Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

gidan wuta Allah kadai ya rayani bacin bakar wuyar danasha asibiti.saida nayi wata uku kwance,wata diyar yayar babana ta yi jinyara,itace ta cigaba da rik'eni har Allah yasa na mallaki hankalin kaina.ninake dauwainiya da kaina in biya kudin karatuna,babu irin sana,ar da ban ba ahaka har na samu nasarar shiga jamiar yar aduwa university.anan nayi karatuna na business administration,Alhamdulilah nasamu result mai kyau ina yin graduation mijinta yace inzo muje abuja inda yake kasuwancin sa,ahanyarmu ta zowa aka kirasa matarsa da d'ansu mota ta banke su sunrasu.
Juya wa mukai muka koma akai zaman makoki naji wannan mutuwa kamar kamarme nadade ban dawo daidai ba,karshe shi bai dawo abuja ba sainine na biyo hanya nazo na kama hayar shago inda yan kudina naja jari nacigaba da yan buge buge na.kaji asalina kaji karatuna yanzu haka banfi shekara biyu dana gama service ba.inanan ina tara kudi zan koma masters."
Jinjina kai kawai Alfah yake yana kallona kafin yace"gaskiya kai namijin gaskene malik ka burgeni Allah yajikan iyayenka yakuma gafarta masu da ita ma marik'oyar taka,abunda za,ai tashi zakai muje part dina kaga d'akinmu don gado daya zamu ringa kwana,zan gabatar dakai wajen mami da Abbi idan ya dawo don tuntuni nayi mashi maganar itama mami harta zak'u da son ganinka inyaso anjima ida kahuta saimuje kakwaso kayanka zuwa safe saimu fita muje kaga komi yadda yake,fatan zaka daukeni kamar d'an uwanka na jini don ni tun randa na fara ganinka ka kwanta man Arai naji ina sha,awar taimakonka don allah malik kazama mai rikon amana karka bari wani yabiyo ta wajenka ya cutar dani,zan iya yafe komi amman banda cin amana banda munafurci Don Allah ka kula,Allah yabamu sa,a ya karemu daga makiya."
Tundaga ranar nazama d'an gida mami mahaifiyarsa jitake dani kamar dai Alfah haka ni'ima yaya sama yaya k'asa,haka wajen Abbi ma na samu karb'uwa sosai don min saba kamar yadda yakeyi da Alfah haka nima yakeyi dani,saidai bangaren umma ko kusa hakan yayi wuya,itadasu zuwairat kamar su cinna man wuta zakiyya budurwar Alfah kawai muke gaisawa sosai ta dalilin kaunar da takewa Alfah,soyayya suka buga kamar zasu cinye juna,basa iya yini zungur basu ga juna ba ko basuni muryar juna ba,duk irin yadda Alfah yake cikim busy to kau yana da time d'in zakiyya.
Kwatsam rannan ya kirani yace ina dauko zakiya intaho da ita nan company sa na fation&designer's gallery's,yinin yau bai ganta ba kuma basuyi waya ba,gashi bazai dawo ba sai dare can.
Waya mukai da ita nace ta saman bakin titi don ma karwani cikin su haulat ko khadija wani yaganta da ni don ranar saita ci bugun tsiya.
Tayi sa,ar samuna bakin titi muka wuce can wajensa,duk yana yin ta babu dadi nace mata"zakiya lfy dai ko,naga duk fuskarki babu walwalah."
Idonta ya kawo ruwa tace"yah malik ina son yah Abdoul,wlh nikaina ban son irin son danake mashi ba,duk wannan bashine damuwata na damuwata itace yadda umma taketa bin kwakwkwafina,ko unguwa nace zanje sai tayi tayi man question daker nake samun nasarar kuccewa,yauma kamar bazata bari na fito ba saida nayi mata karyar cewar makaranta ake nemana,duk abunda su khady keyi dasu yah Amina bata yi masu wannan bin kwakwkwafin saini da nake iyakar kokarina don ganin na kare mutuncina."
Hkr na bata ina kwantar mata da hankali har mukaje company har office d'in sa yana fa fama da files,da resit.
Ya na dora idonsa akanta ya lumshe idon,yana sassanyar murmushi mik'ewa yayi ya fito daga cikin sit din yana bude mata hannunsa.nidai gefe nai ina kallonsu don Alfah ya iya soyayya idan yana son mace,to kau babu abunda zai iya dauke mashi hankali akanta,kuma baya jin kunyar nuna ta gaban kowa.
Isowa yayi gabanta yana langabar dakai idonsa akanta murmushi yayi yace"Alhayat,meke damunki ban saba ganin haka ba karki cutar dani zuciyata baza ta dauki wannan canji naki ba."
Kwallah suka cika mata ido zatai kuka ya tallabo hab'arta yana kallon idonta,cikin sanyin murya yace mata"nasan damuwar,yauma an maki abunda aka saba ko,plss karkiyi kuka nima zan iyayi bazan iya jurar kwallarki na zuba ba,insha Allah komi zai wuce kwanan nan zan jewa Abbi da maganarmu,ayita takare abunda kawai zan ja hankalinki shine duk rintsi duk wuya karki jiya man baya,karki yarda abiyo ta wajenki a dakile mana farinciki.zakiya ban tab'a son wata kamar ki ba,haka bazan sake son wata ba har duniya ta nad'e da kina raye da baki raye.duk bala in umma gabanta zan daukeki na bar gidan dake ranar da kika zama mallakina,naje har bakorin na samu yayan babanku munyi magana wlh zakiya idan kinga ban sameki ba to kece kikace bakiyi dani."
Share kwalla take tana jin tsananin kaunarsa taya ma zata bari umma ta rabata da wannan tsalelen guy,tasan har abada bazata sake samun kamar sa ba,bacin haka Abdoul na da kudi bata da burin daya wuce ta zama matarsa,kodan ganin ta tsunduma cikin dukiyarsa.
Cikin zubar kwallah tace"ka dauka kaine mukulli da kwadon xuciyata yah Abdoul,daga kan ka na rufe na jefa dan mukullin cikin rijiya mai gaba dubu,wlh ni kaina nasan bazan iya rayuwa mai dadi babu kai ba,ina jinka kamar yadda nakejin numfashina,amma ina tsoron kaidin umma kasancewarta uwa ta amman wlh kaidinta yafi karfina don Allah ka sama mana mafita in fita daga cikin wannan tsoran."
Lallashinta yayi tayi malik dai karshe fita nai nabarsu sukaci kaunarsu yadda suke so sai shidda suka tashi tare suka koma gida.wai ashe tun bayan tahowar mu khady na biye damu har wajen company.
Dadaddare muna cikin harabar dake gaban part dinmu ta kirashi.
"Yah Abdoul kana shan kunun aya dakaina na yi inason kasha kaban maki yah zuwairat ce tace wai baiyyi dadi bah."
Murmushi yayi yana operating system yace"aike Hayaty ko kasa kika dama dadi take balle kunun aya,wow zan so insha inji how fah."
Dariya tayi tace "kana ina inzo yanzu "
Gyara zama yayi yana jin dadin muryarta yace"cikin rufa gaban part dinmu."
Saida suka gama magana nace mashi"Alfah ina ganin akwai damuwa,dazun fa khady ta biyomu har company,kudaina yawan had'uwa ina jin tsoron kaidin umma,ba kamar idan tasan aboye kuke soyayyar."
Mirmushi yayi yace"kyaleta ai gobe zan ma Abbi maganar nasan zai mata magana awice wajen,inason zakiya bana jin dar akan duk abunda umma zatai inhar zakiya bazata kwaremun baya ba."
Ban sake magana ba saiga ta tazo ta kawo nan suka shiga kaunarsu kamar ma bana wajen,daga nesa na hango kamar inuwar mutun,na sake kalla wa sosai na gango mutunne kuma hoto yake dauka,tashi nai na nufi wajen kafin na isa ta gudu amman bazan iya gane ko wacece ba.
Dawowa nai ban dai sanar da kowa ba sun jima suna hirarsu sannan tatafi.
Haka lokaci yayata ja Abbi baya zaune Alfah bai samu damar sanar dashi kaunarsa da Zakiya ba,shima kuma ayyuka sun tasushi gaba,don ya fara shirin yin wata tafiya zuwa paris zai d'an jima,ni kuma switheland zanje shigo da wasu kaya da za,a xuba cikin store din Alfah.
Hakanan naji ban son intafi mami ce keta ban kwarin guiwa har nasamu natsuwa,nariga Alfah tafiya da kwana uku sannan ya tafi.
Awannan tafiyar fiyah komi ya faru,don ya rigani dawowa ranar dana dawo na iske wannan tashin hankali,Abbi yasa sojoji sun rik'e Alfah sai dukanshi yake yana halbinsa,yayinda yake kuka yana cewa.
Nayi dana sanin haihuwarka,na gwammace ace b'arin cikinka uwarka tayi da dai inga wannan ranar,matata Abdoul bayan ka gama lalata d'iyarta shine ka dawo kan uwarta,ashe kai mazinacine dan iskane kai,har giya kakesha Abdoul,giya kasha giya agidana menayi maka mena tare maka kakeson kasheni da bakin ciki........kuka yake sosai an rasa mai cetonsa.
Yayinda umma ke gefe tana cewa "Alh in baka kori wannan dan iskan agidan nan ba ni zanbar gidan,kuma wlh saina gurfanan dashi gaban hukuma,Allah na godema da bai bani d'a namiji ba da dai wannan masifar......ta rushe da kuka gefe guda ma ga zakiya kukan take kamar ranta zai fita.
Zuwaira da haulat suna gefe saidai su shige cikin abaya suyi dariya,idan kika ga Alfah awanan rana saikin masa kuka,jikinsa ko ina jinine saida Abbi ya gaji ya kyalesa.
Mami saboda tashin hankali ta kasa kuka saidai ni'imah dakeyi.
Kan kace me harabar gidan ta cika da mutane,anan Alh kwangila yake tambayar Abbi lfy yake sanar dashi cewa cikin kuka.
"Kwangila nai nadamar haihuwar Alfah,Alfah ya kasheni Alfah ya wulakanta ni matata ta sunna yasha giya yayi tatul yayi mata fyad'e,bayan lalata yarta da yayi zakiya ya mata ciki kuma saboda rashin imani ya kaita aka zubar,gashinan yarinyar ta samu matsala.......mezanyi da Abdoul arayuwata na tsaneka na tsaneka Abdoul har abadan abada baxan yafe maka ba.......afusace ya nufesa yana kukan yace"tashi don ubanka d'an iska wulakantacce,babu ni babu kai na yafeka daga cikin zuria ta,idan kabari nasake ganin fuskarka arayuwata saina ga bayanka......wlh kasheka zanyi.
Nan fah mutanen wajen suka ringa zagin Alfah suka ringa tsine mashi albarka,ba kamar Alh kwangila yafi kowa zak'ewa har Alfah ya kasa jurewa cikin wata irin xuciya da ban tab'a ganin Alfa ciki ba ya shak'esa yana wani irin kururuwa saboda zafin xuciya.
Ya d'aga hannu kenan zai kai mashi duka Abbi ya daka mai tsawa yace"kana dukanshi ina tsine maka Alfah,wlh tsine maka zan kabi duniya......zaka sakai ko kuwa"
duk ga yan jarida nan yau sun samu kanun labaran da zasu yad'a su samu kud'i.

"Inajin mutsaya nan fiyah kije kiyo test dinki zuwa gobe ma k'arasa,duk da mun kusa karashewa."
Kwallar dake zubar mata ta share tana kallonsa shikuma yana mata murmushi tace"yah malik Gaskiya abokinka yaga rayuwa,ko ince yana cikin gani meyasa haka ta faru waye da alhakin wanan,wlh zan iya rantsewa bazai aikata haka ba.ayadda naji halayensa naji araina akwai wata ak'asa don Allah ka karasa man na yafe test din anmun makeup."
Dariya yayi yace"rufan asiri kije kiyi test dinki wlh,kodai malamin saurayinkine da har zaiyarda yayi maki wani make-up."
Murmushi tayi had'ad'd'e tace"aa yayan qawata ne kawai muna mutunci."
Mik'ewa yayi yana kiran wani dake wajen yace ya hade abubuwan yayi takeaway dinsa,ya je ya nad'o naman dubu uku mai zafi.
"Kitashi Allah bazan bari ki rasa test din kiba,muje ga mota na can saina saukeki."
Ana kawo mashi ya jawo jakarta ya saka kallonsa tayi tace"yah malik duk nid'aya don Allah kabarshi za,amun fad'a agida fah."
Hanya ya bata yace"no karki bari amaki fad'a in kinje school kici keda qawar fadan Alfah."
Dariya sukai suna dosar inda motar sa take.


*inhar banga comment daya wa ba bazan kara typing ba har sai sabuwar shekara.*

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[8/2, 12:37 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

INA TAYA DUK KANIN MASOYANA MAZA DA MATA MURNAN BARKA DA SALLAH,FATAN ANYI SALLA LAFIYA UBANGIJI ALLAH YAYI MANA TSAWON RAI DA LFIYAR GANIN SHEKARA MAI ZUWA MOM MUHSEEN TANA MAKU FATAN ALKAIRI.


🅿️.........13

MALIK har cikin makarantar ya sauke ta tana masa godiya tare da cewa.
"Yah malik sai yaushe kenan"
Shafa kansa yayi yana murmushi yace"i think sai kin samu time,don naga satar hanya kike."
Dariya tayi tace"wlh yah malik kamar kasani,amman insha Allah gobe zan kokarta infito don hankalina bazai kwanta ba har saina naji karashen wannan labarin,wlh yah malik abokinka yayi matukar ban tausayi,anya zan iya bacci kuwa?wlh labarin yasa na sakejin tausayin sa na kara jin kwarin guiwar taimakonsa."
Jinjina kai yayi yace"karki damu kiwuce karki bata lokaci good luck Allah ya sa ki cinye Duka."
Tana dariya sukai sallama ta wuce ciki bin bayanta yayi da kallo yana ayyana wani abu aransa,murmushi yayi mai tsananin kyau yace "wannan takun ma zai bada kala,zai taimakemu sofiyyah."
Tashin motar yayi yabar cikin makarantar,gida ya wuce don duba Alfah.
Motar Daddy ya gani alamar yazo parking yayi ya fito ya doshi cikin falon.
Alfah na durk'ushe gaban Daddy shikuma Daddy yana ta faman yi mashi fad'a kamar zai ari baki,waje ya samu ya zauna yana kallonsu gaida shi yayi yace"rik'e gaisuwarka Abdoulmalik,yanzu gabanka Abdoul-Nasser yake shan win amman bakai kokarin sanar dani ba,giya fah giyar ma d most high one wadda zata iya kashe sa cikin k'an k'anen lokaci."
Cikin biyayya da taushin murya malik yace"Daddy wlh Allah yasani nayi iyakar yina,nayi nayi da Abdoul akan shan giyar nan amman kamar tunzura shi nake,nasha kwashe duk na cikin frig din gidannan in zubar amman saiyayi kamar bazai barni da raina ba akan haka,sannan yaje ya kwaso wasu wlh Daddy ban san yadda xan da shi ba,gashinan baya jin nasiha baya yarda da hukuncin Allah,yaki hkr yaki fawwala ma Allah lamarinsa,saboda an masa k'azafin shan giya to bari yasha d'in dagaske.kuma har likita yayi mun bayanin cewa yaci sa,a babba da matsalar da take kokarin bashi ba babba bace,don duk mai ta ammali da wannan giyar baya kai labari."
Jinjina kai Daddy yake cike da b'acin rai yana kallon alfah da ya sadda kai k'asa yana jin kamar ya kamasu yayi masu shegen duka.
"To yayi kyau,ni zan kwashe su na zubar don Allah ka sake siyowa kaji ko,nace ka sake siyo wasu kaikuma muddin baka sanar dani ba halin da yake ciki kaida Allah.idan shi yaya ya wofintar dashi hakan bai nufin Abdoul baida sauran na gaba dashi,don haka duk abun da yake ciki ka sanar dani zan dauki mataki mummuna akanka."
Ya tashi malik na tayashi suka kwashe duk wata giya dake cikin gidan suka je suka zubar............ko ajikinsa don ya sa aransa saidai giyar tayi ajalinsa,amman bazai daina ba.
Bayan tafiyar Daddy malik ya dawo cikin falon amman abunda yabashi mamaki cup ne hannunsa da win din aciki yana kurb'a yana lumshe ido........... Sorororo yake kalon sa yana mamakin ina ya b'oye wannan har basu ganta ba,takowa yake cikin falon ya iso har gabansa ya durk'usa gabansa yana dafa guiyawunsa cike da karyewar xuciya yace"haba Abdoul,meyasa meyasa bazaka barmu muhuta ba,bazaka bar kanka ya huta ba.duk abunda muke munayi me don gyaran gobenka,ina tsoron mutuwa ta riskeka acikin wannan halin,Allah babu ruwansa da kazafin da aka maka,har ka yanke wannan hukuncin,don babu ina haka yazo acikin qurani balle hadisi.kayiwa rayuwarka gata ka dawo cikin hayyacinka,kadawo kakoma ga mahaliccinka duk wannan zafin rai bazai canza komi ba,kakoma ga Allah ka rokesa ya bayyana gaskiya.amman ba ka nemi kaucewa addininka ba."
Saika rantse bada Alfah yake ba,shan win dinsa yake idonsa rufe yana girgiza k'afa,nan kuwa banda tafasa babu abunda zuciyarsa keyi,jiyake kamar ya cirota ya jefar,yana shanye win din yayi wata irin jifa da cup din yana bude idonsa akan malik.
Saboda masifa da tsananin xafin rai idon nan yayi wani irin fitinennen ja,da sauri malik yaja baya biyosa yayi shikuma yana sake ja baya,har yayi nasarar shak'osa ya dagane sa dabango idon nan kamar zai fado yake mashi wani irin kallo,cikin kakkausar murya yace.
"Bazan bar shan giyar ba,ehy nace bazan bari ba kabarin mu guda ne? to kashiga taitayinka ina d'aga maka k'afa baka gani ko,to kuskuren da zakai muyi hannun riga shine sanar da Daddy
Wani abu akaina marar dadi."
Ya watsar dashi nan kasa ya nufi hanyar fita falon,har ya kai k'ofa ya juyo yana kallonsa yace"inhar na sake ganin fuskarta agidannan saina kasheta ka sanar da ita wannan."

Mekenan yaga fiyah kenan rannan,Oh Allah na gode maka da bai zo yayi mata wata illar ba,kai wannan bawa naka ya Allah ka kawo mashi sassauci.

A makaranta fiyah sun had'u da feea,take mata maganar Alfah.
"Wai fiyah kinko sake ganin guy d'in nan."
Fiyah na duba question din da suka gama test akanshi yanzu ta ga ko ta ansa daidai,tace mata.
"Ni kuwa ina zan ganshi rafeea,wannan dan zafin kai ai haduwa dashi hadarine."
Dariya tayi tace"haka maganarki take amman kinsan tun daga wannan rana kullum yana cikin raina,tausayinsa nake sosai,inama zan iya taimakonsa inama ace ya dawo cikin natsuwarsa wlh ina jin kamar ina sonsa."
Dagowa fiyah tayi tana kallonta cike da mamaki da al,ajabinta tace"kina cikin hayyacinki kau feea,kirasa wanda zaki kamu da sonsa sai wannan guy d'in,to wlh ki shiga hankalinki inba so kike kirasa jinki ko ganin ki ba.yo daki tunkari wannan damisan mutumen ba gara kin rungumi transformer ba ki huta kawai."
Me feea zatai ba dariya ba,yitake har tana duk'awa saboda dariya.
Itama fiyah dariyar tayi tace'wlh kau kedai kiraba kanki da wahala kurin,kii da d'an salim dinki."
Haka suka ringa hirar suka wuce gida tare.
Sanda ta je gida har yayansu jalal ya dawo ta iske uwar tsaraba,rabin buhun dankalin hausa dana turawa,ga kayan miya kamar banza,ga ayaba da yayo masu kayanta.
Sai takalma na mata masu shegen kyau itda yesmin sai dinkunan baba kala uku hada babbar riga.
Duk na sallah ne dake gaba towa don azumin baifi saura wata daya ba,mama kuwa atamfarta maikyau da tsada da yafin abaya.
Gaskoya yah jalal badai hidima ba Allah yayisa mai zuciyar nema.
Don ko acan ba zaune yake ba yana noman rani acan,ga sim card dayake siyarwa yana samu babu laifi ga kuma albashinsa.
Ranar mun yini cikin farin ciki da annnashuwa don yah jalal yana sake mamu,duk da shima wani lokacin kamar Anty yake.
Baba daya dawo yaga wannan abun arxiki ya ringa saka mashi albarka,yana mashi addua masu kyau.bamu kwanta ba ranar sai sha biyu.
Da asuba na kira malik saida na kaikaici yesmin tana bayi.
"Yah malik na tasheka da sassafe ko."
Gyara kwanciyar sa yayi baccin bayan sallar asuba daya dawo,muryarsa cike da bacci yace "kin cancanci tashina ai,ya kika kwana."
"Lafiya lau yah malik,dama nace ina zan sameka zan fito karfe sha biyu."
Murmushi yayi yace" gida zaki saman."
Zaro ido tayi kamar yana ganinta tace"yah malik gida kuma?nidai aa kafito sai muje wani wajen gaskiya nidai ina tsoron wannan mutumen."
Dariya yayi mata don ya cire mata tsoron zuwan yace"ai bainan yau na samu na turashi company."
Ajiyar zuciya tayi tace"shikenan,amman ni gaskiya yah malik inajin tsoron sa karya mun wani abun don nasan wlh ya rik'e fuskata."
"Karki damu babu abunda zai maki ai inanan."
"Shikenan sai anjima."
Kashe wayar tayi tana sauke ajiyar xuciya gabanta yana faduwa,tana tausansa tana tsoronsa kuma.sannan burin taimakonsa baixai gushe daga ranta ba har sai taga Abdoulnaseer ya dawo ainahin Abdoul din da kowa ya sani.yesmin ce ta tab'ota tace"Adda tunanin me kike nafito inata magana bakijini ba."
Firgigi tayi yadawo natsuwarta "ba komi yesmin,ina tunanin test dina ta jiya kona rubuta ta da kyau gashi yau zai bada ita."
"Kai Adda keda duk abunda kika rubuta kinsan kinci kimabar wani kokwanto,ke ai cinyedu ce wlh."
Dariya tayi tace"ban son xiga fah,waya kaiki cinyewa keda yah jalal."
Nan suka ringa maida magana har gari ya idasa wayewa sukan hau ayyukansu na yau da kullum.
Bayan sun gama kalaci yesmin zata wuce makaranta tace ma mama"mama banga baba ba tunda na tashi,gashi zan ta makaranta karna makara."
Mama dake shan kunun ta tace"wlh ankirashi ne tunda bayan asuba,har yanxu baidawo yayi kalaci ba,amman kije kisamu yayanku ya baki kudin taxi karki makara."
Haka tayi masu sallama ta wuce itama fiyah bayan ta gama duk abunda zatai ta yi wankata kamar yadda ta saba,tasha kyau tsantsagoran sa don fadarsa ma b'ata bakine.
Yah jalal ya bata kudin taxi don har lokaci baba baidawo ba.
Tana isa k'ofar gidan kirjinta ya buga ta sallami mai taxi din ta shiga koran malik.
"Kayo ka shigo dani wlh atsorace nake."
Kashewa yayi ya fito yasha wanka malik badai gayu ba."wannan toron naki dole saikin barshi inhar kina son mucimma nasara,don idan yagane kina tsoronsa shikenan kin bani.don haka daure fuska zakiyi kisha mir kuma fuk maganar daya gaya maki kema kigaya mashi fiyeda wacce ya sanar dake,hakan da zakiyi shine zaizamo kamar makari daga zafin ransa akanki,don tabbas gamonki dashi dake nafarko nasan akwai dabi,kinsan randa kika fara zuwa nan gidan ashe yaganki,amman baimun magana ba sai jiya."
Gabanta ya fad'i amman tasa dakiya ranta tace"meyace yah mali."
Dariya yyi yace"cemun yayi ingayabmaki inhar yasake ganin fuskarki agidan nan saiya ka.......kafinmanyanidasa harta ruga ta koma wajen k'ofa.
Mezaiyyi ba dariya ba binta yayi har waje yana dariya yace"kekuwa ya da rugawa karai kicemun kinfasa wlh fadane kurun yake aibazai iya kisaba kalmrce ke bshi nishadi idan yana fad'a don ya torataka.......zomuje don Allah yau nakeson na idasa maki lbr abunda yafaru ko kinyafe."
Idonta yayi kwalkwal zatai kuka yadan sausauta dariyar yace"kinga wlh bazai iya yi maki wani abu ina nan ba nagaya maki ma baya nan ba yanzu zai dawo ba,karki damu kinko sofiyya."
Badan taso ba ta sake binsa abaya amman fah zuciyarta zillo kurin take...........

Mama nata hidimar sanwar rana dambu takeyi masu mai dadi na shinkafa,har ta dora hawan karshe saiga wasu mutane sunyi sallama gidan,abaya ta sanyo ta leko cikin zauren idinta na sauka kansu hankalinta yatashi cikin rudewa tace"jamiai lfy kodai b'atan kai kukai."
Daya daga cikinsu yace"munzo sanar dake ne mininki yana police station,an kamashi ne da laifin rashin d'a,a ga Alh muazzam canji don haka karku sha wuyar nemansa don yana wajenmu,ba kuma zai fito don yanzunba mun barki lfy,amman karku sha hawalar zuwa belin sa don babu beli saiyaje yari."
Silalewa tayi kasa cikin zauren ta fashe da kuka.

Mrs bb ce
Mom muhseen

09034722970.

Muddin comment bai haura 70% ba *ABDOUL-NASEER ZAI KOMA NA KUDI KOKUMA NA DAINA TYPING HAR SAI NAGA CANJI DAGA GAREKU.*
[8/5, 10:12 AM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........14

Wajen da ya sauketa wancen lokacin nan ya sake saukarta,bayan ta zauna yadan rusuna yace"hajiya me zakisha."
Murmushi tayi tana waigen nayanta tace"rufan asiri kaganni ko airport ni ban tab'a zuwa ba,amman karka damu kanka wlh bana son komi nidai kayi ka idasa mun infece kafin wannan boss din naka ya dawo."
Dariya yayi yana jan kujera ya zauna yace"kinga can gashi can cikin d'akin exercise yana ta faman G-ming kawai dai abunda zakiyi ya taimakeki fiyah shine jajircewa,da fitar sa tsoro acikin ranki koda kinajin tsoron karkibari ya fito kan fuskarki kisha mur kuma duk abunda ya fada maki kiyi kokarin maida mashi wadda ya gaya maki,koma fiye da haka ki fetsare idonki gabanshi,shine zaisa ya sassauta maki kuma hakan zai baki damar shiga jikinsa kuma duk abunda kika zomashi dashi zai yarda."
Murmushi tayi tace"uhmmm yah malik kenan nidai ina jinka kawai aman ina ni ina mayarwa da wancen gagaren magana."
Dariya yayi ya cigaba da sanar da ita cewa.
"Alh kwangila ne yace ma Abbi Alh muazzam zaman wannan yaron cikin iyalinka masiface babba,kamar yadda hajiya umma tace ka korai tokuwa hakan yafi dacewa,ka rabashi da kai ka ahalinka wannan shine mafita inba haka ba............cikin zafin rai da kunan zuciya Alfah ya shak'oshi iyakar karfinsa,ya ringa naushi ga fuska har hakorinsa ya fita,kuka yake yana cewa muryarsa duk ta dishe don kuka karya kake munafuki wlh baka isa ba kana gudun na fallasa.......kafin ya idasa abunda yakeson fada Mutanen wajen suka ringa janshi suna raba shi da Alh kwangila,daker aka rabasu inkinga yadda kirjinsa yake d'agawa saikin zata xuciyarsa fitowa zatai.Abbi ne ya iso wajen yana huci ya fizgoshi bai diresa ko inaba sai gaban mami wadda sai lokacin ta samu hawayen yin kuka,cikin kakkausar murya yace"zan fad'a gaban kowa kuma gabanki,daga rana mai kamar ta yau babuni babu Abdoulnasser na yafeshi daga cikin zuria ta,na barshi har abadan abada sanan wlh wlh wlh duk wanda na kama cikin yaran gidannan yana muamala dashi aboye ko azahiri wlh zaibisa,yadda na korai shima haka zaibisa.ba ga yara ba harke ushe muddin kika bibiyesa ko awaya ko zahiri daga ranar abakin aurenki,kidauka koda ban gani ba to ranar zakibar gidana..........yanzu ba sai anjima ba nakeson ka tattara komatsanka da wancen yaron da ka kwaso ka kawo mun agida,waya sani koshine ya koya maka kufitar mun agida yanzu,kuma karka bari ink'arayin arba da bakaken fuskokin ku,inba haka ba wlh sawa zanyi adaureku har tsawon rayuwarku........bazan anshe duk abunda ka samu daga jikina ba don wannan nayi makane domin Allah da wahalar da dakakemun........muryarsa tayi rauni sosai fiye da lokacin da ya fara magana.........bakayi mun Adalci ba Abdoulnasser ba ka kyauta ma rayuwata ba,duk cikin zuria ta babau wanda nakeso kamar ka,babu wanda ke kyautata mun kamarka,shine zaka yimun haka dole zaka ar jikina kuka Abi yake kamar yaro,kai idan mai hankaline zaka san cewar abun anfi karfinsa ne baida wata mafita........barin wajen yayi yana shashshekar kuka.ina daga can jikin bango ina nawa kukan,inajin inama ace mafarki nake ba gaske bane wannan wace irin bakar rana ce.umma kau tana ganin tafiyar abbi ita dasu haulat mezasuyi ba darinba,har gaban mami tazo tace to sai abi wani sarkin don yaudai tauraron gidan nan haskensa ya dishe har abadan abada mamman shine zai maye mana gurbinsa.
Mami tana durk'ushe gaban Abdoul tana kuka ita da

1 Comments On ABDOULNASSER ALFAH
avatar
mahmud-maaji

1 year ago

Reply

It is a very interesting book

Please Login or Register in order to submit comment