Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

tana kwance tana fitar da numfashi daidai na azaba, wayar sa ya daga da Nadeeya ta kirashi, ya juya ya bar dakin yana amsa wayar da kwantancen dakin da suke, kusan a tare suka iso da Hajiya mama dan ita Nadeeya din daga nesa take, dukkan su a rude suke, suka isa dakin Nadeeya ta riga mama isa gaban Asma'un tana kallon hannun ta

"Karaya?" Tace cike da tashin hankali

"Innalillah wa inna ilaihi rajiun!" Hajiya mama ta fad'a tana kallon Adam din cikin son karin bayani

"Faduwa tayi wallahi mah, a wajen sauka daga stairs bansan dame ta zame ba, wallahi ban sani ba."

Wani kallo Nadeeya ta masa, ta kalli Maman ta fita zuwa wajen Drs din.

"Garin yaya haka ta faru Adam? Garin yaya?"

Girgiza mata kai yayi, yana jin wani iri, abun da be taba ji ba.

"Fad'a kukayi? Ko dama chan har yanzu akwai matsala ne?"

Girgiza kai ya sake yi, ta matsa ta taba jikin Asma'un da ya rure da zazzabi me zafin gaske

"Me zance wa mahaifanta? Waye kake ganin zai yarda da cewa faduwa tayi? Bayan kowa ya san yadda akayi auren nan, sannan kowa ya san halin ka."

Bashi da bakin magana, domin shi kansa be san bakin da zai yi amfani dashi wajen kare kansa ba, adah idan aka ce zai russuna haka har yaji tausayi irin haka zai karyata, amma kuma ya rasa dalili, sosai yake jin tausayin ta musamman ganin irin bakar wahalar da tasha a yanzun, karaya ba abu bane me sauki musamman a wajen wanda ya soma girma ba kamar yara kanana ba, ya taba samun dislocation sanda yana tashen ball ya san wahalar da yasha a lokacin ballanta na ita, yana jin Maman tana ta maganganu be ce komai ba, be kuma bar dakin ba, har zuwa sanda Nadeeya ta dawo da ya lura tana fushi dahsi sosai, har zuwa lokacin da Maman ta kira Abba a waya ta sanar masa.
A tunanin sa zasu zo a take a lokacin, amma babu wanda yazo, da Hajiya Maman ta sake kiran Abban sai yace mata babu komai su ma sun isa zasu shigo da safe, hakan ya sake karyar wa da Hajiyan guiwa, taji da gaske bata kyauta ba, bata yiwa Asma'un adalci ba kuma ba ta yiwa mahaifin yarinyar hallaci ba, ya dauke ta ne tamkar uwa mahaifiya ya kuma amince mata yana bata dukkan girman ta, son kai ya kwashe ta da aikata abinda ba zata taba yafewa kanta ba.
Kwanan zaune sukayi saboda yadda hannun ya matsa mata, sun tausaya mata dukkan su, har shi uban gayyar da ya zama so silent kamar bashi ba, sai gabannin asubah sannan ta samu wahalallen bacci ya dauke ta.
Toilet mama ta shiga tayi alwala Nadeeya ta tsaida shi ganin zai fita, ta tsare shi da ido cikin tuhumar sa tace

"Me kayi mata?"

"Naam?"

"Tsorata kawai tayi ba, shine ta fito da gudu ta fadi, wallahi ban mata komai ba."

Ranta ne ya sake baci sosai, ta nuna masa kofa jin Maman zata fito, ya fice da sauri yana sake rejecting kiran Fido da take ta jera masa shi tun daren.

***Abbati ne yazo tare da Abba wajen takwas lokacin Adam din ya bar asibitin yaje dauko mata kaya, nan fa Hajiya Mama ta saka wa Abban kuka, ya dinga bata baki yaki yarda ya nuna damuwar su ko wani abu, ya kuma sake jaddada mata hakan kaddarar Asma'un ce, babu wani da ya isa ya hanata faruwa. Be jima ba yayi mata addu'a ya tafi, ya bar Abbati saboda ko za'a nemi wani abin tun da Adam din baya kusa.

***Waya umma suke da Ya Hadiza ta fad'a mata abinda ya faru, kuma Abba yace ta kyale Hajiya Maman suyi jinyar kar ma tace zata je ta zauna, hakan ba karamin bata mata rai yayi ba, a kalla dai a barka ka zauna da danka dan yafi bukatar ka akan kowa, hakuri Ya Hadizan ta bata tace gatanan zuwa gidan zata kuma kira Abban a waya, ajiye wayar sukayi umma ta cigaba da shirin tafiya asibitin dan ma yace ta jira Abbati ya dawo ya kaita da tuni ta tsufa a chan dan ba zata iya jurewa ba, dama ta san za'a rina ai tunda aka hada Asma'un da mahaukacin miji.
Har Yaya Hadizan tazo Abbatin be dawo ba, sai kawai umman ta fito suka tafi, a hanya take fad'a mata yadda sukayi da Abban, yana nan akan bakansa be yarda Umman taje ta zauna ba, ya dai amince taje kullum amma ba wai da zuwan zaman jinya ba, ran Umman ya sake sosowa ainun, bata taba yi wa Abban bore ba, tun auren su take masa biyayya daidai gwargado, ba zata bijire masa ba a yanzu musamman da girma yazo, amma bata ji dadi ba, kuma shima ya san be kyauta mata ba.

"Allah Umma kina da hakuri sosai, anya akwai wadda tayi hakurin ki kuwa a cikin mu?"

Murmushin umman tayi, sak Asma'un itace, baki daya halayen ta irin na Umman ne shiyasa take tausaya mata, bata da zafi ko kad'an hakan ya saka tun da ma kowa taka ta yake, ballantana kuma ta hadu da miji irin Adam. Har suka isa asibitin ran Umman be saki ba, ta daure dai kawai suka shiga ciki. Adaidai lokacin Asma'un ta farka, zafin ciwon ne ya farkar da ita, babu wanda be tausaya mata ba, dan ma tana da masifar dauriya, gefe umma ta koma ta dinga share hawaye, zata sake lallaba Abba ita dai ya barta tayi jinyar yar ta, ko ta koma gidan ba zata taba samun nutsuwa ba, ba wai kuma dan tana ganin ba za'a yi Asma'un abinda ya dace ba, sai dan kawai dai wani abun dole sai uwa mahaifi.
Ganin su umman ya sakata sake jin ciwon na dawo mata sabo, tun bayan auren bata ga umma ba, dama jiyan take so ta tambaye shi taje ta wuni dan tayi kewar gida sosai, sai ga tsautsayin da ta gamu dashi.
Allura akayi mata da zata rage mata zafin ciwon, hakan ya saka ta dan samun nutsuwa. Kin motsawa nan da chan Hajiya Mama tayi dan tana tsoron ta bar su Asma'un ta fad'a musu abinda ya faru duk Adam din ya rantse mata be mata komai ba amma bata yarda ba, tana kyautata zaton yana da alaka me karfi da abinda ya farun.
Har yamma likis su umma na asibitin duk su Hidaya sun zo da yan uwan umman, Adam ma ya dawo amma be sake shigowa dakin ba tsakanin sa dai wajen zuwa wajen Drs sai idan abu ya taso haka suje da Abbati. Su kansu su Ya Hadiza sai da sukayi mamakin sa, sun ga sauyawar sa sosai har suka yi tunanin ko dama ya chanja bayan auren dan aure na chanja mutane da dama.
Bayan sun yi sallar magriba sun dawo da yaga an ragu sosai a dakin sai ya shigo, da sauri Asma'u ta rufe idon ta Hajiya mama ma ankare da ita, a dan baya ya tsaya ya gaida umman da rabon su dashi tun bikin, ta tambaye shi me jiki ya amsa kansa a k'asa tamkar ma kirki.

"Ya jikin?" Yace yana kallon gadon da take kwance, bata amsa ba ta sake rufe idon ta sosai, umma dake zaune daga gefe ta dan leko ta

"Inaga ta samu bacci."

Juyawa yayi ya fice duk suka bishi da kallo hatta Maman na cike da mamakin Adam din, kamar wanda aka chanjo mata shi da wani daban, shiyasa ta sake tabbatar da sanin sa, fatan ta daya Allah yasa ba turo yar mutane yayi daga benen ba ma, dan babu wanda ya san ainihin me ya faru ya dai ce zamewa tayi ta fadi.
Tana jin ya fita ta saki kuka me cin rai, bata son sa bata kaunar sa ko kad'an, bashi da tausayi bare imani ko na digo, kanta sukayi dukka kowa na tambayar ta menene, bata ce komai ba, ta dinga kukan ta a hankali wanda kusan duk sun dauki hasken dalilin kukan nata, yana da nasaba da shigowar Adam did, kunya duk ta kama Hajiya Mama, ta dinga borin kunya tana so ta dauke hankalin su daga kan Asma'un amma kuma sun riga sun gane komai.
Sanda su umma suka zo tafiya tayi bacci, dan haka bata san sun tafi ba sai chan wajejen sha biyu na dare da ta farka ta ganshi zaune akan kujera yana danna waya, kansa a kasa yana ta murmushi, wurga idon ta tayi zuwa sauran sassan dakin, babu kowa sai shi kadai ya bada dukkan attention dinsa akan wayar.

"Zan sha ruwa." Ta furta tana kallon gefe, dagowa yayi ya kalle ta, ya dauke kansa ya cigaba da danna wayar sa, ta sake maimaitawa a karo na biyu nan ma yayi biris.
Jujjuya hannun ta, ta dinga yi mara ciwon cikin jin ishirwa sosai, ta yi kokarin daukar na ajiye akan bedside drawer din asibitin amma ta kasa, yayi kamar be san me yake faruwa ba, sai da ya gama abinda yake tas, sannan ya tashi ya dauki ruwan ya mika mata. Kautar da kanta tayi alamun bata so, ya dire mata a wajen ya fice gami da jawo mata dakin!



_ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!! ZAFAFA BIYAR!!_

_ASSALAMU ALAIKUN MASOYA MAKARANTA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR_

_BARKAN MU DA SALLAH, ALLAH YA MAIMAITA MANA, AAMIN_

_KU MATSO KUSA, ZAFAFAN NAKU SUN SAKE ZABUROWA DA ZAFIN SU KAMAR YADDA KUKE KAUNAR SU._

_WANNAN KARON MA SUNZO DA WANI SALO MAI NUTSUWA HADI DA ZAFAFAN DARUSSA NA RAYUWA KANA DA FADAKARWA AKAN RAYUWAR YAU.. BANGAREN KOGIN KAUNA KUWA BAA MAGANA. DOMIN WANNAN KARON SUN SAKE TAHOWA DA ZAFAFAN KAUNANNAKI MASU NARKE ZUCIYOYI._ WANDA ZASU ZO MUKU IN SHA ALLAH

_KADA KU MANTA ZAFAFAN NAKU DE SUNE KAMAR HAKA_

_SAFIYYAH HUGUMA: TAZO DA NATA SALON MAI SUNA: *KUFAR WUTA*_πŸ₯°

_BILLYN ABDULL TA ZABURO DA WANI TAKEN MAI SUNA: *BAQAR INUWA.*_😍

_MAMUH GEE ITAMA WANNAN KARON TA SAKE TAHOWA DA: *NOORUL-ALB*_πŸ₯°

_HAFSAT RANO WANNAN KARON TAZO DA NATA RUBUTUN MAI SUNA: *RAYUWAR MACE*_❣️

_NANA HAFSATU (MSS XOXO) WANNAN SALON MA TAZO DA : *MASARAUTA*_😍

***_DUKA LITTAFAI BIYAR ZASU ZO MUKU NE AKAN FARASHIN YADDA SUKE KAMAR KODA YAUSHE_*

_BIYAR : DUBU DAYA (1k)_
_HUDU: 700_
_UKU: 500_
_BIYU: 400_
_DAYA: 300_

_AKWAI TSARIN VVIP SUITES GA MASU SON HAKAN. FARASHIN SU DABAN, DOMIN KARIN BAYANI SE A TUNTUBE MU TA: _

*_ZAKU BIYA KUDINKU ANANπŸ‘‡πŸ‘‡_*

Bilkisu Ibrahim Musa
1487616276
Access bank

Number shaidar biyaπŸ‘‡πŸΌ

*_09032345899_*

*KATIN MTN*πŸ‘‡πŸ‘‡

09166221261

______________________

ZAFAFA BIYAR

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4Chapter 5
Chapter 6

Please Login or Register in order to submit comment