Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

makaranta, an
nemo mata B.U.K level 1 inda su hidaya
ke level 2 hundred, sun fita da aji daya.
Komai nata na tafia neat a gidan ta
kara kiba ta kara fari da kyau kamar ba
ita ba.
Mamyn su farouk ce zaune tana shan
fruits, ta wani bangaren kuma tana
hango dacewar farouk ya auri Rufaidah,
sai dai bata son ta gaya masa ko ta sanya
shi yayi Dole tafi son ya furta da kanshi.
Zata ci gaba dayi masu addua in Akwai
alkhairi Allah yasa masu son junan su, in
hakan ta kasance sai tafi kowa farin ciki.
Areef kam abu kamar wasa wai
karamar magana ta zama babba tun
ranar da umman su tayi mashi maganar
hameedah ya kasa sukuni, karshe dai
har sai da ya kwanta a asibiti, umma
kuwa cewa tayi whl Areef ko zaka mutu
ka dawo sai anyi auran nan,, ka yarda
ko kar ka yarda babu fashi indai nina
haife ka bakai ka haife ni ba.
Bayan sati biyu ne da fitowar shi
daga asibiti, yaje har gida ya samu
farouk yake gaya masa ya taya shi addua
ga abinda umma tace,, farouk ne ya taso
yazo dab dashi yace abokina don Allah
ka saurare ni da kunnen basira, umma
fa uwa ce a gareka kuma nayi imani
baza ta cutar dakai ba, kayi hkr ka
faranta mata, kaga ita kadai kake da ita
baba ya rasu, kayi kokarin faranta mata
har ranar da zaku rabu, kayi mata
biyayya don Allah, whl baza ka tabe ba,
Amman rashin yi mata biyayya akan
auran nan da take son hada ku babban
kuskure ne kayi hakuri kaci gaba da
addua Allah ya sanya albarka a cikin
auran.
Whl ka ganni nan ni har so nike ace
mamy ta hada ni da watan ma don kuwa
yan matan yanzu sai a hankali har
gwara ma ka auri ta gida, wadda kasan
halin ta, akan ta wajen duk mayaudara
ne akasarin su.
Nan dai Areef yayi ajiyar zuciyar yace
a gaskia farouk ko da zan auri
hameedah to whl ba dan ina so ba zan
yarda da auran amman fa ba zata samu
soyayya taba, don teemah kawai nike so
kuma ita zan so, babu wata mace da zata
samu soyayya ta bacin ita.
Kayi hakuri Allah yasa hakan shi yafi
alkhairi, yace amin.
Yana komawa gida direct dakin
umma ya wuce yake gaya mata ya
amince da auran hameedah, umman taji
dadi sosai ta ringa sanya mashi albarka,
yanzu yaushe kake ganin za saka ranar?
Yace ai komai yana wajen ta duk yanda
tayi, sai in suna bukatar kudi suyi
magana zai basu tun daga hada lefe da
sauran abubuwa, tace Allah ya kai mu
lokacin, ai wata daya za a saka yace yayi
ummina tace yau babana Allah ya maka
albarka.
Nan dai ya tashi ya dakyar don
baijin kwari a jikin shi ya nufi dakin shi.
Umma kam komai yayi daidai harta
fara shirin biki, ankai kudin aure gidan
su hameedah,, ranar Friday ma zasu tafi
Dubai ita kawarta don zuwa hada lefe da
abinda ya kamata.
Hameedah kam sai murna take Allah
ya amsa adduar don tana kaunar yaya
Areef sosai shine dai baya sonta, kuma
ta dau alwashin sai ta bi duk wata hanya
da zata bi,, don ta shawo kansa ya sota
fiye da kowacce mace.
Toh masu karatu muje zuwa dai don
jin yanda zata kasance ku biyo …..
S B R
[truncated by WhatsApp]
[10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[30/7/08:11pm]
SADEEY S ADAM
&
RASH KARDAM
WITH
BEEBAH LUV
MA’YAUDARAH
55~58
Bikin Hameedah da Areef ya kankama
dan an Gama shirya komai lkci kawai
ake jira…
Areef kuwa hankalinsa a tashe
yake duk da dai yayi biyayya amma har
yanxu baya jin ko k’wayar son
hameedah a ransa.
****************
Teemah harka ta k’ara kankama
karuwanci ba Kama hannun yaro,ta
k’ara goge Wa a fagen yaudara..
ta zama hajjaju, yanxu gani take tafi
k’arfin duk Wanda baya da ‘ya’yan
banki(kud’i)
Idan ‘yan mutuncinta sun motsa
takan ziyarci futha kuma duk lkcin da
taje Sai taji kishi kuma tayi sha’awar
dama itace futha
amma idan ta hango zaman guri
d’aya kullun Sai taji auren ya
gundireta…
Ji take bazata iya zaman guri d’aya
ba saboda ta Saba samari na d’aukar
suje guraren shak’atawa kala2,dan hka
gidansu ma bata fiya zamansa ba.
Yau ma kamar kullun ta Gama
shirinta tsaf Tana jiran azo a d’auke ta
su tafi yawon shashancin
Ummanta ce taxo ta zauna kusa da
ita tace “inaso ki nutsu muyi mgna”
“Ina jinki”ta fad’a ba tare da ta
kalleta ba dan kuwa tasan da wacce taxo.
“Fatima inaso ki nutsu ki gane cewa
ita duniyar nan ba Aljanna bace,ya
kamata ki gane kuma ki dawo
hayyacinki”
tad’an yatsina fuska tace “umma wai me
kuma akace na yi?su fa mutane basa son
ganin cigaban mutum sunfi son kullun su
ganshi cikin bak’in ciki”
“cigaban wace Mace ce kamarki
xa’ace har yanxu bata da ko tsayayyen
mijin Aure?tirr da irin wannan cigaban
wlh wannan ci bayane”
“Amma umma……….ki rufamin baki
fatima”
Ta dakatar da ita sannan taci gaba da
fad’in “yau kusan wata 3 dayin bikin
k’awarki amma ko a jikinki,duk sa’oinki
sunyi Aure wasu ma harda ‘ya’yansu
amma ke na rasa abinda ke
damunki,shin Ina kike xuwa kullun dan
kinga na zuba miki ido ko?to wlh kiyi a
hankali duk wannan tarin samarin ace
kin rasa Wanda zaki fidda a ciki?karki
Manta idan an ciza……dole a hura..ki bi
duniya a hankali dai”
“Umma sanin kanki ne nima inason in
ganni a d’akin mijina to ai komai
yanada lkcin umma lkcina ne har yanxu
Allah bai kawo ba”
“Allah ya kawo mana ke dai kikai watsi
da damarki sbda ‘ya’yan masu hunnu da
shuni sun hure miki ido,ki dai bi a
sannu Kar kixo ki rasa mijin Aure
kinsan dai hak’orin dariya shi ke cizon
yatsa”
Duk da dai ta ji haushin kalaman
umman tata amma Sai ta daure tayi
dariya tace “Umma karki damu kinsan
guga inta dad’e a ruwa tafi d’ebo da
yawa,na tabbata akwai Wani tanadi da
ubangiji yamin Wanda Sai kunsha
mamaki kedai Kisha kurumin ki”
(mudai cewa mukai a hakan )
“Allah ya tabbatar da alkhairi”
“Amin umma hka nake so ki tayani
da addu’a”
“Inayi ai kullun cikin yi muku nake”
Haka suka b’arke da hira har xuwa lkcin
tafiyar Teemah sannan tayi Wa umma
sallama ta tafi.
Written by
S B R
[Truncated by whatsapp].
[10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[7/5/6:47am]
RASH KARDAM
&
SADEEY S ADAM
WITH
BEEBAH LUV
MAYA’UDARA
58-60
Teemah tayi sallama wa Umma ta fito
daga gida wani had’add’e mota ne ya
faka a gabanta tare da zuuge glass d’in
motar fiskansa d’auke da murmushi ya
sakar ma Teemah. Cikin ta kun k’asaita
Teemah ta iso gefen motar ta kallesa ta
ce”ai na d’auka bazaka zo ba ne”. Sai da
yayi murmushi ya ce”hajjaju ayi hak’uri
go slow na samu a hanya shiyasa”.
Fitowa yayi ya bud’e mata k’ofar gaban
motan tashiga ciki suka bar unguwan.
Tafiya mai nisa sukayi kafin suka iso
k’ofar wani makeken hotel nan ya danna
hanci motarsa suna zuwa suka fito d’aki
mai lamba goma suka shiga ba laifi
d’akin ya mugun had’uwa bana wasa ba.
Teemah suna Shiga tayi jifa da Jakarta ta
cire hijab d’in dake jikinta wani riga ne
mai hannu best ko cibi bai sauk’a mata
ba, sai wando wanda zamu iya kiransa
da shi da babu duk d’aya ne.
A hankali Nass ya tako gunta tare da
janyota jikinsa nan ta fara aika mata da
sak’onninsa ganin sun shagala da yawa
muka bar d’akin.
Teemah basu bar hotel d’innan ba sai da
magriba ta koma gida cikin ladabi in ka
ganta ka d’auka Ustaziyan gasky ne
hijab har k’asa ga nikaf Umma har tana
alfahari da Teemah tana da nutsuwa,
hankali ga kamun kai.************
3 months latter.
Teemah na hango kwance ta rame tayi
bak’i bakintan nan yayi ja-jazur da shi
ya d’an kwaile, Umma ne ta shigo tana
fad’a “Fatima nikam nagaji kulum kina
kwance a gida ga ciwo sai cinye ki
yakeyi jibi fa yanda kika dawo duk ki
banki kin gama ramewa”. Da kyar
Teema ta d’ago kai ko da muka kalleta
sai da mikayi baya da sauri wannan
kamar ba Teemah ba.
Kasa juran d’aga kai d’in tayi ta koma
ta kwanta Umma ne ta fita ta kira mai
Napep ya zo har k’ofar gida ta shiga ta
d’auko Teemah da ta dawo kamar
kwarangwal suka shiga Napep suka tafi
Asibiti.
Suna zuwa aka basu gado nan aka d’ibi
jininta da fitsarinta aka gwada gwajin
farko ya nuna musu cutar k’anjamau
take d’auke da shi, Likitan da kansa yazo
ya samu Umma sai da ya mata nasiha
kafin ya juya ya kalli Teemah cikin ta
kaici da yaji budurwa ce ya ce Fatima
kina s’auke da cuta mai karya garkuwan
d’an Adam, take Teema ta zaro ido
Umma kam yankan jiki tayi ta fad’i a
k’asa sumamiya, Teema jiki ba k’arfi ba
halin mik’ewa sai dai kuka takeyi, Dr ne
ya kira nurse sukazo bata taimakon
gaggawa.
Cikin ikon Allah ta far-fad’o nan ta fara
tuna mai ya faru kuka ta saki tana
fad’in Fatima ta cucesu ta zubar musu da
mutunci yaushe ta yarda tarbiyan da ta
bata da wannan tunanin bacci ya sake
d’aukanta.
Gidansu Areef biki ake ba sanya Walima
kawai hajiya ta shirya sai dinner ranar
jumma’a bayan Sallah jumma’a dubban
mutane suka shaida auren Areef da
Hameeda auren da ya tara manyan
mutane bayan d’aurin aure maza suka
wuce hotel dan gabatar da liyafa da
yamma kuma akayi waliman mata,
waliman da ya tara jama’a anyi wa’azi
mai ratsa jiki wanda yasaka Hameeda
jin zatai ma Areef biyayya koda zai
wukanta ta don niman aljannata.
Da daddare angwaye suka fito cikin
shirin dinner ko da na kallo Areef shima
yasha kyau ana haka a ka kwashi
kawaye suwa gun Hafcy na hango ta
rik’o hannun Hameeda cikin wani cut
less mai tsada sai kyalli takeyi ko da
Areef ya hango ta sai da k’irjinsa ya
bada rass!!! Cikin zuciyarsa ko cewa ya
ke”tsarki ya tabbata ga ubangijin halita
tabbas Hameeda tayi kyau ba na wasa
ba”. Kasa d’auke idonsa yayi ko mai ya
tuna take yayi tsaki yana mai jin
haushin kansa da irin kallon da yake
mata.
Written by
S B R
[Truncated by Whatsapp].
[10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[10/08/08:41]
_SADEEY S ADAM_
&
_BEEBAH LUV_
WITH
_RASH KARDAM_
*MA’YAUDARAH*
*66-70*
Teemah ce zaune a falon gidansu tayi
tagumi da hannunta duka biyun..
tsantsar nadama take, tayi nadamar
abubuwan da ta aikata a rayuwarta…
Yanxu Ina samarin?Ina gayun?Ina ado
da kwalliyar??,
Duk babu kowa ya gujeta k’awayenta
duk sun gujeta idan ka d’auke Futha da
take k’aunarta saboda Allah…
Umman ta ce ta shigo taga halin da
take ciki,ga abincinta a gefe har ya fara
hucewa..
Nasiha da rarrashi ta zauna tana yi mata
wanda sai da ta zubda hawaye sosai..
Ina ma ace tun kafin wannan larurar ta
sameta ta nutsi…
Kaii d’an adam yaji tsoran Allah dan
kuwa ita darasi ce ga duk wata wadda
take biyewa samari da wadda take cewa
sai ta wanki gara..
Tabbas gara zai wanke ta ya barta a
banza..
A yau Umma kam taji dad’i tunda har
teemah tana kuka sbda nadama….
**********************
Ta gama shirya komai na lunch akan
dining table..
Sannan ta Shiga d’aki tayi wanka ta
cancad’a kwalliya cikin wani _Orange
lace_ d’inkin _towel work_ ne yayi mata
d’as a jiki tayi kyau sosai….
Ita kanta saida ta tsaya a gaban _mirror_
tana fad’in Anya nice kuwa..??
Falo ta sake dawo wa,taga har yanxu bai
fito ba kusan awa uku da gama girkin
har taje tayi wanka amma shiru kamar
baya gidan??
Cikin fargaba ta nufi d’akinsa,
Da sallamarta ta Shiga
Yana zaune a k’asa Yana danna
laptop,ba mamaki _chatting_ yake a
_Facebook_ dan kuwa sai smiling yake
yana ganin ta ya had’e rai kamar ba’a
tab’a halittar annuri a fuskarsa ba..
A tsorace ta tsugunnan tace “Yaya
an kammala abinci fa”
*Mtswww* yaja tsoki ya cigaba da
abinda yake…
irin Mai mijin nan sai ta saka
hannu ta rufe laptop d’in cikin tsokana
tace “ka gama cin abinci kafin ka
cigaba,kasan bana son ka zauna da
yunwa”
Mari ya kifa mata har sau biyu “ke wace
irin jahila ce da xaki rufe Abu ba tare da
an kashe ba,uban wayace ki shigomin
d’aki,to baxan ci abincin ba dole ne?
stupid” ya fad’a cikin d’aga murya…
Rik’e kuncinta tayi sannan ta tashi ta
fita tana kuka.
_By S B R _
[Truncated by Whatsapp]

[10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
[6/8/2:00pm]
BEEBAHLUV
&
RASH KARDAM
WITH
SADEEY S ADAM
MA’YAUDARAH
60~65
Dinner tayi dinner anci, ansha,
kuma anci uban nera don kuwa tayi
kuka sosai,, ba a tashi ba sai karfe sha
biyu na dare, amarya kam tayi farin jini
kuma tayi bala’in kyau, kowa yabon ta
yake kamar wata Queen,, abokan shi
kuwa sai yabon ta suke suna cewa yayi
dacen mata, yakan ji dadi a lokacin da
aka yaben ta, shima tana birge shi kuma
yakan ji wani abu a zuciyar shi sai dai
kuma kome yake tunawa sai yaji yatsane
ta.
Angwaye sun maida amare gida
akan zuwa gobe za a zo daukan amarya,
a mota ango yakan dan janta da hira
kadan badan yana so ba.
Washe gari ankai amarya gidanta,
kawayen da abokai sunyi chilling masu
yin yan mata nayi ansha Cece kuce
shidai ango ba ehm ba ehm ehm, yana ta
imagining dama teemah shi ce abar
kaunar shi da yafi kowa jin dadi, haka
dai suka watse aka bar amarya da ango,
bayan rakiyar abokan shi ya dawo ya
wuce dakin shi ya shiga wanka bai kuma
waiwayen ta ba ya kwanta baccin ma
dai sai barawo ne ya dauke shi.
Itama bayan fitar su bata wani damu
da dawowar shi ba tayi wanka tayi
Sallah tayi addu a ta kwanta daman
akwai gajia a tare da ita bata farka ba
sai 6 har sai da tayi lattin sallar asuba.
Da safe ta cancada kwalliyarta, tace
bari ta zagaya gidan ta gani tayi
deciding abinda zata nemar masu su ci,
ta fita tayi zagayen gidan yayi kyau
sosai ta gode ma Allah ta daya kaita
wannan matsayin,, taji ana knocking
tana budewa taga yan aike daga gidan su
an kawo abinci,, ta jere su bisa dining
table ta dauko duk abinda za a bukata ta
zauna jiran megidan bai tashi fitowa ba
sai kusan 12 saura yayi wanka sai
kanshi yake, yana fitowa taje ta tare shi
ya Areef ina kwana ya amsa a takaice,
da fatan an tashi lfy tace lfy kalau, ga
abinci umma ta aiko mana, ok na koshi
yayi hanyar waje nizan fita bai jira
amsar taba yayi waje,.
Umman teemah ta dade bata farka
ba, wannan ta farfado har a lokacin
kuka take tana Allah wadai da halin da
teemah ta tsinci kanta. Nan dai likita ya
bata baki akan tayi hakuri jarabawa ce
ta ubangiji haka Allah ya kaddaro, ta
kwantar da hankalinta zai dora teemah
akan maganin dazai bata, zata dade
sosai a dunia akwai masu cutar in ta
gansu ma baza tace suna da cutar ba, sai
sanda kwanan su ya kare, yanzu ma
dasun zo da wuri asibitin ya daura ta
akan maganin tun wuri da bai nuna a
jikin ta ba haka, sai dai addua Allah ya
kara kare wa, nan dai yayi tayi wa
teemah fada tana ta zubar da kwalla
tana dana sanin rayuwar datai a baya,
Allah ya yafe mata tana ta kuka. Nan dai
doctor ya bata gado don samun karfin
jikin ta da kuma lfyr ta.
Su Futha amare ana can ana tashan
luv, don kuwa komai bata nema ta rasa
ba haka duk wani motsi nata sai ya
tambaya any problem? An sai mata wata
arniyar mota “BENZ” sannan sunje
honeymoon kusan 4 months sukai acan
kasa she 4 suka je DUBAI, LONDON,
INDIA, sai kuma suka wuce umara wato
SAUDIA,, kai!!! A gaskia Futha tayi dace
Allah yaba yan baya ma haka,, sun dawo
9ja a lokacin da karamin cikin ta wata 4
cip cip,, tayi zagayen dangi daga nan ta
kira teemah tace zata zo ta kawo mata
tsaraba tace sai tazo bata da lfy ma.
Ta wuce daga gidan su, ta shiga da
sallamar ta,, ta tarar da umman su a
tsakar gida tana zaune ta gaishe a a
Futha yaushe kuka dawo ne? Tace yau
kwana 5 umma Allah sarki an dawo lfy,
tace lfy kalau umma ya mai jiki ?
Hmmm umma tace da sauki ta nuna
alamar damuwa ai sai dai addua Futha
Allah dai ya shirya mana zuri a tace
Amin,, Futha dai bata gane me umma ke
nufi ba don bata san meke faruwa ba, Ta
mika mata tsarabar data kawo mata
sannan ta shige dakin, Allah sarki umma
harda kwallar ta dama tata yar itama
bata jefa kanta cikin ukuba ba gashi nan
yanzu tana dana sanin rayuwar ta.
Futha na shiga da gudu ta taso ta
rungume ta tana murna,, Futha tace
teemah wannan wane irin ciwo ne lokaci
kankani kika koma haka kinyi baki,, kin
kwanjame, kin rame, kamar bake ba,,
hmmm nan fa suka zauna teemah ta fara
kuka me tsuma rai hmm kedai bari yar
uwa, kiga dai yanda na koma naki jin
shawarar da kike ban da umma take ban
da sauran mutane keban, yanzu ga halin
dana saka kaina a ciki nan dai ta bama
Futha labarin komai game da ciwon ta
har yanda DR ya bata magani shine fa
dalilin samun lafiyar ta har ta fara
murmure wa,, yanzu dan kudin data tara
dasu take siyan magani,, amman da kam
whl da ta ganta baza ta gane taba,,, gashi
yan unguwa da yan gari duk sunsan
halin da nike ciki duk inda nayi sai
daria ake min nikam na shiga uku na
lalace,, kuma kinsan waya saka mun
wannan cutar Khalid ne,, sai gashi mun
hadu dashi a wurin blood test,,, yace
zaizo gida muyi magana har yau bai
zoba.. Futha tayi kuka tayi kuka sosai ta
kuma tausaya wa kawarta,, nan dai tayi
mata nasiha me shiga jiki, (“Toh yan
uwa maza da mata kundai ga halin da
kawata kuma aminiya ta futha yau
yanda Allah ya maida ita kundai ji
yanda take ada tana ganin rayuwar
banza ita ce rayuwa har gani take ni ban
waye ba, rayuwar banza lyk tara samari
wannan yazo wancan yazo, aje ayi
masha ‘a a dawo ba a tsoron Allah ba a
tunanin gaba,, kece wancan hotel
wancan gida duk kina tunanin birgewa
ne, whl ba birgewa bane karshe dai sai
mutum yayi dana sanin rayuwa ko baka
dauki cuta ba sai kayi dana sani,, don
haka ina me bamu shawara yan uwa
akan mubi dunia a sannu ba
madauwama bace kuma abinda ka
shuka shi zaka girba,, yar uwa kar kiyi
ikirarin cewa sai me kudi zaki aura, da
talauci da arziki duk na Allah ne, kedai
kiyi adduar Allah yayi maki zabi nagari
a duk abinda kika sa gaba,, Allah yasa
mu dace dunia da lahira.”) Ta bata
shawarwari masu amfani a gareta da
sauran yan uwa musulmai tace taci gaba
da istigfari Allah yana son mai neman
yafiya a gareshi,,, Ya Allah ka yafe mana
dukkan kurakuran mu amin..sai kusan
maghrib tabar gidan akan sai ta dawo
duba ita nxt tym..
Kai teemah ranar tayi dana sanin
rayuwa tayi kuka tayi kuka har ta gaji ta
kuma dau alkawarin duqufa ta nemi
aljannar ta, dayin biyayya ga mahaifiyar
ta da tilon yayan ta wanda yake uba a
gareta a yanzu.
**Bayan shekara daya**
Sai muka leka gidan su farouk inda
muka hango su Rufaidah an zama yan
gida hankalinta a kwance ta murmure
abinta tana ta zuwa skul,, gata da
kokari,,, tana birge farouk kullum ji yake
yana kara kaunar ta a ranshi, komai
take so shi ake mata a gidan tun daga
kan mummy har su farouk,,, farouk ya
kasa sanar da ita har yanzu yana sonta
sai dai mummy ta gano shi kuma ita ma
ta gano akwai wata a kasa don kullum
suna tare in bata je skul ba daga ya
dawo daga aiki,, mummy tayi deciding
tayi musu maganar tunda taga alamar a
tartare dasu,.
Hakan kuwa akai ta tara su a
parlour, take ce akwai magana duk suka
saurare ta, tace so take ta aurad da kowa
daga cikin su,, shi tayi mashi mata itama
tayi mata miji,, nan fa suka fara kallon
kallo,, toh fa me mummy ke nufi su dai
sunsan suna son juna Amman basu
gayawa juna ba gashi mummy na shirin
yi masu tabargaza yaya kenan??
Mummy tace kai farouk yar gidan
Anty Laura, ke kuma rufaida dan gidan
baba sani wato haisam,, nan gumi ya
fara aikinsa a jikin su, ita dai rufaida
baza ta iya musawa ba duk wanda
mummy ta bata zata karba, Amman fa
tana kaunar ya farouk,,,. Farouk ne yayi
gyaran murya mummy…… mummy….. ya
kasa magana, tayi daria menene akwai
magana ne? Yace ehhh tace ina jinka,
daman… daman… ya kasa maganar ka
fadi maganar ka ina jinka. Whl mummy
ina da wadda nike so,, tayi murmushi
irin na manya,, tace wacece wadda kake
so din baka gayan ba sai yanzu danai
maka matar ai babu fashi.
Da sauri ya kalli rufaidah,, don Allah
mummy kiyi hakuri whl inban aure ta
ba zan iya shiga wani hali, ina sonta
kamar raina,, wai wacece ne a ina take
yar waye yar wata unguwar ce? Sai da
ya gyara zama sannan yace mummy ba
wata bace a cikin gidan ki take gata ma
a kusa dake ya nuna Rufaidah..
Mummy tayi daria take YAN QOTA ai
daman so nake na tabbatar da abinda
nike gani kuma nike ji a wurin kannan
ku, toh Alhamdulillah daman haka nike
son ji komai ya yi Allah ya sanya
alkhairi a cikin lamarin,, yanzu sai muje
neman auran ta a wurin yayarta ko,,
Rufaidah da sauri tace a a mummy whl
sai dai a tafi katsina daga baya a gaya
mata in anje.
Nan dai suka tsara yanda abun zai
kasance zasu je katsina neman auran
nata, don mummy bata son aja abun da
sauri take so ayi wata daya kacal za a
saka, murna a gidan ba a magana har fa
yar walima aka hada….
Urs…..
S B R
[truncated by WhatsApp]
[10:15PM, 9/21/2016] Rash Kardam:
RASH KARDAM
&
SADEEY S ADAM
WITH
BEEBAH LUV
*MA’YAUDARAH*
_71-75_
Areef wulak’anci kala-kala yake ma
Hameeda tana hakuri da shi in ya
kuntata mata sai ta shiga d’aki tayi
kukanta ta share hawaye, addu’ar ta
kulun Allah ya karkato mata da hankalin
mijinta gareta.
Bikin farouk ya kan-kama yau saura sati
guda duk wani abunda ya dace sunyi
Hajiyar Farouk da kanta ta ke gyara
Rufaida.
*6 DAYS LATER*
Yau juma’a dubban mutane suka shaida
d’aurin auren Umar Farouk da Rufaida
abun sai fatan Allah ya basu zaman lfya
, abin sai son barka, basuyi wani
shagalin k’arya ba Hajiya ce ta shirya
musu walima da yamma aka gabatar.
Da dadare aka kai Amarya d’akinta,
zuwa tara na dare abokai suka rako
ango suka musu nasiha gami da
barkwanci daga nan suka musu sallama,
muma kuma muka mik’e tare da basu
guri don wannan lokacin sirrinsune…
Aunty Farha kuwa tayi nadama
sosai kuka taxo tana yiwa Rufaida kan ta
yafe mata abinda tayi mata dan kuwa
batayi mata rik’on kirki ba…
‘yar Tata da take tak’ama da ita ta kwaso
musu cikin shege ga mijin aunty Farha
ya saketa ya kora su yace baxai iya
zama dasu ba…
Ga yarinyar kullun laulayi take tana
kwance ba lfya…
Tana kuka tana bawa Rufaida hkri kan
ta taimakesu da ko dubu biyu ce suci
abinci…
Kuka sosai Rufaida take ta Shiga
bedroom d’inta ta d’akko dubu goma ta
bawa Aunty Farha…
Sannan tace zata xo ta dubasu idan yaya
Farouq ya dawo…
Haka Aunty Farha ta tafi tana kuka tana
regretting abinda ta aikata ma
Rufaida,yanxu gata cikin daula su suna
cikin tsumma…(Duniya budurwar
wawa).
***********
Areef ne zaune a office wayarsa tayi
k’ara yana dagawa yaga abokinsa Dr
Saif ne ya ke kiransa. Ya d’aga tare da
fadin” Allah ya kare mana likitan
zamani”. Dr Saif ya ce”kana inane Areef
maza kazo yanzu kaga wani abun
mamaki ina cikin asibiti”. Kashe wayar
yayi ba tare da ya ji abunda Areef zai ce
ba.
Cikin fargaba Areef ya dauko key din
motarsa ya nufi asibiti.
Office din Dr Saif ya nufa yana zuwa ya
basa hannu suka gaisa.
dr Saif ya d’akko wani file ya turo
gaban Areef ya ce “duba ka gani”
Cikin fargaba ya ce”na menene wannan
file din?” Dr Saif ya ce” in ka duba zaka
gani”.
Da sauri Areef ya bude, rass!! K’irjinsa
ya buga, ba komai ya gani ba illa
takardan gwajin Teemah da cutar da
take fama da ita har yayi worse sosai.
Hawaye ne ya ke zuba daga idonsa
“tabbas Teema kinci amana ta ni inanan
ina fama da soyayyarki ko matana naki
kusantarta sabida sonki”. Dr Saif ya
ce”zo ka gani”
haka Areef ya rink’a binsa sukaje gun
da ake taron k’anjamau nan yaga Teema
ido-da-ido ana raba mudu gani kyauta.
Take yaji kansa ya sara godiya yayi ma
Dr Saif ya shiga mota kasa komawa
office yayi ya nufi gida.
Yana zuwa ya samu Hameeda tana kuka
ta kifa kanta akan kujera bata san da
zuwan Areef ba. Jikinsa yayi sanyi sai
yanzu ya tuna da ita marainiyace gashi
Hajiyarsa ta basa amanarta. Jikinsa yayi
sanyi a hankali ya taka yaje gun da ta
kwanta ya sanya fuskarta akan nata
shima sai yaji hawaye na sauka masa.
Kamshin turarensa ne ya dawo da ita
daga duniyar tunanin da take yi sai
tajishi a jikinta kaman a mafarki. a
hankali ta daga fuskarta ganin hawaye a
idonsa abun ya bata mamaki, Areef na
ganin ta dago ya durkusa akan
gwiwansa ya had’a hannayensa yana
rokonta gafara nan tasaki kuka tafad’a
jikinsa…
tun daga lokacin suka shirya don
bata da wasu gatan da ya wuce su.
Rayuwa mai dadi su ka gina cike da ban
sha’awa har yana mamakin irin kaunar
da yakeyi ma Hameeda ba yaso yayi nisa
da ita.
Teema a irin taron masu ciwon
kanjamau da take zuwa wani zuwan da
tayi suka had’u da Khaleed nan yaba ta
hakuri nan suka dai-dai ta kansu akan
zatayi Istibura’i sai ya aureta tun daga
lokacin ta bar gari ta tafi gun yan uwan
Ummata….
***********
FIVE YEARS LATER…
Hameeda na hango da yan ‘ya’yanta sun
fito cikin super market Areef na rike da
key din motansa, Teema da Khaleed
suma sun zo, nan suka gaisa Teema taga
matar Areef ta hadu iya haduwa amma
ina yanzu ya mata nisa gata matar wani
fatan alkairi sukayi majuna su Areef
suka shiga mota suka tafi.
*ALHAMDULILAH!*
ala kulli halin..
_komai yayi farko zaiyi k’arshe_
_Anan muka kawo k’arshen wannan
littafin mai suna *MA’YAUDARA*
kuskuren ciki da mukayi Allah ya yafe
mana_ Ameen
*SADAUKARWA*
Mun sadaukar da wannan littafin ga
‘Yan Mata da Samarin Zamani…
*WANNAN LITTAFIN TUKWICI NE GA*
_’Danmu Abin Alfaharin mu our luvly
*AREEF* Allah ya raya mana Kai cikin
tafarkin gskya tare da sunnahr manxon
Allah (S.A.W)_
*Godiya ta musamman ga*
_dukkan group din *Online Hausa
Writers* Allah ya barmu tare.
*TSOKACI*
Yan Mata da Matasan zamani kun mai
da yaudara ya dawo abin ado a gare ku
kunga kadan daga illan masu yaudara da
kwadayin abun hannu saurayi ya kai
Teema ga fad’awa halaka da nadama
mai tarin yawa Allah ya kyauta yasa mu
gane gsky Ameen.
Urs S B R..
Munai muku fatan alkhairi….
Luv u alot swi[truncated by WhatsApp]

Copied By
HAYATU BABA ZUBAIRU
(admin
Novels villa
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
And
Cool novel, makeup and cooking)

WHATSAPP NO:
07039625239

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

Please Login or Register in order to submit comment