Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tashi sainaji kamar an daure ni ne saina kasa tashi.
Haka zaki daure shaidan ne ki dage ki maida hankali zaki samu saukin kuncin da kikeji a cikin ranki.


Nagode kawata awannan ranar Aysher sai dare ta fatima tarakata gida Innar fatima tazo tanata basu labarin yawan kayan auren Aysher tare dayi mata adduar zaman lafiya.

Kaya sunyi kyau antsayar da ranar aure sati uku masu zuwa.


Koda Aysher takoma gida daman da alwalarta datayi tun agidansu fatima dan haka dakinta sukashiga suka zauna fatima tanata bata baki tare da kara kwantar mata da hankali.
Suna cikin wannan hali kiran Ahmad yashigo wayar Aysher wanda haryanzu a vibration yake tuntana tsorata idan tajishi a jikinta harta saba yanzu.

Dasauri tadauka tare da sallama kawai saita fara yimasa kuka nan da nan Ahmad ya rikice yana tambayarta lafiya meya sameta.
Itadai takasa bashi amsa sai sheshshekar kuka takeyi
Daga karshe takatse wayar dan batasan abinda zata ce masa ba.

Sake kira yayi dan yaji ko lafiya duk hankalinsa ya dugunzuma Fatima ce wannan karon Allah yabata ikon daukar wayar dan Aysher kuka taketayi.
Sallama fatima tayi kafin tace"Ahmad kawartace fatima ina wuni"

"Lafiya meyake faruwane dan Allah kiyi gaggawar sanar dani hankalina yatashi"

Akwai matsala Ahmad Aysher takasa fada makane aure za'amata saura........

What......innalillahi wa'inna ilaihi rajiun aure kuma dawaye nan da yaushe kikace na mutu nikam Aysher tayaudareni....


Balaifinta bane Ahmad kusan auren dole za'ayimata da Mahmoud Sharrin kishiyar mamanta ne.........

Inji ubanwaye lallai yau saina goge miki wannan shegen bakin naki keda ubanwaye kike waya kikekai sunana munafuka?

Yadikko ko ce kwatsam tashigo dakin batare da tayi sallama ba yan uwantane sukace tazo ta kira Aysher taga kayan aurenta acire wanda za'akai dinki dan fitar biki toh tana zuwa dakin taji abinda fatima take cewa.


Wayar hannun fatima ta kwace ta makata da kasa atake wayar ta ragargaje alamar bazatayi sauran wani amfani ba.

Yadikko tarufe fatima da duka tare da kwalawa yan uwanta kira wai Fatima tayimata sharri kuma tanason ta lalata auren Aysher........


MAMAN HANAN
[10/19, 3:33 PM] Zeetty: [10/19, 2:34 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 38-39



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA


*GODIYA GA DUKKAN MEMBERS NA GROUP DIN MARYAM YAHAYA SUPPOTER'S ALLAH YABAR ZUMUNCI INAJIN DADIN ADDU'ARKU ALLAHU YA AMSA*


Duka yadikko tayima fatima bana wasa ba daman tanajin haushinta batun yauba saiyau ta samu damar huce haushinta.
Dakyar Baffa Usman ya janye Fatima wanda takasa kukama tsabar azaba...

Tambayarta abinda yafaru yayi amman fatima takasa magana sai hawaye daketa fita daga idonta yajuya kan Aysher itama kukan takeyi sosai takasa cewa komai.

Yadikko yatambaya tafara magana cikin bala'i wato Zuwa nayi nasameta tana waya da wani cewar nine natakura ayima aure saboda haka yayi duk yanda zaiyi auren nan kar'ayishi, daman nadade da fada maka malam karaba yarinyar nan da Aysher kaki toyau ga irinta nan tanaso tasa asirinka yatonu abar maka abin tarihi a gari cewar ankusa auren yarinyarka magana ta lalace nikuwa tsabar takaici shine nakama bugunta.

Kai Baffa usman ya kada kafin yace"Baki kyautaba duk da haka kin aikata badai-dai ba baikamata kidauki irin wannan matakin ba yanzu ina wayar take"...


Nuna inda ta yardashi tayi da hannunta salati baffa yasaki kafin yace yanzu wannan wayar mai tsada kika fasa mata saboda Allah toh baruwana kinemi yadda zakiyi kibiyata bayan dukan da kika mata harda fasa mata waya.

Hakuri Baffa yashiga bama Fatima kafin yace muje narakaki gida nabasu hakuri.

Itadai yadikko jikinta yagama yin sanyi dan ganin irin aika-aikar datayi dakuma irin kudin wayar da Baffa yake ambata.


Chemist baffa yafara biyawa da Fatima yasiya mata magunguna kafin yawuce da ita gida
Sallama yasa tayimasa da mahaifinta.

Bayan yafito Baffa yayi masa bayanin abinda yafaru tare da bashi hakuri akan wayar Fatima da aka fasa yace zaibada wani abu.
Cikin Nutsuwa mahaifin fatima yace bakomai Baffa Usman kaima kayi hakuri yaran yanzu kahaifesu baka haifi halinsu ba maganar waya kuwa kabarta munyafe.

Godiya Baffa Usman yashiga yimasa tare da sanar masa gobe zai wuce lagos shima sai biki yarage kwana biyu zai dawo.
Da haka sukayi sallama.

Mahaifin Fatima yana shiga gida yatarar dasu Fatima da Innarta a kan tabarma a tsakar gida neman guri shima yayi yazauna kafin yafara tambayar fatima abinda yafaru dakuma inda tasamu wayar datake amfani dashi batare da saninsu ba.

Cikin Nutsuwa fatima tafara basu labarin soyayyar Ahmad da Aysher dakuma wayar daya bama Aysher taboye saboda kar yaddikko tagani suke waya a cikinta har zuwa yau da abinda yajawo mata shan duka takara da cewa dan Allah baba karka nunamusu wayar Aysher ce karyakara jawo mata wani matsalar abarshi akan nawane.

Allah ya kyauta abinda mahaifin Fatima yace kenan yakara da cewa wannan abu akwai sarkakiya nima nayi mamakin Yadda wannan auren yataso da wuri haka amman koma meye xamuci gaba da addua maganar waya kuwa daman nace masa munyafe kudinta dayace zairage mana Allah mata zabi mafi Alheri.

Ameen suka amsa gaba dayansu.
[10/19, 3:33 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Bangaren Ahmad kuwa tashin hankalin dayashiga bazai kwatantu ba gashi suna cikin waya da fatima yaji shiru bayan yaji kamar ana musu masifa.

Wani irin sarawa kansa yafarayi daya kara kiran wayar Aysher yajita akashe
Mudansir yakira yana dauka baisaurari abinda yakecemasa ba yafara magana" Nawan yau ba ranar wasa bane pls katafi yola yau kaje aiport kozaka samu flight karna rasa Aysher wai aure zatayi kuma ankusa bansan haka Aysher zataminba Aysher tayaudareni mudan......yakarasa fada cikin raunin murya

Mudansir shima daya gama rikicewa fadi yake"Waye yafada maka haka nawa koma waye karya yake maka Aysher bazata taba yimaka hakaba dan ni shaidane akan irin son datake maka.

Aysher takasa fadamin saboda kukan datakeyi kawartace Fatima tasanar dani itama muna cikin magana da ita naji shiru yanzu nakara kiran wayar akashe dan Allah Mudansir kataimaka kaje kaga abinda yake faruwa nima gobe zanje gurin Ambasador na Nigeria a Makka yasamin baki abani Visa nataho gobe dan Allah Nawan bakaji yadda nakeji ba daman akwanakin nan asan Aysher tacanja daman Jikina yana bani akwai abinda zaifaru ya Allah karka jarabceni da rashin auren Aysher dan komai zai iya faruwa.


Cikin tausayawa mudansir yace"Kayi hakuri abokin ayanzu karfe 9pm bazan samu flight ba kuma ina Abj nida Dad
But nayi maka Alkawari gobe zanbi jirgin safe natafi yola duk abinda ake ciki zansanar maka ka kwantar da Hankalinka Aysher takace babu wanda zairabaka da ita
Mudansir kwantarma da Ahmad hankali yadinga yi saida yaga hankalin Ahmad yadan kwanta kafin suyi sallama tare da cema Ahmad yasha maganinsa na ciwon kai dan yaji yadda Ahmad yake bashi amsa dakyar wanda hakan yanunama mudansir ciwon kan abokinsa yatashi.

Mudansir yana katse wayar yakalli abokinsa da sukayi waya suka hadu a Abj anan mudansir yake fadama abokin nasa cewar gobe zai tafi Yola dan duba wani abu mai muhimmanci.

Shima abokin cewa yayi nima kuwa gobe zantafi yola amman ni mota zanbi da asuba na wuce dan akwai masu farautar rayuwata.

Zaro Ido Mudansir yayi kafin yace"Like seriously Nura waye wannan haka nidaman tunda kacemin kana tare da 'yan siyasa hankalina baikwanta ba"


Anan Nura yalabartawa Mudansir labarin Hon.Mahmoud da Aysher da yadda akayi suka hadu a hoto tare da fadama Nura zuwansa Uku Yola yana neman Ahmad baisamu ganinsa ba amman daga gobe idan yaje yaduba baisamu ganinsa ba yahakura zainemo wata mafita akan auren Aysher da Mahmoud amman Nura yaboyema Mudansir matsalar dake tattare da Hon.Mahmoud.

Rikicewa Nura yayi dajin wannan labari na Nura dan haka yace" saurayin yarinyar abokina ne Nura closer friend dinama kuwa baya kasar yana saudi'a shisa bazaka ganshiba yanzu dan Allah yaza'ayi Alhamdulillahi dagaske ne aurenta za'ayi?

Kwarai makuwa Nan da sati Uku masu zuwa saboda har anbugo katin biki ma.

Nura meye shawararka Hakika idan Ahmad baisamu yarinyar nan ba komai zai iya faruwa ina tausayama Ahmad yasaka yarinyar aransa dayawa gashi jarabawa yakeyi wannan matsalar tasawo kai Nura mutafi dakai mana goben yola.


Girgizakai Nura yayi tare da cewar zuwa yola yanzu bashida amfani tunda abinda zaikaini kenan neman Ahmad ni wallahi banmasan shibane dan na taba ganinsa a gidansu Aysher da daddare amman bangane A.A Hameed bane shege kace ya mato.

Mudansir yace Nura yanzu ba lokacin wasa bane pls meye shawara banason wani abu yasamu Ahmad wallahi.


Anan dai sukayi shawarar yadda zasubi lamarin cikin sauki.


_Masu karatu menene wannan shawarar tasu lokacine kadai zai iya nuna haka_



MAMAN HANAN
[10/19, 5:30 PM] Zeetty: [10/19, 5:21 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 40-41



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA


Bisa ga shawarar dasu mudansir sukayi shida Nura.

Ahmad suka kira mudansir yabawa Nura wayar sukayi magana da Ahmad Nura yace Ahmad yayi kokarin shigowa Nigeria nan da sati daya.

Cikin Alamar karaya Ahmad yace"Nura anhanani zuwa Ambasador dakansa yaki sakamin hannu nataho saboda jarabawar danake zanawa na karshe a makaranta yazanyi dan Allah Nura kataimakamin.

Shiru Nura yayi kafin yace toh zamuyi iya kokarinmu dan ganawa da Mahaifin Aysher kafin Ranar daurin auren amman maganar gaskiya itace kayi kokarin tahowa Dan kafin ranar auren.


Ahmad ya amsa masane kawai batare da hankalinsa ya kwanta da shawararba.


**************



Biki saikara matsowa yakeyi saura kwana goma.

Maigaiya mai Aiki Hon.Mahmoud bakaramin shiri yayima auren ba ganin zai auri karamar yarinya soyake a dirjeta dakyau anan yola kafin yawuce Abj dan bazai iya hakuri harsai tagama zana jarabawa ba.
Da badan wannan jarabawar nata bama da Honey moon zasu tafi
Ganin Aysher bata da wani wayewa a harkan zamantakewar aure shikuma bayaso ya kwaru yafiso takoya dan yadinga samun gamsuwa dakyau yayin amarcinsu dan haka yasa Woman leader ta gombe ta samo masa wata mata na musamman danta koyama Aysher yadda ake mu'amalar auratayya tsakanin mata da miji tare da gyaran jiki na amarya dilka da halawa harma da kunshi ita zatayima Aysher.
Yagana yar maiduguri ce dan haka tataho da shirinta na sati biyu ciff a garin yola.

Aysher taso ta botsare amman Fatima ce tabata shawara akan ta amince zaimata amfani tare da zazzare ido gurin yadikko.

Dan Haka aka fara yima Aysher gyara sosai cikin kwanaki hudun da suka wuce Aysher takoyi abubuwa da yawa.

Bayan gyaran jiki gaba daya Aysher tadawo kamar yar india ankoyama Aysher abubuwa kamar haka:-


*KISSAR TAFIYA*
*KISSAR MAGANA*
*KISSAR IYA ZAMA DA MIJI*
*KISSAR KWALLIYA*
*KISSAR TSAFTA DA KWALLIYA*
*TSAFTAR JIKIN MAIGIDA*
*SHAGWABA*

Duk abubuwan nan da ake koyama Aysher tana makale da kawarta tare ake koyar dasu a dakin Aysher.

Tsumi kuwa da gumba kai harda wani magani wai *TABAJE* cikin roba yagana take bama Aysher da madara.


Hakika ita kanta aysher tasan ta canja komai nata ya cicciko Ana saura sati daya biki Hon.Mahmoud yadiro a yola yadda yaga Aysher jiyayi kamar yaje ya rungumota kai Lallai Allah yakai damo ga harawa zai kwashi dadi a jikin nan.............
[10/19, 5:29 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’



Nura da mudansir sun sauka a yola ana saura sati daya biki dan Ahmad baisamu visa dazai taho Nigeria ba an hanashi yanzu haka yana kwance bashi da lafiya saboda tsananin damuwa.


Dan haka su Nura suka iso yola amman duk yadda zasuyi dan suga Aysher abin yafaskara saboda bata fita ko'ina dan gyaran jikin da ake mata ko sun aika ayi musu sallama da ita sai a turo yaron cewar wai bazatazoba aurenta xa'ayi.

Haka zalika sunnemi ganin mahaifin Aysher anshaida musu bazai dawo ba sai biki yarage kwana biyu.

Jikinsu ba kwari suka dawo kano
Nura ne yace "sunemi mahaifin Ahmad su baiyana masa komai yataimaka yaje yola kafin ranar daurin auren"

Ahmad suka kira dan fada masa shawararsu shima hakan yace yayi dai-dai nima dazau ambasador yace zaisamin hannu abarni nazo so pls barin kira Abban nawa Mudansir kuyi masa jagora idan na'iso shikenan Amman duk yadda za'ayi zandiro kafin ranar daurin auren Aysher koda hakan zaijawomin koma baya a harkan karatuna nayadda dana rasa Aysher.


Addua zakayita yi katashi yanzu katafi kaje kayi dawafi ka kaima Allah kukanka da'alama ma baka addua Ahmad soyayyar Aysher ya makantar dakai to tunwuri katashi tsaye da addua kaida kake gari mai Albarka haka garin da kana roka za'a amsa maka inji Mudansir.


Angama nawan nagode da tunatarwanka gareni wallahi namanta da wani abu waishi addua saboda tsabar rikicewa amman Insha Allahu daga yau nadaina bacci saina mallaki Aysher........



MAMAN HANAN
[10/20, 1:15 PM] Zeetty: [10/20, 1:11 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 42-43



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA





Aranar da Mudansir sukayi waya da Ahmad da daddare suka isa gidansu Ahmad din kai tsaye suka shige cikin gidan dan maigadi yariga yasan mudansir batare da wani bincike ba
Guri Mudansir yasamu ya faka motarsa yafito shida Nura can suka hango saddiq yafito daga kofar dazata sadaka daga cikin gidan kai tsaye gurinsa suka nufa shima ganinsu yasa yanufosu yana Dariya.

Yace"Yaya mudansir ina wuni lafiya kuwa na ganku da daddaren nan"
Mudansir yace"Inafa lafiya dan rigiman abokina yatasomu Abba yana ciki kuwa"


Hahaha kai kake biyema Yaya Ahmad wallahi Abba yadawo tun 7:00pm barinyi masa magana

Shigar saddiq bawani dadewa sai gashi yafito yace Yaya Mudansir wai kushiga ciki bismillah kuzo muje.


Durkushe suke gaban Alh.Aliyu bayan sungaidashi tare da yimasa bayanin dalilin zuwansu.
Shiru Alh.Aliyu yayi kafin kuma daga baya yafara magana "Tabbas Ahmad yafadamin wannan maganar yarinyar nan amman dayake nasan halin shiriritarsa shisa banyi wani yunkurin zuwa gurin mahaifinta ba saboda ina gudun kar Ahmad yabani kunya duk kuwa da cewar nayi mamaki da Ahmad dakansa yace naje natambayo masa auren yarinyar dan abinda baitaba ceminba kenan.
Yanzu kai Mudansiru kana ganin Abokinka yayi Nutsuwar da za'a nemo masa aure?

Cikin sauri mudansir yadaga kai yakara da cewa" Tabbas Ahmad ayanzu idan kaga Ahmad saikayi mamaki ya zama babban mutum mai halin kwarai magidanci kamar yadda kakeso kagansa harya wuce tsammaninka Abba kataimaka kasa hannu abawa Ahmad auren yarinyar nan wanda za'abata kaji yanada matsala babba a tare dashi wanda hakan zaizamo cutuwa ga ita Aysher.

Nura shima yakarba da cewar"Abba taimako zakayima rayuka biyu rayuwar Aysher da Ahmad dan rashinta zai iya zamo babban matsala ga rayuwar shi Ahmad din wanda hakan zai jawo ZUBAR HAWAYE daga kowane bangare"


Shiru Alh.Aliyu yayi cikin dogon nazari kafin yace"Yaushe ne mahaifin yarinyar zai dawo yaushene kuma daurin auren?


Mudansir yace"Gobe Alhamis zaidawo daurin auren kuma ranar Asabar ne"

Toh shikenan gobe kuzo mubi jirgi zuwa yola dukanmu zanyima Alh.Lawan magana yasan da zuwanmu Alh.Labaran daga nan zaimin rakiya tare daku zanyankar muku ticket dikanku madallah da kokarinku nagode"

Suma godiya sukayi masa kafin suyi masa sallama subar gidan.

***********

Party kala biyu Hon.mahmoud ya shirya daya a nan yola za'ayi rabar da aka daura aure da daddare daya kuma a Abj shida jama'arsa.

Ya iso yola tuntuni Hon.Mahmoud kenan


Washer gari misalin 12:00pm Alh.Aliyu suka sauka a garin yola kafin sutaho sunyi waya da Ahmad yace shima yana nan zuwa Ranar juma'a ko asabar da sassafe.


Kai tsaye gidan Alh.Lawan suka fara sauka bayan gaishe-gaishe Alh.Aliyu yayi ma Alh.Lawan bayanin dalilin zuwansu Hakika Innawuro tayi farin ciki dajin wannan labari addua taringayi akan lamarin takara da cewa hakika Ahmad idan yasamu Aysher yayi sa'ar mace tagari.

Alh.Lawan ma haka yace yadinga fada musu kyawun halayen aysher da Nutsuwarta.

Wannan abu bakaramin dadi Alh.Aliyu yaji ba dajin wannan yabo da surukarsa matar dansa insha Allahu take samu. Dan haka Alh.Lawan yace su hanzarta tashi suje su samu baffa Usman tare da biyawa makarantar Almajirai suka bada sadaka ayi musu saukar karatun Qur'ani Allah zaba abinda yafi alheri.



Da yamma suka isa kofar gidan Baffa usman shima dai saukar safe yayi a garin yola.

Ikon Allah bayan sungaisa Alh.Lawan yagabatar da Alh.Aliyu a gurin mahaifin Aysher da bukatarsu suka kara da cewa duk da sunsan neman aure cikin aure haramun ne amman wannan akwai matsala.

Tambayar Baffa Nura yayi cewar shin yayi bincike kuwa akan Hon.mahmoud kuma Baba yakamata kasasu shida Aysher tunda yana gari yaxo suje ayi gwajin jini kasan yanxu ba'ayadda ayi aure haka saboda matsalar cututtuka da'ake dauka wajen mu'amala.


Kai Baffa ya girgiza kafin yace"Hakika naji dadin zuwanku guri na saiyau naji abinda ya dunkule yadannemin kirjina yasauka hakika nima bansan yadda akayi na bawa Aysher auren wannan mutumin ba ganina dashi nafarko hankalina bai kwanta ba Amman kwatsam daga baya naji inason lamarin danhaka idona yarufe nakasa tsayawama nayi wani bincike akansa amman yanzu Alh.Lawan ya za'ayi aure jibi nefa kar amaidani mutumin banza kuma mutumin nan babban mutum ne dan siyasa karna tozartashi kuyi hakuri hakika tun ganina da Ahmad nafarko naji yakwantamin araina ashe Ba mijin Aysher bane.


Kafin kowa yace wani abu Nura yayi saurin cewa "Baba kacema Mahmoud din yazo gobe ayi gwajin jina agani idan har ba'asameshi da wani cuta ba wanda Aysher zata iya dauka mun hakura a aura mata shi idan kuwa yana dauke dashi toh Allah yayi rabon Ahmad ne dan haka ashirye muke jibi adaurama Ahmad aure ko Mahmoud muna tafe da iyayensa gasu kagansu.



Na'am baffa yayi da wannan shawarar dan haka a gabansu yakira wayar Hon.Mahmoud yacemasa bayan sungaisa" Yazo gobe suje lab ayimusu gwajin jini dan tabbatar da lafiyan junansu"

Arikice Hon.Mahmoud yace shifa lafiyarsa kalau kuma baya zargin Aysher.
Baffa yace"Duk da haka kuzo zansa kanwar mahaifiyar Aysher datazo biki tayi muku rakiya kazo da wuri dan Allah"

Baffa yana fama fadin haka yakatse wayar.

Sallama sukayi dasu Alh.aliyu da bayan sun karbi number baffa akancewar xasu kirashi gobe suji abinda ake ciki.


A hanyar komawarsu gidane Nura yake sanar musu matsalar da Hon.Mahmoud yakeda ita hakika suma hankalinsu yatashi sukadinga adduar Allah tona masa asiri mugu macuci.
Sunkira Ahmad tare da fada masa yadda ake ciki tare da kwantar masa da hankalin cewar In sha Allahu Aysher rabonsa ce....


Ahmad komawa yayi dakin ka'aba yace gaba da kaiwa Allah kukansa tare da jiran akira wayarsa dan tahowa Nigeria.
[10/20, 1:15 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Saina Hallaka Nura nayi Alkawari idan Narasa Aysher sainaga bayan Nura dan shine munafiki a tsakaninmu da ita bayan doctor na Nura ne kadai yasan Wannan matsalar tawa.

Hon.Mahmoud kenan yake fadin haka a ransa yana zaune a dakin daya kama a hotel

Doctor dinsa yakira yayi masa bayanin halin tsaka mai wuyar da yake ciki.

Doctor yace "kakwantar da hankalinka ga shawara..........Nan dai sukayi shawarar abinyi tare da cewar yama kashe wayarsa gobe karyaje yabari sai jibi ranar da za'a daura aure.


Farincikine ya kama Hon.Mahmoud godiya yadinga yima doctor nasa tare da yimasa transfer din kudi masu yawa wanda doctor din zai turo masa da maganin da xaiyi amfani dashi gobe.............




MAMAN HANAN
[10/20, 3:09 PM] Zeetty: [10/20, 2:52 PM] Zeetty: πŸ’
πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’
ZUBAR HAWAYE
Page 44-45



Β©ZAUREN LITTATTAFAN HAUSA








Aranar juma'a wato ana gobe daurin auren Aysher da Alh.Mahmoud kua ranar da akayi zaizo yaje ayi blood test saiya kashe wayarsa bisa ga shawarar da likita yabashi.

Aranar Doctor din ya iso yataho masa da maganin dasukayi magana

Nan take Hon.Mahmoud yazuke maganin Doctor yakara da cewar Honourable hakika kawuce gurin ko anje gwajin gobe baza'agano matsalarka ba idan maganin yakwana a jikinka shikenan zaiyi hidding matsalarka for 24hours so kayi kokarin zuwa goben with your full confidence dan baza'agano komai ba.

Sallama makudan kudi Hon.Mahmoud yayima Doctor sukayi sallama yajuya zuwa abj.



**************
Wunin Ranar juma'a baffa yanata neman wayar Hon.Mahmoud akashe duk hankalinsa yatashi dan ganin wannan abu da Hon.Mahmoud yayi hakika jikinsa yafara sanyi da wannan abu daya faru.

Wayar Alh.Lawan ne yashigo masa Baffa yasanar masa abinda yake tafiya.

Alh.Lawan yace ajirasa zuwa goben kafin a daura auren sai ankawo result.

Ahmad sai a ranar juma'a yasamu visa sa tafito zasu taso ranar asabar da asubah.
Baiso hakanba amman yayi adduar Allah yasa hakane mafi alheri tunda suna waya da mahaifinsa da mudansir kuma sunasaka ran samun nasara.

Hon.Mahmoud baikira wayaba sai da daddare wajen karfe tara Hakuri yashiga bama baffa tare da cewa gobe da wuri zaizo suje kafin daurin aure ayi masa hakuri yatafi wani kauye na hanyar Adamawa dan kai wani sako.

Baffa yace bakomai Allah kaimu lafiya.

Aysher kuwa suna tare da Kawarta fatima da dangin mahaifiyarta suna kara kwantar mata da hankali akan auren itama tamika wuya ta karbi auren a matsayin kaddaranta dan tasan Ahmad shi takeso daga kansa kuma bata fatan sake na biyunsa a zuciyarta.







*RANA BATA KARYA*

Ranar asabar da misalin karfe 9:00am Hon.Mahmoud yazo shida abokinsa suka dauki aysher da kanwar mahaifiyarta da fatima bisa umarnin baffa suka wuce Labouratory dan daukar jini.

Bayan ciccike takaddu da biyan kudi aka debi jinin kowa Hon.Mahmoud cike yake da kwarin gwiwa.

Bayan mintina goma sha biyar result yafito kanwar mahaifiyar Aysher ce tayi saurin saka hannu ta karba Hon.Mahmoud baidamu da hakan ba dan yasan he is free....

Anan take Aunty Maryam ta fara bude takardan fatima taga komai nata lafiya bawani damuwa.


Tafata bude na Hon.Mahmoud kenan wayarta tafara ringing taduba taga Baffa usman ne yake mata magana da cewar ya ake ciki da kowanne bangare ancika za'a daura aure meke tafiya ne dan baza'ajira su dawo ba za'adaura auren kawai.


Da sauri tace "Baffa komai na Aysher lafiya barin duba da maigidan nata"

Yi hanzari maryam mutane suna jira ga ranar yayi yawa Baffa ne yabata amsa da hakan.

Dasauri Aunty maryam tafara dubawa tana murmushi dan ganin komai nasa Lafiya ido ta zaro tare da dafa kirji wayarta tayi sauri zarowa hanunta yana rawa takira baffa yana dauka yace ya'akayi ne Maryam.........
Kar a daura baffa bashi da lafiya H.I.V positive Baffa....Maryam tafada cikin murya mai nuna alamar tashin hankali.
Hannu Aysher tasa akanta tafara ihun kuka.

Fatima takalli Hon.Mahmoud wanda yadafe kai yaki yadda su hada ido dasu aunty maryam tace"Allah wadaranka mugu azzalumi Allah ya tsallake kawata daga mugun nufinka a kanta Allah tona maka asiri macuci"


Itama Aunty maryam kwandon bala'i tasauke masa tare da jan hanun Aysher wacce tadawo kamar gunki suka kama hanya dan barin asibitin.

Keke Napep suka shiga dan zuwa gida suna karasawa suka tarar yan daurin aure sun harsun fara watsewa da alamar kuma andaura dan ganin samarin kofar gidan suna tsokanar Aysher da cewar ga amaryan tadawo ashe batanan ma aka daura auren.


Basu kulasuba su aunty Maryam suka shige gidan....


Bala'i yadikko takeyi a cikin gidan cewa"Sharri akayima Hon.Mahmoud lafiyarsa kalau.

Toh bawanda yakulata ita da danginta dake tayata fadan.

Sudai dangin mahaifiyar Aysher dana mahaifinta godiya suka dinga yima Allah daya tsallakar da yarsu daga shariin wannan mutumin.


Fatima ce tayi karfin halin tambayar da waye aka daurama Aysher aure yanzu?

Kanwar Baffa Usman mai suna Adda Hajara itace tabawa fatima amasa da cewar "Baffa Usman yasanar mana da cewar andaura mata aure da wani yaron abokinsa yaron arziki ne bashi da matsala hakika zamansu zaiyi karko.

Kama hannun Aysher Fatima tayi suka nufi dakinta cikin kuka Aysher tafara mata magana " Kawata narasa Ahmad narasashi har abada nakarbi zabin Baffa xuciya daya danyafimin zama da wannan mugun mutumin idan Ahmad yadawo kibashi hakuri ni kima aureshi akan ace watace ta aureshi yanada kirki kawata ......
Rufe mata baki fatima tayi tafara yimata nasiha masu ratsa zuciya ahankali Aysher taji zuciyarta tayi mata sanyi.
[10/20, 3:09 PM] Zeetty: πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’πŸ’


Aunty Maryam aka aiko takira Aysher angonta yazo yana dakin baffa tazo su gaisa.

Taso fatima tayi mata rakiya amman aunty maryam tace Angonta yace ita kadai yakeso yagani baya bukatar rakiyar kowa.
Afili fatima tace lallai wannan angon bashi da kunya aunty maryam haka yace miki.

Kai kawai aunty maryam ta daga mata kafin takama hannun Aysher dan zuwa dakin baffa dake zauren gidan suna zuwa dai-dai kofar shiga dakin Aunty maryam ta tura Aysher ita kuma tajuyo.

Cikin sallama da muryan da baifito sosaiba Aysher tayi sallama Bawanda yaji sallamarta dan haka bawanda yasami damar amsawa...


Ji tayi anyi mata wani irin runguma tare da kissing dinta ta ko'ina.

Gyaran murya akayi daga gefe amman duk da haka Aysher bata fasajin ana kissing dinta ciki salon gwaninta da kwarewa ake aika mata da Hot kiss din.

Haba abokina pls kabari haka mana muyi abinda yakawomu.

Aysher bata gane muryan mai magana ba amman cikin ranta tanajin dadin kwanciya datayi jikin wannan fata lallai kobatason wannan mijin nata tanasaran sonshi nan gaba dan daga gani gwanine wajen iya soyyayya.
Kara gyara kwanciyarta tayi akan faffadar kirjinsa takara boye fuskanta.

Muryan da bazata taba mantawa dashiba ko a mafarki ko a zahiri duk wahala duk dadi shitaji yana mata amo a kunnuwanta yana fadin"Barni Mudansir barni naji dumin Aysher a jikina barni na tabbatar da cewar ba mafarki nakeyi ba Aysher yau tazamo matata Allah nagode maka"

Ahmad ne yake fadin haka bayan yadakata da Aikama Aysher sakon da yake isar mata yakama hannun matarsa yazaunar da ita akan ciyarsa....
Duk Aysher kuma saita kasa sakewa wani kunyarsu taji ya lulllubeta...


Mudansir ne yake fadin"Ahmad kabar yarinya haka dan Allah duk kahanata sakewa kasata tanajin kunya ni wallahi zanfita nabar maka dakin tunda abin naka iskanci ne"..


Toh sai meye tashi kafita mana muci gaba da sha'aninmu dan sa'ido kawai nifa indai nine gwara

Please Login or Register in order to submit comment