Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Abu biyune yatashi hankalinta jin za asakarwa labila barci saikuma abunda yashafi Usman kuma gashi idan boka yayimagana bazai sauyaba

Tacekai mezaisa indami kaina koma nezaifaru yafaru indai burina zaicika anan tayi sallama dabokan dacewar zatajirah harya karkatoda rayuwar Usman zuwagida

Sannan Adan sausautawa labila dazaran andauke khadija atasheta daga barcin"" maganar jinin jinjirin Kuwa abarkomai zatayiii yakasance ashirye ranarkuwa *hatsabibin boka* ya aikomata da mangwaron


Tundaga ranar lubabatu take ta yawon neman masuciki Amman duk wadanda tasani dagamai wata uku saibiyu harsu khadija sukai watadaya adubai batasamu mafitaba

Khadija da Usman kamar zasu hadiye Kansu saboda soyayya yazata itah tazama shi jiyakeyi tamkar yafasa kirjinsa yasakata aciki saboda soyàyya







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 91
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽



Zaune suke cikin falo tayi matashi dacinyarsa yana wasa dagashin kanta waizaiyi mata kitso itakuma sai wash takecewa

Harcikin jininsa yakejin yanayinta yakirah sunanta my heart tace na am hubPublish at www.hausaebooks.com.ng na shiru yayi baice komaiba hakan yasa tamirgina tana kallonsa murmushi yakeyi tace au waidama dankawai kasani amsawane kakira sunana

Tamurguda baki takoma takwanta dariya yayi yace bakin nan nakie ya iyah tsokana sosai shiyasa idan nasameshi bana ragarmasa

Tadafe bakinta tace au ashefa harda mugunta kake hadamun lallai zansan yanda zanyi nasamu Abu maidaci nasaka abakina aidazaran kaji daci zaka cire bakinka

Takai karshen maganar tana tashi daga kan kafarsa tana dariya ido yakuramata aransa yace wai itah komai tayi sainaga takara kyau komai kyau yakemata

Ganin yakafeta da ido yana murmushi taturo baki kamar zatayi kuka subhanallah wani masifaffen kyau takara datayi hakan""" hannunta yajawo tamatso kusa dashi hancinsu yana gugar juna suna kallon junansu yace koda kinsaka Abu abakinki

Inhar zanhada bakina dawadan nan kyawawan labban nakii danyatsansa yasaka yana zagayen karamin bakinta itakuma tanabinsa da kallo yacigaba babu abunda zanji bayan zakie Wanda yafi Zuma dakomai dakika sanie

Ya sassauto da muryarsa yace wlh Deejarh dazanwuni inkwana ina tsotsar wannan bazandamu da abinciba saboda dadinsa muah yasunbaci yan yatsunsa kinga Kuwa komai yarabeshi zaizama sweet ne yakanne mata ido daya

Kanta takada tace bawanin nan sai idanhar ba dacin kalasaba aikomai da mazauninsa zaki danashi haka daci inamai tabbatar maka idan nashafa shuwaka a bakina hmmm kai ko abincima bana tunanin zakaci aranar tadaga masa girah tana dariya

Kuru yayi yana kallonta aransa yace wai idan narasaki yazanyi??? Yayi maganar yana buga uban tagumie Deejarh tatsaya da dariyarta ganin yanayinda yashiga tace meyafaru dad???

Tayi maganar tana jaye hannunsa daga taguminda yayi cikin yanayin damuwa yace wlh inaji ajikina kamar wani bakon al amari zaisameni

Yayi shiru daga bisanie yace inarokon Allah yasa komene zaifaru karyabiyo tawajenki banason narasaki idan narasaki wlh zan iya rasa rayuwata gabadaya

Jikin khadija yayi sanyi takwantarda muryarta tace haba masoyina annurin zuciyata kasani komai ruwa komai iska komai rintsi inataredakai bazantaba gudunkaba

Muddin ina nunfashi adoron kasa bana tunanin akwai wani Abu dazai nisantanie dakai kadaina saka damuwa Aranka Dan Allah

Wlh damuwarka daidai take darashin kafiyata nakwana arba in dazaran naganka adamuwa duka natsuwata nakan rasata kaima kasan inasonka indai tawajenane bazaka samu matsalaba tayi maganar tana riko hannunsa

Yace nasanda haka Deejarh Na nasan bazaki taba gudunaba Amman tabbass akwai abunda zaifaru Dan gabana yana tsananta bugawa akullum kamar lokacinda zanfara haduwa dake

Tuni idanuwanta suka kawo ruwa"" ido yaware yace kesarkin kuka wasafa nake waimakinsan me??? Batace komaiba kuma batadaina kukanba yace tunani kawai nake dazaran munkoma gida duk wannan soyayyarda kike nunamun zakibartaa

Harnadawo kalar tausayi yayi maganar yana turo baki kamar yanda takeyi aikuwa tasoma dariya gakuma hawaye sunazuba a isonta

Yace umm ansamu mugunta dole ayidariya waishinkam agarinku akeyin wannan??? Tace mefa??? Yace kuka da dariya alokaci daya mana abun mamaki🤔

Tace habadai yace mubar zancen wasa Dan Allah koda munkoma karkirika jaye jikinki danie kinjii"" yamarairaiçe fuska kamar zaiyi kuka

Tace toyazanyi kaima kasan inakunyàr mom sannan kuma sahiba haba nidamunkoma zanjaye jikina"" Usman yatsuke fuska yace wannan akekirah taleko takoma"🙁" to idan kikaihaka nikuma menene ribata wlh daredaya zakiji likita yace ciwo yakamani

1 Ciwon rashin jin dimin jikin Deejarh na

2 ciwon rashin tsotsar my sweet

3 ciwon rashin kwanciya taredake

4 ciwon soyayyarta da shakuwarta

Ke atakaicedai zaice maki jinina yahau Amman Na soyayya"" namakance Amman narashin ganinki kusadani nazama kurma rashinjin tsiwar nan takie
Ke intakaicemaki labari zaice zuciyata tabugaa adalilinki wayyo Usman yazama abun tausayi shiru yayi yana kallonta yanda take murmushi yace haryanzu baki sauya ra ayibane ???
.
Tarausayarda kai tace sauyi Sam"🙅🏻" inazankai kayan kunyar??? Yace kizubasu bayan dakinmu mana"" tosaidaifa ayi yanda za ayi ko wlh agabansu inrungumeki insakiji kunta kinga daganan kunyar tafita
.
Tace uhum tanan zaka bullo tosaina daina fitowa sahiba tarika kaimun abincina dakie"" yace karkimun haka kinji wlh badawasa nake maganarba

Tace ainima badawasa nakeba mezaisa naguji mijina bayankuma yazama rayuwata yazama farincikina inhar zan iyah kauracewa numfashinda nake shaka akoda yaushe tozan kauracemaka

Kasa aranka duk sanda kakirah Deejarka acikin zuciyarka zatazo dagudu tarungumeka Tabaka kulawa "" shinko kataba sanin akwai wadansu zuciyoyi masu amsa amo taredajuna sukanyi shawara dajunansu hakazalika sukan amsa kiran junansu wadan nan zuciyoyin bawasu bane face zuciyata da taka

Dani dakai abudayane tanisa waikana tunanin zan iyah yinnesa dakaine"" kasabamun dajikinka nasaba dakwanciya asaman faffadan kirjinka bansan soyayyaba sai akanka kashayardani giyar sonka

Nashata sosai hartana Neman illatani muddin ka kauracemun zan iyah rasa raina saikawai tafasheda kuka tofa wai anadara gadare yayi tuni Usman ya susuce sai sambatu yake saki menene yasaki kuka my heart wlh bazan taba iyah yinnesa dakeba bazantaba kaura cemakiba Dan Allah kidaina yimun hasarar hawayen nan nakie
Tashare hawayenta tace nasanda haka kawai ina tausayin kainane danasabarwa zuciya da soyayyarka wacce zata saka nashiga damuwa aduk sanda nawara ido bangankaba!!


Shiru tayi usman yagano maganarta toyazaiyi??? Inama khadija ce yafara aurah ba lubabatu ba dahar abada bazaitaba iyah yimata kishiyaba" ahankali yasoma rarrashinta yace koda yaushe kikaso ganina zankasance taredake har acikin barcin kima yayi maganar yana dago fuskarta yasoma kissing din bakinta rayuwa kenan soyayya tanada dadi aure maikumshe da rahama da nishadantuwa""" Allah yasada kowa da masoyinsa na gaskiya dankuwa duk matarda Takai mijinta wajen boka danyasota kodan karyamata kishiya kodan tajuyashi yanda takeso inaso tasani wlh karya take bata sonshi

Bawannan ake kirah soyayya ba" abunda ake kirah so kiso duk wani abunda mijinki yakeso farine ko bakine matukar dai abun baisabawa addiniba kuma baisabawa koyarwar *Annabi Muhammad (S A W)* to tazama mai murna dahakan kaitamafi mijin jindadi wannan shine cikakkiyar soyayya



Tuni Usman yamantarda khadija bacinran datake ciki idan sunatare kowannensu mantawa yakeyi dakowa sunaji tamkar babu wadansu mutane aduniyarsu

Tamkar sune kawai suketa shawagi awata duniyar daban usman yana rikita khadija da zazzafar soyayyar shi " shikanshi baisan ya iyah soyayya irin hakaba saiyanzu

Ashedai komai lokacine dashi duk Wanda yake faranta maka bakasanin sanda sonsa da kaunarsa zaiyita linkawa azuciyarka""

Tuni khadija da Usman suka tsallake siradin masoya sunacen sunajin dadin rayuwarsu irinta ma aurata sosai yanzu khadija tasaba dayawan butakar Usman"" dama" cen batadamuwa kuma bata taba nunamasa batasoba kullum tayi sallah tana rokon Allah yasake bata juriya dakuma kokarin biyawa mijinta buktarsa akullum bata mantawa dawannan acikin sujadarta takanyi tsayuwar dare tana rokon Allah karya nuna mata ranarda zata gajie

Cikin ikon Allah dakuma hikimarsa khadija Sam batajin gajiya kamarma karamata karfi akeyi Hakika duk abunda kasa Allah aciki baxaka tabeba hakazalika idan kasa abu aranka Inhar na alkhariine sai Allah yataimakeka wajen cika burinka








Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 92
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽




Akwana atashi babu wuya khadija da Usman harsunyi wata biyu da sati uku bayan sunyi wata da sati biyu adubai daganan sukaje India sati daya sukawuce America sati biyu dagacen sukawuce kasa maitsarki satinsu daya sukadawo madina sukai sati khadija tayi ziyara tasha kukan farinciki bata taba tunanin zataganta kusa da kabarin fiyayyen halittaba Allah kenan maiyin yanda yaso dagacen suka dawo Dubai suka fara shirin dawowa gida


Al amarin sarauniya lubabatu kuwa tunda taga har anyi wata uku harda kwana biyu Usman baidawoba haka zalika duk tayi wayadashi bata taba nunamasa waiyadawo saitace yazauna abunsa yaci amarcinsa

Saibayan sungama wayar takama kuka haryanzu ta gagara samun abunda akace takawo ganin wankin hula yanashirin kaita dare kawai tayanke shawarar ziyartar asibiti taje kasuwa tasiyo likaf da safar kafa"" dama tanada manyan riguna ma aikatan gidansu ta aika suka samo mata mangwaro gashi baijima da farawaba "" yana wuya shima dakyar yasamoshi

Washe gari tashirya tasaka kayanta Amman batasa nikaf dinba tafita cikin motarta saida takai asibitin tasaka nikaf din taxuba mangwaron da boka yabata ajaka Wanda aka. Dibomata ahannu tatusa raggaduda ajikinta tadawo tamkar maiciki dama tanada sarbano saicikin yataso"" sosai
Tafito tana turah ciki tatafi wajen da masu ciki suke zama idan sunzo awo matarda take wajen tafi mace Dari towazataba wakuma zata hanamawa

Mata dashegen kwadayi musamman masu ciki dazaran taga Abu saitace yawunta sunkawo tabbas inhar zata fitardashi awajen bashakka duk matanda suke wajen saisunci aikuwa za ayita haihuwa jikinta baiyarda tayi hakanba dankuwa asirinta zaitonu idan hakan tafaru ga mace sama da Dari alokaci daya

Tatari layi itace ta Dari da talatin"" zaune tayi waje daya"" tayi shiru matarda take kusa da itah sai zubarda yawu takeyi duk saitaji zuciyarta tana tashi mikewa tayi tabar wajen

Takoma cen bayan wani dakin Amman tahanyar masu zuwa awo cen bakin kofar shigowa tahango wata maiciki tafe tanadaga kafarta dakyar"" lubabatu tayi saurin Ciro mangwaronta tanasha Sam batakallon wajenda matar take kamarma batagantaba

Hartakawo inda take zatawuce saita dawo tace asslamu alaikum"" lubabatu wacce taturo ciki tace wa alaikumus salam""

Matar tace Dan Allah baiwar Allah inbadamuwa mangwaron kinnan zakidan sammanie yawunane sukadan tsinke"" lubabatu tasaki fara a tace Allah sarki bakomai barinabaki dama biyune aka samomun tasa hannu ajaka tadauko mangwaron tabata""

Matar takarba"" tasoma sha"" tace Amman ba awo kikazoba naga kinzauna anan??? Lubabatu tace shinazo wlh mutane sunyi yawa sainadawo nan din Amman ke aikin makara bakizo dawuriba

Tace hmm wlh dakafa nakezuwa kuma akwai nisa daganan zuwa gidanda nake"" lubabatu tace ayya to ina maigidanki matar tace kedai bari tasamu kusa da lubabatu tazauna dakyar tace mijina bayason haihuwa

Tunsanda mukai aure Anty saiyana bani wani maganie inasha bansan nahana daukan cikibane sai ranar najishi dadare yanafadawa abokinsa dan nataba samun ciki saida yayi wata uku yazube Ashe lokacinda banda lafiya allurarda akamun tazubarda cikine

Nikuma tundaga lokacin sainadaina shan maganin idan yabani saina kaikaici idonsa inwatsar dayalurah nasamu ciki duk da boyemasa danakeyi duk wahalarda cikin yakebanie aikuwa tunda yagano yace waibanida lafiya bariyakirah amun allurah nikam nace fafur lafiyata qalau dayanace saina nunamasa baxan yardaba kuma naji firarsa da abokinsa

Tundayago naji yace koda tsiya sai anzubar danshi baiyi shirin tara yaraba nayi kukan takaici da aurensa dama shine illar ka auri Wanda bakasan asalinshiba
..
Sanda yazo aurena iyayena basuyi wani bincike akansaba ganin yanada kudi kawai aka auramunshi "" gashi iyayena yan Cameroon ne acen ya auroni"" yakawoni nan banida kowa bansan kowaba"" tundaga lokacin yakwashe kayan abincinsa duka baya bani abinci duk da katon gidan da nakeciki saidai inje inyo bara asace inci abinci idankuma yakamani yace wai Zanzubar masa da mutunci yalakadamun shegen duka Amman banfasa zuwaba saboda bazan zauna yunwa takasheniba tuni yahana kowa shiga gidansama

Ganin bazan daina fitaba shine yasiyo garin kwaki kullum idan zaifita saiyabani gwangwani daya darabi hakanan bakomai haka zanjikashi inci"" saiya fara shigowa dayan matansa suna holewa matansa suna sakani dahuwar abinci tanan ne nakesamu inci maikyau watarana wasuma harkudi sukebani danyacemasu nidin Yar aikin gidansace

Dana lurah cikina ya isah zuwa awo shine nasoma aiki wani gida aboye inamasu wankakau anabiyana harnatara kudi yanzu inajiran kawai nahaihu natara kudin mota zankoma garinmu

Dama date din haihuwata Yakama likita yace dazaran nawuce sati banhaihuba indawo togashi harnakara sati biyu""

Lubabatu taji tausayinta sosai tace natausaya maki gaskiya hannu tasaka cikin jakarta tadibo kudi masu yawa tabata tace idan tasauka lafiya tayi hidimar biki dasu tanata godiya harda kukanta

Tatambayi sunanta tace Mariya"lubabatu tace kefa??? Maicikin tace saudatu""cikinta taji yafara motsawa tace Anty Mariya barinaga likitan zansameki Annanko "" lubabatu tace ah tatashi tanaturah ciki tawuce

Tana barin wajen lubabatu tamike tafita tashiga motarta tacire likaf tana saukarda ajiyar zuciya tatada motar ta cikin farinciki tawuce gida

Al amarin maiciki kuwa tana kaiwa cikin mutane ciwon Mara yataso mata taduke dasuka lurah haihuwace suka dauketa aka Kaita wani dakin akakirah wadansu likitoci kunsan likitoci akwai dagawa kowacce akakirah saita ce akwai abunda zatayi

Matarda taje Kiran likitocin harda kukanta"" dakyar tasamu wata kiristan tace sutafi koda sukazo saudatu harta gama fita hayyacinta gakan danda yafito Amman barai dantuni aljanin yazuke jininsa

Tanazuwa tajawoshi saigawani yakunno kai koda tasoma jawoshi daransa kafin yafito babu rai ko kuka baiyiba itakuma tuni tasuma aljanin yanaganin haka yabace yana mai murna dawan nan jininda yasamu

Matarda takirah likitar tayita kuka tana tsinewa likitocin ba ita kadaiba duk matanda sukewajen laifin likitocin sukaganie aidasunzo dawuri dayaran basu hawalaba harsuka kaida mutuwa

Abunda basu saniba kowa bayawuce kwanansa Hakika hakane Amman dangane da wulakancinda likitoci sukeyiwa marasa lafiya bakarya bane barinma likitoci mata wlh masu imani acikinsu kalilanne

Kumawai musulmai dankuwa MASudan tausayin zakasamu kiristanne Yar uwa Norse shinbakisan ladarda zaki samuba idan kika taimakawa Yar uwarki tasauka lafiya

Karki manta"" biyanki akeyi ga albashi ga ladakuma Abu biyu zakisamu Amman saikuga mace tazo haihuwa wlh wasu har Marin mata sukeyi waisuncika raki tasan bazata iya haihuwaba meyasa tayi aure sanda takejin dadinta damijinta meyasa bata tuna wannan ranarba

Kosuhau yimata fada waitadamesu da kuka ninan shaidace akan wulakancin likitoci mata waikina tunanin Allah bazai kamakibane??? Koke aganinki bakomai bane wannan mezaihana idan akakawo marar lafiya kirika kwantarmasa da hankali

Dagashi harmai jinyarsa kirika fadamasu magana maidadi saikiga kowa yanasonki kobayan ranki wlh zakisamu kyakkyawan yabo zakuji anacewa Allah sarki ai wlh doctor wance mutuniyar arzikice tayikaza tayi kaza Allah daiyajikantà Amman idankedin mugunyacefa kina tunanin Wanda kikayiwa rashin kyautawa danbaida lafiya idan yaji labarin mutuwarki zainema maki gafarar Allah

Bazainemà makiba wlh"" sannan kisani wannan abunda kikai sai anyiwa zuri arki kodakuwa kin mutune acikin yayanda kikabari ko jikoki keharkema bakiwuce hakan tasamekiba tundakema kina rashin lafiya kuma kina haihuwa

Rokona agareku likitoci kusan irin yanda zaku kyautata alakardu da majinyatanku"" kodakedin ba likita bace Amman kinasaran zamowa anan gaba saiki sanyanda zaki kyautata alakarki

Allah yasa masuhakan zasu gyara wadanda basayi kuma Allah yasake sakamasu imani da tausayin marasa lafiya dankuwa duk Wanda kaga bashida lafiya shikawai yasan abunda yakeji aransa idankayiwa Wanda yake gangar ajali rashin mutunci yazakaji idan akacemaka ai majin yacin nan yamutu Allah yakyauta

Saudatu bayan tafarfado akanuna mata gawar yayanta tayi kuka hartagodewa Allah tadangana tasan damacen sudin bamasu tsawon raibane tadauki yaranta koda tafito duk masu ciki sungama awo suntafi tace Allah sarki Anty Mariya watakil tayi nemana bata ganniba kuma gashi bansan unguwarda takeba

Datakoma gida mijinta yaga gawar yayan yayita kuka Allah yadauki son yayan yasakamasa azuciyarsa sanadin hakan yakamu daciwon zuciya

Itakuma tace yasaketa garinsu zatakoma yayita bata hakuri yace wlh yanzun yanason Yaya Allah yadoramasa son Yayansa dukda basa raye harkasa yaduka yana Neman yafiyarta tokunsan tsakanin mata damiji sai Allah tayafemasa Amman tace saiyaje an aunashi Idan bayada cutar HIV batareda musuba yaje tareda itah ma sukaje aka tabbatar bayada cutar komai sannan sukacigaba dazamansu cikin soda kauna kamar yahadiyeta yakeji""" sai rokon Allah yake Allah yasake bashi kyautar yan biyu


Al amarin lubabatu Kuwa tatafi datunanin wannan saudatu din ganin tunanin baida amfani kawai tawatsardashi takama harkokin gabanta

Ranar Usman yakirata yace gasunan zasu taso"" tasa akashirya masu abinci na musamman koda suka sauka bayan isha"i taturah habu driver yaje daukarsu

Sunyi kyau sunyi kiba Usman harwani sheki yakeyi alamun yaji dadin amarci rayuwarsa tayi kyau tunda lubabatu taganshi wani bakin kishi yataso mata baki sake takebinsu dakallo saiga kuka yakwace mata

Shikuma Usman daukarsa kukan murnane dasauri yasake hannun khadija yatafi yarungume matarsa yana saukarda ajiyar xuciya ahankali yasoma shafan bayanta murya cikin kuka tace nayi missing dinka sosai mijina"" cikin zakuwa shima yace nima wlh nayi missing dinki matata kullum cikin tunaninki nake

Khadija tuni tasadda kanta kasa wasu hawaye masu zafi suka sauko mata ganin idan tatsaya tacigaba da sauraren ma auratan kukanta zai iyah fitowa hakan yasa taja kafarta dakyar tahau na urarda zata sadata bangarenta tadauko mabudin bangaren tabude tashiga bangaren duk yayi kurah Amman batadamuba tashige dakin saman gadonta tafada tasoma darzar kuka marar dalili😭😭😭😭






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 93
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽




Ah kuka marar dalili mana tunda batada ikon hanashi kusantar matarsa kamar dai yanda itama matar bazata hanashi zuwa gunda takeba

Aranta tace waidama haka akejin kishi??? Lallai najinjinawa mom danamijin kokarinda tayi harta iyah barwa dad ni tabarmana kwanakinta bayankuma tasan abunda zamu aikata abunda tayin nan koni bazan iyah ba gaskiya.

Gashi daga zuwanmu harnaji daban"" Allah kasamani hakuri acikin zuciyata indinga kauda kaina akansu"" Usman kuwa Sam baisan khadija tabar gurinba sai liliyar matarsa yakeyi"" sundade tsaye sannan taja hannunsa sai alokacin yaduba baiga khadijaba

Aransa Sam baiji dadiba kaitsaye bangarensa suka nufa tahadamasa ruwan wanka koda yafito harta fitomasa dakayan dazaisaka bayan yasaka kayan ya simpida abar sallah yarama sallarda take kansa

Bayan yagama lubabatu tace suje yaci abinci tasan yakwaso yunwa tana makale da hannunsa suka sauko kasa haryazauna yamike

Takalleshi inakuma zakaje"" murmushi yasakarmata yace badadewa zanyiba zanduba Deejarh nane baijirah jin mezata ceba. Yasakai yawuce
Tabishi dakallon takaici kamar tature duka abincin takeji kodayake bakomai aidaga yaune yarinya ""

Koda yakarasa dakinta harkurya yashiga yana karkabe kurah tana kwance saman gado tanajin sallamarsa tayi saurin goge hawayenta tatashi zaune ta amsa sallamar tana kirkiro murmushi tace waiharkayi wanka

Murmushin shima yake yana jefenta dawani kallo kusa da itah yazauna yajuyo fuskarta tanoke kanta yace hmmn kuka kikayiko???

Tace ah ah banyi kukabafa??? Saiga hawaye sunzubo sharrrrr yalakuto hawayen dadan yatsansa yace wannan shine shaidar bakiyi kukanba"" shiru tayi yace saunawa nake fadamaki hawayen nan naki tsadane dasu meyasa kikeyimun asararsu

Cikin dasasshiyar murya tace kayi hakuri bazan sakeba yanzumna nakasa tsaida kukanne"" yace tomezaisa dole saikinyi kuka

Ahankali tadago takalleshi da idanuwanta wadanda sukacika da hawaye tace nikaina narasa dalilinda yakesani kuka

Abudaya kawai nasani nakanji kukan yazo batareda natarbeshiba takai karshen maganar hawayen suna zubowa. Yajata jikinsa ya isah haka Deejarh Na nafuskanceki insha Allah zankiyaye

Tasake lafewa jikinsa tana saukarda ajiyar zuciya bayan wasu lokutta yace tashi inhadamaki ruwa kiyi wanka kingafa ko sallah bakiyiba muje muci abincin nasan cikin nan naki yanajin yunwa

Noke kanta tayi tace kaje kawai innagama zansauko kar mom taga kadade"" yace kinga kitashi konadaukeki dakaina naimaki wankan dasauri tamike tace yihakuri towel tadauka tashiga bandaki shikuma saman gadon yadan kwanta yana kallon silin tunaninsa daya yazaiyi da kishin da yalura khadijansa tanadashi akansa

Sam bayaso yaganta cikin damuwa kuma hakan bashizaisa yadaina kula matarsaba danma yasamu lubabatun maihakurice"" yana kwance hartafito tashirya doguwar Riga tazura bawata doguwar kwalliya tayiba"" tatada sallah saida tagama sannan yariko hannunta suka sauko
.
Lubabatu tunda suka Dade ranta yasake bacii" tadawo cikin falon tazauna takunna kallo"" kamshin turaren khadijane yadawo da hankalinta inda suke saurin kawarda kanta tayi"" kusa da itah yazauna yace rankiyadade inafatardai banyi laifiba "" murmushi tasaki tace wanne laifi kuma kaida matarka kamardai amarcin haryanzu bai ishekaba

Kunya ce takama Usman yadan Sosa kai yana kallon khadija kasa kasa"" itakuwa idonta yana kasa tunda sukazo wajen"" yace bahaka bane maman Abdul"" tace tomene idan amarcin bai ishekaba ashirye nake danasake sadaukar maku da kwanakina harsaikun gajie

Aran Usman yace indai zakibiyemu bazamu taba gajiyaba Amman azahiri murmushi yayi yace ah ah aiwan nan makadai mungode kohakan kikatsaya dolene najinjina maki yariko hannunta muje kibamu abinci nitundaxu hadiyar yawu kawai nake

Yaja hannunta suka wuce khadija tabisu abaya kamar kazarda kwai yafashewa aciki"saman dinner suka zauna sune gefe dagefe sunsaka Usman atsakiya"" lubabatu tazuba masu abincin sukasoma ci tanagefe tana kallonsu

Khadija kam saiyawo take da tsokali acikin plate takasa cin komai"" Usman ya dibo nasa yanufaci bakinta dashi tadago fuska takalleshi murmushi yasakar mata "" yalumshe idanuwansa yabude alamar taci itama tamiyar masa damartanin murmushinsa takarba Sam tamanta da lubabatu tana wajen

Rayuwarsu ta Dubai kawai take tunowa ganin hakan yasa lubabatu mikewa takoma falo tacigaba dakallonta dankarta kalli kayan takaici

Amman acendinma takasan ido take satar kallonsu"" yayita bata tanaci itama tadauko tasoma bashi idan tayi masa babbar loma yakasa hadiyewa takamayi masa dariya

Sosai sun shagaltu sun mantama dawata lubabatu saida suka koshi yagogemata bakinta sannan yaja hannunta suka koma cikin falon suna zaunawa wayarsa tahau ringing yadauko yaduba yana murmushi yamikawa khadija

Ganin ansa Yayana takalleshi saikuma tadauka tareda murmushi"" daya bangaren akace amincin Allah yatabbata agareki Kanwata"" tadaga ido takalli Usman shima itah yake kallo tace taredakai Yayana""

Yace yakike ya gidan Yakuma gajiyar tafiya nasan bakujima dasaukaba da mamaki tace waidama kasan bama NaN??? Yace sosaima aimuna waya da dady tabata fuska kai ya muktar Amman shine kokace abanie mugaisa

Yace kwantarda hankalinki ainakusa dawowa abunda yasaka bance abakiba banason shegen surutun nan naki zaki iyah share mijinki kiyitamun zuba damadai konakirah Dan inji lafiyarkine Kuma dad yafadamun qalau kike saime kuma

Tarausayarda kai tace Amman duk dahaka banji dadiba saina fadawa sahibata"" yace rufanie kisayani bazan iyah da itah ba "" tahauyimasa dariya sundade sunafirah sannan tabawa Usman suka gaisa bayan sungama wayar tace dad kakiramun sahiba inata zuba ido munyi da itah zamu sameta anan Amman bangantaba

Yace gawayar nan ahannunki nantake gaban lubabatu yabada rasss khadija takamo lanbar tayita kirah akace ba network karshe tahakurah dole tabashi wayarsa

Yace yadai batashiga tace ah taredajan karamin tsaki"" mikewa tayi tace mom saida safe"" lubabatu tace harzaki kwanta??? Tayi hamma wlh nagajie mom zaman jirgi badadi"" tace shikenan Allah yatashemu lafiya tace Ameen batareda takalli inda Usman yakeba tawuce abunta

Yakalli lubabatu yace bari narakata indawo kai kawai tagyada masa yamike yabita abaya"" taresuka shiga Na urarda zata sadasu hawa nahudu

Suna kaiwa yasunkuceta zuwa dakin "" saisaman gadon yadireta saman jikinta yakwanta rabinsa yanasaman gadon kallon juna sukeyi ido cikin ido "" daga bisani yahade bakinsu waje daya yana tsotsa ahankali cikin kwarewa

Sundade ahakan ganin yanashirin wuce gona da iri tamirgina gefe"" tanamiyarda nunfashi kamar yanda shima yayi idanuwansa harsun soma rikida ahankali yasake mirginowa zaisake hada bakinshi danata tasa gefen hannunta takare

Cikin kasalallar murya yace menene haka my heart??? Takwantarda idanunta tace basaina fada makaba kasan yau dole zaka kwana wajen mom ne baidace ka aikata abunda kakeson aikatawaba

Katuna yanzun bani kadai bace kaje wajen mom nasan zakasamu abunda kakeso acen itama tanada bukatarka"" tunda tafara maganar yake kallon Dan karamin bakinta hartagama"" yace bazanyi maki komaiba Deejarh kibarni nayi wasa dake"" kafin tabude baki tayi magana haryasake hade bakinsu waje daya"" babu yanda zatayi itama tacigaba damiyar masa da martanie dakyar ya iyah raba jikinsa danata yamike yacemata saida safe batace masa komaiba haryafita tabishi da kallo tareda zartowar hawayenta saman kumatu tashi tayi tarufe kofa"" takoma tazauna tayita darzar kuka harbarci yadauketa


Usman yana fita baisamu lubcy falon kasaba kaitsaye dakinsa yawuce yasameta kwance saman makeken gadonsa tayi daidai idanuwanta alumshe tamkar maibarci

To dama khadija ta takulomasa sha awa ganin lubabatu kawai saiya kashe wutar dakin"" toilet yashiga yasake watsa ruwa yayi shirin kwanciya yakwanta ranarma sosai lubcy tanuna mashi tayi missing dinsa bayan sungama raya dare barci yadaukesu

Da asuba bayan Usman yayi wanka yayi shirin zuwa masallaci lubcy batayarda takoma barciba yanafita dakin khadija yanufa yasamu kofarta akulle yayita bugamata cen cikin barci taji tace natashi"" yasakai yafita yatada sauran ma aikatan gidan suka wuce masallaci

Saida lubabatu taji Tsit alamar kowa yawuce sannan tasadado bangaren khadija takwala mata Kira khadija innalilahi wa inna ilaihir rajiun shikenan labila tatafi tabarni khadija tun lokacinda Usman yake tashinta bata tashiba

Jin ance labila tatafi tabarmu ahirgice tasauko daga kandagon tabude kofa tace mom meyasamu Sahib""batagama rufe bakintaba kawai taji kamar anshafeta nantake tasulale kasa saikuma yasunkuceta batttt yabace

Lubabatu tana ganin hakan tasauka kasa dasauri tanasauka saitaji anbuga kanta dagini nantake tafadi kanta yasoma fitarda jinie

Koda akagama sallah Usman yaji gabansa yana faduwa yaubaima tsaya haske yafitowa kawai yataso yana kawowa yahangi mota tabar kofar gidansa atsiyace dasauri yakarasa kofar gidan tareda daidaikun ma aikatan gidan dasuke taredashi dankwalin khadija yafara ganie dasauri yadauka cikin mamaki yana kallon gidan dagudunsa yayi hanyar gidan

Habune yaga""Farar takardar kofar gidan yayi saurin dauka
yabudeta rubutunda sukejikinta layi dayane darabi mune muka sace matarka kuma kasheta zamuyi karka wahalda kanka wajen nemanta!

Usman yanashiga gidan ahirgice yaga lubabatu kwance cikin jinie kawai rayuwarsa tayardar masa Deejarh sa aka dauke take yayanke jiki yafadi

Please Login or Register in order to submit comment