Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

zata gaya mata ba taji kirjinta yan bugawa,har sukaje gida daker take maida ma feea ansar labarin datake bata.


Mrs bb ce.
Mom muhseen.
[8/8, 5:44 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........17

Har k'ofar gida ta sauke ta yah jalal da wani abokinsa sai d'alha duk suna bakin shagon kofar gidanmu zaune,sukuku haka na nufo gida gaidasu nai na wuce cikin gidan........tun a soro na jiyo muryar Anty jamila nasan itace tazo,kowa ya sanar da ita da wannan tsohon cikin haihuwa yau ko gobe.
Sallama nai ina idasa shiga suna cikin inuwa zaune har lokacin dai fuskokinsu babu wata walwala sosai.
Sannu mama take mun itada yesmin dake duba littafinta,zamewa nai kusa da anty ina mata sannu da xuwa.
"Kamar wadda tadawo k'asa fiyah."
Murmushi tad'anyi tace"wlh yau ban samu nasaka komi cikina ba har nadawo yunwace keta cina nan dakika ganni."
Cikin mamaki mama tace"au dasafe dana ce kin karya me kikace mun safiyyah."
Yamutsa fuska tayi kamar zatayi kuka tace"mama wlh bakina ne babu d'and'ano."
Cikin fad'a mama tace"in haka ne kowa ma aida baici na,kimaida hankali wannan ulcer banzar tatashi wlh zaki gane kurenki,maza tashi ga abinci can kije ki zuba kina girma kina kara rashin wayau."
Daker ta mik'e ta wuce d'aki ta zube kan gadonsu tana sauke numfashi.saida ta huta sannan ta shige wanka tafi minty talatin tana wanka sannan ta fito.
Duk kayan fiyah dogayen rigunane siket basu wuce biyar ba.tayi shafa sannan taje tasa abincin ta dawo tsakar gidan suna ci gaba da hirar,mostly duk akan rufe baba ne da akai,saida nai rabin abincin nace"mama an samu wata nasara ne akan abun,yaushe zasu sakesa."
Tab'e baki tayi tana cewa"wace nasara kuma safiyyah,?nan yayanku ya sake komawa station din da duka suka rufesa cewa inyasake xuwa zasu hada dashi,wannan masifa dame tai kama nidai gaskiya nagaji wlh nagaji,shekara ashirin ana fama da abu guda nidai inhar yadawo to tashi nan unguwar yazama dole,ina dalili ina d'an mafari mutumen nan inba gani yayi munbar masa unguwar ba bazai shafa mana lafiya ba wlh haba."
Anty jamila tace"Aa mama wlh babu inda zaku aiba filin ubansa bane balle na uwarsa,dayake son ganin dole saikun tashi duk bakincikin sa wlh nan gidan yafi karfinsa.munafuki annamimi don dai uncle bai gari wlh da tuni baba yadawo,idan ta k'amarsa yana da kud'i ai bashi kadai Allah ya bawa ba,akwai wad'anda suka fisa."
Mama tace"Gara da baya nan jamila banson maganar tafita har takai ga wataran aimaki gori duk da bana fata,kuma dangin mijinki basu da wannan amman abun gudun shine yauda gobe."
Haka suka cigaba da hirar fiyah na jinsu ta kasa cigaba da tsoma baki............bayan sallar magruba driver anty yazo yadauketa suka tai gida.
Ina daki ina ta duba handout dina,naga sakon malik a wayata.
Na jima ina kallon text din kafin naduba abunda yace.
_FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI DA FARA,A TA ISO GIDA LFY,ZANSO YAU TA KARE FARINCKI NA LULLUB'E DA XUCIYARKI KI KWANA LFY MUTUMENKI YANA GAIDAKI._
ta jima tana bin rubutun da kallo me yake nufi kuma oho abunda take fada kenan cikinn xuciyarta.......balaifi sakon ya yi mata dad'i amman bata mayar masa da ansa ba,karatunta take yesmin kuma tana can tare da mama dakinta.yah jalal ne ya shigo yana ma mama magana tayi bak'o yana son magana da ita,kasa kunne nayi sosai don nasan bai wuce daddy ba shine mukai dashi zaizo.
Saigashi kuma shid'inne ban fito ba inaji suna magana yana bata hkr,kuma ya je yasamu yayansa watau Alh muazzam na shawo kansa zuwa anjima ko gobe za asakesa.ashe yar hatsaniya ce tahad'asu,shi yaya yazo fita daga unguwar shikuma malam yazo shigowa shida mai taxi,sai mai taxi din ya banki motar yaya,to daman mai neman kukane aka jefa da kashin awaki nanfa yaringa yiwa malam rashin kirki har malam shima ya gaza hkr yashiga rama wa shine fa ya kira yan sanda suka tai dashi.....aman komi ya warware malam yana nan dawowa insha Allah,yanzu can zan nufa.
Godiya mama tayi tare saka masa albarka yace"haba ba komi ai malam namune sai inda karfinmmu yakare,Allah ya kiyaye gaba ga wannan asaima yara wani abu,ya jiye mata kudin da yaba fiyah bata ansa ba.
Har mota yaya jalal ya raka shi har yake tambayar dama yana nan,yace ai yazo hutune yana kaduna yana aiki....sundan tattauna sannan ya wuce gidansa ake cikin estate din.

Fitowa nai na samu su mama suna yabonsa don sunce tun zuwan su unguwar shine na farkon daya fara masu mutunci,bacin shi babu mai kallonsu da kima.
Anan mama take basu labarin abunda yafaru tsawon shekarunan dayasa Alh muazzam basa shiri shida malam kabir.

"Abun ya farune lokacin duk watan mu guda da aure nida mahaifinku,sai babansu ya rasu kasancewar da abuja bata kai haka ba don nan wurin idan kun ganshi shekarun baya zakuce wani sansanine.
Gidajen ake wajen basu fi bakwai ba,kuma ba wasu gidaje ne na azo agani ba,mahaifinku shikadai ne ga mahaifiyarsa sai yan uba su uku duk maza,Allah yayiwa mahaifinsa arziki alokacin daidai misali,kuma yabar kadara mai yawa yabar gidaje biyu yabar gidan gona daya da filaye.wannan gidan yana daya daga cikin filin mahaifinsa,kuma shikadaine mahaifinku ya samu sauran du yan uwansa sunyi sama da fad'i da dukiyar,kasanewar gidan haya muke lokacin kuma samun kudin hayar yana wahala,sai malam ya yanke hukuncin zowa nan ya gina mucigaba da xama.
Kwatsam daya fara zuwa da yan aiki wurin sai sukaci karo da Alh muazzam,lokacin ana mashi nashi sabon ginin dake amman ba wannan dayake ciki ba,sunda ga can baya na hayane yanzu.
Kamar gaske suka fara gaisawa da malam,har wataran idan yazo aiki yakance yazo suci abinci ahaka har sukadan saba,rannan suna hira yace masa ni kuwa malam wata shawara nazo da ita,inason filin nan naka tun randa na ganka anfara aikin nan naji sha,awar wajen ta zomun inson yin wani gini awajen,kasiyar mun nikuma konawa kaimashi kudi za siya.lokacima baikai wanan matakin ba dayake kai.
Kaitsaye babanku yace bayarda ba shibadan yasiyar ya mallaka ba,don haka yayi hkr shi ginawa zai yazauna,shine abu guda daya dayake tunawa da mahaifinsa don haka yayi hrk.
Wannan magana ta b'atawa muazzam rai ainun baitanka mashi ba daga ranar ya canza wa babanku,bai mashi magana duk yasa mutanen unguwar suka tsanesa,wai shiba kowan kowa ba amman yazo unguwar masu hannu da shuni zaiyyi wani tsugunnennen gida,aikuwa zaka zama shaniyar ware don babu maiyin hud'd'a dakai kana fak'iri.Alh muazzam yake sanar da babanku haka alokacin saida sukai rigima saida babanku yayi wata uku daure agidan yari,sannan aka sakoshi.
Sadda zai dawo yasamu an rushe mashi ginin daya fara tas sai filin wajen........munshiga tshin hankali ba karami ba,karshe ya shigar da kararsa kasancewar yana da lawyer kuma Allah ya tsaya mashi sai alkali ya ansar mashi hakkinsa,cewa Alh muazzam saiya biya tarar dubu dari takwas ga babanku.amman wlh har yau har gobe bai bashi ba,ba kuma don baidashi ba aa k'etace don yaga yadda zaiyyi yayi wani ginin,babanku bai sake bi takanshi ba tunda yasamu anyi masu tsakani,ya cigaba da hidimar gininsa yasha bak'ar wuya kafin ya yi gidan nan,duk yan kudadensa dayake samu na albashi nan yake zuba su mahaifiyarsa tana taimakonsa daga can wani kyauye dake jahar katsina waishi dutsi,bayan mutuwar mijinta ta koma wajen danginta.........cikin ikon Allah gida ya kammala don har na haifi Abdouljalal lokacin ina wankansa muka dawo nan unguwar,munsha wulakanci babu mai kulamu kowa kallon kaskanci yake mana,ahankali kuma unguwar tafara cika suna gidaje na nuna ma sa,a gasunan gidajen kamar baza mutu ba......ahaka mukaita rayuwa Alh muazzam kullum cikkn neman rigima da mahaifinku yake,shikuma yaki biyewa kunji dalilin wannan gaba nan unguwar duk sunbi bayansa basa mutuntamu.matar Alh kwangila ce kawai hajiya Asiya take huddar arxiki dani shima aboye mijinta baisani ba har gobe,saifa wannan maigidan da yazo daga katsina babu laifi suna gaisawa da malam kuma matarsa tana shigowa don ma basu fiye zama garin sosai ba zuwa suke sutai. To saifa kanensa Alh matawalle daya zo yanzu don shi sunfi ma shiri da babanku sosai da sosai"
Yanzu shekara nawa babu wata fitina tsakaninsu sai wannan karon ashe bai manta ba ya aikata mashi haka,don haka basai na ja kunnenku ba babuku babu hudda da yaransa,kai koda wasa karnaji labarin ganinku tare dasu balle ace kun shiga gidan.
Gashinan dayake Allah ba azzalumin sarki bane d'an cikinsa yayi zina da matarsa uwar gidansa,sannan yayi lalata da agolarta,wannan kadai ya ishesa ishara."
Kirjin fiyah yaba da ras jin kalamin mama na karshe,dagowa tai tana kallonta maganar batai mata dadi ba har cikin k'ok'on ranta bataji dadin yadda ta fadi magana marar dadi akan Alfah ba,bacin ba haka abun yake ba.
Kasa jurewa tayi tace"mama bafa haka akai ba sharrine aka masa."
Duk kallonta suke cike da mamakin maganarta ba kamar yaya jalal kamar ya kai mata duka yace"don ubanki ke ina kika sansa ma da kike karesa."
B'ata fuska tayi tace"nifa yaya ba karesa nai ba,kawai dai abunda naji ana fada kenan."
Mama cikin fad'a tace"koma dai miye bbu ruwanki dasu miye naki inma gaskene inma ba gaske bae ba,kifita idona akan wannan maganar kuna iya tashi na gama magana."
Ranar da maganar nan fiyah ta kwana kamar tayi kuka har cikin ranta bataji dadin maganar ba,kuma wannan matsalar ba zata sata ta fasa abunda tayi niyya ba,insha Allah sai inda karfinta yakare akan Alfah sai mutane sun dawo tausaya masa suna yabonsa,badai tsinuwa ba saboda tausayinsa har kuka tayi ranar daker bacci ya sace ta.
Tana mamakin rashin zuwan feea kila mominsu bata barta ba,sun had'u school gobe taji maganar me take son fada mata.

💞💞💞💞💞💞💞💞
Alfah haduwar sa da fiyah ta zame masa damuwa,don babu wanda yafada masa magana datayi mugun tsaya masa kamar ta tun bayan barinsa gidansu,ya kwana ya yini da bakinciki shiyasa dayaje company yayi tijararsa yadda yakeso kuma ya kori duk wanda yakama da laifi,haka store dinsa duk abunda yaga ba daidai ba yi yake kamar zai cinye ka d'anye,kan yadawo gida saida ya kori mutun uku ba kuma maganar dawowa.
Allah Allah yake yadawo yasameta don yaci burin muddin suka sake haduwa saiya zubar mata da hakora,daga lokacin zata san waye shi bata san shi rayuwarsa yanzu da yaga mace kusada shi gara ya kwana baici komi ba.
(😂yo Abdoul ai cikin ka kaima wa nidai in na cika tunbina ai lfy lau lol🤭)

Washe gari tun takwas saiga feea ta biyowa fiyah,itace ma taringa taya fiya aikinta da takeyi,tana mamakin feea yarinyar da agidansu banda taci ta kwanta bata san komi ba,saigashi itace dayin shara harda yi mata d'aurayar wanke wanke.
Yau tea sukasha da indomi har da kwai sai soyayyen dankalin hausa......sosai feea taci kalacin don ita ata ma tab'acin dankalin hausa ba,su mama nata mata dariya yesmin yau ake exam din karshe sai murna tae tace kafin ta dawo kowa ya ajiye mata gift dinta.Tare suka tai saida suka ajiye yasmin sannan suka isa makaranta.
Suna kan hanya text din malik yashigo wayarta dubawa tayi da murmushi akan fuskarta .
_INA FATAN MA,ABOCIYAR MURMUSHI TA TASHI LFY,I KNOW U ON UR WAY TO SCHOOL,ALLAH YA BADA SA,A IDAN KIN DAWO I WANT SEE._

Kallonta feea tayi tace"duk da ban sani ba kuma baki gaya man ba da alama dai fiyah tayi sabon kamu,kinsan kuwa maganar mu tana da nasaba da haka zanso nima kimun wannan hanyar."
Kallon waje fiyah take tana sauraren kalamanta tana komarin dorasu bisa ma,auni amman iyakar tunaninta tagaza hasaso komi.

*aradu nagaji sorry mu hafu gobe*

Mrs bb ce
Mom muhseen.
[8/9, 4:32 PM] Mom Muhseen: 💞💞💞💞💞💞💞
*ABDOUL-NASSER*
*(ALFAH)*

WRITING BY.

MRS BB
MOM MUHSEEN.

WATTPAD NAME
HUMAIRA7531.

*DEDUCATED TO ZAUREN MRS BB AND ALFAH FANS*

🅿️.........18.

Parking tayi wajen da suka saba ajiye motar suka fito kowace rataye da jikarta,fuskar fiyah tayi fresh bata saka komi ba yau bayan cream din da take shafa wa,saboda duk bata cikin sukuni.
Class din babu kowa na su fiyah sai wani namiji daketa karatu shikadai,sallama tayi mashi tace"ina y'an ajinne."
Yace"ashe tunjiya malamin yakira classrame yafada masa bazai xo ba ya samar da mu,to mafarin kenan duk wasu basu shigo ba sai anjima."
Jinjina kai tayi tafita feea ta hango tana nufo department dinsu,ajiya tana ta d'okin jin abunda feea zata gaya mata,amman ayau saita samu kanta da rashin son jin koma miye takeson sanar da ita,don kawai taji aranta abun azai mata wani dadi ba.
"Kuma babu kowa ajinko?inajin sun canza time din lecture din muje can muzauna."
Cewar rafeatu fiyah bata mata musu ba ta jera da ita suka nufi wani block suka zauna,shiru shiru babu mai cewa komi fea tace "niban tambayeki ba,daman kinyi waya baki gaya man ba."
Murmushi fiyah tayi ta mik'a mata wayar cikin sanyin murya tace"kinganta uncle yahya ne ya siyamun bata wuce 2 week ba fah."
Jinjina kai feea tayi tace"tayi kyau wlh,Kingode."
Daga haka suka sake daukar wani shirun,fiyah nata nazartar ta ta lura akwai magana bakinta,amman tana shayin fada kokuma don bata san ansar da za,abata bane.kawar da shirun fiyah tayi da cewa"ina maganar da mukai dake zaki sanar dani."
Ajiyar xuciya feea tayi tana kallon fiyah dandanan fuskarta ta canza,ta koma kalar tausayi cikin rauni tace.
"Fiyah,banda wata qawa data wuce mun ke wadda zamuyi magana mu kashe murufe tare,kece kadai zan ita sanar da damuwata kiban shawara kuma kitai makeni batare da wani yaji ba."
Kirjin fiyah yabuga tace"inajinki Allah yasa lafiya.?"
Girgiza kai tayi idonta ya cicciko da ruwa take cewa" *SOFIYYAH*,Ina cikin damuwa wlh na farko dai abunda yafi tada man hankali shine Abbana zaiyi aure kuma yarinyar da zai aura class mate d'ina ce,wallahi munyi primary da secondary duk tare,kuma d same class.sannan wlh bata da kunya ta raina kowa idan Abba yayi haka munshiga uku,momi zuciyarta bugawa zatai duk tsawon shekarun nan baitashi auren ba sai yanxu kuma yarinya karama diyar cikinsa,saar diyarsa wlh tunda aka fara maganar momi bata da kwanciyar hankali kullin tana cikin damuwa hat jininta yahau.tace ita ba auren take mawa ba wlh ya aure koma wacece amman banda sa,ar yarta yaje ya nemo babba wadda zata iya zaman kishi da ita ba diyar cikinta ba.amman Abba yaruntse ido yace bazai fasa ba duk ubanda yaji bazai iya zama da shiba yafita.in takaice maki jiya nakoma gida momi ta tafi zaria gidansu."
Hawaye suka zubo mata tana sharewa cikin kuka ta cigaba da cewa,
"Bayan wannan sai abunda ya hana xuciyata samun natsuwa,bana bacci mai dadi banda wani aiki sai tunani,zuciyata banda azalzalara da take babu abunda takeyi,har ciwo take mun wlh safiyyah bana iya cin abinci saboda halin da nake ciki."
Cikin tausayawa take kallonta har idonta ya cika tab da kwallah tace mata"menene kuma bayan matsalar su Abba.
Share kwallar tayi ta d'ago tana kallon fiyah cikin karyewar murya tace "ina sonsa, fiyah soyayyarsace ta ke hanani cin abinci take hanani bacci,ta kuma sani kukan da ba abigeni ba."
Kallon mamaki da al,ajabi take mata bakinta har rawa yake. Tace"way...e......waye shi......in..a yake kuma."
Sadda kai tayi tace" *ABDOULNASSER ALFAH*"
Duka idonta ta fiddo tana kallon rafea kirjinta taji yayi wata irin ansawa,daker numfashinta yake fitowa yana komawa,maganar tayi masifar dukanta bakinta har wani k'afewa yayi saboda iskar data cikashi don abude tabarshi.........kanta taji ya sara xuciyarta tace"duk wannan rudanin na miye,inhar ba kina jin wani abu akansa ba."
Cikin abunda baifi minty biyu ba ta koma yadda take,amman still kirjinta bugwa yake tayi kokarin daidaita muryarta takalli rafea data sadda kai tana hawaye,matsowa tayi tana rik'e da hannunta cikin tausayawa tace"rafeea,Abdoul kikeso? Alfah zuciyarki ta kamu da son sa?gaskiya bazan b'oye maki ba banji dadi ba,ko kadan banji dadin maganar ba meyasa zaki bari xuciyarki ta kamu da son wanda aduniya baida abun tsana sama da mace,idan yaganta jiyake uwa ya kasheta.bansan taya zan lallashi xuciyarki ba gaskiya don datayi shawara dani da bakamu da son sa ba.amman yanzu kinyi nisa bakijin kira."
D'agowa tayi tana kallon fiyah cikin dishewar murya tace"dake na dogara,dake na laru don ke nakeson ki shigemun wajen wannan aikin,fiyah zaki iya inba keba babu wanda zanje na dorama wannan nauyin."
Mik'ewa fiyah tayi cike da b'acin rai tace"oh ni dayake ban son ciwon kaina ba!zanje na samu namiji irin Abdoulnasser nayi maki feating love dinki,karshe duk zuciyarsa dayakeji da ita yajuye bisa na ya illatani yayiwa iyayena sara,koda yake ai su ba masu hannu da shuni bane basu san ciwon y'arsu ba."
Ta juya tabarta nan wajen,aguje fea ta isa wajenta tasha gabanta tashare wayenta tace"karkimun mummunan fassara fiyah,niba nufina kenan ba kema kuma kinsan bazan iya maki wannan gorinba,inda dalilin daya sa nace haka."
Wani kallo fiyah ta watsa mata tace"dalili,! wane irin daliline zaisa kice inje ga wannan mahaukacin ince masa kina sonsa injawo ra,ayinsa akanki haba rafea kinmun adalci kuwam."
Jawota tayi suka zauna tace"abun da yasa nace haka fiyah tsawon lokacin da kika dauka kina hidden abubuwanki,nikuma na ringa binki abaya ina guiding dinki,har gidan dakike zuwa nasani har abokin Alfah da yake d'an kawoki makaramta ina sani,abunda kawai ban sani ba shine mekike zuwa yi gidan? meke tsakaninki da wannan abokin Alfah?din wata zuciyar ta cemun soyayya kuke kuma Abdoul zai sani kuma dagani kuna gaisawar mutunci."
Idon fiyah ya rine da masifa fizge hannunta tayi dake cikin na rafeea tace"watau saboda tsabar munafurci bibiyata kikeyi ko rafeea?har xuciyarki take gaya maki wani banzan tunani ko,to inso kike kisan menake zuwa yi zangaya maki tun kafin sakarar zuciyarki ta kuma gaya maki ina bin maza.......yadda fiyah ke daga murya yasa feaa ta rufe mata baki,ita kuma cikin fushi ta fizge tace "barmi na gaya maki abunda nake ciki tunkan kije gidanmu kice ina bin maza,naga makauniyar soyayyarki ta rufe maki ido komi ma zaki iya........banda wata alaka ta soyayya tsakanina da malik abunda ya hadani dashi kuma aikin ladane,tun ranar da wannan abun yafaru da abbanki yasa aka rufe Alfah police washe gari na yanke shawar zuwa muyi magama da malik akan jin mafarin llacewar abokinsa.
Fiyah ta juye mata halin da ake ciki na kokarin ganin sun dawo da Alfah cikin hayyacinsa.
"Don haka ni babu wata alaka bayan wannan tsakanina da malik,ni babu wani namiji da zan gani inji ina sonsa,kuma taimakon da nayi niyya insha Allah zanyi sai inda karfina ya kare,ina sanar dake cewar haryanxu ban samu zarrar tunkarar Alfah da wata magana ba sai rannan shima kuma Allah kadai ya ceceni kiris ya rage bai karyani ba,saboda ganina dayayi gidansa.to inga inje ince masa wai wannan da kukai rigima bisa titi tace tana sonka ai wlh ranar ba bakina zai fasa ba idanuna tas zai tsoyayar dasu don ba imani ne dashi ba,shida mahaukaci banbancin kadanne.
Idan kinji zaki iya tunkararsa wlh zan maki rakiya har k'ofar gidan,shima kuma dana kaiki zanyi kwana.inkindawo da kafarki kintsira.don naga baida abun sha,awa sai karya kafafun jama,a kome sukai mashi oho"
Jin abunda fiyah kesanar da ita yasa gabaki daya taji jikinta yayi la,asar to wannan wace irin xuciyace Allah yayi masa,bai daukar komi easy Fiyah tace"zanje inshiga aji ga malam can yazo,tajuya tabar feea nan zaune tana tunani.

💞💞💞💞💞💞💞💞
Yau Abdoul zai yi tafiya zuwa Australia,zasu yi ani meeting daabokn kawancinsa na kwana biyar,sanan zaibiya ya bada oder kayanshi akawo ashi har nan abuja.
Kayan sa malik yake had'a mashi shikuma yana kan computer,yaudai fuskar akwai sassaucin rahma ba kamar lokutan baya ba......shiyasa malik ya ma fiyah text inta taso ta biyo ta gidan yana son ganinta.
Tun ranar da tayi masa gorin shan giya bai sake ganin yasha ba,saidai in ya fita don yazu dakin sa bedroom dinsa yake ajiyewa cikin frig dinsa.
Babu riga jikinsa duk halittar da Allah yayi mashi ta bayyana,daka kallai kasan mutunne mai motsa jikinsa always.
Yana da baiwar galgasa irin kwantacciyar nan maibin jiki,kirjinsa ma haka da kafafunsa amman ta kirjin saika rantse salon yake mata(🤭lol),har wani shalk'i take tana walk'iya.
Haka gashinsa na kansa dana fuskarsa,yanada saje wanda yake had'e da gemunsa,kasancewar irin gashin nan na fulani garai kamar na larabawa,sai yasake hasaka fuskar sa idan yagyarasa kyau yake sosai.
Baidamu da manyan kaya ba koda can daya na gida sai idan wani daurin aure zaije kozai raka Abbi wajen manyanmutane,sanan yasaka amman shi yafison kanana don kayansa mostly inyaje waje yake shigowa dasu,ko in malik zaije yabashi sakon da combus kala kala haka yake sawa kuma suna hawan kayan sa suna masifar yi masa kyau,
Malik ya gama hada mashi akwati guda said yar traveling bag dinsa da ake rataya wa ga hannu guda.
Kallonsa yayi cikin tsokananyace "yallabai na gama saura wankan."
Cikin mamaki da al,ajabi yaga ya d'ago yana mashi wani irin smile wanda tunda suka baro gida malik bai samu wannan damar ba ga Alfah..........cikin jin dadi ya iso garesa yace"don Allah sake maimaita wa wlh kabaji yadda naji wani sanyi cikin raina ba,Abdoul inda kasan yadda murmushi yake haskaka fuskarka da baza ka so ka daina ba."
Rufe systems din yayi yana nufar bayi baice masa komi basaida yakai kofar shiga yajuyo yace"fuskarce banso tayi haske,don baida wani anfani akanta muddin haske ya bayyana akanta mata zasuyi kokarin kawo kansu gareni nikuma bana sonsu,nafi kaunar mutuwata akansu."
Yana gama fadar haka ya shige yabar malik da rik'e hab'a,tabbas da ace Alfah yana k'wata fuskarsa da murmushi da fara,a y'anmatan da zasu biyosa basuda iyaka,amma hakan ba hujja bace.
Fita yayi zuwa main falonsu yana jiran isowar fiyah yana son su had'u da Alfah kafin ya wuce.

Karfe uku yau suka tashi ko alamar jiran feea batai ba don tana cike da jin haushinta,tama rasa wanda zatace tana so sai wannan gantalellen mahaukacin,mts aka taringa jera tsaki ta fito daga makarantar,kirane yashigo mata mama ta gani saurin dauka tayi tace"Assalamu alaikum mama lafiya ko."
Cikin farin ciki taji mamar tayi magana cewa"daman ince maki babanku ya dawo babu jimawa."
Itama cikin farinciki tace"dagaske mama?wayyo mungode Allah mungode ma Alha ganinan zandawo insha Allah."
Kashewa tayi sai lokacin taga sakon malik na biyu ayau din nan.
_fatan lectures sunyi dadi,inba damuwa kisaman gida yanzu pls._
Tarar taxi tayi ta gaya mai unguwar dazaikaita suka tai.
KOfar gidan ya sauketa tayi addua sannan tashiga......compound din gidan banu kowa inda suka saba zama bata ganshiba tayi shahadar nufar main falonsu kirjinta yana amsa wa,amman ta saka dakiya da natsuwa kadan aranta ta shiga.
Yana tsaye wajen taga yana shan win din sa ga wayarsa yana danna wa,malik kuma yana cikin daki baikai ga fitowa bah.tunda tayi sallama ta shiga ta hangoshi can tsaye kirjinta ya tsanan ta bugawa,zama tayi tana karanta duk adduar da tazo bakinta.
Juyowa yayi bai sauke idonsa ko ina ba sai inda take zaune kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi haka tayi.
Shan mur tayi ta kauda kai kamar bata ganshi ba,nan kuwa kamar ta saki zawo taji,ganin dagaske wajenta yayo tsoro yasa takasa cigaba da zaman ta mik'e cike da dakiya tana ja baya fuskarta aya mutse idonta a kan cup d'in hannun sa.tai saurin toshe bakinta da hancinta har saida ta dangane da bango sannan ta tsaya,babu sassauci kokadan ga fuskarsa daf da ita yatsaya idonsa tar akan fuskarta,farare tas said shining suke kamar anzuba mangyada aciki.banda daddad'en k'amshinsa da yake nusar hancinta bata jin komi amman saboda ta k'ular dashi yasa ta ringa kauda kai tana yamutsa fuska.hannu tasa tana dakatar dashi da had'e duk kusancinsu cikin yar muryarta tace"dallah malam miye haka,matsa kaban waje nace kamatsa,kar namaka amai ga jiki nibada shan giya ba nida warinta."
Duk cikin kalamanta babu abunda yake b'ata masa rai irin tace yana warin giya.shak'o wuyanta yayi yana huci iyakar karfinsa bayan ya hade hannayenta baya yasake matseta ga bangon.
cup dinner giyar yake k'okarin kaiwa bakinta ta guntseshi ga shida ker take nishi idonta duk sun yo wake sun fara canza kala,cikin dakakkar murya yace.
"Naga alamar kwa'ayinta kike ko,to sha inbaki shata ba saina fiddo mak'ogwaronki shegiya yar iska maibiyo maza gidajensu,ke akaruwancin nakin ma marar aji kikeyi banza gantalalla.ai tsirara zakiyi yawo asan cewar kedin yar tasha ce."
Duk yadda ya shak'eta da yadda ya murd'e mata
Hannu duk bataji zafinsu kamar yadda kalamansa suka tsaya mata garai suke sukarta ga rai.jitai wasu kwallah zasu zubo mata tai saurin maidasu.....afusace yayi watsi da ita bakin k'ofa kadan yarage batabfad'a bisa hannunta ba fitowar malik kenan aguje ya iso wajenta yana sallallami
"Wai Alfah baka da hankaline?wajen ka tazo ne?banson rashin tausayi."
Hannu ya mikabmata ta kama amman ta k'iya ta dafa bango tana mik'ewa daker,cikin zuciya Alfah yace "muddin bata bar zuwa gidan nan ba wlh watarana ferfesun ta zanyi incinye,wawuya kawai ya watso mata sauran win din dake cikin cup din hannunsa,ga fuska......runtse

1 Comments On ABDOULNASSER ALFAH
avatar
mahmud-maaji

1 year ago

Reply

It is a very interesting book

Please Login or Register in order to submit comment