Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

shimpidar maran lpian mika zauna' nace Baffa har ya farka ? Nafada cikin murna 'bansan miyasa
Nidai babban mutuminnan ke birgeni ba 'daga gani yanada riqo ga addini' sbd har sallaya ya pito mai a goshi abin gwanin sha'awa

baffa yace eh mamana ikon Allah ay yadara haka'

Muka hada baki da bintey wajen cewa 'Allah qara sawaqewa yace ameen 'mikadan zauna sannan mika tashi mika fice,

Yau kimanin satin baqonmu 2 har yapara dan dogara sanda ya pita waje ya dawo'

Kamardai yai yau suna tareda baffa, a waje suna Dan shan iska tareda yin pira kmar daman sun San juna'

Yakalle Baffa yayi Dan murmushi yace Mlm attu ' ina godia qwarai da halaccin taimakon da kaimin'na taimakaman dakai a lokacinda bnzata ba' 'ba tare da kuma ka sanni ba yadan' dakata sannan yacigaba da magana babu abinda zancemaka 'face Allah ubangiji yasakamaka da alhaire' nagode 2 qwaran gaske'yashare 'Yar qwallar da ta sulalo masa a piskansa'

Baffa yai saurin katsesa da cewa ya isa hk'bakomi 'kadaina min godia Allah ne abin godewa fiye da bawansa'ni ladana na wajen Allah kaidai muna fatan' Allah ida baka lpia'har kakoma wa iyalenka, cikin faren ciki dukda basusan halin daka tsince kankaba 'Amman ko yanxu suka ganka ay Alhamdu lillah;

Baqon yace, hakane malam Allah saka da akheri Baffa yace amin amin ๐Ÿ˜Š'

Yaci gaba da fadi 'nidai sunana Alhj Abdaullahi ina zaune ne a garin abuja 'inada mata daya da yara 2 mace da namiji'
Namijin sunansa Abdul Kareem macen kuma basmah '

Shi namijin ynx haka yana karatun likitancine a qasar igift ,wannan shekarar yake gamawa '

Ita kuma macen tana yin karatu a jami'a ynxu haka'

Ina kasuwancin shigo da gwala gwalai ne' daga qasa qasa 'zuwa gida nijeria '

Alhj Abdullahi yace, to Mlm Kaji taqaitaccen tarihina ,yaqarashe mgnr cikin sakakkiyar fuska๐Ÿ˜Š'"

Sannan yace in bazakร  damuba Mlm inason sanin tarihinka kaima"''koda a taqaicene "

Baffa Yace to 'to ;ay bakomi Alhj abdullahi yana da kyau ay asan juna daman ' a zaman takewar tare '

Baffa ya soma da cewa' ni ma sunanka gareni 'wato abdullahi anman maipiyata na kirana da Attu' mahaifiyatร  ainahiรฑ sunantร  xayynah ' Amman sai ake kiranta da salah '""'nataso a wannan gari namu na' *TAWA*,

Matata guda daya 'mai suna xuwaira ,wacce Allah karbi ranta wajen aihuwar diyarta ta fari '

Mafaren knn namaidawa jinjirar da sunan ma haipiya ta 'wato *'xayynahh*'
Sbd ,alqawareรฑ da zuwaira taiwa mahaipiyatร  nasa sunanta ' inta haipi mace'saigashi bata da rabon samata sunan da kanta ' yapada yana daรฑ goge qwallar tuno matarsa'yacigaba da cewa,
Dole tasa mahaipiyร ta tadauketa taciga ga ba da shayarda ita 'da nonon shanayemu da raqumma'
Har Allah yakawo lokacin data yaye kanta da kanta 'ta hanyar daina shan abubuwan shayar war
Nata'

'bayan rasuwar mamanta nayi auren mata har 2' kowacensu' babu wacce bata gallazawa mamana ba ga daurร  tallace tallace ' Wanda konayi mgn basu daukanta da muhimmanรงi'

Mafaren narabu dasu knn'dan bnga amfanin xama da matan da suka fi qarfinkaba"

Shine ma daliliรฑ dayasa mahaifiyata wato kakarta ,tadawo nan gidan da zama'

Tokaji labrina Alhj'

Alhj. Yace to Allah yasa hakan shiyapi zama alheri'

Baffa yace ameen ameen"""

Baffa yacigaba da cewa ,gobe kasuwar garinnร n keci'saimije 'nagwa damร ka inda ake buga wayan sailulร  din '

Alhj yร รงe to Allah shikaimu lpia Baffa yace ameen'โœ
[10/4, 10:12 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค
*Editing by Anty ju*๐Ÿ’˜

*FASAHA ONLINE WRITERS*

*labareeen love*๐Ÿ˜

*fg*8โƒฃ5โƒฃto8โƒฃ6โƒฃ

Kashe gari, bayan andawo masallacin juma 'a ,
Su Baffa sukaje kasuwar garin shida. Alhj abdullahi wajen masu hayar handset. '
Ya amsa yasa number ya kira '"

Hajia babba CE wato mahaipiyar Kareem ' zaune tanabawa asabe umarnin ta miqo mata phone dinta dake bedroom dinta'

Asabe taimaza tashiga tadauko mata ' tana miqa mata wayar culling din na tsinkewa'
Nandanan kuma wani kiran yasake shigowa 'tadaga wayan tareda qinyin magana Dan bakasapai tapiya daukar baquwar number ba,

Muryan dataji yasata sakin Yar siririyar daria ๐Ÿ™‚'
Tace alhajina ' yaukuma da baquwan number kake kiran madam din taka? 'kwana kusan nawa kona kira wayanka bayya shiga'

Kasa hankalina duk yatashi ga maparkai marassa dadi danaketayi a kanka'a satittakan baya 'wlh har Kareem nakira nake padama'
Yakecewa kar nadamu
Wataqil inda kasauka ba nertwok'

Mafarin knn hankalina yadan kwanta'

Dafatandai kana cikin qoshin lpia alhjina, ta fada hakan da sigar tambaya?

Dagacen bangaren nasu Baffa Wanda lokacin har sun zauna a daya daga cikin bencinan dake qofar shagon '

Alhj yadanyi murmushi kmar yana gaban madam din tasa yace '

Uhmmm ina lpia madam kawaidai rashin nertwok ne dayaimi. Qaranci a wajen shiyasa '

A ransa yana istigifaren akasin gaskiyar maganar daya boyemata'

Wata zuciyar ke cemasa, kul!!
"Kar kasaki kafada mata gaskiya ynx har sai kakoma gida sannan'

Dan yasan muddin yapadawa madam dinsa hakan Allah Kasai yasan halin dazata shiga''

Dan yasan Ita da bacci sunyi salamun qaulin '

Yacigaba da cewa natapo a jirgin qasane dawowa daga dubai 'baccin ansaukemu nan wajen da train din ke sauke fasinjoji'

Muka sauko' na dauki daya daga cikin motors nawa a inda nasaba ajesu anan wajajen trains din'

Namiqo hanya knn nabiyo ta Niger, motona yasamu matsala ' mafarin knn daga rananne kikaji bakya samun wayana 'sbd rashin qarfin service din wajen 'saidai wani bawan Allah ne yatai makamin da masauki a gidansa 'gashi kuma lokacin wayana namnta ta a motor 'to qa Edar garen sairan sati kasuwansu keci'

To kuma cikin ikon Allah saigashi rashin lpia yakamani hartawani Dan lokaci sannan nasamu Kai na""

Yanzun nanma dakikaga nayomiki waya ' yau kasuwar su keci; shiyasa nabugomiki Dan kisa ado direba yataso dawuri gobe yazonan Niger' a yankin *TAWA*"
Yakawomin mota '


Hjy babba tasauke ajiyan
Zuciya tace to shiknn alhajina'

Nandai sukai bankwana suka aje wayar'

Suka kamo hanyar gida 'yanacewa Baffa Mlm attu ,gobe fa insha Allah tareda kai da kaka Salah da *xayynah* '
Zamuje daku garinmu kuma gidana dan kuga iyalina 'Dan gskia ban fatan zumun cinmu ya tsaya iya haka' yaqarashe maganar da mirmishi"

Baffa yace lalala ๐Ÿค”
Takwarana inamu ina zuwa birni?

Birni ai sai wanda yasaba zama a cikinsa'kamarku dinnan '
Mukuma qauyenmu yafiye mana. Dadin zama๐Ÿ˜Š'

Alhj abdullahi yakafe akan cewa shifa, Allah mai lallai saiya bisa yaga mazauninsa 'a Abuja '

Dole tasa. Baffa ya amince masa kan cewa zasu bishin ganin kamar ransa yadan baci'shikuma bai soรฑ yaga yabata ma wanda yake tare dashi kokadan"

Sannan fa 'baffa yasamu lpiyarsa;

Koda sikaje gida Baffa ya shai dawa kaka Salah ' saidai fatan isarsu lpia tai goben'"



*Niko uwar zumudi qagara nai gari wayaye naganni a garin abuja ' burina naje nayita lilo irin Wanda mikegani a wayar gali direba '
Har saida naje nafadawa bintey zamu binni gobe๐Ÿ’ƒ๐Ÿปdam tsabar murna๐Ÿ’ƒ๐Ÿป,

Washe gari wajajen 12 na rana 'su Baffa sukai bankwana da maqotansu' suka doshi bakin qopar garin , inda direban kejiransu"

Suna isa ado direbaรฑ ya gaidasu ,suka amsa '
Da saure ya budewa alhj gidan gaba sukoma su Baffa set din baya '

Ado direba yakoma mazauniรฑsa na direba,
Zuciyarsa cikeda tunaniรฑ miyakawo maigidaรฑsร  wannan gari" Shiba 'dangin iya ba ,ba na baba ba ';

Ahakadai yatuqa mota' suka dauki hanyar birnin tarayyร  Abuja๐Ÿš˜;

*Xayyneb* ๐Ÿ’ค๐Ÿ’คโœ
[10/4, 10:12 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค

*FASAHA ONLINE WRITERS*

*fg*8โƒฃ7โƒฃto 8โƒฃ8โƒฃ

Tun lokacinda hajiya babba ta ga wucewar ado direba ,zuwa dauko su Alhj '

Akafara shirye shiryen abinciccika kala kala '
Wanda za' a tarbesa dasu'

Qarfe (5 da 22 )na ranar 'su alhaji suka iso gida 'kowa ya firfito daga matan '

Nikuwa xayyรฑร h"nasaki baki inata kallon tsarin gidan da yai matuqar tafiyar min da hankalina ' harda wajen swimming a bangaren gidan dawani lambu lambu mai korayen ganye da iccen mangwaro da gwaba 'wani killing din murmushi nai tareda girgiza kai 'alamun. Zasu gamu dani wadannan bishiyoyin ' insuka saki na hayesu 'sai na shasu ๐Ÿ˜‹๐Ÿ˜‹har raina ya baci ' barema iccen mangwa ronnan dayapi tapiyarmin da hankali' muna gab dashiga falon gidanne kamar ance juya gepe 'nazaro ido๐Ÿ˜ณ' Dan abinda idona yaganemin , wani qaton glass ne maiwani kalar tsawo.da fadi 'cikeda ruwa da kipaye manya manya da qananu , sai wutsil wutsil suke abinsu'

Gaskia gidannan al jannar duniya kenan'
Motocin dake harabar gidan kuwa cikin temple bazan iya sanin yawan suba daga inda Nike tsaye'

Kaka salah ce naji ta fizgomin hannu 'tana fadin kedai xayynah abin kallo baimiki wuya ?' Haba dan Allah kekuwa , sai kace wacce tawarke daga makanta ' mika shiga falon daman Alhj nagaba riqe da hannun Baffa mukuma Mina daga bayansu,

Wayyo nace, tareda piddo ido waje๐Ÿ˜ณ "''nace ina kallon kaka , laaah kaka kalla kiga irin dakunan da ake nunawa a qasar waje ' aikan na idar da maganar ,na fizge hannuna daga cikin nata ,nai tsalle na fada daya daga cikin manya manyan qayatattun kujerun falon na kwanta na mimmiqe ina dariya mai hade da limshe ido 'danjin wani taushi daya ratsamin jikina 'na kujeran tareda wani' jin qamshin Dana rasa ta ina yake bullomin ' qara lumshe idanu wana nai' Wanda har eye lashes nawa suka kwanto lambar a puskana gwanin sha' awar mai duba '

Baffa y -------โœ
[10/4, 10:13 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””
๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*By xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค

*Fasaha online writers*

*Love story*---๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜๐Ÿ’˜
*fg*8โƒฃ9โƒฃto 9โƒฃ0โƒฃ

Baffa yace' haba mamana minene haka kike?,

Daga zuwanki gidan mutane, saiki nemi yimasu barna?
banson shirme maza sauko kona sabarmiki yanzunnan๐Ÿ˜ก'

Jikina yadanyi sanyi duk saina nemi rawar kaina na rasa, a hankali nadan zamo nasauka qasa " ko Saman Tim tim din dake qasan grass carfet din 'irin na gidan sarakai , ban zaunaba turesa nai gefe ganin ynda ran baffana ya baci '

Na sunkuyar da kaina ina fadin Baffa kayapemi. Bazan sakeba , tuni idanuwana suka fara tsiyayar qwalla , Dan nidai na tsani naga na batawa Baffa rai. ,

Alhj abdullahi yace haba abokina. Baka ganin yarinyace gani take komitai ai dai dai da ita ne,

Baffa yadanyi mirmishi a ransa ya firta kudai dayake 'Yan bir nine' kunsaba ganin many an mata a matsayin Yan mata shiyasa ' kukemata kallon ya rinya'

Hajiya ce tashigo falon, da saurinta idonta gaba daya ya rufe gun mijinta ta nupa hannuwa bude''bata lura da su baffanba ,

Tana isa ta rungumesa' tareda fadin alhajina I miss you a lot much ,

Yadan Tureta kadaรฑ daga jikinsa yana cewa , madam duBA bayanki kiga 'tare fa mike da baqi, dasauri ta zabura ta miqe' tanadan dariyar kunya ๐Ÿ˜Œ'

Tace sannunku da isowa suka amsa da ywwa ,kowa fiskansa a sake'

Tace alhj, the table dinner is ready ๐Ÿ™‚


Yace tankyuu madam '
Yaja su Baffa suka hau kan kujerun dasika zagaye table din abincin ,

Kalaluwan abincine kusan kala 7' aka harhada; na gargajiya Dana zamani'banda farfesun Yan ciki Dana kan rago Dana kifi'

Saida kowa yaci abinda yakeso yai haniqan sannan suka dawo falon aka zazzauna' banda zayynah wacce akabaro tana ta faman cin muniyarta friderice' Uwa bata soncin abincin ' saboda ynda take taunarsa a hankali' a qa'eda daman ita haka take cin abincinta'

Abangaren su Alhj kuwa yake fadawa hjy ainihin gaskiyar abinda yafaru dashi, ahanyarsa ta dawowa' da irin taimakon da bayin Allah nnan sukai masa , hnkalin hjy babba yakai matuqa gun tashi kmar gani take lokacin abin yafaru'

Harqasa ta durqusa wa Baffa tana cewa Allah saka masa da alheri' ta isa gun kaka Salah tarungumota' tana fadin Granny ngd miku qwarai' kaka sala ta da gota tana share matร  qwallah tace bakomi 'yata aiduk Wanda yataimaki wani Allah zai taimakesa shim a'

Tsulum nataso daga inda mikecin abinci ,na isa gun hjya nadur qusa a gabantร  da murmushi a fuskana 'nace minene ake nifi da grany ?din danaji kin kira kaka dashi ?

Hjy taidan murmushi ' Dan tunda taga xayynah batasan miyasa yarinyar shiga rantaba '
.
Tace my daughter abinda ake nifi shine *kaka*
Kin fahimta ko ? Nadaga kai nice ehโ˜บ

Naqara tambayarta miye kuma ma' anar my daughter da ta kirani dashi' nanma tafadamiรฑ *diyata*
'Ake nipi

Nai tsalle mai hade da murnar 'ganin nasan Kalmar turanci guda biyu;;โœŒ๐Ÿป๐Ÿ’ƒ๐Ÿป

Nadurqasa agabanta nace 'kinzama mai koyamin karatu n turaรฑci daga yanxu har kan mukoma gida ;๐Ÿ˜„

Sonake na iya turanci , kan na girma nazama likitร  '
Tun kan narufe bakina naji gaba dayansu sun kwashemun da dariya'

Mizanyi kuwa ba turo bakiba da duddura qafana qasaโ˜น;

Hajiya ta jawoni mika zauna a daya daga cikin kujeren falon'

Ta kalli Baffa. Tร ce, Baffa mizai hana kabarmun zayyanh a hannunmu' misata a makaranta Dan ganin burinta yacika nasan karatun likita wlh na miku alqawaren riqeta a mana " taqarร she mgnar cikin sigar ban tausay'๐Ÿ˜”

Baffa yaja wo wani gwawron numfashi yace---โœ๐Ÿป
[10/4, 10:13 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค

*Fasaha online writers*

*LOVE STORY*
*FG*9โƒฃ1โƒฃto9โƒฃ2โƒฃ

Baffa yajawo wani gwauron. Numfashi yace' hajiya nikaina inada sha' awar naga mamana tayi karatun xamani ,kodan nan gaba bansan yanda rayuwa zata zamar manaba 'koda raina ko bashi'

yafada haka zuciyarsa a karye!""kodan ma 'ya'yanta dazata Haifa 'ta taimaka misu ta bangarori da dama,

Yace nidai indai ta bangare nane ba komi wlh nabarmiki xayyah'
Hjy kiriqeta amana ,kuzamar mata iyaye ,
Inda mu bamu kusa,

baffa , Yajuya ya kalli kaka yace kaka kozakice wani Abu kema'?

Kaka Salah tace ba abinda zance. Inda kai mahaifinta ka yanke shawara ay komi yayi , mudai fatanmu kawai , shine Allah yasa zaman dazatai anan din ya an fanemu gaba daya๐Ÿค—';

Gaba dayansu suka amsa da Allahumma ameen'

Alhj yaqara dacewa,zan riqe zayynah tamfar yanda nake riqe da ''Yata basmah insh Allah , suka amsa da Allah Sa hakan'

Nikuwa da naji batun barina da za'ayi nan asani Makaranta wai!, dadi kamar kamarmi nakeji' kamar natashi na kwaso rawar,a aqame qammm๐Ÿ˜œ'

Hjy tace ubanbgiji yabamu ikon riqeta da amana ameen,

Alhj ya dubi Baffa yace takwarana yakamata kashiga daga ciki ay , kadan watsa ruwa , wannan tafiya da mika kwaso'

Baffa yace to shiknn abokina masha Allah sukatashi sika nufi bangaren Sa ' ya gwadamasa toilet din sannan yashiga yahadawa Baffa ruwan dumi Wanda yapito daga famfo ya sirkamasa Dana sanyi ' yayi dai dai wanka, sannan yamiqa masa fara tas din jallabiya, irinta larabawan misra. Sannan yajawo masa qofar toilet din yasauko qasa'

Lokacin hjy babba taje kai kaka itama tadan watsa ruwan '

Tadawo falo ta iskeni sai mai maita turancina nake , ina dariyan farinciki,

Tunkan hjy babba ta qaraso , ta tsurawa zayynah ido' tana mamakin kyau da Allah yaiwa yarinyar baiwa dashi' yarinya kamar tasha hatimin annabi Yusup,๐Ÿค”

Masha Allahu tace ;
Taqaraso wajenda Nike a zaune , itama ta zaunah tareda jawoni , gefenta ,

Tace min zayynah ga alama zakina dinga maida hankali wajen daukar darasi, in the class tafada tana murmushi , tareda shafa tattausaรฑ gashin kaina na usulin buzaye,

Nasaki mirmishi. Wanda har dimple 's dina suka shige ciki gwanin sha'awa,"

Nace minene' in the class?

Dariya tadanyi tace , A cikin aji na koyarda karatu ake nifi 'yata๐Ÿ™‚

Har zansake mgn na hango Alhj yana sau kowร  daga samansa'

Hjy tacemin zayynah maza jeki kema dakin dana kai kaka Salah , inta pito daga wankan kema saiki shiga kiyi,

Namiqe, inacewa to nawuce ;

Alhj yaqaraso gun hjy yakecemata madam yaushe danki zai dawone ? Ko wannan karan bazai zomana nan yaimana hutunba kin hanasa๐Ÿ˜‰
Kamar wancen karon๐Ÿ˜Š?

Murmushi tai itama tace kowan cen' karon alhajina, banhaรฑasร  zuwa mana hutu ba' kasan halin *kareem*'
Cewa yai zaman jirginne ke damunsร  ' Amman jia minyi magana dashi a Twitter Dana bude laptop nawa, yace cikin satinnaรฑ wai zaimana surprise , bazai fadamaรฑa ranan ba saidai migansa 'alhj yai 'Yar dariya yace mai sunan manya kenan ๐Ÿ˜Š, to shiknn Allah kawosa lpia ta amsa da ameen


Da daddare Mina zazzaunne a falo , nasamu wata 'Yar fara qal din mage , inata faman lugwigwita ta danni dai inason mage ๐Ÿ˜
nadage inata shafa mata gashi , itakuwร  tai luff abinta a cinyaรฑa,

Muryar Baffa na tsinkayo yana cewa inshร  Allah u , takwarana gobe zamu dauki hanya r mu takomร wa rugarmu, โœ๐Ÿป
[10/4, 10:14 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค

*FASAHA ONLINE WRITERS*

*Love story*
*fg*9โƒฃ3โƒฃto 9โƒฃ4โƒฃ

Alhj yace, haba takwarana dawurwuri haka. bakwa bari kudan qara hutawa konanda sati daya dai hakan'?

Baffa yace a 'a takwarana hakanma mun gode Allah shibar zumunci, mungode mungode , Wanda yace zai riqema naka bisa amana aibaka da tamfarsa '

Alhj yace to shiknn takwara kaidai kacemin kawai hankalinka nawajen dalibanka ko?

baffa yaidan daria yace kusan hakan takwarana'

Koda lokacin bacci yayi wani daki hajia takaimu mai kyawon gaske tareda gado irin Wanda turawa ke kira nice bed , mukuma hausawa mike cemasa, kwanta sai an tadaka,

Toilet nashiga na sake wanka , Dan gaskia na rigaya da nasaba koda agidane saina yi wankan dare nakejin dadin barci;

Koda na pito na iske kaka tana sallar shafa'e nazauna gefen gadon , danaji taushinsa gwanin dadi , na furta a raina zama kenan inaga an kwanta sa'

Najawo jikkar kayanmu 'nadauko wata fingilan rigata doguwa ta buzaye, irin waddร  ake saqa wa , na zurata na mayarda jikkar inda take,

Ina dawowa nai tsalle na fada saman gadon , jinai katifar tai samadani tadawo qasa, abin gwanin dadi '

Kaka ta ida sallar' ta gama lazuminta duk ina kwance ina kallonta ,

Ta shafa addu'a tamiqe tareda linke sallayar ta'azata gefen gadon'

Tazauna kusa dani tana cewa *zayynah* wai yaushe natsuwa zata gama shigarki ke kuwa' yanxu haka zamutapi mu barki kidinga gwadamisu halinki 'na rashin natsuwa da rawan kai?

Nanfa ba kamarcen bane dakin samu wasu koda ba 'agidannanba dariya za sunamiki da wannan halin naki '

Naturo Dan bakina ina cewa yi haquri kaka na daina '

Kaka salah Tace taficen haka kullum kike fada ay '

Nasaki 'yar siririyan daria nace wollah kaka. Wannan karon dagaske nike nipin gyaran ,

Kaka Salah tasauke ajiyan zuciya' tace to Allah Sa hakan zayynah taciga ba da min fadakarwa maishiga jiki na indinga misu biyayya banda shirme , kuma ko ina na tsinci kaina na yi qoqaren tsare mutuncina , D's

Jikina yai matuqar sanyi da kalamnda kaka take fadamin ' nasha alwashin kuma kwatanta yanda ta koyar dani insha Allah ;
Matsawanai na rungume bayanta a qirjina na kwantar dakaina abayanta ' nadinga cewa yanzu Dan Allah gobe zakutafi da Baffa kubarni da kewarku kaka๐Ÿ˜”'?

Tace insha Allah gobe kamar yanzu ina kan gadonร  na qarfe zayynah๐Ÿ‘ต;

Kasa cewa nai komi nazame na kwanta a gadon , tareda mutsittsikร  yatsun qafana na na shagwaba wa kakaโ˜น, a hakadai har bacci yakwasheรฑi abinka dama da ansha tafiya,

Kaka tai mamu addu'a tashafa mana itama ta kwanta a gefena'

Acikin barcina danakeyi mai dadi "nai mafarkin wani matashin hand som guy Wanda nida shi mike a wata duniya mai yalwa da dadi'
, muna kwance manne da juna' yasaqalo hannayensa ta quguna'yana gogamin karan tsinin hancisa a nawa,yanamin Sumba a dukkan illahirin fuskana'

Cikin kunneรฑa yake radamin babyna zayynah , i luv you as far as in my heart ,
Plesae don't' leave me my zayynah '

Nikuwa idanuwana a lumshe. Inata murmushi'

Nabude baki da ' Yar siririyan muryata nasa
bakina seting kunnensa nai masa wani hot kissing naqara shigewa cikin qirjinsร  yazamanto yanajin tudun dukiyar fulanina a qirjinsa' nasan kuma daman he luv them , sannan nace masa kamar ynda na mannu da jikinka haka nawan , bana fatan wani yashigo tsakani' cikin murna da zumudi yajuyani nakoma qasa y---

Jinai muryaรฑ kaka Salah nacewa zayynah baraki tashi kiyi sallah bร  ne asuba tayi'

Firgigit nai natashi jikina duk ya mutu ,da wannan mafarkin danai '

Murgudร  bakina๐Ÿ˜™ nai ' inafadร  cikin zuciyata, ina ma nasansa dazai wani kama ya rungumemu a jikinsa๐Ÿ˜

Dayasaki baffaรฑa yagansa dasai yaimasa duka,

Gashi yajamana wankan dole kawai da sanyin asubar nan allah sakamin mugu kawai๐Ÿ˜”';

Namiqe xaune nayi addu'ar tashi barci , na sauko daga gadon nanupi bandaki , lokacin kaka har ta kabbara sallah "'

Qarfe 10:00

Mika sauko qasa ina riqeda jikkar kaka Salah mika iskesu Baffa a falo , nandai suka gaggaisร  akahau dining sukayi breakfast,

Kan 1 1 duk mun fito, yimasu rakiya zuwa mota ado direba daman har yagyara farking na mota,

Alhj da hjiya sun hadamusu sha Tara na arziqi suka shiga mota munadagร  juna hannu , fuskana duk hawaye yabatamun' sai kuka nake harda shassheqร ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ๐Ÿ˜ญ;

Inaji ina gani su Baffa suka wuce ๐Ÿš•

Nasake fashewร  da kuk @' hjya ta rungumoni mika shiga ciki---โœ๐Ÿป
[10/4, 10:14 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค
*Editing by aunty just*

*FASAHA ONLINE WRITERS*

*LOVE STORY*
*fg*9โƒฃ5โƒฃto9โƒฃ6โƒฃ

Koda mika shiga cikin falon kan kujera ta zaunar dani, itama ta zauna gefena tajuyoni Mina fuskantar juna,

Tace min kukan ya isa hakanan *xayynah* , tanafadar hakan tana gogemin hawayen fuskana ,

Nadan rage shessheqan danikeyi nakoma ajuyan zuci,

Nandanan kaina naji yadauki dumi 'kankace kwabo wani ciwon kai mai tsanani yasaukomin , kuma nasan Nina jawa kaina shi, Dan shiyasa baffa bayyason yaga ina kuka matsananci, Dan nandanan ciwon kai zai saukomin , Wanda inba kwantawa nai bacci ba bazan taba Samun sauqin saba'

Nazame a hankali na kwanta qasa, hajiya dai nata bina da ido'

Ko minti 2 cikakke banyiba bacci ya daukeni Wanda ke cike da ajiyan zuciya na tsananin kukan danasha ,

Hajiya ta taso ta gyaramin gashin kaina daya rufemin fuskana dikanta, ta dauko follow ta dago kaina tasamin filon , ta gyaran kwanciya Dan na Dan gicce,

Tamiqe tashige beedroom Dan tadan kwanta ta huta , Alhj kuwa daman tun wucewar su baffa yadauki mota yafita,

Abinda ya faru Daren jia shiyakuma zuwarmin a mafarkina,
Wannan karon kuma ganinmu nai tsaye dashi mina sanye da fararen shet a jikinmu da wando jins red , a wani kyakkyawan lambu , mai cikeda korayen ciyayi muna manne da juna , cemin yake babyna nakusa xuwa gareki , ina roqonki plssss ,kodawane irin hali kikaga nazomiki dashi karkisa qiyayyana a zuciyanki, plsss babyna!; kanna kai ga basa amsa mikaji saukar ruwan Sama a kammu,tsawonsa yadan rago Dan yadarani tsawo danshi irin gieant din mazajan nanne,

Muka hada ido ,lokacin kuwa ni har nafara rawar sanyi , haqorana suna hadewa , sbd yanda ruwan yazo da iska da sanyi,

Jinai ya daukeni tsagwayam yanufi wajen shimpidarmu a cikin wata 'Yar bukka irin ta turawannan, yadireni a bisan shimpidar, har lokacin kuwa jikina bai dainamun karkarwar sanyi ba' sai faman rungume jikina nake a qirjina,
Jinai ya dagoni tsagwayam ya bude faffadan qirjinsa , yasani ciki yajawo bargo ya rufemu ruf',

dora fuskansa a bisa qirjina yanata juya fuskarsa a bisansu , nandanan naji jikina yafara amsawa dawani shocking, baidainaba jin ban katsesaba yasa ya fara ballemin boturan gaban rigana , tareda kallon tsakiyan idanuwana , lumshe idanuna nai , Dan bazan jure iya kallon qwayar idon saba ' sbd nakasa fassara ma'anar kallonsa gareni,

Jinai bakinsa a bisa n---
Haba! Wata firgitacciyar qara dana saki itace takawo min qarshen mafarkiรฑ , Ashe qarar danasaki ba iyakarta cikin mafarkiba har saida ta tado hjy gada barcinta,
Aiko da gudunta ta fito taqaraso kaina,

Har lokacin nikuwa bandaina surutai na shirmen mafarkiba kuma ban farkaba , saima jujjuya kaina da Nike cikin magagi nikecewร  ,banso , kai waye ?
Kabi katakuramiรฑ a cikin baccina , tunda nazo garinnร n, kullum saika zoman a mafarkina ' Dan Allah ka bayyanร  naganka a zahiri konaji dadi , inda har kai qoqarin cusa sonka a xuciyar *zayynah* rka kamar yadda ka furta nitakace , nima na amince , plssssss , kazo gareni taqarashe maganar cikin fitar qwalla ๐Ÿ˜ฅ'
Dukda ko idanuntร  suna rufe !โœ๐Ÿป
[10/4, 10:14 AM] Zayyneb Dcmt: ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ””๐Ÿ—ฏ๐Ÿ””๐Ÿ””
*QARAURAWAR SO*

*by xayyneb*๐Ÿ’ค๐Ÿ’ค
*Editing b Anty ju*

*FASAHA ONLINE WRITERS*

*LOVE STORY*
*Fg*9โƒฃ7โƒฃto 9โƒฃ8โƒฃ

Jinai ana girgizani ,
Firgigi nayi nabude ida Nu na,hjy nagani tsaye a kaina ' tana sallallami ,tace ke' *xayynah*
Mike daminki lapiyanki qalau kuwa?
Kodai zafin ciwonne?

Nadago da kaina na dubeta , nasake sunkuyar da kaina qasa , ina murza yatsun hannuna'

Nace wlh hjy wani irin mafarki nake daga jia har zuwa yau Wanda ni kaina bancewa ga inda ya dosa ba'

Hjy tace ,kekuwa kincika shirme xayynah 'Dan kawai kinyi mafarki saiki kama kwara baki kidinga qara?

Ai addu'@ , yakamata kiyi , ni wlh har kinbanma tsoro nazatan wani abune yafaru dake ,

Nabude baki zanyi magana knn mikaji anyo sallama ,

Momy !Momy !

Naji ana kira ' dayake ni naba qofa baya bansan wacece ba , taqaraso tsakiyan falon tasaki trolley din datake jaye dashi ,naga wannan matashiyar budurwar , tanupi hjy da gudunta tafada a jikinta: cikeda shagwaba take cewa, I missing you hajiyana momynร  kuma,

Hajiya ta dagota daga jikinta tace basmah har yanzu dai bakisan kin girmaba ko'

Ta cuno baki tace momyna nai missing nakine

Please Login or Register in order to submit comment