Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

fassara shi
Tsawon wadannan kwanakin babu abinda sukeyi face karance karance dare da rana domin hatta bacci ma dan kadan suke yinsa
Acikon sati na biyun ne da kwana uku suka yi bankwana dattijo kusaid suka kama hanyar fita daga birnin gaba daya
Tsawon wadannan kwanaki sun shaku dashi ainun har suka ji kamar ma ba zasu iya tafiya su barshi ba amma a haka bisa dole dukkansu suka hakura suka tafi suka barshi idanunsu cike da kwalla
Bayan sun fito daga gidan ne kawai sai walisa ta dubi kusail
Tace amma dai yanzu ba zaka sake komawa cikin halayyar sata ba ko?
Dajin wannan tambaya sai kusail yayi murmushi fuskarsa cike da alamun kunya yace
Ai da dinma duhun jahilci ne ya sakani haka amma yanzu ai na gane gaskiya
Kodajin haka sai dukkansu suka bushe da dariya
Sannan suka koma cikin kasuwar garin suka sayi ingarmun dawakai kosassu guda uku sannan suka sayi abincin da zasuyi guzuri dashi
A wannan lokaci gimbiya walisa tana dauke da sandar sadauki hassanul basari
Suna gama sayen dawakan sai suka yi bankwana kusail
Sannan suka kama hanya suka fice daga cikin birnin gaba daya suka kutsa kansu cikin daji domin fita farautar yarima walisu
Duk inda suka gifta da dawakan su saidai kaga kura tana tashi
Kuma suna gudun ne cikin nishadi kamar masu yin gasar tseren gudu

WANNAN SHINE ABINDAYA FARU GASU GIMBIYA WALISA BAYAN SUN KARBI ADDININ MUSULUNCI KUMA SUN SAKE FITA NEMAN YARIMA WALISU

****** ******** ********
Al'amarin aljani dargatul amnar kuwa lokacin dayaci birnin amnatul kais da yaki kuma ya kama hanya ba tareda yasan gurin da zai kara zuwa agaba ba
Sai yayi ta tsala gudu acikin sararin samaniya kamar zai fita daga cikin duniya
Domin cika burin mai gidansa yarima walisu
Sai yayi ta kyalkyala dariya dariya wacce ta dinga amsa kuwwa agaba daya ilahirin samani wacce sautinta yake fita kamar saukar aradu
A wannan yini gudan sai da yaci birane ashirin da yaki kuma ya bazar dasu daga doron kasa
Kuma kisa iri daban daban ya dinga yi aduk inda ya sauka
Awannan ranar saida manyan koramu suka dinga cika da jinin bil'adama
Kasa kuwa ta dinga cudanya da jini abin babu kyan gani
Bayan ya gama da wadannan birane ashirin din ne ya doshi na ashirin da daya
Kawai sai ya tuna da maganar su gimbiya walisa kuma sune akafi bukatar ya fara gamawa dasu da wuri
Koda yin wannan tunani sai take ya juyar da akalar tafiyarsa
Cikin sauri ya nufi can kogon dutsen da su gimbiya walisa suke yana mai tsala azababben gudu
Awannan lokaci sai ya kure dukkan balagar dayake ji da ita cikin wannan tafiyar fiye da wanda yake yi a baya
Tafiya rabin yini kacal yayi ya isa bakin wannan tsaunin
Koda zuwansa sai yaga kofar kogon akulle kamar ba'a taba bude ta ba
Kuma gurin gabaki dayansa babu alamar sawun bil"dama ko kuma na dabba
Koda ganin haka sai yaji wani irin farinciki acikin zuciyarsa
Domin yana da tabbacin cewa su gimbiya walisa basu fito daga cikin kogon ba
Don haka sai ya kwantar da hankalinsa kuma yaji ya samu nutsuwa acikin zuciyarsa
Sai ya yanke hukuncin kawai ya zauna anan gurin ya jira har zuwa lokacin dasu gimbiya walisa zasu dawo
Abinda bai sani ba shine tun tuni su gimbiya walisa sun fita daga cikin kogon dutsen
Amfani sukayi da karfin sihirinsu suka suka boye sawun kafafunsu
Yadda koda an biyo bayansu ba za'a riskesu ba wannan shine dalilin dayasa aljani dargatul amnar ya kasa sanin fitowarsu
Kuma kuskurensa guda daya shine kin yin amfani da sihirin tsafinsa wajen binciken halinda suke ciki don ya san gaskiyar lamarin
Don haka sai. Ya sami guri ya zauna domin jiran fitowarsu
Aikuwa zamansa keda wuya sai take barci mai nauyi ya sace shi ba taredaya sani ba
WANNAN SHINE BABBAN KUSKUREN DAYA AIKATA
****** ******* ********
A can cikin kogon tsafin yarima walisu kuwa lokacin daya shiga cikin
Halwar tsafi domin ya gano wanne irin bala'ine yake neman tunkaro shi
Saiya manta da maganar su gimbiya walisa domin yasan cewa abune mawuyaci su tsira da rayuwarsu daga cikin kogon dutsen sa suka fada
Idan ma har sun samu dama sun kubuta to ya tabbatar da cewa aljani dargatul amnar shine zai taresu akan hanya ya kashesu
Don haka sai ya bata tunaninsa domin ya gama tabbatar wa da kansa cewa
Abinda ke shirin tunkaroshi babban abune mai hatsarin gaske
Acikin wannan sabuwar rayuwar da ya kafawa kansa
Amma kuma ya tabbatar da cewa wannan abin dole yana da nasaba da hassanul basari wanda ya kasance bashi da abokin gaba a rayuwarsa kamarsa
Babban burinsa shine yasan halinda hassanul basari yake ciki
Sai daya shafe kwanaki masu yawa yana wannan binciken
Atsawon wadannan kwanakin baiyi barci ba ko sau daya
Haka zalika koda ruwa makurwa daya bai sha ba
Arana
ta karshe ne da kyar da makyarkyata domin sai daya sha bakar wahala sannan ya gano cewa hassanul basari ya mutu
Koda ganin wannan al'amari baisan sa'addaya bushe
da mahaukaciyar dariyar farinciki ba wanda sautin dariyar saidaya ratsa ko ina acikin fadar tareda amsa kuwwa
Saida yayi dariyar ta isheshi sannan kuma ya hade ransa
Sakamakon tunawa da maganar su gimbiya walisa kawai sai ya shafi madubin tsafin da tafin hannunsa
Take saiga hoton aljani dargatul amnar ya bayyana acikin madubin tsafin acikin daji yanata faman sharara barci abinsa
Daya barin kuma na madubin tsafin nasa ga hoton su gimbiya walisa can suna shirin fitowa daga cikin birnin labtarul halkam bisa ingarmun dawakai

Koda ganin wannan al'amari sai take duk fara'ar da take
kan fuskar sa ta disashe zuwa bakin ciki Cikin matukar
fushi ya daga hannunsa daga inda yake ya zabgawa hoton aljani dargatul amnar duka yana daga inda yake
Awannan lokaci dargatul amnar yana kwance abakin kogon dutsen
Kawai sai ya ji sautin dukan da yarima walisu yayi masa
Saboda zafin dukan baisan sanda ya daka tsalle ba ya tashi firgigit kamar an tsulawa yaro bulala
Yana tashi sai yayiwa yarima walisu sujjada
Jikinsa na karkarwa kamar kace kyat ya ruga a guje saboda matukar firgitar da yayi

Yarima walisu ya dubeshi yace kai kuma aikin dana saka kenan?
Dajin wannan tambayar sai aljani dargatul amnar yace kayi mini afuwa ina nan ina zaman jiransu ne barci ya sace ni ban sani ba
Amma kayi hakuri bazan kara yin wannan kuskerenba
Dajin wannan batu sai yarima walisu ya daka masa tsawa yace
Kai shashashan banza maza ka tashi yanzu kabisu domin basa cikin kogon dutsen nan
Yanzu haka sun fito daga birnin labtarul halkam ka tare su hanya ka gaggauta kashemini su
Idan kuwa kayi wani kuskure ni da kaina zan kasheka
Dajin haka sai jikinsa ya fara kyarma yace kayi hakuri ya shugabana yanzu zan cika umarnin ka kar ka sami damuwa

Yana gama fadin haka sai ya sake bude fuka fukansa ya nufi hanyar da zata kaishi birnin labtarul halkam domin ya riski su walisa ahanya ya kashe su don cika umarnin mai gidansa

SHIN YANA RISKARSU WALISA AHANYA ?
YAUSHENE ZASUYI GABA DA GABA DA YARIMA WALISU?
SHIN RUHIN BOKA SAHIBUL UKUB YANA FITA DAGA JIKIN YARIMA WALISU ?
DON JIN AMSAR WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU AKASHI NA GABA
DAGA NAKU
HABIBULLAH KBR
LIKE, COMMENTS AND SHARE************----HATSABIBAN SADAUKAI

******************CI GABAN ZUBAR DA JINI

********************5 PART A

LBR

*************************HABIBULLAH KBR

Lokacin da aljani dargatul amnar ya bude fuka fukansa ya tashi sama
Sai gashi fuka fukan sun lullube gurin gaba daya sannan ya fara kadasu da karfi
Domin ya gaggauta riskarsu gimbiya walisa tunda yasan cewa idan har yayi kuskure akan aikin da aka saka shi hukuncin kisa yarima walisu zai yanke masa kuma ko kadan bazai tausaya masa ba
Saboda haka sai yayita tsala azababben gudu kamar kiftawar ido haka ya dinga giftawa ta saman manyan birane
Duk inda ya gifta sai fuka fukansa sun yiwa birnin gaba daya inuwa saboda girman su
Cikin kankanin lokaci ya riski su gimbiya walisa alokacin suma suna tsaka da tafiya
Kuma rana ta kwalle sosai suna cikin tafiya sai sukaga
Tun daga nesa suka hango wata jibgegiyar inuwa tana doso inda cikin azababben gudu
Koda ganin wannan inuwar sai duk sukaji jikinsu yayi sanyi domin sun san tabbas wannan abin gurinsu ya doso kai tsaye don haka duk sai suka tsayar da linzaman dawakansu
Domin suga abinda yake shirin faruwa sannu a hankali sai suka fara hango manyan fuka fukan aljani dargatul amnar wanda suka tokare sararin samaniya
Da ganin haka sai dawakan dasu walisa suke kai suka firgita suka fara turjiya suna daga kafafuwansu na gaba sama domin su daga su walisa sama su zubar dasu domin su kara tsira da rayukansu
Amma sun rasa yadda zasuyi domin su walisa sun ruke linzaman dawakan sosai kuma sun tokare ko'ina da kafafunsu yadda dawakan ba zasu iya kwacewa daga hannayensu ba

Daga can sukaji an kece da wata mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu
Tareda wata irin tartsatsjn wuta daya zubo daga sararin sama
Koda wutar ta sauka akan kasa sai take ta haifar da wani wawakeken rami
Wanda za'a iya binne mutum goma aciki
Cikin sauri su walisa suka sauka daga kan dawakan nasu suka sakesu
Domin suma su samu su tsira da rayuwarsu tunda sun san indai akan dawakan za'ayi wannan fafatawar zasu sha wahala sosai
Take dawakan suka ruga da gudu zuwa can cikin daji domin su ceci rayuwarsu

Cikin kankanin lokaci saiga aljani dargatul amnar ya keto cikin hazo
Ya zuro da fuskar kasa yana kyalkyala wata mahaukaciyar dariya wacce tasa dajin gaba daya ya dinga amsa kuwwa
Tunda su walisa suka zo duniya basu taba ganin aljani mai girma da kuma muni irin aljani labtarul halkam ba
Domin su kansu saida sukaji kamar suja da baya su gudu domin tsira da rayukansu
Amma sai suka danne tsoron daya darsu azuciyarsu
Kuma suka tsaya cak ba tareda sun janye kafarsu baya koda da taku daya ba
Daga can kuma sai ya tsuke bakinsa ga barin yin dariyar da yakeyi ya kurawa su walisa mummunan idonsa mai kama da gasasshen dan buda yace
Ku kananun halittu masu ganganci da rayukansu wanne irin ganganci ne
Ya shigar daku cikin tarkon mai girma walisu?
Gaskiya kun tabka babban kuskure arayuwarku da har kuke ikirarin karawa dashi
Ku uku kacal baku da karfin da zaku iya jayayya dashi
Kai bama ku kadai ba duk duniya babu wand iya galaba akansa
Domin shi kadai yaci dubu sai ceto kuma tsautsayima yana shakkar tunkararsa saboda bala'insa
Bayan haka inaso ku sani yanzu kun gama fusata shi da kansa ya turoni nan domin na kai masa kawunan kanku
Kodajin wannan batu sai sarki aryan shima ya maidawa dargatul amnar da martanin murmushin raini yace
Hakika bamu ne mukayi kuskure ba kaine ka tabka babban kuskure
Daka har ka kuskura ya aikoka gurinmu domin ina tabbatar maka da cewa
Baka isa ka tsira ba daga hannunmu duk da cewa azahiri kafimu karfin damtse
Da kuma girman jiki amma ka sani hakan bazai hanamu samun nasara akanka ba
Don haka kaine ka aikata kuskuren zuwa garemu idan har ka isa cikakken namiji sai ka taho mu gwada gaba da gaba
Amma ina rantsuwa da ubangijin musulunci baka isa ka tsira daga kaifin takobin mu ba
Dajin sun ambaci ubangijin musulunci sai dargatul amnar
Ya tuntsure da dariya da katon bakinsa
Daga can kuma sai ya murtuke fuskarsa kamar an aiko masa
da sakon mutuwa yace lallai kun bani kunya tunda har kuka ajiye addinin da kuka gada tun iyayenku da kakanninku
Kuka karbi wani sabon addini agurinku wanda bashi da asali agurinku kuma sabone shi
Kuma wannan itace babbar hujjar da zata tabbatar mini da cewa zan sami nasara akanku
Yana gama fadin haka sai ya bude wangamemen bakinsa da nufin ya zuko su gimbiya walisa gabaki dayansu ya cinyesu
Cikin bakin zafin nama dukkansu suka daka tsalle daga inda suke suka kaucewa harin nasa
Da ganin haka sai ya kara kawo musu sara da kaifin faratan yatsunsa
Nanma suka kara daka tsalle suka kauce wa farmakin daya kawo
Sai gashi gurin da faratan nasa suka sara sun haddasa wawakeken rami agurin
Kawai sai su walisa suka falfala da gudu zuwa inda yake suka. Kacame da azababben yaki
wohoho ai kuwa koda fara wannan bakin gumurzun sadaukan sai
Gurin gaba daya ya sauya yanayi
Wata iriyar kura ta tashi sama tayi tsiri kamar zata tokare sararin samaniya
Kasa kuwa ta dinga girgiza tana jijjiga
Bishiyoyin da suke cikin dajin kuwa suka dinga jijjigowa daga cikin karkashin kasa har jijiyoyinsu suna faduwa kasa
Duwatsun da suke cikin dajin ma suka dinga farfashewa
Suna fadowa kasa kamar an saka musu nakiya ,tekunanda suka ratso ta cikin dajin ma suka dinga tambal tambal saboda masifar da take afkuwa acikin dajin
Ba komai ne ya haddasa hakanba face
Duk sanda dargatul amnar ya kawowa su walisa duka idan suka kauce ya sami kasa take yake haddasa wawakeken rami
Tabbas in badon su walisa suna da zafin nama ba da tuni dargatul amnar ya gama kashesu

Kuma dukkansu sunki yarda su fuskanceshi ta bangare daya domin kasa kansu sukayi gida uku kuma suna fadan suna canja matsaya
Ma'ana
Idan gimbiya walisa ta fusanceshi ta gabansa to ita kuma jaruma marfuza
Zata kasance abayansa ne
Haka shima sarki aryan zai tsaya agefensa
Kuma sunayi suna zazzagaya shi kamar shaidanu tako'ina
Amma da zarar sun sareshi saidai kaji wata irin kara ta tashi kamar haduwar karfe da karfe
Ana cikin wannan hali ne kawai dargatul amnar yasa mafarsa guda yayi bal da gimbiya walisa
Nantake tayi sama kamar an janyeta da majaujawa
Sannan ya shammaci sarki aryan da jaruma marfuza ya sunkuya
Ya shuri kafafunsu yayi jifa dasu a sama kamar yadda yayi da walisa
Sai gasu duk su biyun suna yawo. Asama kamar iska ta debi tari ledoji
Amma saboda matukar naci sai sukaki yarda su fadi duk suka dinga dunkule jikinsu asama suna dira bisa kafafunsu kuma ba'a cure suka fado kasa ba aguri daban daban suka dirga
Amma fa dukkansu babu wanda baiyi aman jini ba saboda dukan da yayi musu
Kawai sai dargatul amnar ya juya inda walisa take domin itace akafi bukatar ya hallakata gadan gadan da nufin yayi mata kisan wulakanci
Ai kuwa tun kafin ya isa inda take tuni ta daka tsalle ta mike tsaye sannan ta daki kasa da hannayenta tare dayin alkafira ta tashi sama kamar tsuntsuwa mai fuka fuki
Kawai sai gata ta dira ajikinsa ta makalkale kamar kadangaruwa tana faman gudu ajikinsa kuma tana saran jikinsa da takobinta
Aikuwa kodasu marfuza sukaga haka sai suma sukayi taho da gudu suma sukayi koyi da abinda walisa tayi
Tun suna saran jikinsa da makamansu harsai da takai cewa makaman nasu duk sun dakushe basu da wani amfani
Suna cikin wannan haline kawai sai dargatul amnar ya karanta wasu sirrikan tsafinsa
Faruwar hakan keda wuya sai su walisa sukaji gaba daya jikinsu ya makale ajikin dargatul amnar yadda koda yatsan hannunsu ba zasu iya dagawa ba
Kawai sai ya bude fuka fukansa ya tashi sama dasu a doron bayan nasa
Sai gashi yana tsala gudu dauke dasu yana ta faman wujijjigasu asama
Tareda kyalkyala musu dariya yana cewa
Ai na tabbatar muku kuskuren ku dayane shine ajiye addinin gado ku karbi sabon addini
Yanzu babu ta yadda zaku tsira da rayuwarku daga sharrina
Yana cikin wannan zance ne kawai sai gimbiya walisa ta tuna wata addu'a da kusaid ya koyar dasu
Aikuwa nan take ya fara karanta wannan addu'ar ba zato ba tsammani sai taji wani irin sabon azababben karfi ya shiga jikinta
Nantake ta banbare jikinta daga nasa
Sannan tayi kabbara da karfi
Karfin kabbarar ne ya rikita dargatul amnar yaji kamar kansa zai fashe
Bisa dole ya saki fuka fukansa ya dawo kan kasa
Haka suma su jaruma marfuza cikin sauri suka fara karanta addu'ar da walisa ta karanta
Nantake suma sukaji duk irin yanayin da walisa ta shiga
Cikin zafin nama kafin dargatul amnar ya sauka kasa tuni
Jaruma marfuza ta daka tsalle ta haye kan gadon bayansa
Ta kwanto doguwar sarkarta ta zura ta acikin hancinsa
Sannan ta ruke da hannuwanta guda biyu
Wohoho ai kuwa sai gashi nan danan ta fara sarrafa dargatul amnar ta dole kamar doki domin sukuwa suka dingayi akansa kamar doki
Haka suka dinga sarrafashi shi kuma a lokacin ya gama gigicewa saboda yadda suka dinga yi masa rugugin bala'i tako ina
Duk da karfin damtsen da yake takama dashi sai gashi ya zama na banza domin bil'adama ne guda uku kacal suke sarrafashi
Koda yaji bala'i sai ya dinga bude bakinsa yana faman yin aman wuta kamar batoyi tana zubowa kasa tana kona bishiyoyi da ciyayin da suke cikin dajin
Suna cikin wannan haline sai itama gimbiya walisa ta kwanto sandar hassanul basari da caka tsininta agadon bayan dargatul amnar
Aikuwa sai take dargatul amnar yayi wani irin gurnani alokacin da jini yayi feshi daga gadon bayansa
Kawai saiya sulale ya fado kasa acikin wani katon daji wanda yake kusa da wata katuwar teku
Sannan ya kama da wuta kamar an zubawa karmami kalanzir
Cikin sauri su gimbiya walisa suka sauka daga gadon bayansa suka fada cikin wannan tekun sukayi nustso aciki
Shi kuma suka barshi a sama yana mai ci da wuta
Su kuma sai sukayita iyo suna ninkaya acikin tekun har saida sukayi nisa da inda yake sannan suka dago da kansu sama suka dawo gefen tekun
Suka fita daga cikinsa, koda fitowarsu sai suka sami guri daya dukkansu suka zauna suna masu jan dogon numfashi
Tsawon lokaci suna zaune suna faman kallon juna ba tareda daya yace uffan ba
Daga can sai sarki aryan ya dubi su walisa yace
Tabbas yanzu na mara imani da cewa babu abin bautawa da gaskiya face ubangijin musulunci
Domin wannan karfin da muka samu karfine wanda sihirin tsafi ba zai iya baka shi ba
Dukkanku kunga abubuwan da suka faru da idanunku
Dajin haka sai marfuza tace kwarai kuwa maganar ka gaskiyace
Tabbas ba don taimakonsa ba da tuni mun rasa rayuwar mu
Suna cikin wannan zancen ne sai walisa tace yanzu babu abindaya dace muyi face godiya ga ubangiji
Sannan ina tunasar daku cewa hanr yanzu zama bai samemu ba
Dolene mu tashi mu ci gaba da tafiya domin da alama bukatar mu tana daf da cika
Don haka ina so na tunasar daku cewa
aduk sanda muka tsinci kanmu cikin mawuyacin hali mu dinga tunawa da ambaton ubangiji
Da kuma neman taimako daga gareshi
Idan har munason mu sami nasara da gaggawa
Yanzu abinda ga kamata muyi shine mu tashi mu kama hanya don zaman cikin dajin nan bai dace damu ba
Tana cikin wannan maganane sai sarki aryan ya dubeta yace
Akwai abu guda daya wanda nakeson na tunatar daku
Da sauri marfuza tace menene wannan abu
Kawai sai sarki aryan yace yanzu shine lokacin da zamuyi sallar azahar
Yana gama fadin haka sai ya mike ya nufi bakin wannan tekun
Kawai ya tsugunna ya fara alwala cikin sauri su walisa suna suka tashi sukayi koyi dashi
Sannan ya shige gaba ya tada sallah su kuma suka biyoshi suka bishi jam'i
Suna idar da sallar sai suka tattara kayansu suka fara shirye shiryen ci gaba da tafiya
A sannan ne suka fara tunanin hanyar da zasu sami jirgin da zasu hau su ketare ta saman wannan tekun dashi
Abinda basu sani ba shine wannan takun duk duniya babu tekun da takaita hatsari bisa wannan dalilin ne yasa
Matafiya da kuma masunta suka daina alaka da wannan tekun don ceton rayukansu
Saida su walisa suka jima a wannan guri suna jiran jirgin dazaizo ya dauke su amma suka rasa domin ko alamar jirgi guda daya basu gani ba
Koda ganin haka sai marfuza ta basu shawarar kan su tsaya a wannan dajin su kera basu jirgin wanda zai daukesu duk su ukun
Nantake kuwa duk suka gamsu da shawararta suka bazama cikin daji suka dinga saro manyan bishiyoyi suna janyo su
Suna tarasu aguri guda har saida suka tara masu yawa
A sannan suka tuna cewa makaman yakinsu sun lalace
Don haka sai suka kunna wuta sosai sannan suka zura. Makaman nasu acikin wutar saida sukayi jajur sannan suka zarosu
Suka dinga sa guduma suna dukansu saida makaman sukayi tsini
Sannan suka dauko dutsen wuta suka dinga wasa makaman dashi har saida makaman sukayi kaifi irin wanda ake cewa gayawa jini
Na wuce
Saboda sufi jin dadin sassake bishiya dasu
Suna gama wasa makaman sai suka koma inda wadannan bishiyoyi suke suka fara aikin sassake su da dai dai da dai dai
Suna tarawa da kullewa har sai da suka tashi jirgin ruwa mai kwarin gaske wanda dukkansu zasu shiga cikin sa ba tareda sun matsuba
Kai hardama dakin kwanciya guda sukayi acikinsa
Suna gama kera wannan jirgin sai suka daureshi da jijiyoyin bishiyoyi suka dinga jansa
Tun yana kan kasa har saida suka janyeshi ya koma cikin tekun ya zauna daram babu alamar tambal tambal atare dashi
Kawai sai suka dinga kama wadannan jijiyoyin suka hau kan jirgin suka zauna daram
Shidai wannan jirgi ajikinsa akwai gurin matuka guda biyu daya abangaren hagu daya kuma a bangaren dama
Can gaban jirgin kuwa daki ne wanda mutum zai kwanta aciki
Asaman dakin kuma mazauni ne wanda aka ajiye kujerar itace a samansa wacce mutum zai zauna ya dinga kalle musu abinda yake gabansu
Koda suka gama shiga cikin wannan jirgi kawai sai gimbiya walisa da sarki aryan suka kama matukan jirgin guda biyu
Ita kuma jaruma marfuza saita karbi jakunkunan kayan guzurinsu ta shige dasu cikin wannan karamin dakin ta ajiye
Sannan ta fito ta hau saman jirgin ta tsaya domin ta fara aikin gane musu abubuwan dake gaban jirgin
Su kuma su sarki aryan sai suka kama aikin tuka jirgin
Sannu a hankali jirgin ya fara motsawa yana tafiya acikin tekun cikin gudu
Tun suna tafiya a gurinda bai da zurfi har jirgin ya nutse ya zauna daram
Yaci gaba da tafiya a saman ruwan,
Suna tafiyar suna hira abinsu ita kuwa marfuza ta zauna daram dam
Ta harde kafafunta asaman jirgin hannunta guda yana kan takobinta tana ta zare idanu da muzurai tare da kallon ko ina na cikin tekun gabas da yamma kudu da arewa tana nazarin tekun don tabbatar da tsaro
Tabbas jaruma marfuza ta cika jaruma domin ko kadan batasan tsoro ba
awannan lokaci ji take kamar idan gaba daya duniya ne zasu taru akanta
Ita kadaice zata iya gamawa dasu ba tareda ta nemi taimakon su gimbiya walisa ba

TAFIYAR KWANA NAWA ZASUYI KAFIN SU KETARE WANNAN TEKU?
SHIN WACCE IRIN MATSALA ZASU FUSKANTA ACIKINSA?
ME ZAI FARU IDAN YARIMA WALISU YASAN CEWA SUN KASHE ALJANI DARGATUL AMNAR?
DON JIN AMSOSHIN WADANNAN TAMBAYOYI SAI MU HADU A KASHI NA GABA
NA WANNAN KAYATACCEN LABARI MAI SUNA
HATSABIBAN SADAUKAI
DAGA NAKU HABIBULLAH KBR

LIKE, COMMENTS AND SHARE**************HATSABIBAN SADAUKAI

CI GABAN ZUBAR DA JIN

***********5 PART B

LBR

****************HABIBULLAH KBR

Lokacin da jaruma marfuza tabar su gimbiya walisa suna tukin jirgi ita kuma ta hau samansa ta zauna zaman dirshan
Tana ta kalle kalle da zare idanu kai kace neman wani abu takeyi
Kasancewar su sarki aryan suna da matukar zafin nama, juriya gami da karfin damtse
Sai gashi suna tuka jirgin cikin karfi da kuma karfin gudun gaske yana tafiya yana ratsawa ta cikin teku
Kai kace mutane masu yawa suke aikin tukinsa
Cikin kankanin lokaci jirgin nasu yayi nisa a cikin tekun yadda idan kana tsaye agefen tekun ba zaka iya hango jirgin ba
Saida sukayi tafiya mai nisan gaske sannan rana ta fadi duhun dare ya soma haskawa
Don haka sai suka hakura da tukin jirgin suka tsaya domin su huta kuma su ci abinci
Nan da nan kuwa sarki aryan da gimbiya walisa suka saki sandunan da suke sarrafa jirgin dashi
koda marfuza taga jirgin da suke ciki ya tsaya cak a saman ruwa baya gaba baya
Sai ta juyo baya don ganin abinda yake faruwa
Koda taga su sarki aryan sun saki matukan jirgin sai tayi dariya tace
Sannunku mazanen kwarai kunyi kokari fa yanzu abindaya kamata kawai shine ku zauna kuci abinci abinku
ni zan zauna naci gaba da

Please Login or Register in order to submit comment