Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

karon sun raba daren gida ukune jaruma marfuza
Ce kadai zata fara gadinsu yayinda su kuma suke barci abinsu
Idan dare ya raba kuma sarki aryan ne sai kuma gimbiya walisa itace akarshe
Ba tareda bata lokaci ba suka kwanta barci abinsu suka bar
marfuza a tsaye akansu tanayin gadinsu
Atakaice dai har shima sarki aryan ya karbi gadin ahannunta
sannan ya maidashi ga gimbiya walisa ba tareda wani abu ya samesu ba
Sai bayan gimbiya walisa ta karbi gadin ne da 'yan dakiku
Kawai sai ta dinga jiyo sautin taku yana tahowa inda take
Da alama wannan takun bana mutum daya bane domin tun daga nesa kasa take amsa takun abinda yake tahowa
Nan take gimbiya walisa ta tattara hankalinta gaba daya ta mika shi hanyar da take jiyo wannan taku domin taga abinda yake tahowa
Sakamakon akwai ragowar hasken farin wata wanda yake hasko cikin kogon
Ba komai ta gani ba face wasu irin munanan halittu masu kama da dodanni
Kuma dukkanninsu babu wanda yake da ido ko guda daya ajikinsa amma haka suke durfafo gurinda take adadin wadannan dodannin kuwa ya wuce lissafi kuma gasu girda girda
Bakinsu kuwa cike yake da zakwa zakwan hakora masu tsinin gaske

YAYA ZATA KASANCE A TSAKANINSU?

LIKE, COMMENTS AND SHARE*************-*-*HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

**************3 PART A

LBR

**********-**HABIBULLAH KBR

Shi kansa gurnanin da wadannan dodannin sukeyi abin tsoro ne
Sannan ga wani ruwa mai yauki da yake dalalowa daga cikin bakunansu
Kafin a dauki dogon lokaci tuni sun cika filin da yake cikin kogon duk inda ka wai waya su zaka gani fulul
Da ganin wannan uban yawa da dodannin suke dashi sai walisa ta jinjina kanta kuma ta tabbatar da cewa dolene su sha gwagwarmaya da wadannan halittu
Cikin sanda ta karasa inda su jaruma marfuza da sarki aryan suke kwance
Ta sunkuya da nufin ta tashesu daga barcin da sukeyi
Ba zato ba tsammani sai taga wani daga cikin dodannin ya dako tsalle daga cikin yan uwansa kai tsaye ya nufo inda take da nufin ya datse mata kai da wani dan guntun gatari da yake hannunsa
Cikin bakin zafin nama sai walisa ta kaucewa harin nasa
Tareda sa kafa ta dokeshi da ita sai da yayi sama kamar an janyeshi da majaujawa
Ba tareda bata lokaci ba, tayi sauri ta tashi su marfuza dake kwance
Take duk su biyun suka mike tsaye zumbur tare da zare makaman su cikin. Shirin kota kwana
Nanfa suka tsaya suka karewa dodannin kallo sannan suka afka kansu aka kachame da azababben yaki atsakaninsu
Duk da kasancewa daga barci suka tashi sai gashi sun tashi da kuzarinsu babu wata kasala
Sai gashi sun shiga tsakiyar dodannin suna fafata yaki dasu
Sai da suka shiga tsakiyar dodannin ne nadama tazo musu domin dodannin suna da matukar karfin damtse fiye da aljanun da suka fafata dasu abaya
Hakama zafin nama domin tako'ina kawo musu sara da suka suke
Sannan abin da yake basu da wadannan dodannin shine duk da kasancewarsu
Basu da idanu amma hakan bai hana su sanin inda su walisa suke ba tamkar masu idanuwa
Abinda basu sani ba shine gabaki daya dodannin suna amfani da kunnuwansu ne wajen gane abin farautarsu daga sautin numfashi
Idan har zakayi numfashi to suma zasu san inda kake da kuma irin motsin da kake yi kamar masu idanu
Nanfa gurin ya cika ya batse in banda sautin gurnanin dodannin da
Kuma karar karafkiyar karafa babu abinda kunnuwa suke ji

Kuma dukkansu makami iri daya ne a hannunsu
Domin duk gajerun adduna ne a hannunsu masu kaifin gaske
Nanfa sukayi musu rubdugu suka kewaye su ta ko'ina suna kawo musu sara da suka ta'ina domin suyi gunduwa gunduwa da sassan jikinsu domin su sami abin kalaci
Duk wannan abinda yake faruwa su walisa sun kasa samun damar kashe ko data daga cikinsu
Domin kaifi da tsini baya tasiri ajikinsu
Duk sanda suka sami nasarar sukar jikin dodannin ko kuma saran jikinsu
Sai dai kaji karar haduwar karfe da karfe ta tashi tareda tartsatsin wuta
Ba tareda sun samu ko kwarzane ajikinsu ba, kuma duk wannan abu da akeyi babu alamun gajiya a tare wadannan dodannin
Domin har a sannan kamar ma kara musu kuzari akeyi haka suke wannan yaki baji babu gani tamkar zasu ci babu
Su kuwa su walisa a sannan har sun fara gajiya saboda tsawon lokacin da suka dauka suna fafata wannan kazamin yaki ba tareda sun sami nasara ko 'yar kadan ba
Ana cikin wannan bakin artabu ne kawai sai wani dodo ya shammaci sarki aryan ya dankara masa sara agadon bayansa
Take ya kwallara uban ihu mai karfin gaske saboda tsananin zafi da kuma zugin da yaji
Ai kuwa sai dodon ya sake kawo masa wani saran a karo na biyu
har addar tazo daidai saitin wuyan sarki aryan sai kawai marfuza ta dako tsalle daga inda take tasa takobinta ta kare saran sannan tasa hannunta guda ta daki tsakiyar ruwan cikin dodon
Saboda karfin dukan saida dodon yayi sama kamar an janyeshi da majaujawa sannan ya fado kasa tim da rufda ciki
Amma sai ya sake mikewa tsaye kamar babu wani abu daya sameshi ya sake danno kansa zuwa inda ake fafata wannan yakin
Cikin sauri marfuza ta debo wani garin magani daga cikin jakar guzurinta
Shi kuma sai ya dinga kare duk hare haren da suke kawomasa
Sannan gimbiya walisa tana taimaka masa
Yayin da ita kuma marfuza ta tsaya abayansa ta shafa masa wannan garin maganin nata
Aikuwa tana gama shafa masa sai yaji gaba daya zugin jikinsa ya gudu kuma jinin da yake diga daga cikin raunin ciwon nasa ya dauke dif
Kamar ma bai taba zuba ba
Kuma yaci gaba da yakin a haka da cikakken kuzarinsa kamar babu abinda ya same shi
Nanfa suka hada karfinsu waje guda wajen tarwatsa su da karfin tsiya
Domin a wannan lokacin dukkansu sun fusata burinsu kawai shine suga sun gano lagon dodannin amma damar hakan bata samu ba duk da cewa kuwa sun hada karfi da karfe wajen wannan azababben yaki ko kuma ince bakin gumurzu
Sai da suka kara shafe wasu sa'o'i biyun suna wannan yaki
Ba tare da sun sami nasarar komai b
Da ganin haka sai walisa ta fusata ta daka tsalle sama ta shuri daya daga cikin dodannin ta makashi da kasa
Sannan tasa hannuwanta ta kamar kansa ta murde masa wuya
Bisa mamaki kuwa sai taji wata kararas ta tashi alamar karyewar kashushuwan wuya
Ai kuwa take ta wullar da gawarsa kasa ya fadi kasa ko shurawa baiyi ba
Ganin haka saita yiwa su marfuza inkiya da su karya kashushuwan wuyan wadannan dodannin
Ai kuwa dajin haka sai duk murna ta kamasu suka fara kokarin yin hakan
Amma ina wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi
Duk inkiyar da tayiwa su marfuza ashe duk dodannin sun fuskanta
Don haka sai suka ki yarda su baiwa su marfuza damar cika burinsu akansu
Ana cikin haka ne kawai sai wani dodo ya shammaci gimbiya walisa ya dankara mata duka agadon bayanta
Saboda karfin dukan saidata fadi kasa sumammiya
Koda faduwarta sai duk dodannin suka daina ganinta suka koma kaiwa su walisa hari ta ko ina sama da kasa
Da ganin wannan al'amar sai su sarki aryan suka fahimci cewa
Wadannan halittu basa iya ganin mutum idan har ya dauke numfashinsa
Koda yin wannan tunani sai marfuza tayi kukan kura ta sabi walisa ta goyata a gadon bayanta sannan Ita da sarki aryan duk sai suka dauke numfashinsu
Ai kuwa sai duk dodannin suka rikirkice hankalinsu ya tashi suka fara laluben su sarki aryan
Wannan damar ce su sarki aryan suka samu suka fara ragargazar wadannan dodannin
Babu ji babu gani haka suka dinga yawo akan dodannin kamar iblisai sunata faman ragargazar su
Nanfa hankalin dodannin ya kara dugunzuma fiye da ki yaushe sakamakon jin gurnanin yan uwansu alokacin da ake karkashesu
Wohoho hakika tashin hankali bashi da dadi kuma duk wanda kaji yana nemansa to baisan illarsa bane
domin kuwa koda wadannan dodannin sukaga yadda ake ragargazarsu ta ko ina
Sai hankalinsu ya kara dugunzuma fiye da ko yaushe
Suka fara tunanin neman hanyar guduwa duk da cewa kuwa sune suka kawo kansu ba wanine ya kawo su ba
Koda su sarki aryan suka fahimci manufar wadannan dodannin sai suka dinga binsu suna kure musu gudu suna ragkesu akasa
Kamar wasan sarki ya hana dawa tsaiwa domin kafin kace wani abu
Tuni sun gama ragargazar dodannin, koda suka gama karar dasu
Sai jaruma marfuza tayi sauri ta kwanto gimbiya walisa daga gadon bayanta sannan ta debo ruws daga cikin battar ta ta fesama afuska
Firgigit gimbiya walisa ta farka daga suman da tayi tareda daka tsalle ta mike daga kwanciyar da take cikin shirin ci gaba da yaki a tunaninta har yanzu fafatawa akeyi
Su kuwa su marfuza duk sai suka daga kawunansu sama suka bita da kallo suna yi mata dariya
Sai asannan ne ta kula cewa gaba dodannin nan babu ragowar ko guda daya daga cikinsu duk sun zama gawarwaki
Koda ganin haka sai taji kunya ta kamata ta sunkuyar da kanta kasa sannan ta zauna a inda suka zauna
Cikin sauri sarki aryan ya dubeta yace sannunki Jarumar jarumai
Hakika na jinjina miki kan wannan irin jarumtaka da kuma dakakkiyar zuciya da kika nuna

Hakika abin a yaba miki ne kuma na kara sallamawa
baiwar da kuke da ita ta iya jure gumurzu a ko wanne irin hali kuka tsinci kanku keda dan uwanki yarima walisu
Tabbas duk abinda kuka saka agabanku dolene kiyi nasara akansa koda kuwa duniya kukayi shirin tunkara
Dajin haka sai walisa tayi masa guntun murmushi tace
Ai ku ya kamata nayiwa wannan jinjinar domin kuwa kune kuka kashe wadannan dodanni bani ba domin lokacin ma bana cikin hayyacina hakan ta faru…………
Caraf sai marfuza ta tari numfashinta tace kwarai kuwa
Maganar da sarki aryan ya fada gaskiya ce
Domin duk nan kin fimu dakakkiyar zuciya domin kuwa yanzu haka ma kin nuna mana ita akan idanunmu
Koda jin haka sai walisa tayi murmushi sannan tace ai shikenan
Yanzu nima na fahimci cewa suma nayi don haka idan ba zaku damu ba zanso ku bani labarin abinda ta faru alokacin dana suma
Ba tareda gardamar komai ba kuwa sai marfuza ta kwashe labarin komai da duk abinda ya faru tun daga farko har zuwa kashe ta fada mata
Kodajin yadda ta kasance sai walisa ta bushe da dariya sannan tace
Gaskiya na yarda da akace idan kaga ki gudu to sa gudu ne baizo ba
Amma nayi mamakin irin wahalar da kuka baiwa wadannan dodannin har da kuka saka su gudun ceton rai
Hakadai sukaci gaba da hirar da sukeyi cikin nishadi dukkansu

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA WALISA ACIKIN KOGON DUTSE
******* ***-**-* *******
Al'amarin yarima walisu kuwa tun lokacin da su gimbiya walisa suka bace masa suka shige cikin wannan kogon sihirin
Sai ya kama hanyar komawa can cikin kogon tsafinsa
Cikin kankanin lokaci ya isa can din ya fara bincike kan halinda su gimbiya walisa suke ciki da kuma yadda zai yi ya bisu cikin kogon tsafin
Ai kuwa take saiga hoton halinda su gimbiya walisa suke ciki ya bayyana akan allon tsafinsa
Tun daga lokacin da su sarki sarki aryan da jaruma marfuza sukayi mata maganin wannan dafin da yake jikinta
Da kuma fitowarsu daga cikin kogon dutsen suka tsinci kansu acikin wannan dajin mai sahara
Sai kuma ya fara tsananta bincike kar yarda zai yi ya bisu can cikin wannan daji domin ya hallakar dasu acikinsa
Sai kuwa alkaluman tsafinsa suka nuna masa cewa bashi da ikon shiga cikin wannan daji
Domin gaba dayansa yana cikin hurumin wannan kogon tsafin ne wanda su walisa suka buya acikinsa
Koda ganin wannan al'amari saiya takarkare ya kwarara uban ihu
Wanda ya sanya fadar tasa fadar gaba daya ta fara girgiza
Kamar ana girgiza ganyayen bishiya yayinda akayi ruwan sama
Haka komai da komai ya dinga yawo acikin iska kamar ana watsi dasu
saida yayi ihun ya isheshi sannan ya tsuke bakinsa kamar wanda aka aiko masa da sakon mutuwa sannan komai ya tsaya yarda yake
Kawai sai yayi wani guntun murmushi na muganta
Yace ai idan ni ba zan iya shiga ciki ba zan iya tura dan aike
Yana gama fadin haka sai ya rintse idanunsa tareda karanta wasu dalasiman tsafi
Faruwar hakan keda wuya sai wani bakin hayaki ya bayyana acikinsa take ya tura wannan hayakin zuwa gasu gimbiya walisa
To shi wannan hayakin shine ya rikide ya koma siffar maridin da suka fafata dashi kuma har suka sami nasara akansa abaya
Tunda yaga sun sami nasara akan wannan maridin nasa bai sake tura musu wasu bala'o'in ba
Kawai sai ya sami guri ya zauna akan kujerarsa ta haske
Ya kurawa su gimbiya walisa walisa idanu yana kallon duk abubuwan da suke aikatawa
Tun daga sanda suka fafata kazamin yaki da wannan mardin nasa
Har zuwa sanda suka hau kan wannan tsaunin na mutuwa
Aikuwa koda yaga yanayin yadda wannan tsaunin yake sai ya bushe da dariya yace lallai su gimbiya walisa basu tsira daga mutuwa ba
Inada tabbacin cewa ko su waye su basu isa su iya ketare wannan dutsen a raye ba.……
Aikuwa yana cikin fadin hakan ne kawai sai yaga wannan kogon tsafin ya dare su gimbiya walisa sun fada cikinsa sun nutse
Kuma adaidai wannan lokacin ne hoton komai ya dauke dif daga kan madubin tsafin nasa ya daina ganin komai face duhu
Koda ganin wannan al'amari saiya bushe da dariya kamar wanda akayiwa albishir da samun mulkin duniya sai da yayi ta isheshi sannan ya tsuke bakinsa
Ba komai ne yasa shi wannan farin cikin ba face sanin cewa da alamu wannan dutse sihiri bata tasiri acikinsa
Wannan shine dalilin daya sakeshi wannan farinciki domin yasan cewa
Duk inda sihirin tsafinsa yaki yayi tasiri acikinsa to babu wani sihiri da zaiyi aiki agurin
Idan kuwa har hakan ta faru to su walisa basu da karfin damtsen da zasu iya ceton rayukan su daga duk bala'in da yake cikin kogon dutsen
Yana cikin wannan tunani ne sai ya jiyo wani sauti mara
dadin ji yana tasowa daga can wani sako na cikin kogon tsafin nasa
Dajin haka sai hankalinsa ya tashi domin a duk sanda
irin haka ta faru to akwai wani mugun abinda yake shirin faruwa dashi idan har baiyi gaggawar yin maganinsa ba
Koda jin wannan sauti sai take yaji zuciyarsa ta buga akaron farko kamar zata faso kirjinsa ta fito waje
Cikin sauri ya juya inda wani madubinsa na haske yake tsaye akan iska
Ya karanta dalasiman tsafin da yake amfani dasu idan bukatar gaggaw ta taso masa
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai shima madubin ya fara kumbura duk hasken jikinsa ya dinga disashewa zuwa duhu
Daga can kuma sai ya fara tsatstsagewa yana neman yin bindiga
Da ganin wannan al'amari sai hankalinsa ya dugunzuma ya tashi fiye da ko yaushe
Cikin sauri ya shafi madubin nasa da hannunsa sannan ya koma daidai
Nanfa yaji kamar zuciyarsa na duka da karfi alamar dole akwai wani mummunan al'amari da yake shirin samunsa
Amma kuma baisan ta bangaren da wannan mummunan abu zai bullo ba
Domin yasan cewa su gimbiya walisa suna cikin kogon tsafin da basu isa su fita daga cikinsa a raye ba
Yana cikin wannan tunani sai ya tuna da labarin masoyiyarsa wato GIMBIYA BAHJHAT DA KUMA SADAUKI HASSANUL BASARI wanda har yanzu bai san gurin da kabarinsa yake ba
Bare ya tabbatar wa da kansa cewa hassanul basari ya mutu ko yana raye
Da kuma irin yadda fafatawarsu ta kasance a cikin shekaru dubu biyu baya

WANNE ABU YARIMA WALISU KO KUMA INCE BOKA SAHIBUL UKUB YAKE TSORO ?

SHIN SU GIMBIYA WALISA SUNA IYA FITA DAGA CIKIN WANNAN KOGON A RAYE?

SHIN SADAUKI HASSANUL BASARI YANA RAYE KO KUMA YA MUTU?
IDAN HAR YA MUTU INA KABARINSA YAKE?
IDAN KUMA YANA RAYE A INA YAKE SHIN BOYE KANSA YAYI KO KUWA?

DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MUN HADU A KASHI NA GABA
NA WANNAN KAYATACCEN
LITTAFI MAI SUNA HATSABIBAN SADAUKAI CI GABAN ZUBAR DA JINI
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR

LIKES, COMMENT AND SHAREba.……***************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JINI

*****************3 PART B

LBR

*******************HABIBULLAH KBR

cikin matukar fusata gami da karaji yarima walisu yasa hannunsa ya daki madubin tsafin da hannunsa
Take kuwa madubin ya fashe yayi daga daga kamar an daka shi a cikin turmi
Kawai sai ya runtse idanunsa tare da karanto wadansu dalasiman tsafi masu matukar wahalar karantawa idan ba gurin manyan matsafa wadanda sukayi shuhura acikin ilimin bokanci irinsu ba
Ai kuwa faruwar hakan keda wuya sai gaba daya sararin samaniya tayi duhu dum dum saboda wani irin bakin gajimare tareda hadari da suka hadu lokaci guda
Wata irin guguwa ta dinga juyawa a sararin samaniya
Saboda karfin iskar hatta mikiyoyi da suke yawo acikin sararin samaniya fadowa suka dingayi kasa suna mutuwa
Bisa dole suka dinga shiga cikin kogunan duwatsu domin su tsira da rayukansu
Manyan tekuna kuwa suka dinga ambaliya suna shafe garuruwan da suke makobtaka dasu

Hankalin mutane, aljanu, tsuntsaye, dabbobi da kuma kananun kwari ya tashi
Sakamakon yadda suka dinga rasa rayukansu, kai a wannan lokaci babu wani bangare na duniya da halittu masu rai suke rayuwa acikin sa
Wadanda basu fuskanci barazanar rasa rayukansu da zubar da jini ba a wannan lokaci
Ai kuwa yana gama karanta wadannan dalasiman tsafin sai da duniya gaba dayanta tayi girgiza
Sannan sararin samaniya ta kece
sai ga wani hatsabibin sadauki, kuma murgujejen aljani mai matukar ban tsoro ya keto ta cikin sararin samaniya yana saukowa kasa
Shi kansa sautin kada fuka fukan nasa saida suka haddasa wata sabuwar guguwa wacce ta janyo asarar rayuka da yawa
Kai tsaye aljanin ya sauko daga sararin samaniya cikin tsala azababben gudu
Tun daga yammacin duniya wannan aljanin ya bayyana
Amma cikin dakiku kadan sai gashi ya shafe duk uwar tafiya kuma ya ratsa birane masu yawa ya isa fadar da yarima walisu yake ciki
Koda isarsa bakin fadar sai nantake fadar ta dinga karawa kanta tsawo da fadi
Harsaida takai daidai yadda wannan murgujejen aljani zai iya sauka acikinta ba tare daya matsu ba
Take ta saki fuka fukan sa
Ya sauka acikin fadar alokacin da duk rufin fadar ya yaye kansa
Sai gashi duk da tsananin girma irin na wannan bakon aljanin amma sai gashi ya zamo dan karami acikin wannan fadar
Kai tsaye yaci gaba da kutsa kai cikin fadar kamar yana tafiya acikin gidansa
Bai tsaya ba sai daya isa bakin kujerar hasken da yarima walisu yake zaune
Da isarsa bakin wannan karagar sai ya saki fuka fukan sa ya rissina tareda yin sujjada ba yarima walisu sannan yace
Gani na amsa kira ya shugabana yau tsawon shekaru dubu biyu da dari uku da tamanin da biyu kenan rabon daka kirani don yi maka aiki.
Sannan ya shugabana na lura da cewa wannan fuskar ba wacce nasan boka sahibul ukub da ita bace
Wata ce da ban ko zaka iya sanar dani dalilin ganin wannan suyi kuma wacce irin bukata ce dakai agareni?
Kodajin wadannan tambayoyi guda biyu sai yarima walisu ya bushe da dariya sannan yace
Kwarai kuwa
Ka sani cewa da tambayarka da amsarka duk abu dayane amsarsu
Yana gama fadin haka sai ya mike tsaye ya dauko wani alkalamin tsafi sannan yaje jikin bango
Take ya zana taswirar fuskar SADAUKI HASSANUL BASARI ajiki
Yana gama zanata sai ya juyo ya kalli wannan bakon aljanin yace
Yakai aljani dargatul amnar ka sani cewa duk wadannan abubuwa da suka faru sun farune sanadin wannan saurayi da kake gani
Ana kiransa da suna hassanul basari bin shurem shine jarumin daya haddasa duk wadannan abubuwa
Ka sani cewa a wancan zamanin lokacin da nake kan sharafina duniya take tsorona
Kuma ake yi mini biyayyar dole a wannan lokacin wannan saurayin shine kadai yaki yayi mini biyayya
Adalilin hakane muka fafata kazamin yaki tsakanina dashi

A karshe ya sami nasara akaina amma kuma nasarar tasa ta banza ce domin har yanzu gani a raye
Shi kuma nayi imani cewa bai da tsawon ran da zai kawo iyanzu
Babban tashin hankalina a yanzu shine bansan matsayin da yake ba
Ko yana araye ko ya mutu duk banida tabbas domin ban sami gawarsa ba
Babu irin binciken da banyi ba akan na gano inda yake amma na rasa
Barinsa a raye a gurina babban tashin hankali ne domin da zarar nayi sake zai iya ruguza mini duk shirin dana dade inayi
.abu na biyu kuma da nakeson sanar dakai shine
Yanzu haka akwai gagarumin aiki agabana guda biyu
Na farko shine neman inda wannan hatasabibin sadauki wato hassanul basari yake
Na biyu kuma shine aikin da nakeyi na yakar duniya da kuma zuba ido akansu gimbiya walisa da su sarki sarki aryan wadanda yanzu haka suna cikin kogon hayatul maut
Dolene mu jira su zuwa sanda zasu fito domin cika buri akansu

Yanzu dai aikinda nakeson kayi mini shine zakaje ka shiga cikin manyan biranen da muke dasu acikin wannan duniyar kaci gaba da bajesu daga doron kasa kamar yadda nakeyi
Sannan kuma bayan haka sai ka jira fitowar su gimbiya walisa daga cikin kogon dutsen da suke ciki
Da zarar sun fito saika hallaka mini su ni kuma yanzu zanje na tsawaita bincike akan shi hassanul basari domin nasan matakin da zan dauka akansa domin kai wannan aikin yafi karfinka
Ni kuma a gurina bazan iya tauna taura biyu a lokaci guda ba
Kodajin wannan bayanin sai aljani dargatul amnar ya bude baki cikin wata kakkausar murya yace
Ya shugabana
Ina neman alfarmar ni ka barni da kaina domin na tunkari wannan sadauki da kake zuzuta jarumtakarsa don nima na ganta da idona
Dajin haka sai sai yarima walisu yayi guntun murmushi mai kama da kukan jaki yace ai wannan aikin yafi karfin ka
Domin masu iya magana suna cewa BABBAN GORO SAI MAGOGIN KARFE
Kai yanzu baka da jarumtakar ko kuma karfin sihirin da zaka iya tunkararsa
Domin shi kadai ya rusa duk tanadin da nayi a wadancan shekarun ya tarwatsa duk irin tarkunan da suke hanyar zuwa fadar nan tawa kuma ya shigo ciki
Amma yanzu na tabbatar da cewa koda yana raye bai isa ya iya shigowa har cikin nan ba a wannan karon
Inaso ka sani cewa shi hassanul basari BABBAN GORO Ne
Ni kuma nine MAGOGIN KARFE don haka kaga kuwa ni kadai ne zan iya tankwarashi kuma na sarrafashi kamar yadda nake bukata,
Kodajin wannan batu sai aljani dargatul amnar ya bushe da dariya sannan yace
Kayi gaskiya ya shugabana tabbas kaine gagarabadau kuma ki gudu maganin sa gudu
Tabbas ilimi kogi ne kuma rashin sani ne yasa nake kokarin hada kaina da abokin hamayyarka
Amma banida kokwanto kan cewa kaine zaka sami nasara akansa domin nasara tana gareka kuma kaine uban kowa acikin wannan duniyar
Kodajin haka sai yarima walisu ya kyalkyale da dariya saboda yabon da yaji anyi masa daga can sai ya tsuke bakinsa ga barin dariyar da yake yi yace
Yanzu dai ba surutu zaka cikani dashi ba kawai ka tashi ka tafi aikin da yake gabanka
Dajin haka sai aljani dargatul amnar yace angama ya shugabana
Yana gama fadin haka sai take ya bude fuka fukansa masu matukar fadi
Ya tashi sama dasu ya luluka ta cikin saman rufin fadar sannan ya tashi sama yana mai kyalkyala wata iriyar dariya mara dadin sauraro
Domin ya sami irin damar daya dade bai sami irinta ba
Kai tsaye dargatul amnar ya nufi wani babban birni mai suna amnatul kais wanda yake cikin nahiyoyin bakaken fata
Shi dai wannan birni na amnatul kais yana karkashin mulkin wani azzalumin sarki ne wanda ya shahara a fannin farauta da kuma kiwo amma kuma gaba daya sarakunan kasashen dake kewaye dasu basa ga maciji da juna
Akullum basu da burin daya wuce yakar junansu domin daya daga cikinsu ya samuya kwace ragowar masarautun da karfin tsiya domin ya tara dukiya da kuma bayi
Sarkin da yake mulkin wannan birni na amnatul kais ana kiransa da suna
Yarmuna kuma ba'a hannun mahaifinsa ya gaji sarautar birnin ba
Domin ko kadan ma bai gaji sarauta ba,
Iya kaci dai ya kasance haifaffen wannan birni na amnatul kais
Tun yana karami ya taso

Please Login or Register in order to submit comment