Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*[7/21, 10:52 PM] Mummyn Yara: *RM*
7

****Kayan ta hau tattarewa tana kuka sosai, duk da dama ta san akwai kalubale a gabanta amma bata taba hasashe ko tunanin rashin mutuncin Adam din ya kai haka ba, ranar da aka kawo ta? Ai ko jaka aka kawo masa a wannan ranar dai ya kamata yayi treating dinta da sauki.
Bata san in da zata fara neman iron ba, haka ta dinga dubawa guri guri har lokacin tana kuka, sai da k'yar ta gano shi a dakin da take da yakinin nasa ne don yadda yake dauke da tarkacen kayan sa, zama tayi dirshan tana cigaba da kukan ta hau goge kayan daya bayan daya wanda duk da gugar su ya hargitsa su kawai dan ya wahalar da ita , bakar gajiya da yunwa su suka fi damun ta, batun bacci kuwa babu shi dan ko jin sa batayi. Tana cikin gugar aka dauke wutar, duhu ya mamaye ko ina, tsoro ya kamata ta yunkura da sauri zata tashi, ta manta shaf da iron din sai ji tayi kafarta a jikin iron din,tayi kara da karfi zafin na shigar ta sosai. Jan kafar tayi ta dinga laluben hanya da k'yar ta fad'a dakin, ta hau laluben wayar ta amma bata samu ba, durkushewa tayi a wajen ta dinga kuka tamkar ranta zai fita,da dade sosai a wajen sai da taji kafar ta rage zugi ta sake lalubawa ta samu gadon ta haye ta kwanta cikin jin tausayin kanta da rayuwar da ta samu kanta a ciki.
Bata san karfe nawa ba, bata san adadin dadewar da tayi a kwance ba tana kuka, ta nemi bacci ta rasa amma kuma idon ta kamar zai cire tsabar zafin da yake mata, haske ne ya gauraye dakin, a daidai lokacin ya turo kofar ya shigo. Tsayawa yayi yana kallon ta kwance a kan gadon sa, itama shi take kallo ya sauya kayan jikin sa zuwa gajeren wandon 3quater, da wata rigar daban da ta dazun, tashi tayi zaune ta hau kokarin sakkowa daga gadon, ya rigata ya hawo ya dora mata karfin sa gaba daya, ya danne ta ya hanata motsi, kafarta da ya kama mata ta dinga kokarin nuna masa tana kukan amma ko gezau be ba, kamar ma baya cikin hankalin sa. Kayan jikinta ya hau kokarin raba ta dasu, yana fincike su da karfin gaske! Bata da karfin da zata hana shi, sai dai kuma tana tsoron abinda zai je ya dawo, tana tsoron kar yayi kokarin take dokar Allah, dan taga alamun so yake da gaske sai ya raba da martabar ta,wanda ko da babu period ba zata taba bari ya kusance ta a yanayin da yake ba, bata san matsayar ta ba, taba san wanne irin aure yayi da ita ba.
Gadan-gadan taga yana neman wuce gona da iri, bata san sanda ta samu hannun sa ta go gantsara masa cizo ba, hakan ya saka shi sakin ta da sauri gami da sakin gara, da sauri sauri ta tashi ta fice daga dakin, ta fad'a dayan dakin ta sakawa kofar key, sannan ta zame a wajen ta fashe da kuka. Wannan wacce iriyar masifa ce?
Tsawon daren bata runtsa ba, ya dade yana buga kofar ta kamar zai balla saboda bacin rai, ya gaji dan kansa ya tafi amma ta san dole haduwar su ba zatayi kyau ba, zatayi iyakar kokarin ta wajen ganin ta gujewa haduwa dashi din ko da zata mutu tayi mushe a dakin.
Da k'yar ta tashi lokacin da hasken rana ya hudo dakin sosai,ta shiga toilet ta gyara jikinta ta fito, ta chanja kayan jikinta ta hau gado ta kwanta tana fatan ta samu ta runtsa ko yaya ne.
Cikin baccin taji kamar ana taba kofa, ta tashi zumbur tana kallon kofar a tsorace. Sake bugawa akayi sai dai bugun na hankali ne,

"Waye?" Tace cikin muryar ta da ta dashe saboda kuka

"Nadeeya ce."

Sakkowa tayi ta bud'e kofar tana kallon bayan ta ko tare suke, dan kallon ta tayi ganin yadda ta fige kamar wadda tayi rashin lafiya me tsawo,

"Ina kwana?" Ta gaishe ta ganin yadda take kallon ta.

"Lafiya lou, breakfast ne Mama tace a kawo muku, yarinyar tayi ta sallama shiru shine Mama tace nazo na gani."

"Wallahi bacci ne ya dauke ni."

"Ba damuwa, ki koma ki kwanta ai akwai gajiya,ga breakfast din nan a kitchen."

"Mun gode." Tace ta juya ita kuma ta sauka k'asa tana ayyana ramar da Asma'un tayi a dare daya kachal.

Kasa komawa baccin tayi kuma ta dinga juyi tana jin duk motsin sa tsakanin daki da falon saman, baya minti biyar sai ya amsa waya wanda yawancin mata ne sai tsirarin abokan sa. Bata dai jiyo me yake cewa amma tana jin sautin muryar sa, tayi tunanin zai zo ya buga mata sai kuma taji shiru, daga baya ma sai taji fitar motar sa daga gidan. Da sauri ta sauko, ta bud'e kofar ta sauka k'asa zuwa kitchen din da ta nemo shi da sauri sauri, ta dauraye plate ta zuba abincin da sauri ta sake hayewa saman ta saka key cike da tsoron kar ya dawo. Har ta gama ci bata ji ya dawo ba, ta tabbatar ya yi nisa ko kuma yana gidan Hajiya Maman, wanda tayi tunanin yi dan dazu bata iya wankan ba tana tunanin zai iya balla kofar ya shigo, a gurguje tayi wankan ta shirya ta dan gyara dakin sannan ta fito wajen da ta bar kayan sa na jiya, babu ko daya duk an kwashe sai ta koma ta rufe dakin ta kwanta ta fad'a kogin tunanin da ya zame mata aboki a yanzu.
Karar bud'e gate din gidan taji, ta leka ta window ta hango su Hidaya da Abbati da Rauda sai yaran gidan da jikoki na shigowa bayan me gadin ya bud'e musu, da sauri ta tashi farin ciki na mamaye ta, ta bud'e kofar ta sauka k'asa a dai-dai lokacin sun karaso balcony din, ta bud'e musu gami da rungume Rauda da take a gaba, dariya suka saka dukka Abbati na tsokanar su, suka shiga ciki suka zauna. Zuwan su ya saka ta manta tashin hankalin da take ciki, ta sake sosai suka dinga hira suna bata labari tana jin su, ta kwaso musu kayan abincin dazun suka cinye tas, sannan sukayi mata wanke wanke da dan gyaran gidan. Bayan nan sai ga yan biki daga gidan Hajiya Mama na ta shigowa ganin gidan amarya, hakan ya sakata sake shagala da abinda yake gabanta dan ko tuno shi batayi, sai yamma likis sannan suka tafi, su Ya Hadiza zasu zo gobe su kuma su kawo gara dangin su alkaki da su dublan, banda garar abincin saboda Hajiya Mama tace wa Abba ba sai anyi komai ba, duk daya ne shiyasa tun kafin bikin ma an dankare komai na abinci a gidan babu ce kawai babu.
Bayan tafiyar su sai gidan ya koma kamar yadda yake kafin su zo, saurin kau da komai take na falon ta koma daki chan sama kar yazo ya tarar da ita sai ga aiken Hajiya Mama tana kiran ta, wasu yan mata ne su biyu aka aiko, su tafi da ita, sama ta koma ta chanja kaya ta fesa turare sannan ta sakko suka tafi, bayan ta cire key din da ke jikin kofar ta rik'e a hannun ta.
Gidan na nan kamar ba'a gama bikin ba, dankare da mutane duk sai kunya ta kamata ta dinga sunnewa tana gaishe su har suka dangana da falon Hajiya Maman in da suke dukkan su a zaune, shi ta fara cin karo dashi yana kallon kofa, ya mike kafafun sa a tsakiyar falon suna hira da Maman yana ta dariya tamkar ba shi ba, tsoro taji ganin irin kallon da yayi mata, ta sauke kanta k'asa ta karasa da k'yar tana harharde kafafu kamar zata fadi. Sai da ta zauna sannan ta gaida Maman ta amsa a sake tana nuna mata gefenta.

"Dawo nan Asma'u."

Da jan jiki ta matsa ba dan ta so ba, suka sa Maman a tsakiya shi da ita, ta shiga yi musu nasiha cikin sigar lallashi, wanda gaba daya a kaikaice da Asma'un take, duk nasihar akan yadda zata kula da adam din ne, da dukkan al'amuran sa, tana jin ta har ta gama sannan tace ta taso su je daki akwai sirrin da zasuyi, su Nadeeya suka fashe da dariya suna tsokanar Maman ta ja hannun Asma'un suka shiga ciki,suna shiga ta kalle ta tace

"Alfarma nake nema asma'u, ga yayanki nan Adam, dan Allah asma'u ki taimaka min, Adam ya dawo cikin nutsuwar sa, kiyi kokari wajen jawo Adam jikin ki, dan Allah ki yi kokari wajen ganin ya bar dukkan abubuwan da suke mara kyau, Adam yana son ki zaki iya amfani da soyayyar da yake miki ki dawo dashi kan gaskiya, babu me iya yi min wannan alfarmar sai ki, kiyi hakuri ki danne duk abinda zai biyo baya, a karshe zamu ci riba, kinji? Dan Allah.

A duk maganganun Mama babu daya da ya tsaya mata a rai wanda dama bata sani ba face wai Adam yana son ta, wai Adam yana son ta. Ta tabbata a kaf duniyar nan babu wacca Adam ya tsana sama da ita, da za'a bashi bindiga ace ya harbe mutum daya ta tabbata ita ce, haka take itama a wajenta, tana jin tsanar sa sosai a zuciyar ta, tsanar da bata taba yiwa wani mahaluki ba, bata son ganin ko da fuskar sa ce, dan ta gama tabbatar da rashin imanin sa, bashi da kirki lamba daya, ta yaya ake tunanin zata iya gyara shi, bayan shi a ganin sa babu wani abu da yake mara kyau? Bayan ba dauke ta a matsayin mutum me daraja ba? Tana ji Maman ta cigaba da magiya, ta amsa mata da kai dan bata san kuma me zata ce mata ba, ba zata taba fahimtar ta ba, tunda ta riga ta saka son kai a cikin al'amarin auren masu, wanda ta tabbata tayi hakan ne saboda personal interest dinta, ba wai dan alakar ta da abban su ba, ba kuma wai dan soyayyar da take ikirarin Adam din nayi mata ba.
Fitowa sukayi in da suka bar su, ta koma kusa da su Nadeeya ta rabe tana jin hirar da suke, kiran sallar magriba ya tashe su daga wajen, ta bi bayan su Nadeeya zuwa daki, sukayi sallah tana zaune a gefen gado suka idar, sai suka cigaba da zama a dakin suna hirar karatu. Mama ce ta aiko ta zo, ta fito ta ganshi a tsaye ya jingina da bangon falon.

"Bishi kuje asma'u, zaa aiko muku da abinci wai Ashe tun da ya fita be koma gidan ba."

Murmushin yake tayi, gabanta ya hau dukan uku uku, yayi mata alamar su je yana nuna mata hanya, ta shiga gaban sa ya take mata baya yana murmushin mugunta.



_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

VVIP SUITES : 3500 (PC/TA PRIVATE KAI DAYA)

VIP SUITES : 3K (VIA GROUP) A VIP GROUP ZAA DINGA TURAWA.

TWO PAGES DAILY
INSHA ALLAH!! MORNING/NIGHT. SAFE DA DARE.

*_TEAM ZAFAFABIYAR_*
[7/21, 10:52 PM] Mummyn Yara: *RM*
6


*_ZAFAFA 5 NA MIKA GAISUWAR TA'AZIYYA ZUWA GA MARUBUCIYA UMMY AISHA, TA KUNGIYAR HASKE WRITERS ASSOCIATION, BISA GA RASHI NA MAHAIFIYAR TA DA TAYI. MUNA FATAN ALLAH YA JIKANTA DA RAHAMA, YA GAFARTA MATA, YA KUMA BASU HAKURIN WANNAN BABBAN RASHI AMIN._*
__________________________________

_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_
_SAKINA VENDIBLES_

_(INDE HARKAR TURARUKA NE MASU KAMA JIKI DA GIDAH KAI HARDA TSUGUNNO. SAKINA VENDIBLES ITACE KAN GABA)_

_SUNA DA KAYA INGANTATTU MASU MATUKAR KYAU AKAN FARASHI MAI RAHUSA.)_

_KINASON ASAN KIN ISA MACE? WADDA ZAKUYI GOGAYYA DA MASU SAKA DESIGNER TURARE AMMA KI FUSU KAMSHI? DUK INDA KIKA GIFTA ASAN EH. KEDIN TABANCE , KIN ZARCE SAURAN MATA)_

_AKWAI KHUMRAH WHITE AND BLACK_

_KULACCAM BLACK (FOR HAIR( AND WHITE FOR BODY_

_WASU DAGA CIKIN KAYAYYAKIN MU SUN KUNSHIπŸ‘‡_

Turaren wuta list*
Queens special
Kajiji mix
Kajiji whole
Gabgab
Brown Hawiii
Special Halut
Sandal balls
Sandal strips
Sandal flakes
Dubai oud
White Hawii
Classy Dufr
Black bange
Black bange
Musky Dorrot(Na tsuguno)
Cous cous

*_DA SAURAN SU DA YAWA_*

*_Handles_*
*Instagram* @sakina_vendibles *Facebook*
@Sakina vendible *Tiktok*
@Sakina vendibles_


****Zuwan angwayen ya saka aka shiga gabatar da bikin gadan-gadan. Babu abinda take ji sai faduwar gaba a duk sanda ta tuna abinda yake tunkaro ta, suna nan zaune aka fara kiran amarya da ango su fito fili. Murmushi ya sakar mata ya miko mata hannu, ta kalle shi a tsorace, ya sake sakar mata murmushin sannan ya kama hannun nata ya mikar da ita, suka shiga takawa zuwa filin tamkar tsofaffin masoyan da suka jima da kaunar junan su.
Sun jima a filin shi da abokan sa na ta tikar rawa, taji jiri kamar zai debe ta, ta daure kanta na k'asa amma tayi matukar gajiya, yana ankare da ita yana sane kuma suka cigaaba da abinda suke, sai da ta gama gajiya likis sannan suka koma suka zauna, ta kalle bangaren da su Hidaya suke, suka hada ido ta marairace fuska, tasowa suka da Rauda suka zo wajen ta, suka zauna a side dinta sai taji kamar an yaye mata dukkan damuwar ta, hira suke mata k'asa k'asa, hakan ya sakata warewa har tana murmushi, nan fa su ya Hadiza ma suka taso suka hawo wajen, daukar hoto. Tasowar yan gidan su ya sakata mantawa da shi da existence din sa a wajen, ta sake sosai har sai da mc yace ya isa haka su koma sannan suka koma amma ban da Rauda da ta rikewa hannu kam ta hanata tashi, sai kawai ta cigaba da zama a gefenta da yake akwai spare kujera a wajen.
An dau lokaci sosai har su Ya Hadiza suka fara deciding kawai su tafi, basa son barin ta ita kadai amma dare yana yi musu sosai hakan kuma ba sabon su bane, bayan haka dukkan su da mazajen su, gashi duk ba gidan umma zasu koma ba sai gobe zasu koma. Waya Hidaya ta kira Rauda daga wajen zaman su, ta daga amma bata jin ta, sai ta mata text tace zasu tafi, suna kallo ta radawa Asma'un, nan da nan idon ta ya ciko da kwalla zatayi kuka,

"Dan Allah karku tafi." Ta rada mata tana sake riketa

"Dare yayi sosai, zamu dawo amma in sha Allah da wuri."

Sakin hannun tayi ta sunkuyar da kanta, tana jin tana mata sallama ta daga mata kai kawai.
Bayan tafiyar su sai da aka kara almost an hour sannan aka tashi, wajen karfe daya na dare, Nadeeya ce ta rik'e ta suka fito harabar wajen bikin, ya karaso wajen su yace

"Kuje kawai zan zo."

"Ok, gidan Mama ko gidan ka?" Ta tanbaye shi ta sigar zolaya. Shafa kansa yayi yana kallon Asma'un da take kallon gefe yace

"Gidanta mana, me zakuyi wa Mama a tsohon daren nan, kawai sun hadu da safe."

Dariya Nadeeya ta saka, ta budewa Asma'un mota ta shiga, ya rankwafo kanta yace

"Get ready for me." Yayi mata shu'umin murmushi sannan ya juya zuwa wajen da friends dinsa ke tsaye suna jiran sa, da kallo ta bi bayan sa, tana kisisiisma iya abinda yake tanadawa a ransa,tasan babu batun sassauci a tattare dashi, ita kuma tayi alkawarin rik'e mutuncin ta har sai ta tabbatar da wanne irin aure akayi mata.
Tafiya motar ta soma yi, tana cigaba da hangen sa tsaye suna ta magana da shewa, baka jiyo me suke cewa amma tabbas ko ma menene suna cikin nishadin sa, sanda motar ta fita daga harabar event centre din a lokacin ta lunshe idon ta, wasu zafafan hawaye masu dumi suka zubo mata, sai kawai ta kwantar da kanta ta rufe idon ruf tana jin duk hirar da suke a tsakanin su, wanda duk maganar yadda dinner ta kasance musu ne.
Tafiyar da sukayi ba me yawa bace kasancewar dare ne babu cinkoson ababen hawa, tana jin motar ta tsaya tayi saurin bud'e idon ta, ta kalli gidan da yake amsa sunan gidan ta, gidan da zata zauna a ciki tayi rayuwa wadda bata san iya adadin ta ba,watakila ma sai dai a fidda gawar ta, ji tayi kamar an sake bubbuge mata kafafunta, taji kamar ta juya ta shiga gari watakila ta samu wadanda zasu fuskanci halin da take ciki, sai dai bata duk wannan damar, tana jin kuma saboda kasantuwar ta mace ce, watakila da itan namiji ce da hakan ba zata taba faruwa ba.
Bin su ta dinga yi tamkar rakumi da akala har zuwa tsakiyar falon gidan, wanda yake fidda shihirtaccen kamshi, amma halin da take ciki ya hanata fahimtar haka, hasalima baki take ganin gidan, basu tsaya da ita ba sai da suka dangana da bedroom din ta, suka zaunar da ita a gefen gadon sannan suka zauna suma suna dan bata baki, hakan ya sakata sakin kuka wanda a da tayi alkawarin ba zatayi ba, sai a sannan ta karyata duk dauriyar ta, domin ba karamin abu bane rabuwa da iyaye ko da kuwa auren soyayya ne balle ita nata da bata ma san a wanne bigire zata ajiye shi ba. Tana jin su suka cigaba da bata baki, suna kokarin ganin ta kwantar da hankalin ta, bata daina kukan ba amma tayi k'asa da muryar ta har suka yi zaton ta riga ta daina, sukayi mata sallama suka tafi. Daga nan gidan yayi tsit babu motsin komai, tsoro ne ya soma shigar ta, ta duba wayar ta taga daya da rabi ta wuce, da sauri ta zame a wajen dan dama bata sallah, ta kudundune jikinta waje daya. Bayan kamar minti talatin da tafiyar su, taji motsi kad'an kad'an alamun tafiya, sai kuma magana da ta kasa tantance ta waye sai da aka matso kusa sannan ta fuskanci shine yake waya, diri-diri tayi ta rasa me zatayi kuma, ta kalli kanta sai kuma ta kalli kofar, ta tashi da azama zata rufe sai dai kafin ta kai ga rufewar ya danno ya shigo, yana sakale da wayar a kunnensa cikin shigar boxer da wata riga armless, saurin ja da baya tayi ya kalle ta yayi murmushi yace

"Baby kina da matsala, na fad'a miki I'm all yours, babu ruwan aurena da alakar mu, you can see me whenever you want,kamar dai ko yaushe."

Dariya yayi yana sake makale wayar, ya shiga ciki sosai ya zauna akan bedside yana cigaba da wayar, komawa tayi ta zauna a gefe a k'asa, har ya gama sannan taji ya taso ya nufo ta, kafin ya karaso ta mike da sauri, ya tsaya a gabanta yana kallon ta.

"Wannan kayan baki chanja su ba, nifa bana son kazanta fa." Ya fad'a a wulakance ya kai hannu gefen wuyanta ya shafo ya kalli hannun

"Duk kin yi gumi baki san miji zai zo wajenki ki dan watsa ruwa ki saka sexy night wears ba, bansan duhun kai fa."

Shiru tayi masa shi kansa dama ya san shirun zata masa, kuma dama ya san a hakan zai tarar da ita dan abokin sa yace haka matan hausawa suke, wai kunya sai a kawo amarya da wasu kaya masu uban nauyi ta yi ta wani nuku-nuku a ciki, shi sam baya son ire-iren wadannan al'adun malam bahaushen wanda suke cike da kauyanci da gidadanci.
Cigaba da bin ta da kallo yayi, zai sake magana aka kuma kiran sa, ya kalli wayar kamar zai daga sai kawai ya fasa ya kashe ta gaba daya ya cillar da ita a saman gadon, sannan ya fizgota zuwa jikinsa ya matse ta.

"Me kika zo dashi?" Ya rada mata a kunne yana zame dankwalin kanta.

"Ina fatan dai sun shirya ki sosai da sosai, bana son matsala ko kad'an, kin gane me nake nufi."

Bata gane abinda yake nufi ba dan duk a kidime take, yana ta jujjuya hannun sa a jikinta ya na zagaye da ita, har ya kai bakin gadon, ya hankada ta baya sannan ya bita yayi mata rumfa, da sauri tace

"Bana sallah."

Kamar be ji ba, sai kuma ya tsaya chak yana kallon ta, kallon neman karin bayani, da girgiza masa kai alamar eh da gaske take, wani irin mikewa yayi da sauri yana ja baya, kamar yaga abun kyankyami, ya fice daga dakin, mikewa tayi ta dauki mayafin ta, ta yafa a tsorace kamar wadda tayi gudu saboda yadda ta rude.
Be jima da fita ba sai gashi ya dawo, rik'e da wasu kaya masu yawa, ya watsa mata a fuskar sa sannan yace

"Ki goge min kayan nan tas kafin naje na dawo, tunda baki da amfani kika kuma karya min lissafi baki isa ki kwana haka ba wallahi."

Kaya ne masu yawa nasa jeans jeans da tshirts, su yake so ta goge da wannan uban daren,

"Ba zakiyi ba?" Yace yana zare mata ido, bata amsa ba. Ya matso sai jin saukar mari tayi da ya kusan sakata sakin fitsari a wajen.

"Wayyo Allah na!" Tace a karon farko tun shigowar ta gidan,sake matsowa ta ga yayi, da sauri ta hau kwasar kayan tana kuka

"Stupid, tunda baki da amfani sai dai kiyi min aiki."

Ya juya yana tsaki, ya shiga dialing number Fido dan ba zai iya asarar daren ba!





_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO)

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment