Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yakeciki Yakoma dasauri yadauko key din mota riga ahannu yafito

Haryanzu usman jijjiga ameena yakeyi idanuwansa sunyi jajir tamkar gauta kadan yarage yasoma darzar kuka saidai kawai danyana namijine yanada juriya"" tuni driver yabude masa bayan motar yashiga da itah shikuma yazagaya yafita dasauriii zuwa hospital""

Tunkafin sukai yakirah family doctor dinsu yasanar dashi yace yana asivitin dan yana dutyn dare ne"" sunakaiwa yanabakin asivitin tareda wadansu nurse tareda gado""" yanayin pkng yadaukota akaturahta saman gado zuwa emergency

Abakin kofa akabarshi Saikai kawo yakeyi tamkar yayi kuka"" tunda suka shiga da itah sukahau dubata saidai Ashe raiyayi halinsa"" zuciyarta ce tabuga!!

Sosai yayi mamakin ciwon zuciya dahar yacita haka haryayi mata wannan illar Amman Sam shi baisan ciwon nata yakai hakanba"""

Jiki asanyaye yafito dakin tareda sauran nurse "" Usman yana ganinsa yasoma tambayar lafiyar meenal""

Doctor yajikinta ???? Tasamu saukiko???? Dan Allah zan iyah ganinta?? Banaso narasata doctor haka yayita jeromasa tambayoyi tamkar maitabin hankali

Gabadaya yabawa likitocin tausayi"" yace doctor bakace komaiba yajikin meenal din?? Yanisa yace tasamu sauki yadafashi saidai kayi hakuri Usman

Koda kukashigo asivitin nan tuni Allah yakarbi abarshi""" cikin razana yadago manyan idanuwansa yadorasu akan doctor din

Hannunsa yasaka yature hannun doctor dayake kan kafadarsa yayi cikin dakin dagudu doctor yabishi yana kiran sunansa

Yanaashiga yajaye kyallenda aka rufeta dashi fuskarta tayi fayau tamkar tana murmushi tayi haske dukawa yayi akan guiwarsa yariko hannunta cikin nashi

Cikin rawar murya yace yanzu dama tafiya zakiyi kibarni meenal duk wannan abun dakikemun na bankwanane take yafashe dakuka """

Doctor ne yadafashi yace hakuri zakayi Usman lokacintane yayi babu magani saimuyi mata fatar Allah yajikanta yasa tahuta"" ayanzu adduarka kawai takebukata

Mikewa yayi yayi hanyar fita""" saidai yaji yarabke yafadiii dasauri yakarasa wajensa yanakiran nurse "" dagudu sukazo akadauki Usman akadorah akan gado take aka bashi taimakon gaggawa

Ganin yafarfado yasaka akajona mashi Karin ruwa tareda allurar barcii "" driver"" yana waje baisan halinda uban gidansa yake cikiba"" saida doctor yasanar dashi"""

alokacin ansoma kiraye kirayen asuba" wayarsa doctor yadauko aka Kira hajiya akasanarda itah"""

Karfe bakwai darabi yamata acikin kaduna tuni labari yakai gidansu ameena"" mahaifin Abdul da Abdul suna asivitin
Tuni akadau gawar ameena zuwagida dangin ameena saidai sukaji mutuwar kamar dagasama

Koda yafarfado hajiya da Hafiz sunakusa dashi hawayene yasoma sauka gefen idanunshi hajiya tace sannu babangida""

Runtse idonsa yayi yace mom tatafi tabarniko??? Tashafo kansa tace addua zakaimata babangida lokacintane yayi"""

Yanisa inason ganinta kicewa Hafiz yakirah doctor"" takalli Hafiz tace yakirashi yace to tareda juyawa Abdul yadawo kusadashi yadafa kansa Amman yakasa cewa komai"" yana tausayin abokinsa danyasan yanason ameena sosai

Doctor yanazuwa yace badamuwa yana iyah zuwa"" taresuka fito suka dunguma"" saigidansu Ameena sunsamu har anyimata wanka""" Usman yamatsakusa da itah yayi mata addua tare akai mata sallah

Tatara mutane sosai akakaita makwancinta""" Sam babu Wanda yatuna da kaleed saibayan da hajiya takoma gidan tasameshi yanata kuka sosai ta tausaya masa"""

Saida akai sadakar uku kubra tazo tareda mijinta"" itakanta tasha kuka datasamu labarin"" Usman yakoma shiru shiru dagashi har kaleed sunrame danbasacin abinci sai hajiya tayi dagaske

Bayan wata biyu darasuwar Ameena zuwa yanzu Usman yafauwalawa Allah lamarinsà"" Yakoma wajen harkokinsa Amman haryanzu baikoma daidaiba

Hajiya takoma tareda kaleed hannunta saboda haryanzu yaki kwantarda hankalinsa"""

Kwance take tanajuyi cikin barcinta"" zunbur tatashi "" tasoma dube dube mafarkinda tayi kamar almara"""ihun murna tayi tamike yauzataga handsome dinta towadanne irin kayama zatasaka tarasa inda zatasaka ranta danjin dadi

Mikewa tayi tafada wanka"" agurguje tayi wanka tashirya cikin atamfa takawo hijabinta tasaka harkasa"""

Wayarta kawai tadauka tafita unguwar kowa yayi mamakin ganinta da hijabi akafa take tafiya tayi nisa da unguwarsu sosai wata motace tayo cikinta sauran kadan tabugeta tayi gefe dasaurii Amman dukda haka saida yasameta aikuwa tafadiii kiiii yatsaida motarsa yafito dasauriii dasauriii yana furta innalillahi tadago takalleshi tuni tawashe hakorah tunawa dazancen *hatsabibin boka* yasa tayisaurin dukadda kanta gabanta nafaduwa

Muryansa maisanyice taratsa dodon kunnenta sannuko inafatardài bakiji rauniba??? Kaitagyada masa tamike tana karkabe hijabinta"" yakuramata ido takeyaji Sonta yashiga ransa talurah da irin kallondà yakematà dadi kamar tafasa ihu arantakuwa tana aiyanawa ashema yafi kyau afili





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 25
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽


Muryansa tasake katsemata tunani yace inazakije yanzu??? Cikin sanyin murya tace mamana ta aikeni inyomata cefane"" yayi murmushi yace to idan bazaki damuba muje mana kisiyo daganan sainakaiki gida nabada hakuri

Tadan waro ido tace hakurin mezaka bayar nifa banji ciwoba"" yasake gyara tsayuwarsa yace duk dahaka sainakaiki gida daganan sainaga waje aiko ??kobakyaso zumuncin mu yadorene?? nalurah kinaso kidatseshi iyah nan""

Munmushine ya subuce akan fuskarta tace waceni aiban isah ba Amman naga kaima kanada uzuri kawai kabarshi nagode zanhau Dan adaidaita"" harararta yayi cikin wasa yace tozanga yanda zakihau Dan adaidaita gani kusa ashekuwa yau akwai rigima

Tace la abunfa duk baikai hakaba"" nayarda muje Amman idan mukaje unguwarmu nesa dagida zaka ajeni"" yace najidai muje

Dakansa yabude mata gaban mota sukashiga yaja yasoma tafiya kifa nunamun wajenda akesiyarda kayan miyan"" batareda takalleshiba tace kana cikin legos kace bakasan inda ake siyarda kayan miyaba"""

Murmushi yasaki yace ashekuwa yauzamuyi tayayo agari idan harsaini zan kaimu wajen"nida nake bako saiyanzu takalleshi tace wai dagaske kake???? Yace todakumafa nayimaki kamada yan Lagos????
Tace ausu yan legos harwata kamane dasu????

Yace sosai aidakingansu zakiganesu kullum suna sanye da dangakallun kaya"" sannan Kuma basada Faraa gadukkan alamu kema ba yarnan dinbace""tace ya akai kasanhaka??? Yace dabi unki mana"" ke komainakima so nice

Murmushi tayi maidan sautiii tace kaidai wlh kafaye zolaya!" Sunakawowa daidai wata kwana tace nan zakabi""" tayita nunamasa hanya harsuka kawo

Karyafa tasheramasa dankuwa bata tabazuwa siyen kayan miyaba"" toyanzu idanma tafita batafitoda ko asiba"" karfa asirinta yatonu yagano karya tashekamasa jitayi yabude mota""" zatafita yayi saurin dakatarda itah yace dame dame za asiyo??? Cikin rawar murya tace komaima

Kaitsaye yawuce wajen maikayan miyan dayake inyamurine yace yahadamasa kayan miya"" na dubu biyar komai ahada"""

Nankuwa akahada komai harda cucumber da kabeji dasu carrot" saida yanuna mata yace dubakiga ko akwai abunda babu asiyo"" tace komai akwai sannan akazuba bayan but sukakoma

Tace kayan miyanfa sunyi yawa"" yace to kibawa wani idan sunyimaki yawa"" kidai nunamana hanya karmu bace""

Dariya tasoma kai malam akwaika daban dariya wlh"" takasan ido yake kallonta tana matukar burgeshi sosai"" yace basunana malam ba sunana Usman"

Ido tawaro tace sunan uncle dina"" yace dagaske kenan nima nazama uncle" dinki""" tace sosaima
Yanda sukeyin firah hankali kwance idan kagansu saika dauka sundade dasanin juna"""

Suna kawowa unguwarsu tace ajeni nan zankarasa"dakafa
Batareda yakalletaba yace babu amfanin zuwan nawa kenan tunda banga gidaba"""

Ahakan tanuna masa gidansu""" yayi hon maigadi yahangame masa kofa yakutsa kan motarsa kamar wani dangida""" bayan yatsaya da motar"" yajuyo yana fuskan tarta yace gashi harmunkawo Amman bakifadamun sunankiba"""

Naga abun yar rowar sunace""murmushi tayi taboye fuskarta cikin hijabi tace sorry aiban isah nayiwa uncle rowar sunanaba"""

Yamurmusa yace nifa banyarda da uncle din nanba''' tarausayarda kai tace saime???? Yace aboki daganan kuma saiyayi shiru yana kallonta yanadariya kasa kasa

Murmushi tasakeyi tace bari nashiga gida kar mom taga nadade""" yaduba agogon hannunsa yace shikenan ataimaka abani phone no"""
Wayarsa yamika mata afuskar wayar PIC dinsane da Ameena kaleed yana tsakiya""" talurah da pic din saikawai tawuceshi tasaka masa Tamika masa
Tace katsaya koruwa kasha""" ah ah inasaurine wlh akwai abunda nazoyi gobema zankoma Amman zansake zuwa gobe saimu gaisa""

Tabude motar tafita"" kayan miyar yafitomata dasu tabawa maigyaran fulawa tace yashiga dasu cikin gidan

Sukai sallama tasake masa godiya tawuce yace amm jimana"" tajuyo ciikin wani salo Wanda yakusa sumarda Usman da ido tamasa akamar menene??? Yace sunan???/

Tadan dafe kai sorry namanta lubabatu tanafadàr maganar tayicikin gidan Usman yabita da murmushi wani sanyi""yaji yanaratsa dukkan sassan jikinsa rabonsa dayaji farinciki haka tunranarda meenal tabar duniya

Murmushi yayi yashiga motarsa akabude masa get yafita Sam baiso zuwa legos dinba Ashe arzikine yake kiransa aransa yake ayyana hakan

Tanashiga tasamu mom dinta tanadubà kayan miya""" tanaganinta tace lubcy wadan nan kayanfa??? Batareda takalletaba tace kiyi amfani dasu wanine yasiyamun tawuce bangarenta

Mom dinta tajidàdi aranta tana adduar Allah yasa saurayintañe dantamatsu lubcy tayi aure

Tanashiga daki tacire hijab tawurga akan gado tasoma tikar rawa tana murna harda ihu wayartace tasoma ringing tadauko dasaurii ganin sabuwar nomber tasan shine takidagàwa hartayanke akasake kirah batadaukàba saida yasake kirah tadauka cikin yanga kamar yanaganinta ta amsa sallamarsa sannan tace waye





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠


chapter 26
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽


Murmushi yasaki maidan sautiii yace nashiga tara yanzun har ammanta dani ba aje ko inaba anya kinason zumuncin nan yadaure kuwa"""

Gabantane yafadi karfa garin jan ajinta ta lalata komai""" tayi saurin taran numfashinsa tace bahaka bane uncle kaga aibansan nomber nakaba kuma kasan waya yana sauyawa mutane murya dat way banganekaba!! Amman kayi hakuri

Ajiyar zuciya yasaukar wacce har lubcy tajiyota yace najisanyi araina"" itama murmushin tayi"" sukataba firah daganan sukai sallama

Lubcy tamkar tazuba ruwa akasa tasha Dan Murna"dole"yau taturàwa *hatsabibin boka* kayan aiki nagodiyà!"""
daren da itah dashi kasa barci sukayi kowa yana tunanin dayansa Usman jiyake tamkar kirjinsa yafaso zuciyarsa tafito saboda tsabarso nda yakeji nata yanahudashi"""

Kwance take cikin dakinta tana danne danne dawaya saiga kiran Usman yashigo"" da murmushi tadaga tareda sallama daya bangaren ya amsa""

Yace gani akofar gida"" tawaro ido harkazo??? Harararta yayi kamar tana ganinsa yace dolekice harnazo danke bakidamu da niba nida nadamu dake darenjiya kasa barci nayi"""

Tarike baki yihakuri uncle bawai haka nake nufiba ganinan fitowa"" takashe wayar akahau safe safe da feshe feshe saigata tafito das da itah tasaka hijabinta tafita""" mom dinta tanacikin falo zaune tace mom nayi bako kibawa kande kayansha takaemasa muna falon bakiii

Tawuce abunta" yanajingije jikin motarsa yakurawa kofar gidan ido yanaso kawai yaga bullowarta"" kirjinsa sai harbawa yakeyi dasauri dasauri yakuramata ido yanda take tafiya tamkar hawainiya komai nata tsaf

Kamar yanda yaraja.a akallonta itama haka shigarta yau Tayimasa kyau yau kananun kayane ajikinsa sabanin jiya dayasa manyan kaya idan kaganshi wlh koda anrantsemaka bazaka yarda yatabayin aureba sai idan kaganshi da matar kakuma tabbatar lallai itace

Damurmushi takaraso inda yake tagaidashi"" tace karaso ciki sukajerah harcikin falon bakin"" tazauna nesa dashi suka gaisa""" yace badadewa zanyiba zuwanayi kawai mugaisa zanwuce

Sam bataji dadiba Dan fuskar tama. Tanuna hakan cikin sanyin murya tace sai yaushe kenan?? Nasan dakyarne idan zakasake dawowa legos tunda bawajen zuwanka bane

Yayi murmushi yanawasa da key din motarsa yace zancen baya kikeyi aiyanzu zuwa legos yazama dole dankuwa nayi babbar mantuwa acikinta

Tace mantuwa?? togashi baka fitaba kakoma kadauko mana"" murmushi yasaki maidan sautiii yace kinaso ayimun ihu ace nasaci abunda banawaba!! zandauka Amman bayanzu zanjirah har abun yaxama mallakina

Tace inamaka fatan alkhairi""yace nagode daidai mai aikinsu tashigo dauke datire cike dakayan motsabaki na marmari dakuma danbun nama"" saida ta aje taduka tagaisheshi """

Ya amsa cikin skin fuska"" zatafita yakirata kudii yaxaro cikin aljihunsa zasukai dubu goma yabata"" taki karba saida yamatsa mata sannan takarba tayi godiya""

Bayan tafita bajimawa yaduba agogo yace yakamata intashi haka"" karnayi dare ahanya"" gashikuma ban gabatar maki dakainaba""

Nasandai bakimanta sunanaba"" inaxaune a kaduna yanzu haka anan nake tafiyarda harkokina Amman iyayena akano sukeda zama

Mahaifina Allah yamasa rasuwa inada kanne biyu kubra tayi aure sai Hafiz nataba aure karkiyi tunanin ni saurayine fuskarsa cikin murmushi yafurta hakan""

Yanisa Amman Allah yadauki abarsa tatafi tabarni dayarona daya kaleed tuni idanuwansa suka koma jajaye yace inasonsa sosai fiye dakomai arayuwa banajin zanso wani Abu samadashi

Idan naganshi yana debemun kewar meenal azuciyata"" banason abunda zaitabashi komai kankantar abun" wlh lubcy yaron tausayi yakebani

Yanzun yana hannun mahaifiyata "" inason narikajiñ dimin jikinsa akusa dani nasan mom bazata banishiba tunda bansan yanda zanrika kuladashiba aganinta zanraba hankalina gida biyu

Shine nakeson nayi aure" kozansamu wacce zatakula damu dannikaina inabukatar kulawar""" yadago yakalleta yace kinji takai taccen tarihina aranta tace duk nasan wannan"""

Afilikuwa tace Allah sarki Allah yajikanta""" yace Ameen toyanzu mekikace??? Tadanyi yake tace nikuma mezance???? Yasake gyara zamansa yace tomenene amfanin sanardake tarihina???

Takada kafada maybe kasanar danine as ur friend""" """ yace ya inatubka kina warwarewa"" dariya takwacemata ganin yanda yayi maganar

Yace dolekimuñ dariya danbakyajin abunda nakeji gamedake""basaina tsaya kwanakwanaba agaskiya lubabatu tunda naganki naji nakamu dasonki

Sobana wasaba""" kuma aurenki zanyi bansaniba kozaki iyah aurena amatsayina nawanda yataba yin aure yakai karshen maganar yana kallon fuskarta

Tadanyi Jim yace please lubcy"" tarausayarda kai tace tokabani lokaci inyi shawara"" yayi saurin tarar numfashinta yace yanada kyau hakan amman nanda gobeko????

Tawaro ido gobe kuma??? Nanda satidaya dai"" bakiyabude cikin mamaki yace um lallai dasaurana bansamu shigàba""bari nasamu wajen zama a legos

Dariya tasoma tanarufe bakinta tace lala nina isah nafurta hakan ayihakuri to abani nanda kwana uku"" yace biyudai koshidai sainakai zuciyatà nesa danzata iya bugawa!! tace to abarshi biyun
.
Yace yauwa amman please karkice baxaki aurenibà"!! Danzan iyah shigawani halin"" tayi murmushi saidai kajini kasha lemun mana tayimagana tareda nunamasa tirenda kedauke dakayan marmari"""

Yace banajin zan iyah cin wani Abu harsainaji matsayina yayi maganar yanamikewa"" tace Amman kasandai banji dadiba acekayi bako koruwan gidanku baishaba

Ahakan nasan iyah matsayinà"" yace yihakuri kinsan bansan yanda akeyin zancenba Ashe idan kazo dole kasharuwa

Zansha Amman bayanzuba sainasañ matsayiña




Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 27
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽


Tace shikenan"" saimunyi wayako"" yace ah Amman aizakimun rakiyaba ko anan zakibarni kamar saniyar ware???

Dariya tayi kai wlh kacika sa mutum dariya mujeto"" yace tofa dagayanzu kuka zanrika sa mutane.

Nidai banceba baban kaleed""" sosai yaji dadin sunanda takirashi dashi har farincikinsa yakasa boyuwa yace nagodefa" daidaii get din gidansu tamasa sallama takoma gida""

Yabawa maigadi kayanda yasiyo mata yace yakaimata cikin gida sannan shima akabashi dubu goma"" zokuga bakinsa harkunne saikirari yakewa Usman shikam saidai yace kara da akayi

Cikin gidan yashiga dasauri yana sallama niki niki dakaya"" ya aje gaban mom yace uwar dakina gashi inji alhaji"" takai bakin kofar dakinta tace barsu wajen mom tayi shigewarta

Mom tabita dakallo aranta tace anya lubabatu batada aljanu??? Koda tafita gidan nan tana fara a Amman tadawo fuska yakunai yakunai kamar lawashin albasa"" idan yakwana

Maigadine yakatsemata tunaninta yace yaunashiga uku uwardakina tana nema tamun bakinciki yanzun wannan Dan zinariyar tana nufin baiyimataba???.

Hajiyarce tace wayafada maka ado?? Kaidai bakagani saika maganta tashi katafiii"" yace toya za ayi hajiya wayaki alhairi"" dubu gomafa tashi daya wlh hajiya kingansu a aljihuna yayi maganar yana bubbuga aljihunsa yacigaba tunda nake samartakata kawowa yanzu babu Wanda yataba mun kyautar dubu goma

Keko dubu biyu ma duka alhazan dasuke zuwa wajenta shegiyar rowa tayimasu kanta aduwawu babuwanda yajeso yacire naira yabawani"""

Amman wannan tunda naganshi nasan Dan albarkane""🤓 Dan Allah hajiya kirarrasheta kartace batasonshi

Dama inada kwadayin dakwalen kajii kafin ayi auren na murmure"tace ado fisabilillahi kakoma wajen aikinka waikai meyasane kafaye shegen surutune uwa aku"""

Yace saihakuri hajiya sai hakurii"" matsalarda akasamu kenan"" ranarda aka haifeni gidanmu anataron biki wannan hayaniyar tayan bukiii haya haya sanadinta tatakulo nakuda nayowaje

Ashe surutun yanbikin yataba kakwalwata tun ina jariri idan nasoma dariya ina witsil witsil sai abun yabaki tsoro""

Yanbarka kowayazo saboda dariya sai yayi hawaye babana yakaini wajen likita yana tsammanin haukace takamani koda likita ya aunani yagano inada dauke da ciwon surutu kuma babu maganinsa harsaina cinye kaza Dari

Tunda aka haifeni zuwa yanxu inakan lissafi naci kaxa ashirin dabiyar hargamida ta amarcina kinga koyanzu akwai sauran 75 tukuna inwarke

Hajiya tace aikuwa baburanar dazaka warke dawannan surutun"" yace dainamun wannan fatar hajia kina raina surutuna kinsanfa magana jarice inaji ajikina dawannan surutun nawa zanyi arziki

Tace ahakan? Aiwannan surutun bayan duka babu abunda zaijamaka"" aisaidai yajamaka tsiya"" um um hajiya raina kamafa kaga gayya"" inamai tabbatar maki sainayi govno agarin nan

Hajiya batasan sanda takwashe da dariya "" auwal ne yadawo yayan lubcy yanata faman hon yaji shiru afusace yafito zuwa cikin gidan

Yace haba ado waikai saiyaushe zaka daina wannan surutun Mara amfani nayi minti goma inabuga hon Amman kananan kanazuba

Yace haba maigida toyazanyi banjikabane kasan bakyau akunkume baki saiyayi duyi""😆

Hajiya tanadariya tace waifa cewa yayi saiyayi governor agarin nan akan surutunsa"" auwal yaharareshi yace Na mahaukataba

Ai wannan nangaba gadinma saiyarasashi "" yawuce fuuu kazokuma kabudemun kofa"" ado yawuce yana ta zuba ganinan zuwa karka gididdibani gida gida

Lubcy tanashiga dakinta tayi wurgi dahijab tacije danyatsa tanakasa tanadabo kenan """ asheni banyi komaiba

Dasake wlh kenan yafison dansa akaina???zai aurenine dannakula dayaronsa"!! Babbar magana nasan muddin yaron yanaraye lallai bazansàmu wata soyayya awajensaba

Zairaba soyayyarsa gida biyune"" ina bazaitaba yiyuwaba dole naga *hatsabibin boka* yaudin nan Saikai kawotake acikin dakinta tanajiyo hirar ado da hajiya taja tsakii mstw surutun ado haushi yakebata idanyana magana bakinsa harkunfa yakeyi

Tana zaune saman kujerah tana tunanin maganar Usman saigakiràñsa yashigo"" tadauka sukagaisa yakesanarda itah yakai

Tayimasa sannu Allah yahutarda gajiya"basujima suna firaba yamata sallama yace ansoma kiran magrib zaiwuce masallaci sukai sallama yakashe wayar sake mikewa tayi akan kujerah batajima dakwanciyaba barci yadauketà

Momdinta tashigo tasameta tanabarci saitafita karfe daya tafarkà taje tawanko idontà tadawo lokar kayantà tabuda tadauko karamin akwatin tabude tadauko madubin yana nan"" yanda ta ajeshi

Saman gado tazauna tasahanñu tashafiii madubin tareda kiran sunan *hatsabibiñ boka* sau uku saigawani haske yashiga tacikin madubin saigashi yawashe *hatsabibin boka* yabayyana samañ kujeràrsa

Cikin damuwa tace akwai Matsala sarkin bokayen duniya haryanzu tanakasa tanadabo""" yace yakikeso ayimasa??? Bataredà fargabar komaiba tace aturashi wajen mamarsa aganina zaifisàmun kwanciyar hankali darayuwa ataredani
.inaso gabadaya danginsa sumanta dashi sukuma mantada mahaifiyarsa

Inaso Usman yaji aransa baitaba haduwa dawata diyamaceba saini aciremasa son kowa adasa nawa"""

*hatsabibin boka* yakeceda wata hatsabibiyàr dariya yace angama lubcy jeki kikwanta abunki kafin nandakwana 2 angama komai

Bakaken aljanu sunagaisheki sunyaba dajininda kika aikomasu kamar walkiya hasken yafita daga madubin boka yabace tamkar walkiya.

Lubcy tamaida madubin cikin jindadin bukatàrta tabiya takoma saman gado tayidaidai tañabarçiñta cikin kwanciyàr hankali.





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 28
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽



Bayan kwana biyu kamar yanda sukai da Usman saigashi yakirata"" cikin zumudi tadauka cikin rausaya"

Tace aminci yatabbata agareka annurin zuciyata"" wani sanyine yaràtsa sassan jikinsa yalumshe idonsa sannan yabude

Yace taredake ma abociya sassanyar murya

Dafatar kina lafiya??? Tasake rausayarda kai qalau nake tareda tarin dinbin soyayyarka

Yace wow Amman najidadin hakan sosai abisa dukkan alamu tarkona yakama tsuntsu

kanta tagyada tace aitunima "" yace Amman shine baki sanar daniba kikabarni inata shawagi duniyarda bakowa acikinta saitarin furanni da ababen more rayuwa. Tace to aikuwa hankali kwance tunda kasamu jindadi aduniyar

Yace kisani bazasu burgeniba matukar babu tauraruwa acikinta""

Zuciyata tayita jiran bakuwar soyayya wacce zata tallafeta zuciyata tazama fanko bakomai acikinta tana bukatar abokin zamanee

Cikin zolaya tace to ai akwai kaleed"" gakuma marganyiya mamarsa"" shiru yayi kamar maison tunawani Abu daga bisani yace makotanku suke??? Cikin rashin fahimta tace suwaye???

Yace kaleed danaji kin ambata mana"" takyalkyale da dariya tace kainifa danka nake magana akai""

Yace danakuma??? Wanda zakihaifamun inmunyi aure??? Tace dankadai nayanzu yace Wayafadamaki inada da??? Yaushe harnayi auren dazan haifi da??? Wani sanyine yaratsa zuciyarta lallai boka yagama aiki saitace bakaine kasanardaniba kanada yaro mamansa tamutu

Dariya yayi haryana rike ciki yace badainiba abunda nafadamaki kawai nacemaki nataba aure Amman fa ba azahiriba cikin mafarki mukai auren kuma munyi soyayya doguwa da itah Amman bata haihuba saitarasu tanarasuwa nafarka abarci wlh yanzu ko kamanninta bazan iyah kawomakiba kingakuwa shirmene

Tasake shekewa da dariya tace hakane" yace yanzu idan kin amince zansanarda mamana anemamun aurenki

Dannagaji dazama gauro abokina yayi aure nibanyiba nasan rashin auren ne yasaka naketa mafarkin nataba aure tace shikenan zan sanarda dad komai yace zakaji bayani yace yauwa tawan

Sunkwashe tsayin wata daya sunabuga soyayya usman yamaida legos tamkar dakin kwanansa bayawuce kwana biyu baijeba

Yasaba da ado maigadi sosai lubcy tagabatardashi ga mahaifinta a matsayin wanda zata aurah tasanardasu saurayine baitaba aureba

Baban lubcy yace yaturo magabatansa"" ranarda lubcy tasanar dashi ranar yayiwa kano tsinke"" tunda mom taganshi sai fara a yakeyi sunazaune cikin falo yatankashe kafarsa kasa yanashan kankana

Hafiz yana saman kujerah yanabuga game hajiya tace wainikuwa babangida wanne irin farinciki kakeciki nagatundazu saiwasar hakorah kakeyi???

Yasaka kankana cikin bakinsa yace hmmm mom albishirinki"" tace goro fari tasss tana gyara zamanta"" Allah yasa alkhairine

Yasake murmusawa yasosa kansa yace sosaima "" tace tofadamun inji"" yace nasamo maki suruka mom Allah yakarbi adduarki nasamu wacce nakeso

Aikuwa hajiya tarangada guda kai Amman najidadin wannan labari haba kokaifa duka abokanka sunyi aure Amman kai katsaya ganin garii inason nima insamu jika

Yasunan surukar tawa??? Yana murmushi maikunshe dajindadi yace lubabatu saiyanzu Hafiz yayi magana yace Allah yasanya alkhairi

Suka amsa da Ameen"" aikuwa hajiya tasanarda abokan mahaifinsa kasancewar yan uwan babansa bakusa sukeba"" Dan asalinsu buzayen Niger ne""

Cikin satii daya akagama komai anbiya sadaki dakudin angani anaso"" akasa bikin nanda wata daya""" ranar lubcy tasiye dabbobi guda goma ta aikawa *hatsabibin boka*

Usman dakansa yaje Dubai yahadomata lefe Wanda ya amsa sunan lefe akwati talatin kowanne akwatin shake yakeda kaya sannan dasabuwar mota hul duk acikin lefen

Lubcy saida tahada gagarumin farty gabadaya kawayenta sadiya.aneesa.rabiatu.larai.sajida"" suma saida kowaccensu tazo datata tawagar kawayen awani babban hotel sukayi fartyn kowannensu saida yagirgiza daganin kayanda akadirkowa lubcy amatsayin lefe

Ranar sun gwangwaje sosai saikusan magrib suka watse""

Cikin watadaya lubcy da Usman tamkar suhadiye Kansu Abdul ma saubiyu Usman yana zuwa dashi wajenta

Biki yakarato kowanne bangare sai shirye shirye ake kubra matazo da dankaramin cikinta ansoma hidimomi Usman yagyare gidansa an sake komai kuma anyisabon fenti

Bangaren lubcy kusan sati biyu sukayi suna program event itakanta tasan takere sa a ta auri mijin nunawa sa a

Bikinsu Na gogaggun yan boko ko ince yankarya Dan yanboko akwai karya kankanba danuna sudin wata tsiyane

Ranar lahadi dubban jama a suka shaida daurin auren lubabatu da Usman akan sadaki million 1
Karfe uku motochin Amarya sukadauki Amarya zuwa kano wajen mahaifiyar
Usman yankai Amarya censukà kwana tareda kawayenta

Washe garii akawuce da itah dakinta ai kawayenta basu tsureba saida sukayi arbada aljannar duniya acewarsu

Dan babuce kawai babu acikiñ wannan katafareñ gidan kowa sai santin gidan yakeyi saidare akawatse akabar amarya

Daren Usman ya angonce zokuga ririta tamkar zaimiyarda itah ciki sosai takemasa ladabi hartakan mantar dàshi kowa muddin yanatare da itah

Bayan wadansu watanni lubcy tafara gajiya dabukatarsà saitatsiri ciwon karya kofashin sallah"" lokacinne kubra tahaihu mace akasamata suna bilkisu hidimar kwana biyu tasaka lubcy tadan sarara





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠



chapter 29
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽



Bayan wata uku lubcy tafara laulayin ciki ranarda doctor yasanardashi tanadauke daciki zokuga murna daga hajiya har Usman tamkar suhadiyeta tuni labari yakai wajen kubra

Takirata tatayata murna taimata fatan sauka lafiya cikin sosai yake wahalda ita gakuma yawan kwadayi kamar manya""

Aikin komai tadainayi acikin gidan saidai taci takwanta saikuma Usman yasake manne mata da lakuwa kamar danyaye""

Cikin yana shiga wata Tara kafafuwanta suka kunburah komai bata iya yikobanza gatada sonjiki sai akagamu akadace

Ranarda nakuda takamata akadauketa sai hospital tasha wuya Amman haihuwa tayi tsayinta gashikuma tagalabaita

Likita yace dole Usman yasaka hannu aimata aiki aciro yaron domin dan cikin yawahala tareda mahaifiyarsa "" Usman hankalinsa yayi matukar tashi

Saida doctor ya rarrasheshi yasaka hannu akashiga da itah dakin tiyata akaciro kyakkyawar bePublish at www.hausaebooks.com.ng maikamada Usman sak tamkar yayi kaki yatofar

Bayan anyimata dinki aka kaita dakin Hutu"" sosai Usman yakejin son jaririyar harcikin ransa take yadauki waya yasanarda hajiya da Abdul da kubrah yakirah gidansu lubcy yasanar

Ranar duka sukazo saigashi ancika asiviti makil damasu dubiya har makotanta saboda tanada mutane sosai"" satinta daya sannan aka sallameta kaitsaye Lagos akawuce da itah"" aikuwa Usman yamaida Lagos garinsu kullum yana zaryar hanya

Anasaurah kwana biyu biki kubra tazo""" sosai sukejida yarinyar ranar suna akaradamata suna labila

Usman gida biyu yakasa kansa"" bayawajen aiki baya Lagos aikuwa tanayin arba in akahadota tadawo

Sosai tadan huta da jarabar Usman kwana biyu Amman ranar taraina kanta dankuwa saida yafanshi nakwana arba in datayi basatare danyagaji iyakar makurah

Labila tayi wayonta sosai ko ina tanazuwa tanada shekara daya dawata bakwai aka yayeta"" lubcy batasake samun cikiba saida labila tacika shekara uku

Shima wajen haihuwa saida aka fasata saboda wahalarda tasha yaron yamutu cikin ciki"" tunlokacin batasake samun cikiba

Saida labila tacika shekara goma"" sannan tasamu ciki shima hallau tiyatarsa akai mata tace ajuye mata mahaifa dantagaji Amman badasanin Usman ba""

Katon danda akaciro mata shima kyakkyawa Amman labila tafishi kyau Dan ita ta fidebo kamannin mahaifinta""ranar suna akasa masa suna abdul-majeed sunakiransa majeed

Yana isah yaye tayayeshi domain sun shirya wata tafiya tareda kawayenta "" tatambayi Usman duk da badason ransaba Amman bazai iyah musamataba ita tadauki nauyin tafiyar har aje adawo

Sukayi shirye shiryensu ranar talata jirginsu yadaga zuwa charo satinsu biyu acen usman yadameta da azarbabi

Please Login or Register in order to submit comment