Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

talatainin dare ne ai.To amma a yanxu da bala ya haska agogo da fitilarsa sai yaga ashema gari yawaye domin qarfe shida da yan mintuna na safe.

Ba abanza bala yake wannan muguwar farkawar ba ba domin dimbin bashin da ake binda ko sayar dashi akayi baxai iya biya ba.

Bashin farko dai wani dattijo ne yake binsa dari biyar da ashirin kudun goro.Hakanan wani mai tireda yana binsa kudin taba yakai naira dubu hudu, sannan akwai abokinsa dayake binsa naira dubu dari da ashirin lokacin daxai sayi gidansa wanda yake ciki a yanxu.Anfi shekara yana alqawari yana sabawa don haka yanxu abokin nasa yakai maqura tun yana kallon kan bala da gashi har yaxo yafara cewa xai miqashi gurin hukuma duk wannan rigimar mai sauqi ce akan gidan dan qanwarsa daya siyar.
Gidajen guda uku ne da mahaifin yaron ya mutu yabar masa tun yana dan jariri.Qanwarsa ta amince dashi don haka saita miqa masa takardun gidan sannu a hankali bala yabi duk gidajen ya sayar ya bushe sama da kashi daya bisa biyar na kudin kashi biyu ya miqasu ga matan banxa sauran adadin kuma ya kashesu a gun abokansu yan duniya.Don haka a yanxu kakannin wannan yaron bangaren uba sun fara shirin maka bala a kotu wadannan qananan basussuka dama wasu sama da guda arbain wadanda shi kansa baxai iya tunawa dasy ba su suka tru suka hanashi bacci suka kuma hanashi sakat a rayuwarsa ta duniya.

Bala da akafi sani da likitan mata ,,,,,
kura da kan Rago

11

Bala da akafi sano da likitan mata ne dogo mai wankan talwada yan dakon kai kamar jirgin qasa qirar da.Hakanan yana da wasu dogwayen yan yatsu sirara masu kama da mabirgin miya, yan yatsun da suka dade suna barna a doron qasa.shekaru goma sha biyar da suke wuce Bala bashi da aikin daya wuce xubarwa da mata ciki. Don haka a yanxu da bala yajingina da jikin bangon yana bulbula hayaqin tabar sama sai yafara Allah wadai da wannan mummunar sanaar tada bawai don ya yarda da muninta ba sai dai duk irin kudin dyake samu basu tsinana masa komai ba dai bashin da ake binsa.
"To daman matisyata duk qananan karuwai ne suke tayi min sintiri"
Bala yafada a fili kai kacr dashi da wani yake magana. Ya xuqi hayaqin sigarin sannan yafesa sama yabishi da kallo dai ya shiga tunani .lokaci guda kuma yana adduar Allah yasa maganar tsohon dan giyar nan taxama gaskiya. duk dayaji abin kamar almara..Kura da kan Rago

12

Adai dai lokacinne yaji ana buga qofar shigowa gidan cikin dauri bala ya miqe dagashi sai gajeren wando.ya lalubi jallabiyya launin makuba yasa kana ya nufi qofar dakin cikin sauri kuma cikin mamaki domin ga al ada maziyartansa cikin tsakar dare suke xuwa ba kamar haka ba da sassafe. ko kuwa matar da tsohon dan giyar yacr zatazo ne.yatambayi kansa. Aka sake buga qofar nabiyu
"Ganinan ganinan in xuwa"
bala yace sannan sai yaji gabansa ya fadi saar da wani tunani yazo masa."kada dai kakannin yaron nan ne maraya, to yaya xaiyi? wannan tunnin shi yasanyashi canxa shawara, don haka maimakon yabude qofar sai ya sanya bakinsa da gefen jallabiyar kana ya shaqe murya yace.
"wanene?"
"nice" wata zazzaqae murya mai kama da darewa tacr a raunane.
Cikin sauri jiki na rawa bala yasaki wani tattausan murmushi sannn ya xare sakatar qofar gidan.To a wannan lokacin ne ya hadu da abin daya sa numfashinsa tsayawa cak.
nashiga ukua.saar daya qara dubanta a karo na biyu da farko ya dauka matar da mahaukacin dan giyar nan yace xataxo ne.Amma saar daya ga kyakykyawar fuskarta sai yaji shakkun hakan shi dama yasan da wahala idan maganar dan giyannan yace gaskiyane.
"Zita kai amma dai wannaa mace tayi kyan dan maciji indai ciki xaa xubar mata"yafada a ransa.lokaci guda kuma yakalli fararen idanu matar dake tsaye a qofa tana karkada maquliin mota.Akwai alamar damuwa qarara a fuskarta hakann indai ba idanunsa ne suke qoqarin yi masa gixo ba yaso yago shatin hawaye a kyakykyawan kumatunta mai annuriKura da kan Rago

13

sannu daxuwa' yasami bakinsa na fadi batare daya shirya ba. yana fada axuciyarsa yau kuma wannan kyakykyawar shedaniyar nasamu.
"mushiga daga ciki" matar tace dashi cikin rarraunar murya tana kada muquliin hannunta. tana yan waige waige a farfajiyar gidan.Bala yalura kamar a tsorace take meyiwuwa bata son kowa yasan taxone.wannan ba sabon abu bane domin yasha ganin daruruwan matan da suke xuwa gurinsa.Don haka baiyi musu ba sai ya juya yana dan waigenta a fakaice.ga mamakinsa sai yaga kamar tana dingishi amma bashi da tabbacin hakan tunda dai har yanxu bai iya juyawa yayi mata kallon tsaf ba. Suka shiga tsakiar farfajiyar gidan mai yan shuke shuken furanni na qarfin hali acan gefe guda har da wata bishiyar ayaba.wani sangartaccen famfo sai xubar daruwa yake a qarqashinta.mai yiwuwa mantawa yayi bai kashe ba tun daren jiya.
"ma iya shiga daga ciki? bala ya tambaya yana shakka tare da kallon qofar dakin.
"Dazaifi dai " matar ta fda sannan ta miqa dantalelen hannunta ta tsinko wani fure dake kusa da ita, ta sunsuna sannan ta jefar. bala yaji wani farin ciki ya lullubeshi .'Tabbas cikine da ita. Suka shiga wani dakin shaqatawa irin na tuxurai.kujeru takwas ne suka yi wa dakin qawanya.A tsakiyarsu akwai teburi na katako mai sheqi dauke da wani kurtun zuba shayi, da faranti guda biyu wadanda ke dauke da guntun shinkafa da taliya da bal yaci jiya.Tuni har sun fara wari.

Matar ta dubi kurtun shayin cikin damuw.
"kayi haquri na tasheka da sassfe ko?hala ma ko break fast bakayi ba"
"ah ah wallahi." Bala yafada yana kikkifta idanu kamar barawon akuya."zauna mana"
Matar ta xauna a hkali gefen kujera .xamanga keda wuya sai dan yalolon gyalen dake kanta ya xame yafadi a qasa.Bala yariqe numfashi saar dayaci karo da kykykyawar surarta ta bayyana a fili.sai da mayafin ya sulube ya fahimci ashema shekrunta basu kai yanda yake xato ba.Tabbas yarinyace baxata wuce irin budurwa a birni ba.

Bala yaqurawa gashin kanta idanu wanda ya sauka har kafadarta sai sheqi yake duk kuwa dacewa har yanxu da sauran duhu.

'kaine likita bala?"matar ta tambaya kanta na sunkuye batare data damu data gyara mayafin ba.
"sunana kenan"bala yafada bakinsa na rawa,a xuciyarsa kuma yana cewa 'oh lallai duniya tagama lalacewa,yaishe xaace kyakykyawar yarinya kamar wannan ta shiga karuwancin da har xata dau ciki?'
wannan tunanin shiyasashi wani tattausan murmushi ya kusa subucewa.
'Likitan mata ai ita nata da sauqi ma gakanantsohon mai laifi' bala yafada a xuciyarsa ko shakka bala bayayi idan xaiyi amfani da qwarewarsa da shekarunsa dayayi yana xubarwa da mata ciki yasan wannan kyakykyawar ma abin daya kawota kenan.
Don haka xuwanta bai wani bashi mamaki ba amma kyawunta shiya rudashi don tun da yake bai taba xubar da cikin mai kyau kamar nata ba.

'likita wata babbar matsala ce ta kawoni' tafada bayan ta katse masa tunani.
likita bala ya boye wani guntun murmushin dake niyyar subuce masa kana ya gyara xama
'wacce irin matsala ce dake?" yana cewa a xuciyarsa "sannu a hankali' xaki fadi abin daya kawoki munafuka,sai kin fada min ko watansa nawa" Har yanxu idanunsa basu daina kallon surar jikinta ba a fakaice.
Matsatsun kayan dake jikinta sun fito mata da surar jikinta a fili, hakanan ya lura masu tsadar gaskene matuqa kuma sunsha banban da na karuwan daya saba xubarwa da ciki wannn shiyasa yafara tunanin irin kufin daxai karba a gurinta.koda yake yadanganta da watannin cikin
meyiwuawa dubu ashirin, ko arbain ko hamsin.Wnnan duk daga inda tafito karuwar manya ce.

matar tadago kai tadubeshi kamar xata fashe da kuka tace cikin rarraunar murya mai kamar rada
"Likita matsalata itacr so nake nasami haihuwa, ,,don Allah ka taimakeni na kasa daukar ciki"
Tafada tana sheshsheqar kuka..Kura da kan rago

14

Akwai lokacin da wani abokin bala yataba ce masa bayaji mgn sosai.
'qarya kakeyi 'bala yace da abokinsa a fadace, "ni ko maciji zai gaya min ji ne?"
a yanxu da ayanxu da kalaman kyakykyawar yadoki kunnesa sai yafara fargabar kada fa mganar abokinsa taxama gaskiya.
"ban fahimceki ba yan mata ,kina nufin so kike a xubar muki da ciki?"
"so nake nasamu ciki ko bakaji?"matar tace dashi cikin qaraji.Bala yayi saurin toshe kunnensa din kada ta fasa masa dodon kunne.
"Shikenan don ni kadai aka tsana sai ace duk inda naje baxan dauki ciki ba tayi tsiro ta lalace dayawa.wajan likita shida nje kowa idan yadubani dai yace baxan sami haihuwa ba"ta fara kuka a tausashe, akwai alamun yanke qauna a tattare da kalamanta.
shin ko mahaukaciya ce? likita bala yatambayi kansa,adai dai lokacin ne maganar dan giyar nan ta qara fado masa.
tabbas wannan itace matar dayace xataxo

kuyi haquri yayi kadan amma xan xo anjima insha AllahKURA DA KAN RAGO

15

kodai wannan itace matar dayace zataxo masa neman haihuwa.yanxu kam yarage yanasa kodai yabi abin kamar yanda aka tsara ko kuma a fasa.Tsawon lokaci likitan na kallonta bai ce da ita qala ba, har saida ya tabbatar ta nutsu sannan ya tausasa mura yace,
"kina da miji ne?"
"idan bani da miji don me xan nemi haihuwa"
Bala ya sunkuyar da kai yana tunanin abin dazai fada mata.
"wacce hujja sauran likitocin suka gaya muki akan cewa baxaki dauki ciki ba?
Hawaye yayi sartu akan kumatun matar.
"nafada maka cewa suke wai mahaifata ta lalace baxata iya daukan ciki ba"
Likita bala yayi ajiyar xuciya saar data harba a tsakanin haqarqarinsa.
"kigafarceni idan nafada ba dai dai ba" yace da ita yana duban fuskarta." shin kin taba shan qwayoyin hana daukar cikine acan baya"
matar tadanyi jim sannn ta gyada kai
"kullum bana rabuwa da qwayoyin ha daukar ciki domin sau uku ana xubar min da ciki" ta share hawayen sannan takaiwa wani qaton quda duka dake sunturi a gefen fuskarta.
likita bala ya sunkuyar dakai yana jinjina abin data fada.
matar ta dubeshi a tsorace saar data dubeshi ya sunkuyr dakai, akwai alamun karaya qarara akan fuskarta"baxan iya daukan ciki ba ko?"Hawaye yaci gaba da sartu akan fuskarta kamar ruwa a jikin kwalbar qarnqara.
Likita bala ya girgiza kai a hankali.Bai iya duban fuskarta ba duk kuwa dacewa yana son qara ganin kyakykyawar fuskarta.
"Gaskiya ranki yadade ina fargabar sanar dake cewa indai abin dakika fada gaskiya ne ,baxaki iya sake daukar cikiba.kinsan wani irin tsiro qwayoyin suje a cikin mahaifar.wani saain idan aka ci saa ana iya yin tiyata a yanke tsiron, amma idan akaci gaba dasha bayan an yanke to xai lalata mahaifar tayanda ciki baxai qara xama ba" yayi shiru yana dubanta sannan yaci gaba"kiyi haquri da abin danace". Lokacin daya gaya mata maganar yadauia xata sume masa qasa.amma ga mamakinsa sai yaga ta sunkuyar dakai sannn ta xunkuda kafada tace
"Na haqura."sannn tamiqe tadauki gyalenta tayafa.Tadubi likitan ido cikin ido"mai yiwuwa akwai hanyar daxan iya samun cikin kaboye min ko don kana tunanin baxan iya biyanka abin daya dace bako?" ta dubeshi tana murnushi.
kudi ba matsalata bace indai xan iya daukar cikinnan ,xan iya biyanka tun daga kan qwandala guda har xuwa miliyan guda indai har xan sami haihuwa, kuma nayi alqawarin duk sanda xaayi birthday na abin dana haifa, nayi alqawarin xan baka sabuwar mota duk shekara har sai abin dana haifa yakai shekara bakwai"
Bala yajo gabansa ya fadi.Yanxu kuwa yagama imani da abin dadan giyarnnn yafada masa abokinsa.Tabbas matar xata iya bada komai indai anyi mata alqawrin samun ciki, miliyan guda din data ambata tamkar dukan guduma ne akan qirjinsa,Nan da nan yafara tara dimbin bashin da ake binsa, da miliyan guda xai iya cin qarfin bashin koda bai iya biya gaba daya ba, sannn yadubeta bakinsa na rawa,
"lallai idan nafahimceki kin matsu da haihuwar nan ko?"
qwarrai kuwa fiye da yanda kke tsammani domin idan bn sami ciki nan da wata uku ba to babbar bishiyar danake qarqashinta xata iya bushewa ganyen ya fado nakoma rana
kura da kan rago

16
Matar tayi shiru bayan tagama wannan kalaman.Har yanxu tana tsaye a hankali tanufi tagar daki wada kai tsaye waje take kallo ta leqa nadan lokaci sannan tajuyo ta dubeshi."wannan motar ma tana iya zama taka indai har kayi min dalilin haihiuwa tadanyi shiru batarr data dubeshi ba sannan tace"zo kaganta.
Likita bala ya miqe cikin mamaki sannan ya nufi qofar dakin kai tsaye lokaci guda kuma yana satar kallonta ta gefen idanu.

Danqarereyiyar motace baqa jeef qirar marsandi ta fara gaishe da idanunsa, sannan sai hanakalinsa yakai ga lambar motar a jikinta an rubuta "Bana 3" Ganin wannan number yasa numfashinda daukewa,amma bai bari kaduwarsa ta bayyana a fili ba yar autar hantar cikinsa na bari yabaro jikin tagar yakoma gunda yake tun farko yaxauna kana ya dubeda ido ido da ido yace ranki yadade alhaji bana ne mijinki?
matar ta gyada kanta a hankali
"kasanshi ne?"
bala ya lashi fatar bakinsa domin tafara bushewa.Yataba karantawa a jarida cewa alhajo bana a cikin wata guda yasayi guda bakwai daban daban
kura da kan rago

16
Matar tayi shiru bayan tagama wannan kalaman.Har yanxu tana tsaye a hankali tanufi tagar daki wada kai tsaye waje take kallo ta leqa nadan lokaci sannan tajuyo ta dubeshi."wannan motar ma tana iya zama taka indai har kayi min dalilin haihiuwa tadanyi shiru batarr data dubeshi ba sannan tace"zo kaganta.
Likita bala ya miqe cikin mamaki sannan ya nufi qofar dakin kai tsaye lokaci guda kuma yana satar kallonta ta gefen idanu.

Danqarereyiyar motace baqa jeef qirar marsandi ta fara gaishe da idanunsa, sannan sai hanakalinsa yakai ga lambar motar a jikinta an rubuta "Bana 3" Ganin wannan number yasa numfashinda daukewa,amma bai bari kaduwarsa ta bayyana a fili ba yar autar hantar cikinsa na bari yabaro jikin tagar yakoma gunda yake tun farko yaxauna kana ya dubeda ido ido da ido yace ranki yadade alhaji bana ne mijinki?
matar ta gyada kanta a hankali
"kasanshi ne?"
bala ya lashi fatar bakinsa domin tafara bushewa.Yataba karantawa a jarida cewa alhajo bana a cikin wata guda yasayi guda bakwai daban dabanKura da kan rago

17

Hakanan wani abu da kowa yasani cewa shike da mallakin saa da kashi sabain na hannun jarin dake kamfanin sadrwa na Bana.com. wata jita jita da dumi duminta nacewa yayo odar jirage guda bakwai na sama, wadanda xasu fara tashi shekara mai zuwa masu suna bana airlines .Shikuma ko ina fastarsa ce a lilliqe a ko ina sbd magana tayi nisa ta fitowarsa takarar dan majalissar wakilai ta tarayya mai wakiltr kudancin jiha.Koda yake mutane suna tofin Allah tsine sbd fitowa takararsa, Suna cewa yaya mutumin da baisan darajar mutane ba baya taimaka musu badini da xahiri shi xai wakilcesu.Bala yayi ajiyar xuciya.don me xata tambyeshi koya san mijinta,wanee duk fdin garinnan bai san alhaji haruna bana ba.?

'yanxu kayarda dacewa duk abin danayi maka alqawri xan iya ko?'
yayi saurin gyada kai.
"indai har wannan mutumin shine mijinga to mahukaci nake indai nabari wannan damar ta wuceni" bala yafda a ransa.
"fadu duk abin dakke so indai xan sami haihuwa to ka qaddara kaxama miloniya"
Bala ya qura mata idanu yana sauraron bayaninta. a xuciyarsa yana cewa rabo na minallahi wai tsuntsu daga sama gasashshe.Wannn itace damar daya dade yana nema sai yanxu tazo masa a bagas.
"kina iya xama " yafada bakinsa na rawa.

matar tayi ajiyar xuciya sannan takoma taxauna.
"ni daa nasan xaka iya wannn aikin saida aka fada min
cewa kai kadai ne xaka iya wannan aikin idan kakasa saidai nahaqura,wanan shiyasa nazo gurinka.Tadanyi shiru tana dubansa.Ganin baice komai ba sai ta dora"kai nake jira, yaya xaayi nasami haihuwar don Allah kada na wulaqanta?"

Likita bala yayi mamakin irin wulaqantar da takr nufi bayan dimbin dukiyar da mijinta yatara a duniya.Tsawon lokaci kansa a sunkuye cikin tunani, can sai ya dubeta a tsanake yace,
"zaki iya daukar ciki,amma ina fargabar hanyar daxaabi dawahala idan xaki amince da ita ,shiyasa ma tun farko ban ambaceta ba.

Cikin sauri tadago kai ta kalleshi har gyalenta yakuma xamewa.
"fadi muji ko wacce irin hanyace indai xan dauki ciki xan iya binta"
Likita bala yadan girgixa kai a hankai
"anya kuwa xaki iya bi abin nada wuyar shaani don sai mun dan kauce hanya"
"menene shi" tace akwai alamun dagewa a maganarta don har goshinta yafara tsatstsafo da gumi.
"kauce hanyace"bala yaqara maimatawa

Matar ta matso gaba kamar xata fdo akan kujerar tace dashi a fusace"kaga idan xaka fadamin kafada min, da sau nawa ina kauce hanyar don yanxu na kauce a naqarshe sai me?"
likitan yayi ajiyar xuciya kaa yajinjina maganarta sai ya sunkuyar dakai.

"zaki iya daukar ciki amma, ,,,,yayi shiru bai qarasa ba."Amma me?" matar tafada a dan tsorace
"Amma ba tare da mijinki ba sai dai dawani"KURA DA KAN RAGO

18

"Amma me?matar ta tambaya a dan tsorace

Amma ba tare da mijinki ba saidai dawani.
Matar ta zabura cikin kaduwa,bata zaco abin daxai fada ba kenan.
"kana nufin nabari wani qaton banza ya tabani bayan mijina?"
ta tambaya a yatsine
"Haka nake nufi ranki yadade indai kina son kidauki cikin amma fa badole bane idan bakya so dama nagaya muki abin nada wahala"

matar taqurawa dan tsololon likitan cikin tararrabi. tadubi qaton goshinsa da nanannen hancinsa gami da mici micin idanunsa masu kama da maciji saboda tsabar karatu da akasha a makaranta.haka nan fuskarsa yamushe take kamar nunanniyar mangwaro wadda ta dade a ajiye. "Allah yakiyaye nabari wannan yamushashshen yataban jikina indai abin dayake nufi kenan" matar tafadi a xuciyarta sannan tace a fili bakinta yana rawa"kai kana tunanin kamar matsalar a jikin mijina take?

Bala ya girgixa kai, "ba abin danake nufi ba kenn,watau irin maganin daxan baki baxaiyi tasiri akan mijinki ba sai a gun wanda bai taba kusantarki ba"

matar tadanyi jimm sannan sai tayi ajiyar xuciya tace"ka tabbata idan akayi haka xan sami cikin?"
"kwarrai kuwa" likitan yace ba tare daya dubeta ba"irin wannan aikin ba akanki na fara ba sai dai kamar abin dana fada muki dafarko abin nada wahala yadanganta ne kawai da amincewarki.

matar ta muskuta akan kujera kyakykyawar fuskarta murtuke"to ai anyi ba ayi ba kenan idan nasami cikin dawani ba mijina ba,ni abin dake so shine nasamu da mijina"

a karon faro bala yadubeta da murmushi"ai duk daya wai makaho yayi dare tunda dai mijin naki ba ganewa xaiyi ba damn nagaya muki kauce hanyace tuni kin kakkauce kuma dama kamar yanda kikacr, kinga yanxu idan kin kauce a naqarshe saime?
matar ta sunkuyar da kai bata iya yarda sun hada idanu ba
"wa kake tunanin zamuyi dashi?"KURA DA KAN RAGO

19

wa kake nufin xamuyi abin dashi?"tace a tsorace tana kallon busassun hannun likitan masu kama da farin katako.
"sai wanda ranki yake so, kina iya kawo duk wanda kike ganin kin amince kinaso kuma xai rufa muki asiri"

Jin haka keda wuya sai tayi ajiyar xuciya ta kalli dakin da a gurinta bai wuce na kiwon zomaye ba
"A ina xamu hadu idan na kawo mutumin?"
likita bala ya share qaton goshinsa yana kallonta a fakaice"akwai gida na musamman dana ware don irin wannan aikin, kingane ai ,kada kisami damuwa duk wanda kika samo sai kuxo mutafi gidan akwai magani da allura daxan baku kuyi amfani kafin kufara komai"

matar ta miqe tsaye"Yau nawa ga wata?" cikin sauri likita bala ya ciro wayar tafi da gidansa, yaduba"yau tara ga wata "yace da ita
"kabani sati biyu kafin nan xanzo da wanda xamuyi dashi, "
"Idan zakuxo saiki bari sai wajan qarfe goma sha biyu na dare idan zaki iya"
Bata dubeshi ba saita lalubi jakarta ta dakko cakin na kudi ta miqa masa
"ko qarfe ukun darene zan iya xuwa, shiyasa nace kabari sai nan da sati biyu saboda mai gidana xaiyi tafiya"tadanyi shiru a daidai lokacin da bala yake karbar cakin kudin"Naira dubu hamsinne kawai kafara tabawa kafin nadawo"
saboda qarfin hali da latsi irin na bala sai ya dubi cakin nakudin yace"bai kamata nakarbi komai a gurinki ba har sai mun sami nasara"qirjinsa yafara dukan uku uku lokacin daya fadi haka, da ace xata miqo hannu a lokacin da baxai iya bata cakin din ba.
"kada kadamu ai wannan baya cikin kudin aikinka, kyauta kawai nabaka.Tana gama fadar haka tanufi qofar dakin

Jikinsa na rawa yabita suka fice daga dakin har xuwa gunda motarta take,a xuciyarsa yana mamakin abin dayasata dingishi ita ba gurguwa ba, meyiwuwa ciwo taji,yakuma fada a xuciyarsa
"to likita nagode"tafada saar data tayar da motarta xuciyarta tana ta saqe saqe.Tabbas tun saar daya gaya mata yanda xaayi a sami cikin tagama yanke shawarar wanda xata dakko,duk da dai sau biyu kawai suka taba haduwa amma tana da qarfin gwiwar xata iya yaudaro shi.Tayi mamamkin abin daya hanashi kiran wayarta,tun saar dasuka hadu a watan daya gabata.

"Gashi kuma har xamu rabu baki fada min sunanki ba sannan idan babu damuwa ina son nasan lambar wayarki.
sukayi musayar lambar waya
"to shikenan ni xan tafi sai munxo din"
"ranki ya dade baki fada min sunnki ba"
ta dubeshi da murmushi a karo na farko taca a tausashe sunana
"LAURIYYA"
TAbbas itace matr da dan giyar nan yace xataxo lauriyya ya nanata sunan a ransa tabbas itace

Yau dao zan dana idan har comment bai yi yawaba to zan dasa aya adidai wannan gurin hhhhhhhKURA DA KAN RAGO

20

Asabar 10 maris 2007

Lauriyya ta shigo qayataccen dakin shaqatawr daga ita sai daurin qirji da wani qyalle fari so dashi mai gashi cikin rausaya kaar dawisu.Tanufi wani dogon madubi na musamman da aka saka mata shi daga can quryar dakin .lauriyya ta tsaya a jikin madubin tana naxarin kyakykyawar syrarta cikin takaici ,idan banda ya uxura'ta fadawa kanga. Babu yanda xaayi nayarda da yafita daga wannan kyakykyawar surar

wata qawarta ta taba cewa da ita 'bar ganin wannan mulmulallen jikin naki ,wallahi kina haihuwa daya duk ragwagwgwabewa xakiyi kamar tsohuwar mota.kinga dai yanxu bakifi sha takwas ba amma kina haihuwa xaki zama kamar yar arbain'a lokacin ko shekara batayi da aure ba aka bata wannan shawarar .tun daga wannan lokaci ta daura gaa da haihuwa
cikin farko data fara dauka qawarta ce taraka aka xubar haka ma nabiyu
ya kamata naraka ki gurin dr uche yanda xaki dinga samun qwayoyin xubar da ciki ciin sauqi ba saikinsha wuya ba" qawarta tace bayan an xubar mata da ciki na biyu,sannan taci gab da cewa" don me xakiyi tashan wahalar xubaf da ciki bayan kina da kudin daxaki iya siyan qwata komai tsadarta(point to be noted ladies try to have a good friends plx)

Tun daga wannan ranar ne lauriyya ta mayar da qwayoyin ruwan shanta kullum saita hadiya kamar xakara.Gaba daya wannan baifi shekara shida ba amma saboda yawan qwayoyin datake sha sun wuce kia shiya jefata halin datake yanxu.
Lauriyya ta dubi gashin kanta a jikin madubin ta kuma dubi dogon wuyanta kamar na barewa, tadubi shafaffiyar mararta kaar ta shekara bata jefa hatsi ba a tunbinta.ta dubi santala santalan qafafunta suna ta sheqi kamar tagwayen macixai, sai tayi tsaki saar data yi tunanin akwai banbanci da wadda ta karye da wadda bata karye ba.kallonta ya gangaro a hankali har xuwa kan xra xara sawun yan yatsunta wadanda kamar tunda suke basu taba taba qasa ba(oh nasan su oh oh fa sun qyasa to qwalelenku wannan sai mu yan dagwai dagwai iyalan baba hhhhhhh) sai tayiwa kanta murmushi tace
"wanene xai dubeni yace nayo shekara bakwai da aure" ta tambayi kanta tabar jikin madubin tana rausaya tanufi wani dan duqurqushin firji fari wanda akayiwa ado da xane xanen tagulla.a hankali tasa wani dan mabudi tabude kana ta dakko wata farar robe dauke da kofin ruwan sanyi tamayar ta rufe sannn tadawo ta lume a daya daga kujeru masu numfashi dasuka yiwa dakin qawanya taxauna sannu a hankali ta ajiye kofin da robar a kan wani teburi na tangaran.(wannan yana daga abin dayake sawa aure yake samun matsala a rayuwa idan har mace xata dinga hanqoron irin wadannan gidajen to kuwa xata jima bata samu mai sonta tsakani da Allah ba, yar uwa kiyi haquri da samun mijinki ko saurayinki watarana sai labari, hasashen yusuf ilyasu kenan wajan gudunmawar marubuta a harakar tabarbarewar aure)
Kura da kan rago.

21
lauriyya ta dafe kai tana naxari maganin har yanzu kanta na sarawa kadan kadan.Bayan barin ta da likitan jiya bata tsaya a ko ina ba sai asibiti inda ta wuce kai tsaye zuwa kantin dattijonnan dayake jira.Tana xuwa ta tambayi dattijonan ko yasan inda saurayin data taba bayar da saqo yake? dattijon yace bai sani ba amma dai yasan sunansa Ahmad,amma yayi mata alqawrin indai yazo zai gaya masa tana nemansa.A take ta qara rubutawa dattijon number dinta tace idan yazo lallai a bashi.

Lokaci guda sai fargaba ta mamayi zuciyarta,tasan da wuya idan Ahmad ya koma

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment