Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yayeshi lokacin zee ko batan wata bata taba yiba gashi xamansu sai ahankali. ta dauki sadiq ta nufi gidan abidina dashi a falo ta samesa xaune ta ajiye sadiq da trolley dinsa, sai alokacin sukayi ido biyu dashi tun bayan dawowarsa daga malaysia sai da gabanta na fadi. cikakken matashi dan shekara ashirin da tara ya xama qaton gske yanada wata irin halitta da kalar fata mai daukan hankali da fisgo xuciya xuwa gareshi musamman daga fitinannun matan da sukasan qirar namijin duniya, sai take ganin rashin lefin xee dan ta maqalemasa, dogo ne sosai mai ginannen jikinda babu qiba babu rama acikinsa, mawuyacin haline ka banbance nationality dinsa saboda haiba da kamalarsa yaxama chocolate bature,kyawunsa suka cakude suka bada surar giant idanunsa kadai suna narkarda xuciya(oily eyes), tayi saurin kawar da tunaninta ido cikin ido take kallonsa ga yaronka naxo ma dashi nayi dawainiyar rainon cikinsa nikadai batare da kulawarka ko dayaba,na haifosa na kuma shayar dashi na tsawon lokaci, inaji kamanta mgnr da mukayi dakai a baya na dawainiyar yara xaka auro wacce xatayi shiyasa naxo ma dashi kabawa xee shi tayi masa tarbiya kamar yanda kace ta juya tafice battre dataji mexaiceba yabita da kallo hrta fice [7:07PM, 2/23/2016] Pherty🎤👯: a ransa yace xee batada tarbiyar da xata bawa yarona wadda ta wuce ke mahaifiyarsa kibasa sai ya dauki sadiq ya nufi gida dashi tana tsaka da karatunta halima ta shigo a fusace tace ashe ke wawiyace nusayba, idan wannan shine hankalin dakike tunanin kinyi to kinyi asara tunda hr xaki iya kyautar da yaronki ga kishiya wacce bakisantaba bakisan.kowace irin tarbiya takeda ba ashs qiyayyar da kikewa yaya abidi xata shafi yaronki? tace tor miye.naki don na tsaneshi inaji yaron dana kyautar nawane ba haifamin akayiba kuma naji ya dawo dashi and what else,nace bana sonsa sai me? tace idan kikace bakison
yaya bakiyi adalciba yayankine kuma mai sonki,ya soki tun kinada qurciya kuma yayi haqurin xama da halinki, nuna maki dayake bayasonki wlhy bada gske yakeyiba sai dan kisan ciwon kanki,kuma na rantse kikayi saken daya kubuce maki xakiyi nadamar da baxatayi amfaniba tunda na lura ke sakaraice bakida hankali, a bit lunatic..!!! ta fada cikin daga murya tana xaro idanu saboda takaici da bacin rai. tace nice banida hankali halima, lunatic? Ni???ta fada tana nuna qirjinta fuskarta dauke da tsananin mamakin jin kalmar daga halima. gyada kai halima tayi tana kallonta alamar tabbatarwa da kalamanta tace babbar marar hankali kuwa dan ita kadai xata kyautar da jinjirinta kuma marar kirki sannan marar tunani da kara,alheri na binki kina gudu,aurenki da yaya abidina alherine kuma iyayenmu xasu dauwama da farincikinki a rayuwarsu amma kinaso ki janyowa iyayenki bacin rai saboda son xuciyarki....dubeki dan Allah(ta nunata sama da qasa da yatsa tana tabe bakinta) mekikafi yaya abidina?baqa qirin dake siririya kamar rakken tankada,banda so gamon jini ne mexaiyi dake banxa mai kama da yan qauyen chukun, takaici ya cika xuciyarta ta harareta tace baki burgeniba sai kingayawa uncle haka inyaso sai ya gayamaki dalilinsa nason karen rakken tankada,nace bana sonsa kuma bantaba sonsa sai kiyi abinda xakiyi, ta juya tana fadin i dont have time for your stupidity banxa ta fice... itama halima taja dogon tsaki ta fice cike da bacin rai. Sadteeyash💝 📝Hausa novel📚 [8/20, 9:17 PM] ‪+234 812 673 9684‬: [8:34AM, 2/23/2016] Pherty🎤👯: .......ADOTAFIYA🚵🏻 ©🏻Fertymerxarah💝 81 to 85 Tunda ta tashi barcin rana takejin qamshin turaren daya kasa gushewa daga tunaninta,tasan su biyu ke amfani da turaren amma tun bayan dawowarta daga Malaysia daya qare bata qara ganin irinsaba. Tor waye mai wannan turaren? Ta sauko daga saman gadon tana miqa tare da fadin Alhamdulillahi lazi ahyana ba'adama amatana wa ilaihir nushur. Ta fito falon cike yake da yan uwa da abokan arxiki maqota masu xuwa yimata barka da haihuwa,ta tunxure bakinta, Ita wannan taron da ake masu a gida ya soma isarta sai kace basu taba ganin jaririba a rayuwarsu,bata kula kowa ba ta fice suka bita da kallo suna sannu nusayba amma taqi ta amsa, Gab da zata fice taji an riqota ta juyo cike da masifa caraf suka hada ido ai kuwa sai tasoma qara tana kiciniyar raba Halimatu daga jikinta Abbu ya fito da sauran mutanen dake falon,Halima tasaketa jikinta a sanyaye idanunta sun kawo kwallah Tace nikike gudu nusayba? Tace aike ba mutum bace fatalwace ance idan mutum ya mutu baya dawowa,aka soma dariya,ta fashe da kuka Tace wlhy ta mutu, abbu ya dafata Yace bana gaya miki bata mutu ba tana kwancene a asibiti Tace amma uncle ne yace ta mutu fa Halima tace cewa ne yayi kawai Dan ki nutsu amma baki cnxaba,ina kwance a asibiti dana Sami lfy yakaini gidan abokinsa acewar qila xakiyi hankali, ta juya tana kallonta Kice wlhy baki mutuba? Halima tayi murmushi kawai tafice umma tamiqo mata jariri Tace jekibasa abincinsa sai kuka yake,ta tunxure baki tana buga qafafunta a qasa ta maida hannuwanta baya alamar bata karbansa Tace ni shikenan sai yata shamin kaya alhali ni bn taba sha Masa feeder ba😳 Ankayi shiru ana kallonta umma taja hannunta a fusace tayi daki da ita fuskarta a daure Tace karbar shi kibashi yasha kona cimaki mutunci ynxu, ta karbeshi tana hawaye ta soma bashi tana rumtse idanuwanta Tace umma akwai xafi, Tace nasani ki daure mana haihuwa batayi wuyaba sai shayarwa.. Cikin kuka tace wlhy nima sai nasha feeder sa na shanye madarar dake ciki🙆🏼 Umma tace tor shikenan..... Kwana biyu sai dar_dar take da Halimatu takasa sakin jikinta da ita kamar da duk ynda halima taso,ko jariri ta dauka nusee xata aika akarbo wai karta cinyeshi. Ranar suna nema tasaki jiki da ita duk shirin daxatayi itake gyaramata, Yaron yaci sunan Abbu wato Abubakar suke kiransa sadiq. Taron sunan ya qayatu anyi biki sosai kuma gwargwado daddy ya kashe kudi, Duk inda ake bikin kudi ko babu gayyata sai kagahalamcy Nadaisan nusee ta gayyaci gudan jini da tsoka Aysher da serdy, gasu kheedy,ummi aysher, mmn khady, mmn boy, mahasin, mami gimba,xarah dange,sally moh, ru'aiya,xinatu,xee, hassana ,rabi'a,nabila, rashida,sa'a,fidoo, kofa, bebinga da duk ma masoyan nusee daban ambataba nasanma yawa ndaku👪👪👪👪👪👪👪👪👪👪nidai pherty kobaa gayyaceniba bakomai tunda ga kishiyhalamcy😜xata wakilceni kuma dole nasamu babbarabo👯. 86 to 90 Bayan suna tana xaune tana harhada kayan data samu ga bikin da kyaututtuka da daddy da umma suka mata sai ga Halima tashigo taxauna a kusa da ita hade da atishawa Tace Alhamdulillah,tayi shiru ko xataji nusayba xata iyar mata amma sai taga hankalinta na gun kayan datake hadawa [8:35AM, 2/23/2016] Pherty🎤👯: Tace nusayba nayi atishawa nace Alhamdulillah bakice komai ba, batare data kalletaba Tace mexancene me ake cewa,ni bansaniba, tayi shiru tana kallonta da mamaki Dan tasan atare aka koyardasu a islamiya Tace baki saniba fa nusayba? Ta tunxure bakinta Tace na manta, ke bakisan xafin haihuwa bane,idan ka haihu ance kana mantawa shine nima na manta komai nayi formatting yanxu. Halima ta sauke ajiyar xuciya Tace Annabi s a w yace idan dayanku yayi atishawa to yace ALHANDULILLAH dukkan yabo ya tabbata ga Allah, idan wanda ke kusa dakai yaji sai shima yace YARHAMUKALLAHU Allah yayi maka rahama,sai kai kuma kace YAHDIKUMULLAHU WA YUSLIH BA'LAKUM Allah ya shiryaka ya kuma kyautata halinku. Amma idan kafiri yayi atishawa ya godewa Allah to sai kace YAHDIYKUMULLAHU Allah ya shiryardakai, kada kace YARHAMUKALLAHU baxakace Allah ya Masa rahama ba, Nusee ta dago a raunane tana kallonta Hakane fa sai ynxu na tuna. [8:35AM, 2/23/2016] Pherty🎤👯: idan kinyi anjima xn qarasamaki, halima ta janye kayan datake hadawa tana kallonta tace ynxu kin haihu nusee kinxama uwa yakamata ace kinyi hankali kindaina duk wasu abubuwa ynxu saboda girman da Allah yabaki, ki xauna kiyi tunanin ynda zaki gyara rayuwarki da aurenki idan baso kike kixama baxawara ba tace wacece baxawara? tace by defination baxawara itace wadda ta tabayin aure ta fito adalilin saki ko dalilin mutuwa. tace tor menene aure? tace aure sunnanh ce ta annabi mohd s.a.w, shine mace ta sadu da namiji, ita wadda tayi aure kota sadu da namiji kobata sadu da namijiba a society sunanta baxawara, kuma society na kallonta as less-privilleged than the unmarried one, inhakane kenan duk wadda tasadu da namiji a waje komai qanqantar shekarunta sai dai a liqa mata suna budurwa amma baxawarace. tace to ai nima baxawarace uncle ya sakeni. tace ya fada maki da bakinsane? tace a'ah yabani takarda tace kin karanta saki nawane? tace a'ah na boye halima taja dogon tsaki mtsewww kedai bakida wayo wlhy, xo ingaya maki mgn a kunne kada pherty taji tagayawa fans dinta.......ta kyalkyace da dariya tacd tor naji xn fara kuma xnxama babbar mace qasaitacciya kamar yanda sadteeyash sukacemin da sukaxo biki. halima ta xube mata littafan hausa a jikinta tace kifara karatu daga anjima inaso kisami experience kisan kanki kamar kowace mace ki ajiye wasa a gabanki,kisan ynda mace k kwatar yancinta agun namiji,ga dayan littafin fauxiya d. suleman matsalolin ma'aurata da ynda xaa gyarasu shima ki karanta, duka littafannan abu mai kyau nakeso kiyi koyi dasu kiyi watsi dana banxa, kinga koda yaya xaixo xaiga cnji daga nusee xuwa nusayba ko? ta karba tana dubawa tace tor shikenan xn karanta amma ni banason uncle gsky, halima tayi jim kafin tace kidai karanta tace tor..... halima ta tashi ta fice tana murmushi tabarta da tulin littafai...... Sadteeyash💝 📝 Hausa novel📚 [8/20, 9:17 PM] ‪+234 812 673 9684‬: [9:12PM, 2/26/2016] Pherty🎤👯: .......ADON TAFIYA🚵🏻 ©Fertymerh xarah💝 110 to 115 Kuka take tana qarawa a ynda takeji batada wani xabi wnda yawuce wannan da aka dorata akai, ta share hawayenta tana sauraren fadan da inna da umma ke.mata daga qarshe suka mata umarni da tatashi tabi mijinta gidansa dan baxasu cigaba da xuba mata ido suna kallonta da aure ba, ta tashi hade da qara sautin kukanta kamar wacce akayiwa mutuwa ta fita kota kan sadiq bata biba, aharabar gida su abbu da daddy na tsaye ta wucesu tana kuka ta bude motar ta shiga da qarfi ta rufeta sai da abidi ya tsorata, halima ta tabe bakinta tace yaya karkayi mgn shiga motar muje. hr suka xo gidan bata daina kukan ba, halimatu ta rakata hr nata sashen yana tsaye yana kallonsu, ya nufi sashensa kai tsaye dakinsa ya xarce batare daya nemi xee ba yana xaune halima ta shigo ta dubesa a sanyaye tace yaya ni waxai kaini gida da wannan daren, yace driver xai kaiki ki masa mgn akwai key hannunsa tace tor shikenan sai da safe ta juya ta fice hrta kai bakin qofa ya kirata tadawo ta xauna, yace nusayba metakeyi? tace wlhy bnsaniba cos rufe qofar tayi inaji kukan dai ne. kamar bashiba saboda muryarsa datayi qasa sosai ta nuna wani mutum mai axabtuwa da soyayya, yanayine da halimatu bata taba ganin dan uwanta a ciki ba yace halima dan Allah a matsayinki na mace mai qarancin shekaru kuma shaqiqiya agareni wadda nakeda tabbacin baxatagayamin qaryaba dan naji dadi ta boyemin gsky dan na cutu inada wani aibu ko hali marar kyau da nusayba ta tsaneni haka tausayin dan uwanta ya kamata tace wlhy yaya bakada shi. yace tor miye laifina dan na dora nusayba kan turba mai kyau dan na nuna tasan kanta tadaina wauta? ta runtse ido tace ba laifi bane yaya tunda koni ina dorata akan hanya kuma bata tsaneniba [9:47PM, 2/26/2016] Pherty🎤👯: ba abinda k damun nusayba hr ynxu sai qurciya da wauta hr ynxu batasan kantaba batasan so ba tunda ko sadiq bata damuwa dashi kamar ko wacce uwa. ya bude baki yana.kallonta da mamaki who told u? nasan komai yaya kada kamanta tare muka taso mukayi rayuwa tun muna qanana, nusee xata iya bada lbrn kamar ynda xn iya bada nata above all ma tun tasowarmu, i'm far more sociologistic than a political scientist,kaga kuwa nice nafi kowa sanin halinta. yayi shiru yana kallonta yace ni inaji ajikina wataran xatasoni ta rungumi yaronmu
tunda ynxu.muna inuwa daya da ita ina sonta fiye tsammaninki amma baxan iya roqonta akan ta soni ba kada ta rainani (a ranta tace)yaya abidi ho ! sannu dason girma wane raini yayi saura tsakanin miji da mata, ai da daban, ynxu daban babu xancen discipline sai unity and cooperation a fili kuma tace tough kaima kanada laifi yaya mace yar rarrashice tanaso anuna mata xahirin soyayya ciki da waje ,baka rarrashinta tarairayarta da nuna mata xahirin soyayya idan kayi laakari da xaman ku na farko ba komai aciki sai fada da fushi wannan shi ya janyo tsana a tsakaninku kuma tun farko baka koyamata ynda xata soka ba. ka duba ynxu kaga ynda ta cnxa rayuwarta karatunta kawai tasa agaba, kanta na cikin duhu batasan komai ba sai wnda aka koyarda ita, batasan soyayyar miji da mata ba, batasan ynda ake rarrashin miji ba,batasan ynda ake kula da miji ba,kishima batasan ynda akeyiba, idan ka lura kallo bai dametaba tun dawowarta daga malaysia,bata karance karancen nan na littafi danaso na dorata akai taqi, batada qawa ko aminiya,bata riqon waya balle ta shiga yanar gixo,she is not exposed to modern society....not interested to social networks e.g whatsapp,bbm, twitter, fcbuk e.t.c.....she is just acting according to her experiences kamar yadda aka tafiyar da rayuwarta abaya, idan ko hakane yaya nusayba na neman rarrashi da tarairaya ka mantarda ita komai ka koya mata ynda xata soka a ynxu babu abinda xai ragu daga gareka idan ka jure wulaqancinta watarana xata sauko? murmushi yayi yana mamaki a ina halima tasan wannan,meyasa tafisa xurfin tunani da hankali......sai yayi qoqarin kawarda mgnr ta hnyar cewa k yaushe xakiyi auren ne? ta rufe fuskarta da tafin hannuwanta tana dariya ta fice tana fadin kai yaya bari dai na turoma gimbiyar. tunda halima tagayamata kiran take xaune tana saqe saqen taje kokarta je a tunaninta mexatayi meyasa yake nemanta a wannan daren.... ta tashi ta dauki hijab dinta ta fice.... ya fito wanka daure da towel a jikinsa da qarami towel yana tsane gashin kansa sai ga xee ta shigo tace honey ashe ka shigo shine baka sanardaniba, yace akoda yaushe ina gayamiki muhimmancin sallama da kuma dimbin ladar dake cikinta amma meyasa kike butulcewa ne? cikin halin ko inkula da mgnrsa ta qaraso garesa tana shagwabe fuskarta next tym xn qoqarta naji ko xn iya ina mantawane ya tabe bakinsa hade da dauke dubansa daga gareta ya isa bakin mirrow ta bishi ta karbi towel din tana tayashi tsane gashin kai dai dai lokacin nusayba ta shigo da sallama ya amsa a raunane hade da juyowa yana kallonta tana tsaye bakin kofa bata shigo ba kuma bata fita ba, yace ki.....bai qarasaba taja dogon tsaki ta juya ta fice hade da bugo masu qofa gammmmmmmmm🙉 Sadteeyash💝 📝Hausa novel📚 [8/20, 9:17 PM] ‪+234 812 673 9684‬: [12:18AM, 3/5/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚴🏻 ©Fertymerh xarah💝 131 to 135 Fardawowar su yayi dai dai da shigowar xee a rude Dr.bakori gaba tana bayansa. a rude nusee ta sauko saman gadon da aka kwantar da ita idanunta taf da hawaye take kallonsa tace likita da gaske duka sun mutu... yace kiyi haquri,mutuwa na kan kowa,kullu nafsin xa'iqatil mauti duk mai rai mamaci ne hawaye suka cigaba da xobo mata, jikinta har rawa yake qafafunta nason gaxa daukarta ya fice yana fadin ku biyoni ynxu, atare su uku sukabi bayansa kowane jikinsa a mace hr xuwa dakin da abidina yake kwance tare dasu daddy, lokaci daya duk sun fita hayyacinsu Dr.bakori yigaba da fadin,inaji wannan yasami matsala a qafafu to confirm it sai Dr.maina yaxo amma ynda naga matsalar daga spinal cord dinsa ne banajin xai cigaba da tafiya. dirshan halimatu ta xame ta xauna cike da jimami yayin da nusee ta dora kanta akan gadon da yake kwance ta saki kuka mai narkar da xuciya....iya rudewa daddy ya rude sai dai ya kasa nunawa saboda kar hankalinsu halimatu ya qara tashi xee na tsaye sai yamutsa fuska take ita batajin xata cigaba da rayuwa da gurgu,tayama xatayi rayuwa da musaki,komai son da take masa dole ta barsa kuma dole ya sake ta dan.baxata iya.lalurarsaba baxata iya.kula dashiba,ta goge guntuwar kwallar dana xubo.mata ta tausayinshi, ta cigaba da taunar cingam dinta ahankali tana.kallonsu umma da inna.......... BAYAN KWANA UKU.... Ya farfado daga doguwar sumar da yayi tym din hr angama ukkun din abbu(Allah yaji qansa😪)nusee nadaga gefensa hannunta sanye a hannunsa daya tun lokacin da ya farfado yakasa furta kalma ko daya,duk iya qoqarinsu daddy akan yayi mgn yaqi hakan ya qara tada masu hankali indai babu internal injury akansa... su biyune a dakin xee ta shigo rataye da jakarta da wata irin shiga danayi matuqar gigita nusee kamar ba matar aureba a hankali ta tako inda suke kwance tana taunar cingam tace ya jiki, bai amsa ba illah idanu daya xuba mata tayi jim kamar baxatayi magana ba sai kuma ta nisa [12:47AM, 3/5/2016] Pherty🎤👯: tace baxan boye ma ba na cutar da xuciyata Allah ya gani baxan iya xama da musakiba,komai son danake masa kuma komai kyaunsa da kudinsa, am sorry to say inaso ka sakeni, idanu xare nusee k kallonta tace ke bakisan Allah ya haramta mace tanemi saki a gun mijintaba. ballantana ma wannan dake jinya yau fa ya farfado kuma kinsan yana sonki dan Allah karkije kibarsa ki xauna dashi xaiji dadi.... a fusace tace keee kimin shiru qaramar yarinya,me kika sani a rayuwa,idan k xaki iya ni baxan iyaba dan dama dan uwankine,dole sai ya sakeni kuma dole nabarsa komai sonsa danake.... cikin kuka nusee ta soma roqonta musamman data ga ta ciro memo da biro ta cilla masa a gadon dayake kwance tace bana nemanka da fada inaso muyi rabuwar arziki albarkacin son danake ma amma na roqeka da girman Allah ka sakeni...... ba musu hannunsa hr rawa yake ya dauki biron sai dai yakasa daukan memo hr sai da nusayba ta taimaka masa da kyar ya iya rubuta NA SAKE KI! NA SAKE KI!! hr sau biyu xai rubuta na uku nusee ta kwace biron tana girgixa masa kanta, xee ta karba tana fadin ai da kinbarshi ya qarasa, tayi murmushi tana fadin wannan ma yayi Allah ya sadamu da alheri xn koma gida malaysia idan nasami tym xan riqa xiyartaka ina duba lfyrka da hannun yayi mata alama karta dawo taje hr abada....tayi murmushi tasa kai ta fice..... sai ya maida kallonsa ga nusee ko itama xata rabu dashine ga mamakinsa sai ta fada jikinsa tana kuka sosai mai tsuma xuciya, sai alokacin hawaye nasami damar xubo masa, suna haka Dr. bakori da Dr. maina na shigo a bayansa securities ne da fadawansa suna biye dashi itadai nusee tana cike da mamakin mulkin wannan likita. cike da qasaita ya xare madubin idanunsa ya miqawa abidi result din da ya shigo dashi yace congrat, iya bincikenmu mun gano hasashenmu ba gsky bane bakada matsala a spinal cord kuma qafafunka lafiyarsu qalau illah wasu jijiyoyine da suka daure insha Allah nan da dan wani lokaci xasu saki kacigaba da tafiya kamar da. A tare shida nusee suka saki ajiyar xuciya fuskarta dauke da murmushi da hawaye take kallonsa tace likita da gske xai tashi yayi tfy kamar da? ya gyada kai yana gyara masa drip yace amma ba ynxu ba sai an dauki lokaci kadan tace kwana nawane likita? ya juyo da mamakinsa yana kallonsa sai yaga kamar yasan fuskar,ya tsuramata ido yana kallonsa hr sai ya gano ko ina yasan fuskar hakan ya qular da abidi ya tsargu da kallon da yake mata nan da nan fuskarsa na sauya shikuma bai dauke idonsa akantaba hr sai daya tuna inda yasanta yace ba lallai bane na iya tuna sunanki but i knw you by face, tace ni na manta, ya tabe bakinsa yatuna amma baxai iya gayamata ba kuma yana son sanin meta haifa, cikin yayi girma a lokacin amma yana ganin idan ya tambaya mulkinsa da qasaitarsa sun xube a qasa dan haka sai ya share xancen yace anjima Saif Bakori xaixoma da magani tare da allurar da xaayima, abidi bai amsaba bai kuma sake kallonsaba sai ya dauke kansa daga garesu yana kallon wani guuu shima maina bai damu ba ya juya ya fice fadawa na xubewa qasa suna masa ikirarin sarauta yayinda wasu fadawan k biye dashi da sauri suna sauya masa labcoat xuwa alkyabba.... nuseee tabisa da kallo cike da mamaki wannan dame yake taqama Mulki ko Sarauta? ta sauke ajiyar xuciya ta maida kallonta ga abidi dake kallonta. Sadteeyash💝 📝Hausa novels📚 [8/20, 9:18 PM] ‪+234 812 673 9684‬: [12:48AM, 3/6/2016] pherty🎤👯: ........ADON TAFIYA🚴🏻 ©Fertymerh xarah💝 136 to 140 Bayan kwana biyu, kai tsaye Dr.merah ya dauki annual leave tare da abidina yana son xuwa dashi pheonix dama adubasa sosai, nigeria batada kayan aiki kamar waje cikin lokaci qanqani daddy yayi masu visa gabaki dayansu bnda inna da umma suka dunguma sai Phoenix. Alhamdulillah anyi aiki cikin nasara sai kuma fatan samun lafiyarshi, sai dai a ynxu anbashi wheel chair akoda yaushe nusee ce k tafe dashi tana xagaya asibitin dashi, abu dayane k damunta dashi rashin maganarsa hr xuwa wannan lokacin, a tsarin halittar dan adam(personality) yana cikin rukunin al-ummar da ake.kira (introvert) kasancewarsa (sociable)bayason magana da.kowa da wuya kaga dariyarsa sai dai idan ana hira guri ya qure yakanyi murmushi dimple din da cleft dinsa su motsa. A wani dare bayan kowa ya watse ya rage su biyu sai nusee tasa masa kuka, ba kukan komai ba face kukan rashin maganarsa, a hankali yakai hannunsa akanta yana shafar gashin kanta,ta dago a raunane tana kallonsa idanunta taf da hawaye sunyi jawur ga mamakinta sai taji yayi magana yace nusayba wanene ya haliccemu? tace Allah s.w.a, yace tor meyasa kike kuka kike damar da kanki abinda Allah ya riga ya rubuto akaina kenan cikin ikonsa kuma zan sami sauqi sai abinda Allah yaga damar hukuntawa a garemu, mu kuma dole ne mu zamo masu godiya idan muna son imanin muya cika, nusee ta jinjina kai tana mai jinjina karfin imani irin na abidina da tawakkalinsa. Lafia garkuwar jiki sauqi ya samu a gun abidi har yana tashi da qafafunsa ya taka da taimakon nusee ko halimatu ganin haka yasa daddy ya koma gida nigeria dan ya dubasu ya dawo, cikin lokaci qanqani shaquwa mai tsanani ta shiga tsakanin abidi da dr.merah hr suka xauna suka bawa junansu labarin rayuwarsu
da matansu, a dan xamansu suka tattauna game da matsalar nigeria ganin waje basu da matsalar komai a rayuwa ya cigaba da fadin pheonix tayi kuma ta hadu tana da hanyoyin cigaba ta kowane fannin mussaman a wurin man fetur amma mu nigeria cigabanmu har yau baixoba ko yaushe nigeria xataci gashin da Allah ya bata? gashidai qasace mai cike da albarkatun kasa musamman man fetir amma suna tsadarsa kuma the problem is with our leaders ,they dont know how to harness the resources available,inkaga talaucin da akeyi acikinta north & south da dilapidated infrastructure sai ka tambayi kanka ina shuwagabanninmu ke kai arxikin Nigeria? [12:55AM, 3/6/2016] pherty🎤👯: Dr. Merah yayi qasaitaccen murmushi hade da xare madubin idanunsa yace ance an bawa nigeria yanci kai amma baa daina bautar da al,ummarmuba, haka suka cigaba da tattauna matsalar nigeria hr abidi ya soma nuna gajiya da hirar dan bai taba tsammanin kasaitar merah xata barshi yayi doguwar hira haka ba, sai ya dafe kansa da hannunsa yace yakamata muje gida haka Dr. tunda lokacin tashinka asibiti yayi kaina ke ciwo(dayake merah ya maida xamansu a gidansa ya hada nusee halimatu da affiya) As a professional medical doctor a take dr.merah ya gano cewa bawani ciwon kai a tare dashi kawai he is helpless a cikin soyayyar matarsa, sai yayi murmushi ya tashi ya taimakamasa ya tashi suka nufi mota. Sadteeyesh💝 📝Hausa novel📚 [8/20, 9:18 PM] ‪+234 812 673 9684‬: [8:42AM, 3/1/2016] Pherty🎤👯: ..........ADON TAFIYA🚵🏻 ©Fertymerh xarah💝 121 to 125 Fitarsa keda wuya ta juya tabi bayansa a harzuqe, yana kiciniyar cire jallabiyar ya sauya da kayan barci ta ixo qofar da qarfi, ko kallon inda take baiyiba ya cigaba da abinda yakeyi. tace andaiji kunya kuma kaji tsoron Allah. a raunane ya juyo yana kallonta yace dama akwai kunya tsakanin miji da mata ne? ba zina nayiba matatace fa, tace dan matarkace sai ka fake kaci amanata ai yau girkina ne,kuma

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment