Join Our WhatsApp Group

Idan ku ka ga kun taba wani wuri ya fitar daku a shafinmu, sai ku danna back kuyo baya, ku sani yanzu muna amfani da tallan Popunder a shafin, so karatu zai muku dan wahala, amma ta hakanne kadai zamu iya cigaba da rike shafinnan. idan har bakwa son talla sai kuje ku yi subscription na shafinnan akan karamin kudi ku runga downloading kawai. SUBSCRIBE


DOWNLOAD

You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register
DOWNLOAD


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ILYA DAN MAI KARFI-01

ABUN AL'AJABI 1

A wani gari can cikin kasashen Gabas, an yi wani ana kiransa SAHABI, da matarsa wai ita MURJANATU.

Suna zaune cikin gidan gona Ba wadansu wadatattu ba ne sosai, amma kuma ba matalauta ba ne. Suna da yan dabbobi da gonaki. Abin da dai ya rage musu jin dadin
zaman duniya shi ne rashin magaji kawai. Allah bai nufe su da samun da ba.

Shekara da shekaru suna ta neman haihuwa, amma ba su samu ba. Ran nan kwanci tashi, sai Murjanatu ta samu ciki. Wai kada ka so ka ga irin murnar da Murjanatu da Sahabi suka yi. Tun cikin yana da wata hudu, Sahabi ya soma tanadin iccen wanka.

Ran nan da rana tsaka, Sahabi yana aiki a bayan gida, cikin gona, sai ya ji an rafsa guda,
Ayyururui... Ayyururui....har sau uku. Sahabi ya jefar da fartanya, ya sheko da gudu cikin gida. Da zuwansa kuwa ya tarar da abin da ya ke fatan ya gani. Murjanatu ta sauka, ta sami da, namiji, santilo. Da ranar ta kewayo, jama'a
suka taru, aka rada wa jaririn suna ILIYA.

Ana nan har yaro ya kusa ISA yaye, sai rashin lafiya YA same shi, kafafuwansa duka biyu, da hannu guda, suka shanye. Shikenan ya zauna a
haka, har ya girma. Daga kan dan gadonsa ba ya iya fita ko ina, sai dai a fitar da shi. Iyayensa suka yi bakin ciki kwarai, suka hakura Wata rana iyayen Iliya sun tafi gona, ba kowa gidan sai shi kadai, kan gadonsa, yana ta tunanin yadda duniya take, yana kulle-kullen abubuwan da zai yi, da yana da kafafu. Kwatsam, sai ya ji anyi sallama, Salamu alaikum, salamu alaikum! Sai Iliya ya amsa, Alaikas Salamu.

Kowane ne ya shigo! Sai ga wadansu mutane su uku, suna sanye da tufafi irin na Larabawa, sun yi shigar alhazai. Ko wannensu yana rike
da doguwar tasbaha, yana ja Suka zauna. Iliya yayi musu maraba, suka amsa masa da murna
Iliya ya dubi mutanen nan dakyau, ya ga ba irin mutanen da ya saba gani ba ne. Sai yazaci ko irin mutanen nan ne da ya kan ji ana cewa suna bi gari gari suna wa'azi.

Malaman nan suka tambayi Iliya ko akwai wani abinci yabasu su ci. Iliya ya ce Ba za'arasa ba, ku duba, inda duk kuka gani, ku dauka ku ci. Bana iya tashi, balle in duba muku." Suka tambaye shi abin da ya same shi. Ya ce, "Wurin nan da kuka ganni tun da aka haife ni a nan nake. Ban taba leka ko kofar gida ba.

Ko bayan daki ma sai ankai ni. Allah Sarkin jin kai! Ashe malaman nan ba mutane bane Mala'ikune aka aiko su jarraba Iliya, kuma su warkar da shi. Sai dayansu ya debo ruwa cikin kwarya, ya yi addu'a ya ba Iliya, ya ce, Wanke
fuskarka da Jikinka. Iliya ya karba da hannunsa
mai lafiyar, ya wanwanke. Kamar kiftawar ido, sai ya ga jikinsa sarai, kamar ba nasa ba. Kafafunsa da hannunsa shanyayyu duk sun mike, har in ba wanda ya sani ba, ba wanda zai zaci Iliya ya taba samun wata tawaya.

Ya miko kafafuwansa kasa daga kan gado, ya gurfana gaban malaman nan, ya yi musu godiya Cikin murna yaje ya dauko madara ya durkusa ya ba su. Wannan yakurba, ya mika wa wancan, har ya kewaya dukansu. Sa'a nan babbansu ya mikawa Iliya ya ce, Kaima karba ka sha Iliya.

Iliya ya karba ya sha Jim kadan, daya daga cikin malaman ya ce wa Iliya Yaya ka
ke jin jikin ka yanzu ??

Iliya yace, Na ji wani sabon karfi ya zo mini, har
ina jin kamar kasa ba zata iya daukata ba.
Sai babbansu ya ce wa Iliya yakara kurban madarar Bayan da Iliya ya kara shan madaran sai malamin ya ce, To, Iliya, ka gaskata TSARKAKKEN SARKI ALLAH Ka bi umurninsa, ka yi dukkan abinda ya hore ka da shi, Za ka fifita daga dukkan mutanen kasar nan. Za'a ji sunanka ko ina cikin duniya.

Komai wahala, kome hatsari kada ka yanke kauna ga Ubangijinka. Kuma wannan abu tabbatacce ne kuma rubutacce ne, cewa ba za ka mutu a wurin yaki ba kome tsananinsa.

Duk cikin duniyar nan ba wanda zai sami nasara akanka, sai mutum daya tak.
Ana kiransa da WARGAJI.
Za ka hadu da shi, amma ko kadan kada ka yi fada da shi.

Yanzu ka dauki aniya, ka tafi Birnin ƘIB......ILYA DAN MAI KARFI-02

Duk cikin duniyan nan ba wanda zai sami nasara a kanka, sai mutum daya tak. ana kiransa Wargaji, za ka hadu da shi, amma ko kadan kada ka yi fada da shi. Yanzu ka dauri aniya, ka tafi Birnin Kib, kada ka ce za ka tsaya ka bata karfinka a gona, ko a lambu, ko a daji."

Suna kare magana, sai Iliya ya nemi malaman nan ya rasa. Ya dimauta. hankaiinsa ya tashi, domin bai san dalilin da za shi Birnin Kib ba. Ga shi kuwa malaman sun bace balle ya tambaye su. Ya ga abun duk kamar cikin mafarki Zuwa can, hankalinsa ya dawo, ya yi godiya ga Ubangiji, ya nufi gona wurin iyayensa. Ya tarar da su, sun yi aiki, sun gaji, suna kwance, suna ta sharar barci. Ya yi sallama, ba su farka ba. Sai ya matsa. ya dauki gatari. ya dubi wani katon reshen kuka ya sare Cikin inuwarsa kuwa iyayensa ke kwance. Da karar saran, da ta faduwar itacen duka ba su sa iyayen Iliya sun farka daga barcinsu ba. Sai ya dauki sauran gatarorinsu ya kafe su a jikin itace, ya koma wani wuri ya Boye, yana dariya. Ya ce a ransa, "Idan sun farka za su yi aiki, ba su ga gaturansu ba, ai sa nema."

Can da zafin rana ya buge su, sai suka farka firgigit Suka duba sama, suka ga an sare reshen kukar, suka yi mamaki. Don sun tabbata sare wannan ice cikin dan lokaci haka, sai dai kamar katta goma. Suka duba ba su ga kowa ba, sai gaturansu kafe ga itace. Suka yi, suka yi, su cire, suka kasa. Da Iliya ya ga sun kasa sai ya fito yana dariya, ya sa hannu daya ya cire musu gaturansu. Ganin Iliya haka, sai suka bar mamakin sare ice, da na kafe gatura. Suka koma mamakin Iliya Duk wuri ya yi tsit, da uwar Iliya da ubansa suka kafa masa ido kuri, amma ba su gane shi ba sosai. Don kuwa sun san irin halin da suka bar shi a gida. Uban dai sai dubansa ya ke daga kasa har sama. Can suka gane dai dansu ne, Iliya, ya zama haka. Sai uban ya ta da kansa sama, ya yi wa Allah godiya.

Saboda mamaki iyayen Iliya suka kasa ce masa kome. Sai Iliya ya durkusa gabansu, ya ba su dukan labarin abin da ya faru. Ya kuma nuna musu zama irin nasu ba zai yi masa ba. Ya ce an umurce shida ya taf Birnin kib.

Iyayensa suka yi ta murna ganin dansu ya Mike amma kuma suka yi juyayi, da bakin ciki saboda rabuwa da shi. Iliya ya sake durkusawa, ya tausasa murya, ya ba iyayensa hakuri, ya yi musu magana mai dadi, yadda ransu zai yi dan sanyi. Sa'an nan ya roke su gafara, ya yi ban kwana. Tun daga nan wurin ya kama hanya zuwa Birnin Kib.

Yana cikin tafiya, sai ya gamu da wani mutum yana jaye da dan dukushin doki. Iliya ya tambayi mutumin ko zai sayar masa da shi. Abu kamar wasa, mai dukushi ya yarda, suka yi ciniki. Iliya ya san bashi da kudi, amma don kada a kure shi, sai ya sa hannu kawai cikin aljihu, kamar da wasa, sai ya ji kudi a ciki. Ya dauko ya biya doki. Daga nan sai wani tunani ya zo masa, ya ga ya fi kyau ya koma gida, ya kiwata dokin sa'an nan ya sake fita. Sai ya juya ya koma gida.

Iliya yasawa dokinsa suna KWALELE. Ya shiga kiwonsa yana horonsa yadda zai saba da wahala, da jure yunwa. Kafin wata uku dukushi ya cika, ya zama ingarma, wanda ba kamarsa a nan kurkusa. Ya zama sai harbin iska ya ke yi aturke, har ya fi ubangidansa kosawa a tafi.

Da Iliya ya ga lokacin tafiyarsa ya yi, sai ya je wurin iyayensa ya shaida musu. Ya roke su gafara, suka yi. masa kyakkyawar addu'a, suka yi ban kwana da juna Kashegari tun da asuba Iliya ya shirya, ya hau Kwalele, yatafi

GAMUWAR ILIYA DA WARGAJI.

Ilya ya mika cikin daji yana ta tafiya, bai san inda ya ke nufa ba, har dare ya yi masa. Ga gajiya da yunwa, ga kishin ruwa, kuma ga dokinsa ya gaji, yana dai ta tafiya ne kurum. Kwamtsam sai ga wani lambu a gabansa, cike da 'ya'yan itatuwa da furanni masu ban sha'awa. Daga tsakiyar lambun kuma akwai wata alfarwa wato tanti, ta farin alharini, a kafe. Iliya ya sauka ya daure dokinsa, ya je ya leka cikin alfarwar bai ga kowa ba, sai gado na karfe, da shimfidu, da matasan kai. Bai yi wata wata ba, sai ya haye gadon ya yi kwanciyarsa, ya yi ta sharar barci, har gari ya waye. Rana ta sake faduwa, dare ya yi, gari ya sake wayewa, har dai wajen kwana uku, bai farka ba.

A ranar dare na ukun Iliya yana tsakar barci, sai Kwalele ya rika jin wani irin motsi da rugumniya an nufo wajen alfarwan nan Kamar dai hadari ya taso, kasa na motsi kamar za ta tsage. Itatuwa suna ta faduwa, har koguna suna fantsamar da ruwa cikin daji. Sai Kwalele ya yi haniniya da karfi, don Iliya ya farka. Ya yi masa ishara da cewar ya tashi maza ga wani abin firgici nan tafe. Ashe wurin shan iskar Wargaji ne, wanda aka fadawa Iliya kada ya yarda su yi fada da shi.

Can, sai Iliya ya yi firgigi ya tashi. Kwalele yayi masa ishara da ya hau sama ya Boye. Nan da nan Iliya ya haye bisa wani dogon ice, na cikin lambun, ya make. Kwalele kuma ya sami wuri ya Boye shima.

Zuwa can, sai Wargaji ya iso, yana bisa wani doki kato, daga nesa kamar tsauni. Ya sauka abakin kofar alfarwar. Iliya ya dube shi da kyau, ya ga lalle ya isa abin tsoro, don bai taba ganin mutum da girma kamarsa ba. Shi mutum ne mai fadi, ga tsawo, har ya kere itatuwan da ke wurin. Sai ya ga ya jawo wani dogon akwati daga bayan dokinsa, ya dauko wani irin mabudi na zinariya, ya bude akwatin. Sai ga wata kyakkyawar 'ya, jawur da ita, kamar aljana ta fito. Ta ci ado da kaya iri iri na zinari, da lu'ulu'u, da jauhari Tana sanye da wadansu irin takalma na sakakken jan alharini. Fuskar ta sai kyalli ta ke yi kamar madubi Tana da dogon wuya ga idanu dara-dara, hanci har baka, gashin kanta sai tasa hannu ta tattara shi don kar ya zube Kasa.

Wargaji ya kama hannun matan nan suka shiga cikin alfarwa. Ta bude wata jaka, ta fito da teburi ta girke, ta fito da abinci da abin sha. Suka zauna suka ci, suka sha, suka koshi. Sa'annan Wargaji ya hau gado ya kwanta, ta rika yi masa fita. Nan da nan barci ya kwashe shi. Da ta ga ya yi barci, sai ta fito don ta mike kafa, ta kuma debe kewa, cikin lambu. Tana tafe tana rera wata irin waka a hankali, mai dadin gaske, wadda ke jirkita hankalin mai saurarenta. Can sai ta daga ido sama, ta hangi Iliya bisa itace make. Ta dube shi da kyau ta ce. "Ya kai wannan kyakkyawan saurayi, sauko."
Nan da nan lliya ya sauko da rawar jiki. Ta kama hannunsa suka shiga cikin alfarwar Wargaji yana ta sharar barci. Ta bude bakin aljihunsa, ta saka Iliya ciki. Iliya ya ji kamar an saka shi cikin wata rijiya mai zurfi.

Bayan an jima kadan Wargaji ya tashi daga barci, ya shisshirya, ya dauki yarinyan nan ya saka akwati ya kulle. ya sarkafa akwatin a kucciyar sirdi. Ya kama hanyar gida. Ya doshi wadansu dogwayen tsaunuka da a ke kira "Tsarkakkun Duwatsu" Wannan wuri ba mahalukin da ya taba zuwa gareshi. Babu kuwa mai iya zuwa wurin. Nan ne fadar GIJIGIJI UBAN WARGAJI. Akwai gine gine masu kawa iri iri a' wurin. Akwai dukiya da samun duniya kowane iri a wurin.

Shi Gijigiji ya fi Wargaji girma, da cika, da kasaita, da kwarjini, da cika fuska. Amma ya tsufa ainun, har ya kai ga makancewa. Suna cikin tafiya sai Wargaji ya ga dokinsa ba ya sauri sosai kamar yadda ya saba. Kuma yana tafe yana sassarfa kamar zai fadi. Wargaji ya yi fushi ya buge shi. Sai dokin ya yi ishara, ya ce, "Yi hakuri, ya shugabana. Karfina na in dauke ka kai da uwargidanka ne kadai, amma ba ni da karfin da zan dauki halitta uku."

Wargaji ya dudduba ko ina bai ga kowa ba, sai ya ji aljihunsa da dan nauyi. Ya sa hannu, ya dauko Iliya. Ya dube shi da kyau, ya ce, "Kai Bil'adama, yaya aka yi har kazo nan, har kuma ka shiga cikin aljihuna?" Iliya ko yaushe mai tawakkali ne ga Ubangiji, kuma ba ya da tsoro, ya dubi Wargaji sosai, ba da wani tsoro ko razana ba, ya ce, "Shugabana, uwargidanka ce ta saka ni cikin aljihunka, ya shugabana." Nan da nan Wargaji ya cika da hushi, ya dauki akwatin nan da matar ke ciki, ya yi jifa da shi bisa wadansu duwatsu a tsakiyar wani kogi, ya ce, "Zauna nan, mutuniyar banza, Aljana ba. Nan za ki yi ta zama har ranar tashin kiyama."

Wargji ya dauki Iliya ya rungume a gabansa kan doki, suka ci gaba. Zuwa can Wargaji ya huce, ya tambayi Iliya kasarsu, da garinsu, da labarinsa duka dai. Iliya kuma ya kwashe labarinsa tun daga farko har karshe ya fada masa. Nan take sai soyayya ta kullu tsakaninsu. Suka ci gaba da tafiya suna ta labari kamar abokai.Amma kafin su isa gida, sai Wargaji ya fada wa Iliya cewa idan sun isa gida, zai kai shi don ya gai da Gijigiji, wato ubansa. Ya fada masa idan Gijigiji ya miko hannu don su gaisa kada Iliya ya mika masa hannu, Ya ce masa da sun isa, akwai makera a kofar gidan, Iliya yayi maza ya saka karfe a wuta, idan Gijigiji ya miko hannu su gaisa, ya mika masa karfen nan a maimakon Hannunsa. Ilya ya ce to, suka ci gaba da tafiya, har suka kawo kofar fada. Iliya ya cika da mamakin irin ginin wurin, watau yadda aka yi shi da farin dutse, aka yi masa zane iri iri. Daga ciki kuma ko ina ka duba sai kujeru da shimfidu. Hatta tagogin gidan na madubi ne ga labule launi iri daban daban, ga fitilu ko ida. Da dai sauran kayan daula da ni'imomin duniya.

Zuwa can Gijigiji ya fito ya tsaya a kofar zaure don ya yi wa Wargaji barka da zuwa. Ya tambaye shi garuruwan da ya je. Wargaji ya fada masa ya je kasashen Gabas ne. Har daga can ya samo aboki. Gijigiji ya ce a kawo Iliya su gaisa.

Da ma da isarsu Iliya ya sa wani katon karfe cikin wuta ya yi ta zuga ya yi ja wur, yana jira ne a kira shi. Wargaji ya zo suka tafi. Gijigiji ya miko wa Iliya hany don su gaisa, sai Iliya ya mika masa karfen nan. Gijigiji ya runtse karfen kamar wanda ke gaisawa da wani Zuwa can ya saki, karfen ya yi sanyi, ya ce, "Lalle Wargaji ka samo aboki wanda ya kamace ka. Ya cancanci ya zama abokinka sosai."ILYA ƊAN MAI KARFI-03

Kashegari Da suka fito kofar gida, suka tsaya suna hangen filin karkara da itatuwa. Iliya ya duba haka ya hangi dokinsa Kwalele yana kiwo kusa da gidan Murna ta kama Iliya ya ruga ya kamo shi. Wargaji ya yi ta mamakin wannan irin doki. Nan da nan suka daure shi a turke, aka zube masa abinci aka ba shi ruwa ya sha.

Maraice na yi su Wargaji suka hau dawakansu suka tafi shan iska. Suka bi ta gefen tsaunin nan totar, suna tabi, suna annashuwa. Suka yi ta tafiya har suka kai ga wani wuri mai duwatsu. A kusa da duwatsun sai suka ga wani akwati a bude, an rubuta "Wannan akwati an yi shi ne domin mai shi, ba kuwa zai yi daidai da kowa ba cikin duniyan nan sai mai shi." Ashe da ma wannan akwati saboda Wargaji aka yi shi. Sai Iliya ya ce, "Bari in gwada in gani ko nawa ne." Ya sauka ya shiga cikin akwati, amma bai yi masa daidai ba, ya fito. Wargaji kuma ya ce, "Lalle nawa ne, bari mu gani." Sai shi kuma ya sauka ya shiga ciki, ya kuwa yi daidai da shi. kamar da dai saida aka gwada da shi sa'annan aka yi shi. Ya cika shi har baya iya motsawa. Daga ciki, ya miko hannunsa ya rufe bakin akwatin. Shikenan sai akwati ya kulle kam, ba ko 'yar kofar da iska zai iya shiga.

Amma Wargaji bai yi wa Iliya bankwana ba, bai kuma bar masa wata wasiyya zuwa ga ubansa ba. Saboda haka ya ce lliya ya bude shi, zai yi masa wasiyya, kuma su yi ban kwana da juna. Iliya ya sa hannu, ya yi, ya yi ya bude akwatin, amma ya kasa motsa ko da murfin. Ransa ya ɓaci, hankalinsa ya dugunzuma.
ya ce wa Wargaji da karfi, "Ba na iya bude akwatin ?" Wargaji ya ce. "Dauki takobina na yaki, ka sari gefen akwatin." Iliya ya sa hannu zai dauki takobi, amma ya kasa cira shi saboda nauyi. Ya fadawa Wargaji ba zai iya daukar takobin ba. Wargaji ya ce. "Matso kusa da ni." Iliya ya matsa. Wargaji ya feso wa Iliya dukan Karfinsa. Nan da nan Iliya ya dauki takobin da sauri, kamar wanda ya dauki kara. Ya sari akwatin da karfi. Karar saran ta cika dajin tsaunuka suka kama wuta, duk wurin ya rude kamar sama da kasa za su hadu don firgita. Tartsatsin wuta ya watsu ko ina. Maimakon murfin akwatin ya bude, sai ya kara kullewa da karfi.

Wargaji ya cewa Iliya, "Kara sarawa dai da karfi." Iliya ya sake saran akwati. Amma saboda tsananin karar. har lliya da kansa ya gigice. Wuta ta kama, hayaki ya murtuke wurin. Akwatin kuwa ya kara kulewa..
Can da kura ta kwanta, Wargaji ya cc, "Iliya, matso in kara maka karfi. Zan baka dukan Karfin da ke gare ni." lliya ya ce, "Ya shugabana, idan karfin da ke gareni ya fi haka, ko kasa bazata iya dauka ta ba. Na gode kwarai. Ina so ka fadi dukan abin da ka ke bukata, idan ina iyawa zan yi maka.Wargaji ya ce, "Ba sauran abin da za ka iya yi mini Ni dai tawa ta kare. Ka ga akwatin nan, kabarina kenan. Na gode maka, Allah ya yi maka albarka. Allah ya fid da kai daga sharrin mutane. Idan ka sami damar komawa, ka yi mini ban kwana ga mahaifina. Ka fada masa irin kaddarar da ta same ni awannan wuri. Allah ya kaddara saduwarmu a Darussalamu."

Wannan magana ta Wargaji ta sa hankalin Iliya ya tashi kwarai, ransa ya baci, ya rasa abin da ke masa dadi cikin duniya. Ya kuma rasa abin da zai yi. Sai ya fashe da kuka. Ya roki Wargaji gafara, ya yi masa kyakkyawar addu'a. Ya dade nan a gefen akwatin, yana kuka. Can da hankalinsa ya komo, ya tuna komai kaddara ce ta Ubangiji, saboda haka, sai ya yi tunani a ransa, ya ce, "Ni Iliya, yanzu in koma in fadawa Gijigiji me? Ai ba zai yiwu in koma wurin nan ba." Sai ya taka dokinsa ya hau, ya yi ta tafiya, bai san wajen da ya ke nufa ba. Ya bi gangaren tsaunin nan ya yi ta tafiya har ya yi nisa, sa'an nan ya waiwayo, sai ya hangi hawayen Wargaji suna zuba ta kafar akwatin. Tausayi ya kara kama shi, ya sake fashewa da kuka. Sai ya sauka ya zauna yana ta tunani, bakin ciki ya rufe shi. Bayan ya dade a zaune, sai kuma ya tashi ya ci gaba da tafiya.

ILIYA YA SHIGA DUNIYA

Iliya ya yi ta tafiya kwana da kwanaki har ya kai wani dan gari, ya sauka ya huta kwana biyu. Ba da dadewa ba mutanen garin nan suka saba da shi, suka yi murna da zuwansa. Ya zama dai kamar wani dan uwansu ne da ma ya tafi wani wuri ya komo. Bayan ya huta, ran nan sai ya ce musu zai wuce zuwa Birnin Kib. Mutanen suka yi mamaki kwarai.A kan hanyar Bimin Kib kuwa akwai wani gawurtaccen dodo wanda ke tsare ayari, ko taron yan yaki, ya kore, su, ya kwashe musu dukiya. Kome jarumtakar mayaka, dodon nan yana iya korarsu. Labarinsa ya shahara ko ina cikin kasar, har ma ya kashe hanyar sam, babu mai binta, Ana kiran dodon GOGAJI.

Gogaji Yana da 'ya'ya tara. Daga cikinsu akwai wata yarinya ana kiranta MALELE tana da ido daya. Ita ce ta gaji dukan sihirce-sihircen Gogaji, da halayensa.

Saboda sanin dodon nan, mutanen garin nan suka yi matukar kokarinsu su hana Iliya zuwa Kib, amma ya ki. Da suka gaji, sai suka kyale shi. Suka shawarce shi da ya sake hanya. Ya nace lalle da shi ta wannan hanyar zai bi. Suka yi ban kwana da shi, ya tafi.

Iliya ba ya takama da kome sai takobi, da karfin da Allah ya ba shi. Sirdinsa yana da majayi goma sha biyu. Takobinsa kuwa ko dutse ya sara da shi zai raba shi biyu. Sa'an
DOWNLOAD
DOWNLOAD
Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3Chapter 4

Please Login or Register in order to submit comment