Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ba, tana dai da abin da yake so a tattare da mace, amma batun kyawun fuska yafi son fara sosai, ita kuma tana da duhu musamman da take cikin fararen tas dan duk yan uwanta sun fita haske hakan ya saka ake ganin har kyau din ma sun fita. Jingina dogon tunanin da ba zai amfane shi ba yayi, suka shiga dakin Mama in da take tare da manyan kawayenta, ai sai kawai ta rungume shi cikin farin ciki, baka jin tashin komai sai gud'a da sambarka, ita kadai tasan yadda take ji da auren nan nasa, a kalla idon mutane zai bar kanshi, kuma tana fatan Asma'u ta shirya mata shi, ya bar duk wata banzar al'adar sa, dan ita a ganin ta ma, idan har mace ta kasa daidaita dabi'u da al'adun mijinta, zuwa nata da take so to tabbas bata kai mace ha, ko tace ma kawai ta rako mata duniya ne. Sun dan jima a dakin sannan suka fito suka rankaya gidan Abban.
Sanye yake da riga jamfa da wando babu batun babbar riga dan babu ita a tsarin sa, musamman lokacin zafi ne ko da Mama tayi masa magana sai yace mata ai tana mota zai saka idan sun fita, nan kuwa ko dinka ta be ba, hula ma dan dai kawai babu yadda zai ne, amma tabbas yana dawowa zai cire kayan dan ba zai iya ba, saukinta ma a dinner din suit zasu saka da ace manyan kayan zai sake maimaitawa toh da an samu matsala dan shi a rayuwar sa baya son abinda zai zo ya takura masa.
Sanda suka isa gidan sauran yan daurin auren basu gama watsewa ba, da yawan su ma suna zazzaune ne a kofar gidan an saka rumfa suna shan iska ana hira cike da Raha, yawanci su yan Sumailan ne sai yan tsirari da suke abokan Abba. Shi kansa Abban yana wajen tashi yayi ya amsa waya ya dawo.
Labarin isowar angwayen ya riski cikin gidan, aka shiga shisshiryawa shigowar tasu, asma'u da taji abun daga sama sai da taji wani ras a kirjinta, tayi saurin dafe shi ta mike tana kokarin neman hanyar ficewa daga gidan, tun dazu umma take sababin su koma gidan Safiyya a aiko musu da abinci amma ya makale a dakin Umman taki fita, sai gashi yanzu tana son fitar amma bata san yadda zatayi ba, dan dole idan tace zata fita sai sun ganta, abinda ita kuma bata so kenan. Ganin take taken ta na son guduwa ya saka Aunty Hauwa ta dakatar da ita, ala dole ta dawo ta zauna tana kudundunewa a cikin mayafin ta.
Hargowar su ta fara jiyowa alamun sun shigo ciki, tana jin wasu mata da bsta gane su waya ba suna ta tsokanar su,su kuma suna biye musu, irin dai wasan jika da kakan nan, shine a gaba wajen zakewa da amsawa tamkar bashi ba, kamar ba ango ba ma dan babu wata alama da zata nuna a jikinsa da zaka gane ango ne, tana jin sanda suka dungumo suka shigo falon umman, lokacin su Aunty Hauwa duk sun fita falon, nan dai akayi addu'a wanda aunty hauwan ce ta assasa da babu me wannan tunanin a cikin su, sannan suka yi waje suna cigaba da hayaniyar su. Wani ne cikin abokan ya tabo shi, yace

"Ina amarya ne?"

" Ba za'a hadu wajen dinner ba, kyale ta kawai pls."

" Ok."

" Ku jirani a waje ina zuwa." Yayi hanyar dakin su Abbati, suka sheke da dariya, wato ba zasu ga Amaryar ba amma shi zai ganta, ba komai ai akwai anjima. Waje sukayi shi kuma ya shiga dakin ya tarar dasu da abokan su, Abbati yayi saurin tashi suka gaisa sannan yace ya taimaka ya kira masa ita, fita yayi sauran abokan ma suka fita ya zama sai shi kadai a ciki, a tsaye yake be zauna ba, da ba dan ace yana so ya kara jaddada mata maganar dinner din ba , da babu abinda zai saka shi nemanta, tunda dai an daura ai shikenan, duk ma abinda take tunani ko ji dashi zasu gauraya ne, daga shi sai ita yadda zai nuna mata shi din gogaggen dan duniya ne, idan aka ce ta sake gaya masa magana ma ba zata sake ba.
Sanda kiran ya isketa kusan shidewa tayi, bata hango rangwame wajen Adam ba, shiyasa bata son duk abinda zai hada su waje daya daga shi sai ita, narai narai tayi da fuska, kamar zatayi kuka dan har kwalla ta cika mata ido, ganin yadda ido ya dawo kanta ya sakata tashi ta bi bayansa, duk taku daya da take ji take kamar ta saki fitsari a wando saboda zulumi. A hankali ta tura kofar sai kuma ta tsaya ta kasa shiga, yana kallon inuwar ta, ya ja tsaki ganin zata bata masa lokaci, ya fizgota da hannun sa ta dawo cikin dakin,durkushewa tayi da sauri jikinta na rawa tamkar mazari. Kallon ta yake yana kokarin ganin ko tayi abinda ya sakata, yana nan zanen kamar jiyan babu abinda ya chanja. Dogon tsaki ya ja, sai yayi maganin ta kuwa, yanzu ba wannan ne ya kawo shi ba tukunna

"Ina kayan da na bawa Abbati ya kawo miki?"

Shiru tayi, ya sake maimaitawa bata amsa ba, sai da ya daka mata tsawa me karfi sannan tace a kidime.

"Suna wajen Hidaya."

"Ok." Yace yana matsowa daf da ita, ya daga ta gami da fizge mayafin da tayi lullubi dashi, ya rage daga ita sai tsuran kayan jikinta, riga ce fitted da skirt da yayi daidai da jikinta, bin ta ya dinga yi da wani shu'umin kallo, ya lashe lips dinsa na k'asa yana kallon saman kirjinta, hannu ta sa da nufin karewa ya sa karfi ya murde hannun har sai da tayi kara.

"Baki isa ki hanani abinda na saka kudi na siya ba, karki sake idan ba haka ba, zaki fuskanci hukunci me tsananin."

Yawo maganar ta shiga yi mata akai, siya? Kenan ba auren ta yayi ba ma, siyan ta yayi, da lefen kenan ya siye ta ko da sadaki? Bata gama tunani ba sai jin hannun mutum tayi a jikinta, ta firgice tana kokarin guduwa, hannu daya ya saka ya matse ta kam, ya shiga taba ta duk in da yaga dama, kuka take sosai ta rasa yadda zatayi dan ya hana mata ko da kwakkwaran motsi ne, sai da ya ga dama dan kansa, sannan ya ture ta da karfi tayi baya saura kad'an ta fadi Allah ya taimaka ta tsaya a kafarta, be ko kalleta ba ya juya ya fice yana maida numfashi, ba zai iya resisting ba idan ya tsaya, komai zai iya faruwa.
Durkushewa tayi a wajen ta saki kuka me cin rai, bata taba ganin aure irin nata ba, duk wata amarya a wannan ranar tana cikin farin ciki mara misaltuwa saboda auren wanda take so yake son ta. Sai dai ita akasin haka ne a gareta, babu digon soyayyar ta a tattare da adam, tun tana yarinya Adam be tana kaunar ta ba, be taba tausayin ta ba, illa ma duk sanda suka hadu ko a gida ko a wani waje sai yayi dwewrieiririwroieoei e pie I i a little more Ta yaya zata iya? Me yasa babu wanda yake hango mata abinda take hangowa a gaba, me yasa? Ko kuma dai suna hango matan kawai babu yadda zasu yi ne, musamman Umma da tafi kowa saninta, ita ya kamata tafi kowa tausaya mata, amma sai taga kamar itama bata damu ba. Cigaba da zama tayi a dakin har sai da yamma tayi likis, sai da Abbati yazo sannan aka san tana dakin, dan har hankali ya fara tashi abna tunanin in da taje, idonta ya yi luhu luhu saboda tsabagen kuka, haka dai aka babbata baki sannan ta wuce dakin Abba, kasancewar daga wajen dinner din za'a wuce da ita ba zata dawo ba, nasiha sosai yayi mata wadda ta sake kashe mata jiki, ta kara volume din kukan ta dan kukan ne kadai yake rage mata radadin da take ji a ranta. Shi kansa Abban duk dauriyar da yake sai da yaji ya karaya, hawayen da ita suka tsaya masa a rai, ya nemi dan guntun farin cikin da yayi saura ya rasa, ya dinga ganin baiken sa, da ya barta zuwa lokacin ta, da be yi gaggawa ba. Shi da kansa ya dinga bata hakuri, tayi shiru tana sauraren sa cikin yanayin karaya, umma kuwa kasa cewa komai tayi, har Ya Hadiza ta shigo ta taimaka mata zuwa dakin ta, sannan ta sakata shiryawa saboda dinner din, bata musa ba, dan musun bashi da amfani tunda aikin gama ya riga ya gama, sai dai tana wanka tana kuka sosai, hakan ya jawo mata dadewa sosai a ciki, sai da Rauda ta kwankwasa mata sannan ta fito, suka taimaka mata ta shirya a cikin gown din da ya kawo, gown din da bata da maraba da ta arna sai dogon hannun net da ke jiki, mayafi fari ta dora akai da ya rufe mata duk wajen da yake a bude a rigar, kirjinta da sangalalin hannun ta, takalmin ne dai ba zata iya sak'awa ba saboda ya mata tsayi da yawa, bata ma iya tafiya dashi ba.
Duk abubuwan bukatuwar ta sun yi gaba kafin ta iso, hatta kayan sawarta da komai rankatataf an kai mata su, yadda ana gamawa zasu wuce chan gidan, dama duk wanda suke da bukatar ganin gidan Amarya sun gani tuni, shiyasa kawai aka yanke shawarar musamman ganin dare zai yi kuma shi kansa Adam din ya fadawa Mama yau yake so a kawota, har su Nadeeya na tsokanar da yayi rashin kunya, yayi kuwa mirsisi yana jin su yayi gaba abin sa. Ita kuwa Mama farin cikin da take ciki ba zai fadu ba, ta hasaso shiryuwar danta, tunda duk alamun sa sun nuna yana son Asma'un, a kalla zatayi galaba a kansa a wasu abubuwan da yawa.
Tuni wajen ya cika da jama'ar Adam da kawayen Mama sai su Nadeeya kowa da jama'ar ta, sai bangaren su Asma'un suka tashi yan kad'an, duk suka koma suka darare dan babu ma wanda ya nuna jin dadin ganin su, dama basu da yawa dududu su goma ne kawai, sai Asma'un da Rauda da Hidaya, sai kawarta guda daya, zuwan su ne ma wajen ya saka su Nadeeya nuna sun gansu, aka raka amarya wajenta duk kunya ta isheta, kamar ta tsaga kasa ta shige dan ita ire-iren abubuwan nan tun da ma ba zuwa take ba. Tana zama suna isowa cikin zugar su guda, sun sa suit bakake sai uban gayyar da ya saka fara tayi masifar karbar sa kasancewar shi fari sosai. Nan da nan wajen ya kachame. Baka jin komai sai tashin kida me masifar kara da ya saka haifar mata da matsanancin ciwon kai. Zama yayi a gefenta, daf da ita har tana jin jikinsa a gefen nata, kafarta ya take mata bayan ya zauna, ta kalle shi da sauri ya watsa mata harara, tayi saurin tun k'asa da kanta. Tana jin shi ya lalubo hannun ta, ya matse shi sosai har sai da tayi kwalla, ya sakar mata murmushi yana matsowa daf da ita kamar zai fad'a mata wani abu, ta runtse idon ta da sauri, tana jin sanda ya furta.

"Kinyi kyau matar Adam!" Ya saki murmushin gefen nan, wanda shi kadai yasan manufarsa sai ita da take hasashe!

Rayuwar Mace labari ne daya tamkar da dubu, akwai kalubale a rayuwar asma'u, a rayuwar da yawa yawan mata! Amma sai dai me?
Me zai faru? Wanne irin zama ne zai kasance tsakanin ta da shi? Mata da yawa suna zaune da mazaje masu halin Adam ko fiye, amma kullum magana daya ce, muyi hakuri!
Akwai haske tattare da RAYUWAR ta a gaba, hasken da zai yaye mata dukkan damuwar ta!
Soyayya me tsafta, soyayya me tsayawa a kalbi! Ku biyo zafafa biyar dan ganin yadda zata kasance a RAYUWAR Mace! Rayuwar Asma'u


_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/21, 10:52 PM] Mummyn Yara: *RAYUWAR MACE*
_Hafsat Rano_
Free Page (3)

***
Tun da suka dauki hanya suke masa shakiyance be ce dasu uffan ba, ya riga ya san dole suyi yadda ya dinga kuranta musu ita, ba karamin bata masa rai tayi ba ta kuma maida level dinsa baya a cikin abokan sa, ba dan ya kwallafa rai akanta ba babu abinda zai sa ya aureta dan shi baya son mace me duhun kai. Tsaki ya dinga ja har suka zo in da zasu rabu, ya sauke su ya fizgi motar kamar zai tashi sama sai gida.
A falo ya tarar da Hajiyar da tarin akwatunan lefe tare da sisters dinsa su uku da suka je hado kayan, suna zaune suna dubawa ya shigo ransa a bace zai wuce Nadiya ta dakatar dashi

"Boy baka gammu bane?"

"Na ganku mana." Yace yayi wucewar sa ya haye sama ya barsu da wagaggen baki.

"Ina ga dai an batawa boy rai, yadda yake zumudin auren nan ai ya tsaya ya ga komai."

" Gaskiya dai, abun ya motsa."

Fadila tace tana dariya

" Bari naje naji ko menene ya faru." Nabeela ta mike Hajiya ta dakatar da ita

"Ku rabu dashi kila shi da abokan sa ne, zai sauko anjima kadan idan ya watsa ruwa."

Komawa tayi ta zauna suka cigaba da maganar auren suna hada kayan da lissafin abubuwan da za'a siya kuma, Hajiyar na jin su tana amsa waya akai-akai Adam din ya sauko ya zauna a kusa da Nadeeya ya tankwashe kafar sa yana kallon kayan.

"Have a look, kayan wife din ka ne."

Dan wara idon sa yayi akan kayan sai kuma ya dauke kai yana kallon Hajiyar

"Mah ba zai yiwu a dawo da bikin nan next week ba?"

"Next week kuma? Ai kamar yau ne upper week din Adam, hakuri zakayi a samu ayi shirye shiryen komai a nutse."

Shiru yayi be sake cewa komai ba, ya ja baya ya jingina da kujera ya ciro wayar sa ya shiga chatting da yan matan sa, hakan ya saka shi manta abinda ya faru, har ya sake suka shiga hira da su kafin su tattara su tafi akan zasu dawo gobe saboda wasu kayan da basu gama siya ba.

***Tsaye Ya Hadiza take a kanta tunda ta shigo take kuka ta ki fad'a mata abinda ya faru, ita kanta ji take kamar tayi kukan dan ta san yanayin da Asma'un take ciki wanda ta taba shiga kusan irin sa Allah ya kiyaye Abba ya sakko aka daidaita, shiyasa take matukar tausayin ta dan mutum irin Adam ace shine mijinka ba karamin tashin hankali bane.

"Ki fad'a min abinda ya faru dan Allah, hankali na ba zai kwanta ba kuma wannan kukan sai ya saka miki ciwo."

Bayan hannun ta, tasa ta share hawayen sannan ta hau ciro hijab din jikinta saboda zafi da hucin da jikin ta ke fitarwa. Duk Ya Hadizan na tsaye akanta har ta cire ta ninke sannan ta hau kokarin kakalo murmushi ta dora a saman jar fuskar ta.

" Wani abu yace miki?"

Da ka ta amsa mata tana jin wasu hawayen na neman zubowa.

" Karki yarda ki biye wa maganganun sa dan irin Adam xasu iya karar miki da hawayen ki tas babu abinda ya dame su. He's not worth your tears, ki nutsu ki shiga kai wa Allah kukan ki, sai kiga komai yazo da sauki ta inda bamu zata ba."

" In sha Allah." Tace tana kwanciya.

Fita Ya Hadizan tayi bayan ta kara bata baki, ta barta tana sakawa da warwarewa, ta riga ta san rayuwar ta tazo karshe, dan tana jin komai zai iya faruwa a zaman ta da mutum kamar Adam, bata san yadda zata kasance ba amma tana da yakinin zaman ba zai taba dadi ba.

Shirye shirye ya kankama sosai a baangarorin biyu, ita Umma dai tana yin komai ne domin ya zama dole amma ba wai don son auren ba, sai dai bata da damar nunawa saboda Asma'un da Abba dan ba zata yarda ta bata kofar da zata bijire wa mahaifin ta ba. Satin ta guda ta dawo gida a lokacin ne aka shiga yi mata yan gyararrakin mata na al'adah duk da ba wani zafafawa akayi ba amma kuma dole dai zaka yi auren 'yarka ka dan tabuka wani abu ko yaya.
Komai baya mata dadi duk abinda ake mata kawai tana bi ne don babu yadda zata yi, saukin ta ma tun da yazo gidan Ya Hadiza be sake dawowa ba, sai magana da yayi mata a whatspp akan abinda take bukata tace babu, sai missed video calls dinsa da ta gani sau biyu bata bi ba, shikenan shima be sake bin kanta ba dama Nadeeya ce tace masa ana tambaya shiyasa ma ya tambaye ta, abinda tayi masa ranar yayi masifar bata masa rai shiyasa ya tattara ya watsar da ita ya cigaba da shirye shiryen sa dan babu fashi a auren dan yadda yake ji idan be aure ta ba akwai matsala.

Saura sati daya bikin suka kawo lefe, akwatuna goma cif masu kyau da tsada, tun daga nan hankalin ta ya kara tashi sosai, ta yarda da gaske dai auren babu fashi, babu abu daya da ya burgeta a kayan dan bata son duk wani abu da ya danganci Adam din, sosai take jin tsanar sa. Bayan an karbi lefen kowa ya watse su Ya Hadiza suka zauna zaman yi mata nasiha dan idan aka shiga satin bikin babu me sukunin zama yayi mata, jin su kawai take dan duk abinda suke fad'a bata jin zata iya yin guda daya, ita dai kawai ta riga ta san zatayi aure ne dan biyayya ga mahaifin ta.
Da daddare kafin duk su watse sai gashi ya zo, gabanta ne ya fadi da taji Areef yace yazo, duk suka zuba mata ido tayi saurin zamewa daga zaunen da take ta kwanta kuka na taso mata.

"Tashi zakiyi kije, kiyi hakuri." Ya Hadiza tayi maganar tana mikewa, tashi tayi daga kwanciyar, ta ja hijab dinta dage gefe zata saka ta girgiza mata kai

" Musulunci ma ya halatta mishi ganin wani abu sashe na daga gareki, ki saka mayafi dan Allah, sai ki dauki Hibba kuje."

Bata yi mata musu ba, ta ajiye Hijab din ta karbi mayafin dake jikin kanwarta Rauda ta yafa, ta rik'e hannun hibba din suka fita, already ya shigo yana falon Abba shi da Abbaty da Yaya Ibrahim. Da sallama ta shigo duk suka juyo suna kallon ta, sannan suka amsa, murmushi yayi mata tayi kamar bata gani ba, ta samu gefe chan ta zauna sai suka tashi suka fita ya zama daga ita sai shi sai Hibba da ta makale a kusa da ita dan tana da kiwa. Tsam ya taso daga wajen zaman sa ya dawo kusa da ita, har tana jin kanshin turaren sa sosai, bata dago ba ta gaishe shi ya amsa yana bin ta da mayen kallon sa, riga da skirt ne a jikinta simple dinki amma tayi kyau sosai, fuskar ta fayau babu hoda sai yar rama da tayi akan ranar da ya ganta a kitchen.

"Fine baby, ya sunan ki?" Ya mika ma Hibba hannu ta noke yayi murmushi

"Madam ya gida?"

"Madam?" Tace a ranta

"Lafiya lou." Ta amsa tana mummuraza yan yatsun hannun ta. Kallon hannun yayi, ya kai nasa hannun ya kama tayi saurin janye wa a tsorace ta kalle shi, a lokacin ta lura da shaddar dake jikin sa an masa karamin dinki iya guiwa kansa babu hula ya rage gashin sa sosai.

"Menene haka? Kamar kin ga wani dodo." Ya tambaya cike da mamakin ta

"Ka daina taba ni." Tace kai tsaye tana kokarin tashi daga kujerar yayi saurin fizgo mayafinta yana zaro mata idon sa.

"Me kike nufi? Aure fa zamuyi? Me yasa kike behaving kamar baki san yadda rayuwar ta zama bane, bana fa son kauyanci."

Kallon sa tayi cike da mamakin sa, ta lura akan rayuwar da yake so yake ganin daidai ce nan da nan zaka ga fushin sa, ita kuwa ta gwammace duk abinda zai fad'a ya fad'a fushin sa ba komai bane akan fushin ubangiji. Tana jin sa ya cigba da gaggasa mata magana san ransa, tayi biris kamar ba da ita yake ba, tana da yakinin zafin zuciya ce dashi, kuma bakin sa bashi da control wejan gasa magana. Sai da ya gaji don kansa yayi shiru yana jan tsaki. Ya zaro wayar sa ya hau kira yana cigaba da huci akan kawai ta hanashi taba jikinta.

"Babe where are you?" Yace bayan an daga wayar

"Ok I'm on my way." Ya kashe kiran ya mike yana kallon ta

"Ba zan yi tolerating kina hana min abinda yake nawa ba, ba zan sake dawowa ba idan an kawo ki gidan zaki ga yadda zanyi dake."

Daga haka ya juya yana taku dai-dai yayi ficewar sa, be ko yi sallama da kowa ba ya kama gabansa sai gidan Fido, daga chan ya wuce wajen abokin sa ya karbi wasu kaya sannan ya wuce gida.

Tun ranar da ya tafi bata sake jin duriyar sa ba, Hajiya Mama dai tazo sau daya da maganar yadda bikin zai kasance tunda duk abu daya ne bangaren ta da na Abba, umma dai bata ce komai ba, duk abinda suka tsara suka yanke ita bata da ta cewa dan ko da tace din ma ba lallai suyi amfani dashi ba. Daga haka aka shiga satin bikin.
Ranar laraba aka je akayi kafi, gidan yayi kyau sosai sama da k'asa sai parking space, a jikin gidan Hajiya Maman yake dan katangar su daya, dama tace ko Adam zai yi aure yana tare da ita bata so yayi nisa ko kad'an, balle kuma da zai auri Asma'un sai take ganin ai shikenan ma dama Asma'un ikon ta ce itama. Alhamis aka shiga bikin gadangadan, gidajen biyu ko ina biki ya kankama Hajiya Mama dai saboda yawan mutanen wasu sai dan karamin hotel hotel din dake bayan gidan aka kama musu musamman abokan Adam din da sukayi karatu a turai tare suka zo daga wasu states din.








It's better to marry late than to marry wrong! (Kamar haka dai bature yace, na manta dai.

Don't marry out of desperation dan aure ya wuce duk tunanin me tunani!




_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment