Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ke da kayan aiki, Idris taimakon farko (first aid) yake yi muku don Allah ki amince mu je”.
Lallashin duniya Dr. Hamza ya yi, amma baiwar Allahn nan ta ki. Allahu akbar! Kwanansu uku a Kano Allah ya karbi ran Inna Ramatu, ranar litinin a kan sallayarta, bayan ta idar da sallar isha’i tana lazumi.
Adda ce ta shigo mata da abincin darenta, sai ta yi tsammanin bacci ne ya dauke ta a kan sallayar. Ta ajiye abincin ta matsa ta dauko filo don ta gyara mata kwanciya, nan ta tarar Inna Allah ya amshi abinSa.
Salatin Adda cikin fadin, “Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Shi ya janyo hankalin jama’ar gidan da ke tsakar gida an shimfida manyan tabarmi suna jam’in sallar isha, wadda Daddy ke limanta.
Fadin irin gigicewar da Ambasada hamza ya yi na rashin nagartacciyar mahaifiyarsa abin ba a cewa komai, sai dai a yi gumm! Zuciyar maza ta girgiza ta azabtu. Ba abin da yake so a duniya in ka cire Baffa da iyalinsa kamar tsohuwar nan tasa. Inna Ramatu uwa ce abin koyi, abar alfahari a gare shi. Ba ta haifi kowa ba sai shi, don haka ba karamin so ta ke yi masa ba. Kamar wani abokinta haka ta dauke shi. Duk damuwar da yake ciki da ya yi tozali da Innar nan ta yi masa murmushin nan nata, zai neme ta ya rasa. Bare in ya zauna a gabanta tana yi masa nasihohi a kan rayuwa da yadda ake maganin kalubalenta don samun nasara cikin rayuwa. Inna kan ce, “Hamza kada ka bari duniya da daukakar da Allah ya ba ka su sa ka wulakanta dan Adam, ko ya ya yake wallahi watarana zai yi maka rana. Ka ji tsoron Allah, ka rike sallah, ka taimaki na kasa da kai. Ka rike addininka su ne sirrin zama lafiya da cimma nasarar komai a rayuwa”.
Gaskiya tun bayan rasuwar kakansa Malam Abdullahi Dakata ba a kara yi masa mutuwa ba. Don haka mutuwar Inna ta doke shi yadda ba’a zato. Da safe aka yi janazarta, lokacin da suka kama gawar ta shi da mahaifinsa suka sa a kabari, sai ya yanke jiki ya fadi.
Haka Baffa Atiku ya taro shi, aka kwashe shi aka sa a mota aka yi asibiti da shi. Ya sha dirif ba adadi, kwanansa uku sannan ya dawo hayyacinsa. Dakin asibitin cika yake makil da ‘yan uwansa, ‘ya’ya da iyaye, duk wanda ya zo wucewa sai ya tabbatar wannan majinyacin dan dangi ne. Ko da ya dawo gida ranar sadakar uku ya zauna wajen karbar gaisuwa ba shi da kuzari, tsoron duniya yake da abin da ke cikinta. Ya yarda ba komi ba ce komin daukakar da Allah ya yi maka, rana daya za ka fadi, kuma ba ka san ranar ba, ka je ka girbi abin da ka shuka.
Ya kan tuno ‘memories’ na rayuwarsa da mahaifiyarsa da yadda ta yi ta hidima da shi tun yana yaro, ya samu gatan uwa har girmansa. Wani bai samu ko nononta ya sha ba, hakika gatan UWA ya fi komai dadi ga dan adam a duniya.
Gabansa ya yi wata mummunar faduwa da wata fuska ta zo ta gilma ta gabansa. A sanda yake zaune yana wannan tunanin, ba wata ba ce yarinyar gidansa ce Suhaana (Hafsat) ta wuce ta gabansa ba tare da ta kula da shi ba, kasancewar ba shi kadai ba ne zaune a kan katuwar tabarmar da aka shimfida ba a kofar gidansu, shi da abokansa ne biyu da suka zo masa ta’aziyya daga Abuja, Ambassadan Najeriya a kasar Senegal Dr. Yahya Garba, da Ministan huldar kasuwanci da kamfanoni na kasa baki daya (minister of commerce and industry) John Akure, a gefe kawunsa Minister Abdulkarim Dakata ne da nashi jama’an suna ta karbar gaisuwa.
Ido ya bi ta da shi har ta tsaya a inda aka aike ta, wata (kiosk) ce nan kusa da su mai fentin gidan wayar MTN (yellow), da alama shagon waya ne. Ta mika kudi aka ba ta katin waya na dubu da dari biyar ta juyo. Fuskar uwarta ta gilma masa saboda yadda suke bala’in kama, hatta tafiyarsu iri daya ce don yakan ganta a kai-akai in tana hidima da yaransa a falo ko tana shirya abinci a (dining) kafin Allah ya dau ranta.
Ya hanga ya duba a fadin wajen nan duka ‘yan uwansa ne na jini, da aminan arziki. Ita wannan yarinyar ba ta da ko mutum daya da za ta nuna ta ce nata ne, ba ta da wanda za ta yi tinkaho da shi a duniya da sunan ‘IDENTITY’ dinta. Ya hana a bata nono, ga shi rai da alkawari, Allah ya raya ta har ta soma balaga. Kalmar ‘sannu’ wannan ba ta taba hada shi da ita ba alhalin ta rayu a gidansa cikin iyalinsa tsayin shekaru goma sha uku.
Anya abin da yake yi a kan marainiyar Allahn nan Allah ba zai tambaye shi ba? A kan wata akida ta kafurai wadanda suka samar da ilimin BOKO? Mahaifinsa ya ba shi ilimin addini yadda ya kamata, mahaifiyarsa ta hore shi da zama mutum mai tausayi, da jin kan na kasa da shi ba tare da tunanin abin da gobe za ta haifar ba, ko abin da za a saka masa da shi ba. Ya tuno ayoyi na alqur’ani mai tsarki da suka yi umarni da babbar murya da a kyautata wa maraya.
‘Wa ammal yatima falaa taqhar’ (DHUHA; 9).
‘Wa yas’alunaka anil yatamaa, qul islahul lahum khair, fa’in tukhaalidu hum fa ikhwanikum.... Wallahu ya’alamul mufsidu minal muslih, walau sha’Allahu la’a’anatakum, innallaha azizun hakim (Baqrah; 220)
‘Wa’abudullah walaa tushriku bihi shai’an wa bil walidaini ihsanan, wa bi zilqurbaa wal yataamaa wal masaakin...” Har zuwa karshen ayar (Nisa’i; 36).
A karshen ayar Ubangiji subhanahu wata’ala ya kara da cewa.
“Innallaha laa ya hibbu kulla mukhtalin fakhoor”. Fassara;

- “Amma maraya kada ku cutar dashi/cinye gadonsa”
- Suna tambayar ka (Yaa Muhammadu) akan lamarin maraya, ka fada musu cewa abin da Allah yake umarni shine kyautata musu, idan kunyi cudanya dasu to ‘yan uwanku ne. Allah ya san mai gyarawa daga mai batawa a cikinku,da Allah ya so da ya shiryar da ku. Hakika Allah mai iko ne mai hikima cikin lamuransa.
- Ku bautawa allah shi kadai kada kuyi shirka da shi, ku kyautatawa iyayenku da ma’abota kusancin zumunci, da marayu da miskinai da makotan ku na gidaje da matafiyi da kwarkwarorinku/bayinku. Hakika Allah baya kaunar wanda yake marowaci mai fariya.

Tunaninsa bai gushe ba ya ci gaba da tuna masa yadda ya wanzu yana kuntatawa maidakinsa ‘yar uwarsa, abar kaunarsa, matar rufin asirinsa don kawai ta yi jihadin yin ceton rai don Allah da neman sakamako a wurin Ubangiji. Ya muzguna musu tsayin shekaru goma sha uku ba tare da sun yi masa laifin komai ba, ba tare da zaman yarinyar tare da su ya rage shi da komai ba. Zai iya rantsewa tun daga ranar da yarinyar nan ta shigo gidansa yake ganin albarka da ci gaba iri-iri a rayuwarsa. Maryam ko uwarta ba ta taba gaya wa cuzgunawar da yake yi mata a kan yarinyar nan ba, balle tashi uwar har Allah ya dauki ranta...
Hawaye masu dumi suka biyo idanun Ambasada Hamza, bai damu da ya kai hannu ya share ba, haka ya barsu suna ta malala a kan kundukukinsa. Abokan nasa suka ci gaba da ba shi baki, ba su san kuka biyu yake yi ba, kukan rashin mahaifiya da kukan nadama. Rayuwa kenan.
Hafsatu ba ta san bidirin da Daddy ke yi da zuciya da kwakwalwarsa ba, ta sayo wa Mammah katin wayar da ta aike ta ta kamo hanyar dawowa, kanta na sunkuye ta ke tafiya don ba za ta iya daga ido ta dubi taron mazan nan da ke zazzaune a kofar gida ba. Kamar an ce da ita ‘dago kanki’ gab da za ta shiga gida ta dan daga kai saboda jikinta ya ba ta ana kallonta sosai, ai kuwa karaf sai idanunta cikin na Daddy. Ta ganshi yana shatatar hawaye kamar karamin yaro suka yi ido hudu da shi. Tuni ta gigice ta ci uban tuntube da wani dutse dake gefe ta fadi kiff! A kasa. Don ta tsammaci a cikin taron mutanen nan balbale ta zai yi da bala’in da ya saba.
Ji ta yi an sa hannu biyu an dago ta. Ta ji zafin faduwar sosai da sosai, gwiwoyinta duk sun kukkuje lebenta ya fashe jini ya wanke bakin. Ta cira ido a sannu cikin dauriya ta dubi wanda ya daga ta; Hamza Atiku Dakata ne.
“Wace irin tafiya ki ke yi haka Adda? Ba kya kallon abin da ke gabanki? Adda in don ni ki ka rude haka don Allah ki yi hakuri, kar ki sake firgita in kin gan ni, ba dodo ba ne ni, BABANKI ne”.
Hafsat-Suhaana, ba abinda ta iya yi banda ta runtse idanunta, mafarki ne kawai ire-iren mafarkan da ta saba yi a kan Daddyn, saboda yadda ta sa damuwa da lamarinsa a ranta. Ta ki bude idon don ba ta so ta farka daga wannan daddadan mafarki. Daddy ya sa hannu ya dauko hankicinsa daga aljihu fari tas ya shiga goge jinin da ke zuba daga bakinta. Tuni mutane wajen biyar suka taso suka isko su cikin girmamawa wani likita abokin Uncle Idris ya kama hannunta ya rusuna ya ce da Daddy zai tafi da ita asibiti, ya koma ya zauna ba komai.
Dr. Isah ya kama hannunta tana tafiya da kyar saboda azabar da gwiwoyinta ke mata. A gaban motarsa ya sanya ta, ya shiga motar ya ja zuwa wani (private hospital) da yake aiki, ya gyara mata ciwuwwukan ya sa magani ya nade da plasta. Ya ba ta wasu ‘yan magungunan a leda ya dawo da ita gida.
Tuni labari ya isa ga Mammah daga bakin dan Anty Mariya, wai Adda ta fadi a waje, Daddy ya sa a tafi da ita asibiti. Sai ta ji maganar banbarakwai, ina ruwan Daddy da Suhaana har da zai ce a kai ta wani waje? Kar dai fa ya aika da ita gidan marayun da yake ikirari! Ai sai ta zabura ta mike da gudunta zaninta na kwancewa tayi sa’ar riko shi kafin ya kai kasa, ko mayafi babu a jikinta ta yi hanyar soro. Luba ce ta dau mayafi ta bi ta da shi ita ma da gudun. Uban karo suka yi ita da Daddy da ke kokarin shigowa, saura kadan ita ma ta fadi. Jikinta na bari, muryarta na karkarwa cikin son fashewa da kuka ta kama shi tana girgizawa.
“Ina ka tura a kai ta? Ina ‘yata, ina marainiya ta, ina ‘yar amanata?”
Gani da ta yi yana hawaye ya sa jikinta ya yi matukar sanyi. Ta fada jikinsa ta fashe da kuka.
“Don Allah kada ka raba ni da Addata, na roke ka Daddy duk abin da ka ke so zan ci gaba da yi, in har za ka barmu mu rayu tare. In ka ce ma ba za ta bi mu ba na yarda mu zauna a nan, ka kara aure ka tafi da matar, wallahi na amince”.
Girgiza kai yake yi, ya raba ta da jikin sa, ya ce, “Cool down Maryam, I have realized my shortcomings and I promised to become a changed person. Zan taya ki son ‘yarki da kula da ita har karshen rayuwarmu. Trust me!” Ya fada cikin sanyin murya yana share mata hawaye da tafukansa.
“Maryam faduwa ta yi, na ce a kai ta asibiti. Na rantse miki da Allah bayan wannan babu wani abu”.
Maryam Dakata ta bi shi da kallo, irin kallon kurillar nan na son karanto zuciyar mutum. Kamar Hafsat ita ma ta dauka mafarki ta ke yi. Ta sanshi, ta san halinshi ba ya fadar abin da ba haka yake a zuciyarsa ba, wani irin frank person ne shi, saboda ba ya shakkar kowa, ko ya fadi abu don ya faranta maka bayan ba shi ne a zuciyarsa ba. Kwayar idanunsa masu haske da sheki sun gaya mata komai, saboda ba yau ta sanshi ba.
Hakika ta yi hakuri da shi shekaru rututu, yau ga ribar hakurinta ta girba. Da ma an ce mahakurci mawadaci, kuma komai ya yi farko zai yi karshe da ikon Allah.
Sosai ta rungume mijinta tana kukan da a yanzu ya san na farin ciki ne.
Luba da ta biyo ta da mayafi ta dade a soron farko rike da mayafin tana jiranta. Da ta ji kamar tattaunawar sirri suke sai ba ta labe ba ta koma cikin gida, wannan ba tarbiyyar da Adda Hafsatu ta yi musu ba ce, (wato labe).
Ibrahima autan Adda ne ya taho cikin gidan don kiran Daddy ya gaya masa ya yi wasu manyan bakin daga lagos, sai ya tadda su a haka a soro. Da sauri ya juya zai koma, suka saki juna Daddy ya kira shi. Ya dawo kansa a sunkuye ya fadi sakonsa, Mammah ta koma cikin gida, shi kuma ya fita.
Hafsat ta shigo tana dingishi ta sha plasta a baki da kafafu. Tun kafin ta zauna Mammah ta taso ta taro ta tana tambayarta,
“Garin ya ya ki ka fadi?”
Kowa sai sannu yake yi mata, bakin ya haye ya yi suntum. Halim ya dube ta, sai ya kyalkyace da dariya. Ta harare shi da kumburarrun idanunta, ya yunkura zai fice yana ta dariya yana yi mata sannu, sannan yace “Ina ruwan alkubus! Ya hau ya yi fam!”
Baba Azumi ta kai masa duka ya fice da gudu.
Ta ce, “Mommah tuntube na yi da dutse. Ga katin wayar ga canjinki”. Ta mika mata abin da ta kudundune a hannunta na dama. Duk azabar da ta sha bai sa ta zubar dasu ba. Tsabar girmama komai na Maman ta. Mammah ta karba tana fadin, “Ni wannan katin waya da ba a je siyansa ba!”. Wata zuciyar ta ce da ita.

“Gara da aka je siyansa, watakila shi ne silar dawowar Daddy kan kyakkyawar turba”.

Da aka yi sadakar bakwai Mammah ta sa direba ya dauki Baba Azumi suka kama hanyar Sokoto, domin ta ga ‘ya’ya da danginta kafin lokacin wucewarsu Brussels (Belgium).

*****
Haka suka ci gaba da rayuwarsu cikin ‘yan uwa cike da alhinin rashin Inna Ramatu. Sati biyu a tsakani suka wuce Abuja.
Abdul’azeez bai san da rasuwar Inna Ramatu ba, ya samu gurbin da ya nema a jami’ar Ibadan, sun ba shi kwas din da yake matukar so, wato LAW, inda zai karanci LLB tsayin shekaru biyar. Kafin isorwar mutanen Jeddah ya fara jarrabawar zangonsa na farko, Daddy na sane da hakan shi ya sa ya kyale shi kawai don kada ya raba masa hankali. Inna ta riga ta tafi, babu wanda ya isa ya dawo da ita.
Azumi ta samu ‘ya’yanta da jikokinta lafiya a gida Sokkoto, ta sauke musu sha tara ta arzikin da ta tara musu. Maimaikon su ga tsufa mai yawa tare da ita, sai suka ganta ras! Kamar an kwashe mata shekaru goma an zubar, da ma kuma aike ba ya yankewa tsakaninta da su, duk shekara in an zo aikin hajji daga Sokoto. Sun riga sun san a gidan Ambasada ta ke cikin kwanciyar hankali.
Ba ta dawo Abuja ba, sai a satin da za su tashi zuwa Brussels, dukkan shirye-shiryen tafiyar tasu ya kammala. Hankalin Mammah da na ‘yarta ya kwanta sun zama cikin nutsuwa da kwanciyar hankali domin da gaske Daddy ya canza a kan Addar Mammah ya cure ta cikin su Isma’el, Usman da Halim. Babu nuna bambanci, babu duk wannan hayagagar. Sau da yawa sai ya yi mata abu su bai yi musu ba. Ya bude mata (account) a Brussels kamar yadda ya bude wa gabadaya ‘ya’yansa duk wata yana sanya musu kudi daga albashinsa saboda lalurar rayuwa mai zuwar ma dan Adam watarana ba tare da ya shirya ba.
Daddy na shiga office dinsa da sati daya ya sanya ‘ya’yansa duka a makaranta, bayan ya karbo musu (transfer) daga makarantunsu na Jeddah. Amma kasancewar ba su iya Dutch, Wallonian ko German languages ba daga Larabci sai Turanci, dole ya sanya su a wata makarantar daban inda ake koyar da wadannan harsunan, don da su suke amfani (as formal language) a kasar bakidaya.

‘ST. John Berchmans Collage’ ita ce makarantar su Hafsat Dakata a Brussels. A nan din ma an bai wa Ambassador gida a jerin gidajen jakadodinsu, mota da direbobi kamar a Jeddah, direbobi su kai shi office, su kai ‘ya’yanshi makaranta su dauko su. An sanya Hafsat aji daya na sakandire, Halim aji hudu, Usman da Isma’eel an sanya su cikin masu zana jarrabawar shiga jami’a na shekarar gabadayansu dama tsiran aji daya ne tsakaninsu, Ismael ya kammala sakandirensa a Jeddah har ya yi jarrabawar shiga jami’a. Amma da suka zo nan Brussels tsarin jarrabawar nasu ba iri daya ba ne da na Saudiyyah, suka ce dole ya jira zuwa shekara mai zuwa ya maimaita irin tasu don haka zasu zana lokaci daya da Usman kafinnan shi Usman ya kammala. Babban burinsa ya samu gurbi a jami’ar ‘Harvard’, jami’ar nan mai tsohon tarihi a Amurka, don haka ya dage da karatu baya wasa kafin lokacin jarabawar ya zo tareda malami Belgian da Daddy ya daukar masa, Usman ma in yana gida yana zama a yi dashi, ba ya wasa ko kadan don ganin cikar mafarkin sa na zuwa Harvard.
Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba. Hafsat na girma tana kwankwadar ilimi mai tsada, kwakwalwarta na kara budewa da ilimin zamani. Burinta na zurfafa shi na kara karuwa a zuciyarta. Ta samu kanta da wani mayataccen ‘determination’ na son yin ilimi mai zurfi domin ta zama wani abu a rayuwa ta dogara da kanta. Tana ganin yadda Daddy ke wahala da su, shekaru na kara tura musu shi da Mammah, sun karar da kuruciyarsu bakidaya wajen hidimarsu, cinsu, shansu, sutturarsu da iliminsu. Tana so ta zama uwa kamar Mammah, ta yi wa ‘ya’yanta abin da Mammah ke musu ko ta kwatanta. Tana sha’awar Daddy da zurfin iliminsa wanda ta tabbata shi ne silar matakin da yake kai a yau.
Don haka hafsat ta kudiri aniyar yin ilimi har sai ta kure shi in ana kurewa, za ta iya yin komai a kan a barta ta yi karatun zamani mai zurfi. Tun a Jeddah sun yi haddar Alqur’ani mai girma, sun yi ilimin addini sosai, shi ma tana so ta fadada shi har fiye da ilimin bokon in ta samu dama.
Mammah da kanta ta yi tunanin daukar musu shehin malami da zai ci gaba da ba su karatun addinin musulunci a gida, a ranakun karshen mako. Ta gaya wa Daddy, ya samo wani Malami Basudane ya ci gaba da ba su karatun littattafan addini. A gefe daya suna tisa haddar su. Yadda suke fahimtar boko haka suke fahimtar addinin musulunci fiye dashi, sabida foundation dinsa da suka ginu akai tun suna kankana.
A tsayin shekarun da suka yi a Belgium sun je gida sau uku, su Baffa Atiku, Adda da sauran dangi sun zo Brussels sau biyu, Baffansa Abdulkarim duk sanda ya samu sarari yana zuwa da iyalinsa su yi hutu. Abdul’azeez bai zo ko sau daya ba. Ba shi da sha’awar Belgium, wani irin mutum ne murdadde mai ra’ayi da akida, babu abin da ya isa ya sauya shi daga kan perceptions dinsa (beliefs), burinsa ya zama babban attorney wanda kasarshi za ta yi alfahari da shi. Yana so ya zama lawyer na farko da zai kawo sauyi cikin tsarin shari’ar da kasarmu ke tafiya a kai ta son zuciya da danne mara karfi. Yana so ya kauda cin hanci da rashawa da suka yi wa kotunan kasarsmu katutu. A kauda karya a tsayar da gaskiya, ba shi da burin zama lauya mai zaman kansa; lauyan gwamnati yake son zama. Ta haka ne zai samu damar taimakon al’umma marasa karfin kwatar hakkinsu. Hakan ba zai kasance ba sai ya kai kololuwa a karatunsa na lauya, sannan sai in ya zabi ‘CIVIL LAW’ ya zama gawurtacce a cikinta.
In haka ne kuwa ashe yawon hutawa a kasashen Turai ba nashi ba ne. Lokacin hutunshi shi ya kamata ya zame masa lokacin jajircewa don cimma burin rayuwarsa.
Daddy ya dade da kama masa dan kyakkyawan muhalli daura da makaranta a garin na Ibadan tun lokacin da ya ce ba zai samu dinga zuwar musu hutu ba saboda yanayin karatunsa. A waya suke jin lafiyarsa, ita din ma sai karshen mako yake kunnata. Minister Abdulkarim da ‘ya’yansa su Farhan sa’o’insa kan yi tattaki lokaci zuwa lokaci su ziyarce shi har Ibadan, idan ka ganshi ba za ka ce dan Ambassador ba ne, sabida irin rayuwar (typical Nigerian) da yake ciki, gwagwarmayar neman ilimi yake yi yadda sauran masu rangwamen gata ke yi a jami’o’inmu na kudu dana arewa. Ba shi da wanda za a kira abokinsa na jiki sai ko abokin karatu. Ba ya tambayar Babansa kudi shi da kansa yake sanya masa duk wata. A ganin Abdul’azeez Hamzah Attikou, jin dadi da rayuwar jin dadi, za su biyo baya ne sa’ilin da dan Adam ya samu cikar burinsa. Amma gwamutsa seeking goal attainment (neman cimma buri) da rayuwar hutu da jin dadi irin ta gidansu is a barrier to goal achievement (shinge ne ga cikar buri). Saudiyyah ma da ya yarda yake zuwa sabida ita dole ce ga kowanne musulmi, kuma yana koyon karatun Alqur’ani da sauran karatun addini, yana Ibadah a Makkah da Madinah.

****
A wannan shekarar da ake ciki ya fito da (LLB) mai daraja ta farko. Duk wani masoyin Dr. Hamza ya taya shi murnar wannan hazikanci na Abdul’azeez, gabadayansu sun zo gida don yin bikin sallah karama. Sun yi sati daya a Kano suna cin bikin sallah su Hafsat na zuwa cikin gari kallon hawan sarkin Kano (Durbar) kullum ita da su Haleem da ‘ya’yan su Furerah, Hafsat abin ya burge ta saboda ba ta taba gani ba sai wannan karon. Ta shige cikin sa’anninta ta saki jiki yadda Mammah ke so. In tana gwara hausarta su Halima ‘yar Anty Mariya da su Saimasu yi ta cin dariya. Wani zubin ma sai Haleem ya maimaita musu abin da ta fada suke ganewa, yaren Dutch (Flemish) ya mamaye bakinta ko turanci ba sosai ta iya ba, larabcin ma ta dade da manta yadda ake yi sai ‘yan kananan kalmomi saboda rashin abokinyi. Mammah ta bula mata hanci gefen dama da ‘yar barima ta danyen ‘gold’ wadda ba karamin kara mata kyau ya yi ba.
Har suka koma Abuja Abdul’azeez bai zo Kano ba yana Ibadan, sati biyu dama yaran za su yi dan hutun nasu ba mai yawa ba ne. Za su koma tare da Baba Azumi su yaran saboda makaranta. Daddy da Mammah za su tsaya ‘convocation’ din Abdul’azeez a Ibadan wanda za a yi sati na sama. Su Hafsat suka tafi cike da kewar iyayen nasu.

Hajiya Maryam ta daga ido tana kallon babban dan nata, wanda ta kwashe lokaci mai tsawo ba ta sanya shi a idonta ba. Yana cikin kayansa na barin jami’a kamar sauran dalibai ‘graduates’ ‘yan uwansa, a cikin jami’ar Ibadan-Nigeria. Ya zama babban matashi fiye da tunaninta. Wasu irin ilhamomi sun bayyana a tare da shi da ba duk maza Allah ya halitta da su ba. Ga wani siririn saje da ya kwanta gefe da gefen fuskarsa. Sauran ‘ya’yanta duk sun fi shi haske, amma kalar fatarsa ta fi ta kowa ban sha’awa. Ya fi kama da mutanen Qatar din Misra ko ko larabawan Habasha da aka fi sani da Ethiopians.
A yau ne ya cika shekara ashirin da biyar idan har lissafin da ta ke yi daidai ne. Ga tabon sujoud nan ya bayyana a saman goshinsa. Alamu ne na ba ya wasa da sallolinsa biyar kamar yadda ta hore su bakidaya. Wani matsanancin farin ciki ya ziyarci zuciyarta. Ta daga hannayenta biyu sama tana kara rokon Ubangijin sammai da kassai;
“Rabbi ja’alni muqimassalata wa min zurriyyaty, Rabbana wataqabbal du’a!” Fassara;
“Ya Ubangiji ka sanya na zamo mai tsaida sallah ni da zurriyata, Ubangiji ka amshi addu’ata”.
Daga Ibadan Kano suka wuce, Baban su Sha’aban ya hada get-together-party a Dakata na taya yaran nasu murnar kammala digirin, Farhan da Sha’aban

Please Login or Register in order to submit comment