Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

Ibrahima don ya fi Sanata Abdulkarim sakin hannu.

****
An gama komai na shirin hijirar Ambasada Hamza Atiku Dakata, da iyalinsa kasar Saudiyyah. Washegari suka wuto gida Kano. Babban gidan ya kacame da murnar zuwansu. Ga shi ya kama lahadi ce, su Luba da yaransu duk sun zo kamar yadda suka saba duk lahadin karshen mako. Uncle Idris ma ya zo daga Maiduguri yana (housemanship) a asibitin Malam. Iyalin Sanata Abdulkarim ne kawai babu suna Abuja kuma dama dai akwai matsala ta fanninsa domin abin a zahiri yake, babu iyalin da zai yiwu ace babu baraka ko yaya take a cikin su, hakika Sanata Abdulkarim Abdullahi Dakata, bai yi sa’ar mata ba. Ko kusa Anty Zuwaira (matarsa) ba ta so ya rabi danginsa ko ya wahalta musu, ba kuma ta so suma su rabe shi. Da wuya ka gansu a Kano sai dai ya yiwo waya ko aike, kowa a cikin zuri’ar ya kwana da sanin wannan.
‘Ya’yansa ba su saba da ‘yan uwansa ba, sai na mamarsu da yake ita ma diyar wani kusa ce a Abuja. Ta kan dan yi zumuncin da Hajiya Maryam tunda ita ma mijinta mai matsayi ne kamar su koma fiye da su. Akwai sanayya tsakanin yaranta uku Farhan, Ramadhan da Sha’aban da su Abdul’azeez, amma ban da na sauran dangi da ke Kano.
Gidan ya cika sosai da zuri’ar Malam Abdullahi mazansu da matansu da ‘ya’yansu. Adda Hafsatu da mai aikin gidan nata zirga-zirga tsakanin madafi (kicin) da tsakar gida don hada abin da za a ci da rana. Kuma da ma kafin su zo labarin abin alkhairin da ya samu Dr. Hamza ya riga su isa. Don haka ana zaune ne a babban falon marigayi ana sallama da juna, da hirar zumunci. Dr. Hamza ke tambayar kawunsa Idris (autan su Baffa Atiku) wanda malam Abdullahi ya haifa a shekarun girmansa matakin karatunsa, ya sanar da shi yana (housemanship) ne yanzun a nan Kano. Ya koma kan su Lubabatu kannen Hajiya Maryam, Luba koyarwa ta ke a karamar sakandire da yake NCE kadai gare ta. Ya ba ta shawarar ya kamata ta tafi karo karatu (in-service), haka nan zai dauki nauyin karatun. Luba ta ce, insha Allah zatayi amfani da shawarar sa. Furairah ba ta aiki da yake maigidanta ba ya so. Dr. Hamza ya dade da ba ta jari tana kasuwanci yanzun ma kara mata ya yi don ta fadada kasuwancin nata. Murja na yin (masters) ta ce a barta ta kammala kafin a nema mata aikin ba ta son hada taura biyu a baka. Ya gaya wa Gyatumarsa Inna Ramatu da surakuwarsa kuma uwarsa Adda Hafsatu su zamo cikin shiri tunda duk suna da (passport) na Hajj da Umrah da yake kai su duk shekara, da sun yi (settling) a sabon muhallinsu zai aiko musu su tafi su ga sabon matsugunninsu.
Da dare a dakin Adda Hafsatu, ita da babbar diyarta Hajiya Maryam suna hirar sallama irin ta Da da mahaifi, Adda ke tambayar dan gaban goshinta, wato Abdul’azeez ba ta ganshi tare da su ba. Hajiya Maryam ta fada mata duk yadda suka yi da shi, da amincewa da Babansa ya yi ya maida shi makarantarsu ta kwana (Regent, Abuja) kafin su taho Kano. Adda ta yi dariya, ta ce, “Dan baiwa kenan, mai ra’ayi da akida ba irin na kowa ba kamar Kakansa. Ni ina ki ka samo sabuwar mai aiki ne, ina Jamilar? Kyakkyawa da ita kamar ba mai aiki ba. Da ganinta bafullatana ce. Ke kam ba kya gajiya da canza masu aiki”.
“Adda, Jamila ta yi aure. Kuma Adda masu aiki ba sa zama ne, kowacce sai an saba da ita, sai ta ce ga uzurinta za ta koma gida”.
“Ita wannan din tare za ku tafi har Jeddan?”
“Eh Adda, gara na dau ta gida da in je can in neman mai aiki Takari, da yawansu basu da amana kuma yawancinsu ba mutanen kirki bane kuma basu da takardar shaidar zama (igama)”.
“Har yanzu kina nan da halinki na saurin yarda da mutane Maryama? Da za ki dauki wadda ba ki san asalinta ba ki tafi da ita inda ke ma ba ki da kowa? Ba kya fada a nema miki cikin dangi tunda babu wanda zai samu wannan damar ya ce a’ah?”
Hajiya Maryam ta girgiza kai da sauri tareda gyara zama, “Adda, bana so jinina su yi min aiki, sabida hali irin na dan Adam. Dan uwanka in ya zama mai aikinka ba ka da sirri a dangi, kuma ko me za ka yi masa ba zai gode ba. Bar ni dai da baren. Ki kwantar da hankalinki a kan Habiba Adda. Wallahi haka nan na ji ta kwanta mani a rai tun ganina da ita na farko. Ba ki ga yadda ta ke kula da yara ba bilhaqqi ga zafin nama da tsafta”.
Adda ta gaji da koda Habiba da Maryam ke ta yi ta tare ta da cewa, “Allah ya zaunar da ku lafiya da juna, Ya kade sharri, Ya hada ku da alherin da ke tare da ita”.
“Ameen, da addu’o’inku gare mu Adda ba za’a cutar da mu ba,1- insha Allahu”.
Adda ta janyo katuwar (Ghana Must Go) ta ajiye mata a gabanta. Tanadin tafiya ne ta yi mata na kayan girki, yaji, daddawa, kubewa busasshiya, busasshen kifi, kayan kamshi na gargajiya, kuka da sauransu. Ba karamin dadi Hajiya Maryam ta ji ba, wani abu sai mahaifiya. Ta yi ta godiya tana kara son Addar tata a zuciyarta.
Washegari suka kamo hanyar Abuja cike da kewar gida, iyaye da ‘yan uwansu.
Ranar Asabar, biyu ga watan biyu, na shekarar alif dari tara da casa’in da shidda (2/2/1996). Ambassador Dr. Hamza Atiku Dakata da iyalinsa suka daga kasar Saudiyyah. Ko da jirgi ya sauke su a birnin Jeddah ba su shiga gidansu ba, wucewa suka yi Madinah suka fara aikin umrah. Habiba ta kasa gasgata abin da idanunta suke gane mata, wai yau ita ce a kabarin Manzo sallallahu alaihi wasallam. Ko da wannan ta tsira kadai ta san Allah ya fara yi mata sakayyah ne akan abin da ya rabo ta da gida. Ta faki idon Hajiya Maryam ta share hawayen da suka zubo mata data tuno kananan ‘ya’yanta. Kwanansu biyar a Madinah suka nufo Makkah suka cika umararsu, sannan suka wuce Jeddah inda gidansu yake a unguwar (Albasatin). Ambasada ya shiga sabon ofishinsa a ranar Litinin.

****
Aikin Habiba a gidan Ambasada kullum shi ne, kafin Daddy da Hajiya su fito ta shirya yara shirin zuwa makaranta, sunan makarantar da suke zuwa (Hala International School). Direba ya debe su zuwa makaranta har Halim shi ma an sanya shi ajin rainon yara. Daga nan ta dora wa Hajiya sanwar safe kafin ta fito ta karasa, ta share ko’ina na kayataccen gidan duk da yana da girma, Habiba ba ta raki. In ta tashi da asuba ba ta komawa barci, ta yi (mopping) ko’ina, in Mama ta sakko kasa ta kama mata su hada (breakfast) na Daddy, na yaran ita Habiban ce ke yi. Ta kwashe ta jera a tebirin cin abinci, ta gyara dakin yara ta tattare kayansu da suka wargaza. Ta wanke duka bayin gidan (toilet, ban da na Daddy, wannan Mammah ce ke yi da kanta. Sannan ne za ta wuce dakinta ta yi wanka ta kintsa kafin Mama da Daddy su gama karyawa ya tafi office.
Daga Daddy har ‘ya’yansa da mota uku suke amfani, direbansa daban na yara daban, wata babbar (Limousine) ce baka wuluk ta kai yaran makaranta, shikuma wadda yake shiga karama ce (Hyundai). Bayan ita akwai babbar cherokee jeep duk na hawansa ne shi kadai. Yaran na riga shi fita kullum.
Basu rufa watanni uku ba Hajiya Maryam ma ta shiga makarantar islamiyyah ta karfe sha dayan rana zuwa azahar, don haka ya zamo duk al’ummar gidan ba sa zama sai Habiba.
Cikin watanni hudu sai ga Habiba ta soma canzawa, sakamakon cima mai kyau da muhalli mai kyau. Kyawunta na fulanin usli ya bayyana muraran, duk da ba kwalliya ta ke ba, kullum cikin bakaken jallabiyoyi ta ke, wadanda Mammah ke sai musu ita da Habiban don fita waje da zuwa Harami. Duk juma’ah suke shiga harami su yi Dawafi da sallar juma’ah, sai yamma lis suke dawowa Jeddah.
Watanninsu hudu kenan a Saudiyyah, Habiba ta dade tana samun wasu sauyuka a tattare da ita. Amma jarumtarta ba ta bari ko ya ya Mammah ta ga gazawarta ba. Inna Ramatu da Adda Hafsatu sun zo sun yi sati biyu sun shiga Makka da Madinah sun yi umrah sun koma.
Yawan kasala, zazzabin dare, da tashin zuciya suke damun Habiba. In gari ya waye kuma sai ta yi garau. Duk da haka ba ta gaza komai a ayyukanta ba, tana daurewa tana yi don ba za ta iya barin Mammah da aiki ba, kuma in ta hadiyi (Paracetamol) da suke da shi a kicin tana samun karfin jikinta.
Yau da gobe Habiba ta gane cikin jikinta ne ke girma. Wanda ta dade da manta yana tare da ita. Don dai ita doguwa ce, shiyasa bai fito sosai ba. Ba ta yi wani mamaki ba, don tun a gida ta san da hakan, soyayyar abin da ke cikin nata ya lullube ta. Ta kara kaimi wajen lullube jikinta ruf da manyan bakaken abayoyinta. Wani lokacin Hajiya Maryam kan ce da ita ta dinga cirewa tana shan iska mana, sai in za su fita. Ba ta cewa komai sai dai kawai ta yi mumushi.
Haka Habiba ta ci gaba da rainon cikinta har tsayin watanni takwas wanda yabi tsayin jikinta da fadin jikinta ya yi kwanciyarsa ba tare da sanin uwargijiyarta ba.
****

Abdul’azeez ne ya zo hutu, zuwansa na uku kenan tun dawowarsu Jeddah, don haka gaba daya iyayen da ‘ya’yansu cikin farin ciki suke. Duk da shan kamshinsa yana son Habiba, sabida yadda ta ke haba-haba da shi idan ya zo. Duk wata hidimarsa a wuyanta take, kulawar data ke masa daban ce da wadda take yiwa kowa a gidan, yaron ya shiga ranta sabida kyawunsa da sanyin halinsa. Shima AbdulAziz yana son Habiba ne saboda a cewarsa yana son girkinta, ta iya girki. Sannan ita din mai tsafa ce yadda yake so fiye da duk masu aikin da Mammah ke yi.
A kicin Abdul’azeez ya tadda Habiba tana aikin abincin rana. Lokacin Mammah tana makaranta, iyakacin shi bakin kofa ya dube ta da murmushi a ransa yana cewa, ta yi kiba, ta zama katuwa kamar ana hura ta.
“Anty Habiba abin nan da ki ka yi wa Mammah jiya nake so in kara ci”. Ya fada da tattausar muryarsa.
Habiba ta juyo da murmushi, “Dan gidana wanne a ciki? Jiya girki uku na yi wa Mammah, akwai dan wake, akwai burabusko akwai kuma faten acca”.
Ya dan kanne ido alamar tunani, har ya ba ta dariya, “Mai ruwa-ruwan, ba mai duwatsun ba”.
Habiba ta yi dariya ta ce, “Faten acca ba burabusko ba?”
Ya ce, “Ehh, ba mai kwaya-kwayan ba”.
Abdul’azeez ba zai daina ba ta dariya ba, ta sake murmusawa,
“Ba ni minti goma sha biyar toh”.
Ya shigo kicin din ya ja kujera a gefe ya zauna,
“Bari to in jira ki a nan, kina yi kina yi min hirar garinku, ina son labarin kauye. Duk masu aikin Mammah daga kauye suke, suna yi min tatsuniya irin ta garinsu”.
Murmushin fuskar Habiba ya dauke nan take, kafin ta ce.
“Ni ba daga kauye nake ba Abdul’azeez, daga cikin birni nake. Halin rayuwa ya sa na zabi in yi nisa da gida”.
Abdul’azeez ya tattara hankalinsa ya bai wa Habiba,
“Na sha yin tunanin ba daga kauye ki ke ba Anty Habiba. Sam ba ki yi kama da kauyawa ba, sannan ba ki da kauyanci. Anty Habiba ya sunan garinku?”
Haka kawai ranta ke son yaron, saboda yaro ne mai tarin baiwar hankali da nutsuwa. Ba shi da sakin jiki da mutane, amma ita yana sonta. Alkawari ta yi wa zuciyarta babu wanda za ta fada wa daga inda ta fito ko abin da ya rabo ta da gida, don kada a ce za a maida ita. Yin nisanta da mijinta da ‘ya’yanta shi ne babban abin da ya fi mata kwanciyar hankali. Yanzu ji ta ke kamar tana rayuwa a kan gajimare don dadi da kwanciyar hankali, tunda ta rabu dasu, duk da lokaci-lokaci tana tuna su ta ji kewarsu. Wani dan guntun hawaye ya tsattsafo cikin fararen idanunta, Abdulaziz na lura da ita ya kara tattara hankalinsa a kanta,
“Ki yi hakuri in don na ce ya sunan garinku ne ki ke kuka Anti Habiba....... insha Allah bazan kara tambayar ki ba”.
Ta juyo ta dube shi cikin girgiza kai, “Sunan garinmu JIMETA cikin jihar Adamawa”.
“To Anty Habiba ina mijinki? Ba ki da ‘ya’ya?”
Ta tsura wa AbdulAziz ido, kaunar yaron na shiga ranta. Shi ne mutum na farko da ya tambaye ta wani abu da ya shafi rayuwarta tun fitowarta gida. Duk wadanda ta hadu da su a gaba suna duba amfanin da za ta yi musu ne kawai, ba ruwansu da (personal life) dinta. Ta yi masa murmushi, ta ce, “Abdul’aziz duk ina da su”.
Cikin mamaki ya ce,
“Kuma mijinki ya yarda ki tafi aikatau ki barshi da yaran?”
Ta kura wa yaron ido cikin tunanin abin da za ta ce masa, amma ta rasa. Sai idanu da ta zuba masa, irin yaran nan ne masu son bin kwakkwafin abu da ake kira (inquisitive), wayonsa da nisan tunaninsa ya wuce shekarunsa. Da ya tabbatar Habiba ba ta da amsar da za ta ba shi, sai ya ce, “Ya’yanki nawa ne Anty Habiba?”
Yatsunta uku ta daga masa, wato su uku ne. Ba ta kara ce masa komai ba, sai hawaye da ta ke sharewa.
Hankalinsa ne ya gaya masa cewa ya kyale ta, ga dukkan alamu ba ta son zancen mijin da ‘ya’yan da yake yi mata kamar yana yi mata fami a kan wani gyambo ne. Mikewa ya yi ya nufi hanyar fita daga madafin, ita kuma ta ce,
“Ai ya kusa nuna faten, bari in juye maka”.
Ya ce, “Miko min library, wani littafi zan duba ina da ‘holiday assignment”.
Da haka ya karasa ficewa daga kicin din yana jin tausayinta, ta ko’ina ba ta yi kama da ‘yan aiki ba, and she has her own family (tana da nata iyalin), amma ta zabi ta bauta wa wasu iyalin ta bar nata a kan dalilin da ya tabbata ba kudi ba ne (talauci) kamar sauran masu aikin Mammah.
Habiba ta juye kyakkyawan faten accan da ta kammala a karamin (foodflask) ta hada da plate da cokali ta nufi dakin karatun yaran gidan, wanda ke kan wata matattakala guda uku a cikin babban falo. Sai an bi ta kan matattakalar ne za a shiga (study room) din. Ta hau matattakala ta farko ta hau ta biyu, santsin (marbles) da silifan kafarta dan madina ya kwashe ta, ji ka ke timm! Ta yi wata mummunar faduwa rub-da-ciki a kan cikinta. Ta saki wata irin kara mai amo, wadda ta ratsa har kwanyar Abdul’azeez da ke zakulo littattafai daga kan kantarsu.
Da gudu ya jefar da littafin ya nufo falon. Habiba ce ta fadi a kasa ga ta nan tana murkususu male-male cikin jini. Fate-faten ya watse a kasa, plate din tangaran din ya tarwatse ba abin da yake ambato saboda gigicewa sai “Subhnallah, zamewa ki ka yi?”
Babban abin da ya ruda shi wannan jinin da ke malelekuwa daga kafafunta. Ya rasa me zai yi ya taimaka mata, ba a kiran Mammah a waya in tana islamiyya, bari kawai ya kira asibiti kai tsaye, don Daddy ma ba ya gari yana garin ‘ABHA’.
Kan wayar falo ya nufa da sauri ya duba ‘code’ na kiran (Accident & Emergency) na asibitin su ya kira, a takaice ya yi musu bayani suka ce suna tafe da ambulance.
Isowar jiniyar motar asibitin gate din gidan ya yi daidai da dawowar Mammah, direba ya dauko ta daga islamiyya ta ga an fito da mutum kwance bisa gadon daukar marasa lafiya, jini kaca-kaca an shiga ambulance an ja motar an tafi. A sukwane ta fada cikin gidan suka gabza karo da danta Abdul’azeez shi ma a firgicen yake, gabadaya ya gigice ya kamata ya rukunkume ya ce, “Mammah Habiba ce, faduwa ta yi”.
Kamo hannunsa ta yi suka fito, direban nasu ba bahaushe ba ne, dan Sudan ne sunanshi Salah, motar suka fada Mammah ta ce da Salah su bi bayan ambulance din.

Likitoci ne rankatakaf a kan Habiba, abinki da kasar da aka san darajar rayuwar dan Adam fiye da ko’ina. Mammah da Abdul’azeez na bakin kofar dakin da aka shigar da Habiba suna ta safah da marwah, bakin Hajiya Maryam dauke da addu’o’i iri-iri. Tana rokon Allah ya tada kafadun Habiba, ta rabo baiwar Allah da kasar haihuwarta ba tare da ta san komai a kanta ba, ko inda ta fito. Allah ya gani duk masu aikin da ta ke yi ta san asalinsu da yawansu har kauyensu tana zuwa, amma Habiba ta karbe ta (while she was desperate) a neman mai aikin ba tare da wani bincike ba, kuma tunda suka zo ba ta bincike ta a kan komai nata ba, idan ta mutu a ina za ta nemo danginta? Sannan me za ta ce musu ya kashe ta?
Hawayen tausayi da tashin hankali ya zubo mata, ta kai bakin hijabinta tana sharewa.
Abdul’azeez ya yi tagumi a zaune kan wata kujera ta silver. Rokon Allah yake cikin zuciyarsa, Ya sa ba wani mummunan lahani ya samu Habiba a dalilin yi masa girki ba. Ya dauki alhakin hakan kacokam ya dora a kansa. Tana cikin aikinta yazo ya sata aiki. Duk da haka bai yi hawaye kamar Mammah ba, idanunsa ne suka kada suka yi jazir, hankalinsa na kara tashi in ya tuna sanda ta ce masa ai ta gama, ya zauna ya ci a kicin din, ya ce shi a’ah sai dai a biyo shi da shi library.
Wajen mintuna talatin suka kwashe a haka kafin daya daga likitocin ta fito, likiciyar Balarabiya ce mutuniyar Egypt, ta ce da Mamma ta biyo ta ofishinta. Mammah jiki na rawa ta bi ta.
Wayar Mamma na hannun Abdul’azeez ya ga shigowar kiran Daddy. Da sauri ya amsa, ya ce, “Daddy ka dawo?”
Ya ce, “A’ah Azeez ina bisa hanyar dawowar, ina Mamarku ba ni ita, jikina na ba ni wani abu na faruwa shi ya sa na kira ta”.
Abdul’azeez ya ce, “Eh Daddy, muna asibiti ma yanzun Doctor ta yi kiranta”.
“Waye ba lafiya?” Ambasador ya furta cikin faduwar gaba, sannan cikin sanyin murya.
Abdul’azeez ya gaya masa duk abin da ya faru, a karshe cikin rawar murya ya ce, “Ni na jawo ko Daddy? Da ban sa ta aikin ba da ba ta fadi har ta ji ciwo jini na zuba daga jikinta ba ko Daddy?”
Daddy ya ce, “Cool down my son, kwantar da hankalinka ba kai ka jawo ba, tsautsayi ne wanda ba ya wuce ranarsa. Ko ba ka sa ta girki ba in Allah ya yi za ta fadi a yau ta ji ciwo za ta fadi ne. So kwantar da hankalinka za ta warware insha Allahu, kai wa Maman wayar har ofishin likitar a gaya min ko me ke nan”.
Hajiya Maryam, uwargidan Ambassada Hamza Dakata na can ta daskare a zaune ta zama mutum-mutuma a kujerar da ke fuskantar likitar mata Dr. Unaisa Jamaal da takardu a hannu. Ta fi yarda da ba daidai likitocin suka dubo ba dai, wai Habiba za a cire wa baby (CS) dan wata takwas saboda ba za ta iya haihuwa da kanta ba, ta zubda jini, sannan ta bugu ta inda har mahaifarta ta samu lahani, idan kuma ba a gaggauta raba ta da babyn ba za a iya rasa su bakidayansu. Rayuwarsu cikin hatsari ta ke.
“Ciki! ?”
Hajiya Maryam ta tambaya tana zaro wa likiciyar manyan fararen firgitattun idanunta.
Dr. Unaisa ta gyada kai cikin tabbatar mata.
“Kuma bai kai lokacin haihuwa ba, za mu cire shi ne don tserar da rayuwarta da ta abin da ta haifa. Ku yi gaggawar sanya hannu don a shiga da ita dakin tiyata.
Tsananin rudewa Hajiya Maryam ta gama fita hayyacinta, shin da ma da ciki ta dauko Habiba, ko a nan Jeddah ta samu abinta? Tsananin rudewa ya sa ta kasa lissafa iya watannin da ta yi da Habiban. Yau watansu shida tare a birnin Jeddah in haka ne Habiba da abinta ta zo yana dan watanni biyu.
Jikinta yana karkarwa ta zura hannu a jaka don dauko wayarta ta kira Ambasada, tsabar rudewa ta ma manta wayar na hannun Abdul’azeez. Daidai lokacin yaron ya murdo kofar bayan likita ta bashi iznin shigowa ya mika mata wayar. Ta kira Ambassador da sauri, bai bata lokaci ba ya amsa don a lokacin ya gama magana da Abdul’azeez, wayar tana hannunsa.
“Daddy zo ka sa hannu don Allah a yi wa Habiba tiyata, baby za a cire mata. Wai ashe duk tsawon lokacin nan Habiba ciki ne da ita ba ta fada min ba, ni kuma ban taba ganewa ba, ni wawuyar ina ce Daddy?”
Dariya Ambassada ya yi, “Ah toh! Wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho. Garin kwashe-kwashenki watarana fin haka za ki kwaso. Ina cikin Jeddah ku ba ni minti goma zan karaso, ba ni likitan”.
Ta mika wa Dr. Unaisa wayarta jikinta yana ta mar-mar,
“Ungo maigidana zai yi magana da ke”.
Ta karba suka yi magana kadan, ta mayar mata. Mammah ta kara a kunnenta, Daddy ya ce, “Ke da ki ka kwaso abinki sai ki sa hannu, sun ce ba za su iya jirana ba, babu lokaci”. Ya kashe wayarsa.
Jiki na rawa ta karbi takardun ta rattaba hannu suka mike tare ita da likitar suka fito. Nan inda ta bar Azeez ta tadda shi suka hadu suka zauna jigum-jigum ta kasa gaya masa ko me ke akwai. Ita kuma Doctor ta wuce su suka shigar da Habiba dakin tiyata.
****
An dauki awanni biyu kenan, daidai lokacin da aka kira sallar la’asar. A lokacin ne Abdul’azeez ya tuna ko sallar azahar ba su yi ba shi da Mammah. Yana mamakin yanayin da ya ga Mammah a ciki na gigita fiye da sanda suka zo tun lokacin da likita ta kira ta ofishinta. Ya zarce na ace ciwon Habiba ne kadai ya sanya ta a wannan hali.
“Mammah mu je mu yi sallah”. Ya fada har sau biyu, kafin Hajiya Maryam ta ji me yake cewa, da yake tana cikin lalura sai ta ce, “Je ka kayi, zan zo daga baya”.
Ya mike ya bar reception din zuwa masallacin cikin asibitin. Tashinsa da fitarsa ya yi daidai da fitowar likitoci biyu daga dakin da aka shigar da Habiba daya daga cikinsu rungume da jariri sai kyanyara kuka yake nannade cikin shawul fari kal, wanda ta san ita dai ba ita ta ba su ba. Mikewa ta yi tsaye cikin hailala ta tare su tun kamin su iso ta mika hannu ta karbi jaririn da ba ta san mace ne ko namiji ba. Ta maida dubanta ga likitar cikin zakuwa, “Habiban fa?”
Sai a lokacin ta lura da fuskokinsu dukkaninsu babu mai walwala.
“We are sorry...”. Dr. Unaisa ta fada cikin turanci.
Ba tare da damuwa da yadda Hajiya Maryam ta fiddo ido cikin dimaucewa ba ta ci gaba da yi mata bayani cikin lallashi.
“Mun yi duk iya kokarinmu mu yi saving dinta Allah bai ba mu nasara ba. Ta zubar da jini da yawa, kuma tana da hawan jinin da ba ya samun kulawa, ta hadu da jijjiga (pre-eclampsia) hakoranta sun datse harshenta da muka sa mata ruwan nakuda ba tare da sanin cewa tana da hawan jini ba (induced labour). Dole muka yi fida don ceton ranta bama ta abinda ke cikinta ba, ko kafin mu gama, ta cika”.
Hawaye suka ziraro daga idanun Mammah masu zafi na kewa, sabo, tausayi da kauna. Ta rungume jaririn tsam a kirjinta. Daidai lokacin da Abdul’azeez da Daddynsa suka shigo, Dr. Unaisa ta ce ta ba su jaririn za su binciki lafiyarsa don ba ya numfashi yadda

Please Login or Register in order to submit comment