Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da lambarta ya jefar bai san inda yasata ba ,gashi kuma bai kwafi lambar a wayarsa ba.

Ahmad ya miqe tsaye ,sannan yanufi wani dan qaramin teburi mai tarin littafai a gaf da gadonsa na tuxurai

ya dakko wani kundin ajiye hotuna kana yadawo ya zauna, faga inda yake xaune yana iya jiyo hayaniyar qannensa da mahaifiyarsa a tsakar gida

Ahmad ya bude kundin hoton sannan ya xubawa hoton badariyya idanu. Ada bai taba gajiya da kallon hoton ba a qalla a rana yana iya kallonda sau goma koma fiye da haka.Amma a yanxu da ahmad ya qurawa hoton idanu a karo na farko a wata guda sai ya girgixa kansa cikin mamakin kansa.mutum yayi mamakin yanda hasken rana yake dakushe hasken farin wata cikin dan qanqanen lokaci. Ahmad yace cikin xuciyarsa.sannan sai ya mayar da kundin hotunan yarufe ya jefar dashi gefe guda sai ya koma kan gadond sa ya kwanta
"Ta yaya xan sake ganinta? Ahmad ya tambayi kansa da kansa .A iya yan kwanakin da suka gabata Ahmad ya lura da cewa tabbas ya rame domin wuyansa har ya fara dan tsayi kamar na barewa, ga qashin wuya ya fara bayyana a fili domin baya iya cin abinci sosai, ya dorwa kansa tunanin matar wani. Ahmad ya san cewa wannan tunanin daya ddorawa kansa tamkar yankewa kare ciyawa ne don bashi da wani afani. Shin da zai sake ganinta ma yaya zaiyi tunda dai matar wanice? idan bata da aure ma tafi qarfina" Ahmad ya fadawa kansa.

" Salamu alaikum" wata murya ta katse tunaninsa. Ya dago kai daga kan gadon ya dubi, ,,,,,

To xakujini shiru kuyi ta haquri dani nima ba a son rainaba hakan ke faruwa yanayine kawaikura da kan rago

31

salamu alaikum "
wata murya ta katse masa tunaninsa ya dago daga kan gadon yadubi qaninsa shafiu yace" menene banace kada kowa yadameni ba?"

shafiu ya sunkuyar da kai da dan wani murmushi ,ya miqawa ahmad wata tsohuwar naira hamsin da tsohuwar takarda yace" tun rannan daxanyi wanki na tsinci wannan a cikin aljihunka"

ahmad ya xaburo daga kan gadon ya tashi zaune jiki na rawa ,ya karve takarda ba tare daya karbi naira hamsin din ba kana yace da qaninsa baki na rawa"jeka ka kashe wannan na baka"
Hannunsa na rawa ya bude takardar ,xuciyarsa ta harba tsakanin haqarqarinsa,tabbas takardar dake hannunsa itace wadda lauriyya tabashi.wani zazzafan gumi yafra sartu akan
fuskarsa saar daya dakko wayarsa yafara daddanna lambobin dake jikin takardar yakara a kunnensa yana sauraro.
"hello wanene?" sassanyar muray tace dashi daga can bangaren,ahmad yaji am kwarawa xuciyarsa ruwan sanyi

*****
*********
qarfe takwas saura kwata n dare lauriyya tashigo wani tsukakken kwararo mai yawan kwaxaxxavai a cikinsa, cikin wata qatuwar mota baqa kirar honda jeep duk da irin tudun da kwaxaxxabon dake layin ,lairiyya bata damu ta sassauta gudun datake sheqawa ba sbd dalilai guda uku.
nafarko, dama can direbn da aka sa yakoya mata mota bai koya mata tuqi a hankali ba,don haka duk saar datake tuqi guje xaka ganta kamar an korota. na biyu kuwa, qatuwar motar datake ciki bata ma san da wani kwari ko tudu a gurin ba balantana ma jikin lauriyya yabata ta sassauta gudun.dalili na uku kuwa, sauri take takoma gida domin qarfe tara da yan mintuna maigidanta alhaji aruna xai dawo daga r taron siyasar daya tafi tun qarfe bakwai na wannan dareKura da kan Rago

32 a

lauriyya ta taka birki taci taya kusa da motar zayyanu launin toka toka dake ajiye a qofar gidan, wasu kaji guda biyu dasuke kwance suka tashi a firgoce saar da sukaji qugin cin tayar motar, yanxu kam sun san basu sami gurin kwana ba.

Lauriyya ta fito daga tata motar kana tarufe ta tadubi motar xayyanu cikin qunan rai saar data tuna irin naci da maitar da yayi mata kafin ta saya masa motar akan kudi naira miliyan uku da gida biyu, a hankali ta gyara lullubi dake kanta kan ta gyara jakarta dake rataye a kafadarta, tadubi tsukakken kwararon, babu kowa a cikin kwararon sai wau almajirai guda biyu da suke xaune a kan dabe a qofar wani qaton gida mai fitilu..Daya daga cikin almajiran abinci yake ci lokaci guda kuma yana jifa da dan abin daya rage a hannunsa cikin kwatamin dake gabansa. yayin da dayan almajirin yake kaiwa wasu kwari duka da suka mamaye lantarkin dake qofar gidan.

Lauriyya tayi tsaki tace " asarar kudi" lokacin data dubi qerarrun gidajen masu gajeren kyau amma babu magudanar ruwa masu kyau ba, bbu yanda batayi da zayyanu ba akan yabari ta saya masa gida a wani gurin amma yaqi yace sho anan yake son ya xauna abinsa.

Lauriyya ta danna qararrawar gidan lokaci guda kuma tana adduar Allah yasa ba a buge yake ba domin tasan halin abinta..KURA DA KAN RAGO
32(B)

Shiru na dan lokaci tana jira. Daga yanda take tsaye tana iya jiyo sautin tattausan kidan xamani yana fitowa daga ciki, lauriyya tana qoqarin ta sake buga qofar kenn sai taji motsin zayyanu ya nufo qofar. bayan yan daqiqu sai yabude qofar.Lauriyya tayi ajiyar xuciya saar data dubeshi taga ba a buge yake ba Xayyanu ya dubi rigar baccin dake jikinsa ,kana ya juya kana lauriyya tabishi a baya ba tare dasunyiwa juna magana ba, hat suka shiga cikin qayataccen falon suka zauna, sannan to lauriyya ta dubi yyanta cikin bacin rai ganin kwalaben giya akan wani qaton teburi .
"kai dai wallahi bakaci ribar xaman turai ba, dubi duk yanda kabari giya ta lalataka, dubi ko ina a hargitse. ko shara baka iyayo."

zayyanu ya dubi qanwarsa cikin wani busashshen murmushi.
"idan bnci ribar xaman turai ba aike kinci ta sanadiyyata,tunda gashi nayi muki hanyar auren biloniya gashi yanxu muna hutawa a bagas ,in banda abinki wacce riba ce tafi wannan?

Lauriyya ta sunkuyar da kai na yan daqiqu kana ta dago kai ta dubi yamusashshiyar fuskarsa cikin takaici. Lauriyya ta kasa imani da cewa wai kyakykyawar fuskar da akasha musu tsakani iyyensu akanta itace ta yamushe haka. kamar ganyen salad a cikin rana. Ga idanunsa sun qanqance sun koma ciki sunyi xuru xuru kamar wanda ya tashi daga amai da gudawa.ki wannan lalacewa dayawa take. lauriyya tace a cikin xuciyarta.

kema ai kinsan babu hadi zolayace kawai irin taki amma kinsan ai xayyanu yafi lauriyya kyau nesa ba kusa ba" mahaifinsu yake fada watarana ana karin safe ana shirin kao lairiyya makaranta.A lokacin xayyanu baifi shekara sha takwas ba ita kuma lauriyya sha biyar.
"Allah ya kiyaye namiji yafi mace kyau ai wallahi lauriyya tafishi kyau."

mahaifiyarsu ta mayar da martani .mahaifinsu ya fashe da dariya"kada kibari jininki ya hau uwar son kai, ni duk yyana kyawawane kamarki bbu wani mummuna
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment