Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
1⃣➡5⃣

By Harphsart Rano✍


Tafiya take cikin matsanancin tashin hankali wanda sam bae sa ta lura da inda take sa kafarta ba.. Tafiya kawae take hawaye ya wanke mata fuska.. Tana dana sanin kasance warta cikin wannan duniya.. Why? Why?? Shine abunda take ta nanatawa a zuciarta..

Wani matsanancin gudu yake a dalilin kiran gaggawar da akae masa cewa jikin mominsa ya rikice.. Bai lura da ita ba sam.. Sae dayazo daf da ita.. Wani wawan birki ya taka hade da danna horn iya karfinsa..

duk yanda yaso ya kauce mata be samu nasara ba sae daya bangaje ta tae wata razananniyar kara.. hakan ya jawo hankalin mutane da suke wucewa jefi jefi suka yo kanta dan kawo agaji.. Fitowa yae daga motar a rude "ohh shit damn it. Ya karasa wurin tare da nan russunawa a gabanta tana sheshekar kuka.. ta dan kurje kadan amma bata samu wani mummunan rauni ba..

mutane nata mata sannu suna Allah ya kiyaye gaba.. Ta mike jiki ba kwari ta kama hanya tana dan dingisa kafa, hakan yasa yae saurin shan gabanta tare da cewa pls kiyi hakuri dukda kece me laifi kina tafiya wt out checkin d road.. Bata tanka masa ba illa cigaba da tafia da tayi.. yace baiwar Allah ina sauri ne amma ga wannn ki saya magani.. A hankali ta furta ka barshi na gode.. Ta cigaba da tafianta tana dingisa kafa.. Noke kafada yayi alamun i dnt care ya fada motarsa ya bata wuta..

Allah Allah yake ya gansa gaban mominsa. Karfe shida da yan mintuna ya matsa horn a kofar wani hadadden get.. Me gadi ne ya leko ta wata yar kofa ganin me horn din ya sashi bude get din cikin ajama.. kafin ya gama budewa tuni ya shgo tare ta ftowa cikin sauri wanda har yaso ya mnta da rufe motar.. Ya juyo da sauri ya danna securityn motar ya haura balcony..

Momynah! momynah! Shine abunda ya shgo yana fada.. Yae saurin haurwa sama ganin ba kowa falon. Momy ya hango kwance kan sofa gefenta daddy ne,, sae twins en momy islam da iman.. Sae auta khalil wanda suke kira da little khaly , .. Saurin karasawa yayi ya rike hannun momy tare da cewa momyna ya jikin.. Shafa kansa tayi tare da murmushi tace my boy har ka iso.. Jiki alhmdlh.. Ya juya zua ga dady ya gaisheshi.. Ya amsa masa da kulawa.. tare da tambayarsa hanya .. su iman ma suka gaisheshi..

Bayan sunyi sallah sun dawo duk suna zaune a falo daddy yae gyaran murya yace dama inason na ftrda momynku india akan matsalar nan tata shine nake ganin mene shawarka?? Ya jinjina kai yace daddy shine tunanin da nake nima.. Daddy yace ina da bussnss da zae kaini india kuma atleast zanyi wajen 1month.. kaga sae mu tafi tarr.. Anan suka yanke shwaran ftar da momy india nxt week ..

A hankali take tafia hadda karaso kofar wani kurkutacchen gida wanda duk unguwa babu gida mafi muni irinsa.. Tura kyauren gidan tayi hade da sallama..

Umma ta mike da sauri ta riko hannunta gami da cewa "Me faru dake nurr?? Me ya tsayar dake haka kuma naga kin shgo hankalinki a tashe ko wani abun kawun yayi miki?? Bata samu damar amsa mata ba saboda zafin da kafar ta ke mata ga wani zugi da dan yatsanta ke mata.. Umma ta cigaba shisa nace karkije karkije kika nunan ba abunda zae faru gashi nan abunda ya faru ta fada tana share kwalla da gefen zaninta.. Nurr ta fashe da kuka hade da cewa umma kafata zafi hannu na😭..

Mota ce ta bige ni umma.. Umma ta rafka salati mota nurr garin yaya?? Ta wawuro hijabinta tace wuce muje wurin habu me chemist ya dubaki.. Nurr ta riko hannun umma hade da cewa umma ina muke da kudin zua chemist.. Sai a lokacin umma ta tuno basu da ko naira biyar.. Ta rausayar da kanta gefe tace tou ya za miyi muje ko bashi ya bamu inasa ran hajia zata biyani kudina. Tace umma ba komi akwai ragowar rop bari na shafa ta wuce ciki tana dan dingisa kafa amma bata bari umma ta fahimta ba saboda taga yanda umma duk ta rikice ita kuma bata son damuar ummanta..


Cikin sauri ya shgo rike da wata bakar leda yana shgowa ya tarar da ummansa da nurr a zaune a tskar gida nurr ta bawa umma labarin yanda sukae da kawunsu dazu..

Da sassarfa ya karaso ya jawo kujera yar tsuguno yace umma sannu da gida, ta amsa da abbana sannu da kokari Allah yai maka albarka.. Amin Yace umma wlh yau aikin ne baya tafiya sosae shisa kukaga nayi yamma. Amma ga abunda na samo gami da mika ma umma ledar. Nurr ta mike ta dauki leda ta shga wata yar rumfa ta dauko wani kwano ta juye Zogale ne da kuli kuli.. Ta zo gaban umma ta ajiye hade da komawa ta debo ruwa a kwano tazo ta ajiye ta koma gefe ta zauna.. kabir ne ya lura da dingishin da kanwarsa take ya juyo cikin kulawa yace kanwata me sameki a kafa?? Umma tace wlh mota ce dazu ta bige ta tana dawowa daga gidan kawunku. Subhanallah mota umma garin yya?? Nan umma ta labarta masa yanda nurr da shaida mata. Yace ai ya kamata aje a duba ko tayi targade ne.. Amma kuci abncin sae na rakata gidan talatu ta duba ko targaden ne.. Umma ta jawo kwanon suka fara cin abinci a hankali shikuma kabir ya kwantar da kansa jikin bangon hade da lumshe idonsa yana tunanin rayuwarsu...
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
5⃣➡1⃣0⃣

By Harphsart Rano✍


Yau ta kama monday, an gama wa momy shirye shiryen komai, wednesday jirginsu zae daga zua india..

Malam Idi me gadi ne yayi sallama ya durkusa ya gaida momy ta amsa cikin sakin fuska kasancewarta mace me karamci.. Hajiya wata mata ce a waje take son ganinki.. Tace tau ace ta shigo mana malm idi
Ya mike yace an gama hajiya ya fice.. Ya koma inda ya bar matar ya sanar mata hajia tace ta shga.. Ya juya bakin aikinsa.
Sallama tayi Momy ta kalleta cikin murmushi ita kuma tai saurin dukawa tace sannu hajiya ina wuni?? Lafiya lau jummai ina ta zuba ido ashw zakixo. Tace wlh hajia yarinya ta ce ta haihu dole sae dana fara biyawa na duba ta.. ayya me aka samu cewa momy, Allah ya raya.

Bayan sun dan taba hira hajiya ta muskuta tace jummai kinsan laraba zan tafi india akan wannan matsalar tawa jiki yaki dadi yau cio gobe lafiya, shine nakeso ki samo min me aiki dattijuwa wadda zata kular min dasu khalil.. Kanwar Alhaji ce da zatazo kuma aka samu yar matsala.

Jummai tace ayya hajiya in sha Allahu zan samo miki zuwa gobe tunda jibi ne tafiyar taku. Momy tayi godiya.


Salamu alaikum, salamu alaikum.. Umma ta fito daga daki tana gyara dankwali wa alaikumussalam jummai ce a gidan namu? sannu da zuwa. Bayan gaishe gaishensu jummai ta kalli umma tace dije alheri ne ta kawo ni fa, umma ta muskuta tana murmushi tace Allah jummai?? Tayi shewa tace wlh dije wata hajiya ce take niman wadda zata kular mata da yaranta guda uku zata fita india neman lafiya. Umma tae daria tace kai haba jummai, jummai tace shine naga ba wadda ta chanchanta sae ke. Amma ya kika gani??

Umma tace wlh jummai nakuwa gode me zae hana nayi dama zaman nan ya ishen ga yarinyar nan an korota a makaranta bamu da kudi. Kinga in na fara aikin zan dan ragewa kabiru wasu wahalhalun..

jummai tace tou sae ki shirya gobe da safe sae muje kiga gidan.. Umma ta rako jummai bakin zaure tana kara mata godiya da alkawarin in sha Allah zata shirya da wurwuri..

Da daddare suna zaune akan tabarma ita da umma wanda ta lura umman na cikin farin ciki, ta numfasa, umma wai me faru ne na ganki cikin farin ciki yau.. kafin umma ta bata amsa kabir ya turo kyauren ya shgo.. A ah umma da autarta ya fada yana murmushi. Nurr ta turo baki umma kinga yaya ko? umma tae daria tace kadowa abbana.. ya sami gurin ya zauna gami da cewa wash umma wlh na gaji.. Tace ai dole sannu allah maka albarka.. Nurr ta mike ta debo ruwa ta dan russuna tace yaya ga ruwa.

yayi mrmushi yace nagode kanwata.. Umma me ake tattaunawa ne na shgo na ganku cikin annashuwa..
Umma tayi murmushi tace albishirinku? Na sami aikatau gidan wani alhaji dazu jummai tazo take gayan yanzu gobe zanje naga gidan.. kabir yae saurin ajiye kwanon ruan hannunsa yace umma aikatau kuma??
Me zakiye da aikatau umma?? Kin manta wulakancin da matar nan tae miki umma.. ? Gaskia sam ban amince ba umma, zanyi iya kokarina naga na kyautata rayuwarku umma.. In sha allahu koame ya kusa zua karshe..

Umma ta murmusa tace abbana bawae na raena kokarinka akanmu bane.. Amma aikin nan zae taimaka mana ko da kudin jarrabawar kanwarka , sannan kuma nasan zamu dinga samun abinci kaga an samu sauki..

Yayi yake yace umma bawai naki ta taki bane amma umma wulakanci nake gudar miki. Umma tace kayi hakuri in sha Allah hakan bazata faru ba kuma watarana sae labari..

Yae shiru na dan lokacin hakan ya bawa umma damar maida kallonta ga nurr wadda tunda aka fara magana bata samusu baki ba.. Wannan na daya daga cikin dabi un nurr bata taba magana inde ummanta da yayanta na magana. Umma tace yadae auta baki ce komai ba, tayi murmushi tace umma duk yanda kuka yanke yayi.. Kabir ya ce umma ba komi Allah zaba abu mafi alkhairi ya mike game da cewa bari na samo mana ko breadi ne ya fice.. Umma ta bisa da kallo tasan har ga Allah bae so aikinta ba amma ya za tayi zaman ya ishe ta haka..

Tunda nurr tayi sallar asubah bata koma barci ba ta tashi ta fara kichiniyar shirya gdan saboda tanaso tabi umma gidan da zata in taga zaa wulakanta ummanta dole ta hakura ita taji zatae aikin umma kuma ta dawo gida.. Umma ta fito ta tarar da ita tana shara bayan ta hada itace ta dora musu ruwa kasancewar ana dan sanyi garin.. Sannu yar albarka taji ance tae saurin juyowa da murmushi ummana har kin fto.. Ina kwana??
Umma tayi daria na fito auta sannu kinji. Ta ajiye tsintsiyar ta zari bokita ta zuba ma umma ruwa ta kai mata bandaki ta dawo tace umma ga ruan chan na kai.. Nagode miki Allah miki albarka

Bakwai daidai sun gama shiryawa suna jiran jummai.. Kabir ya fto yace umma har kun shirya kenan. Tace Mun shirya abba jummai muke jira, ga kokonka chan cikin kwano.. sallama suka ji wanda yake nuna isowae jummai.. bayan gaishe gaishe suka dau hanya sae gidan Alhaji naseer..
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar 🎀
2⃣1⃣➡2⃣5⃣

By Harphsart Rano✍

Bayan ya fito ya tsaya jikin kofa yana tunani.. Dama a talakawa akwai masu kyau (kaji safwan😅)..
Amma kuma tayi karama ,shikuma a tsarin sa ya fison matured mace irin yar jami ah.. (lalle ma safwan dinna)..lol

Ya koma daki ya kwanta ya rufe ido amma kwata kwata barci ya kaurace wa idonsa.

wai meke damuna ne? Ya ayyana a ransa, mesa zan tsaya wannan yar karamar yarinyar.. Mtsw yaja tsaki gami da mikewa, yajawo system dinsa ya cigaba da aiki, duk dan ya mantar da zuciarsa..


Bayan ya shirya cikin bakar suit, ya dauko brief case dinsa ya fito yana duba tym.. 7:05am agogon ya nuna..

Zaune ya samesu sun shirya cikin uniform, suka gaisheshi cikin girmamawa..

Wayarsa ce tai kara, Ganin me kiran yasa shi saurin dagawa hade da yin sallam

Lafiya kalou daddy ya ambata, hakan ya nuna da wanda suke waya.
Jin haka yasa khalil matsowa da sauri kusa dashi

Bayan sun gama magana da daddy, ya mika musu wayar daya bayan daya sukai magana da iyayen nasu.. Ganin khalil zae bata musu lokaci yana tai wa momy shagwaba, yasa shi saurin karbe wayar yace momy zusuyi late a skul.. Sukai sallama ya kashe.

Yace me kuke jirane?? Iman tace malam habu muke jira bae zo ba har yanzu,.. lalubo number malam habu yayi yai dialin,

ayya Allah ya bata lafiya ya fada yana sauke wayar.. Sae ku tashi mu wuce na sauke ko.. Malam habu bazae samu zuwa ba..

Islam tace tau in munje wazai dawo damu?? Ya shiru yana tunani, gashi yana da important abunda zaeyi yau dinnan..

Chan idea ta fado masa, yace jeka kira mun wannan dinnan, Wae anty nurr? Khalil ya tambayasa.. Umm ita, ya amsa ya fice su islam suka bi bayansa..

Yana ganin fitowarsu ya kauda kai, dauko hijab dinki ya fada ba tare da ya kalleta ba..

Ta juya da sauri duk a tsorace take dashi tun tsawar nan da yayi mata..

Daedae bakin gate din makarantar suka tsaya, su iman suka fita daga motar suna dagawa yayan nasu hannu.. Ganin bae ce mata komai ba yasa itama ta kama kofar zata bude..

Ina zaki kuma ya fada cikin husky voice dinsa, jikinta ya dau rawa.. ya dan kalleta ta mirror ya tabe baki,

Inaso anjima by 12 kixo nan skul din ki dauki su khalil.. Hope zaki gane hanyar ya fada yana dubanta..

Ta dago da idonta karap idonsu ya hadu, wani shock yaji tun daga kansa har kafarsa.. Ya dan kura mata ido kadan sae kuma ya basar..

Ita dinma kasa magana tayi don ganin yanayinsa, tunani take zae kara mata wata tsawar..

Bata gama tunani ba taji yace dake nake magana, cikin inda inda tace eh zan gane..

Sae ki dawo nan mu wuce inada abinyi. Ta fto jiki na rawa ta koma gaba..

Daidai bakin gate ya tsaya ya zaro dubu daya ya mika mata.. Ga kudin napep

Hannu biyu tasa ta Karba ta wuce, sae bayan ta shige ya wuce yana tunanin abunda yake damunsa kwana biyun nan..

Mesa yake jin wani irin abu akan wannan yarinyar.. Kuma shi yana ganin kamar ma ya santa.. Ya taba ganin face dinta amma kuma ya manta aina ba...

Tana shiga falon ta tarar da umma tazo har ta fara aiki.. Ta ajiye hijab dinta agefe ta karba moper hannun umma ta cigaba da aikin..
Nan take bawa umma labarin abunda ya faru tsakaninta da safwan.. ita fa tana tsoron wannan yayan nasu

Umma tace karta damu kanta yanayinsa ne haka...

Kwanci tashi ba wuya, yau saura kwanan su uku su momy su dawo..

Bayan umma ta dawo daga gidansu safwan.. shigowarta kenan, ta dauki buta don ta kama ruwa, taji an banko kofar gidan da karfi..

A tsorace ta juyo ganin kawu tsaye yana huci yasa tai saurin ajiye butar, baki na rawa tace kawun yara kaine a gidan sannu da zuwa..
Daga mata hannu yayi sannan yace cikin zafin rai, wlh dije kinyi asara, ban kara sanin bakida tunani ba sae yau.. Ace kidau yar ki kikai ta chan wani gida karuwanci..

Umma ta dago da sauri tana kallon kawu, ya dora" emana karuwanci don ban yarda da wani aiki da akace tanayi ba,

Gidan aikin da masu gidan basa nan sae yayansu.. wanne irin aiki ne wannan

dan an raina mun hankali an nuna mun bani na haifeta ba..

Tau wallahi ina baki shawara kiyi gaggawar zuwa ki dawo da ita kafin kiga hukuncin dazan dauka akanki..

Ya juya fuuu ya banko kofa saura kadan ya balla kyauren..

Umma ta tsugunna a gurin kirjinta na zafe.. Wai sae yaushe ne zata fita daga wannan matsalar ne.. Innalillahi kawae take maimaitawa.....

Ko wacce irin matsala umma take ciki?? Menene asalin su Umma? Ina mahaifinsu nurr?? Ku biyoni..




🤓 Harphsart khabeer
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
2⃣6⃣➡3⃣0⃣

By Harphsart Rano✍


Dafe kirjinta tayi wanda ta kejin yana mata wani zafi...

Tananan a tsugunne kabir ya turo kofa ya shigo, ganin halin da umma take ciki ya sashi saurin karasowa


Lafiya umma?? Meke faruwa? Kasa amsa masa tayi illa girgiza kanta da takeyi,..

Kamata yayi a hankali ya kaita daki, Ruwa ta furta a hankali wanda yasa yae saurin juyawa ya kawo mata..

Bayan tasha ruwan ta lumshe idonta.

Kasancewar umma na fama da hawan jini yasa yaranta suke kokari wajen faranta mata rai.

Zuciyar kabir ta shiga tunanin me ya sami umma haka?? Yasan dai lalle koma mene ya matukar bata mata rai..

Nan take ya tuno ai yaga fitar wata mota kamar ta kawunsa lokacin da yake shigowa layin..

Jinjina kansa ya shga yi, yana ayyanawa a ransa; inde kuwa kawu ne wlh sae yaje har gida ya masa rashin mutunci..

Sae yaushe ne zae kyalesu su huta, wannan karon bazata sabuba... Ya gaji da cin kashin da ake musu, dole ya dau mataki...


Bayan ya idar da sallah isha, ya tarar da umma kwance alamun tana jin jiki.. Sannu Umma ya fada yana dubanta da tausayawa..

Murmushii tayi masa wanda daga gani kasan karfin hali ne.. tace yawwa abbana..

Yace Umma ya kamata gobe da safe muje asibiti a dubaki, a awna bp dinki, dazu Alhaji ya bamu kudin aikinmu(kabir yana zaman shago ne a kasuwar kwari)

Umma tace a ah abba na kudin zae mana wani amfanin.. Samomin paracetamol gurin habu me chemist, Ina sha shikenan, dama cion kaine ke damuna kawai..


Cikin dare umma jiki yayi zafi, sosae take jin jiki, kabir duk ya damu yana ta mata firfita.. Allah Allah yake gari ya waye ya kaita asibiti..

Gari na wayewa ya samo adaidaita sahu ya dora ta suka wuce asbiti..

Shiru shiru nurr tana sa ran ganin umma, hankalinta ya tashi tasan dole ba karamin abu ne zae hana umma zuwa ba..

Tana nan a zaune bayan tafiyar su iman skul, ta kasa tabuka komai, safwan ya sauko, kamshin turarensa ya sata juyo wa, kafe ta yae da ido yana dan nazarinta..

Basar wa yayi ya wuce zuwa dining area, Ina kwana tace, ba tare da ya kalleta ya amsa da lafiya..

Mikewa tayi a hankali tazo ta wuce shi ta shige kitchen..

To ita kuma wannan me yake damunta? Ya ayyana aransa.. da ganin yanda take bata cikin nutsuwarta..

Har zae fice, sae kuma yaji bazai iya tafiya ba tare da ya tambayeta meke damunta

saurin juyawa yayi, tsaye ya ganta a kitchen tana goge cooker gas..

Alamu taji ana kallonta yasa ta juyo tae saurin tambayar sa ko wani abin yakeso..

Murmushi ya sakar mata wanda shi kansa bai san ya iya shi ba..

Mamaki ne ya kamata wanda yasa ta tsayawa galala tana kallonsa..

Ikon Allah, ashe yasan yanda yake bala'en kyau idan yayi murmushi shi yasa bayayi..

Bata san sanda ya zo kusa da ita ba, sae ji tayi yace meke damunki?? Baki da lafiya ne??

Kasa bashi amsa tayi, mamaki ne ya kamashi, wai ko dai kurma ce,? kai ba kurma bace ai ya tuno lokacin da ta bashi hakuri..

Sake maimaitawa yayi a karo na biyu, a hankali ta furta, um um lafiya ta kalou.. Kusan mutuwar zaune yayi, dama haka ta iya magana.. Ko shisa bata son yi..

Murmushi ya kara sakar mata yace tou mesa na ganki kamar kina cikin damuwa..

Umma ta ta bashi amsa a takaice.. me sameta ya kara tambaya..

Nan take fada masa taji shiru har yanzu bata zo ba..

Shiru yayi na dan lokaci, sae kuma ya sauke ajiyar zuciya,.

Ba komai karki damu.. Ba abunda ya faru da ita, kila wani abun ya tsaida ta.. dauko hijab dinki muje mu gani kinji ko, ya samu kansa da furta mata..

Daga masa kai kawai tayi ta wuce shi da sauri ta tafi dauko hijab..

Yana nan tsaye yana tunani meke shirin faruwa dashi ne? Mesa baya iya controllin kansa indai yaganta.. Ta fito da sauri..

Ya wuce gaba tana binsa a baya.. Bayan sun shiga mota yake tambayer ta unguwarsu tace masa hotoro..



Harphsart khabeer✍
[9/13, 3:21 PM] Fati Novel: 📿📿📿📿📿📿📿

🎀Guguwar So🎀
1⃣0⃣➡1⃣5⃣

By harphsart Rano✍

Sun isa gidan misalin 8:30 dalilin dan tarazar dake tsakanin unguwowin biyu.. Jummai ta jagorancesu zuwa falon inda suna saka kafa Nurr taji wani ni imantaccen sanyi ya buge ta.. ta lumsje idon ta tana ayyanawa aranta lalle masu kudi sun hutu abunsu.. Wuri suka samu suka zauna suna jiran fitowar matr gidan.
Nurr ta rakube a gefe tana tunanin koya zaa karbe su a wannan gidan me kama da aljannar duniya.. Allah sa kar a wulakanta su.. Suna nan zaune suka ji karar saukowa daga sama.. Zuru sukae gaba daya suna jiran suka me saukowa..

Da fara'ar ta ta karaso a ah jummai ashe kun karaso.. gaba daya muka gaisheta ta amsa cikin sakin fuska.. Duba daya nurr tai mata ta fuskanci mace ce mai kirki.. Nan ta
DOWNLOAD
DOWNLOAD

Please Login or Register in order to submit comment