Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

suka motsa nakiyoyin suka tashi
suka watse ramikan karkashin kasa na boyar soja
.
Hayaki ya turnuke kura tayi sama,kafin kura ta lafa sojojin tanka sun haura da tankoki sama da uku
ta kwalekwalen katakon da suka hada su saki wuta armuka ginin karkashin kasan maboyar soja da
kayan yakinsu , gurin ya hautsine wuta ta kama , gine-gine da sauran tantunan sojoji suka kone
kurmus
.
Sojojin da suka taso don hana sojan misira haurawa cikin kankanin lokaci aka gama da suwajen
guda dari sukayi saranda, sauran aka kashe su, daga nan larabawa suka yiwo kora, suka kame
sansanin mai girma a yankin.
.[Kada ku sha'afa ni dinne dai Shuraih 99%]
Ta amfani da gurnati da yollar wutar aka kone yahudawa da kayan yakinsu. Kafin yammar wannan
ranar jiragen yaki masu saukar ungulu suka yi ta jigilar sojoji da kayan yakinsu.
.
Sojan kasa dauke da makaman atilare suka mamaye yankin sinar sun keta sinar ta wajeje biyar
sukayi kaca kaca da sojan izra'ila suka lalata barakokinsu da kauyukan yahudawa , sun kama da
yawa a masayin fursunoni, wajejen da suka fi barna mai yawa shine bakin gabar fu'ad da ismailliya
an yiwa izra'ila barna mai yawa a Qatara
.
Sojan misira sunyi kokarin haurawa da jiragen saukar ungulu a Ras da sudr, sunyi asarar jirage
goma kuma kowanne yana dauke da mutum 30 zuwa 40, kwamandoji sun yi kokarin katse hanyar
samun kayan sojan izra'ila amma basuyi nasara ba sun harbo jiragen izra'ila sama da arba'in 40 sun
yi asara nasu sama da goma,
.
Yahudawa sun lugudan wuta Shuraih Usman inkiya shuraih 99% mai tsanani ta sama da tankoki,
Amma bai yi tasiri ba
.
Rundunar sojan izra'ila tayi kokarin karya sojan misira Amma duk shirinsu ya zama a abanza
jiragen yakinsu , abin da suke mana zarra, sun gamu da garkuwar makamai masu linzami wadanda
ake harba su daga kasa "surface to air missile" duk jirgin daya shigo cikin yakin sinai sai yayi karo
da mizal ko Roka ya kone,
.
Ko bindigogin harbo jiragen sama ,jiragen amurka kirar phantom da hawk da sauran jiragen masu
saukar ungulu sun sha lugudan wuta da ruwan mizayal da rokoki, ko ina ka duba a sama sai kaga

jirage na faduwa kasa suna ci da wuta , wasu kuwa a sama zasuyi bindiga su watse hayaki ya cika
sama kaman gajimare mizayal sam 6 yana harbo duk jirgin daya tashi sama sosai kamar kafa 40,000
a sama wanda yayi kasa kasa domin yin bomb akan tankoki zai ci karo da sam 3 ko sam 2 wanda
aka saita su don harbo jiragen da yake kasa kasa
Shuraih usman 99%
.
Tarun ayarin tankokin yakin da izra'ila ta turo a yakin sinai sun sha wuta sun yi dai dai suka watse a
cikin hamada suna cin wuta, saboda sun gamu da sabon makamin kone tanka, don haka tarun
tankoki sama da dari hudu basuyi komai ba
.
Illa zama kaskon suya yahudawa, tilas sojan suka fita daga tankokinsu suna jifa da makamansu da
hulunan kwanansu suna zubawa aguje suna ihu
Wasu sun bace a hamada wasu sun haukace wasu sun kurmance ko'ina takalma da hulunan da belt
da bindigogi kirar amurka zaka gani birjik
.
Sojan kasar siriya sun kai farmaki daga barin gabas takan tudun golan sun share sojojin izra'ila
acikin AWA 48 suka danna har wasu kauyuka sun kone gevel kibbuts da heamek.
.
Wayewar gari jiragen izra'ila sun kai hari kan garuruwan fararan hula sun kone gidaje da asibitoci
da makarantu sama da mutum 1000 sun mutu a rummaneh.
.
"Mummunan yakin atilare da tankokin yaki ya fara da misalin karfe biyu na yamma bayan da suka
sha kashi a shuraih Usman inkiya 99%
Hannun siriya, tankoki samfurin cneturions da patton suka dirkako zuwa tuddun golan nan suka yi
karo da tankokin siriya aka gwabza yakin tanka mafi muni da tsanani a tarihi
.
Hayaki da wuta ko'ina ga rugugin bom da manyan harsasai da inji tanka kawai zaisa kunnen mutum
ya kurmance, anyi kare jini biri jini ko'ina karekican konannun tankoki da gawarwakine suke yashe
kamar kasa
.
Can kuma jiragen saman amurka na phantom suka dinga ruwan boma bamai kamar ruwan sama
akan tankokin siriya sun yi lugudan wuta mai tsanani na lokaci mai tsawo,anyi daga sosai mutum da
kansa zai bude tankarsa ya fito ya ruga da gudu, sama wuta kasa wuta tsakiya masifar zafi
.
Kashe gari da taimakon jiragen yakin amurka da bayanan sirri na watan dan adam daga amurka,
izra'ila sunyi raga raga da tankokin siriya sun kuma lalata garkuwar makamai masu linzami da suka
hada jiragen izra'ila suka karya Shuraih Usman inkiya 99% rundunar sojan siriya suka sake kama
tuddan golan an sake fafatawa sosai akan golan sama da tankoki 1500 suka gwabza aka yi kazamin
yakin tanka a tarihi
.
Hakazalika wayewar gari a lardin suwiz sojan izra'ila sunyi nasarar karya sojan misira da suka
hauro cikin hamadar sinai, saboda sun kai tankoki masu yawa , sun kumayi nasarar lalata cibiyar
makamai masu linzami da suka hana jiragensu haurawa.
.
Wannan ya baiwa yahudawa damar raunaa ragowar tankokin da suke hamadar sinai ba tare da wata
kiryar mizayal ba , rashin sabbin tankoki da zasu ci gaba musu da raunatesu.
.
Rundunar sojan izra'ila sun keta garkuwan jiragen saman yaki ta yankin sinai sun lalata rumbunan
rokoki da mizayal da taimakon amurka da kayan yakinta da bayanan sirri na watan dan adaam, sun
lalata cibiyar bada umarni ta makamai masu linzami sam 6 sam 3. Amma haka bai faru ba sai da
amurka ta shiga kai tsaye
.

AMma dai kafin wuta a tsagaita larabawa sun kwato Shuraih Usman inkiya Shuraih 99%. Da dama
daga filayensu da izra'ila ta mamaye a yakin kwana shida 1967. Martabarmu ta dawo a idon duniya,
mu larabawa ba abin da muka tsana face ayi galaba da mu kuma a din ga kallonmu a mutanen
banza,
.
Abin dayasa muka samu nasara bai wuce cewa sojanmu sun samu kyakkyawan horo da ingattattun
kayan yaki na zamani irin wanda izra'ila take tinkaho da shi ba, kuma sojojinmu sun shiga fagen
daga da niyyar ko cin nasara ko su mutu, Amma ba su gudu kamar yadda sukayi a yakin kwana
shida ba, mun nuna wa izra'ila cewa mu ba kanwar lasa bane"
.
Matarsa ta shigo tare da wani mutum suka gaisa ni da abduljalil muka yi sallama da shi bayan nayi
masa godiya mai "nine zan gode maka da ka taho tundaga wata kasa don binciken yadda
rayuwarmu take da halin da muke ciki, ka nunan kana kaunarmu kwarai"
.
Ya saki hannuna nayi masa alkawarin zan dawo muci gaba da shira akan halin da aka jefa
falasdinawa a ciki
.
Har na juya zan tafi sai na tuna da maganar neman gidansu Nagiz nayi masa maganar sarkin ramalla
yace " sai na dawo ma ci gaba "tayaya zanje gidan " na tambayeshi
.
"An rushe gidan tuntuni don mu daina tunawa da shi, ba komai yanzu sai fili kawai, amma yana da
'ya'ya ya mike tsaye ya dauki Shuraih Usman 99% kwagirinsa ya rakoni kofar ya sunkuya kamar zai
sumbace ni " yana da diya sunan ta Nagis taana da kanwa Ikram dukkaninsu suna cikin kungiyar
hamas, bansan inda nagis take ba yanzu kada kaje nemansu
.
Ba mamaki jami'an tsaro su halakaka don kowacce ana nemanta ruwa ajallo"
Ya dafa ni kamar yana bani shawara sai ya fadi wasu kalmomi da sunan wani layi a cikin ramalla
yace na tambayi wani mutum na fada masa abin daya fada mini "zai taimaka maka kaga daya daga
cikinsu na gaya maka ne don na amince da kai maga alamar kai mujahidi ne"
.
Muka fito da abduljalil ya shiga mota zuwa gida ni na tafi cikin Ramalla
.
.
Anan zan tsaya sai mun hadu bayan kwana biyu
Nine naku akoda yaushe Shuraih Usman
Inkiya 99%
.
Abun dayasa kukaga bana post kullum kuma banayi da yawa shine
Nafi ga ne nayi post kadan mai amfani
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi Daurawa
Littafi na daya 1
Page 8
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
ZIRIN GAZA
--------------------Na shiga garin ramalla a wa daya bayan rabuwar mu da abduljalil kai tsaye na shige masallaci nayi
sallar azahar bayan sallama limamin masallacin ya mike yayiwa masallata wa'azi yana fadakar da su
abin da yake gabansu na fafatawa da yahudawa

.
"Dole ne mu sauke nauyin daya hau kanmu dole mu kwato kanmu daga kan gin bautar 'yan kaka
gida , falasdinu ta falasdinawa ce kuma masallacin kudus na musulmi ne"
.
Kabbara mai karfi tama sallata ta katse shi da aka lafa yaci gaba "duk musulmin duniya ya
haukansu suyi yaki don yantar da masallacin daga hadarin da yake ciki,
.
To amma mune makwabtan masallacin don haka mune zamu fara nuna kin yardarmu , da
bijirewarmu sannan muyi tawaye , mu yi fito na fito mu fafata, mu hautsina da yahudawa don mu
nuna wa sauran musulmin hanya"
.
Aka sake kabbara mai karfi har sau uku, da haka yayi bayani na zaburar da matasan dake cikin
masallacin ya kuma kare da "Allah ya tsinewa masu danne hakkin mutane, ALLAH YA TSINE
WA 'YAN TA'ADDA" masallacin ya kaure da kabbara yayin da ya ce "ALLAH YA TSINE WA
IZRA'ILA, ALLAH YA TSINEWA AMURKA"
(Nima shuraih 99% nace Allah ya tsinewa yahudu, jama'a kuyi comment da Allah ya tsine masu)
.
Cikin dabara wasu matasa suka sashi a tsakiyarsu suka fice da shi daga masallacin suna kabbara
suna daga hannuwa, wannan lamarin ya farkar dani samun wani kuzari a ruhina, duk da labarin
yakin da abuja'afar ya bani wanda yasa jikina yayi sanyi bakin ciki kuma ya rufeni wannan bayanan
da kuma kumaji da kuzarin da ruhin gwargwarmayar dana gani tare da matasan Ramalla ya bani
kwarin guiwa da farin ciki a raina, domin naga alamun daukan fansa a tare da matasan
.
Kai tsaye na tafi inda akayi min kwatance bayan na gama nazarin gurin a taswirar matafiyata dana
saya na nablus, na sauka daga bus na yi tattaki mai dan nisa , kwatsam sai (shuraih usman inkiya
99% bazan taba daina fadin Allah ya tsinewa Izra'ila ba ) jikina ya bani kamar ana bina cikin
hanzari na waiwaya naga wani mutum dogo dan tsattsama yana sauri yasa bakaken kaya da hula
hana sallah.
.
Ina ganin sa gabana ya fadi na sassauta tafiyata na saurara ya cimmini ya dan bangajeni ya shige
.
Ganin haka sai na koma baya ina isa bakin hanya wata motar limousine mai kofa shida , gilashin
motar bakine yana daukar ido ta tsaya a gabana a hankali, ganin ta tare hanya sai na kauce zan gifta
sai naji wata murya kamar na taba jinta amma na manta inda na taba jinta , nayi kamar ban jiba sai
na sake ji " may I give you a lift "
.
Muryar mace matashiya mai taushi lokacin na tabbata na taba jin muryar, don haka na waiwaya
sosai na sunkuya don inga mai maganar, ban iya ganin ta ba, sai gabana ya fadi ras, don haka ban
amince na shiga ba naci gaba da tafiyata
.(Shuraih Usman inkiya 99%
Na fara tafiya amma ban san inda zan nufa ba ganin ina kokarin ciro taswira daga aljihuna sai motar
tayo gaba ta cimmin "can I help you" har zance a'a sai kofar motar ta bude wata yarinya ta fito
sanye da siket iya cinya da tabarau baki a idonta tasa takalmi mai tsini rigarta shara shara wacce ta
bayyana dukkan surinta kusan mamanta a waje suke, hannun ta akwai agogon gwal
.
Ta tsaya a gabana tana kanshin turare kana ganinta kaga ba Amurkiya, hakika na san cewa akwai
inda na taba ganinta amma saboda halin da nake ciki na kasa gane ta
"Kai bakone anan ko" tace dani na dubeta
"Ni dan yawon bude idone " ina gama fada mata nayi kokarin tafiya tayi murmushi
"Ina kake son zuwa ne in kaika "ta duben tayi dariya "kana jin tsorone" jin haka na gaya mata inda
zani
.

Ta girgiza kanta "bana shiga nan akwai hatsari garemu"
Tai mun kwatance na kama hanyar shiga motar tayi gaba har da dago min hannu
.
Na shiga unguwar datai mani kwatance, nayi ta shiga lunguna har nakai ga fadar sarkin ramalla ba
komai sai fili kato an kewayeshi wayar mai kugiya sojoji suna Shuraih Usman inkiya 99% gadin
filin suna dauke da bindigogi masu sarrafa kansu, a gefe daya akwai wata yar rumfar soja an
kewaye filin
.
Ban aune ba sai naga wani soja a gabana rike da wani jifgegen kare mummuna yana haushi sun
tsaya a gabana "no tresspassing mister"
Sojan ya fada cikin fusata na rufawa kaina asiri nayi gaba
.
Na isa masalacin ramalla don nayi sallar la'asar ina sallama ba shida nisa da filin , shine masallacin
sarkin ramalla , baban nagis ne ya gina kafin yahudawa su kasheshi, bayan na idar da salla na
tambaye wani dattijo ko yana da labarin filin can da sojoji suke gadinsa,
.
"Wani yace maka wani abune game dashi" nayi shiru zuwa can nace masa "ni dan yawon bude
idone , ina dai son jinko yana da wani tarihi"
.
Yadubeni sosai "daga wacce kasa kake" cikin sauri nace masa "nazo daga Nijeriya" ya nade
carbinsa "zo na kai ka wajen wanda zai baka labarinsa"
.
Yana gaba ina binsa a baya cikin ladabi muka shiga wani dan karamin gida a cikin wani lungu a
tsakiyar unguwar, muka shiga can kuryar gidan, muka iske wani mutum yana zaune akan wata
darduma mai alfarma irin ta da matasa majiya karfi sun kewayeshi, muka Shuraih Usman inkiya
99%. Gaisa bayan dattijon ya gabatar dani na gaya masa labarina
.
"Ni ina daga cikin 'yan gidan sarautar Ramalla sunansa abdullahi ya fada mini kai tsaye,
"Wacce sheda za ka nuna mini" na tambayeshi yayi murmushi "wannan sune shaiduna" dattijon
daya kawoni ya katse mu shi dan jinin sarautar gaba na baya"
.
Wannan yasa nayi farin ciki gani ban sha wahalar da na zata zan sha wajen neman kanwar Nagis
don haka cikin zakuwa nace "ina son ganin 'ya'yan sarkin Ramalla yanzu"
.
Wani matashi a gefe yacee "ba shi da 'ya'ya" na kalleshi "yana da su mana "na mayar masa . Wani
abu kake da shi muhimmi haka da kake sin ganinsu"
,
Dan gidan sarautar ya fada yana kallona "kwarai kuwa ina son ganin Nagis binta Taziz da
kanwarta" sai nayi kallamar da abuja'afar ya fada mini gaba dayensu suka kura mini ido, can yace
bani da labarin Nagis Shuraih Usman inkiya 99% yanzu na samu labarinta jiya amma ban tabbatar
ba ance dan aike zai zo yayi min bayani
.
Amma kanwarta tana cikin zirin gaza, suna kiranta da sunan bintul jihad a gaya mini layi har da
gidan da zan same ta .
.
Cikin murna da farin ciki na barsu, kamar cewa aka yi gata nan, ashe dala dashi da shiga biirni
bane, nayi sallama ko labarin dalilin girke sojoji a filin ban tambaya ba
.
*** *** ***
Gaza birni ne mai girma yana da fadin kilomita mirrabba'in 350 yana kuma da fadin kilomita 40km,
birni ya fada hannun sojan izra'ila a lokacin yakin kwana shida a shekarar 1967 ,kafin lokacin yana
hannun misra tun daga yakin shekara 1948 har zuwa 1967,

.
noma da kasuwanci shine sana'ar mazauna birnin, akwai mutane wajen miliyan daya mazauna
birnin , sannan akwai unguwannin yahudawa 'yan kama guri zauna da suka yi kaka gida aduk gurin
da yake da wata ni'ima an yi musu barkoki sojoji suna gadinsu dare da rana cikin shigar yaki
.
Gaza duk sauran garuruwan Shuraih Usman 99% nake da tarin sojoji cikin kayan fada sabodaa
cibiya ce ta tashin hankali
.
Doguwar bas din dana ke cike tayi birki a gaban wani katon shingen binciken shigi da ficen sojoji
da karnuka masu sansanar bom,
.
Da na'urorin sansanar bom sun bin cika gurun akwai matsanancin tsaro agun sosai zaiyi wahala
mutum ya shige da ko allura batare dako na'ura ko karnuka sun ganoshi ba, haka dai muka shige
.
Muna isa cikin garin na fara ganin kayan abinci iri iri da yayan itatuwa baja baja a ko'ina an baza
sana saidawa kamar yadda zakaga shagunan sai da kayan tireda idan ka shigo birnin kano
.
Mutane birjik suna harkokinsu na yauda kullum , sai dai kuma dole mutum ya tsorata idan bakone
kamar ni irin yadda sojan izra'ila da yan sanda da sauran jami'an tsaro suke kaiwa da komowa layi
layi,
.
Matasa kuma suna cikin halin harzuka da shirin fito na fito da jami'an tsaro kamar an yi musu
allurar yaki, kafin na shiga cikin garin Gaza na sha bin cike da caje caje barkatai da tambayoyin
yaya kazo duniya........
.
Yo ana zan tsaya
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99%
Mamallakin shafin hausaebooks da
Keffians News Teller nake cewa
ALLAH YA TSINE WA IZRA'ILA
Kai/ke ma ku tsine masu
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 9
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Karfe biyar da rabi na yamma daidai na shiga cikin garin gaza, jami'ar tashin hankali makarantar
koyon gwagwarmaya da daki ba dadi , fagen daga kwami filin yada kanin wani
.
Na duba agogona naji kausar ta fado min arai na yanzu saura sa'o'I goma sha biyu alkawarin da na
yiwa kausar na komawa ya su cika, kuma shine yayi daidai da sauran sa'o'I araba'in da takwas na
lokacin da aka diba mani na zama kasar izra'ila ya kare gashi ban ga kanwar nagis ba
.
Amma nasa araina nan da sa'o'I biyu ko uku komai dare na gama abin da ya kawoni. Gobe na kai
ziyara masallacin kudus na kammala komai na koma sarayebo wajen kausar kafin mako guda na
koma gida najeriya Shuraih Usman inkiya 99% ina tawa Allah na tasa kuma ta Allah ce mai
tabbatar ko ina so ko bana so
.

Alokacin da muka ratso ta bazar din gaza na ga shaguna duk a rufe na za ci har sun rufesu ne haka
da wuri, na tambayi abokin zamana cewa da wuri ake rufe kasuwa ne?"
.
Ya dubeni "kai bakone ko" na amsa masa maimakon yayi wani bayani sai yayi shiru kawai zuwa
can wani agefe yace " intifada ta shigo kasuwa kenan" sai yayi kabbara munzo daidai da wasu yan
sanda, wani matashi a kujerar gaba,
.
Yana sanye da suwaita fara mai tmabarin pLO da wando baki yasa tabarao shima baki ya yafa
makawuya mai rodi rodi fari da baki , kakkarfa dashi ya mike ya leko ta taga yace " al mautu lil
izra'ila" ya fada da karfi cikin motar suka amsa masa
.
Kafin kace kwabo sun durkusa kasa suka dinga yo mana harbi gadan gadan gilas din baya na motar
ya zube shar kamar ruwa na gaba yayi caba caba da hudojin Shuraih Usman inkiya 99% arsahshi
.
Direba ya take kwano, cikin motar maimakon ya rude da kara da hargowa kamar yadda zai abku
inda ace a sarayebo ne cikin sauri sai kowa ya kwanta cikin motar wasu akarkashin kujera wasu a
karfen motar suna kabbara suna AL MAUTU LIL IZRA'ILA
.
Ni kadai na rage a zaune ina son ganin kwakwaf na dauka abin wasa ne , wata mata mace agefena
tana yi mini ishara na kwanta naki, koda gilas din gefena ya zube ya tarwatse , tartsatsinsa ya same
ni a fuska cikin rabin dakika daya nai tsalle nabi lafiyar kwano
.
A guje muka ratsa bazar din , muna gab da fita wasu sojan izra'ila suka ja daga suka durkusa
kowanne ya dana bindigarsa ya saito mu, abin dana iya gani kenan na sake bin lafiyar karfen motar,
.
Dakikoki biyu ko uku a tsakani sai gilas din gaba ya zube, direban yayi kara ya saki matukin motar
ya fadi a gefe jini yana zuba ta kansa, motar tayi sartu damu a guje ta tunkuyi wasu jerin rumfunan
kayan marmari ta shige ciki tayi karo da bango gao!
.
Shuraih Usman inkiya 99% tana tsayawa na nemi inda kofa take na laluba gun da nasa jakata na
jawo ina tsima nayi waje na taka mutane cikin jini na bazama da gudu ban san inda nake ba
.
Nabi ta bayan rumfunan na bullo ta wani kwararo dogo ina kaiwa tsakiyarsa, sai na hango yan
sandan izra'ila guda biyu da bindigogi a gabana suna muzurai suna jiran na karasa, cikin sauri na
waiwaya baya na hango soja da bindiga ya biyoni da gudu, nayi tunani cikin kankanin lokaci na
rasa mafita gaba kura baya siyaki nace araina
.
Halt halt, sojan ya kwalan tsawa na tsaya cak. "Am a tourist don't shoot me please"na fada cikin
kaduwa kafin na rufe bakina har yayi harbin iska guda biyu, na tsaya na kama salati a cikin zuciyata
.
Yan sandan suka kariso "hands up" suka ce dani na daga hannuwa sama gabana yana faduwa ,
lungun shiru ba motsin komai, mari mai karfi cikin sauri ya sauka a fuskata har sai danaga walkiya
ta gifta,
.
Dan sandan ya kufuteni a baki dayan kuma ya hada mani Shuraih Usman inkiya 99% naushi da
mangari, daga nan sai mari, naushi da kutifo da managari ta ko'ina ya dinga sauka ajikina
.
"Ku saurareni kuji matsayina mana" na dinga fada ina rokonsu, amma kememe suka ki saurerena
sai duka suke min kamar Allah ya aikosu,
.
Sojan yana karisowa ya tabe iya karfinsa yakai min duka da gindin bindigarsa bai fi taki daya ba
bindigar ta sauka akaina na lura cikin sauri da hanzari na ban mamaki na kauce cikin dabara na

hankada dan sandan dake gabana nayi tsalle gefe guda, bindigar na sauka akansa yayi kara kafin ya
fadi idonsa ya juya yif ya fadi kasa kamar itace
.
Ganin haka daya dan sandan yaja da baya ya fito da bindigarsa daga kugunsa a cikin rigarsa, kamar
na rumbacceshi ta irin salon da aka koya mini yadda ake kwace bindiga in an rutsa mutum,
.
Amma ganin bayana akwai soja da bidiga, naji gabobina sun tsaya cak kamar an zaren min laka,
sanyin karfen bindiga akeyata shi ya karyan lago Shuraih Usman inkiya 99%
.
"You are under arrest" sojan ya fada da kakkausar muryarsa, na daga hannuna sama "kayi amfani da
karfi akan jami'an tsaro" na bude baki zanyi magana sai naji kakat yana shirin harbi don haka na
tsaya kam bana ko motsi
.
A hankai suka bincike jakata suka dauken american express card dina da kudina sam dala dubu
ashirin dina na takardar dala dari dari acikin sin kinsu, suka dauki fasgo dina suka bincike kasar
jakar suka dauko sarkar wuya ta nagis, suka duba sosai "ancient atiquity" dan sandan ya mikawa
sojan, yadaga sosai precious jewellery of the middle age " ya saka a aljihunsa yasa dariya
.
Naji kamar an cire mani zuciyana koda nayi kokarin magana sai "zamu kashe ka yanzun nan" suka
sa dariya cikin kankanin lokaci nayi tunanin sarkarnan ita ta kawoni nan , sannan ga alkawarin dana
yi wa Nagis gashi nazo garinsu mintuna kadan ya rage na kaiga mai sarakar,
.
can na tana ai jiya ba yau bane ,yanzu ina da Shuraih Usman inkiya 99% horon soja na kuma kware
a fagen dabarun yaki naga kuma yaki nayi shi na shiga hatsari daban daban , don haka dole na
kwace sarkar nan ko da zan mutu kuwa, wannan shine abin da zanyiwa Nagis bayan ranta
.
Na saki jikina nakama rokonsu na marairaice har da hawayen karya, mai bindigar yana dan
waiwaya don duba wanda ya suma cikin hanzari na shammaceshi ni kai na nayi nayi mamakin irin
saurin danayi nasa hannuna na bige bindigar da karfi
.
Kafin dan sandan dayake gabana ya danna kuna man bindigarsa ne na dauke shi da kafata tayi sama
cikin sauri da azama na sunkuya kasa, yayin da sojan ya kawo harbi harsashi ya sami dan sandan
aka yayi tsalle ya fadi kasa tum
.
Nakai kasa Shuraih Usman inkiya 99%cikin sauri nayi kwabo na kwashe kafafunsa ya saki bindigar
ya zube da baya cikin sauri da azama nayi tsalle na hau ruwan cikinsa , muka kaure da kokawa
naiya kokawa don ni gwanin kokawane tun ina yaro
.
Ganin nayi biji biji da shi kuma bazai iya galaba da ni ba, ya zaro wuka a kugunsa ya kai min suka
nayi tsalle na goce gefe, ya sake kai mun wani wawan suka Allah ya kiyaye na sake gocewa
.
Ganin na daga shi sai ya tashi idonsa a rufe ya nufi bindigarsa ina share kafafunsa , ganin zaici da
baka dole ya saki wukar don ya ceci hakoransa daga zubewa ban san ya akayi ba sai naji ya kurma
ihu, wukarsa ta nutse a cikinsa jini na zuba hanji waje
.
Cikin sauri na kwashe kudina da sarkar da katuna na na harhada kayana cikin hanzari na rataye
jakata, ina ratayawa motar yan sanda ta gifta kwararon tana jiniya ban san lokacin dana daka wani
wawan tsalle ba na hau katangar rumfar kasuwar nayi sulu a bangon gini, Na dire waje na rarimi
jakata na kama cin gudu
.

Matsanancin gudu kamar raina zai fita ya kaini cikin wani lungu inda palasdinawa suke karfina ya
kare na yanke jiki na fadi, cikin murya mai taushi akayo mini sallama wasu hannuwa suka ci cira ni
zaune na bude ido na duhu ya fara yi "ina ne wajen saukar baki"
.
Na fada ina haki, wani ya karbi jakata yabani dabino, wani kuma ya kuma ya mika mani jaka cike
da tuffa da inibi da lemon zaki
.
YOH KAGA MUSULMAN DUNIYA KENAN
.
Anan zan tsaya maci gaba a page 10
Nidinne dai Shuraih Usman
Inkiya 99% mamallakin shafin hausaebooks da
Keffians News Teller ke cewa
ALMAU'TU LIL IZRA'ILA
AWA 48 A ZIRIN GAZA
Na Ibrahim akhatibi daurawa
Littafi na daya 1
Page 10
Typing:- shuraih Usman
Post shuraih 99%
.
.
Mun isa wani gida wasu matasa rike da bindigogi masu sarrafa kansu suka kewayeni, sun rufe fuska
da makayuwa idonsu kawai ake gani, a kusurwar gidan akwai wasu dauke da "rocket propelled
launcher"
.
Kowanne yana rike da madubin kawo nisa kusa ,muna isa daya ya dirgo yasa sauko yana bani
mamaki, kuma ya tuna min da yadda yan hamas suke dirga yabani hannu muka gaisa
.
"Na hango yadda kayi da la'annun can ka birgeni ko ka taba yaki ne" ya saki hannuna na bashi
labarin zuwana da kuma gaskiyar cewa ni dan

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment