Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

wanda ya shiga cikin kogin kankara
Koda wuya tayi wuya baisan sa'adda ya kwallara karaba saboda bala'in da yaji ajikinsa kuma bisa dole ya rufe bakinsa ya daina karanto wadannan dalasiman tsafin
Shima ya tsaya domin ganin me zai faru garesu in yaso sai suyi tunanin mafita
A daidai wannan lokacin ne kuma sukaga wata irin iska mai karfi ta fito daga cikin katon ramin ta zukesu gabaki dayansu suka fada cikinsa
Babu irin kokarin da basuyiba domin sauka daga bayan aljani zarikul laham
Amma suka kasa saboda suma jin jikinsu sukayi kamar an daddauresu da murtuka murtukan sarkoki
Suna kara nisa acikin ramin suna karajin tururin zafin na kara ninkuwa fiye da farko
Koda sukayi nisa acikin sai sukaga wani irin katon dutse yana narkewa yanaci da wuta
Kamar tafasashshiyar dalma Ita kanta wannan wutar abar tsoroce
Domin launinta ma kalar makuba makuba ne sai ci take tana fallatsi a sama kamar tafasasshen mai

Tun daga nesa kafin su riski inda wutar take sukaga wani katon dutse ya fada cikin wutar
Koda saukar dutsen a cikinta sai wata iriyar kara ta tashi ji kake cuuuuuu!!!!!!!!!
Kamar an zuba ruwa a cikin tafasasshen mai take shima wannan katon dutsen ya narke ya zama kamar ruwa
Koda ganin wannan al'amari sai sukaji wani irin tsoro a karon farko ya darsu acikin zukatansu suka tabbatarwa da kansu cewa mutuwa zasuyi don haka duk sai suka rufe idanuwansu

ME ZAI FARU DASU IDAN SUKA FADA CIKIN WANNAN MASIFAFFIYAR WUTAR SIHIRIN?
SHIN YARIMA WALISU NA GASKIYA YANA FARAWA DAGA CIKIN BARCIN DA YAKE?
ME ZAI FARU IDAN YAGA SABON WALISU YA KASHE SU GIMBIYA WALISA TUN KAFIN SU ISO DAJI NA FARKO?

DAN JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
NA WANNAN KAYATACCEN LABARIN MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKE, COMMENTS AND SHARE*****---******** HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

***************6 PART B

LBR
********---*********HABIBULAH KBR

Lokacin da su gimbiya walisa suka runtse idanunsu. Saboda sun gama saddakar da cewa babu makawa sai sun fada cikin wannan wutar sun kone gabaki dayansu
Sai daya rage baifi saura taku ashirin tsakaninsu da wutar ba
Har ma sannan ta fara laso jikinsu tana konasu ba zato ba tsammani sai sukaji sun tsaya cak a saman iska ba tareda sun fada cikin wutar ba
Cikin sauri suka bude idanunsu domin suga abin daya rukesu ya hanasu fadawa cikin wutar
Kawai sai sukaga babu komai face iskar da take kadawa agurin
daga can kuma sai sukaga wannan iskar ta sake zukosu zuwa sama ba tareda sun fada cikin wutar ba
Daga can kuma sai sukaji an bushe da wata mahaukaciyar dariya
Wacce saboda karfinta sai da sukaji kamar kunnuwansu zasu fashe
Daga can kuma sai sautin dariyar ya dauke kawai sai sukaga wani irin abu yazo ya tsaya agabansu kamar madubi
Acikinsa kuma sai sukaga fuskar yarima walisu yayinda yake kyalkyala musu dariya acikin madubin
Sai da yayi dariyar ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa ga barin dariyar
Ya dubi su walisa yana mai nuna yu da tafin hannunsa
Yana mai cewa
Lallai sai yanzu na yarda cewa dukkanku taron kanananun kwari ne
Yanzu ku da wannnan dan kankanin karfin sihirin naku kuke tunanin zaku iya yaki dani ?To ina mai tabbatar muku da cewa kun tabka babban kuskure
Inda ace yanzu nayi niyar kashe ku da ko guda daya daga cikin ku bazai tsira daga wannan azabtacciyar wutar ba
Dajin haka sai sarki fadarul munnar ya daka masa tsawa da cewa
Kai yaro karyarka tasha karya baka isa ko mutum daya daga cikin mu ya hallaka a hannunka ba
Dole mune muke da nasara akanka kuma koda ace ka jefa mu acikin wannan wutar taka bata isa ta iya cutar damu ba
A zahirin gaskiya shi kansa sarki fadarul munnar ya firgita da lamarin walisu
Kuma yana da tabbacin cewa idan suka shiga cikin wannan wutar ko tokar su ba zata tsira ba
Kawai dai dakewa yayi kuma ya nuna tsantsar rashin tsoronsa
Dajin haka sai walisu yayi masa wani dan guntun murmushi mai kama da murmushin mugunta yace
Ammafa wannan taurin kan da kuma jiji da kan naka ya burge ni
Tabbas walisa kai ta gado a gurin wannan dakewar zuciyar
Dama ance barewa batayi gudu danta yayi rarrafe ba

Amma ai shi kenan yanzu za'a banbance tsakanin aya da tsakuwa tunda har kuna ganin kuma wuyanku ya isa yanka kuna da abin dogaron da zaku kwaci kanku daga tarkona
To ai sai ku gaggauta tahowa nan fadata idan har kun iso a raye ni zan farin ciki da hakan
Yana gama fadin haka sai take hoton fuskar tasa ta dauke dif suka daina ganinsa gaba daya
Sannan kuma gurin daya zaizaye wuta take ci acikinta
Take gurin ya hade komai na gurin ya koma daidai kamar yadda yake a da
Mai makon Aljani zarikul laham ya kada fuka fukansa yaci gaba da tafiya saiya tsaya cak a saman iska yana duru duru ya kasa yin gaba ko baya saboda razanar da yayi
Da ganin haka sai sarki fadarul munnar ya daka masa tsawa yace
Tsayuwar me kakeyi ne maza ka kara gaba don muga abubuwan daya zuba acikin tarkunan nasa kuma mu fasa su da karfin tsiya muje har fadar tasa
Da jin haka sai zarikul laham ya kara kada fuka fukansa da karfin tsiya ya kara gaba cikin azababben gudu ya nufi daji na farko
Wani irin gudu ya dingayi da karfin gaske sai da ta shafe rabin sa'a yana wannna gudun sannan suka tsinci kansu
Acikin wani kasurgumin mai matukar muni da kuma abubuwa masu firgitarwa
Tun afarkon dajin suka lura da yanayin sa yasha banban da irin dajijjikan da suka saba gani a rayuwarsu
Domin ita kanta kasar cikin dajin motsi takeyi sai kace tsutsa
Kallo daya zaka yiwa dajin ka san cewa dole akwai mugayen halittu
Koda isowarsu wannan dajin sai aryan, marfuza da gimbiya walisa sarki fadarul munnar suka kalli junansu domin sun san cewa dole akwai wani mugun abin acikin sa

Shi kuwa aljani zarikul laham saiya rage karfin gudun nasa ya dinga tafiya kamar baya son yi
Da ganin haka sai jaruma marfuza tace dashi kai kuma menene yasa ka rage gudu?
Dajin wannan tambayar sai ya juyo ya dubeta yace ya shugabata ai wannan gurin da gani kinsan babu tambaya domin dolene a sami abubuwa masu hatsari acikinsa don haka dolene mu sawa kanmu nutsuwa idan har munaso mu fita daga wannan daji lafiya
Kafin ya gama fadin abinda yake bakinsa tuni yaji an kawo masa wata iriyar mahaukaciyar wafta
Cikin bakin zafin nama ya kucewa harin da aka kawo masa
In badon yayi saurin kaucewa ba da tuni an tsarga wuyansa kan nasa daga jikin gangar jikinsa
Ba komai ne ya kawo masa wannan harin ba face wani
Irin gajeren dodo amma kuma hannunsa yana da mahaukacin tsawo domin ya ninka gangar jikin sau goma a tsawo
Koda su sarki fadarul munnar suka sunkuyo da kawunansu kasa
Sai suka wangame bakinsu suna kallon abin mamaki domin wadannan dodannin ne suka dinga bubbukowa daga cikin kasar gurin
Fitar burgu daga cikin rami dukkan wadannan dodannin jikinsu gaba daya an halicceshi ne da duwatsu masu matukar karfi
Kai da ganinsu kasan cewa dolene sh kasance sihirtattu kuma masu matukar juriya
Kuma wani abin da zai baka tsoro da kamar yadda wadannan dodannin suke da matukar karfin tsalle domin tsalle daya kawai suke
Sai ka gansu sun tashi sunyi kololuwa a sama ta yadda komai nisan da tsuntsu ko kuma aljani yayi bai isa ya iya ketarewa ta saman dajin ba face sun gama dashi
Tun daga nesa wadannan dodannin suka ankara da zuwansu sarki fadarul munnar
Don haka sai sukayi kwanton bauna suka zauna zaman jiran isowarsu sarki fadarul munnar domin suyi musu kwaf daya
Koda wadannan dodannin suka gama bayyana akan doron kasa
Sai suka daka tsalle alokaci guda suka tashi sama suka yanyame aljani zarikul laham
Dasu gimbiya walisa da nufin suyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu
Suna masu kai masa mahaucin sara da suka da wasu dogayen adduna da suke hannunsu
Koda suka kawo musu mugayen hare hare, cikin zafin nama sai su gimbiya walisa suka zare nasu makaman yakin da suke jikinsu
Suka kare harin da dodannin suka kawo musu koda makamansu suka hadu da juna take wata iriyar kara mara dadin ji tare da tartsatsin wuta kamar ana dukan karfe a makera suka tashi
Take cikin karfin tsiya suka tarwatsa dodannin suka tarwatse suka basu hanya
Amma saboda naci irin na dodannin sai sukayi kukan kura lokaci guda
Suka daka tsalle suka kewaye aljani zarikul laham a sama suka hanashi samun damar da zai kara koda tafiyar taku guda
Saboda tsananin karfin da suke dashi bisa dole aljani zarikul laham ya saki fuka fukansa ya sauko kasa domin a hadu guri guda ayi dauki ba dadin da zasuyi
Koda dirarsa akan kasa sai suka far masa gaba daya akachame da azababben yaki
Nanfa guri ya rincabe in banda sautin karar karafiiyar karafa babu abinda kunne keji
Duk inda su walisa suka ratsa saidai kaga suna banke dodannin da karfin tsiya
Amma da zarar sun fadi sai kaga sun kara mikewa zumbur
Nanfa kura ta turnuke guri ya yamutse kura ta tokare sararin samaniya yadda koda tafin hannunka
ba zaka iya gani ba saboda azababben yakin da suke yi
Sautin gurnanin dodannin ya cika dodon kunne gami da wani irin sautin gurnani da dodannin suke yi
Wanda shi kadai kan iya razana mutum idan mace mai tsohon ciki ta ji wannan gurnaninda sukeyi take zata haife abindake cikinta
Idan kuwa karamin jarumi ne zai iya haukacewa ta dalilin wannan fafatawar da sukeyi
Saboda irin bakin gumurzun da sukeyi kasa ta dinga girgiza kamar ana yakin duniya
Da zarar makamansu sun sauka ajikin dodannin saidai kaga tartsatsin wuta ya tashi
Gumurzu yakai gumurzu duk inda su sarki fadarul munnar suka ratsa sai dai kaga suna banke dodannin
Amma duk wannan abin sai ya zama na banza domin ko kadan makamansu baya tasiri ajikin dodannin
Su kuwa su walisa badon suna da zafin nama ba da basu isa su yi koda dakika guda ba agaban wadannan dodannin
Saboda duk da kasancewarsu gajeru suna da matukar karfin damtse, naci da kuma taurin kai
A wannan lokaci aljani zarikul laham yaga ta kansa saboda duk da kasance sa aljani sai daya rai na kansa agurin wadannan dodannin
Sai da takai ga cewa su gimbiya walisa ne suke hada karfi da kafe wajen taimaka masa suna kareshi daga sharrin wadannan dodannin
A wannan lokaci ne sarki fadarul munnar ya nunawa su gimbiya walisa banbancin tsohon kashi da kuma sabo
Domin duk wanda ta daka daga cikin dodannin saidai kaga ya tashi sama kamar an doka kwallo sama ya fadi a can nesa
Su kuwa su walisa kawai kuzari suka fishi saboda sunfishi ji da samartaka
Duk da cewa suna samun nasarar dukan dodannin sai hakan ya zama na banza
Saboda sun kasa samun nasarar koda kashe daya daga cikin dodannin domin kaifi da tsini basa tasiri ajikinsu
Amma saboda taurin zuciya sunki yarda su sallama kansu ga wadannan dodannin
Kuma babu abinda yake dada tayar musu da hankali ba
Face tsananin yawan da dodannin suke dasu kuma basu isa su iya ratsawa su wuce wannan dajin ba face sun kashe dodannin gabaki dayansu
To abin tambayar anan shine tayaya zasu iyatarwatsa su?
Tambayar da sarki aryan yayiwa kansa kenan kuma bai da amsar wannan tambayar
Haka dai suka shafe sa'o'i uku suna wannan fafatawar har tsawon wannan lokaci basu sami damar koda kashe daya daga cikin dodannin ba
Kuma a wannan lokaci dukkansu sun fara gajiya kai hatta shi kansa sarki fadarul munnar da aljani zarikul laham saida sukaji sun fara gajiya a wannan lokaci
Har saida yayi mamakin wannan gajiyar da yayi alhalin yasan cewa yana iya shafe mako guda yana. Yaki ba tareda ya gaji ba
Abinda bai sani ba shine wadannan ba irin halittun daya saba gamuwa dasu bane
Koda yaga lokaci na neman kure musu sai ya fara karanta dalasiman tsafi yana watsawa dodannin
Amma da zarar sihirin nasa ya sauka ajikinsu sai kaga yaki yayi tasiri ajikin nasu
Ana cikin wannan halin ne kawai sai wani dodo mai tsananin naci ya dankarawa sarki aryan sara agadon bayansa
Nantake ya kwallara ihu saboda zafi da zugin da yaji
Bai san sanda ya takarkare ya kwarara wata kabbara da karfi ba
Saboda karfin kabbarar saida gaba daya dajin yayi tsit hatta shima sarki fadarul munnar saida yaji gabaki daya tsigar jikinsa ta tashi kuma jikinsa yayi sanyi sakamakon jin sautin kabbarar da yayi
Cikin bakin zafin nama sarki aryan ya daka tsalle sama ya kaiwa dodannin wani mahaukacin sara sai gashi lokaci guda takobin nasa ta tsarge guda goma a alokaci guda
Take duk kawunansu suka rabu da gangar jikinsu suka tashi sama kamar anyi watsi dasu
Koda ganin abindaya faru sai sai suma su walisa suka fara karanta addu'o'i acikin zukatansu domin neman taimakon ubangiji
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai fadan yasha banban domin wata irin ragargaza suka dinga yiwa dodannin
Duk inda suka ratsa saidai kaga kawuna suna zubewa kasa kamar ana sassabe a gona
Jini ya dinga fallatsi. Asama yana zuba sai mace ana ruwan sama
Kasa ta dinga dudufniya a wannan lokaci koda wahala tayi wahala
Sai dodannin suka daina gurnani suka koma ihun fitar rai
Sai gashi sun zamewa dodannin alakakai ko kuma once wasan sarki ya hana dawa tsaiwa suka dingayi da dodannin
Shi kuwa sarki fadarul munnar duk da kasacewar shima yana saran dodannin amma ko kadan makaminsa baya yin. Ko kwarzane ajikinsu don haka da sukaga shi da aljani zarikul laham ne kadai basa iya cutar dasu
Duk sai suka harzuka sukayi gunji suka falfala da gudu zuwa kansu
Suka lullubesu kamar taron kudan zuma suna kai musu sara da suka tako'ina domin su sami abincin kalaci
Koda suka ga abjnsa yake shirin faruwa sai sarki fadarul munnar da zarikul laham sukayi kukan kura gami da karaji
Sukayi katantanwa atsakiyarsu
Take suka tarwatsa su gabaki dayansu sai gasu suna yawo a saman iska suna fadowa kasa
Amma saboda tsananin bakin nacin da suke dashi sunki hakura kawai dada tasowa sukeyi suna kara lullubesu domin da zarar sun gaji anan gurin zasu gididdiba namansu su cinye don haka sai suka bar inda su walisa suke
Koda jaruma taga abindake faruwa gasu sarki fadarul munnar
Saita kwarara uban ihu wanda yake firgita maza acikin filin daga
Sannan ta falfala da gudu zuwa inda su sarki fadarul munnar suke tana maj karanta wasu addu'o'i acikin zuciyarta domin neman taimakon ubangiji
ai kuwa sai take taji wani irin sabon kuzari ya shiga jikinta
Yana isa inda ake suke wannan bakin artabu sai ta daka tsalle sama
Ta dira a tsakiyar dodannin tana mai kai musu sara da suka
Cikin bakin zafin nama, juriya da bajinta adaidai wannan lokaci suma su sarki aryan suka lura da halinda su sarki fadarul munnar ke ciki
Don haka suma sai suka tarwatsa ragowar dodannin da suke kewaye dasu suka taho inda marfuza take domin tayata yakar wadannan dodannin
Ai kuwa koda suka hadu guri guda sai sukayita shayar da dodannin gidauniyar mutuwa saboda karfin addu'o'in da suke karantawa
A wannan karon basu kara shafe wasu sa'a biyu ba suka gama karar da dodannin gabaki dayansu
Ya zamana dajin in banda karnin jinin dodannin babu abinda hanci yake shaka
Ita kanta kasar dajin sai data rine da jini gabaki dayanta
Koda suka gama da wannan rukunin na farko basu taya wani bata lokaci ba domin su huta
Kawai sai suka mike dukkansu suka goge jinin dake jikin makaman yakinsu
Sannan suka tashi suka haye bayan aljani zarikul laham
Ya daukesu suka nufi daji na gaba saida sukayi tafiyar sa'a hutu
Sannan suka isa rukunin daji na biyu wanda babu komai acikinsa
Face wasu manyan duwatsu masu kama da tsaunika
amma kuma abin mamakin shine gabaki daya wadannan duwatsu ba a zaune suke akan kasa ba
Suna yawone a saman iska kuma kowacce kusurwa daga jikinsu zakaga dutsen yana aman wuta ta gurin
Duk abin kuwa da wutar ta sauka akansa take kuwa zakaga ya kone kurmus hatta tokarsa ma ba zaka gani ba
Koda kuwa karfene

MAI SAI FARU A WANNAN DAJI?
WADANNE IRIN HALITTUNE SUKE RAYUWA ACIKINSA
KUMA SUWAYE ZASU IYA KETARE WANNAN DAJIN A RAYE?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
DAGA NAKU

HABIBULLAH KBR
(YARON MARUBUTA)
LIKE, COMMENT AND SHARE*********HATSABIBAN SADAUKAI

CIGABAN ZUBAR DA JINI

******************************6 PART C

LBR

******************HABIBULLAH KBR

Gabaki daya dajin haka yake wani irin hucin zafi yana dukan fatarsu
Koda isowarsu wannan daji sai aljani zarikul laham ya tsaida fuka fukansa
Sakamakon ganin wasu manya manyan tsuntsaye daya gani masu girman gaske
Kowanne daya daga cikinsu girmansa yakai girman rikakkiyar mikiya
Kuma suma jikinsu gaba daya ci yake da wuta kamar yadda duwatsun dajin suke
Da zarar daya daga cikinsu ya bude bakinsa yayi ruri saidai kaga
Tartsatsin wuta yana tashi kamar ana kira a makera
Idanunsu ma jajur suke kamar garwashin wuta duk inda ka hanga acikin wannan dajin babu abinda zaka gani face wadannan tsuntsaye da kuma duwatsu
Domin duk tsuntsayen daga cikin duwatsun wutar suke fitowa
Kuma ba tareda yayi musu komai ba saboda suma jikinsu na wutar ne
Kasan dajin ma babu komai face wannan wutar tsububu
Duk wanda ya kuskura ya fada cikinta take anan zai kone
Koda ganin wadannan abubuwa sai su kansu su walisa
Suka saki bakinsu suka tabbatar da cewa tabbas yau sun shiga tsaka mai wuya
Gurin da babu wanda zai iya cetonsu face ubangijin musulunci
Domin suna da tabbacin cewa a wannan guri tsafi ba zaiyi tasiri ba tunda gidansa sukazo
Shi kuwa sarki fadarul munnar sai ya fara karanta wasu dalasiman tsafinsa
Domin su sami kariya daga sharrin wadannan tsuntsaye
A daidai wannan lokacin ne tsuntsayen suka kura dasu sarki fadarul munnar
Don haka sai nantake suka falfalo da gudun tsiya zuwa kansu
Suna wani irin kuka mara dadin saurare wanda shi kadai ma zai iya kashewa mutum dodon kunne
Ai kuwa sai suma suka falfala kan tsuntsayen da gudun gaske
Lokaci guda suka hadu a tsakiyar dajin suka kaure da mahaukacin fada
Guri ya rincabe in banda sautin kukan tsuntsayen babu abinda kunne keji
Tsuntsayen suka saka aljani zarikul laham atsakiya suka hanashi yin gaba ko baya ta ko"ina kawo masa hari sukeyi
Da zarar su walisa sun kaiwa tsuntsayen sara saidai kaga makamin nasu ya ratsa jikin tsuntsun da suka sara ta wuce sannan jikinsa ya sake komawa ya hade kamar babu abindaya taba samunsa
Idan kuwa suka saka hannu suka daki jikinsu dashi take hannunsu yake konewa
Bisa dole suka daina dukan tsuntsayen da hannuwansu domin sune suke jin zafin dukan
Haka dai suka daure sunata faman yaki da wadannan sihirtattun tsuntsaye tun da hasken rana a gari har dare yazo ya raba basu daina wannan yakinba
Kuma suma su gimbiya walisa basu iya kashe ko guda daya ba daga cikin tsuntsayen
Ana cikin wannan haline adaidai lokacin da gumurzu yakai gumurzu
Kuma hasken gari ya dauke ya zamana ko tafin hannunka ba zaka iya gani ba
Saboda duhun gari kawai sai daya daga cikin duwatsun da suke aman wuta acikin dajin yayi bindiga
Take sai dutsen ya tarwatse kawai sai wutar dake cikinsa
Ta zubo akan fuskar aljani zarikul laham nantake sai fuskarsa ta babbake gabaki dayanta
Ta zama toka shi kuma ya saki fuka fukansa domin fadowa kasa
Don tuni ya dade da shekawa barzahu koda sarki fadarul munnar yaga abinda ya faru
Ga aljani zarikul laham sai hankalinsa yayi mummunan tashi ya dinga
Karanto wasu sirrikan tsafi a zuciyarsa,
Su kuwa su gimbiya walisa basu san sanda suka fara yiwa allah kirari ba
Suna mai neman taimakon sa domin sun san cewa ba zasu iya kwatar kansu daga wannan bala'in da suka shiga ba
Kafin su gama addu'ar tuni zarikul laham ya gama narkewa ya fado cikin wutar
Gimbiya walisa ce ta fara dira akan kasa ba zato ba tsammani
Sai taga ta zauna daram acikin wutar ba tareda wutar ta cutar da ita ba
Tana daga kanta sama sai tayi arba da mahaifinta yana fadowa
Kuma ta tabbatar da cewa idan har ya fada cikin wutar nan konewa zaiyi
Domin tsafinsa ba zai taimakeshi ba ,kodayin wannan tunani sai ta daka tsalle
Sama kamar ta kasance tsuntsuwa ta cafo mahaifin nata ta goyashi agadon bayanta sannan ta dira akasa
Suma su sarki aryan da jaruma marfuza haka suma sauka acikin wutar ba tareda tayi musu komai ba
Kafin suyi wani yunkuri tuni tsuntsayen sun gama lullubesu an sake kacamewa da
Masifaffen yaki fiye da wanda sukayi abaya domin a wannan lokaci su kansu tsuntsayen a matukar fusace suke
Haka suma su gimbiya walisa shi kuwa sarki fadarul munnar
Kwallar takaicice ta zubo masa domin ganin cewa wannan ce rana ta farko a rayuwarsa daya kasa taimakon kansa saidai wani ya taimaka masa
Domin ya tabbata tsafinsa bai isa ya kwaceshi daga sharrin wannan dajin wutar ba
In badon 'yarsa gimbiya walisa ta ceceshi ba da tuni ta sheka barzahu
Haka dai su walisa suka cigaba da karanta addu'o'in neman taimakon ubangiji acikin zukatansu
Don haka bisa mamaki sai sukaga duk tsuntsun da suka sara da makaminsu take yake tarwatsewa ya kama da wuta kurmus ya mutu
Kafin cikar dakiku sittin sun gama kashesu gabaki dayansu
Suna gamawa da tsuntsayen ne kuma sukaga wadannan duwatsun wutar
sun tahi kansu gadan gadan tun kafin su iso gimbiya walisa bata san sa'adda ta kwanto sandar SADAUKI HASSANUL BASARI
Ba daga bayanta ta ruke ta da hannayenta biyu
Koda duwatsun wutar suka iso saita dinga kai musu duka da wannan sandar
Take duk wanda ta doka ya dinga bindiga yana faduwa cikin wutar sannan kuma kaga ya bace bat kamar bai taba wanzuwa ba
A haka ta suka gama da wannan dajin gabaki dayansa
Sannan suka tashi suka kara gaba suka ci gaba da tafiya
Saida suka shafe wata guda suna tafiya busa kafafunsu
Kuma suna ratsawa ta cikin manyan dajujjuka masu hatsari wadanda sukafi
Wadanda suka ratsa a baya hatsari sosai, domin ko wanne daji halittun dake cikinsa
Sunfi na baya hatsari, yawa da kuma karfi amma a haka da kyar da sidin goshi suka wace gabaki daya wadannan dajujjukan suka isa daji na karshe wanda anan ne sabuwar fadar YARIMA WALISU take
A cikin tsakiyar wani katon teku wanda ruwan cikinsa
Ya cika ya batse har wani hankoro ruwan yakeyi idan igiyar ruwa tana kadawa
Ruwan kuma har wani irin tururin sanyi yakeyi domin gabaki dayansa sanyi ne dashi
Tun a kan saman ruwan idan ka kura ido zaka dinga ganin wasu irin manyan dorunonin ruwa suna yawo a saman ruwan
Ba tareda sanyin ruwan kuma ya cutar dasu ba domin suma duk jikinsu sanyi ne dashi
Dole saika ratsa ya cikin wannan teku sannan zaka riski fadar yarima walisu domin a tsakiyar sa take
Koda isowarsu wannan guri duk sai suka tsaya sukayi cirko cirko
Kuma gabaki daya dajin babu bishiya ko daya wacce zasu hada kwale kwale da ita
Suna kallon wannan takun da kuma fadar da yarima walisu yake ciki
Suna nazarin yadda zasu iya ketareshi har su shiga cikin wannan fadar
Daga can sai walisa ta dubi sarki fadarul munnar tace ya abbana shin yanzu ka gani da idanunka abindake cikin wannan teku
Idan har munason ketareshi dolene mu ratsa ta cikinsa
Kai kuma yanzu babu makawa idan ka shiga cikin sa zaka iya rasa rayuwarka
Domin sihirin da kake takama dashi nan ne gidansa ba zai taba tasiri ba a wannan guri
Domin kaimaka gani da idanunka abaya cewa sihirin ka baya tasiri tunda muka shigo daji na farko na wannan daji
Inbadon taimakon ubangijin musulunci ba da dukkanmu mun dade da shekawa barzahu
Kodajin wannan batu sai sarki fadarul munnar yayi wani yake
Cikin jin kunya yace yake 'yata hakika duk maganarda kika fada gaskiyace
Amma inaso ki sani nima bawai ina jayayya da lamarin ubangijin sabon addinin da kuka shiga bane
Amma inaso na sami cikakkiyar hujjar da zanyi imani dashi
Wannan ne yasanya na baro gida na biyo ku domin naga ranarda zata zamo karshen zalunci a duniya gabaki daya
Wannan shine babban burina tun kafin a haifeku bayan an haife ku kuma na dinga baku horon yaki har kuka kai matakin da kuke

Please Login or Register in order to submit comment