Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

asibitin tunda dai ba ana yake aiki ba.Yanzu idan bata sami Ahmad ba yaya zatayi? Koda yake tasan akwai samari da dama yan duniya wadanda da wuri zata iya yaudaro su da kudi,to amma Ahmad na dabanne.Kyakykyawa nutsatstse,akwai alamun ilimi a tattare dashi.Kai da ana auren maza biyu da babu abin daxai hana ta aureshi.

Wadannan tunane tunanen su suka haifar mata da ciwin kai.Idan har akwai abin da qwaqwalwarra bata iya jurewa to yawan tunanine, Ashe ma bata san tunani yanzu tafara ba.

A hankali sai lauriyya ta dakko robar maganin ta xaxxago wasu adadi saita watsa sannan tadauki ruwa xata zata kora kenan sai taji wata kakkaurar murya tace
"baki daddara da dukan danayi muki jiya ba kenan ko"?
tajuyo a razane.A tsaye a baqin qofar dakin mijinga ne alhaji haruna yana ta huci a fusace kamar bijimin sa.Cikin zafin nama na ban mamaki saita miqe ta suri wata farar wuqa dake kan teburin irin ta feraye kaya marmari taja da baya tana kallonsa a fusace "kada ka tabani wallahi kana tabani zan yankeka da wannan wuqar, kadaina dukana ballantana har ka karyani baqin mugu"
Alhaji haruna ya dubi kyakyjyawar matarsa cikin takaici
"watau har yanzu baki daina shan maganin daukar cikinnan ba ko? wato dole ne saikinsani nayi abin da bana so ko? to bari kiji na fada muki ,ni banda raayin mata biyu abin dana fada kuma xan qara fada a karo na qarshe.Yadanyi shiru yana mayar da numfashi"Idan baki samu ciki ba nan da wata uku wallahi sai dai kibar gidannan na auro wata" muryarsa ta karye ya fara sheshsheqar kukan baqin ciji, "yanzu ke ko tausayina bakyaji?"

Gaban lauriyta yafadi saar dataji abin dayace.Idan akwai abin data tsana a duniya to bai wuce rabuwa da mijinta biloniya ba, domin tun tuni tayi imani da cewa shine babbar inuwarta mai hana mafa jin zafin rana

"Ba maganin da kake tunani bne ,maganin ciwon kaine" tace bakinta na rawa a tsorace.sannan a hankali saita ajiye wuqar dake hannunta ta ajiye gurin data dauka amma a tsorace.Lokaci guda kuma saita dauki robar maganin ta miqa masa"Gashinan duba kagani kaje katambayi duk wanda ka amince dashi sai kaji ko maganin menene"

Alhaji haruna ya dubi fuskar kyakykyawar da yabxu ya dakushe yadaina sashi farin ciki ko qanqani.A dai dai wannan lokacinne tunnin tsohuwar matarsa marigayiya hauwa ya fado masa nan da nn sai ya juya cikin sauri ba tare daya karbi robar maganin da lauriyya take miqa masa ba, kai tsaye ya wuce xuwa wani qayataccen dakin alfarma wanda ke fuskantar wanda yafita.Yana shiga sai ya wuce wajen wani qaton firinji wanda babu mai budeshi sai shi,Hannunsa na rawa ya dakko wata yar madaidaiciyar kwalbar barasa mai tsadar gaske ya bulbula a wani dogon kofi na tangaran, ko xma bai damu dayi ba sai ya fra bulbula ruwan bagajar a cikin qaton tunbinsa.A dai dai wannan lokacin ne yaji kamar motsi a bayansa.Yana juyowa yayi ido biyu da lauriyya."me kuma kikazo kifada min iyye?" yafda yana qaraji

"Nazo ne nayi maka waazi"
idanunsa suka zazzaro cikin jazur dasu."waazi fa kikace yau kuma kece da waazi?"

comments dinku ne yake qarfafa mana gwiwa idan babu cmmnt to kmr bakwa bi kenan idan bakwabi kuwa banga amfanin rubutawa baKURA DA KAN RAGO

22

Kwarrai kuwa abin yabaka mamaki ko.
Tadanyi shiru tana dubansa"na dauka yanxunnn kagama yimin fadan shan qwayoyin hana daukan ciki saboda kana son haihuwa ko?" tadanyi shiru tana kallon kwalabar giyar" kalli abin dakake sha, babu kunya babu tsoro .Yanxu a haka kake son tsayawa takarar jamaa? a haka kke son ka wakilci jamaa? kullum ka tsaya a gabansu da qatuwar riga da hula kana fada musu qarya da gaskiya wai kai mutumin kirki na Allah ko?yadai kamata kanutsu da shan giyar nn da sauran kayan maye kamar yanda kullum kake min fadan hana shan qwayoyin daukan ciki,kuma wallahi idan ka yaudari jamaa suka xaveka ko kuma ka yaudaresu da kudi domin kaxama wakilinsu a jamaa ka cucesu.domin banga abin daxakej ka fada ba bayan kaima ba acikin hayyacinka kake ba.Kaga jamaa idan suka xabeka sunyi kuskuren fahintarka a matsyin mutumin kirki kmili ashe basu saj kurace da kan rago ba, wallahi duk wanda yaxabeka yayi zaben tumun dare". Tana gama fadin haka saita juya xata fice daga dakin.

"Lauriyya." yakira sunanta muryarsa na rawa

Lauriyya tayi turus sannan tajuyo kana ta fuskanceshi.

"ashe yanzu ke har kina da idon daxaki kalleni kixargeni da shan giya? ai idan idonki da kunya bai kamata ki dubeni kifada min haka ba domin a duniya wayene yafara sani na dandani giya a duniya?"
hakan dayace shiyasa ta tsaya a dakin cak

"Naji nina fara shan giya amma ai yanxu kasan bana sha ko ,don haka kaima saika daina.Tana gama fadar haka saita juya tafice daga dakin da sauri kana ta banko qofar da qarfi.

Alhaji haruna sai yaji kamar tasa guduma ne ta doddeke gwuwoyinsa cikin sauri sai ya nemi gefen gado ya zauna shagwaf kamar kayan wanki.Yadubi kofin giyar dake hannunsa yaji kamar ya ajiyeshi amma maimakon haka sai ya kurbe sauran abinsa sannan yayi jifa da kofin ya tarwatse a jikin bango.Sannn sai yafara tsuma jikinsa na rawa sai kuma xuciyarsa ta tafi dogon tunanin wani zamani daya gabata..kura da kan rago

23
Abu uku basa xama guri guda abbana" mahaifin alhaji haruna yace dashi.abban shine sunan dayake kiransa dashi domin sunan kakan alhaji haruna ne lkenan. Likacin dasuke wannan hirar xaune suke a qofar gida bayan sun idar da sallar isha shida sauran qannensa bakwai.
"kasan abu uku bazasu taba haduwa da juna ba "mahaifinsa yaci gaba da fada yana jan tasbaha."watau maganar aurennan nakce take ta kai kawo a xuciyata kaga har yanzu baka da wata sanaar kirki a hannu.Shiyasa kaji nace abu uku watau mace da mijinta dakuma talauci basa xama a guri daya.wannan xancen babu shakka.Dafarko dai zakaga kodai talauci yatafi yabar mata da mijinta ,ko kuma miji yatafi yabar mata da talaucin, ko kuma ita matar idan ba mai tsananin rabo bace tatafi tabar mijin da talaucinsa.To kaga abu uku basa xama guri guda kenan, duk da yake iyayen yarinyar dakake son aura sun tarbiyyabtar da ita amma duk da haka yana dakyau kayiwa kanka tunani ,kaga yau shekara uku kenan da kammala karatunka babu aiki ga ba sanaa to yaya xakayi da matar?"
Dan saurayi haruna ya muskuta kansa a sunkuye yace" jarrabawar damukayi kwanki tafito, nasami aiki a banki"

mahaifinsa ya dubeshi cikin mamaki lokaci guda kuma farin ciki ya bayyana a fuskarsa"to alhamdulillahi Allah yasanya alkyri, to kaga yanxu idan Allah yaso sai ka kori talauci kaxauna da matarka"

Baafi watanni goma ba da hira tsaaninsa da uban aka daura auren hauwau da haruna.Hauwau wata kyakykyawar budurwace bafilatana mai alkunya ,lokacin da aka kawota gidansa saida tayi kusan shekara bata iya hada idanu dashi ko sunansa bata iya fada.

sannu a hankali sai shekaru goma suka bata yana aikin banki, rannn sai tsautsayi ya gifta aka koreshi saboda wani aringixo dayayi bisa kuskure daxai bawa wani mutum kudi.

Ashe rabon arziqi ne yasa aka koreshi.lokacin da aka korshi yyi saa yaa da yan wasu kudi daya adana a asusunsa,don haka korarsa keda wuya sai yafara tunanin meyakamata yayi, a lokacin yyansu uku da hauwau.

Haruna yana da wata muguwar dabia wadda jmaa da dama sukayi masa shaida da ita, marowacine na qin qarawa dyk dayake dai yana kula da iyalansa yanda yakamata.amma a gurin abokansa na muamula kamar xumbuli yakeKura da kan Rago

24

Hatta qannensa da suke uw daya uba daya dashi tofin Allah tsine suke masa,duk wanda yazo gurinsa da larurar dubu daya sai ya miqa masa dari idan ma baiyi saa ba sabaain.idan kuwa mutum yanuna rainuwa sai ya dubeka fuskarsa a murtuke yace"idan kaji haushi tafi kaima kayi karatu kamar yanda nasha wahala nasamu"
Don haka saar da aka sallameshi daga aiki ,jamaa da dama sun nuna murnarsu a fili, sai dai baa dade ba murna ta koma ciki domin Allah yayi masa nasibi a harkar mai.Kamar wasa haruna yafara saye da sayarwa na man fetur ta hanyar baqar kasuwa.Daga wannan jihar xuwa waccan.sannu a hankali cikin abin da bai wuce shekara biyar ba ya mallaki gidajen sayar da man fetur sama da goma.Hakanan ya mallaki gidaje sama da arbain da wata sinima da wani qaramin kamfani na sabulu da ake kira da Bana soap. wannan suna bana ,haruna ya samoshine tun lokacin dayake karatu a jamia,idan abokinsa ya tambayeshi aron kudi ko biro ko littafi na karatu kai hatta ashana, sai yadubi mutum babu kunya ba tsoro yace Bana bayarwa, saboda tsabar rowa.Tun daga wannan lokacin abokansa suke kiransa da Haruna bana.

Sannu a hankali arziqinsa yaci gaba da habaka, tuni kasuwancinsa ya tsallaka xuwa qasashen qetare yana safara, sbd ya fahimci a safara ne kawai kana sayo kaya ribarka xata zo hannunka.
Matarsa hauwau tashiga cikin niima da yayanta guda biyar maza biyu mata uku a lokacin har an sawa babbar yarsa asmau aure bikinta baifi wata shida ba.Rannn da da daddare sai haruna yadubi matarsa hauwau yace, Nan da kwana uku zaku tafi saudiyya kusauke farali.
Matarsa tadubeshi cikin kaduwa tace
"Haba alhaji ,tunda dai kai kaje makarnan yafi a qirga to bamu yakamata muje ba"
yadubeta cikin mamaki yace
"wayene yafiku gurina?"
hauwau ta tausasa murya gami da sunkuyar dakai don gudun bata masa rai,don haka aka koya mata a gida"kamafa yyi mahaifanka da wasu daga cikin qannenka yakamata su fara tafiya kafin mu" Alhaji haruna ya tausasa murya yagigrgixa kansa cikin sauri,don duk da masifa irin tasa da balaain fadansa yana dagawa matarsa qafa,duk duniya babu wanda yake so sama da ita da yayanta, don yar mutunci ce kuma tana yi masa biyayya
"kada kidamu suma badi zan kaisu"
"Amma bakajin hakan zai dada janyo min baqin jini a cikin danginku? kanaji dai kullum basu da abin zagi saini ganinsu ni nake hanaka taimako"
ya katseta cikin daga mata hannu."kudinane sai abin danaga damar yi dasu,kada kisake bari wannan tunnin yadami zuciyarkimni duk duniya ke nafiso da yayanki domin kune dolena,ki manta da dangina, kinga lokacin da ina makaranta babu irin wahalar da bansha ba waye ya taimaka min da sisin kwabo a cikinsu?"kura da kan rago

25

Hauwau tadubeshi cikin damuwa"To amma dai baban asmau wannan bai isa ya zama hujjar qin taimaka musu ba,domin bazai yiwu a rayuwa don kai kasha wahalar samun duniya kace bazakayi taimakao ba.Ba ka ganin wani tun kafin kazo duniyar yake wahalar neman duniyar amma bai samu ba, kuma duk da haka yake tsakurar abin dayake dashi yataimaka.ina son ace a rayuwa koda goro kasamu to ka rabashi biyu kabawa dan uwanka rabin."

Alhaji haruna ya miqe cikin fushi sannan ya dubeta"don dai kece hauwau amma duk duniya babu wanda ya isa yagaya min wadannan maganganun ban kyakykyetashi ba.Haba hauwa yaushe kika baci da sauraren waaxin bakin kasuwa?"

*************
Ranar jumuah da asuba jirgin su hauwa da iyalanta ya keta hazo xuwa qasa mai tsarki.Baafi ko saa daya da tashinsa ba jirgin yayi bindiga a sararin samaniya,babu wanda ya tsira a cikin jirgin sai wani tsoho mai qusumbi dayayi saar fadowa a wani tafki, shima din baa sameshi da yanyatsun sa na hagu ba da kunnensa guda daya.

Lokacin da a fadi labarin hatsarin jirgin a qafar sada labarai sai alhaji haruna yayi tsale ya fado a sume sai da akayi sati biyu baisan a inda yake ba.
Sannu a hankali watanni biyu suka wuce, tun bayan rasuwar iyalansa alhaji haruna bai sake tabuka katabus bamkullum yana gida a kwance sai yaransa ne ke tafiyar da kasuwancin.Ranan sai wani abokinsa dan duniya ya shawarce shi su tafi london hutu domin yasami nutsuwa kuma wai hakan zai taimke shi yamanta da rashin dayayi.

Zayyanu abokin alhaji haruna sun fara haduwa ne a wajen kasuwar baje kolin duniya da akayi a qasar sin.don haka bashi shawarar keda wuya sai ya amince daman bai taba zuwa qasar landon ba yafi zuwa nahiyar asiya a qasasgen turai holland yaje.

sun sauka a landon ana maka makan sanyi dusar qanwara nata xuba babu qaqqautawa abin yawuce qima a wannan shekarar domin an ruwaito a jaridar cnn cewa sanyin yakai maqura domin hatta agwagin ruwa mutuwa sukeyi duk kuwa da amanar dake tsakaninsu da ruwa.
wannn damar da ita shaidanin abokinsa zayyanu ya koya masa shan barasa
kura da kan rago

26

Kadan sha kadan mana menene? zayyanu yace dashi watarana suna xaune suna hira a gidan barasa.

ban taba shaba kuma yanxun ma baxan sha ba, kaga taba ma nadaina sha tunda matata hauwau tahanani
zayyanu ya dubeshi tausashe"lokaci yayi daya kamata kamanta da ita tunani bashi da amfani, kuma ma ni daxaka bi shawarata dana hadaka daa macen da kyawunta kadai ya isa yasa kamanta da hauwau
Alhaji haruna yaduni zayyanu a mamai yace" yanxu har akwau wata mace a doron qasa daxata gusar min da tunanin hauwau?"
zayyanu ya saki wani busashshen murmushi kana ya kurbi barasa yace"qwarrau kuwa qanwafa ce uwa daya uba daya anan landan takr zaune amma tunfa kana shakku bari kaganewa idanka ai gani ya kori ji"batarr daya baiwa alhaji haruna damar cewa komai ba sai ya dakko qatuwar wayar tafi da gidanka ya fara daddana lambaboi yakara a kunne yafara magana da sauri

baa fi saa va sai gata ta iso.basu ba hatta turawa yan birnin landan saida syka juyar da kawunansu suna kallon wannan kyakykyawar halitta.sannu a hankali ta qaraso tana sanye da wani wando ja mai santsi wanda ya dameta yafito da surar jikinta a fili

"sannunku da xuwa" tace dasu cikin harshen turanci sannan tajawo kujera ta xauna

zayyanu ya dubeta da murmushi yace"wannn babban abokina ne babban dan kasuwa ne tre muka xo dashi daga nijeriya sunansa alhaji haruna"
oh Allah sarki malamsannu da xuwa ashe babban baqo mukayi daga gida"tace cikin harshen hausa sannan sai ta dubi farantin barasar dake gaban zayyanu tace yaya kabar baqona bbu abin shaKura da kan Rago

Nas

27

Zayyanu ya dubi qabwarsa cikin murmushi sannan ya dubi abokinsa haruna.ya lura tunda ta shigo dakin barasa idanu da duk wani hankali na alhaji haruna yakoma kanta hakan ya faranta masa rai

nace a kawo masa ruwan barasa yace ah ah.mu anan maganin sanyi ce da debe kewa kawai.kyakykyawar ta girgixa kai lokaci guda ta miqe tsaye, "bara a kawo maka kawai ba wani bugar dakai daxatay, mufa giyarmu ba irin taku bace ta hatsi"

ah ah kibarshi kawai saboda",,,shhh ta katseshi ta hanyar dora kyakykyawan hannuta a kan lebenta,sannn saita ranqwafa bayan kujerarsa kusan rabun qirjinta yana bayansa sannan tayi masa rada kunne"baka ganin kowa a nan sha yakeyi,idan kaki sha baxanji dadi ba a matsayin na mai saukarka kuma xan dauka baka girmama saukar danayi maka ba" cikin sauri ta miqe sannan ta yafito hadimin mai rabon barasa.
mintuna biyu saiga barasa a gaban alhaji haruna.tun daga wannan lokacin suka rantsar dashi .abin daya bashi mmaki shine lokacin daya fara kurbar barasar sai yaga kyakykyawar ta bude lemon kwalaba coke tasa dogon tsinke tana kurba abinta.

" yaya naga ke bakya sha sai lemo?

matar ta girgixa kai ta haskeshi da fararen idanunta tace
"wannn ai kayan shanmu ne mata ku kuwa maza saida mai dan dumi dumi"

Bayan sun baro gidan barasar alhaji haruna yadubi lirwanu saar dayaji wani abu yafara juyawa akansa kamar gare gare,kana ya dubi kyakyjyawar fuskar qanwar zayyanu, tun da yake bai taba ganin mace mai kyawunta ba. ko matarsa hauwau saidai ta nuna mata biyayya, ita ma din waya sani? yafadawa kansa.

"yaya sunan qanwar takane?" yatambayi zayyanu
cikin murmushi xayyanu ya dubi qanwarsa
"Lauriyya abokina na son magana dake bara nabaku guri"

watanni uku da suka biyo bayan auren abin gwanin ban shaawaKura da Kan Rago

28

Duk da dai alhaji haruna ya lura kamar lauriyya tana da dan girman kai gata da masifar fada ba kamar hauwau ba.to amma yana jin dadin zama da ita musamman idan yafita da ita taro ko liyafa gurin abokai yakanji alfaharin a ganshi da wannan kyakyjyawar a matsayin tasa.

katsam rannan sai ta fara watsa dan farin cikin dayake wanxuwa a tsakaninsu.Abin yafara ne watarana yana neman inda ya ajiye dan maqullin motarsa,sai kawai yaci karo da kwalabar magani.Abin yabashi mamaki don shi a iya saninsa sai yashafe sama da wata guda baiji tayi koda qorafin ciwon kai ba.sannu a hankali yana cin karo da irin wadannan kwalaben magani har shekaru hudu suka wuce babu alamar koda bari ballantana ciki.Gashi kuma yanxu a duniya bbu abin dayake so sama da biyu, nafarko dai haihuwa domin yana kewar yayansa biyar daya rasa sanadiyyar hadarin jirgin sama,gashi babu magada ga dukiya yatara. Abu nabiyu kuma dayakeso shine mulki.kudi Allah yabashi don haka sai yayi amfani da shawarar abokansa yan birni ya tsunduma iya wuya a cikin harkar siyasa, domin ya fahimci bayan bankuna da kuma mai,babu wani abu dayake ci a qasarnan sama da siyasa musamman idan kai ke riqe da saniyar. wannan shiyasashi tsayawa takarar dan majalisar wakilai mai wakiltar kudancin jihar

Ana cikin wannan al amari ne sai rannan yasake cin karo da kwalabar magani ,bai mata magana ba domin dama tuni jikinsa yabashi,da yamma liqis an dauke ruwa lokacin sai ya kira likitansa yace wai maganin menene? likitan ya tabbatar masa da cewa maganin hana daukan ciki ne.

A ranar kwana yayi bai runtsa ba sbd baqi ciki.shekaru biyar yana ganin irin wadannan magungunan,gaskiya fa ko bari bata tabayi ba, "yaya zatayi min haka?"ya tambayi kansa.dafarko yayabke shawarar kawai yayi mata kishiya wadda zata haifar masa magaji wanda zaike gani yana jin dadi, don yau rabonsa da jin dadin iyali shekara shida kenan,tun lokacin matarsa hauwau da yayansa nada rai.
wannan shawarar ta sake aure ko daqiqa batayi ba a xuciyarsa ya kawar da ita domin a raayinsa yafi son xama da mace daya kamar hauwaunsa.

Alhaji haruna ya fashe da kuka cikin wannan daren, yabude firinji yana ta fito da kwalaben giya yana kwankwadewa.A wannan daren ne yayiwa lauriyya dukan tsiya har saida garin kokawa taxame ta karyr a qafa.

bayan an sallamota ne daga asibiti yadubeta cijin qunan rai yace " nabaki nan da wata uku idan baki sami ciki ba wallahi zama na dake yaqare"

Lauriyya ta dubeshi cikin kaduwa.dafarko ta dauka da wasa yakeyi amma saar data dubi fuskarsa tasan wannan dan giyar da gaske yake.

" Amma dai kasan bani da ikon nayiwa kaina ciki ko" tafada cikin qarfin hali

" Amma ai kina da ikon xubar da ciki ko,
to bari kiji kamar yanda kika san ki xubar dashi saiki samo hanyar daxaki sameshi"

Alhaji haruna yayi ajiyar xuciya bayan yadawo daga dogon tunanin daya tsunduma.Jikinsa na rawa ya ajiye kwalabar giyar dake hannunsam sannan sai ya nufi falon yana tangadi
Lauriyya ta dago kai ta dubeshi a fusace
"dubeka don Allah ko kunya bakaji"
Alhaji haruna ya dubeta cikin qunan rai yace"wata biyu kacal suka rage muki idan banga ciki a jikinki ba zaki tattara naki yanaki kibar gidannan lauriyya"

****** ********
Lahadi, maris 2007kura da kan rago

29(a)
Lahadi 11 maris 2007

Ahmad ya jefar da alqalamin dayake hannunsa yayi ajiyar xuciya ,ya dubi tulun takardun da suke gabansa

Tun asuba dayayi sallah bai koma bacci ba, maimakon haka si yayi ta making jarrabawar dalibansa dayake koyarwa a secondary ta gwamnati ,domin ya makara shi kawai ake jira yakawo domin ragowar malaman tuni sun kawo nasu.

shekaru biyu kenan yana koyarwa a makarantar tun daya gama jamia,da yan kudin dayake samu ya ququta yakuma komawa jamia karatu domin yin digirinsa na biyu, duk da irin wahalhalun dayake fuskanta na karatu bai taba makara ba wajan makin din jarrabawa

kuyi haquri zuwa dare insha Allahkura da kan rago

30

Lahadi 11 maris 2007

Ahmad ya jefar da alqalamin dayake hannunsa yayi ajiyar xuciya ,ya dubi tulun takardun da suke gabansa

Tun asuba dayayi sallah bai koma bacci ba, maimakon haka si yayi ta making jarrabawar dalibansa dayake koyarwa a secondary ta gwamnati ,domin ya makara shi kawai ake jira yakawo domin ragowar malaman tuni sun kawo nasu.

shekaru biyu kenan yana koyarwa a makarantar tun daya gama jamia,da yan kudin dayake samu ya ququta yakuma komawa jamia karatu domin yin digirinsa na biyu, duk da irin wahalhalun dayake fuskanta na karatu bai taba makara ba wajan makin din jarrabawa ba sai wannan karon
domin kwanakinsa hudu da rabuwa da lauriyya aka fara jarrabawar yaran.Ahmad yayi saa lokacin yagama tasa jarrabawar amma duk da haka saida ayyuka dalibansa suka taru sukayi masa yawa.ganin kyakykyawa lautiyya duk ya ruda masa tunani ,tun ranar daya dora idanu akan fuskarta bai sake samun nutsuwa ba cikakkiya,duk aikin daya kamata yayi ya jangabe su a gefe guda kullum a tunani yake da tashin hankali.

Abin dayake daga masa hankali shine yar guntuwar tajardar data bashi mai dauke da lambarta ya jefar bai san inda yasata ba ,gashi kuma bai kwafi lambar a wayarsa ba.

Ahmad ya miqe tsaye ,sannan yanufi wani dan qaramin teburi mai tarin littafai a gaf da gadonsa na tuxurai

ya dakko wani kundin ajiye hotuna kana yadawo ya zauna, faga inda yake xaune yana iya jiyo hayaniyar qannensa da mahaifiyarsa a tsakar gida

Ahmad ya bude kundin hoton sannan ya xubawa hoton badariyya idanu. Ada bai taba gajiya da kallon hoton ba a qalla a rana yana iya kallonda sau goma koma fiye da haka.Amma a yanxu da ahmad ya qurawa hoton idanu a karo na farko a wata guda sai ya girgixa kansa cikin mamakin kansa.mutum yayi mamakin yanda hasken rana yake dakushe hasken farin wata cikin dan qanqanen lokaci. Ahmad yace cikin xuciyarsa.sannan sai ya mayar da kundin hotunan yarufe ya jefar dashi gefe guda sai ya koma kan gadond sa ya kwanta
"Ta yaya xan sake ganinta? Ahmad ya tambayi kansa da kansa .A iya yan kwanakin da suka gabata Ahmad ya lura da cewa tabbas ya rame domin wuyansa har ya fara dan tsayi kamar na barewa, ga qashin wuya ya fara bayyana a fili domin baya iya cin abinci sosai, ya dorwa kansa tunanin matar wani. Ahmad ya san cewa wannan tunanin daya ddorawa kansa tamkar yankewa kare ciyawa ne don bashi da wani afani. Shin da zai sake ganinta ma yaya zaiyi tunda dai matar wanice? idan bata da aure ma tafi qarfina" Ahmad ya fadawa kansa.

" Salamu alaikum" wata murya ta katse tunaninsa. Ya dago kai daga kan gadon ya dubi, ,,,,,

To xakujini shiru kuyi ta haquri dani nima ba a son rainaba hakan ke faruwa yanayine kawai
kura da kan rago

29(a)
Lahadi 11 maris 2007

Ahmad ya jefar da alqalamin dayake hannunsa yayi ajiyar xuciya ,ya dubi tulun takardun da suke gabansa

Tun asuba dayayi sallah bai koma bacci ba, maimakon haka si yayi ta making jarrabawar dalibansa dayake koyarwa a secondary ta gwamnati ,domin ya makara shi kawai ake jira yakawo domin ragowar malaman tuni sun kawo nasu.

shekaru biyu kenan yana koyarwa a makarantar tun daya gama jamia,da yan kudin dayake samu ya ququta yakuma komawa jamia karatu domin yin digirinsa na biyu, duk da irin wahalhalun dayake fuskanta na karatu bai taba makara ba wajan makin din jarrabawa

kuyi haquri zuwa dare insha Allahkura da kan rago

30

Lahadi 11 maris 2007

Ahmad ya jefar da alqalamin dayake hannunsa yayi ajiyar xuciya ,ya dubi tulun takardun da suke gabansa

Tun asuba dayayi sallah bai koma bacci ba, maimakon haka si yayi ta making jarrabawar dalibansa dayake koyarwa a secondary ta gwamnati ,domin ya makara shi kawai ake jira yakawo domin ragowar malaman tuni sun kawo nasu.

shekaru biyu kenan yana koyarwa a makarantar tun daya gama jamia,da yan kudin dayake samu ya ququta yakuma komawa jamia karatu domin yin digirinsa na biyu, duk da irin wahalhalun dayake fuskanta na karatu bai taba makara ba wajan makin din jarrabawa ba sai wannan karon
domin kwanakinsa hudu da rabuwa da lauriyya aka fara jarrabawar yaran.Ahmad yayi saa lokacin yagama tasa jarrabawar amma duk da haka saida ayyuka dalibansa suka taru sukayi masa yawa.ganin kyakykyawa lautiyya duk ya ruda masa tunani ,tun ranar daya dora idanu akan fuskarta bai sake samun nutsuwa ba cikakkiya,duk aikin daya kamata yayi ya jangabe su a gefe guda kullum a tunani yake da tashin hankali.

Abin dayake daga masa hankali shine yar guntuwar tajardar data bashi mai dauke

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment