Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daman tunda ya shigo take hangenshi ta sama,�ara gyra fuskarta tayi sannan tasa hijab dinta tace ma Anani Kamal yazo ita ta tafi, kitchen ta fara shiga ta hado mashi drinks da ruwa, sannan taje,zaunawa tayi tace."sannu da zuwa sahiba."
Kallonta yake yana murmushi dan kallonta kawai yana sashi farin ciki, balle tayi magana, cewa yayi. "Yauwa masoyiyata fatan na samu ki cikin koshin lafiya."!?
"Lafiya lau Alhmdulh, ya gida ya Momy dasu Husna."!?
"Duk suna lafiya lau, suna ma gaidaki."
Murmushi kawai tayi, sannan ta sauko ta zuba mashi drinks din yasha bayan ta gama sha tace mashi."Dady yace ka turo iyayen ka, suyi magana asa baikon bikin mu."
Wani irin farin ciki ne ya lublubeshi, dan bai san sanda ya furta."Alhmdulillh, Allah na gode maka."
Cigaba da kallonta yayi sannan yace."masoyiyata da gaske ne ko kuma mafarki nike."
Kulle fuskarta tayi da tafe hannunta sannan tace. "Da gaske ne ba mafarki kake ba, nice nan gabanka nike gaya maka Dadyna yace ka turo iyayen ka gobe."
tashi yayi yace mata."zafi zafi kan buga karfe masoyiyata, ni zan tafi yanzun naje na gaya ma magabata na, dan yau ji nike kamar ance an daura auren ma."
Ita dai Smile kawai take bugawa dan Zainaba ba daga baya wajen iya murmushi, raka shi tayi bakin mota sai da taga tafiyarshi sannan ta koma cikin gida ta gaya ma Anani yanda sukayi dashi.


Daga gidan su Zainaba gidan Sadiq kawai ya wuce, bayan sun gama gaisawa yace mashi."Abokina Zainaba tace man Dadynta yace na tura iyaye suyi magana asa baikon bikinmu, wata shawara kake da ita kuma."!?
"Alhmdulillh ai Kamal komai yazo cikin sauki, yanzun ka tashi kaje gida karda Momy taga baka dawo da wuri ba ku samu matsala, gobe da safe sai kaje ka gaya ma Baba Bala, sai yaje ya nema maka auren ta."
"Hakane, amman Sadiq nayi ma Momy adalci kuwa idan taji kawai ansa man biki ba tare da ta sani ba."!?... Shiru Sadiq yayi yana kallonta tabbas yasan irin son da kamal yake ma Momy bai san bacin rainta ko kadan, amman idan ba ta haka aka bi ba taua zai samu Zainaba din da yake so, idan har aka cigaba da biye ma Momy to tabbas Kamal zai mutune baiyi aure ba, murmushi ya danyi yana cewa... "Wannan shine adalcin Kamal, da kaje ka ja mata abun magana, ai gwara kayi auren kasan ma rabonka ne yazo kusa shiyasa, idan kuma Momy ta matsa tace zata hanaka wallahi rabo yana iya kasheta kaga gwanma taji kawai ansa bikin nasan ko zatayi maka fada, amman kuma dole tayi hakuri."
"Maganarka gaskiya ce Sadiq, ni na tafi, komai kenan sai kajini."
"To angon Zainaba bada kanka asare kaje gida kace ya faWi."
Dariya kawai yayi ya tafi gida dan yaga lokacin dawowarshi yana son kure mashi, baida lokacin tsayawa ba Sadiq ansa.

Bayan ya koma gida wanka ya fara yi sannan yaje apartment din Momy, abinci suka ci sannan suka wuce massalaci, bayan sun dawo wajen Momy suka koma sukayi firar dare, dan duk daren duniya tare suke fira da Momy sai 11 suke zuwa su kwanta.
Bayan sun koma apartment dinsu waya ya kira Zainaba suka sha wayar su sannan suka kwanta.
Bayan sun gama breakfast ya ce ma Momy ya tafi wajen aiki, daga nan ko bai wuce ko ina ba sai gidan Alhaji Bala.



Yako yi sa'a ya tadda shi a gida bai kai da fita ba, bayan sun gaisa da matarshi ya shiga dakin Baban nashi, zaune ya tadda shi yana karanta newspapper, bayan ya gaidashi ya fara yi mashi bayanin abun da ya kawo shi."Baba daman zuwa nayi na gaya maka inda nike neman aure ance na tura iyaye na, amman maganar gaskiya Momy bata san ina neman auren ba."


Kallonshi Alhaji Bala yayi yana cewa...."Subuhanillahi, Kamalu, ya akayi zaka fara maganar aure amman baka gaya ma Momynka ba."!?
Sosa kai ya fara yi sannan ya dukar dakanshi kasa ya fara ce mashi."Baba na lura Momy bata san taga munyi mata maganar aure, da zaran munyi mata maganar aure zatace bamu isa aure ba, sama da shekara goma kenan, ina nuna ma Momy aure nike so, amman sai tace ita ban isa aure ba, idan nayi aure Yanzun to matar da na aure wayau zatayi man ta kwashe man kudi ta gudu, ko kuma tayi man wayau ta dunga anshe man kudi, haka sukayi da Yaya Usman, da ya matsa mata sai ta barshi yayi auren amman a gabana take sa yana sakin duk matar da ya aure tace mashi ai tayi mata rashin kunya, ni kuma wallahi aure nike so shiyasa na yanke shawarar ban gaya mata dan ko na gaya ma ta ba saurara zatayi ba balle ta anshi uzirina shiyasa nace sai dai taji ansa man baikon biki, amman mudun taji zanyi aure wallahi sai ta hana, kaji dalili na Baba."


Zuface ta wanke Alhaji Bala da kuma tarin mamakin Momy, tabbas bari yayi kama da mutun, shiyasa duk sakin da Usman yake ma matanshi bai taba jin tayi complain ba, aikuwa idan har maganar Kamal gaskiya ce to tayi na karshe dan zai nuna mata karfin ikon uba kan yaranshi, kallon Kamal yayi yace...."Ita Saudatun take wannan aika aikar Kamalu."!? Duk da har kasan zuciyarshi baiji dadin tonama mahaifiyarshi asiri ba a wajen yayan babanshi, amman ba yanda ya iya dan baida choice da ya wuce wannan dan ya tabbata Baba bala ne kawai zaiyi masu maganin matsalar Momy shida Usman a hankali yace..."Eh itace Baba."



Girgiza kai kawai Alhaji Bala yayi ya cigaba da cewa..."Allah ya yi maka albarka, yanzun gaya man gidan da ita yarinyar take, daman yau zani abuja maganar auren yayanka, kai kuma wani gari take ita yarinyar."!?
"Nan kaduna, a unguwarmu, sai dai ba layinmu daya ba, Alhaji Masa'ud speaker din governor to diyarshi ce."
"Masha Allah, ai tare mukayi secondary school dashi Baban nata, Abu yazo da sauki ma, sannan dan Allah Kamalu idan akayi auren nan karka biye ma Momynka kayi na dan'uwanka kaji."?
"Eh Baba insha Allah."
"Yauwa Allah yayi maka albarka, kace masu gobe insha Allah zani zo, yau dai Abuja zani zuwa anjima insha Allah."
"To Baba, Allah ya kaimu na barka lafiya."

Bayan tafiyar Kamal ya kira Zainaba yake shada mata gobe iyayen nashi zasu zo, ta gaya ma Dady, dan yau bai samun damar shigowa da marece, bayan sun gama waya ya tafiyarshi wajen aiki, ranshi tas.....


*>�� SDEENDTM DATA SERVICES>��*
*MTN* . *Airtel*
1GB = � 300. 1GB = � 300
2GB = � 600. 2GB = � 600
3GB = � 900. 3GB = � 900
4GB = � 1200. 4GB = � 1200
5GB = � 1500. 5GB = � 1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = � 350. 500Mb � 500
2GB = � 700. 1.5GB � 1100
3GB = � 1050. 2GB � 1600
4GB = � 1400. 3GB � 2000
5GB = � 1750. 4GB � 2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
=�G�<���=�G�<���=�G�<���=�G�<���=�G�<���
*>؀�08066268951*


*Muje Zuwa.... =ؤ�*


*Yar'mutan kankia cec'�*

Share domin Allah


*�&�NIDA UWAR MIJINA�&�*

_By_

*'Yar mutan kankia c'�*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ


_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via 08160508316_


<ؓ�<���0�� 9�� �%�1�� 0��



Tunda Kamal ya tafi office yake cikin farinciki,yasan shi yau baida wata damuwa,duk da idan ya tuna Momy bata san da maganar auren nan nashi ba sai yaji jikinshi yayi sanyi sai yaga kamar bai kyauta mata ba a matsayinta na mahaifiyarshi mai kaunar duk wani cigabanshi,Amman ba yanda zaiyi dan idan baiyi aure ba da matsala kuma shi maganar gaskiya hakurinshi ya kai geji.
Alhaji Bala yana gama duk abunda yake ya hau motarshi sai garin Abuja,yanda Usman ya turo mashi addresses haka yabi har yaje gidan su Maryam,bayan yayi parking a cikin compound din gidan su,yasa gate man yayi mashi sallama da Babanta,daman sun san da zuwan nashi an shirya mashi tarba ta musamman,bayan angama kawo mashi Kayan lashe baki da makulashe,abunka da anzo gidan da naira ke kuka,ruwa kawai da lemu yasha sannan yace shiko Alhamdullilah ba zai ci abinci ba,ba yanda ba'ayi dashi ba,amman yace hakan ma ya godiya kuma ya yaba da tarbiyar gidan,hakan yayi mashi dadi sosai.
Bayan sun gama gaisuwa da mutanen gidan yake gaya masu abunda ya kawoshi,duk da sun san abunda ya kawo su Amman ya sake maimaitawa saboda nema ma Usman mutunci a cikin idon surukanshi.
Suma sunji dadi sosai,kuma sun na'am da tarbiyar da Usman ya samu a wajen iyayenshi,ko da Alhaji Bala ya gaya masu mahaifin yaron ya rasu,shine yanzun ya rage masu basu da kowa sai shi da mahaifiyarsu,bayan sun gama suka tsada ranar aure nan da wata biyu,sannan ya taso ya taho kuma yaji dadin tarbar mutuncin da surukan Usman suka yi mashi.



Tunda ta gaya ma Anani iyayen Kamal sunce zasuzo yau,ta shirya ta wucewarta wajen aiki,bayan ta gama abunda take ta wuce gidan su Sa'adatu close friend dinta ce sosai,kuma unguwarsu da'ya bayan ta yi parking din motarta ta shiga cikin da gida da Umminsu ta fara gaisawa sannan ta wuce room din Sa'adatu,kwance ta tadda tana hutawa dan itama dawowarta kenan daga wajen aiki take hutawa.
Sallama tayi sannan ta kadamata bugu tana cewa."halan tun dazun kike kwance ko."!?
Cewa tayi."wash Allah,Besty wallahi na tsorata sosai,ga kuma wannan uban bugun da nasha duk ni da'ya."....ta fada tana sosa wajen da Zainaba ta bugeta tana shagwaba fuska.
Tsayawa Zainaba tayi kallona dan ba abun mamaki bane dan Sa'adatu tayi haka cewa tayi."gaskiyane Auta lokacin kine,dole kiyi abunda kike so gida daga ke sai Ummi baki aikin komai daga zuwa office sai kwanciya kiji dadinki."
Murmushi itama sannan tace."ai kema kina jin dadi ta biyun Autar Anani ,harma kin fini,yanzun na dawo wallahi duk na gaji kinsan aikinmu na kananun yara dole ake gajiya ba irin naku ba na manya,zama kawai kuke kuna yin sing kinga ai da banbanci ko."!?
"Ba wani banbanci Besty kedai Allah yasa mudace,Amman wannan zamanin ba abunda zamu iya cewa sai Allah yatsare mu kawai."
"Amin ya Allah,ya Anani dasu ango Autan Anni."!?
Hhhhhhhhh!"wai Besty kinji labarin Auta shima aure zaiyi kenan."!?
"Naji mana Besty,da yake kinsan Muhisin ba kunya ne dashi ba sosai,jiya ba na kiraki waya ba nace kizo ki rakani saloon ba kikace man baki samun damar fita kanki na ciwo."!?
"Eh hakane anyi haka,wani abu ya faru kenan."!?
"Aa ba abunda ya faru sai abun dariya,bayan na fito da motata ina shirin yin reverse kenan sai ga Muhisin shima ya kunno hancin motarshi muka tsaya zamu gaisa nan yake ceman tunda muki yin aure shi ya shirya dan ankusa yin bikin shi ya zama Dady shima Kamar yanda su Yaya Anna's suka zama."
"Ikon Allah,wallahi ko Besty ban taba ganin marar kunya ba Kamar Auta,nima yau da safe yace man karna sake cemai Auta,Idan ban iya kiranshi da Muhusin to ya hutar dani kiran sunanshi na dunga cewa wane,dan ba yanda za'ayi yana shirin zama Dady ina kiranshi da suna Auta."
Uhmmmuhmmmuhmmm!"ai naga sai rawar kai yake,Allah dai ya tabbatar da Alkhari."
"Amin,Besty nima fa yau za'azo a tsada rana,daman Dady yace rana daya zaiyi mana aure nida Auta."
"Woow,Besty naji dadin wannan labarin ko,ina fatan dai da Kamal za'ayi."!?
"Wallahi ko Besty dashi za'ayi,yanzun mai kike ganin za'ayi a bikin."!?
"Kawai ayi kamu da wa'azi Kamar zaifi dan kinsan idan aka cika yin program a biki a wannan zamanin da muke cikin akwai problem kinga kawai gwara ayi kamu,shima kamu karda su Adije suce ba'ayi ba kinsan su da son harka sosai."
"To shikenan hakan ma yayi Besty,bari na shiga wanka sannan na tafi gida nasan har iyayen sun zo yanzun ko ya kika gani."!?
"To shiga,bari na dauko mana abinci sai muci kafin su tafin."
"Ok."




Shiryawa Alhaji Bala yayi ya kama hanyar gidan su Zainaba daman ya gaya ma Dadyn Zainaba yau zai shigo ,duk anshirya mashi tarba da mutunci,dan Dady yaji dadi sosai da yaji Kamal an kanin Alhaji Bala hakan yayi mai dadi sosai,bayan sun gama shirya komai suka jira isowar shi.
Tunda ya shigo yake murmushi dan sun dan Jima basu hadu ba ,huging din juna suka yi sannan Dady yace."Sannu da zuwa abokina ya hanya."!?
Cikin murmushi da jindadi Alhaji Bala yace."lafiya lau Abokina ,Fatan na samaiku cikin koshin lafiya."
"Alhamdullilah wallahi,muna lafiya kaima ya kabaro gida."!?
"Lafiya lau Alhamdullilah."
Nan suka shiga part din baki inda aka fara tule mashi abinci kala kala ,tun yana mamaki har yazo da ya daina,dan abun ma har mamaki yake bashi kallar wannan tarba haka sai kace wani bako?
Bayan duk angama Jere mashi abinci ,akazo aka zuba mashi nan ya zauna yaci,ji yayi da kunya yace ya koshi,duk abun abinci nan dan shi daya akayi shi ai babu batun cewa ya koshi,haka yaci ba laifi yasa ruwa da lemo,sannan su Annas suka zo suka gaidashi,bayan sun gama gaisheshi Dady ya shigo suka fara maganar abunda ya kawo su,sunyi magana ta fahimta sannan aka tsada ranar auren Kamal da Zainaba nan da wata Kamar yanda aka tsada na Usman kuma rana daya za'ayi da na Muhisin shima.
Sun kara gaisawa sannan yace shiko ya wuce gida sai kuma sun sake haduwa,daga gidan su Zainaba Alhaji Bala gidan su Kamal ya wuce.


Bayan ya dawo daga wurin aiki gida ya wuto,sai da ya fara yin wanka sannan ya wuce apartment din Momy zaune ya tadda ta tana kallo hankalinta kwance,duk da taso ta dan shiga cikin damuwa da Usman yace mata zaiyi aure,su Husna suka bata hakuri gami da kwantar mata da hankali,shiyasa ta sauko dan ko da ko abinci kasa ci tayi sai da suka hada da lailashi gami da ban baki sannan suka shawo kanta.

(=��=��=��Niko nace baki shiga tashin hankali ba Momy tunda baki san aika aikar da Kamal yake kullawa ba,amman fa Fans ina tausayin Zainaba sosai fa=�-�).

Zaunawa yayi kusa da ita yace."Momyna sannu da hutu.".....kallon shi tayi gami da yin murmushi tana shafar kanshi tace."yauwa yaron albarka ya aikin."!?
"Aiki Alhamdullilah Momy,Yaya Usman bai dawo ba kenan."!?
Hmmmm!!!"taya zai dawo bayan yana wajen Wanda na haifamawa?tun yanzun ya fara fifitata akanmu ina da yayi auren."!?
"Momy please wallahi babu dadi idan kina irin kallar wannan maganar,nasan wani abune mai mahimmaci ya hana Yaya Usman dawowa da wuri fa Momy."
Hmmmm!"kamal kenan bakajin abunda nike ji shiyasa zakace haka,kuma kai yarone shiyasa bakasan komai ba,mu zuba ido ai muna jiran dawowarshi tunda wani abu ya tsadashi."
"Yauwa sweet Momy haka nike son naji kince ai."
Kallonshi tayi sannan tace."ai kaji nace Kamal ,maza tashi kaje kaci abinci karka tsaya jiran gawon Shanu."
"Ok Momy."
Nan Kamal ya tashi yaje ya zuba abinci yana ci yana kallon Momy dan yana tunanin yanda zasu kwashe da Momy idan taji ansa mashi biki yau,dan Zainaba tayi mashi text tace Baba Bala yazo harma ya tafi.
*Niko nace Kamal baka san gidan ku yayi ma tsinke ba=��.*
Yana cikin cin abinci Usman ya shigo da alamu daga part dinsu yake dan har kaya ya chanza gaida Momy yayi sannan ya wuce dining shima ya zuba abinci ya fara ci suna cikin cin abinci suka ji sallamar Baba Bala...



*>�� SDEENDTM DATA SERVICES>��*
*MTN* . *Airtel*
1GB = � 300. 1GB = � 300
2GB = � 600. 2GB = � 600
3GB = � 900. 3GB = � 900
4GB = � 1200. 4GB = � 1200
5GB = � 1500. 5GB = � 1500

*GLO* . *9MOBILE*
1GB = � 350. 500Mb � 500
2GB = � 700. 1.5GB � 1100
3GB = � 1050. 2GB � 1600
4GB = � 1400. 3GB � 2000
5GB = � 1750. 4GB � 2500

*VALIDITY: 30DAYS/1MONTH*
For cable subscription or sell recharge card
Call this number or whatsapp
=�G�<���=�G�<���=�G�<���=�G�<���=�G�<���
*>؀�08066268951*


*Muje zuwa..=ؤ�*


*Yar'Mutan kankia cec'�*
*�&�NIDA UWAR MIJINA�&�*

_By_

*'Yar mutan kankia c'�*


*MANAZARTA WRITERS ASSOC*


https://chat.whatsapp.com/KBHTLLgPYd6Ir7V3PXpBGJ

_It's 500 via account number 0777512438 jamila Abubakar Bello access bank, shidar biya via 08160508316_


<ؓ�<���1�� 1�� �%�1�� 2��



Waigowa Kamal yayi yaga Alhaji Bala yana shigowa, kasa hadiye abincin da ke bakin shi yayi, dan duka jikinshi rawa yake dan bai yi tunanin zuwan Baban nashi ba, kallonshi Alhaji Bala yayi ya gane yanayin da ya shiga, amman ya zaiye baida zaSi dole ya zo ya gaya ma mahaifinyarshi bikin nashi.
Kallon Alhaji Bala, Hajiya Saude tayi tana dariya, dan taji dadin zuwan yayan mijin nata, cewa tayi."lalai marhaban sannu da zuwa Yaya Bala."
Kallonta yayi shima yana murmurshi yace."yauwa Hajiya Saude, ya gida? Ya iyalin."!?
Cewa tayi."duk suna lafiya Alhmdullh, ya ka baro su Yaya."!?
"Duk suna lafiya."yace yana samun waje ya zauna, kallonsu yayi yace duk su tashi su basu waje zai yi magana da mahaifinyarsu, haka suka tashi suka fita, shiko Kamal ji yake kamar ya kurma ihu, dan yasan yau mai rabashi da Momy sai Allah.

Bayan sun tafi, su Husna suka kawo mashi ruwa da lemu, sannan suka wuce room din su, suka zaune suka cigaba da yin chating.
Sai da yasha lemun da ruwa ya kalli Momy yace."mu sake gaisawa fatan dai komai lafiya lau dai ko."!?
Murmurshi Momy tayi, dan tana jin dadin yanda dagin mijinta suke nuna kulawarsu garesu, hakan yana Webemata kewar rashin mijinta da tayi, cewa tayi."Alhmdullh komai lafiya lau, Yaya Bala."

"Masha Allah."

Alhaji Bala yace, ya kusan minti uku, sannan yace."abunda ke tafe dani ba komai ba ne ila na gaya maki sa bikin yaran nan."
Kallonta yake, dan ya lura da chanzawarta lokaci guda da ya ambaci aure, bai damu da sauyin da tayi yace."Saude nan da wata biyu insha Allah masu zuwa za'a dauren Auren Usman da Kamal, insha Allah."
Wata irin razana Momy tayi tana kallon Alhaji Bala, girgiza kai ta fara yi sannan tace."Yaya Bala, Usman dai ko? Ka manta kace Kamal."
Murmurshi yayi irin nasu na manya, wanda babu wasa a cikin shi yace."tabbas Saude su duka biyu, Kamal da Usman, Saude kiji tsoran Allah maiyasa kike san shiga hakin yaranki."!?
Kallonshi kawai Momy take dan ko ta kasa yin magana, ita abun baki daya ya daure mata kai, shi Kamal yace yana son aure ko kuma shi Bala ya ga dacewar haka ya nema mashi aure da kanshi?
Cigaba da cewa yayi."Saude baki gudun Ya janyo mana abun kunya? Har yaro ya bude biki yace maki aure yake so, amman ki dage da cewa bai isa aure ba, anya kin dauko hanya mai bulewa? Sannan kuma shi Kamal shekararsa talatin harda biyar a sama, idan baiyi aure ba yanzun yaushe kike so yayi Saude."!?
Numfasawa tayi, sannan ta fara magana."Yaya Bala ni ba aurene bansan Kamal yayi, Aa nidai Allah yasani bansan azo a aurar maka yaro a shiga tsakaninka da yaronka, nidai kayi man afuwa amman gsky dan yanzun ban shirya aurar da Kamal ba, sai nan gaba."
Cikin Fushi yace.

"da yake ke kikeyin iko dashi ba, dakata kiji Saude auren Kamal yana nan babu fashi, dan wannan ba hujja bace ta kwarai, dan haka ki fara shirin aurar da yara biyu, niko na gama magana, kinga tafiya ta."
Haka Alhaji Bala ya tafi ranshi Saci, dan ya lura Momy bata ciki hankalinta ma.



Tunda Kamal ya bar gida, bai wuce ko ina ba sai gidan su Zainaba, bayan yaje suka gaisa da maigadi, sannan ya wuce cikin gida, da Muhisin ya fara gaisawa sannan ya wuce garden yana jiran isowar Zainaba.
Tunda Kamal yace ma Zainaba yana hanya ta fara shiryawa, sannan ta kira Sa'adatu tace tazo Kamal yazo sai suyi maganar yanda bikin zai kasance.
Bayan ta gama shiryawa sannan ta fito wajen masoyin nata, tana isa ta ajiye juices, zama tayi tana wasa da yatsan hannunta sannan tace."sannu da zuwa one love, kazo lafiya."!?
Murmurshi yayi, dan ganinta da yayi ya sashi ya dawo cikin natsuwarshi, kallonta yayi sosai yana tausayin zaman da zatayi da Momynshi, amman ya daukarma kanshi duk tsanani duk wahala ba zai rabu da Zainaba ba, ce mata yayi."Yauwa one love, fatan kina lafiya."!?
ShagwaSemashi fuska tayi sannan tace."lafiya lafiya dai."
Mutuwar zaune Kamal yayi, dan shagwaSar da Zainaba tayi mashi ta tafi da imaninshi, cewa yayi."one love, maike damunki."!?
Cewa tayi." bakai bane."
Gyara zama yayi yace."nasan nayi laifi, kwana biyu ban shigo ba, ayiman afuwa yanayin aiki ne one love."
Tashi tayi ta fara zuba mashi juice sai da ta mika mashi tace."Allah ya taimaka."
Ansa yayi yace."Amin one love."
Cigaba da soyayyarsu suke sai ga Sa'adatu ta shigo, zama tayi suka gaisa, sannan suka fara maganar yanda komai zai kasance, shi Kamal baisan ayi progrm da yawa daga kamu sai wa'azi kawai zasuyi, bayan sun gama ya tashi ya wuce gida, dan yaga mangariba ta gaba to.



Driving yake yana tunanin yanda zasu kaya da Momy, dan har ji yake gabanshi na faduwa, innalillahi kawai yake cikin zuciyarshi, dan har ya rasa yanda zaiyi.
Bayan ya shigo gida massallaci ya fara shiga suka yi sallah sannan ya wuto, sai da ya shiga apartment dinshi yayi wanka, sannan ya taho apartment din Momy.
Sallama yayi ya shiga, kallon shi Momy tayi ta kauda kai gefe, wajen ta yaje yace.


"Momy lafiya?mai ya faru na ganki haka."!?


Wanka mashi mari Momy tayi, sannan ta sake maya mashi wani, sai da tayi mashi mari hudu zatayi na biyar din Usma ya rike hannunta yana bata hakuri.
Cikin fushi gami da Sacin rai tace."Wallahi Kamal ka bani kunya ka bani mamaki, har ni mahaifiyarka zaka yaudara, ka munafintata kana neman aure baka gaya man ba, sai da aka tsada ranar bikin ko."!?
Cewa yayi."Momy wallahi... "Yi man shiru Kamal, ai sakaiyar da zaka man kenan ko? Hallacin da na cancanci da kayi man ai ko? Nagode na yarda baka daukeni a matsayin mahaifiya ba, dan haka kaje Allah.... "Momy dan Allah karda kiyi man Allah ya isa, kiyi man addu'a Allah yasa ma auren albarka Momy, Momy Wallahi dole tasa nayi haka kiyi man uzuri Momy."


Kallonshi Momy tayi hawayen bakin ciki na sintiri bisa kumatunta tace..."Uzuri! Uzuri fa kace Kamal? To tsaya kaji zan barka kayi aure amman da sharadi, kaga na farko baka zama ko wane gida sai nan gida a apartment din ka, na biyu kuma dole idan ta dafa abinci sai ta kawo man shi nima naci abunda kukeci komaiye, na uku kuma komai zakayi mata nima sai kayi man, na hudu kuma ban yarda ka dunga yin shawara da ita ba, komai zaka yi to ni uwarka zaka zo ka tambaya ba ita ba, tunda ni na haifeka naci kashinka da fitsarinka."
Kallonta yake, dan condition dinta sunyi mashi yawa, saboda baiyi niyar zama da Momy gida daya ba, hango rayuwar da zasuyi shida Zainaba a gidansu da Momy, cewa yayi."To Momy duk na yarda."

Cewa yayi."Momy dan Allah ki yafeman."
Kallonshi tayi tace."wallahi Kamal idan baka bani waje ba, Allah kaWa ya san abunda zanyi maka walllahi ko Kamal."
Rike kafarta yayi yace."Momy ki rufaman asiri, dan Allah Momy.. "Zaka tashi ka ban waje ko sai

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment