Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

kasaba gani dan agaban kowa zan iya nunama Aysher soyayya i can't hide it"

Mtswww saikayi kuma wato korata kakeyi bayan kagama yimana 'yar murya da lalllami akan mu nemo maka auren Aysher ko?

Kafin Ahmad yabashi amsa wayar Mudansir yafara ringing Alh.Aliyu ne yace suzo da sauri shida Ahmad yanzu Zeemans Hospital wasu mutane da ba'asan kosu waye ba sun harbi Nura.

Salati Mudansir yafarayi kafin yayima Ahmad bayani suka mike a hanxarce dan tafiya Ahmad yacema Aysher zaishigo da daddare.

Itama Aysher jikinta yayi sanyi tace Allah yakaimu Allah bashi lafiya..... .....




MAMAN HANAN
[10/21, 2:40 PM] Zeetty: [10/21, 12:25 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 45-47



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA

_Up up Members na group din Maryam yahya hakika ina matukar alfahari daku ga takenku nan_
πŸ₯ *Abinda yake raina zani fitar inhuce takaici, soyayya kedamuna zana fad'a bazan 6oye ba*





Hello Doctor anyanka ta tashi asirina ya tonu abinda nake gudu ya kasance hakika Firstlady ta cameron ta cuceni dakuma son zuciyata amman niyanzu babban tashin hankalina kar abinnan ya fashe kowa yaji hakan zai jawomin matsala a takarar kujerata.

Doctor yace" kayi hakuri Honourable nasan dole hankalinka yatashi wallahi saidai in matsala aka samu amman maganin yanada karfi sosai nabama mutane irinsa dayawa.

Tsaki Hon. Mahmoud yayi kafin yakatse wayar falon dakinshi na hotel din ya fito nan yaga abokansa da sukazo daga Abj da Gombe suna zazzaune a falon suna tattauna yadda wannan al'amari yafaru.

Alh. Barde ne ya kalli Hon. Mahmoud yace" shin Honourable daman iyayen yarinyar nan basuyi niyyar baka aurenta bane ko niyyar Tozartaka sukayi ne dan muna zazzaune mukaji ana sanarwan andaura Aure wai da wani Ahmad sa6anin kai kuma ko waliyyanka basusan dalilin fasawar auren ba dan ba'afada musu ba wannan wane irin tozarci ne"

_Cikin zuciyar Hon.Mahmoud wani Ni'ima ne yasaukar masa dan ganin abinda iyayen Aysher sukayi masa na rashin tona masa asiri dan yayi niyyar idan asirinsa yatonu yarasa kujerarsa saiya wulakantasu toh yanzu yayi musu sassauci haka Allah ya rubuta Aysher ba matarsa bace Amman koma meye saiyasa an wulakanta Nura dan kuwa shine yakai Gulmar cewar asakasu suyi gwaji jini dan haka Hukuncin Nura kisa_


Dariyar yake yayi a fili kafin yace"Bakomai Barde kansu suka tozarta mahaifinta yamaida kansa karamin mutum nidai Abinda nakeso daku shine kuyi hakuri kuma ni akayima amman nayafe nagode da karramawarku gareni"


Nan dai sukayi sallama dan anfasa wata dinner tunda ko auren ba'adaura ba a ranar suka juya zuwa garuruwansu.

Bayan Hon.Mahmoud yadawo daga rakiyar abokansa wayarsa tafara ringing alamar anakiransa asanyaye yadauko wayar daga Aljihunsa gabansa yana faduwa OKO yagani dasauri yadanna yakara a kunnensa"Ya akayine oko"?

Maigida ga Nura mungani akan mashin muna binsu abaya batare da saninsu ba amman da'alama tashar mota xaije yahau mota........


Karku barshi oko nasan Nura munafiki nane idan kunada kunama ku dana masa akai yadda bazai moruba"..


Angama maigida.
Suna katse wayar Oko yazaro bindigarsa daman sunzo gurin da babu yawan jama'a kuma shima yanakan mashin dinne dan haka yasaita kan Nura ya harbeshi........ Salati Mai mashin din yaji Nura yanayi kafin yafado daga kan mashin din arikice mai mashin din ya faka dan neman wanda sukayi wannan aika aikar amman ko alama babu dan haka Maimashin yafara ihun neman taimako nan da nan akazo aka saka Nura a mota sai Asibiti.
Awayar Nura police din a aka samu yaga last call dinsa wato Alh.Aliyu dan haka shisuka fara nema yataho Hospital din.


************


Dagudu Aysher takarasa dakinta ta tarar fatima ta dafka uban tagumi riko hannunta Aysher tayi cikin farin ciki tace"Alhamdulillahi kawata hakika nazamo mace mai sa'a kinsa kuwa waye angon nawa"

Fatima ta girgiza kai alamar a'a

Toh bakowa bane face Gwarzon jarumi kuma sadaukin Raina wato Ahmad Aliyu Hameed wani Ihu fatima tayi tare da rungumo kawarta cikin tayata farin ciki tace"Kina abin Allah ko hakika Babu ta inda Allah baya nuna ikonsa yanzu ina yake muje nagaidashi"

Yatafi Asibiti shida yaya Mudansir an harbi Nura.
Salati Fatima tayi tare dayimasa fatan samun lafiya.

Fatima tace"Sai hanzarta tunda kuka yakare muje kiyi wanka yagana tayi miki kwalliya kinga ai yau garanar gyaran da Yagana tayi miki.


Hakane kuwa kawata.
Wanka Aysher tashiga da ruwan turaren da yagana ta hada mata dan batason abinda ke faruwa ba
[10/21, 2:35 PM] Zeetty: A asibiti kuma ashe Bullet din bata shiga kan nura ba gogansa tayi a gefa ta fadi rikicewane yasa nura suma dakuma Inda harsahin ya taba yake fitar da jini.
Likitoci sunyi kokarin shawa matsalar tare da yima Nura Alluran bacci.
Yan sanda sunce zasuci gaba da bincike akan lamarin.
Alh.Aliyu yahanasu Ahmad tafiya sai bayan magriba a lokacin Nura ya farfado harsun gaisa dashi
Dan Haka Alh.Aliyu yace yafasa komawo kano a ranar sai washe gari Alh.Labaran dai yawuce tun bayan daurin aure.


Wajen karfe 7:00pm suka wuce dan barin asibitin Ahmad da Mudansir a cikin daya daga cikin motar Alh.Lawan da Mudansir ya karbo tunda safe yaje airport dan tahowa da Ahmad.

Driving mudansir yakeyi Amman Ahmad gani yakeyi kamar baya masa sauri dan haka yafara magana cikin bacin rai"Nifa nawan na lura ana jamin rai dayawa tunda rana Abba yahanani komawa nagana da matata sai yanzu kaikuma kazo kanayimin driving kamar mace"

Tsaki Mudansir yasaki kafin yace"Kagama ganinta anan duk tsiya dai bazaka juya da ita Saudia nan da sati d'aya ba anan zaka barta"

Wani zaro ido Ahmad yayi cikin razana da dafe kirjinsa kafin yace"Kana nufin bada Aysher zamu tafi ba abokina pls explain it to me"

Kwarai kuwa dan Mahaifin Aysher sungama magana da Abba Aysher zata zana jarabawa nan da wata daya dan kammala karatun sakandire"

Bazaiyiwu ba Ahmad yafada yana kada kansa Kafata kafar matata banga wanda ya'isa yahanani tafiya da ita ba Wallahi.



Shiru Mudansir yayi masa dan bashi da amsar da zai bama Ahmad dan yaga alamar ransa ya baci.


Neman guri Mudansir yayi yafaka motarsa kafin suka bude suka fito.
Yaro suka aika akira musu fatima dan sunsan tana tare da Aysher.
Tare yaron suka juyo da fatima bayan ta gaishesu tace sushigo dakin baffa.
Gida tashige bayan kamar minti goma suka dawo tare da Aysher suka shiga dakin da sallama wannan karon Muryan Aysher Choiii
Da sauri Ahmad ya mike yakara ya riko hannu matarsa bayan Fatima tasaketa kusa dashi yakaita yazaunar da ita Itadai Aysher kanta yana rufe cikin gyalenta"

Gaishe dasu sukayi suka amsa a tare nan Ahmad yafara kici-kicin bude fuskar matarsa ita kuma taki yadda ganin haka yasa Fatima mikewa danta fice Mudansir yamike shima a zafafe yana fadin"Jirani Fatima mufice wannan bakyunya ne dashi ba ya siyar mun kwashe bana fatan yakoyama kawarki wannan fitsarar tasa"

Kanku akeji cewar Ahmad..


Suna ficewa daga dakin Ahmad ya yakara matsowa kusa da matarsa jawota yayi sosai jikinsa tare da bude mayafin data rufe fuskanta.
Ahankali yace"My Dear Haka ake gaishe da miji? Toh nidai wannan gaisuwar taki ban karbeta ba inaso ki nunamin a zahiri kinyi missing din ganina kamar yadda kike fadamin a waya"

Shiru Aysher tayi sai wasa takeyi da zoben hanunta dayaga bata da niyyar masa magana saiya kamo fuskanta da nufinson hada bakinsa da nata Nan Aysher tayi saurin bashi hakuri idonta yafara zubar da hawaye"

Rikicewa Ahmad yayi yafara bata hakuri tare da fadin yadaina tunda bataso.

Cikin shagwaba wanda hakan yakara rikitar da Ahmad tace"Nayi shiru amman karka kuma tabani pls"


Bazan iyaba indai ina kusa dake bazan iya hakura da taba jikinki ba gaskiya yanzu dai abar wannan maganar yaushe zamu wuce.

Cikin zaro Ido Aysher tace"Ina zamuje"

Saudiya mana kinsan nakoma makaranta yanxu zanyi Masters saurana shekara daya da wata biyu nagama Nikuma bazan iya yadda natafi nabarki ba gaskiya dan haka bari zanyima Abba magana yasamu Baffa asan abinyi mukoma nan da wata daya hutun dana samu kenan.....
Bazan iya barinki kiyi wata jarrabawa ba gwara ayimana biki Mukoma tare gaskiya so what is your suggestion?

Aysher tayi shiru kafin daga baya tace"Duk yadda kace Haka za'ayi Mijina"

Kara jawota yayi jikinsa yana mata godiya tare da shakar turen dake jikinta mai sanyin kamshi.
Batare da Aysher ta ankara ba taji bakinsa cikin nata yana tsotsa kamar yasamu alawar lollipop sun dade a haka..........
Yana kokarin zura Hannunsa cikin rigarta kenan kiran wayar Mudansir yashigo wayarsa yadauka a kasalance"Idan kagama saika fito mutafi Abba yana kiranmu gobe xai wuce da safe kano" mudansir yana gama fadin haka ya katse wayar.

Cikin wani irin yanayi Ahmad yadubi Matarsa idanuwansa yarine zuwa jawur yace"Zan tafi zandawo gobe nifa inda hali gobe ma kitare gaskiya daman ni bawani bidi'a nakeso ba ina bukatarki" yafada cikin wani irin murya yana jira yaji Aysher tace masa wani abu amman takasa da alama itama sakon maigidan nata yafara isa gurinta.

Inajinki Sweetheart zantafi Abba yana nemanmu.

Allah yakaimu lafiya sai goben kugaida maijiki.

Kiss yasakan mata a goshi tare da mikar da ita yakamo hanunta suka fito saida yakusa shigar da ita tsakar gidan kafin yasakar mata hannun tare da fadin I love u kikularmin da kanki matana...............

Cikin mota masifa Mudansir yaketa masa tare da cewa "Kai wallahi mugun dan jaraba ne yarinya tana gidansu kana kwakularta kabari sai ankai maka ita mana ni wallahi ina tausaya mata dan naga alamar yadda kake farin shigarnan bazaka bita a hankali ba ko ka tausaya mata Allah yasa acema saika gama karatu ta tare"


Kaji mugu toh a fada mana dan iska kawai idan suka ga natafi nabarta ciki yabaiyana a jikinta za'aturomin da matata bashiri nifa son da nake yima Aysher ma anya zaibarni nayi mata wani abu.....kasan fa ni abin nan baidameniba kodacan kabarni da kiss da romancing"

Toh zamu gani dayake kai waliyyin Allah ne meyasa kadamu ta tare to dan rainin hankali kawai sanda zaka wuce makadi da rawa muna ina........

Toh ya isa haka dan
Allah kasamin baki gurin Abba abani matata mutare ni sonake kafin mubar kasar nan ma na bata ajiyata tunda ance amaren yanzu akofa suke tuntube dashi..

Hahaha Lallai Nawan toh ai cikin a ruwa zatasha ko?
Bazan saka bakin ba sai anbaka ita kafara tsare mana gida kai gaka mara mutumci korarmu xakayima inaji daga gidan sai randa zaka bar kasar may be mu hadu a airport

Haba abokina Allah yakyauta nayi maka haka ai kullum ana tare.
Shiru mudansir yayimasa dan yasan halin abokin nasa.....






MAMAN HANAN
[10/21, 9:30 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 47-48


Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA


*Sorry Pls nayi mistake gurin Numbering daga 45-47 ina nufin 45-46*

_Ina mika gaisuwata ga kawata Hafsat Aliyu mafara wacce tayi rashin kakarta ayau Asabar 21-10-2017 a garin kano Allah yagafartama hajiya Allah kyautata makwancinta idan namu tazo Allah kasa mucika dakyau da imani_



Yanzu ke fiddausi saboda Allah bazaki duba maraicinki ba ki fitar da miji kiyi aure kin tsaya jiran wani Ahmad kusan shekara guda kenan da rabuwarku kinki ki fitar da wani cikin manemanki yafito kuyi aure.

Wacce akakira da fiddausi takalli mahaifiyarta tace"Nifa mama wallahi duk duniyar nan banga namiji dazan iya aura nazauna ba idan ba Ahmad ba Mama bakisani bane wallahi guy din mugun dan love ne ina nan da number sa a wayata ina jiran yadawo kuma fa kwanaki muna waya time din yana yola may be yayi tafiya ne amman mama kidaina bata bakinki nidai Ina nan ina jiran A.A Hameed.


Toh Allah yakawoshi lafiya ayi auren nan ahuta ko zaki daina wannan shashancin naki ko shine yakoyamiki wannan shaye shayen ma ne?


Ahhhh haba mama bashi bane nifa kawai shi love mukeyi ya iya eehhh kema kigane mana mama......
Hmm fiddausi kenan Allah shiryamin ke ja'ira mara kunya.





_Masu karatu idan har baku manta ba nasan zaku iya tunawa da Feedo budurwan Ahmad toh gatanan bata hakura ba tana dakon jiransa dan suyi aure kamar yadda yayi mata alkawari_


*WACECE FEEDO KO FIDDAUSI*


'Ya daya tilo da Allah yabama iyayenta mahaifinta Abdulhameed asalin bakano ne mahaifiyartama haka bayan aurensu sun dade basu samu haihuwa ba Abdulhameed yakasance mafadaci sosai wanda yana ganin yaran makota ko a hanya sunyi abu ba dai-dai ba saiya aibatasu misali :-kaga tsinannen yaro, ko kuma yace" wannan yaron/yarinyar daga gani 'yar iska ce"


Da Allah yatashi bashi haihuwa saiya bashi fiddausi wanda tazo tafi karfinsa dan maza samarinta har gida take kawowa babu abinda bata sha.
Duk da haka Abdulhameed baya ganin laifinta dan akwai sanda kaninsa yazo yadauketa yakaita gidansa yasaka mata mari
Har gida Abdulhameed yaje yaci masa mutumci tare da fadin"Dan me zaisakama 'yar sa mari ita ba barauniya ba"
Anan dai sukayi baran-baran kaninsa yace yacire hanunsa daga kan Feedo.

Tun tana shekara 20 takware a harkan karuwanci da shaye-shaye.

Ahmad yadaukota lift ne daga baya yake zagayowa dan shan sweet toh ita kuma ashe duk duniya bataga mijin aure ba sai Ahmad dan taso yayi mu'amala da ita shikuma yaki kafin tafiyarsa yola..

Mahaifinta yarasa sanadiyyar mutuwa ta farat daya a dakinsa batare dawani cuta ba bayan mutuwar mahaifinta feedo likafa taci gaba har kasashen waje take raka samari kuma bata kunyar fadama uwarta duk maganar dayazo bakinta.

Idan tafada mamanta saidai tayi mata dariya itama bata tsawatar mata tana tsoron fushin 'yar nata dan haka komai feedo tace yazauna.......


Muje zuwa




MAMAN HANAN
[10/24, 12:41 PM] Zeetty: [10/24, 9:38 AM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 49-50


*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*



*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*



_Ina mika ta'aziyya ta ga daukacin family Abdullahi mai jaki Ubangiji yagafatama Baba yasa mutuwa Hutuce a gareta Allah bamu hakurin rashinta_






A Gidan Alh.Lawan suka tarar da Alh.ALiyu bayan sunk'ara gaishesu tare da yima Iyayen nasu Godiya.

Alh.Aliyu yakalli Ahmad yace"Toh nizan wuce gobe idan Allah yakaimu kaikuma yaushe zaka koma kasan dai haryanzu baka cika wata takwas ba saura wata d'aya ko?
Kai Ahmad ya gyad'a kafin yace"Abba yanzu ina cikin hutu ne harna tsawon wata Biyu"

Dasauri Alh.Aliyu yadago kansa yakalli Ahmad d'in kafin yace"bangane kana hutu ba daman har huto shi Fallata yabaka batare da ya sanar daniba?


Dafarko ina neman gafararka Abba bisa ga rashin jin maganar ka da banyi ba hakika ni ba Noma da Kiwo nakeyi a saudi'a ba kamar yadda ka buk'ata asalima Masters dina nakoma dan nayi a makarantar KING FAHAD dake madina kayi hakurin rashin sanar maka da banyi ba nayi hakanne saboda na baka mamaki Abba amman kagafarceni"

Shiru Alh.Aliyu yayi kafin yakalli yayan matarsa Alh.Lawan murmushi sukayima junansu kafin Alh.Lawan yafara magana da cewa"Alhamdulillahi lallai Allah abin godiya Ahmad girma yazo tabbas chanjawar da abokinka yake cewa kayi ashe gaskiya ne ni tundaga zuwanka na fahimci hakan Allah yataimaka ya kuma k'ara shirya mana ku"
Ameen suka amsa gaba d'ayansu kafin Alh.Aliyu yace"Niba wannan ba Ahmad ina kasamu kud'in registration da sauran abubuwa ko Fallata ne yabaka Abin yabani mamaki ya akayi katafi da takaddun karatunka bayan bamu tafi da su ba ko dai kazo Nigeria ne a 6oye bamu sani ba ka koma inaso kasanar damu komai a yanzu"

Ahmad kansa a sunkuye yafara magana "Abba kayi hakuri daman nabar takaddu na a gurin Mudansir sanda kazo mutafi bayan naje Asir Abu-Fallata dakansa yacemin bazai ta6a mantawa da Alherinka gareshi ba dan haka bazai iya horar dani ta hanyar dakace masa ba yanemi shawarata akan haka.
Nikuma cikin farin ciki nayi masa bayanin inason komawa makaranta da burinka kenan daman akaina.

Abu-Fallata yacemin bashi da kudin da zai mayar dani makaranta yarantsemin da saiya mayar dani batare da saninka ba nikuma anan nace masa inada kud'i a account d'ina masu d'an dama toh Abba da wannan kud'in nafara karatu kuma ina juyawa anayimin business daga saudi'a zuwa nan kasarmu Nigeria da kuma Dubai.

Komai yana tafiya ta hanun Abokina Mudansir takaddun makaranta na kuwa Mudansir ne yakawoma Saddiq yakaima Agent din dayayi mana Visa aka biyashi yaturomin da su Abba yanzu nayi nisa a karatun masters d'ina Abba Inda nasamu kud'i kuma Abba shine kud'in dana samu danayi wakar nan ne dafatana zaka gafarceni" Ahmad yakarasa fadar tare da karasawa gurin Mahaifin sa durkusawa yayi a gabansa gwiwoyinsa a kasa alamar yana neman gafara.

Alh.Aliyu dafa kan Ahmad yayi tare da fad'in Alhamdulillahi Ahmad naji dad'in samun Nutsuwarka Allah yamaka Albarka bakomai nayafe maka yanzu saura maganar matar ka dan Mahaifinta yacemin abarta anan tazana jarrabawa kuma na amince masa mezakace?


Gyara zama Ahmad yayi Mudansir ya zuba masa ido dan jin abinda zaice dan yanaso yak'ara tabbatar da rashin kunyar Ahmad.

Ahmad yace"Abba nidai a son raina abani matata kawai mutare tunda wata biyu zanyi inyaso kafin hutuna yak'are ta gama zana jarrabawarta zanyi mata registration makarantar da Saddiq yayi nasa kaga Center d'insu tanada kyau dan haka Abba kataimaka kasa baki a fasa wancan maganar ta tare a kano ni banason wani biki ma duk bidi'a ne"

Murmushi mahaifinsa yayi dan yasan halin a 'Dan nasa zaiyi abinda yafi haka ma musamman akan Aysher dan haka Alh.Aliyu yace"Badamuwa zanyi masa magana akan hakan dan tunda kamin magana akan zakayi wata biyu nima nafara wannan tunanin bazai yiwu abarta tayita zama gaban iyayenta ba maganar biki kuma kasan bazai yiwu ace anfasa ba Mahaifiyar ka bazata yadda ba kodan akanka zamu fara aurar wa dan haka gobe zan wuce sai kutsara yadda komai zai kasance kafin kutaho jibi zan nemi mahaifin ta naji yaushe zasu kawota Alh.Lawan meye zakace akan haka.

Alh.Lawan yace hakanma yayi Alh.Aliyu gobe sai muje musami Baffa Usman d'in kafin mu wuce"

Tattaunawa sukaci gaba dayi kafin su Ahmad suyi shirin tafiya masaukinsu dake gidan Alh.Lawan





Nifa abokina naso abani matata mutafi tare k'afata k'afarta wai dole ne sai 'yan uwanta sunkaita ne mtswwww wannan Al'adar batayi ba wallahi.

Kanka akeji nidai nagama nawa k'ok'arin cewar Mudansir yana fad'in haka yawuce bayan gida dan watsa Ruwa........




MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/25, 8:06 AM] Zeetty: [10/24, 10:01 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE



*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*



*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*

Page 51-52





Tattaunawa a kayi sosai tsakanin iyayen Aysher wato Baffa Usman tare da Alh.Lawan da Alh.Aliyu an tsayar da magana ranar Alhamis iyayen Aysher mata zasu wuce da Amarya tare da sharad'in zata zana jarrabawar kammala karatun sakandire a kano.


Ahmad ba haka yaso ba yaso ace tare zasu tafi da Aysher domin shi ranar laraba zasu wuce da mudansir bayanda zaiyi haka dole ya hakura.



A kano shirye-shiryen biki sosai Umma takeyi da 'yan uwanta tare da abokan arziki sanarwa akeyi a k'afafen yad'a labarai tako'ina bikin Ahmad Aliyu Hameed da Amaryan sa Aysher Usman Damare.



Da daddare Ahmad yaje gurin Aysher dan suyi sallama saboda sammako zasuyi dan a mota zasu tafi Fatima ya aika aka fara kira masa bayan ta fito sun gaisa Ahmad ya fad'a mata yanaso tayi masa magana da Aysher ta amsa tare da shigewa cikin gidan.


Mintuna kad'an suka dawo tare da Aysher wannan karon d'akin Baffa akwai bak'i dan haka a k'ofar gida suka tsaya mota Ahmad ya bud'e ma Aysher yace tashiga ta zauna batayi musu ba ta shiga yazaga d'aya gefen yazauna ita kuma Fatima suna waje da mudansir.

Kan Aysher a sunkuye ta gaida Ahmad ya amsa tare da fad'in "Amarya bakya lefi kin wuni lafiya"?
Aysher tace "Lafiya kalau ya gajiya?

Ahmad yace " Lafiya k'alau Alhamdulillahi gobe zamu wuce gobe da wuri meye kike buk'ata kayan aurenki gobe zasu taho dashi wad'anda zasuzo tafiya dake daga cikin dangi na kina bukatar wani abu ne ki fad'amin mata na?


Kai Aysher ta girgiza kafin tace"Bana Bukatar komai Allah ya sauke ku lafiya Ubangiji ya k'ara bud'i"

Sabuwar waya Ahmad ya bata tare da sabon layi sannan ya ajiye mata rafar kud'i 'yan dubu d'aya guda d'aya yace"Ga wannan kud'in kirike a hanun ki kafin ku shigo kano ga waya zan dinga neman ki ba number kowa a ciki sai nawa a kwai kud'i nayi miki recharging nashi duk wasu shirye-shirye kuma Fatima da Mudansir zasu tsara komai ko akwai wani matsala kuma?

Bakomai Nagode amman da kabar kud'in babu abinda zanyi dashi.

Kai Ahmad ya girgiza mata kafij yace"A'a kidai rike banason aja maganar pls kayan wancan mutumin an mayar mishi da su ko ba naso ki tafi ta kayan shi koda Allura ne"

Aysher tace"Tun washe garin d'aurin aure yaturo danginsa suka zo aka had'a musu har kyautar da yake aiko min dashi na bayar daman banyi amfani da su ba"

That is my wife (Yauwa matata) Ahmad yafad'i haka yana murmushi"Naji dadin hakan da kikayi matata Allah yabani ikon faranta miki da rikon amanar ki Ameen"

Mudansir ne yazo yace musu dare yayi sosai fa dan haka a gurguje Ahmad yayi sallama bayan ya bawa Aysher kiss a kumatu badan ransa ya so rabuwar su da matar sa ba babu yadda zaiyi ne dole ya hakura cikin mota ma Mudansir tsokanar sa ya dinga yi"
[10/24, 10:09 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’




A gidan Radio Feedo taji sanarwan auren A.A Hameed wani ihu ta saki kafin ta zubo wani uban Ashar fad'i take yi"Karya ne Ahmad ba aure zaiyi ba dan bashi da wata mata sai ita yayi mata Alkawari"

Wayar ta ne taji yana ringing da sauri ta d'auka kawarta ce 'yar auta,
Feedo tana d'auka taji 'yar auta tana cewa k'awata kin samu labarin bikin A.A Hameed kuwa dan har an daura auren a yola biki za'ayi amaryan ta tare a nan kai kawata munada chasu fa biki ne na manya"

Kee 'yar auta kinci kaza-kazar ki na rantse da sarkin dake busan numfashi duk wanda ya halarci gurin nan indai yaje sunan sa k'o nanne ni Ahmad zaiyima haka ni zai yaudara na rantse da Allah daga shi har Amaryan tashi da duk wanda zai halarci gurin bikin sunan sa k'onanne......



MAMAN HANAN
ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA
[10/26, 5:25 PM] Zeetty: [10/26, 5:17 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE



_Ina jindadin zama tare daku, ina matuk'ar kaunar ku, 'yan Group din Zauren littattafan Hausa_




*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*



*FOLLOW US ON THIS DETAILS:*
----
*LIKE OUR FACEBOOK PAGE:*
↓↓
*Fb.me/ZAMANIWRITERSASSOCIATION*
----
*CHECK OUR BLOG'S*
↓↓
*Zamaniwriters.blogspot.com*
----
*DROP YOUR COMMENTS AND REPORTS ARE HIGHLY WELCOME ON THIS EMAIL ADDRESS:*
↓↓
*Zamaniwritersassociation@gmail.com*





Page 53-54



Ranar laraba mutanen kano suka sauka a garin yola domin juyawa da Amarya washegari, kar6a na mutum ci sosai suka samu daga gurin dangin Aysher da na mahaifin ta.


Sun taho da kayan aure akwati biyar da d'an kit cikon na shidan, masha Allah komai yaji dan Yadikko a ranar sai yanke jiki tayi a gurin ta fad'i daga an kira ta tazo taga kaya, kayane sun ninka na Honourable sau uku a tsada da kuma yawa.


Cicci6ar Yadikko akayi aka kaita d'akin ta tare da d'ebo ruwa aka yayyafa mata, ajiyar numfashi tayi gami da bud'e idonta tana k'arema d'akin kallo da jama'ar d'akin kafin daga bisani ta lumshe idanuwan ta.


Washe gari Alhamis da wuri aka shirya Aysher dan tafiya kano, motoci guda 5 aka turo daga kano dan haka sunyi komi nasu cikin shiri da tsari suka shirya kowane mota mutum 4 za'a dauka baya mutum uku gaba kuma mutum d'aya, wani abin burgewa shine garar da Baffa Usman yayiwa 'yarsa dan kuwa yayi k'ok'ari ba kad'an ba.


Motar da Aysher take ciki ita da Fatima ne da k'anwar mahaifin Aysher Adda Kubura, Sai gaba aka saka mutum d'aya, Ahmad yanata kiran wayar Aysher yaji muryan ta amman kunya ya hanata d'auka tanajin ringing d'in wayar a cikin jakarta.

Dan haka Ahmad yakira Mudansir dan yazo d'aukar Amarya a cikin motar sa ma aka saka Amarya, dan Ahmad yace bai yadda kowa ya d'auko masa matar sa ba sai Mudansir saboda tuk'in sa kawai ya yadda dashi.

Cikin salon tsokana Mudansir ya d'auki wayar tare da fad'in"Ango kasha kamshi munzo ance anfasa bamu amarya sai gobe juma'a"

"Dan girman Allah Mudansir dagaske?"

"Kwarai kuwa gamu dai anata fafatawa munce yau ango yakeson matar sa a kano"

Cikin muryan lallashi Ahmad yace"Abokina kataima ka a bada ita yau tunda har na wakilta ka kazo kayimin iyaka k'kokarin ka pls kamar ina gurin, ni yanzu je ka nemo min ita ka had'ani da ita a waya yau kwata-kwata banji muryan ta ba wani iri nake jina."


"Sannu rasa kunya idan baka da kunya, ni inada ita, bazan iya zuwa neman Aysher ba ka kwantar da hankalin ka tana mota na yanzu zamu taso da yadda Allah amman magana awaya kam ha hali saboda sai anyi siyan baki a Al'adance" Mudansir ya bama Ahmad amsa da hakan.

Tsaki Ahmad yayi kafin yace"Wannan al'ada yakamata a dainata tunda ba addini bane Allah ya kawoku lafiya" yana gama fadin haka ya katse wayar da alama ransa ya 6aci.




Sun sauka a kano da

Please Login or Register in order to submit comment