Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ta dai Takarin da bata so.
A nan unguwarsu Albasaatin ta yi kawaye biyu ‘yan Nigeria matan ma’aikatan Embassy, daya matar mataimakin Daddy ce Safiyya sun fi su dadewa a Saudiyyah sosai, bayan ta gama girkin rana ta kira Anty Safiyya ta ce ta cigita mata mai aiki don Allah Takari, ta ce ta bari sai Juma’ah za ta shiga Misfalah in ta je Harami za ta taho mata da ita. Ta yi godiya suka aje wayan.
A daren ranar, Hajiya Maryam ta yi shiri kamar yadda ta saba ta nufi turakar maigidanta, aiki yake yi a tsakiyar gadonsa cikin na’ura mai kwakwalwa. Ciki-ciki ya amsa sallamarta ba tare da ya dago daga abin da yake yi ba. Kokarin sauke baby ta ke daga bayanta don ta koma ta dauko gadonta. Da hanzari ya dago ido ya dube su. Ya zare farin gilashin kara karfin gani da ke idanunsa, cikin kaushin murya yake magana.
“Ban gane ba? Kina nufin tare zan kwana da yarinyar nan? Ta ya ya ki ke tunanin zan iya jure kukan jaririn da ba nawa ba? Excuse me please,Maryam! It’s enough wallahi, abin da ki ke min a kan yarinyar nan ya ishe ni. You are forcing me to be a father of your adopted daughter while i’m not. To bari ki ji in gaya miki, wannan ya zamo na farko kuma na karshe. Daga yau sai yau, kada ki kara kawo min ita dakin barcina. Ke kanki na hakura da ke in har za ki hada hidima ta da tata, ko za ki hada mana makwanci. Idan duk alfarmar da na yi mata ba ki gode min ba zan ba ki mamaki wallahi, don aure zan kara ki ji dadin kula da ‘yarki......”
Tana kuka sosai ta juya da ‘yarta a kafada jikinta har rawa yake, domin Daddy fada yake sosai. Cikin babban sauti wanda ba ta taba sanin yana da shi ba. Tana fita ya banke kofarsa yana sakin tsaki. Haka suka kwana kamar jiya zukata babu dadi.
Washegari bayan yara sun tafi makaranta, shi kuma ya tafi office, kamar jiya yau ma bai kula abincin da ta bata lokaci ta shirya masa ba. Tun asuba ta tashi ta soya masa waina (masa) don ta san yana matukar sonta, haka ya tsallake ya bar mata kayanta kamar jiya ya sa ‘ya’yansa a gaba suka tafi. Su kansu yaran ba sa cikin walwala ganin halin da iyayensu ke ciki na rashin walwalar suma, yanayi ne da ba su taba ganinsu a ciki ba tun tashinsu. Daddy da Mammah suna matukar kaunar junansu, sun fahimci juna, ra’ayinsu daya kusan a kan komai na rayuwa, sai yau a kan ‘yar Habiba, kowanne gani yake shi ne a kan gaskiya.
Shi Dr. Hamza ba muguwar zuciya ce da shi ba, ba rashin tausayi gare shi ba, ba kin taimako gare shi ba, a’ah, ra’ayi ne na rikau irin na Malam Bature, duk wani taimako da zai wa mutum ko jininsa ne ya fi yarda ya yi masa shi daga nesa komin girmansa, amma ban da ya dauko shi ya kawo cikin family dinsa. Ita kuma Hajiya Maryam tana matukar son Habibah, son ne ya shafi abin da ta haifa, sannan tana tunanin in ba ta rike yarinyar nan ba ina za ta kai ta? Ba ta san komai da ya dangaci Habibah ba ba ta san daga inda ta fito ba, sannan in ta kai ta gidan marayu tana tausayin rayuwar da za ta taso a ciki. Za ta taso ne a shegance, a shegantata bayan ita ta yarda yarinyar nan ba shegiya ba ce da ubanta, akwai abin da ya rabo Habiba da mahaifinta. Me ya sa Daddy ba zai yi mata alfarma ba?
Hantsi na dagawa ta samu wayar Anti Safiyyah ta daga suka gaisa da tambayar lafiyar yara. Anti Safiyya ta ce, “Mai aikin babba ki ke so ko yarinya, ko budurwa?”
“Babba dai, wadda ta san ciwon kanta. Ban da wadda ba ta kai shekaru hamsin ba”.
Safiyyah ta ce, “To alhamdu lillahi an samu. Sunanta Azumi, ‘yar Sakoto ce, zan kawo ta ranar juma’a insha Allahu. Za a dinga biyanta Riyal dari biyu duk wata, duk irin hidimar da ki ke so ta yi miki za ta yi miki, ku dai tattauna a tsakaninku”.
“Na gode Safiyyah sosai. Na gode Allah ya kara zumunci”. In ji Mammah. Da haka suka ajiye wayar.
A cikin wannan hali na zaman doya da manja, zuciya ba dadi, Hajiya Maryam ta ci gaba da zama da mijinta a dalilin ‘yar mai aikinta. Ana i’gobe za su cika kwana bakwai da baro asibiti tunanin ragon suna (haqiqa) ya dame ta. A yadda Daddy ke kumbure-kumburen nan za ta doshe shi da zancen yanka ragon suna? Ta yi tunanin ta bai wa Salah ya sayo da kudinta kamar yadda ta yi amfani da kudinta wajen siya mata suttura, madara kam ya saya katan-katan kamar yadda ya furta, sai dai wani (positive) tunani ya shige ta. Bai kamata tun yanzu ta soma yin gaban kanta a kan yarinyar ba, dole ta ba shi hakkin da yake cewa tana ‘forcing’ dinshi na zaman uban yarinyar yana so ko ba ya so, in ta sayi rago ta yanka mata ya tabbata ita ce uwarta, ita ce ubanta kenan,
“You must be the father you don’t want to be Daddy!”. Ta fada a fili.
A daren ranar ta cancada kwalliya, turare kala-kala ta feshe jikinta da shi, a gobe ta ke sa ran za a kawo mata sabuwar mai aikin. Ba za ta iya barin Baby ita kadai ba, don haka ta kira Usman da Isma’eel da Halim ta jere su a gadonta ta ce su kwana a nan.
“Isma’el ba ka da nauyin barci, ka kula da baby in ta motsa. Ga madararta, ga ruwan zam-zam dinta ka duba pampers akai-akai”.
“Dont worry Mammah, je ki lallasar mana Daddy ya daina fushi da ke. Mammah tausayinki nake ji, ya ce wai wata sabuwar mata zai kawo mana ke kin daina sonsa sabida jaririya”.
Murmushi ta yi, ta ce, “Isma’el Allah ne ya halatta masa auren mata har hudu in yana da iko. Ba saboda jaririyarmu ba ne. Kuma ba saboda ita yake fushin da yake yi ba, ni ce na yi masa laifi”. Ta fadi hakan ne don kada su fassara mahaifin nasu a matsayin mutum mara tausayi da adalci. Wanda tuni hakan ya fara darsuwa a zuciyar Isma’el tunda ya fi Usman da Halim wayo. Amma yanzun ya yarda da abin da Mammah ta ce, sai dai ko kusa ba ya son Daddy da wata macen bayan mahaifiyarsu. Akwai abokinsa a makaranta a Abuja da yake ba shi labarin cewa Mamansa ta rasu wajen haihuwarsa a hannun (step-mother) dinsa yake, kullum sai ta dake shi ta sa babansa ya dake shi, kuma ba ta bashi abinci sai mai aikinsu ce ta ke ba shi. Wannan labari da Salim ya ba shi ya tsaya masa a zuci, ba ya so ya ji an ce za a kara aure.
Da haka Mammah ta wuce ta barshi yana tunani, yana kallon Baby da ke barcinta cikin kwanciyar hankali a cikin kyakkyawan gadonta da ke gefensu. Usman da Halim tuni sun yi barci.
Mammah ta yi sallama a kasaitaccen (bedroom) na Ambassador Hamza Dakata, tuni ya kashe fitila ya rufe kwamfuta yana azkar din barci, dole ya amsa sallamar don bai zaci ganinta a lokacin ba. Kwana shida kenan rabon da su hada makwanci, in ya ce ba ya kewar Maryam ya san ya yi babbar karya ya kwana da yunwa. Mace daya tamkar da dubu wadda ta mamaye filin mata goma a zuciya da ruhinsa, ta haifa masa sanyin idaniya ABDUL’AZEEZ HAMZAH ATIKU, in ya ce zai hada matsayinta da na wata mace da sunan aure ya san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakinsa ko ya huce haushi amma Maryam ta wuce nan a zuciyarsa.
Jin ta ya yi ta kwanta a gadon bayansa ta sanya tausasan hannuwanta ta rungume shi, hawayenta na sauka saf-saf a kan kafadunsa. Runtse ido ya yi wani sanyi na ratsa zuciyarsa. Ta ja bargon da yake kokarin rufawa ta ajiye a gefe.
“Ka yi hakuri Daddy don Allah ka yi hakuri, na yarda laifina ne, na kasa hakura da tsarinka in yi maka biyayya. Na yi ne don neman lada a wurin Ubangiji ba don in bata maka rai ba Daddy”. Ta fadi cikin shesshekar kuka mai motsa zuciya balle zuciyar masoyi. Kamar ba zai yi magana ba sai kuma ya dago ta ya juyo suka fuskanci juna.
“Why Maryam? Me ya sa ki ka zabi farin cikin wasu bare da ba ki hada alakar komai da su ba a kan nawa? Na dade ina mamaki, ina tambayar kaina anya Maryam dina ce? Ta bar ni kwana shidda ba tare da ta san halin da nake ciki ba? Ya ya nake rayuwa? Me nake ci nake rayuwar? Anya Maryam ke ce???”
Hawaye ta ke sharewa sosai,
“Tunda ka gaza fahimtata Daddy, ka kasa mara min baya mu ceci rai, mu yi jihadin rikon maraya tare, mu yi domin neman lada a wurin Ubangiji na amince ka fadi duk yadda ka ke so a yi da jaririyar nan na maka alkawarin zan bi, in har za mu koma rayuwarmu ta baya ka kuma fasa auren da ka ke cewa yara za ka yi. Ba zan iya hada ka da kowacce mace ba Daddy ‘depression’ zai kama ni”.
Bai san sanda dariya ta kwace masa ba, ya yi sosai sannan ya gintse fuska, “Ina nan fa ina jiyo laccar da ki ke wa Isma’el yaushe ki ka juya ta a baibai?
Kin ce Allah ya ba ni iko, yanzu kuma kin ce ‘depression’ zai kama ki, dole in yi aure Maryam don in samu mai kula da ni, ke kuma ki ji da ‘yar da ki ka fi so a kaina. Me ye laifina a nan?”
Ta share hawaye da tishu ta ce.
“Ai na ce ka fadi yadda ka ke so a yi, ko cewa ka yi in jefa ta a kwatami zan jefa tunda ba ka sonta”.
Ya hade fuska, “Ni na ce miki bana sonta? Me ta min? Kawai kin kasa fahimtata ne ke ma, amma a bar zancen haka, kowa ya zauna a kan ra’ayinsa. Amma abubuwan da ki ka dauko hanyar yinsu ba zan lamunce su ba, dole ki ba ni dukkan kulawar da ki ke ba ni a baya. Ban amince ki canza ko kwaya daya ba, bana son zama da masu aiki amma na amince ki daukar mata Nanny zan biya ko nawa ne. Ki daina hada lamarina da nata, daga sanda na dawo office karfe shidda na yamma har zuwa wayewar gari in fita (office) lokacinki nawa ne da yarana ki bar ‘yarki can wajen mai rainonta. Kuma ki ci gaba da bincike a kan danginta, duk ranar da suka bayyana za ki mayar musu da ‘yarsu”.
Gyada kai ta yi cikin hadiyar zuciya, “Na amince Daddy, wallahi na amince. Na gode, Allah ya kara rufa maka asiri duniya da lahira. Alfarma ta karshe da nake nema ka yi mata haqiqa, ka sanya mata sunan duk da ka zaba, ka yi mata khutbah gobe da safe kafin ka wuce office, already na nemi Nanny din wallahi, gobe Safiyyah za ta kawo ta........”.
Ta cika shi da surutu, bayan shi kuma cike yake da wata irin kewarta, janyo ta ya yi kawai ya sanya cikin kirjinsa, ya rufe su ruf da bargon mai tsananin taushi da kamshi. Can kusan makoshinsa ya ce,
“Ke don Allah ya ishe ni haka, gobe zan yanka mata ragon...”
Da haka hirar ta kare, ta koma mai ma’ana da kara dankon kauna. Hakika ta yi kewar mijinta, shi ma Daddyn ya yi kewarta yadda harshensa ba zai iya fassarawa ba, sai dai ‘emotions’ dinsa a daren ranar bakidayanta sun nuna mata hakan.

“Daddy kenan! Zuma, ga zaki ga harbi”.

Maryam Dakata ta fadi cikin zuciyarta cike da shaukin mijinnata, dan uwanta, uban ‘ya’yanta.
*****
Washegari da Salah ya sauke shi a office ya ba shi umarnin ya sayo babban rago a yanka da sunan ‘yar Mammah, da ta ce ta ba shi zabin sunan da za a saka wa jaririyar, cewa ya yi shi fa babu ruwansa. Ta sa wa ‘yarta sunan da ta ke so idan kuma haqiqar da ya yi mata ma ba ta gode ba, to don Allah ta kyale shi haka. Da yake lallaba shi ta ke, sai ba ta ja da nisa ba. Ta mika masa bebin tana marairaicewa.
“To don Allah amshe ta ka yi mata khutbah da sunan Addah, wato Hafsatu”.
Harara ya dalla mata, “A dalilin me? Ga sunan uwarta za a ce na uwata zan saka? Ba gara ki sa mata Habiban ba don a gane danginta da sauri?”
A ranta ta ce, “Bakinka ya sari danyen kashi. Hmmm! Ko an gane ba wanda zan bawa, ‘ya ce Allah ya riga ya ba ni, iyayena da ‘yan uwana sun isa su zame mata dangin”.
Ta sake kwantar da murya, “Daddy, ba zan taba mance sunan uwarta ba, don Allah ka sa mata Addah, don ta biyo kyawawan halayenta”.
Yana cin magani ya amsa, ya zauna a bakin kujera ya kai bakinsa saitin kunnenta yana yi mata khutbar. Dadi ya kashe Mammah a zuci.
Bayan ya fita da awanni uku Anti Safiyya ta yi sallama, matar biye da ita. Kyakkyawar tarba Hajiya Maryam ta yi musu. Bayan sun ci abincin rana suka soma tattaunawa. Azumi ta amince za ta taya Hajiya Maryam ayyukan gida, za ta yi rainon Hafsat da amana. Shekarunta arba’in da biyar, nitsattsiyar mace sosai. Mamma ta miqa mata Hafsat din da ta yi wa lakabi da SUHAANAH kasancewar sunan mahaifiyarta ne, a take Azumi ta karbe ta ta goye. A gaban Anti Safiyyah Hajiya Maryam ta zaunar da Azumi a kan kilishi, ita da Anty Safiyya suna kan kujera ta soma magana cikin nutsuwar da Allah ya halicce ta da ita.
“Azumi ga ni ga wadda ta kawo min ke, kawata Hajiya Safiyya, na daina zama da ‘yan aikin da ban san asalinsu ba. Tsakani da Allah ki gaya min daga ina ki ka fito a Nigeria, da inda iyalinki suke. Zan kuma yi bincike idan kin yi min karya”.
Anty Safiyya ta gyada mata kai, “Haka ne kwarai. Azumi muna sauraronki”.
Dattijiyar ta gyara zama cikin hankali ta ke magana.
“Daga jihar Sokoto na zo Saudiyyah, idan na yi miki karya Allah ya hukunta ni daidai da abin da na aikata na yaudara”.
Mammah ta ce, “Sokoto wace unguwa? Gidan wa?”
“Unguwar Mabera, gidan Malam Isuhu Maishanu, mun zo Saudiyyah ni da mijina muna neman na kanmu a Shari Mansur shekara biyar a baya, muna kawo goro da sauran abubuwan da mutanenmu ke bukata, an sha kama mu har sau biyu ana mayar da mu Najeriya muna dawowa, kamar yadda ki ka sani in ka dandani zaman saudiyyah ba ka iya bari da sauki, to hakan ce ta faru da mu ni da maigidana.
Shekarar baya ya rasu ya bar ni da ‘ya’ya biyar namiji daya hudu mata. Namijin Yusha’u ya jima da yin aure a Maishanu. Na aurar da mata biyu a can gida Sokoto, ta ukun wato Harira da autar Ladidi kuma suna hannun kanwata a Talata Mafara. Idan akwai karya cikin abin da na fada Allah ya hukunta ni da laifin yaudara da cin amana”.
Anty Safiyya ta dafa kirjinta da hannunta na dama ta dan fiddo mata ido ta ce,
“Ni ‘yar Sokoto ce gaba da baya, Iyayena da kakannina, don haka zan bincika abin da ki ka ce daga yau zuwa gobe. A unguwar Nakasari da unguwar rogo iyayena suke na san Mabera sosai”.

Azumi ta gyada kai alamar amincewa.

Hajiya Maryam ta nisa, sannan ta dubi Azumi, “Abin da ya sa na yi miki wannan titsiyen ba rashin yarda bane, mai aikina ta baya ce...........” Tiryan-tiryan ta ba su labarin tun kawo mata Habiba Abuja zuwa yau. Azumi ta sakko Hafsat ta kara rungume ta a jikinta, ta sa mayafinta ta kara rufe ta sosai daga ita har Anty Safiyya sai da suka yi hawaye. Safiyyah ta karbi Hafsat ita ma ta rungume tana kallon kyakkyawar fuskarta, ta ce da Hajiya Maryam.
“Na rantse da Allah na dauka haihuwa ki kai, ganin yarinyar nan fara tas kamar ‘ya’yanki. Kina da tsayi, kina da dan jiki ba a fiya ganewa ba idan irinku nada ciki. Allah ya ba ki ladan wannan jihadi na ceton ran maraya da sadaukarwa saboda Allah”.
Murmushi ta yi, ta ce, “Amin”. Amma ba ta gaya musu halin da ta ke ciki da maigidanta a kan lamarin ba. Ciki ba don tuwo kawai aka halicce shi ba, wani abun yana bukatar sirri.

Bayan tafiyar Safiyya, Azumi ta goye Hafsat wadda Mammah ta kira (Suhaana) suka ci gaba da ayyukan gida tana nuna wa Azumi kan komai na gidan. Ta nuna mata dakinta. Kwarai dattijuwar mai hikima da azanci ce, har girkin dare ita ta yi, kuma Hajiya Maryam ta yaba, tuwon shinkafa da miyar busasshiyar kubewa da ta ji naman ragon sunan Hafsatu. Sai Mammah ta yi na Daddy kawai, su Isma’el suna ta santin girkin Baba Azumi, yadda Mammah ta koya musu su dinga kiranta.
****
Kyakkyawar kulawa Suhaana ke samu a hannun Mammah da Baba Azumi. Tuni ta murmure ta yi kubul-kubul abin sha’awa cikin watanni uku kacal ta iya zama, har tana karya kafa tana so ta fara rarrafe. Yarinya mai kyau da ban sha’awa ga gashi fal kanta duk da an yi mata askin suna. Mammah ba ta gajiya da yi wa gashin ado da ribbons kala-kala da yi masa style iri-iri. Duk sharuddan da Daddy ya gindaya mata a kan rayuwar Suhaana a gidansa tana kokari wajen kiyayewa. Daga karfe shidda in suka shige daki ita da uwargoyonta Azumi ba sa kara fitowa sai lokacin da Azumi za ta dora sanwar safe, za ta goye ta ta shiga kicin bayan ta cika mata ciki yadda ba za ta yi kuka ba. Dakin da Habiba ta zauna a nan Mamma ta sanya Azumi, yana daga can gefe suna da nisa sosai da bangaren Daddy.
Cikin watanni ukun nan bai fi sau biyu Ambasada ya dora ido a kan Suhaana ba. Na farko Isma’eel ne ya sanya ta cikin keken koyon zamanta ya tura ta harabar gidan, inda suke wasan kwallo shi da wasu yaran makotansu larabawa. Usman da nasa abokan suna wasan tseren keke a layin, Halim na tsaye jikin keken nata yana yi mata wasa. Hancin motar Daddy ya sako kai, yana hakimce a gidan baya na galleliyar Hummer-Jeep, Salah ke tukawa.
Da sauri mai kula da shukoki da wanki da gugarsu mai suna Habibullah ya zo ya bude wa Daddy kofar bangaren da yake zaune ya fito. Da gudu Haleem ya turo keken Suhaana zuwa gare shi yana,
“Daddy oyoyo”.
Daga shi ya yi sama ya girgiza ya dire, daidai idanunsa suka sauka a kan yarinyar. Kyakkyawa ta kin karawa kamar larabawan Jiddan suka haife ta. Tsafta ta kama jikinta sosai. Ya kalle ta na minti biyu ya dauke kansa ya yi cikin gida, Haleem ya tura ta suka ci gaba da wasansu.
Ganinsa na biyu da ita ranar ‘open day’ na su Usman ne, an bukaci iyayen yara duka su zo don sanin halin da yaransu ke ciki a makaranta da karatunsu. Mota daya suka yi amfani da ita shi da iyalin nasa, ya ganta a hannun Azumi wadda ta sha hijab bakikirin ta shigo bayan motar, ai bai san sanda ya bude wuta ya fara fada ba,
“Me jaririya kamar wannan za ta je yi makarantar yara? Maza ku koma gida, ai ba gidan biki ba ne”.
Sum-sum-sum Azumi ta fito daga motar jikinta a salube. Ba tun yau ba ta fahimci uwar dakin nata na fuskantar kalubale daga mijinta a kan rikon yarinyar in ta yi la’akari da yadda ta ke faman cewa su zauna a daki in Daddy yana gida, kada ta bar Suhaana ta yi kuka. A lokutta da dama kuma da ta ji dirin motarsa ya dawo za ta zabura ta sunkuci ‘yar ta yi daki da ita tana cewa Azumin,
“Ku shige, sai Allah ya kai mu gobe”.
Duk me ya yi zafi? Me ye laifin wannan ‘yar yarinya abin son ganin kowa? Duk inda suka shiga sai an yaba ta, ana nuna sha’awa a gare ta, to shi Ambassada saboda Allah wane irin mutum ne kenan? Ta kasa fassara shi, domin kuwa mutum ne mai yawan taimako da faram-faram da jama’a, ko dai shi ya yi wa Habiban cikin ta haife ta shi yasa ba ya son ganinta? Ta yi saurin yin istigfari tana rokon Allah ya yafe mata wannan mummunan zato da ya ziyarci zuciyarta. Mutum ne na gari, mai rikon addini da kaunar iyalinsa, da kula da matsalolin al’ummar Najeriya mazauna Saudiyyah matuka da lafiyarsa, jiki da aljihunsa da matsayin kujerarsa. Ita kanta shi ya yi mata takardar zama tare da su a matsayin family dinsa. Ta watsar da tunanin ta shiga hidimar Suhaana.

Watannin Suhaana hudu kenan ta fara rarrafe, Mamma ta yi tunanin komawa islamiyyarta tunda Hafsat ta yi wayo, hidimarta ta ragu, ga Azumi na taimakonta bilhakki da zuciyarta daya. Tsakaninta da Ambasada lafiya lau, tunda tana kiyaye duk abin da ya ce mata ba ya so din. Ba ta kuma damuwa ta yi masa uzuri da ajizanci irin na dan Adam, dukkanmu masu nakasu ne ‘in one way or the other’, sannan tunani da halayya kowa da irin nasa.
Lokacin Hajji ya zagayo, su Adda Hafsatu, Baffa Atiku, Inna Ramatu dasu Luba na shirin zuwa, duk Ambassador ya ba su kujerar hajji, tare za su taho da Abdul’azeez ya samu hutun karshen shekarashi ma ya wuce Kano tun satin da ya wuce. Anty Zuwaira ma ta yi mata waya za su zo aikin Hajji ita da su Farhan ban da Sanata. Don haka suna ta shirye-shiryen zuwan bakin ita da Daddy da Azumi, duk da ba jimawa za su yi a Jeddah ba kwana uku za su yi su tattara su wuce Makkah har masu gidan. Amma tarba sosai suke shirya wa iyayen nasu da ‘yan uwansu.
Ranar laraba jirginsu ya sauka, suka je ita da Daddy da yara suka dauko su a filin jirgin saman sarki Abdul’azeez. Azumi da Suhaana na gida, ko da suka iso Azumi na hidimar jera abinci a ‘dining’ goye da Suhaana har hada baki suke wajen tambaya, “Maryama haihuwa ki ka yi?”
Har da masu zaro ido.
Murmushi ta yi, ta karbo ‘yar daga bayan Azumi ta dora a cinyar Adda Hafsatu,
“Karbi takwararki Addah”.
Da matsanancin mamaki Adda Hafsatu ta karbi ‘yar da ita da sauran duka suka zuba mata ido, ba ta kama da kowa a gidan kawai farar fatarta ce irin tasu. A hankali Adda Hafsatu ke tunanin ina ta san wannan fuskar?
Tabbas ta taba ganin mai irin wannan fuska har digon tawwadar Allah a goshi irin na wata fuska da ta dade da gani ne. Sun damu ta gaya musu inda ta samo ‘yar, ta ce sai sun ci abinci, in son samu ne su yi mata hakuri zuwa gobe su Zuwaira ma su iso sai ta gaya musu tare. Dole haka suka kwana cikin tararrabi da tunani, sai dai kowannensu yarinyar ta shiga ransa, musamman Anty Luba.
Washegari iyalin Sanata Abdulkarim su ma suka iso, suka dauko su a airport ita da Abdul’azeez da Salah direba, don ba jituwa ce sosai tsakaninta da dangin mijin nata ba cikinsu babu wanda ya damu da harkarta, haka ake rayuwar. Don ‘ya’yanta ma ta koya musu irin halinta na raina mutane in ba wanda suke (under the same social class) ba. Da Hajiya Zainab da nata iyalin kawai ta ke mu’amala, tunda su masu farcen susa da mukami ne.
Ita Mammah ba damuwa ta yi da harkarta ba, ita ta ke shige mata duk da haka babu wanda ya nuna mata wani hali mara dadi, an yi mata barka da zuwa kamar kowa, yaranta sun shige cikin su Usman suna ta harkokinsu, Abdu’azeez tun zuwansa washegari ya wuce Tahfiz dinsa bayan sun dauko Anty Zuwaira.
A daren ranar bayan an gama cin abincin dare, Mammah ta kwance

Please Login or Register in order to submit comment