Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya karasa kusa da Aysher durkusawa yayi a gabanta tare da cewa"My baby kunyarki tayi yawa a fulanin kekam dabance pls yau kadai ki kalleni kice kina sona idan ba hakaba zan shiga wani hali"

Kara sunkuyar da kanta tayi takasa dago kanta takalleshi tana wasa da yatsun hanunta.

Ahmad yakalleta yana murmushi gami da fadin " Aysher dan Allah karki gujeni duk wuya duk tsanani pls be with me zan zamo jarumi indai akan soyayyarki ne zan iya komai koda ace shadi za'ayi bisa al'adar garinku zanyadda inasonki ne tsakani da Allah,


Allah ya doramin sonki kuma jikina yana bani kece matata shisa nazo garinnan da niyyar karatu Kinsan ance matar mutum kabarinsa Ina sonki ina matukar kaunarki Fatana Allah ya nunamin ranar da zanganki a dakina amatsayin matata uwar 'ya'yana.


Hakan daya furta yasa Aysher rufe fuskanta da tafukan hannayenta.


Yakara da cewa"Aysher kece muradin raina abin fahari na kinzamo fitila mai haske "yan mata na nad'aki sarauniyyar birnin zuciyata I love u so much my wife"

Dariya Aysher tafara harda kyakyatawa kafin tace"Ya labarin gurinsu mom dafatan suna lafiya kagaisheta idan kunyi waya pls"

Dariya Ahmad yayi yace"So kike kiyimin wayau bakyaso kifurtamin cewar kina sona ko badamuwa su mom lafiya kalau mun kwana biyu bamuyi waya ba cos i switch off all my phones but nakunna yanz......


Wayarsa ce tafata ringin yaduba sunan mai kiran my Bro yagani a rubuce dan haka yadauka da sauri gaisheshi saddiq yafarayi kafin yace"Yaya meyasa ka kashe wayarka tun last 3 days toh akwai problem dad yagano komai cewar kaine kayi wakar nan so yanzu haka yatafi abj jiya zaka iya ganinsa ako da yaushe ma'ana yau ko gobe ko jibi a garin yola yarantse kabar sake karatu a garin yola difffff wayar saddiq ta dauke Ahmad yakira yaji it's not reachable dan haka dole ya hakura ya kalli Aysher tare da mikewa yana fadin Swthrt barin tafi zandawo gobe in sha Allah tunda munsamu babanmu yadawo nasan bamu da matsala zanzo gobe da daddare.


Aysher tace Allah yakaimu kahuta gajiya kacema Yaya mudansir sai da safe.......
[10/14, 7:11 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Lokacin da aka aika dasu Ahmad suka aika ayi masu sallama da aysher baffa Usman yana zaune a tsakar gidan wanda ya sauka garin yola da safe.


Abin yabashi mamaki dayaji yadikko tana fadin aje ace musu anyima Aysher mijin aure.

Dakatar da dan aiken yayi ya dubeta tare da cewa "yau she nace miki nayi mata miji bayan asalima bansan wani da yake zuwa gurintaba dan bata fita zance sai yau amman kina cewa kinyi mata miji"

Cikin dakewa yadikko tace"Nayi mata mana mallam lokacin kana lagos kuma kaga yau kadawo bamu samu wani dogon zamaba sosai nidakai shiyasa banyi maka bayani ba.

Kai Baffa Usman ya girgiza tare da cewa mata!Mata!!mata!!!
Sai abarku kunada wuyar sha'ani Aysher yakalla yace ke kinsan anyi miki mijine kuma kina sonsa...girgiza kai tayi alamar bata sani ba dan Haka baffa Usman yamike yasakai yafita shine yasamu su Ahmad a waje.


Cikin gidan kuwa Rankwashin Aysher yadikko tadinga yi tare da cewa'Aradun Allah dole saikin auri dan Abj ko kinki ko kinso bari shima uban naki zaishigo ya sameni ne"

Toh shigowar baffa ne yasa tadakata da bala'in da take surfawa Aysher...

Wannan kenen


***********


Daga Abj kai tsaye Alh.Aliyu da Alh.Labaran yola suka yima tsinke bayan sun kama hotel gidan Alh.Lawan suka yima tsinke bayan gaigaisawar da sukayi tare da tambayar bayan rabuwa Anan Alh.lawan yake bama Alh.Aliyu labarin karar Ahmad da uwar yar aikinsu takawo cewar a rabashi da yarta tundaga wannan rana yau kwana kusan sati daya ban kara ganin Ahmad a gidan nan ba nayi binciken sirri a makarantarsu an tabbatarmin baya attending lectures ma gaba daya amman ana ganinsa a cikin Compound na Hostels din school din so may be yana tare da wani abokinsa ne dan haka nasa kudi mai tsoka akan a ganomin dakin dayake kwana kuma waye wannan abokin nasa dan haka kayi hakuri mujira wayar sa daga yau zuwa gobe.

Alh.Aliyu yayi na'am tare da godiya gami da bawa Alh.lawan hakuri tare da cewar yasamo kauyen da zai turashi a can saudiyya inda kwata kwata babu wani dan Nigeria sosaima a gurin ballantana yasamu abokan lalacewa......




MAMAN HANAN
[10/15, 12:25 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE

Page 25-26



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA




Hankalin Ahmad yatashi sosai dajin maganar zuwan mahaifinsa babban damuwarsa ayanzu shine mahaifinsa bazai ta6a sauraransa har yayi masa uzurin zuwa gidansu Asher dan neman masa aurenta ba.


Kana kallonsa kasan yana cikin tashin Hankali

Zama yayi a gefen katifar dake dakin Mudansir yadafe kansa da Hannunsa (Ciwon kansa yatashi) cikin karfin hali yadago idanuwansa da sukayi jawur yakalli Mudansir yace"Mudansir abokina nasan kai abokine nagari dan Allah ga amanar Aysher tunda kana garin nan kasamin ido akanta karka bari a cutarmin ita karka yadda a aurar da ita da wani idan bani ba zan iya mutuwa idan narasa Aysher inasonda dayawa dan Allah nawan.

Mudansir cikin tausayawa yakalli Ahmad _Hakika yana cikin wani hali cos Ahmad yana karfin hali da jarumta da wuya kagane abinda yake damunsa but akan son Aysher gashi yau Ahmad yakaraya yazamo rago yana neman yafara ZUBAR HAWAYE_

Mudansir yadafashi cikin sanyin murya yafara magana da cewa"Ka kwantar da hankalinka Nawan in sha Allahu Aysher matarka ce baka da wata mata sai ita da yaddar Allah nasan ma Abbanku bazai dauki komai da zafi ba karka damu kaji"..

Mudansir yafada masa haka da ya kara masa kwarin gwiwa.

But Ahmad cikin karaya yace"Nasan halin Abba I know him very well bazai ta6a yadda yabar ni ba zai dauki mataki akaina ne dan yasha fadamin abokina kai kanka kasan banajin magana amman wallahi a Da ne yanzu na nutsu narage wasu abubuwan ni babban tashin hankalina ma za'a nesantani da aysher"


Awannan daren Bacci kauracema idanun Ahmad yayi saida Mudansir yayi masa dabarar bashi lemo wanda yayi mixed da codin kwalba daya batare da sanin Ahmad ba ya kwankwade aikuwa mintuna kadan bacci yayi awon gaba dashi.

**********


Hello!

Yauwa Alh. Kanajina mungano Dakin dayake jiya da daddare anan hostel din Apti ne dakin wani abokinsa wanda bincike yanuna mana tare sukazo daga kano shima abokin dan kano ne Hostel Room number sa 15 sunan abokin nasa Mudansir.

Toh madallah nagode xakuji alert yanzu nagode. Cikin doki Alh.Lawan ya labar tawa su Alh.Aliyu komai nan take suka mike daniyyar tafiya dan yamma tayi kuma suna nesa da School din.

Waya Alh.Aliyu yajawo ya fara kira bugu daya aka dauka.

Hello!
"Abba ina wuni ya yola dasu baffa"

"Duk lfy kalau saddiq kaje airport gurin agent dinnan kaga komai yana zuwa da sauki kace masa anga yaron yashirya mana komai gobe morining flight nakeso mubi zuwa Saudiyya dan ko gida bazamuzo ba saina dawo"..

Toh Abba barin karasa daman ina kusa airport sadiq ya katse wayar.

Jikinsa har rawa yakeyi wajen kiran dan uwansa *Allah sarki naka sai naka*



Ahmad yana zaune yagama shirya kayansa yana jiran abinda zai faru nan gaba yamika komai ga Rabbi.

Yaji wayarsa tana ringing *My bro* yagani a rubuce dan haka yayi saurin dauka.

Hello Yaya ina wuni kayi sauri ba time sosai kashirya komai naka gasu abba sun gano inda kake zasuzo......

Ahmad cikin sauri batare daya saurari karashen bayanin kanin nasaba ya katse wayar cikin sauri yakalli mudansir yace" Nawan bawani time sosai gasu Abba nan zuwa hostel pls ka adanamin wadannan abinda nabaka idan na bukace su saddiq zaizo yakarba and pls karka kawosu gidansu Aysher duk abinda zasuyi kujirani anan barinje nayi mata sallama dan Allah karka kawosu karikesu banaso atayar mata da hankali sai nadawo".


Yana gama fadin haka baijira cewar mudansir ba yasakai da gudu yafice daga dakin.


Ta boyayyen kofar fita daga Hostels din yafice yatari mashin sai Anguwae Damare.

Yana zuwa a gurguje yasamu yaro yaturashi yayi masa sallama da Aysher.


Yadawo yace gatanan zuwa
Aysher tafito fuskanta da alamar annuri amman tana kallon gogan nata tasan cewar yana cikin tashin hankali gaisheshi tafarayi ya amsa tare da tambayar yadda take tace tana lfy lau.

Cikin jarumtaka Ahmad bayaso Aysher tanago weekness dinsa yafara magana da cewa" My love a gurguje nazo ne nayi miki sallama babana yazo xamu tafi tayiwu nadawo nan kusa may be kuma sai an kwana biyu so pls Aysher ta dan Allah ki tsaremin kanki karki fada tarkon masu yaudara masu jan hankalin 'yan mata kituna kullum aranki cewa dukkan yanwa tana tare da sauki
[10/15, 1:23 PM] Zeetty: [10/15, 12:45 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE

Page 25-26



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA




Hankalin Ahmad yatashi sosai dajin maganar zuwan mahaifinsa babban damuwarsa ayanzu shine mahaifinsa bazai ta6a sauraransa har yayi masa uzurin zuwa gidansu Asher dan neman masa aurenta ba.


Kana kallonsa kasan yana cikin tashin Hankali

Zama yayi a gefen katifar dake dakin Mudansir yadafe kansa da Hannunsa (Ciwon kansa yatashi) cikin karfin hali yadago idanuwansa da sukayi jawur yakalli Mudansir yace"Mudansir abokina nasan kai abokine nagari dan Allah ga amanar Aysher tunda kana garin nan kasamin ido akanta karka bari a cutarmin ita karka yadda a aurar da ita da wani idan bani ba zan iya mutuwa idan narasa Aysher inasonda dayawa dan Allah nawan.

Mudansir cikin tausayawa yakalli Ahmad _Hakika yana cikin wani hali cos Ahmad yana karfin hali da jarumta da wuya kagane abinda yake damunsa but akan son Aysher gashi yau Ahmad yakaraya yazamo rago yana neman yafara ZUBAR HAWAYE_

Mudansir yadafashi cikin sanyin murya yafara magana da cewa"Ka kwantar da hankalinka Nawan in sha Allahu Aysher matarka ce baka da wata mata sai ita da yaddar Allah nasan ma Abbanku bazai dauki komai da zafi ba karka damu kaji"..

Mudansir yafada masa haka da ya kara masa kwarin gwiwa.

But Ahmad cikin karaya yace"Nasan halin Abba I know him very well bazai ta6a yadda yabar ni ba zai dauki mataki akaina ne dan yasha fadamin abokina kai kanka kasan banajin magana amman wallahi a Da ne yanzu na nutsu narage wasu abubuwan ni babban tashin hankalina ma za'a nesantani da aysher"


Awannan daren Bacci kauracema idanun Ahmad yayi saida Mudansir yayi masa dabarar bashi lemo wanda yayi mixed da codin kwalba daya batare da sanin Ahmad ba ya kwankwade aikuwa mintuna kadan bacci yayi awon gaba dashi.

**********


Hello!

Yauwa Alh. Kanajina mungano Dakin dayake jiya da daddare anan hostel din Apti ne dakin wani abokinsa wanda bincike yanuna mana tare sukazo daga kano shima abokin dan kano ne Hostel Room number sa 15 sunan abokin nasa Mudansir.

Toh madallah nagode xakuji alert yanzu nagode. Cikin doki Alh.Lawan ya labar tawa su Alh.Aliyu komai nan take suka mike daniyyar tafiya dan yamma tayi kuma suna nesa da School din.

Waya Alh.Aliyu yajawo ya fara kira bugu daya aka dauka.

Hello!
"Abba ina wuni ya yola dasu baffa"

"Duk lfy kalau saddiq kaje airport gurin agent dinnan kaga komai yana zuwa da sauki kace masa anga yaron yashirya mana komai gobe morining flight nakeso mubi zuwa Saudiyya dan ko gida bazamuzo ba saina dawo"..

Toh Abba barin karasa daman ina kusa airport sadiq ya katse wayar.

Jikinsa har rawa yakeyi wajen kiran dan uwansa *Allah sarki naka sai naka*



Ahmad yana zaune yagama shirya kayansa yana jiran abinda zai faru nan gaba yamika komai ga Rabbi.

Yaji wayarsa tana ringing *My bro* yagani a rubuce dan haka yayi saurin dauka.

Hello Yaya ina wuni kayi sauri ba time sosai kashirya komai naka gasu abba sun gano inda kake zasuzo......

Ahmad cikin sauri batare daya saurari karashen bayanin kanin nasaba ya katse wayar cikin sauri yakalli mudansir yace" Nawan bawani time sosai gasu Abba nan zuwa hostel pls ka adanamin wadannan abinda nabaka idan na bukace su saddiq zaizo yakarba and pls karka kawosu gidansu Aysher duk abinda zasuyi kujirani anan barinje nayi mata sallama dan Allah karka kawosu karikesu banaso atayar mata da hankali sai nadawo".


Yana gama fadin haka baijira cewar mudansir ba yasakai da gudu yafice daga dakin.


Ta boyayyen kofar fita daga Hostels din yafice yatari mashin sai Anguwae Damare.

Yana zuwa a gurguje yasamu yaro yaturashi yayi masa sallama da Aysher.


Yadawo yace gatanan zuwa
Aysher tafito fuskanta da alamar annuri amman tana kallon gogan nata tasan cewar yana cikin tashin hankali gaisheshi tafarayi ya amsa tare da tambayar yadda take tace tana lfy lau.

Cikin jarumtaka Ahmad bayaso Aysher tanago weekness dinsa yafara magana da cewa" My love a gurguje nazo ne nayi miki sallama babana yazo xamu tafi tayiwu nadawo nan kusa may be kuma sai an kwana biyu so pls Aysher ta dan Allah ki tsaremin kanki karki fada tarkon masu yaudara masu jan hankalin 'yan mata kituna kullum aranki cewa dukkan yalwa tana tare da kunci,
Dukkam wahala yana tare da dadi Aysher hakika da nasan zan hadi dake a garin nan da ban aikata laifin da zaizamo kaddarar da zai nisantani dake ba danabi shawarar Mudansir yariko hannuwan Aysher cikin nasa yana ZUBAR HAWAYE yana fadin kirikemin amanar kanki duk wuya duk tsanani karki bari a rabani dake zan iya hakura da aure idan narasaki ko ciwon sonki yazamo sanadiyyar barina duniya, ga Abokina mudansir nayadda dashi kidaukeshi matsayin yayanki duk wata matsalarki kinemeshi ga wayata guda daya ki rike zan kiraki a duk inda Allah yakaini"

Aysher cikin nata ZUBAR HAWAYEN tace karike wayarka kar anemeka a cikinta wai meye kayi ne haka kuma ina xaka tafi?

Yace"Ba ishashshiyar lokaci aysher but kitambayi Mudansir zaifada miki komai xoben hanunsa yaciro yasaka mata tare da cewa ga wannan yazamo madubin da zai dinga hasko miki ni a idanunki aysher waya kuma karki damu bawanda zaikira cikinsa sai ni I love u Aysher stay bless.
Yajuya da sauri dan bayaso Aysher tagano Karayarsa da kukan daya zo masa.


Yadanyi mata nisa Tadaga muryanta da karfi tace"I love u too Ahmad bazan manta dakaiba in sha Allahu banda wani miji sai kai"


Dasauri Ahmad ya juyo fuskarsa cikin farin ciki _Hakika Aysher ta wanke masa zuciyarsa yau tafurta tana sonshi da bakinta wow_

Murmushi mai tsayawa masoyi arai suka yima junansu Ahmad ya daga mata hannu a dai-dai lokacin mai mashin yazo wucewa Ahmad yatare yahau baisake juyowa ba amman kuka yake kukan zuciya...kukan rabuwa da masoyi.
[10/15, 1:23 PM] Zeetty: *Bayan ke azuci banda kowa uwargidata daga ke na rufe*

*Bayankai azuci banda kowa miji na aure maisani farin ciki*

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Suna tsaye sunyi cirko-cirko cikin Hostel din anyi-anyi da mudansir yafadi inda Ahmad yake yaki yace baisan inda yajeba amman ga kayansa ya ajiye yanzu zai dawo.

Cikin fushi Alh.Aliyu yakalli mudansir yace"Wato saboda rashin jin magana har hada baki kukayi kukazo state daya karatu saboda baku da wanda zaifada muku kuji ko? Kai meyahanaka kazamo mawakin meyasa?

Mudansir yace "Wallahi Abba nima daman Already Babana yasamomin wannan makarantar sai Ahmad yazomin da tasa maganar cewa shima nan zaizo wallahi banda masaniya kuma ba hada baki mukayi ba,
Maganar waka kuma nahanashi Abba koshi Ahmad din zaka tambaya bansan yaje yayi wakar ba dan nahanashi yaki jine kawai"

Alh.Aliyu gyada kansa yayi alamar gamsuwa kafin yace"Kayi sa'a nasan halinka tun a kano kanada rashinji kaima amman ba kamar Ahmad ba kuma nasan Ahmad yanada taurinkai baka isa hanashi abinda yayi niyya ba....dan haka naji uzurinka yanzu dai bazaka fada mana inda yatafi ba kana cewa zaidawo-zaidawo munfi minti talatin a tsaye a gurin nan kodai hada baki kukayine ma yagudu".

Kai Mudansir ya kada yace"Wallahi Abba zaidawo ba guduwa yayi ba Ahmad fa yafara Nutsuwa.......

Kul karka karasa fadin haka haryanzu dasauranshi nasamo maganin.......

Tsayawar Mashin a kusa da su dakuma Saukowar Ahmad shi ya tsayar da mahaifin Ahmad daga maganar dayakeson karasawa.

Ahmad yakaraso gurinsu yana sosa keya kansa a sunkuye idanuwansa sanye cikin bakin glass yafara gaishe da iyayen nasa.
Alh.Labaran da Alh.Lawan ne kawai suka amsa Alh.Lawan yakara da cewa Kakyauta Ahmad saika gudu ba sallama.

Ayimin hakuri baffa yana magana yana satan kallon mahaifinsa shima mahaifin nasa kallonsa yakeyi *Hakika tsakanin 'Da da mahaifi sai Allah dan wani irin soyayyar Ahmad ne yatasowa mahaifinsa hakika Allah ya dora masa son dan nasa na fari kawai bayason nunawa ne cikin iyalansa saboda gudun fitina amman Ahmad bayan rashin jinsa yanada zuciya mai kyau*


Mota suka bude Ahmad yana gaba shida Alh.lawan hannu yadagowa Mudansir cikin magana mai karfi yace karka manta ka kulamin a jiyar dana baka wannan sakon kuma za'azo akarban min idan nasamu sararin hakan.

Hawaye Mudansir yake gogewa hakika sabo turken wawa inasonka nawan Allah ya tsaremin kai aduk inda kake.



***********

Kai tsaye Airport sukaje jirgin da zaitafi kano suka shiga.

Suna sauka a airport na kano suka samu saddiq da agent dauke da passport din Ahmad dana Alh.Aliyu jirgi saura 15minute yatashi dan haka agurguje Alh.Aliyu da Alh.Labaran sukayi sallama.

Ahmad a gurguje yace"Saddiq akwai sakona gurin Mudan a Yola idan ina bukata zannemeka ka karbomin kuma inaso kaga Agent dinnan sosai dan zaitaimakeni nan gaba"

Baijira cewar Ahmad ba suka shige gurin screening.

Lokaci yana cika suka haye jirgi sai Airport na Sarki Abdul'azeez nidai nace Safe landing Ahmad Allah yasa Aysher rabonka ce.

*A SQUARE*



MAMAN HANAN
[10/16, 12:51 PM] Zeetty: [10/16, 12:50 PM] Zeetty: [10/16, 12:08 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE

Page 27-28


Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA


*ABOKAN ZAMA, ABOKAN AIKI*


_ZAMANTAKEWAR GURI GUDA GIDA 'DAYA KO WURIN AIKI 'DAYA DOLE TA HA'DA MUTUM DA ABOKAN HUL'DA NAKIRKI DA MARASA KIRKI, MASU GASKIYA DA MARASA GASKIYA_
_'YAR UWATA MUSULMA NASIHATA GAREKI ITACE, IDAN HALIN RAYUWA YASANYA DOLE SAIKIN FITA AIKI KO SANA'A KO CINIKI, KAR KIYI KAWANCE DA MARASA GASKIYA, MASU HA'INCI, FASIKAI, MASU GULMA, MASU DAGAWA, MADU KUSHE, MASU ALFAHARI, MASU RAINA ALHERI IDAN KINYI HAKA BAZAKI SHIGA LOKON DA BAYA BILLEWA BA, RAMI MAI WUYAR HAUREWA, ALLAH YA TSARE_

_LALLAI KINEMI MASU GASKIYA MASU SANIN KIMAR AURE, MASU SANIN DARAJAR MAZAJENSU, MASU SANIN ALHERI DA RIKON AMANA_




Hon.Mahmoud tun bayan dawowarsa daga Abj yasallami Nura saboda kai kararsa da Nura yakai gurin shugaban jam'iyyarsu cewar zai auri yarinya karama kuma cutarta yakeson yayi.

Shugaban party yayi-yayi da Nura yafadi dalilinsa maikarfi wanda zaikawo cikas a auren Mahmoud da Aysher but Nura yakasa fada, bazai iya tonawa ubangidansa asiriba wannan sirri ne amman duk yadda zaiyi bazai bari a cutar da Aysher ba.

Cikin masifa Hon.Mahmoud yake fadin"Ni zaka ciwa mutumci Nura kakai karana har wajen shugaban party anya Nura ba hada baki kukayi da 'yan adawa suka siyeka ba toh narantse da tsarkin mulkin Allah yau basai gobe ba kadaina cin abinci a karkashina kuma Aysher da yaddar mai duka saina aureta naga yadda zakayi bantaba sanin kai makiyina bane sai yau so leave my office now bana fatan nasake ganinka a rayuwata zan iya rabuwa da kowa akan Aysher albashinka na wannan watan zakaji alert"

No kabarshi kawai ai Alhamdulillahi natara nawa na halak ba yaki haram yaki halak ba so nayafe maka Allah yaganar dakai Allah ya kubutar da wannan yarinya daga sharrinka nabarka lfy.
Nura yana gama fadin haka yabar office din.

Cikin daga murya Hon. Mahmoud yace zaka gani nura dani kake magana zansa a kawarmin dakai daga doron duniya tunda da alamar haryanzu baka ladafta ba.


Nura yana zuwa gida yacema matarsa ta shirya tunda ana hutun school gobe su wuce garinsu zari'a _dan yasan halin Hon.mahmoud bazai barshi haka ba_

Waya yadauka yakira hukumar yansanda yasanar musu yana bukatar police mutum biyu wanda zasu kwana gidansa.

πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’

Jirginsu yana landing fasinja aka sassauko drop din mota Alh.Aliyu yadauka haryanzu baicema Ahmad kala ba yasanarma driver inda zaikaisu cikin harshen larabci.


Shidai Ahmad rarraba idanuwa yake dan ganin kauyukan larabawa da aketa wucewa.

*سوف Ψ’Ψͺي Ψ₯Ω„Ω‰ عسير*

*WELL COME TO ASIR*

Haka aka rubuta jikin wani Singboard

Ahmad yakaranta lokaci guda kirjinsa yabuga dan hango gidajen dake kauyen sunata wucesu a mota kafin su karasa gidan abokin mahaifinsa
[10/16, 12:51 PM] Zeetty: Sun kauka A asir Lafiya Ahmad dai hankalinsa a tashe dan ganin irin kauyen da babansa yakawoshi da sunan Horo wannan dama a gida yabarsa Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un hakika ganin yadda garin yake yasa Ahmad fiddarai da auren Aysher da sauri yakarasa gurin mahaifinsa suna tare da mutumin da yadankawa amanar Ahmad a hanunsa yasan mutumin sosai suna haduwa akai-akai idan Alh.Aliyu yazo aikin hajj ko Umara dole ne saiyazo asir sun hadu da *Muhammad fallata* (Sunan mutumin kenan wato fallata yana nufin fulani)

Garin Asir larabawane masu kiwon shanu da kuma noma ana kawo musu renon yara wato matan garin asir din kenan.

Dasauri Ahmad yakarasa gurinsu bayan yagama nazarin kauyen da gidajen lakan dayake jere a garin durkusawa yayi cikin taushin murya yace"Abba kayafemin dan Allah nayadda kamin komai kowane irin horo ne Abba akan kabarni a wannan garin basajin yarena Abba nima banajin nasu rayuwata zata wahala Abba gwara kamaidani gida ko gidan yari kakaini harna tsawon yadda kakeso akan barina a wannan kauyen"...


Wani Kallo mahaifinsa yabishi dashi kafin yace"Nariga nagama yanke hukunci Ahmad bakaji idan har zamanka anan garin baisaka shiryuwaba Narantse da Allah nafidda rai da shiryuwanka zan mikawa Allah komai nasaka maka ido amman dole kazauna anan na tsawon shekara daya kafin nazo na waiwayeka naga halin dakake ciki idan naga alamar ka ladafta to falillahilhamdu zamu koma tare idan kuma naga dasaura toh zan kara baka wata shekarar."

Yakalli Fallata cikin harshen larabci yace"Gashinan abokina karka tausaya masa karka dubi tsakaninmu kadinga sashi yana zuwa kiwo ko noma sosai tunda yaki karatun ace shine babba yaki nutsuwa haryanzu"


Cikin tashin hankali Ahmad yace"Abba Naji zanyi maka biyyaya insha Allahu zanzamo 'Da nagari zakayi Alfahari dani for the first time arayuwarka but Abba Inason Aysher Abba kataimaka kajemin neman aurenta kafin nadawo karsu bada ita dan Allah Abba mudansir zaiyi excorting dinka gidansu dan Allah Abba I love her very much wallahi idan na rasata bazan iya auren wata ba Abba"

Ahmad yakarasa fada yana ZUBAR HAWAYE


_Hakika Alh.Aliyu yatausayama dan nasa abinda zaisaka Ahmad kuka ba karamin abu bane dan Ahmad jarumine na gaske dawuya kagane yana cikin damuwa but akan Soyayyar Aysher yadawo mace mai rauni dole zanje nagana da Mahaifin yarinyar nan tabbas Ahmad yafara shiryuwa may be ma harda taimakon Aysher dan haka zanje na nemo masa aurenta_

Alh.Aliyu yayi murmushi for the first time tun tasowarsu daga Nigeria yakalli dan nasa yace"Ahmad zanje maka neman auren Aysher In Allah yaso amman sai naga yanayinka kafin ayi auren ina nufin sai bayan shekara daya"

Kai Ahmad ya girgiza tare da cewa nayadda Abba Nagode Allah saka da Alheri zan baka mamaki Abba.

Sallama Alh.Aliyu yayi da Fallata yakarasa gurin mai taxi daya dauko drop dan aranar zai koma cikin mecca dan jirginsu zuwa Nigeria zai tashi da asuba ne.



Ya bude bayan motar zaishiga dasauri Ahmad yakarasa gurin Mahaifin nasa ya tsugunna tare da ajiye kafafunsa a kasa kamo hanun mahaifin nasa yayi yana Mai ZUBAR HAWAYE tare da fadin"Abban kayafeni dan Allah duk laifin danayi maka a baya da bacin ran dana saka ka a ciki kayafemin In sha Allahu saina zamo abin fahari a gareka zan baka mamaki zan zamo fiye da yadda kakeso nadawo Abbana I will missed you kacema Umma tayafemin zankirata na roki gafararta Nasan nasaku bakin ciki amman In Allah yaso daga yau yazama tarihi Abbana.


Alh.Aliyu shima ZUBAR HAWAYEN YAKE cikin ransa kuwa fadi yake *dole ne zaisa nabarka Ahmad inasonka fiye da sauran yarana dole ne zaisa nadauki tsawon shekara batare da nasaka a idona ba*

A fili kuwa cewa yayi"Na yafe maka Ahmad ubangiji ya yafe mana kuskurenmu zan turo maka da kudi idan kana bukata amman na bama fallata wasu kudaden masu dama I love u too my son Allah maka Albarka"

Ahmad cikin jin dadi yadinga cewa Amin Amin Abba inada kudi sosai a account dina ma nagode Dad Allah yasaka maka da Aljanna.


Cikin dariya Alh.Aliyu yace wow naji dadi Ahmad lallai kafara hankali kaine zakace bakason kudi kacemin nabarshi Alhamdulillahi Ahmad lallai kafara nutsuwa Allah maka Albarka Allah kara shiryamin kai.

Dakyar shima Alh.Aliyu yatafi yabar 'Dan nasa suna dagama juna hannu.


Fallata dakin da Ahmad zai zauna ya nuna masa daki dayane da toilet a ciki da katifa a kasa.

Addua Ahmad yayi Allah yasa hakane mafi Alheri a gareshi Amman baisan yazaiyi da rayuwa cikin larabawa da basajin hausa ba sai larabci kadan daga cikinsu ne suka iya turanci....

Wannan kenan


MAMAN HANAN
[10/18, 3:40 PM] Zeetty: [10/18, 3:40 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 29-30


Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

*Maman hanan lafiya kuwa yau naga typing din naki ba page kuma da alamar kamar badaga inda yakamata kifara ba kenan*


_Nagode da kirana dakukayi kuka ankarar dani kuskurena hakika maman hanan tana jin dadin yadda kukebin wannan novel din nata nagode ayimin hakuri mistake nayi gurin posting zantafi dauko Hanan daga school ina saurine_




Artabu akayi sosai tsakanin yansandan dake gadin gidan Nura tare da wasu mutane guda biyu wanda suka boye fuskokinsu.


Saida

Please Login or Register in order to submit comment