Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

DPO "ku kullesa har sai nina bada damar fiddoshi"aguje malik ya iso wajen yana tare Alfah agigice yace"baza su sake kullesan ba wlh,sannan kushiga taitayinku zaku yi dana sani akan hakan."
Alhaji kwangila shima cikin bala,i yace"ubansa kadai zaizo nan na hakura kuma bazai tab'a zuwaba domin kuwa wannan dan iskan yaron ya riga yafita daga cikin zuriar su,kunsan kuwa abunda yayi kunsan irin bala,in dayayi har iyayensa suka korai to bari kuji wannan dakuke gani,matar.............jikake tas tatas Alfah ne tsaye gaban Alhaji kwangila ya wankesa da kyawawan maruka har uku.
idonsa yayi wani irin fitinennen jaa,dai-dai sadda wani babban mutun yashigo station din wada tacika da mutane,cikin shakewar murya da ta dishe saboda tsananin bacin rai "wlh kasake furta magana marar dadi akaina saina kasheka,saina fiddo yan hanjinka don ubanka katon banza katon wofi,b'arawon gwamnati baka iya komi ba sai yad'a karya da sharri.........kai *Abdoul-nasser* kul akul nace in ka sake magana saina sasab'a maka awajen nan."
Wannan babban mutumen daya shigo yanzu yake fad'ar haka.
Ajiye hannunsa yayi da yake nunnuna Alhaji kwangila dashi kamar zai kaimashi naushi,huci yake fiddawa yanajin kamar yadunga dukan bango kozai huce haushinsa......yace"Daddykabarni na koya mai hankali,kabarni na keta mashi rashin mutunci.ni....ni..zai....wulak'anta.......sai wasu zafafan hawaye suka shiga zarya kan kuncinsa.
Malik kanshi hawayen yake na tausayin amininsa kuma dan uwansa.
Mutumen yace"nadai ce karka sake magana idan ba haka ba zaka ga b'acin raina.
tunda ya shigo duk aka k'ame ana sara mai,saboda shine comissioner of police. kallon su yake shima fuskarsa babu walwala ya kalli Alhaji kwangila yace" kagani ko,u see i tall u last time ka guji tun karar shi kar watarana ya baka kunya,Abdoul ba kunya ce ta isheshiba tun wancen karon balle yanzu da yasake firgicewa baijin kunyar yaga maka rigar mutunci,gashi kuma hakan akai bacin malik yaje ya kirani da banson iyakar abunda zai maka ba wlh awajen nan."
Zufa yake share wa yana jinjina kai duk ya gigice,feea na gefe na kuka ganin yadda aka wanke ubanta da mafi,wanda yafi nata. fiyah kuwa kamar kazar da aka tsamota daga cikin ruwan zafi,duk ta firgice.
Cikin taushin murya Alhaji kwangila yace ma mutumen daya ke magana "nagane hakan Alh maude,zan kiyaye."
Alh ya kalli Alfah dake huci kamar tukunyar da aka gama sanwa da ita yace mashi.
"Abdoul."
Kallonsa yayi ido jawur batare da yace komi ba,yace"wuce kutai gida zanzo in sameku,malik idan yayi wani misbehave tell me."
Jinjina kai malik yayi yana cewa"thank u Daddy."
Jinjina kai yayi kurin yana cewa Alhaji kwangila "kana iya koma wa ga aikin ka,amman ka kiyaye don wataran abunda yafi haka zai maka,kekuma kiyi hkr kiyiwa Abdoul uziri ba halinsa bane."
Feea dake hawaye tace"wlh ni daman nace mashi nayi hkr shine yace sai ya kullesa."
Girgiza kai Alh maude yayi yace "uhm shikenan kawai kuna iya tafiya zanje namasa nasiha anjima."
Kamar kububuwa Haka Alfah yafito daga station d'in,malik binsan yake cikin sauri don yasan wannan fushin sai yayi kwana uku yana yinsa,inbai samu wanda yajuye haushin sa akai ba.
Tuni fiyah ta yanki hanyarta,don tace ma feea bazata bisu ba akwai inda zata bata d burin daya wuce tasan waye wannan guy d'in,ita sai take ganin kamar yana mata kama da yaran gidan *ALH MU'AZZAM CANJI* amman zuciyarta ta kasa yardar mata da haka,saboda in d'an gidanne mezai fiddoshi daga gidan yazo yana irin wannan rayuwar,girgiza kai tayi tanajin matukar tsananin tausayinsa na cika zuciyarta.
Hango malik tayi ya tare masu taxi gudu-gudu sauri-sauri haka take had'awa har ta samu ta tari itama taxi d'in tace mai yabisu baya,binsu yake har k'ofar gidansu tace yayi parking daga nesa,
Azafafe ya bude kofar motar yafito, sai soka hannunsa yake cikin kansa yana ya mutsa kyakkyawar sumarsa kamar ta larabawa,isa yayi bakin get din gidan nasu yana jiran malik dazai sallami mai taxi,dora hannunsa yayi ga bango sannan ya aza kanshi sama,daka kallai kasan yana cikin wani irin hali.
Hawaye taji sun sulalo mata bata ma sani ba.
malik ya iso inda yake yana bude masu karamar kofar shiga,yana mashi magana amman bazata iya juyo abunda yake cemai ba.saida taga shigarsu sannan tace ma mai taxin ya kaita maitama estate.
Don lectures din da zata koma tayi anriga angama,kuma daman ita kadai ta rage mata.
Har taje gida tana hawaye,ganin sun kusa isa yasa ta goge kwallarta tana daidaita natsuwarta,sallamarsa tayi ta wuto zata shiga gidan, ganin buta tayi bakin shagonsu ta dauka ta wanke fuskarta,yadda baza,ai mata tambayar kukan me tayi ba.
"Sofiyya yau ba magana."
Maitsaron shagonne yayi mata maganar,watau dalha cousin dinsu ne ta wajen mahaifiyarsu,sadda aka gama had'a shagon ta je har rimi ta daukoshi don daman zaman banza yake acan.
Rimi garine cikin katsina
Cikin rashi kuzari ta juyo tana yak'e tace"ayya d'alha wlh nagaji ina sauri inshiga gida,sannu da aiki ya kasuwar."
Murmushi yayi yace"da godiya,maza hanzarta kar acinye babu ke."
Murmushi mai kyau tayi ta shige tabarsa.
Sallama tayi yesmin dake kwashe shanya ta ansa mata.
"Sannu Adda kin shawo rana."
Jinjina kai tayi ba ta bata ansa ba,bin bayanta tayi da kallo cike da nazarinta,da alama Adda na cikin damuwa.
Mamace tafito daga cikin daki tace"kamar sallamar fiyah naji ko."
Yesmin dake linke zane tace cikin rashin jin dadin ganin yayar tata haka "itace mama,amman kamar bata da lfiya tashige d'aki."
"Subhanallahi,bari inje inji."
D'akin nasu ta shiga tana kiranta,bata cikin dakin amman jiyo karar ruwa cikin bayinsu yasa tajuya,
tabarta ta fito.
Haka Allah ya yi sofiyya da daukar damuwar wani ta zama tata,mace ce mai tsananin tausayi abu kadan zai karya mata zuciya,duk da halayenta sunda yawa amman abu mafi bayyana tare da ita shine,san yinta kafin kaga zafin ta zaka jima sannan akwai zurfin ciki sosai,tana da shanye damuwa abu zai jima yana damunta bata bayyana shi ba.
Wankan ta fito tana shafa amman yanayin fuskarsa take hangowa,da zafafan kalaman da abban feea yake gaya mai,runtse ido tayi hango yadda idonsa yayi jajawur gwananin ban tsoro........haka ta gama murza man ta saka kaya marasa nauyi tayi sallar azahar da la,asar sannan ta fito tsakar gidan.
Mama da yesmin nata hira tazo ta zauna,ta dora kanta bisa cinyar maman tana shagwabe fuska.
"Mama yunwa nakeji."
Shafa kanta take tace"yesmin dauko wa Addarki d'anwakenta yau mutumen ki akai zakici ko."
Daga kai tayi tana sake narkewa daman fiyah badai shagwaba ba,ajiye mata yesmin tayi tana cewa"Adda d'azun ina magana baki tanka niba."
Murmushi tayi mata mai sanyi tace"sorry my little,ban cikin natsuwa ne kiyi hkr kinjiko."
Tana murmushi tace "bakomi Adda nayafe maki,kinje gidan Antyn."
D'an waken take ci cikin rashin kuzari,har yanxu amon muryarsa takeji sadda yake mayar wa da Abban feea magama cikin,kunci da bayyana bakin cikin da yake ciki.kamar bazata tan ka ba tace"banje ba yesmin,ban samu time ba kilan sai gobe."
Ko kwatar dan waken bata ciba ta ajiye tace "na k'oshi mamana."
Cikin kulawa tace"haba yar sofyna mekikaci anan kefa kikace yunwa kikeji,anya kuwa bakina b'oye man wani abuba."

*wlh saboda ku yau banci abincin rana ba sai la,asar kuyi manage pls,sannan inhar banga comment 70% ba gaskiya zan dakata da typing,don haka na nuna bakwa jin dadinsa.*

Mrs Bb
Mom muhseen. Lov u all masoyanaπŸ˜˜πŸ˜‰
[7/16, 6:20 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........6

Runtse idonta tayi ta bud'e tace"Aa mamana,babu abunda nake boye maki kawai dai banjin dadi ne kwata-kwata."
Yesmin duk ta koma kalar tausayi don jin halin da yayarta ke ciki.
Wayar maman ce tayi kara yesmin ta dauko ta tana cewa"wlh Anty ce ai daman nasan tunda kikace bakije ba wlh saita kira."
Mika ma maman wayar tayi tana zama kusada Addarta.
Daukar wayar maman tayi tare da sallama.
"Mama ina fiyah,wlh ranta sai yayi mugun b'aci yesmin bata gaya mata sakona ba."
Shiru maman tayi har saida ta gama sannan tace"sallama ta ma bazaki ansa ba jamila zaki hau yimun sababi,ko nice sofiyyar ne ban sani ba."
Cikin tausasa murya tace"Aa mama ba haka bane kiyi hkr."
Itama cikin d'an fad'a tace"aikin tambayi dalilin rashin zuwanta bawai kihau yin fad'a ba,."
Sake kwantar da murya tayi tace"to mama kiyi hkr don Allah,meyasame ta ina take ban ita."
Fiyah na kwance har lokacin kan cinyar mamar idonta lumshe eyelashes dinta sun wani kwanta gwanin sha,awa tunani take ta yadda zata shiga rayuwar *ALFAH* taji waya kan kunnenta maman ta aza mata.
Cikin cool voice dinta tace"Anty ina wuni."
Daga can ita ma face"lafiya lau fiyah,lafiyarki kuwa naji muryarki tayi sanyi sosai."
Gyara kwanciyar ta tayi tace"Anti kiyi hkr wlh nataso banda isassar lafiya,kaina naciwo ga gajiya shiyasa ban biyo ba,amman insha Allah gobe ina nan zuwa."

Ajiyar xuciya ta sauke tace"daman muhseen ne yake son kuyi bankwana zai koma spain,yama tafi aman yabar sak'o abaki."
Haushi taji ya kamata yadda Antyn ta matsa mata akan wani muhseen,itafa bata ra,ayin wannan guy din mai shegen yangar tsiya kamar mace,ta gode Allah ma daya tafin.
"Toba ma saina zo ba kenan."
Cikin fad'a tace"ban son iskanci bacin kinji nace maki yabar sak'o,to mezanyi dashi in baki zo kin ansa ba."
Dariya tayi k'asa k'asa tace"to zanzo goben insha Allah agaida man uncle da onborn baby."
Ta fad'a tana dariya.
Tace"marar kunya kawai zakizo ki saman."
Tana dariya ta kashe wayar.
Antynsu akwai zafi itada yayansu jalal,ga saurin hagula,dan danan zaka bata masu rai amman dan danan zasu sauko,daga mamansu har baban su babu mai tsananin su,suma wajen kakanni suka gado.
Itada yesmin kuwa sanyin su har yakusan yawa,amman ita fiyah akwai lokutan da takeda zafi,zafinma sosai amman tana daukar lokaci baka ganta cikin irin wanan yanayin ba.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Tun da suka shiga cikin gidan Alfah ya zube cikin falon yana wani irin huci na ban tsoro,malik ya rasa gaba d'aya natsuwarsa duk ya gigice yana jin wani tsananin tausayinsa yana cika zuciyarsa,bai wuce abunda ya faru tsayin shekaru ba yake dawo mashi sabo,saboda aduk sanda akai wani abu daya tuno mashi abun,ko yaga wani nashi ko wanda abun ya shafa,to fah wannan halin yake kasancewa cikinsa,koma fiye da haka........tunaninsa ya katse jin sautin kukan sa kallonsa yayi cikin tausayawa jin yadda yake kukan cikin bayyana tsananin kuncin da zuciyarsa take ciki,duk da yana tsoron tun kararsa ahaka cikin wannan yanayin nasa. zuciyarsa takasa hkr ya nufesa shima kwallar cike da idonsa.
Durk'usawa yayi gabansa yadafa kafad'arsa yace"kayi hkr Alfah Allah yana sane dakai............cikin wani irin yanayi na zuciya da fushi ya watsa malik gefe muryarsa har lokacin bata fita sosai yace"hkr,hkr fa kace inyi. bazan ba bazan tab'ayin hkr ba malik,antozartani anci mutuncina an goge duk wani kallon kima da mutunci da masoyana kemun,an yayatani ga media........cikin sarewa ya silale k'asa cikin shashshekar kuka kamar ransa zai fita ya cigaba da magana wadda ba sosai kakejin taba muryar ta dishe sosai cikin kuka da tarin kunci yace.
"Suka Koran,sun aibatani sun zagan sun wulakantani sun lalata man carria,sun lalata sunana duk inda na shiga k'yamata ake aibatani ake,zagina ake babu maisona........malik babu maisona duniya ta tsaneni duniya na mun kallon fasik'i,wlh malik niba fasik'i bane ban fab'a ba bazan tab'a ba kayarda niba d'an iska bane kamaryadda sukace ko,?kayarda ni mutumen kirkine ko?"
Malik kuka yaci karfinsa isowa inda yake yayi ya rungumeshi yana kuka iyakar karfinsa shima ya matseshi kamar zai ballashi tare suke kukan kamar yanzu abubuwan ke faruwa.
Cikin kuka malik yace"kai mutumen kirkine,kai ba dan iska bane kai ba fasik'i bane ABDOUL-NASSER kamilin matashine,natsatstse mai addini mai girmama nagaba dashi,burinsa shine ya tallafawa masu karamin karfi,mai biyayya g iyyensa..........yaja numfashi yanajinsa yana ajiyar xuciya bugun zuciyarsa yana raguwa cigaba yayi da cewa"sharrin macene yaja maka duk wannan Alfah,kaddarsrka tazone ta wajenta karka zargi iyayenka abunda suka gani dashi zasuyi anfani.........fincikoshi yayi daga jikinsa idon nan babu kyan gani yatura shi kan kujera kamar ba shine yanzu yayi sanyi ba.
"Karkasake mun maganarsu,natsanesu ban sonsu har abadan bazan sosu ba."
Malik na hawaye yace"Alfah kagane mana...........bazan tab'a gane wa ba,kafita anan ban son ganin kowa karka sake zuwa inda nake,nagane cewar kaima munafukine baka kaunata nace kafita!!! Yafada cikin ihu da har gagi.
Malik na kuka ya fita ya barshi.
table din glass dake tsakiyar falon Alfah ya dunga duka har saida ya tarwatse,ya dunga boll da duk wasu kaya dake cikin falon,masu fashewa nayi masu watsewa nayi.hankalin malik inyayi dubu ya tashi kuka yake yaciro wayarsa yana kokarin kiran Daddy,tsotsai yasa wajen sauri wayar ta silale ta fad'i aikuwa fuskar wayar ta fashe,..........cikin haushi da takaici ya zube kasa yana dora hannu saman kai.
"Wannan wace irin rayuwace haka,har sai yaushe abubuwa zasuyi sauki,cikin kuka da magiya yake rokonsa,Alfah karka raunata kanka,inbaka son rayuwarka ni inasonta kayiwa girman Allah kadai na."
Amman Alfah baijin ma komi malik yake fad'a saida ya hauka ta falon yajiwa kanshi raunika sosai.
ya zube yana kuka mai cin Xuciya,yanajin wani irin ciwo cikin zuciyarsa jiyake kamar yacirota ya jefar ko zai daina jin wannan ciwon amman kamar tira mashi ciwon ake frig ya nufa ya dauko kwalaben giyarsa ya cire masu hanci yadunga bulbulawa cikinsa,daya shanye sai ya dauko wata itama ya gama mata aiki,atakaice saida Alfah yasha kwalba biyar,amman baiji koda kadan cikin ciwon daya keji yaragu ba,a haukae ya dauko kwalbar daya shanye giyar ya buga ta da kasa ta fashe,ya dauki b'allin kwalbar ya saita jijiyar hannunsa zai yanke yaga hakan bai mashi ba,ya jefar da kwalbar yafasa wata irin kara yabuga kanshi ga bango sai gashi ya xube kasa babu numfashi.

πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž

Da dadare bayan sun gama cin abincin dare wanda har lokacin fiyah bata daidai taba,gata nan dai kadaran kada han ko baban su saida ya tambaya ko tana lafiya tace kanta ke ciwo amman tasha magani yayi sauki.
Bayan ya gama cin tuwonsa yafita waje wurin d'alha da radion sa ga hannu.
Hira suke cikin gidan yesmin ce keta ba mama labarin yadda jara barawar su ta gobe zata kasance masu,fiyah dai tayi lamo gefe tana sak'awa tana kwancewa tab'ota mama tayi tai firgigi ta juyo tana kallon maman.
"Sofiyya,kallan ninan bazaki iya boye mun damuwarki ba saboda yana yinki ya nuna cewar damuwar babbace,kuma tana damunki matuk'a don najima ban ganki cikin wannan yana yin ba,don haka maza gaya mun abunda ke damunki yanxu nan."
Raurau tayi da ido zatai kuka don bata san taya zata gaya ma mama abunda ya faruba,amman dole zata boye wani abun don tasan makamar abunyi.
Cikin dakoya da kokarin boye abunda ke ranta "tace mama bafa wani abu bane kawai dai wani abune daya faru yake daure man kai tunda abun yafaru duk nakejin babu dadi."
Duk natsuwa sukai suna saurarenta mama tace "inajinki meye ne Allah yasa ba akan karatunki bane."
Kwanciya tayi jikin yesmin dake gefenta tace"wanine yayi hadari bakin titi,yawwa mama inkin tuna rannan wanda nace maki ankasa tai makarshi."
Cikin kulawa da maida hankali kan abunda take cewar tace mata"eh natuna sofyna meyafaru bayan nan."
Ta sake mazewa yadda maman bazata gano komi ba tace"wlh mama abunne yaketa damuna tun rannan to yau naga mutumen kamar wani mahaukaci bakin titi yaci kwalar wani mutun daker aka kwaceshi,ni mama sai nake ganin kamar nasan shi wlh,kuma abunda yaban tausayi gareshi mutane sun zagayeshi sai duka suke ga wani Alhaji sai tijara yake yana zaginsa maganganu marasa dadi hada ce mai wai iyayensa ma sun gaza dashi balle wasu,abun dai babu dadin ji wlh harfa cemai yake dan iska fa mama.wlh yaban tausayi ya kira yan sanda suka tai dashi.
Naji mai taxi din daya taho damu nida wani yana cema wanda ya dauko mu tare wai kowa yasan shi dan iskane kuma da iyayensa masu hali akwai abunda yayi suka korai."

Shiru mama tayi tana jin abunda fiyah ke sanar da ita taso d'ago wanda take maganar kanshi amman bata tabbatar ba,cikin kulawa tace mata"dawa kikace yake maki kama."
Aranta tace yawwa anzo wajen don daman so take tasan dagaske dan gidanne kuma me ya fiddashi inhar dan gidanne.
"Mama yama sunan wancen mutumen mai kudin unguwar nan,uhmmmm yesmin yama ni wlh mance sunansa nake ma saboda mugun halinsa."
Tayi hakane don ma kar mamar tagane dagangan tayi haka........cikin sauri yesmin tace "nagano shi wlh,mu'azzam canji tabbas sunan kenan ko mama."
Wani irin kallo mama kewa Fiyah cike da tuhuma ganin haka yasa fiyah takiyarda su hada ido da maman don tabbas idan suka hada ido tasan zata gane karya tasheka mata do dai ta samu wani bayani.


More comment more typing.

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[7/20, 8:44 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ..........8

Kallon gidan take cike da sha,awa shuke shuke ne masu ban sha,awa take kallo dake can cikin guiden.
Yana gaba tana biye dashi baya har zuwa inda wata rumfa take ta cicci,irin dai rumfunan nan da akeyi na shak'atawa.kujerune masu kyau wajen,yaja mata daya ta zauna,sannan yace"Ina zuwa plz."
Hanya ya dauka yashiga cikin gidan nasu,don inda ya sauke tan cikin compound din gidan ne.
Bai Jima ba yadawo yana rik'e da Dan tire na silver mai shegen kyau.
Ya ajiye gabansu ya zuba mata ruwan Lipton cikin wani d'an cup Mai daukar ido,ya tura Mata wani had'ed'den cake yace"bismillah."
Murmushi tayi tace"am OK banajin yunwa."
Rungume hannu yayi ga kirji yace"bakiso mu yi magana kenan."
Rausayar da Kai tayi tace"yi hkr zansha."
Ta dauki cup din ta d'an kurb'a ta ci cake d'in kadan shima sannan tace"kamar yadda kaji sunana haka yake,zuciyata ta cika da tsananin tausayinsa bansan dalili ba,amman abunda na sani shine inason taimakonsa,yadda abunda ya faru station hakan ya nuna man Abokinka yana cikin tsananin bukatar mataimaki,duk Wanda zaigansa sai ya gane cewa yana cikin tsananin damuwa da kuncin.malik da zuciya guda nazo wajenka don Kaine zamu had'u mu fiddosa daga cikin duhun da yashiga,akoda yaushe fuskarsa babu walwala babu rahma,duk da ganina dashi bai wuce uku ba Amman na lura da hakan.ya kake ganin za,ai,don tun jiya dana koma gida ban samu natsuwa ba saida na samu wasu bayanai wajen mahaifiyata."
Shiru malik yayi yana saurarenta wani dadi yakeji jin irin abunda tazo dashi,hakika hakan yayi matukar yimashi wannan wata dama ce tazo mashi don haka bazai yi sanya ba,jin kalaminta na karshe yasa ya nisa yace"me mahaifiyar taki ta sanar dake."
Sauke ajiyar zuciya tayi tace"nayi Mata tambaya ne akan abokin naka."
Sake jefo Mata wata tambayar yayi yace"mekika ce Mata kenan."
Murmushi tayi tace"nace mata ne Abokin ka yana mun kama da yan gidan Alh muazam shine take sanar da cewa ai Karon gidanne shine babba,naso na sake samun wasu bayanan Amman tace baza,aji mutuwar sarki bakinta ba."
Jinjina Kai yayi yatashi daga kwanciyar dayai cikin kujerar yana gyaran murya yace"naji dadin maganarki sofiyya,ko dai ince fiyah kinfi jin dadinsa."
Dariya tayi tace"no i like inji ankirani da full name dina."
Smile yayi ya cigaba da cewa"tabbas kamar kinsan neman wacce zata taimakeni nake,don kuwa lamarin Alfah kullum sake hauhawa yake,tsawon shekara biyar da wata biyar kenan.hakika Na yarda dake sofiyyah,kuma insha Allah Allah zai cika mana burin mu,sannan kamar yadda kikaji cewar Alfah dan gidan Alh Muazzam ne haka maganar take,dan sane na cikinsa,Ku ma shine first born agidan,haka zalika shine kadai namiji sai karamin kanensa.mahaifiyarsa itace Mata tabiyu agidan Alh muazzam.labarin rayuwar Alfah labarine Mai tsawo fiyah,don cikin kwana d'aya bazan iya gama maki shiba,Amman tunda wanna Karon farkone na had'uwarmu insha Allah next inmun had'u Zan Fara warware maki labarin *ABDOUL-NASSER ALFAH.*."
Shiru tayi tana jinsa kafin tace"shikenan malik,xanjiraka akoda wane lokaci kabukaci gani na namaka alkawarin zuwa,Amman banda waya kaban no d'inka Zan nemeka idan nakoma gida,yanzu makaranta zanje inada darasi."
Murmushi yayi yace"babbar budurwa like u kice bakida phone har kuma kinshiga jamia,gaskiya baidace ba to yanzu ina Zan rubuta maki no d'in tawa."
Itama kyakkyawan murmushi tayi tace"karanto mun zakai Zan iya rik'ewa."
Tafi yayi yana mik'ewa yace"good fiyah,gaskiya dagani kina da k'ok'ari a school."
Itama dariyar take sun jera suna tafiya zuwa k'ofar fita.
Tace"aa kawai dagiya ce irin tamu ta ma rasa galihu,kasan irinmu kobamuda kokari tofa zamu dage don ganin mun fita kunyar iyaye mu."
Murmushi yayi yace"kin fad'a ne don inyarda ko?"
Tad'aga Kai yace"to ban yarda ba."
Dariya tayi itama har zuwa sanda suka k'arasa bakin k'ofar yafara karanta Mata no dinhar karshe,yana gama fad'a ta maimaito masa itama exactly yadda ya karanto mata.
Alamar jinjina yayi Mata da hannu yace"good,dan banyi wanka ba dana saukeki,Amman duk da haka bari ga driver can saiya ya kaiki."
Tace"aa malik wlh ngd,Zan idasa da kaina sai munyi waya."
Sukai bankwana ta tari taxi ta wuce makaranta.

Lectures sukai yau masu zafi,don semester tazo karewa shiyasa KO wane malami soyake yayi covering Kan lokacin exam yayi don har sunfara test ma.
Sun had'u da feea cap wajen cin abinci take cema ta.
"Fiyah ashe guy d'inan bakaramin k'usa bane aharinnan,kinsan kowaye babansa kuwa."
Fiyah saita nuna kamar bata sani ba cikin mamaki da al,ajabi tace"Kai haba,bani insha."
Tace"kinsan Alh muazzam canji,na cikin estate dinmu,to wlh shine ya haifesa wani babban laifi ya aikata ma shi ya korai tsawon shekara da shekaru kenan,nayi nayi da momi aman tace baruwanta wlh."
Jinjina kai kurin fiyah keyi tace"lallai banyi mamaki ba,saboda tun farko naga muguwar kamarsa da y'angidan.Allah ya kyauta gaba ya sasatanshi da iyayensa."
Feea tayi tagumi tace"wlh yaban tausayi jiya,tsoro naji ai karya shak'oni ya dunga jibga karshe ya kasheni abanza.don naga jiyake da karfi kamar doki."
Dariya fiyah tayi tace"ba take yake ba lokacin ai."
Feea tace"wlh kuma guy din ya gama had'uwa ban tab'a ganin ruwan kyau ga namijiba irin nashi Zan so in samu saurayi kamarsa."
Dariya fiyah tayi tana kallonta tace"kozaki shiga daga ciki naimaki hanya."
Zaro ido feea tayi tana rufe baki tace"rufaman asiri wlh ko k'ashina bazai bari ajikina ba,keee wannan guy d'in banga fitsararrar dazata tunkarai da maganar soba,aikoba so wannan ixxarsa ma da kwarjininsa sun sata rugawa,balle yadda naga yana da bakar zuciya."
Dariya kurin takeyiwa feea ganin duk ta rud'e lokaci guda alamun dai wannan Marin bata manta dashi ba.

Karfe d'aya da kwata tafito daga cikin makarantar,feea tace tazo suwuce tace ai bagida tayi ba,zata dawo karfe hud'u suna da test.
Bata sha wuyar samun abun hawa ba tawuce gidan Anti jamila,don yau idan bata jeba tashiga ukunta wajenta,takakkiya zatayo Mata har gida.
Babu laifi mijinta yana dashi,don babban gidane Mai plat biyu shiga tayi tana doka sallama,Mai aikinta ce take ta ansawa,shiga tayi cikin falon tana kallonsa an sake mashi kujeru da TV plasma,ansaka wata kantamemiya ga sabon canis kafet Mai shegen laushi,andai gyara falon kamar na sabuwar amarya,bama falonba ta lura gyaran duka gidanne.
Magana tajiyo cikin bedroom d'in kamar ita da wata ne, kasa kunne tayi tajiyo muryar wata tana cewa"wlh jamila maganin nan shayanzu magani yanzu,kinsan da kanwata tayi anfani dashi,saigata da kanta tana nemana ruwa ajallo,dakau kamar bazata siyaba,kinga wannan sunan sa rijiya tunjum,wlh shima badai aiki ba nake gaya maki makociyaya data siyai,can cikin dare naringa jiyo ihun maigidanta,washe gari saigata wai insiye matashi duk,Abban Ahmad bai tab'a Mata kuka ba insuna tare sai jiya,ai ban sayar da kayan banza kinsani.yo in gaya maki da mijin yayata dan rainin wayau ne,yaraina ta nake gaya maki,baya kusantarta saiya ga dama haka bai zaman gida,ke Abu yazo har yakai ga Saki jamila,dakerfa iyaye suka shiga lamarin,lokacin Ina Ibadan Dana dawo lokacin ta koma najefa na tsumata,nahad'ata yadda yakamata karshe saigashi duk inda zata shine kekaita yana rik'eda jikkarta."
Ajiyar xuciya ta sauke tace"lami ya isa haka,ki ajiyemun wannan da wad'annan,na wane kud'insu."
Tana washe baki tace"wlh don kece Zan maki sauki ki bada 10k ai babu cuta tsakaninmu."
Tace"toshike nan ki ajiyemun sy wajenki karki sugar wa da kowa,in na ta shi zan ansa."
Dahaka suka fito tana yimata sai anjima,ganin fiyah falon yasa ta rik'ebaki tace"shegiya kin zo shine baki sallama."
Matar ficewa tayi tabarsu fiyah tace"anti ya za,ai kiji bayan kunshige ciki sai ciniki kuke,wai anty da wannan uban cikin ma sai kinsha kayan Mata,baki bari ki haihu."

KUYI HKR WLH NAGAJI,MUHADU GOBE IDAN ALLAH YASA MUNKAI DA RAI DA LAFIYA.

MRS BB
MOM MUHSEEN.
[7/22, 9:37 PM] Mom Muhseen: πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
πŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’žπŸ’ž
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

πŸ…ΏοΈ.........9

"Don ubanki cewa nai zan sha."
Dariya fiyah tayi tana kunna kayan kallo tace"Allah yabaki hkr,naji ai sai bayani take kora maki kuma inba siye zakiyi ba mezai kawota."
Tsaki taja tana shigewa wata k'ofa tana cewa"to siyen zan don uban mutun ya hanani,ince kud'i nane bana wani ba."
Fiyah dai dariyar take don sun saba indai halin anty jamcy ne.
Fitowa tai da wata fation leda ga hannu ta zauna daker don cikinta yatsufa.
Tace Mata "inkina jin yunwa ga abinci can kan dining,akwai kunun aya a

1 Comments On ABDOULNASSER ALFAH
avatar
mahmud-maaji

1 year ago

Reply

It is a very interesting book

Please Login or Register in order to submit comment