu ko rufe su basu yi ba wasu sunyi karfin hali sun tsaya rufe kofofinsu
.
Cikin sauri na samu naja jiki na rakube a jikin gyaren rumfar ita ma tayo ciki, cikin sauri muka rufe
kofar ta matse matsen kofar na samu wata yar kafa data bani daman kallon abun da yake faruwa
acikin kasuwar
.
Matasar dana gani suna kaiwa da komowa a cikin kasuwar rike da bindigogi suna harbin mutane na
tabbata falasdinawa suke harbewa
.
Cikin mintina biyar kasuwar ta yaye ba kowa sai jami'an tsaron yahudu suna zirga zirga wasu a kasa
wasu acikin landorobobi
.
Suka shiga kama wanda aka harbe suna jefawa acikin motocinsu wasu kuma suna bin falasdinawa
da gudu suna kamasu izan sunyi gardama sai su harbesu wasu kuma suna kofofin rumfunansu suna
kamo mutanen da suke ciki wannan yasa na gane dalilin dayasa wasu suke guduwa daga
rumfunansu
.

Matan ta mike ta janye katakon da ake leken waje nan da nan ta rude ganin suna ta jifgar mutanen
da suka kama , na lura da inda motarmu ta tsaya ba komai sai karikiceta dai-dai da direbanmu cikin
jini, hannunsa ya cire idonsa ya fita sai kafarsa ce take dan motsawa ganin wannan ya tayar min da
hankali sosai bansan lokacin dana fara kyarma ba zufa na keto mani , "wai da ban fito sayen lemo
ba da yanzu bani " nace a raina
.
Motar asibiti tazo tana jiniya tazo ta kwashe gawarwakin mutane ban san kowane bane , akwai
wasu mutum hudu da suka rasa sassan jikinsu motar janwai motocin da bomb yayi kaca kaca da su .
.
Ko mintina goma sha biyar ba ai ba an kwashe gawarwakin an janye mushen motocin an wanke
jinin . Wama ya nuna cewa lallai yahudawa sun shirya da irin wannan ranar sosai kuma basa son
kowa yasan irin barnar da suke
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Ina shirin cewa ta bude kofar ganin kura ta lafa sai naji hayaniya da kawar mutane sai na hango
mutumin da muka shigo mota tare ya shiga motar jami'an tsaro ya tafi da fari nayi mamaki amma
dana tuna akasar yahudawa nake ko ince kasar da su ka kwace da karfin tsiya banyi wani mamaki
ba
.
Alokacin da motar shiga-ba-biya take shirin ficewa daga kasuwar a lokacin hayaniyar jama'a ta
karaso cikin kasuwar wasu matasa a guje suna kabbara suna jifansu da duwatsu suna tunkararsu,
.
Batare da ko bindiga ba kowani kwakkwaran makami ba , ganin haka ban sana lokacin dana
wangame kofar ba na fito don na kashe kwarkwatar idona ba
.
Rannan naga ikon Allah matasan falasdinawa suka taho gadan gadan ba wani tsoro ko fargaba a
guje a daya barin soja da yan sandan izra'ila cikin sauri suka dinga dirgowa daga cikin motocinsu
wsu suka durkusa wasu suka sunkuya wasu kuwa suna harbi suna gudu da haka suka tarbi
falasdinawa masu jefa da duwatsu kamar soja yayi karo da abokin gabarsa soja afilin daga [shuraih
usman inkiya shuraih 99% ke magana]
,
Mamaki da al'ajabi ya kamani ,ina mamakin yaya soja da muggan bindigogi zai harbi farar hula da
bashi da makami, alokaci guda kuma ina al'ajabin yadda akayi mutum ba komai a hannunsa ya
tunkari mai bindiga ,
.
Aka ja daga daya barin karar bindiga daga daya barin kuma kabbara gurin ya kaure
.an shafe sama da mintina ashirin ana dauki ba dadi falasdinawa suyi kora soja da bindiga kaga ya
ruga da gudu har yana fadiwa, in anjima kuma kaga falasdinawa suna gudu abin kamar al'mara ,
.
An harbi falasdinawa da yawa an jikkata wasu wani abu daya bani mamaki shine duk wanda aka
harba yana faduwa na bayansa zai zo da gudu ya daukeshi
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
.
Sannan kuma wani nan take zai maye gurinsa, don haka babu wata gawa ko masu rauni da sojan
yahudawa suka kama
.
Ana cikin haka sai wasu falasdinawa suka hau saman rumfunan suna kabbara , suna jifansu da
duwatsu wasu kuma suka biyo ta bayansu ganin za'a yi musu kofar rago sai suka jefar da wadanda
aka kama suka tsere a guje n nan da nan kasuwar ta rude da kabbara da sowar falasdinawa suka
mamayeta
.

Wannan shine abu na farko daya bani mamaki a saukata a cikin falasdinu . Na kirata falasdinu
saboda shine sunan halal ba izra'ila ba kamar yadda yahudawa yan kaka gida suke kiranta
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Tambayar da nake yiwa kaina kuma na rasa amsar ta shine wane abu ne ya ingiza mutum ba
makami ya kori mai bindiga har ya gudu yana faduwa yana barin bindigarsa
.
Me ya baiwa falasdinawa karfin guiwa har suka fuskanci yahudawa rike da bindigogi duk da sun
san cewa harbesu zasuyi ga kuma sheda agansu sunga an kashe da damansu,
.
Sannan kuma wane daliline yasa mutum yana gani an harbe dan uwansa zai tsallake gawarsa ya
shige gaba ya kuma tabbata shima harbeshi za'ayi sannan kuma me yasa suke dauke gawan wanda
aka harbe
.
Wannan tambayoyin da wasu irin kamar son jin dalilin da ko'ina aka saka jami'an tsaro suna gadin
dauka cin garin kamar anci garin da yaki kuma na ajin tsoron kwace shi koda wane lokaci, me yasa
aka tsaurara matakan tsaro bayan kuwa su falasdinawa ba su da makamai da zasu iya yaki da
yahudawa,
.
Kai kona kare kai basu dashi sannan wata kuma me yasa duk matakan tsaron nan ba su hana
falasdinawa yunkuri da yin bore a kasuwa ba ?
.[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Hakika wadannan tambayoyi ne da suke bukaar amsa wanda duk wani dan jarida mai kishin aikinsa
zai so ya gane bakin zaren abin da na kuduri niyya kennan duk kuwa da cewa ba neman labari na zo
ba , na zo ne neman yar uwar NAGIS don na bata sarkar wuyanta to amma yaya za ace ni HADI
dana shiga cikin runtsi a bosniya lokacin da ban san komai ba a dabarun yaki, yaki ta rutsa da ni na
fito lafiya cikin ikon Alla
.
Sannan ga wata dama ta samu ta aikin jarida na hakika na kiyin wani abu sam-sam ba zan iya
hakuri ba idan kuwa na hakura ban bincika na , to ba sunana hadi hantsi leka gidan kowa ba, neman
labari ya zame mini jini da tsoka don haka naji ba zan iya barin wannan damar rubuta halin kunci da
kuntatawa da yan uwana musulmin falasdinu suke ciki ba.
.
Wannan shiya sauya mini makasudin tafiyata, shu'urin aikin jarida ya motsa sai dai kuma na san
cewa nan fa ba a maraba da yan jarida domin yahudawa sun san tasirin yada labarin abun da suke
aikatawa, don haka basa yiwa yan jarida da suke aiki bil hakki da wasa , saboda basa son duniya taji
labarin irin danne hakkin dan adam din da sukeyi .
.
Kawai sai na gabana ya fadi ras dana tuna da gargadin mr. Doyin
.
Har kullum dai nine Shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 5
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
Na bude kofa zani wajen da aka fafata matar nan ta riken hannu " kai bako ne kada kaje su kamaka
bari in rufe muje gida in saukeka" ta fada mini sunanta "ismi zulaikha" ta fara hada kayanta cikin

sauri "motar ku aka sawa wa bomb ko" ta tambaya tana kallona na gyada kai sauran mutanen da
suke cikin rumfar kowa yayi ta kansa
.
Ta shige gaba ina bunta muna gudu-gudu sauri sauri ta kurda can ta kurda nan . Da haka muka fice
daga kasuwar jami'an tsaro suna yiwa kasuwar tsinke , tafiya mai dan nisa ta kai mu wani dan gida
a cikin rukunin wasu jerin gidajen talakawa, duk unguwar larabawa ne acikinta idana kaga
bayahude toh babu shakka jami'an tsaro ne babu ja wai kare ga mutu a saura , sai da cikin unuguwar
babu jami'an tsaro a ciki sosai
.
Tayi sallama ta kwankwasa kodar wani karamin gida bayan yan mintina wata yarinya doguwa
budurwa mai matsakaicin kauri ta bude kofar, gashin kanta har kirjinta tana da fararen idanu kamar
madara a koko ga dogon karan hanci har baka , tana da siraran lebba da yalwar gashin gira
shekarunta zasu kai goma sha bakwai ko sha takwas , muna hada ido ta rufe kanta da mayafi.
.
[shuraih usman inkiya shuraih 99% ke magana]
A hankali ta bude kofar ta karbi kayan zulaikha sannan ta kalleni tayi min barka da zuwa kuma ya
karbi jakata muka shiga dakin saukar baki, shine na farko da cikin gidan daga hannun dama ta bude
kofar tace na shiga na zauna a cikin akwai kujeru guda uku tsofaffi da dan karamin teburin shan
shayi, sai kananan kofuna na shan shayi a gefe guda na wani gadon katako tsoho.
.
Na zauna kenan yarinyar ta shigo da butar shayi ta daureye kofunan dake kan teburin ta zuba min
shayi ta fice tana tafiya cikin nutsuwa, sannan ta shigo da yayan itatuwa irir iri da ruwan sha ta
fita,shayin dana sha ya sana ji karfina ya dawo na kuma wartsake yayan itacen da sha sun gusar min
da yunwa
.
Ni dinne dai Shuraih 99% ke typing
.
Alokacin ne na nutsu sosai na shiga hayyacina na dauke takarda na tsara abubuwan daki daki,
wannan al'adace a gareni duk sanda zanfara wani aiki sai na zauna a tsanake na tsara komai dalla
dalla , saboda kashin bayan cin nasara a kowace irin harka ta duniya kota lahira shine kyakkyawan
tsari, da shiri mai inaganci ,
.
Domin kuwa duk wanda bai tsara al'amarunsa ba to kuwa ya dauki matakin ruda kansa.
.
Abu na farko shine lokacin dana ke da shi kankane ne ,kuma abin da yake gabana yana da yawa, ga
kuma wahala ba kamar yadda ba zata ba, yadda jami'an tsaro suke ta safa da marwa babu wani
yanci walwala, ga tashin hankali iri iri ga harsashi na yawo.
.
Akwai hatsarin na shiga neman yar uwar nagis kai tsaye don ban san matsayinta ba agun jami'an
tsaro ko taba cikin wadanda ake nema ruwa a jallo ,sannan jin cewa ina nemanta kuma na taso tun
daga sarrayebo, wannan zai bada haske ga jami'an tsaro su tasani a gaba don su halakamu gaba
daya,
.
Sannan kuma ban san waye jami'an tsaro waye da leken asiri ba, sannan na tuna da wanda muke
tafiya tare na tabbata dan leken asiri ne , nayi hamdala da Allah ya raba mu cikin sauki
.
Nagode nine dai Shuraih 99%
.
Babban abinda yake damuna nake son kuma sanin bakin zaren shine dalilin da falasdinawa suke
cikin wannan kunci da takura, koma meye harzukasu, suke dauki ba dadi da su haka, Na tsara
komai cikin dabara da yadda zan sami amsoshin wadannan tambayoyi ba tare da wani jami'in tsaro

ya sansano wani abu ba, kuma ba tare da mai bani labarin yasan cewa yana fadamini wani
muhimmin abu labari ba,
.
Zan lullube komai da sunan ni dan yawon bude ido ne da san jin tarihi ne wannan abu ne mai sauki
wajaen kwararren dan jarida musamman idan ya samu kansa cikin hatsari, Amma ba abu ne mai
sauki ba Izra'ila
.
Kuna tare ne dai da Shuraih 99%
.
Zulaikha ta shigo tare da wani saurayi da wannan yarinyar suka zauna"wannan yayana ne " tace
"sunansa Abduljalil shine wanta ita ana kiranta zakiyya shi yana karatu a jami'ar jaffa , ita daliba ce
a kwalejin yan mata ta jaffa
.
Bayan shirin yan mintuna sai na jeho musu tambaya cikin dabara "ko kun san labarin sarkin
Ramalla na karshe?"
Na zuba musu ido , wannan ne karo na farko dana fara aikin daya kawoni, ya kalleni sosai yasa
hannunsa a aljihun kirjinsa ya fito da kwalin taba ya kasta ashana sai zakiyya ta fice waje "ban san
labarinsa ba" ya gumtsu hayaki ya fesar "wani tsoho abokin babanmu yasan komai na labarin
falasdinu kafin a mamayeta da bayan an mamayeta da irin yake yaken da akayi tun kafin a haifemu,
duk sanda nake da wani aiki daya shafi tarihi shi nake ziyarta ya bayyana mini komai" ya dube ni ya
kalleni mahaifiyarsa " idan bazaka damu ba dana hada ka da shi mutum ne mai son bakon da yake
son sanin tarihinmu zai gamtsar da kai da duk wani bayani da kake bukata"
.
Shuraih 99% ke cewa
.
Nayi murna da jin haka don haka nace " muje na ganshi mana yanzu "ya dubeni yayi murmuishi
"Ba a nan garin yake ba sai gobe zan kaika wajensa a nablus ne " na duba agogona naga lokacin da
nake dashi bashi da yawa "ina son ganinsa yau don sauri nake akwai wani uzuri da nake da shi"
Ya kada kafadarsa " banda hali zuwa nablus a yau , ina son zuwa jami'an ina da jarabawa kuma
kafin agama dare yayi, kasan nan ba'abari ayi tafiya da daddare daga wani gari zuwa wani garin ,
karfe shida zuwa bakwai na dare dole kowa ya koma garin da yake da zama ko ya fuskanci tuhuma
.
Shigewar zakiyya da farantin abinci ta ajiye a agabana tafice " zan biyo ka jami'ar nace masa bayan
da yayi mini bismillah
.
Jami'ar jaffa tana daya daga jami'ar da larabawa suka gina suke gudanar da ita da harkokinta, akwai
falasdinawa da yawa suna karatu wasu kuma suna koyarwa,
Haka zalika akwai yahudawa har ma da turawa dalibai da malamai
.
Hukumar yahudawa ce ke lura da tsara tsaren makarantan da manhaja da ake amfani da ita , tana da
shashen karatu mai zurfi akan ilimin kimiyya da aikin likita, tarihin da aikin injiniya
.
Abduljalil yana koyan aikin likita yana da sekara ta biyu muna shiga ya shiga aji bayan ya kaini
dakin karati, ina shiga na dukufa binciken littatafai, da kasidun tarihi daban daban akan kasar
izra'ila amm banga abin da nake son gani ba , labarai ne wanda ko agida najeriya na iya samu, sai
dan abin da ba a rasa ba,
.
Wanda ya karamin haske akan binciken dana ke son yi
Kuna dai tare ne da shuraih 99%
.
Bayan ya gama yazo muka fita zuwa gida a tahowar mu mun shafe kasa da mintuna goma sha
biyar , amma akan hanyar komowa mun shafe sama da mintuna arba'in saboda cunkoson da jerin

gwanon abun hawa "me ya kawo wannan Jerin gwanon" na tambayeshi "abduljalil yace "larabawa
da yawa suna aikin leburanci a da sauran aikin karfi a tel-aviv da saura garuruwa na yahudawa da
suka mamayee in sun kwana a gidajensu da sassafee kuma su sake neman iznin shiga garuruwan
domin neman abun da zasu ci, wannan yasa duk safiyar Allah da kuma La'asar hanyoyi suke cika
makil da abin hawa saboda kowa yana kokarin zuwa gida kar lokacin fara tare mutanee yayi
.
Nayi shiru kawai ina kallon jama'a a cikin dogayen motocin bas da sauran ababan hawa makare da
mutane ,
.
Yauwa anan zan tsaya na dan huta sai mun hadu a page 6
.
Dan Allah ku saka ni acikin Addu'anku
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 6
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
[Shuraih 99% nake cewa daku]
.
Toh jama'a sai daikuyi hakuri don kuwa fallayen littafin sun babbale, a saboda hakanne zamu danyi
tsallake ,
.
Amurka da sauran kasashen turai sun tara musu dimbin makaman yaki na zamani wasu ma ba'a taba
jarabasu ba sai a lokacin, yahudawa suna da cikakkiyar masanaiya game da duk wani motsi da
sojojin larabawa sukeyi , domin suna samun bayanan sirri kai tsaye daga ma'aikatar tsaro ta amurka
kada ka manta kuma shugabannin wasu kasashen labarawa munafikaine
.
"Wannan nasarar ta basu daman waftar kasashen larabawa, don haka min sake fafatawa da su
ashekarar 1967, wannan shine yakin kwana shida, kwanan bakin ciki"
Abuja'afar yayi shiru banyi wani kokarin tambayarsa ba don na lura fuskarsa ta sauya idanunsa sun
kada sun yi jawur don haka na lura abin daya ke son fada ne yake masa ciwo matuka zuwa can sai
hawaye ya dinga tsattsafowa daga idanunsa yana bin kumatunsa a hankali
.
Ni dinne dai shuraih 99%
.
Cikin murya mai rauni tana rawa cike da sauti mai ban tausayi ya labarta mini labarin yakin kwana
shida " yakin kwana shida yakine yakine da larabawa ba zasu taba mantawa da shi ba har abada,
domin kuwa mun tozarta acikin kwana shida mun kaskanta mun ga wulakanci , munyi asaran
filayen mu, an kashe mana mata da yaya iyalai masu yawa bazasu sake gaini juna ba.
.
Domin iyalai da yawa an watsasu acikin duniya suna yi gudun hijra cikin kaskanci da yawa sun
halaka matayenmu da yawa sun ga wulakancin da basu taba zata ba domin kuwa an yiwa da
damansu fyade,
.
Yi tunani a ranka cewa matar da bata taba fita waje ba ko kuma wacce wani namiji bai taba ganin
fuskarta ba , balle kirjinta, rana daya ta samu kanta cikin fasikai sui mata tsirara suna lalata da ita a
gaban ya yanta ko danginta , sannan a yasar da ita a filin Allah bako sutura,
.

Tuna yaya zakaji izan matarka ko yarka ko mahaifiyarka ce a kayi wa a gabanka, abubuwa munana
mafi muni kuma awannan yakin ne yahudu ya kwace kudus gaba daya har masallacin al'aksa
.
Kai gaskiya na tausayawa larabawa, ehm Shuraih 99%
.
Amurka ta gina rundunar sojan izra'ila ta kuma sabunta kayan yaki ta da na zamani mafi inganci,
tun a shekaar 1948 duk shekara suna wasu wasu makudan kudade na musamman da suna
"development Aid" da kuma "military Aid" domin gina kasar da rundunar sojanta, suna kuma ba su
kayan yaki wanda basa sayarwa kowacce kasa irinsa
.
Sannan suna ba sojansu horo na musamman ga kuma bayana da rahotanni na sirrin na watan dan
adam
.
"Kwatsam izra'ila ta farwa kasashen larabawa don cimma burinta na kafa izra'ila babba , acikin
kwanaki shida akayi mummunar fafatawa a tsakanin larabawa masu tarin kayan fada marassa
inganci ga sojoji mara kwarewa cikin kankanin lokaci suka yi mana kaca kaca, sojojin mu suka
zubar da kayan yakinsu su suka gudu, suka bar mu da abun fada ana dariya
.
Izra'ila ta mamaye lardin sinai mai tarihi na kasar masar, sun mamaye rabin jodan wanda ya hada da
gabanshin gabar kogin jodan sun wafci wani bangare na kasar siriya bayan anyi kazamin yaki a
tuddan golan
.
Nidinne dai shuraih Usman inkiya shuraih 99%
Sun mamaye ilahirin ZIRI GAZA da sauran gabar kogin jodan (west bank) sun kuma kame
daukacin darussalam (jerusalam) suka kwace masallacin kudus suka keta alfarmar masallacin suka
kashe daukacin mata da yaran da tsofaffin da suka fake a cikinsa jini ya malala cikinsa kamar ruwa,
suka kuma sake kwace wani bangare na kasar larabawa
.
"Acikin kwana shida sun yiwa larabawa wulakancin da ba a taba yi musu ba , tun bayan zuwan
Annabi muhammaduu (SAW) mun ga tasku da wulakanci iri iri a hannun yahudawa har ta kai mun
rasa inda zamu sa kanmu an kashe mata iyaye an yi lalata da yan mata , an kakkaraya mana matasa
an zuba su a rami an rufesu da ransu, matayenmu,yayanmu a gabanmu akayi musu fyade, an
wasashe dukiyarmu an kone an kuma rusa mana gidaje an mayar da mu yan gudun hijra a cikin
kasarmu, Ta gado
Shuraih 99% ne din dai
.
Falasdinawa da yawa sun watsu a duniya da sauran kasashen larabawa suna shan wulakanci iyalai
da yawa sun halaka, iyaye basu sain inda yayansu suke ba , dangi sun warwatse yanzu akwai akwai
faladinawa yan gudun hijra sama da milyan daya a cikin duniya basa ko tunanin dawowa kasarsu ta
gado sai dai a mafarki......
.
Abduljalil ya fashe da kuka yana fadin babana ko yana ia oho.."
Can kuma sai ya dinga fadin wallahi zamu rama sai mun dauko fansa komai dadewa sai mun kwace
kudus ko duk zamu kare"
.
Na lura duk ya sake jikinsa yana tsuma yana karkarwa, bayan ya nutsu abuja'afar yaci gaba
.
"Yakin kwana shida yasa larabawa sun farka sun shiga cikin hankalinsu sosai sun san kuma duniya
ta canja, sun gane cewa ba wani shirin daukan fansa da dawo da martabarsu a idon dunia.
.
Ashekarar 1973" cikin kukan abujafar muryarsa a karye yadan saurara sannan yaci gaba "kasahen
laraba sun nunawa duniya sun dauki darasin abubuwan da suka fari sannan an kuma samu sabbin

shugabannin masu jini a jika masu kishin larabawa, wadanda sukayi aiki tukuru sukayi shiri na
musamman acikin watan azumin wannan shekarar yakin da ake kira "yakin october" ya faru
.
Yahudawa suna da wata rana da suke kira "yom kippur" a wannan ranar basa aikin komai hatta
jiragen sama basa tashi ko sauka balle wani aiki , muna zaune a unguwanmu dan ba damar shiga
garuruwan yahudawa ranar hutu
.
"Na bude rediyo sai naji anacewa "meat pie" sea wolf and woll stringl wannan kalmomin sojane na
siddabaru ana kiran sojan kota kwana da su dawo bariki cikin sauri"
.
Cikin sauri na katseshi "ya akayi ka gane kiran soja akayi musamman da kace kalmomin siddabaru
"code word" na lura abduljalil bai ji dadi dana katseshi ba "nasan hakane saboda na shiga wata
kungiyar karkashin kasa ta fada da manufofin izra'ila na mamaye palasdinu kuma ina aikawa da
labarin sirri ga wasu kungiyoyin leken asiri don haka na san wannan dama wasu kuma wasu bayan
da za fada maka a gaba na sansu ta irin wannan hanya ina fatan ba zaka tambayeni hanyoyin dana bi
na sani ba,
.
Da kuma hanyar dana kebi na sanar da nawa bayanan asiran" nayi shiru bance masa komai ba.
.
"Bayan wannan sai muka ga motocin sojoji cike da sojoji da kayan yaki sun doshi bakin iyakokin
da suka shatawa kansu, misalin goma na safe manyan rundunonin sojan izra'ila ssu dinga motsawa
bakin daga cikin sauri,
.
Jirafe saman yakinsu suka dinga shawagi kasa kasa a cikin gari ko'ina daga nan kuma sai muka ji
muryan firmiyan lokacin "golda meir" a redio tana cewa "bama wata tantama game da nasararmu,
an yiwa abokan gaba mummunar barna" daga nan kuma muryar dan ta'adda moshe dayan yana
cewa "larabawa ba zasu ci moriyar wannan yakin ba kafin a tsagaita wuta, kuma mutane birnin telaviv zasu samu suyi barci sosai"
.
Rugogin jiragen saman yaki yasa mutane gudu cikin gidajensu abin daya sabawa al'adar "yom
kippur" ranar hutu da zaman jagwab, ta koma ranar yaki zazzafa,
.
Ranar da yahudu ba zai manta da ita ba domin a wannan rana sun dandana kudarsu, tunanin da suke
nacin nasara cikin sauki ya koma kokarin kwatar kai ta kowane hali.
.
Yauwa hakann na keso shuraih 99% ke magana
.
"Ayakin ramadan ko yom kippur ko black october"
Kamar yadda yahudawa suke kiransa an gwabza shi sosai anyi gumurzu kuma kazamin yaki mafi
muni a taihi yakin zamani tun yakin duniya na biyu anyi kazamin gumurzu a guraree guda biyu da
yakin sinai da daya kewaye na tudda golan
.
"Kasar masar sanadiyar kwace mata sinai tayi shiri sosai sai a kewayen sinai, ta sawo kayan yaki
sabbi daga kasar rasha, wanda ya hada makamai masu linzami samfari sam 6, sam 3 da sam 2 da
rokoki da bindigogi kakkabo jiragen sama na zamani,
.
Sun hada da garkuwan sararin samaniyar mai sarkakiyar a yakin sa sinan , sun tara tankoki masu
inganci da saukin sarrafawa a cikin hamada da sauran bindigogin atilare na zamani masu amfani da
na'urar mai kwakwalwa.
.
Wanda kwamandojin kasan rasha suka hada masu

.
.
HMM LALLAI ZA'AFAFATA KAZAMIN YAKI
.
Kafin nan dai nine Shuraih Usman
Inkiya shuraih 99%
Nake cewa daku muhadu a page 7
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 7
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Cikin dare wasu kwale kwale dauke da masu nutsu suka haura gabar ta suwiz (suez canal) suka dasa
nakiyoyi a bangaren izra'ila ,cikin sauri a lokacin da sojan izra'ila

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment