Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

daidai shigowarsu habu da sauran ma aikatan gidan bayan habu yasanardasu abunda takardar takumsa







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 94
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽




Dasauri suka karasa inda yake habu ne yacewa muhd taimakamun da ruwa Dan Allah dasaurinsa yadibo ruwan yamika masa ya yayyafawa Usman Amman komotsi baiyiba"" aka yayyafawa lubabatu tana farka takwamtsa ihu nashiga uku zaku kasheni"" habu yace kwantarda hankalin hajiya aimune sai lokacin tabude idonta

Idanuwanta tasaukar akan Usman Wanda ko motsi bayaya dashi dagawa duk daya dasauri tamike tayi wajensa tace mesuka masa?? Kufadamun mesuka masa""

Habu yace bakomai muje asiviti muhd ne yadauko mota suka taimaka akasa Usman cikin Mota sai asiviti"" likito wajen biyar suka rufa kansa Amman ko motsi baiyiba""

Take hankalin lubabatu yasake tashi tarasa inama zata sanya ranta taji sanyi karfa aljanun *hatsabibin boka* sun tsotse masa jinie Amman aiba hakan mukai dashiba

Ganin harrana tayi daya saura bawani haske kawai habu yakirah hajiya yasanarda itah tace itama tana asiviti labila ce batada lafiya Amman tafarfado yanzun hankalinta atashe tace ayimaza azodashi kano khalifa teaching hospital tanajiransu Zata sanarda doctor dinsa

Amman basu fadamata musabbabin abunda yasameshiba""" sunsanarda doctor zasu daukeshi zuwa kano akabasu sallama suka kama hanya har kano

Koda suka shiga sunsamu hajiya bakin kofa takasa zama anaganin su akazoda gadon Daukar mara lafiya akaturashi zuwa dakin taimakon gaggawa

Duk iya kokarinda zasuyi wajen ganin yafargado abun yafaskara abunda yayi matukar basu mamaki gashidai baya nunfashi Amman zuciyarshi harbawa take dasauri dasauri


Al amarin aljanie hayyanul zairi kuwa kwananshi daya dayini daya yana gudu asararin samaniya harzuwa lokacin khadija bata farfado daga doguwar sumarda tayiba sakamakon bangazarta dayayi

Baisake sa a guda yana guduba khadija tafarfado ahankali tabude idonta Kalmar dabakinta yasoma ambata kalu innalillahi wa Inna ilaihirrajiun

Saiyanzu take tuno abunda yafaru ahankali tasoma kallon wani bakon al amari kamar anagudu da itah acikin iska bakinta ne yasoma Karanto a uzubikalimatil lahi tammat min sharrima halaka""

Aljanie hayyanul zairi baisan Khadija tafarka daga doguwar sumaba radadin da yasomaji akirginsa tamkar ya chachumo wuta ahannunsa sune suka ankarardashi

Kafin yayi aune tuni sun lankawo daga sararin samaniya zuwa kasa kafin sukawo tunie khadija iskan dake tashi sama yasake sumarda itah

Saurah baifi sa o i susauka kasaba akayi wuffff akatare khadija tafada hannun wata farar mata maicike da kwarjini sannu ahankali tasaukarda itah kasa yayi daidai da farkawar khadija

Ganinta awata duniyar daban yasaka tafara jadabaya daga zaune wata iskace mai karfiii sukaga tatunkarosu bayan tagama saukowa saiga aljanie hayyanul zairi yabayyana cikin siffar jemage

Wani irin wargajine girmansa zaikai tsayin daki fadinsa ma haka""" faratansa manyane masu dauke damanyan kumbuna

Bakinsa dauke yake da zakwazakwan hakorah masu matukar tsinie ko wanne daya tsininshi yakai tsinin mashii kaurinshi kuma kamar kaurin takobie

Idanuwansa kadai abun tsorone "" idan yayi huciii wutace take tartso abakinsaa

Daganin wannan halittar wani mugun tsoro yakama khadija hantar cikinta takada tunda take ko acikin fina finai bata tabayin arba dawata halitta maigirma dakuma firgitarwa irin wannan ba """ Amman wannan karamar aljannar

Datake gabansa kamar bera yatsaya agaban kurah Sam bata tsorata daganinsaba""" wata kururuwa yayi wacce tasaka khadija shedewar kunnnuwanta na dakiku arba in

Tsawarsa daidai take da tartsatsin wuta gaba daya dajin kansa saida yasauya launi sakamakon wannan karar yayi girgiza saigashi yasake zama wanie katon basamude"""

Kallon kallon sukafarayi da aljannar daga bisanie yabude bakinsa Cikin nuna isah dakuma takama yace yake wannan aljannar kisanie wannan kalacina ne kigaggauta barin wajen nan tunkafin fushina yasauka akanki

Cikin murmushi tace kai awa kuma kaiwanene dazanbaka itah"" inabaka shawarar Kayi saurin barin wajen nan tunkafin raina yakaiga bacii

Dariya yafashe da itah yace ke kinsan kodawa kike magana??? Tace bandamu dasanin kokai waye bane Amman nasan zaluncine zaka aikata kuma ni naharamta hakan acikin yankina

Wata kuru ruwa"" yayi yace yanadakyau yarinya kisan kodawa zakija kafin kifara fada! Nasan kaf duniyar nan babu wani aljaninda baisanda zaman"" jajirtaccen matsafi kuma gawurtacce Wanda yafi kowa sanin sirrukan sihiri wato *hatsabibin boka* wannan dakike ganie aikinsace kuma nine akabaiwa itah jininta amatsayin ladar aikina""

Aljannar tasakeyin murmushi akaro nabiyu tace bandamu dakaiba hakazalika fadar sunan bakin azzalumin shugabanka bazai tayarmun da hankaliba inamai baka shawara ka gaggauta barin wajen nan

Aljani hayyanul zairii yayi wani huciii saiga wutaa tayi tartsatsi dasauri wannan aljannar tasa hannu takare dazaran wutar tataba hannunta saikaga tamutu tamkar acikin ruwa take
Wannan yasake fusatashi yataso mata kamar zaicinye namanta danye take itama tayi girgiza saigashi tarikida takoma katuwar kada mai tsananin girma dakuma bantsoro

Hakoranta manya manya faratanta kamar fartanya kaifinsu da tsininsu yakai kaifin takobiii take itah ma tasoma kururuwa tayi girgiza saisuka fara kallon kallo dagabisani suka rugo dagudu nantake kura tatashi sama bakako ganin gabanka jikake kafff sukahade waje daya karar hadewarsu kaisaikace dutse da dutsene sukahadu


Hmmm wai ance fada inba ruwanka dadin kallo zamuga yanda fadan aljanu zaikaya shin ko aljani hayyanul zairi zaiyi nasarar kashe wannan aljanar yatafi da itah??? Kokuwa wannan aljanarce zataci galaba akansa??? Waishinma itah wannan aljannar wacece??? Ya al amarin Usman Wanda yasuma haryanzu bai farfadoba??? Shin labila tafarka daga barcin da aljani saaagakimu yasakata??? Duka amsoshin wadan nan tambayoyin suna cikin cigaban labarin saiku kasance taredanie


Kuyi hakuri banda chaji wannan kawai kukasamu







Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 95
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽





Tunie Khadija taja baya tana kallon ikon Allah"" sun dade suna murkususu sannan sukasake jabaya kowannensu yana hucii

Abun yabawa hayyanul zairi haushi taya wannan tatsitsiyar zata hanashi abunda yayi niya bakaken aljanu ma shakkarsa sukeyi ballantana wannan dabaiwuce yayimata lakuma dayaba""

Bari kawai kafin wankin hula yakaishi dare yanuna mata ruwa ba sa an kwandobane" " aikogaba da gabanta"" take yayi kukan kurah yadauke kadan sama" yasoma wujijjigata"" karshe yawurgar da itah tafada saman wata bushiya take bushiyar takarye saiga aljanar tadawo cikin suffarta tafarko bakinta da hancinta duk yana yoyarda Jini kamar mayanka"" tayi matukar galabaitaa


Aljani. Hayyanul zairi ya kyalkyace dawata mugunyar dariya yace bake bace banda abinki mezaikaiki fada dawanda kikasan yafi karfinki??? Tunfarko dakinbani itah cikin lalama dahakan baisamekiba"" bari kiganie agaban idonki zanshanye mata jinie idan ma bakiyi wasaba kema zanhada dake inkashe tunda kikayi kokarin jadanie

Yana kai karshen maganar yasake kecewa dawata hatsabibiyar dariya yatasamma gurinda khadija tace tuni khadija tasoma jada baya gabadaya tsoro yahanata yin addua Batasan wanne irin tashin hankali take cikiba

Aljanar nan tanadago kai taga bakin aljanin baifi Saurah kamu hudu ya isah wajen khadija ba "" dakyar tabude baki tace ya Allah"" tareda mikewa dakyar tarikede izuwa wani katon basamuden namiji tanarike dawani babban takobi mai matukar tsini dakaifiii cikin guguwa tawuce fuuuuu saigashi ta isah gaban khadija

Hayyanul zairi yakalleta da mamaki danbaiyi zaton rauninda yayimataba zatasake tashi kafin yagama mamakinsa muryanta takatsemasa tunani tace kaibakin azzalumi mushuriki kasani Allah bazaitaba baka sa a akainaba bazaka taba shanjinin wannan bil adamarba saboda yafi karfinka

Akaro nabiyu inabaka shawarar kagaggauta barin wajen nan idankuma kaki lahira tayi babban bako"" hayyanul zairi ya kyalkyace da dariya jin abunda tafada yana nunata da yatsa yace "" kenan Yar fitsitsiya harkin isah kitsoratani da alamu kingajie da duniyar toyanzu kuwa zanturaki inda ba zaki dawoba take shima yayi girgiza Yakoma wani katon sadauki jikinsa daddaure da kayan yaki kowanne damtsensa daya yakai kaurin cinyar babban mutum

Gurayen jikinsama kadai kaganie saika firgita dogone sosai"" tsayinsa zaiyi kamu ashirin tuni wannan aljanar takoma tamkar kiyashe agabansa kwatakwata tsayinta iyah kaurinsa tatsaya

Khadija tamatukar firgita daganin yanda yakoma lallai dakyarne idan wannan aljanar zatayi galaba akansa"" wannan aljanar bakinta tabude tasoma hura masa iskaa mai matukar karfiii amman ko gyangyadawa baiyiba""

Takobin dayake hannunta tadaga iyah karfinta tabuga masa akaurinsa"" abun mamaki jitayi yayi kara kamar ajikin dutse tabugashi take takobin yakarye yazube akasaa""

Hayyanul zairi yana tsaye kikam yarike kunkuminsa yana kallonta""" saibayan data gama abunda takeyi""" yadaga kafarsa daya yataketa gabadaya fadin kafarsa bakako ganinta saimotsi take shikuma yacigaba da busar dariyarsa

Dakyar tadaga jikinta taciro wata karamar wuka tasoka masa atafin kafarsa taredakiran sunan Allah tuni wukar tahudashi zafinda yajine akasan kafarsa yasa yadaina dariyar dayake yakwalla kara yadage kafarsa wacce takemasa zugi dakyar ya iyah fincike wukar yayar jinin jikinsa yadinga zuba akasa take kasa tasoma zurmawa

Duk inda jininsa yadiga yashige cikin kasa saikawai kaga bakin maciji yakunno kai yafito yatasamma wannan aljanar tuni itama tajawo takobinta

Tasoma fillemasu kai Amman Abun mamaki duk Wanda tafilleewa kai maimakon yamutu saikuga wasu kawunan sunsake tartsowa ajikinsa

Tuni macizan suka kewayeta""" ganin hakan yasa itama tayi kururuwa tatofarda yawunta akasa yinhakan keda wuya saiga wata katuwar mesa tatsago kasa tafito wata irin shirgegiyace """ girmanta zaiyi girman kada babba bakinta yana feshin wutaa

Dagama fitowarta kawai tatasamma wadan nan macizan haka tayita lakumarsu tamkar tanacin cinnaku"" ganin haka yasa dai dagacikin macizan tasoma hadiyar yan uwanta tana kara girma saida tahadiyesu duka saigashi tadawo wata katuwar macijiya wacce taruba wannan mesar sau biyu tsayi dakuma fadii takekuma suka soma fada tsakaninsu hayyanul zairi shima saiya tasoma wannan aljanar suka soma fada dazaran yadaga kafa zaitaketa saita goce itakuma takaimasa Sara duk da ko alama bayajin saran""

Sun sake shafe sa o"I biyar suna wannan fadan haryanzu aljani hayyanul zairi baici nasaran sake takar taba"" bakinciki yasake turnukeshi yayi matukar fusata take yakwantsa ihuuu yasoma huro iska tabakinsa tuni iskannan yadauke wannan aljanar dakuma macijiya tareda wannan katuwar mesar yasomayin hajujuwa dasu sama khadija kanta inda Allah yataimaketa tanakusa dawani katon icce

Shitakama tarike kam tanata rusar kuka tunda take banda cikin film bata taba ganin bala i irin wannan ba"" kananun bishiyoyi tuni suka soma fincikowa daga kasa sunayin sama komai nadajin yahargitse wannan aljanar tuntanayin kokari dantasauko harta kasa anyi wajen mintuna goma suna shawagi Asama sannan yazubodasu kasa ragafff take wannan mesar dakuma maciji suka mutu ko shurawa basuyiba"""

Itakanta wannan aljannar dakyar take iyah daga yatsanta batako ganie daidai "" bayan sa"a guda komai Yakoma daidai sannan aljani hayyanul zairi yatako zuwa gaban aljanar da babban Dan yatsansa yasaka yaturata tamirgina tadawo daidai fuskarta tana kallon sama

Yakyalkyace da dariya yasoma yiwa kansa kirari kamar haka"" saini Aljanie hayyanul zairi dangidan kabusa"" fada"dani bala ine mai shirin gaba dagaba Dani saiyashirya "" yaro aikona goye yasan kura saini na *hatsabibin boka* uban hatsabibai duk Wanda yajadakai sunansa matacce asoka kaki mutum mutum yakiga yakwana kiyama"" saini angon mirqiyanatu"" uban sakafilu"" maidakawa maza gunba" faduwar gaba kotsoro badai gareniba da inja baya gayaki kara namutu danni bazan barwa Yayana abun fadaba!" karyarki yarinya bakaken aljanuma sunbuga sunbarni ballantaana ke"" yanagama wannan surutun yajuya wajenda khadija take

Tanaganin haka tasake kankame wannan bishiyar tana kuka" girgiza yasakeyi saigashi Yakoma katon jemage mai fukafuki yasaki fiffikensa yasoma tashi daniyar yasunkuce khadija yayi sama da itah

Amman kafin yakai gareta saiyaga tabacewa ganinsa wata iskace maikarfii yaji tasha gabansa lokacin yajuya da mamakin inda gawar wannan aljanar take baiga komaiba""

Ashe lokacinda yakoma jemagen nan wannan aljanar ta farfado ganin yakusa dauke khadija saitazama iska tabi ta karkashinsa tasunkuci khadija tabace acikin iskar

Saigasu wani katon gidaa maicike dakayan more rayuwa tsakiyar falon aljanar tasauka ahankali ta aje khadija itakuma tafadi gefe tana nisawa dakyar bakinta da hancinta suna zubarda jinie"""

khadija kam tun lokacinda wañnan aljanin yasoma tunkarota takankame bishiya tana kuka tasadakar mutuwa zatayi saikawai taji ansureta anyisama saiyanzu tadaji an ajeta kamar asaman kafet sannan tabude idonta

Tasoma kallon falon har tasaukarda idonta akan wannan aljanar dasauri takarasa wajenta tadago kanta tadora akan cinyarta tana kuka ganin abunda yasami wacce ta taimaketa

Aljanar tasakar mata lallausan murmushi Wanda dadukkan alamu nakarfin haline tabude baki ahankali tace karkiyi kuka Allah yanatare dake babu Wanda zaicutardake Amman rayuwarki tanacikin hatsari


Tasoma tari Cikin kuka khadija tace kaina yakulle wlh inane nan??? Meyakawoni nan?? Ina mijina??? Kuma ke wacece??? Waye wannan aljanin dakukai fada dashi??? Kumani menaimasa dayakeson kasheni??? Kifadamun yazanyi nakoma gida??


Wannan aljanar tamurmusa tace babu lokacinda zansamu damar amsamaki tambayoyinki kirike tambayoyinki harnadawo tasakeyin tari yajimin ciwo ajikina dole naje nayijinya kafin raunin yacigaba datafiya ajikina
Kizauna nan harnadawo karkisake kifita kofàr gidan nan









Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 96
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽




khadija tace ina nibazan zauna ananba"" wajen mijina zantafi " aljanar tasake murmusawa tace kiyi hakuri Amman fita dajin nan agareki babban hatsarine

Wannan gidan dakike ganie gidanane kuma shine kawai adokar dajin nan babu wani matsafi ko aljani dazaiganshi ko abunda yake cikinsa

Wannan aljanin bazaitaba tafiyaba inhar baisha jininkiba kuma yasan bakibar dajin nanba danyanajin kamshin jininkin Amman bayaganinki"""


Muddin kikafita gidan nan kasheki zaiyi danbazai bar dajin nan ba""" duk abunda kikaji karkisake kifita kiduba ko ina agidan nan duk abunda kike nema zakisamu inafatar zaki ji shawarata nabarki cikin amincin Allah tanakaiwa nan tazama hayaki tatashi sama khadija tadaga kai tana kallonta haryanzu data daina kukaba"" harsaida tadaina ganin hayakin taja jikinta kusa dakujerar datake falon tasake barkewa dasabon kuka


Al amarin aljani hayyanul zairi kuwa lokacinda yanemi khadija tareda wannan aljanar yarasa sai hankalinsa yatashi yasoma dube dube gashidai yanajin kanshin jininta Amman baya ganinta hakan yasa yasoma sunsunar kasa yanabin saitinda yakejiyo kamshinta yayita tafiya yana sunsune haryadaina jin kamshinta dole yadawo baya indayakejin kamshin nata yaja yatsaya saikuma yafashe dakuka tareda kururuwa aikuwa khadija tamike afirgice Dan kamar agabanta yake haka takeji

Tuni tasheka tabude wani dakin tafada ciki kai dakin yahadu iyah haduwa Amman tashin hankalinda khadija take ciki baisa talura da haduwarsaba ""

Saman makeken gadonda taganie cikin dakin tafada cikin tsoro""" Dan itah gidan kansa tsoron sa takeyi gatagama yarda dazamansaba ""


Aljani hayyanul zairi kuwa yadauke wajen sa o"i goma yana kuka """kukanda yakeyi bawai na wahala bane kukan bakincikine ai abun kunyane agareshi ace wannan karamar aljanar tahanashi Khadija hakan na nuna kenan taci galaba akansa?// dakarfi yace ina wlh karyane ba ataba bashi aiki yakasaba saboda banda yake aljani kuma shima matsafine bayan haka kuma majiyi karfine sadauki yanzu kwatakwata shekaransa Dari biyar aduniya"" kaf aljanunda *hatsabibin boka* yakedasu shine babba bawai agirman shekaruba saboda hazakarsa dakuma kwazonsa babu wani aikinda yake gagararsa duk inda akaturashi babu makawa saiyayi nasaraa dajin Iraqi da *hatsabibin boka* yaturashin yaje yayi fada damugayen namun jeji masucin naman aljanu dakuma bil Adama yakarkashe su yadawo cikin nasara shiyasa *hatsabibin boka* yake jidashi duk cikin dakarun aljanunsa""


Tayama zaikoma wajen shugabansa "" toyace me idan haryafadi ainahin abunda yafaru bashakka girmansa zaifadi kuma zaijawa Yayansa dakuma matarsa abunfada Wanda zaiyita yawo aduniyar aljanu harnabaya susamu abunfadi ga zuri arsa

Damadai aikinda akabashi yadauketa kuma yacika aiki jininta ladarr aikinsace yasan duk inda taboye acikin jejin dole tafito kokuma yunwa takasheta gabanza""

Kawai zai zagaye dajin da mugayen tsafaffin namun jeji dazaran tafito sugama da itah shikuma yatsotse jininta yabasu gangar jikinta zaicewa boka yagama aiki yasandai bazaiyi bincike akan hakaba tunda yayarda dashi dawan nan shawarar yayarda"" yayi busaa saiga manyan namun jeji sunata yawo awajen kuraye zakuna damisa bauna giwa "" dadai sauran namun jeji masu firgitarwa

Dakuma cutarwa"" sannan yazama iska yatashi sama yabace cikin gajimare"" lokacinda yayi wannan tsapin khadija tasomajin kukan kuraye dana namun jeje hankalinta yasake tashi tasoma kiran sunan Usman tana kuka maimatukar ban tausayi


*Kano*
Hospital dinda aka kwantarda Usman tareda labila wacce tasoma farfadowa tasake komawa barci likitoci atunaninsu barcin arzikine takeyi Amman basu saniba barcin ciwone domin zaizama cutarwa arayuwarta

Yau kwanan Usman biyu kenan dasuma Amman ko alamar farfadowa baiyiba duk wani taimakonda yakamata suyimasa sunyi amman sunkasa nasarar farfado dashi
Sun yanke shawarar dayakai gobe baifarfadoba saidai afitardashi waje


Lubabatu tunda taga halinda usman yashiga dakuma yarta labila sai hankalinta yakara tashi lallai yazama dole ta nemi boka aibahakan tace ayiba"""

Suna zagayeda Usman har hajiya damasu aiki sunyi. zugum zugum lokacinda khadija tasoma kiran sunansa saiga Usman yasoma motsa Dan yatsansa"" kamar anturoshi yatashi dakarfi yace khadeeja!!!!

Badai khadeeja na akadaukaba bazai yiyuba hajiyace tafashe dakuka tace badai hauka takamakaba babangida meyasamu khadijar??? Saiyanzu hajiya talurah da waima bada khadija akazoba

Habu ne yasheka dagudu yakirah likitoci dakyar aka rirrike Usman ganin yana nema yafi karfinsu yasa akaimasa allurar barcii

ahankali yake kiran sunan khadija harbarci yadaukeshi"" hajiya tana share hawaye takalli lubabatu wacce take sharar kwalla tace wai meyasamu khadijar??? lubabatu kam batace komaiba saidai tabita dakallo saida tasake tambaya habu yace suma wlh basu saniba sundawo masallaci kenan sukasamu"" wata bakar jeep tawuce kofar gidan atsiyace koda suka kawo saisukaga alhaji yadauki dankwali saikuma yaruga cikin gidan

Nikuma sainaga takarda kasa"" nadauka nakaranta mukayi cikin gidan dasauri saimuka sami alhaji dahajia duk asome bamusan menene musabbabin sumarsaba
Hajiya tarabka salati tace tomeyasamuu Khadija???




Hakuri hakuri hakuri wlh banda chajiii fatan alkhairi agareku





Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 97
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽




Hajiya tace aibaikamata kutaho dukaba sai asanarwa yan sanda habu yace nayi tunanin hakan kuma ai munbaro maigadi tareda maibawa fulayoyi ruwa da idi maiwankin mota"" duk da bagidan yake kwanaba nasan yanzu yasamu labari

Hajiya tace duk dahakan kukoma kusanarwa yan sanda dama anzo dawayar babangidan saina kira abokinsa dpo lubabatu tace suje kawai idan anfadawa yan sandan saita dauko wayarsu dakuma kaya Dan itah ko mayafi batatsaya daukaba

Hajiya tace shikenan Amman kidaina kukan nan haka insha Allah zasu samu sauki lubabatu tagyada kai"" da itah da muhd da habu driver suka dawo kaduna

Koda sukaje suka sanarwa yan sanda ashema har maidagi yatafi tun ranar yakai report anyi nema har angaji Amman ba agansuba"" anyita sanarwa kafafen yada labarai dagacen gida suka wuce bayan lubabatu tasake jaddada masu asake tsaurara nemanta

Bayan sunkai gidan akabude masu get suka shiga"" habu yatsaya magana da ma aikatan gidan "" Tace su habu sujirata tafito kaitsaye tashiga gidan


Dasauri tahaye bangarenta tajawo akwatin tadauko madubin tashafa tareda kiran *hatsabibin boka* shafawarta keda wuya saigashi yabayya asaman buzunsa

Lubabatu tayi shiru kanta yanakasa takasa cewa komai dominkuwa bataga idon wasaba Dan fuskarnan tashi murtuke take sanadin kuwa wannan karon saboda rudanie ko kayan aikinma bata turoba

Jin surun yayi yawà yace idan bakida abuncewa meyasa kika kiramu alhalin muna cikin wani aikin??? Tace tuba nake uban hatsabibai inacikin tashin hankali dakuma rudanie

Mijina dakuma yata yaukwanansu biyu basa motsi kuma bahakan mukai dakaiba nidaikawai nace adauke khadija tomezaisa ataba Usman da yata???

Yace maganar yarki yanzun zata farka sauran sihirin barcinne baisaketaba mijinki kuwa dama saida nafadamaki bansan abunda zai iyah faruwaba bayan dauke matarsa

Tunfarko kinason mijinki bakyaso kirasashi meyasa kikace akashe kishiyarki??? Tace boka menene alakar kishiyata dakuma mijina

Yace soyayya"! Soyayyarda yakemata talinka wacce yayiwa matarsa tafarko danhaka kikaga yashiga wannan halin"""

tace to boka mezaihana itah ma acireta dagacikin zuciyarsa"" yace abune maiwahala tamarairaice fuska ataimakamun boka banaso yarika tunawa da ita idankuwa harzaituna da itah kagakuwa babu amfanin kashetan da akayi

Kayan aiki daban turoba wlh afirgice nake hankalina yarigada yatashi"" yace karkidamu zanbaki wata laya kisamu kabari sabo wanda akarufe yaudin nan saiki Gina kabarin kisaka layar dazaran kinsaka shikenan koda mijinki yafarka kikaji yana ambatar sunanta karkidamu

Danbazai manta da itah lokaci dayaba saidai adadin kwanakinda gawar zatayi cikin kabarin kullum anacire masa itah aransa akwana atashi haryamanta da itah duka wannan itace kawai hanyarda za abi bayanta kuma babuwata hanya yakikaganie

Wannan layar dakike gani dazaran kin binneta duk acikinsu har yan uwanta daduk Wanda tasani sannu kan hankali zatafita aransu kamar yanda kikasan idan mutum yamutu lokacinda yamutu anajinsa arai anakwana anarage jin zuzin harma kiga magadan sunsoma mantawa dashi suncigaba da sha aninsu tokamar hakane awajensu tamkar matatta zatazamo tunda damacen bata duniyar saidai wani lokacin zasurika tunawa da itah dankuwa abune maiwahala acireta aransu farat daya


Tace abunda kace aihakan za ayi godiya nakeyi boka Kajima kayi karko"" yajinjina kai yace kiduba zakiga layar agaggauta birneta yaudin nan

Tace angama boka takeyabace tamiyarda madubin to dama magriba takawojiki har an soma kirah tacewa habu baritaje gidan malam tanemu tasa ayi saukar Qur ani duk indasuke saisundawo da itah yace aihakan yanadakyau

Tanafita gida kaitsaye makabarta tanufa tasamu maigadin wajen
Suka gaisa tace Dan Allah wani taimako zakamun"" shikam yaga hajiya damota dama yasaba da irinsu Amman saiya tsuke fuska yace wani irin taimako a makabarta??? Dajin hakan sai lubabatu tazuge jaka tadauko daurin kudi yan dubu dubu dubu hamsin tace wannan ne ladar aikinka"" aikuwa yawashe baki yace tome kikeso acikin sassan jikin bil adama"" murmushi tayi tace duk ba wannan ba ankawo sabuwar gawa yau??? Yace dazun nan kuwa aka birne uwani yargidan malam habu "" kai yarinyar akwai"" lubabatu ce tadakatar dashi tace bawai sonake kafadamun halintaba ko dangantakarta da mutane

Yace tuba nake tadauko laya tace tsakiyar kabarin nakeson katona kasakamun layar

Yace Abu maisauki aikoda nera darima zan iyah yimaki wannan yakarbi layar yashiga tana biye dashi harsuka kai kabarin yatona yasaka layar yamiyar yarufe sannan suka fito tayimasa godiya tashiga motarta tawuce""

Bayan takoma tacewa su habu kawai suwuce bawani bata lokaci suka kama hanyar kano koda suka isa hospital sunsamu inna da malam garba dukkansu sunsamu wannan mummunan labarin

Dasukazo ganin labila hajiya take sanardasu ansamu nasara labila tafarfado Amman batacewa uffan tunda su lubabatu suka shiga takurawa lubabatu ido kamar maitunanin wani Abu tuni jikin lubabatu yayi sanyi karfa labila tatona mata asiri kodayake ai anrufemata baki dawan nan tasaki ranta"" andade ana jajantawa juna"" wannan al amarin hajiya tatambayi su habu kosun sanarwa yan sanda sukace ah aikoda sukaje harmaigadi yasanar masu

Tace toshikenan "" Allah yasa aganta"" suka amsa da Ameen"" lubabatu tamatsa kusa da labila tace mata yajikin illah kawai tabita da kallo batace komaiba""

Hajiya tace aitunda tafarfado batace kalaba saidai binmu dakallo takeyi oh ni binta wannan Abu duk alokaci daya Allah yabaku ikon cinye wannan jarabawar"" suka amsa da Ameen

Saikarfe goma allurarda akaiwa usman tasakeshi tunda yafarka baice uffan ba shima sai tsirarun hawaye dasuke zubomasa akai akai yana sharewa hajiya sai sannu takemasa yanabinsu da kallo

Bayan kwana biyu jikinsu yayi dansauki suna amsawa idan anyimasu sannu ganin haryanzu ba labarin khadija su malam garba suka Kira muktar akasanar dashi ranar yataso koda jirginsu yasauka kano Tara nadare kaitsaye yatari dan adaidaita zuwa gida

Da sallama yashiga gidan kamar wani mahaukaci yasamu su innah dasu gwaggo hassana sunyi zugun zugun dukawa yayi yagaidasu suka amsa sunyimasa ya hanya yace alhamdulillah

Shirune yabiyo baya sannan yace yanzu ina dadyn yake??? Inna tace aitunda yaga dankwalin khadijar baimatsaya jin itah suka daukaba yayanke jiki yafadi yanzu suna asiviti itama labila sai shekaranjiya ta far fado muktar yace nifa abun nan yadauremun kai satar mutum kuma harcikin gidansa ni wlh bana zargin kowa sai Abba danhaka nigobe yola zanje koyabani Kanwata ko wlh inmakashi kotu malam garba yace Dakata dakata bahaka za ayiba taya zakace shikake zargi gadukkan alamu mahaifinku baisanma akwai cikin khadija ba"" kamardai yanda mahaifiyar Ku tace sannan kuma baisan tayi aureba baisan inda takeba haba muktar aiko anan yaci kagane

Yayi shiru tokuwa inhakane saidai shi Usman din inyanada abokan gaba lallai dole yaganshi yanadakyau yaje asivitin

Yanisa inna to ansanarda yansanda??? Tace ansanardasu"" Amman sunce basukama suba sunanan dai suna bincike yanzu matsalar Usman yasamu lafiya

Inna tayi tagumie tace ni wlh tsorona kawai karsu cutarda itah"" wadan nan masu satar mutanen dabasuda imanie tayiyuma kidnapping ne

Muktar yace bahaka bane inna Aida kidnapping ne kudi zasu tambaya yanzu wanne hospital din aka kwantarda dadyn""

Malam garba yace ah to yanadakyau kaje danyanajin jiki saidai kabari saida safe mukammu munason sake ganinshi

Yace shikenan yamike zuwa bangarenda dakinsu yake zuciyarsa tanayimasa kuna""

Al amarin khadija kuwa tun lokacinda taji kukan namun jije ya yawaita saitaji hankalinta yatashi kwance datake tana kallon agogo tuntana kuka tanakiran sunan Usman hartagaji dankanta tayi shiru

Tashi tayi tashiga toilet tasamu akwai ruwa tadibo tayi alwala tazo tayi azahar la asar tadauko Qur'anin dataganie tabude tasoma karatu ahankali taji zuciyarta tanayimata sanyi tana nan zaune hardare gashi babu fitila duhu yafara take tasakejin tsoro

Kamar walkiya taga kwayayin lantarki nagidan duk sunkama haske ya mamaye ko ina tamkar rana


Saikunyi hakuri yaugashi daya kuka samu wlh yau fitanayi kuma gobe biki zanje zanyidan kokari inyi biyu goben in Allah yayarda I love u all






Aisha✍🏼
☠ *HATSABIBIN BOKA!!*☠




Chapter 98
Publish at www.hausaebooks.com.ng
Gentle Lady💃🏽



Ganin hasken yasaka taji hankalinta yadan kwanta da agogo take amfanie idan lokacin sallah yayi sai wajen

Please Login or Register in order to submit comment