Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

ZUCIYA DA KWANJI 2
.1)Abdullahi ya mike ya fara ja da baya ba tare
da fuskarsa ta bayyana tsoro ko shakka ba, sai
da ya dangane da bango sannan ya daga mata
hannu alamar sallamawa, yana kuma dariya ya
ce. "Wai dukana zaki yi ne? Kawai sai ta ci
kwalarsa cikin yanayi na fita hayyacin ta,fara
magana da sarkewar murya. "Ai wallahi ba ka
isa
ba... Na rantse ka yi kadan ka tozarta
rayuwata.... In aure ka in ci me da kai....? Ni ba
na sonka.... Na rantse yau sai ka sallame ni na
bar gidan nan, in ba haka ba sai dai mu kashe
juna ni da kai". Sun fi minti biyar a haka tana
sakin maganar da ranta ya raya mata tana
kuka,
sannan tana faman jijjiga shi har da duka. Ya
tsaya kawai ya zuba mata ido,tun yana dariya
har dariyar ta gagara..... Sai da ya. Tabbatar ba
ta da niyyar ta hakura ,sannan ya yi
maganinta.
Ya riko gashinta da karfi,wanda. Ya karya.
Lagonta ta fara kara,ya dago kanta tana
surutai
na cin fuska gare shi,kawai sai ya rufe bakinta
da
nasa. Ya kuma nuna mata shi jarumi namiji
ne,inda ya saki gashinta ya matse ta sosai cikin
gwaninta ya fara juya harshenta da nasa Ya
rufe
bakin masifa duk kokarinta ta kasa kwatar
kanta
ita da kanta sai da ta ji a ranta akwai inda
mazan suke. Numfashinsu ya sarke da na
juna,ya
daga aikawa kwakwalwarsu wani sako mai wuyar
fasara. Ya dai yi nasarar motsa duk wata
halittar
soyayyarta da ke zuciyarsa,ya gadar masa da
doki da fatan kasancewar su tare matsawar
numfashi.shaukin da ke shake numfashinsa bai
taba jin rabinsa daga wata ba....... Akwai
bambanci tsakaninta da shi,ita halin da ta sami
kanta bai wuce kwakwarewar komai a
kwakwalwarta ba. Ma'ana ya sauke farashin
masifarta da cushe mata zuciya kuma ya
sassauta mata zafinsa da kiyayyarsa da ta ke ji
a
makogwaronta,sai ya sanya mata raunin jiki da
na zuciya,yayin da kwakwalwarta ta dauki wani
aikin daban. Sai da Abdullahi ya fahimci hakan
sannan ya kyaleta,ya rungume ta tsan tsan a
jikinta,ta saki runane kukanta mai tsuma
rai,sai
ra bar shi da hawayen zafin kauna. Ya dago
kanta da rikitacciyar murya ya kira.
Sunanta,ya
fara girgiza mata kai... Bai jira ta ce wani abu
na
ya fara dauke hawayenta da halshensa,sai ya
....
Ashe bakinta,ya ja ta kujera ya zaunar sannan
ya
zauna gabanta a kasa da nasa kwallar ya fara
magana a tausashe. "Fatima kar ki wahalar da
numfashinmu,ba zamu iya rabuwa ba. Ban aure
ki don na saki ba tun kafin na dora idona a
kanki.... Ya ya kike tsammanin zan iya sakinki
bayan na ganki soyayyarki ta shige ni da zafi?
Ban taba dandanar so mai zakin naki ba fatima
ban taba jin a raina zan iya mutuwa a kan
mace
ba,sao akanki. Na kuma ji a raina ni ne zan da
ce
da mijinki ni dai ana aure domin bauta.....
Aurenmu ne zai samar da riba biyu, wato rayuwa
mai dadi, wadda kuma zata samar da lada,ki ba
ni dama mu gwada wannan sa'ar fatima,sai kin
sami kanki a aljannar da ta zarce ta gidan
Alh,don ba kudin ne kawai jin dadin rayuwa
ba,sannan ki sami Allah kin mai biyayya ga
umarnisa,amma me kika tanadar tsayawa
gaban
Allah idan kin yi zaman haramci da Alh?
Like · React · Report · May 15, 2015
Xaeenab Umar Yaqub
tnx
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
2) Da tana ta shesshekar kuka,sai a wannan
gabar ta tare shi. "Ina ruwanka? Ko kana da
kaso
a cikin hisabina? Idan haka ne ka fada min?"
Ya
kara zagewa da rarrashi. "Wannan hisabin mu
uku,ya shafa,da. Alama kuma zan fi kowa
tabewa
tunda ban mori komai ba a duniyar..... Koda
yake
ku ma din ba zaku mora ba, shaidan ne kawai
yake rudinku,ko ba ki tuna yadda kike kin Alh a
da? Sai bayan ya sake ki shaidan ya kawata miki
shi, shi ma shaidan ya kara haska masa ke har
kuka sami damar ture komai kuka halatta
haram.
Hawaye ya bushe a idonta ta fara magana a
sanyaye,sai dai klaman nata da zafi. "Ko ina
son
Alh,ko bana sonsa binciko wannan ba zai amfane
ka da komai ba, don kai dai bana sonka,kuma ba
zan taba iya zama da kai da kai ba.... Kuma
dole
ne ka sake ni idan ba haka ba sai dai cikinmu
wani ya bar wa wani duniyar. "Ko a jikinsa,ya
ce
mata. "Ai na shirya,ina fatan ke ma haka....
Na yi
mutuwar so ke ki yi taki,zan yi farin ciki idan za
mu bar duniyar tare sai mu tashi da juna".
"Allah
ya kiyaye". Ta fada da karaji. Ya tashi da sauri
tare da dora yatsa a lebe,sannan ya fara yi
mata
inkiya da window da kofa alamar kar makota su
jiyo ta ya ce. "Na riga ki a wajen Allah, ga shi
kuma alhairin na je masa da shi ba sharri ba,
fatima kar ki batawa kanki lokaci na fada miki
ban aure ki don na saki ba..." Sai ta yi zuru
tana
kallonsa lokacin da zuciyarta ta kai matukar
kuntata. Ya rabu da ita ya sa kai ya shige dakin
baccinta ya yi kwanciyarsa. Ta yi kukan,ta yi
rurin har ta hakurkuratar da kanta ta nufi
bandaki
ta dinga wankin bakinta, sannan ta zo ta dau
hijabinta ta nufi kofa.yana jinta. Ta bude
kofar
dakin ta fita tana faman kukan,ya yi dif yana
sauraronta don yasan babu inda zata iya
zuwa.illa kuwa sai gata a guje ta dawo ta shigo
falon ta rufe. Ya koma ya kwanta yana dariya.
Ta
fice karfe biyu da rabi a falo tana kuka,ta rasa
ta
inda zata fara wannan rayuwar bakin cikin da
kuma tunanin makomar lafiyar Alh da ya
kwallafa
ransa a kanta,to ga jarrabar da Allah ya aiko
musu. Babu dabara ta kwashi kafa ta tafi gidan
su wanda tafiyar ce zata to asirin abin da suka
binne idan Abdullahi ya bara.gara ma ta zauna
su
gurji juna duk wanda ya ji jiki sai ya sallama.
Sai
da karfe uku ta gota ya daina jin shesshekar
kukunta.da ya lallaba ya leko sai ya ganta kife
kan kujera bacci ya kwashe ta. Ya fito da bargo
a
hannunsa neman yadda zai gyara mata
kwanciyar ya zama jidali,dole sai bargon ya
rufe
mata ya wuce bandaki ya dauro alwala ya zo ya
gurfana gaban mai share hawaye. Sai hudu da
rabi ya dan kwanta ya runtsabaccin rabin
awa,sannan ya farka domin sallatar sallar
asuba.
Bayan ya dauro alwala ya zo ya bude fuskarta
yana yarfa mata ruwan hannunsa. Frigigit ta
bude
idanunta da suka yi jawur,ya ce mata. "To
sarkin
kuka tashi ki yi sallah,in yaso sai ki kai wa
ubangiji kara ta,ki dinga addu'a sai ki ga Allah
ya
warware miki duk wani kulli da ke cikin
zuciyarki,yanzu ina amfanin da kukan da kika
kwana kina yi jiya,ya samar miki? Da kin yi
dabara sai ki yi alwalarki ki kai wa ubangiji kara
ta.idan babu khairi a tare da ni ya canja miki
ni".
Ta yunkura ta tashi tana janye jiki.ya bita da
kallo da yanayi na nuna kulawa. "Me yasa ba ki
shiga wancan dakin kin kwanta ba, idan ba za ki
hada daki da ni ba? Sai ki takura kanki a nan
fatima?". Ta gyara zama tana zabga masa
harara,ta ce. "Ai ni na gama jin dadin
rayuwa,in
dai da kai zan yi ta. Ya yi murmushi,tukunna
tawa tare, tunda ni ba ni da rayuwa mai dadin
da
babu ke, sai kuma ka yi sa'a muka yi haduwar da
babu rabuwa". Cikin girgiza kan girmmar bacin
rai,ta ce "Allah ba zai cikawa maci amana irinka
burin ba Abdullahi...."
Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji 2
3) Ya tare ta yana kallon kwayar idonta. "Da
na ci amanar wa? Ke ba ki san an ce mafi
sharrin
mutane shi ne wanda yake salwantar da
addininsa domin duniyar waninsa ba? Matsayin
na ke nan idan kuka yi tsani da ni kuka kulla
zaman haram...... Kuma da kike maganar Allah
ba zai cika min buri ba, ai ni Allah ya cika min
buri a kanki fatima,ya aura min soyayyarki
wanda
ina cike da fatan hakan. Tunda har Alh da kika
aura bisa kaddara kika yi zaman dole da shi ya
sami gurbin son da kike jin zaki iya zaman
haram
da shi,balle ni da kika zaba a matsayin
jaruminki
fatima.... Karkari ki yi boren ba ni da kudi, to ni
zan tabbatar miki kudi ba su kadai ne nasarar a
rayuwa ba". Ta yi kasake kawai tana kallonsa,
ya
ya aka yi ne yasa tsakaninta da Alh haka?
"Tashi
ki yi sallah" Ya fada lokacin da ya daidaita kan
sallayar,sannan ya tayar da kabbarar
raka'atainil
fijir.bayan ya idar ya sa kai ya fice masallaci.
Cikin sanyin jiki ta tashi wasu abubuwa na yawo
a ranta.dole ta yi taka tsan tsan da Abdullahi
tunda ya san abubuwa da dama a kanta. Ta
dauki shawararsa wajen kai kukanta wajeb mai
duka sannan ta takure akan sallayar har ya
dawo
masallaci ya same ta. Kai tsaye wardrobe ya
wuce ya bude yana nazarin ciki,sannan ya fara
yo
waje da kayan wankin kayan da ta shafe
kwanakin ta a gidan tana sanyawa ba tare da ta
nemi mai wanki ba. Ya ware wadanda suka
kamata akai wanki ya kulle,sannan ya kwashi
kananan kaya irin su vest da underware da su
rigunan bacci zai fita da su. Fatina da ke satar
kallonsa tun dazu sai ga ta tsaye. A kulule ta ce.
"Ina zaka kai min kaya?" Ya tsaya yana
dubanta,ya ce. "Wai gaisuwar ke nan?" A
tsiwace
ta ce masa. "A matsayinka na wa zan gaishe
ka?" Ya yi mata kallo da gefen ido,sannan ya
ajiye kayan a gefe yana cewa. "To ko in zo in
nuna miki matsayina?" Ta yi saurin komawa ta
zauna tana kunkuni. "Abin da ka iya ke nan".
Ya
tuntsure da dariya ya dauki kayan ya fice.
Yana
cewa. "Ashe har kin fahimci ni?" Can baya ya
zagaya ya wanke kayan tsab ya shanya sannan
ya dawo ya yi musu sassaukan karin kumallo.ya
shirya ba tare da ya tsumaye ta ba ya
nasa.takwas dai dai ya same ta a dakin bacci
tana zaune bakin gado tana faman kuka,kafin
maya yi magana ta riga shi. "Abdul ka cuce ni
wallahi,sannan ka cuce Alh wanda na tabbatar
zai yi wahala wannan bai zama sanadin tashin
hawan jininsa ba. Idan ya rasa ransa ta wannan
hanyar ka shirya zaka daki alhakin
mutuwarsa?"
Babu wata shakka ya amsa mata..... "Idan ke
da
kika yi sanadiyar jaza masa ciwon zuciyar ba ki
dauki hakkin mutuwarsa ba, ya ya kike
tsammanin ni zan dauka?
Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.4) Ai ni masoyinsa ne mai son saukaka masa
hisabi,idan mutuwar ce ta zo ina masa fatan
samun zaukin kwanciyar kabari". Sai da ta yi
nazari sannan ta amsa. "Sai ka bi a hankali don
kai ma dab nake da jona maka ciwon
zuciyar.idan
kuma ya kashe ka bai min asara ba sai dai ya yi
wa wadancan akuyoyin da ka ajiye". Ya yi
murmushi har kumatunsa suka lotsa ya ce.
"Allah
ya asuttura min nayi ciwon zuciya a kanki,shi
ma
Alh kaucewa umarnin manzo Allah (S . A. W) ya
yi yasa hanunsa ya yi turbaya, amma ni tsaye
nake da kafafauna. Kuma yarda ke daya ce
daga
kyallin duniya.don ...... Jajircr nake ba zan
salwantar da addinina da lafiyata dalilinki ba,
tunda lahira ba zaki amafane ni da komai ba.
Sannan idan na mutu na barki wani na za ki
aura.
Zata yi magana ya tare ta. "Kinga da Allah ya
isa,ni zan fita akwai abin da kike bukata?" Ta
yi
banza da shi,don haka ya iso gabanta yana
cewa.
"Bari na sami ladanki na rage miki wadananan
hawayen". Tuna yadda suka yi jiya ya sanya ta
zuabara ta mike,sai ga ta a hanunsa. Ba ta yi
wani yunkurin kwatar kai ba don ta san ba ta da
tsiri,kawai sai ta kwantar da kai a kirjinsa tana
kuka a hankali. Ya rungume ta da sassauci
alamar rarrashi yana fada mata kalamai masu
sanyaya rai. "Haba fadima hawayenki fa ba
abin
banza ba ne da zaki dinga salwantar da su a wofi
ba,kar ki ga ina sharewa kukanki na min ciwo
wallahi,ki ba ni lokaci na nuna miki irin kaunar
da
nake miki na rantse ba irin wadda za ki zuba a
kwandon shara ba ce".6) Haba sadiya ta yi masifar zuwa wuya, cikin
bala'I ta ce. "Wai duk aikin dubu biyu da dari
biyar din ne wannan kike....?" Hindatu tari
numfashinta ta ce. "Kwarai da gaske,tunda
wani
bai taba zuwa a gidanku ya bani kobon shi ba,
kuma har wajen Allah ban zama kaza ci ki goge
baki ba. Na hadiye alkhairi kuma na yi girgiza in
yi hamayya da wanda aka yi min ta silarsa".
Fuuu.... Sadiya ta ajiye kayan ta fice daga
wajen.Da sauri fatima ta tattare kayanta ta
gudu
daki don ba ta saba da masifa da hayaninya irin
wannan ba, ta kuma sha jin labarin fadan
kishiyoyi, yanzu idan sadiya ta fito da tabarya
da
me zata kwaci kanta? Hindatu ta ci gaba da
karatunta, sai ga sadiya da kudi 2500 ta watsa
mata, wadda ba ta yi ko gezau ba don tuni ta
saba da wannan bala'in na sadiya. Sadiya na
huci ta ce. "Sai ki hada ki kara kwazon aiki,don
ni a kansu ba zan sarayar da 'yancina ba".
Hindatu ta kwashe kudi ta bude tsakiyar
littafinta
ta zuba tana cewa. "To yanzu da ba ki sarayar
da
yanzcin naki ba fada min ribar da kika samu,
don
kin ki yarda ne, amma shi Allah babu ruwan
sa,ba a yi masa dole,kuma dole ki san sarki
goma ne zamani goma, abu turab ya gama
yayinki,sai dai ki rungumi sorry ki adana
tsufarki....." Ba ta jira cewar sadiya ba ta ture
kujera ta yi tafiyarta ta bar sadiya a nan
tsaye.
Fatima ta zube kaya kan kujera cikin
hawaye,da
me zata ji, da ganin duhun gidan nan da
ma'abocinsa,ko kuma bala'in wannan matar?
Kamar hindatu ta san yadda za a yi,karfe biyar
saura minti goma Abdullahi ya dawo gida,ko
kallon dakinsa bai yi ba ya sauke gajiyarsa a
dakin fatima,wadda jin dirin motarsa ya sanya
ta
rarumo hijab ta saka, sannan ta nemi guri ta
zauna ta bata rai. Ko kala bai ce mata ba,bayan
sallama bai kuma matsawa kansa kallonta bam
ya shiga da jakar lap top dinsa dakinta, sannan
ya fito ya wuce kicin ya dauko lemo ya dawo ya
zauna a gajiye. Don neman ta kula shi, sai ya
dauki remote ya sauya tashar da ta ke kallo
zuwa
kwallon kafa. Nan ma sai ta share ta kwantar da
kai jikin kujera kawai tana kallon rufin dakin
da
fanka na juyawa wadda kamar tana hadawa da
numfashinta, shi yasa ya sami damar hakura da
kallon kwallon yana kare mata kallo. Can ya
nakara da kayan wankin,ya dan tara gira ya ce,
"Ba ki debo kayan nan da wuri ba ko?" Ta watsa
musu harara shi da kayan,sannan ta kawar da
kai a raunane ta ce. "Daya ke nan daga cikin
cutar da ka yi min, wadda ba zan taba fanshewa
ba. Da idanuna ba zan kalli mai mata na aura
ba,
bare har matansa su zame min matsala a
rayuwa.... Ni ba kaunar zama da mijinsu nake
ba,
amma haushi na suke ji". Kai tsye ya gano inda
gizo ya yi sakar,ya kuma san aikin sadiya ne
don
ya sha jinsu da Hindatu,kwanaki sai da suka
tashi hankali akan haka don haka ba shi da ta
cewa,ga shi kuma dole ya nemo,sai ya yi
murmushi ya ce. "Za su ji haushinki ne don kina
son mijinsu ko kuma dan mijinsu yana sonki?
Da
zaki yi dabara sai ki toshe kofar da za adinga
sanin tsakaininki da mijinki,dan ki ba wa mara
da
kunya.duk sharrin mutum dai ba sai ya ga abin
fada zai fada ba? Dan bata kaya sai na kuma
wankewa,mijinsu suka wahalar ba wani ba. Bai
ma saureta ba ya kwashe kayan ya fita ya kuma
wankewa ya shanya har da matsewa da clip,ya
kwashi kayan sadiya wadanda sun bushe ya kai
mata har dakinta ya ce. "Adana kayanki sun
bushe". Dan takaici sadiya kasa magana ta
yi,shi
kuma ko a jikinsa ya kada kai ya fice zuwa
dakin
fatima,ya yi wanka zuwa magarib ya fice
masallaci. Duk da haka ba zai rasa burgewa da
ya dorar a cikin zamansa da fatima wanda ya
fahimci ya fara ne tun daga ranar da sadiya ta
taka mata kayan shanya. Wato duk bala'in da
ke
tsakaninsu dairin yadda ta ke wulakanta shi a
dakinta agaban mutane karrama shi ta
ke,yadda
ko hindatu da sadiya sai dai su yi msu hasashen
matsala ba wai ta hanyar gani da ido ba, sannan
duk lokacin da take guri to sadiya ba ta isa keta
idon Abdullahi ta yi masa rashin kunya ba tare
da
ta shigar masa ba. Ya gama fahimtar ko kadan
ba sa jituwa ko sadiya ba ta zunguro bala'I a
tsakaninsu ba sai fatina ta zunguro yanzu su
tashi 'yar karamar fitina,Allah. Bashi idan sun
kebe ta hau masa boren ya kawo ta cikin
matansa suna nema jaza mata hawan jini.
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
.7) Ranar
wata asabar fatima ke da girki,amma har karfe
goma sha daya ba ta bude dakin baccinta ba,har
ya gaji da kwankwasawa ya sa mata ido,ya yi
zamansa a falo yana nazarce nazarce a
computer. Can sai gata ta bude kofar ta fito
tana
ta faman atishawa da alama sabuwar mura ce ta
kamata.ta wuce kicin mintuna kamar goma sai
gata da ruwan citta a cup zata kuma shigewa
daki. "Fatima idonsa kan computer ba tare da
ya
dube ta ba. Ta yi turus amma ta ki tankawa. Ya
dago ya kalle ta, ya ce. "Fatima wai ba ki ji
ba?"
Sai ta juyo ta nemi kujera ta zauna ba tare da
ta
dube shi ba, ta fara kurbar ruwan cittarta
fuskarta
a bace. Ya yi nazarinta a nutse sannan ya kara
kyautata murya ya ce. "Wai komawa zaki yi ki
kwanta ba zaki yi wanka ki karya ba? Ta shere
kamar da dutse ya yi batunsa. Bai damu ba sai
ya kuma dorawa. "Kin san kuwa abin da ya jaza
miki murara nan ba zai wuce kunshe kanki da
kike a daki kina fama da sanyin A C da iskar
fanka,amma ba kya gaurayawa da hasken rana
da sassanyar isaka ba? Ta kuma sharewa,sai
kawai ya tashi ya shige toilet ya hada mata
ruwan wanka,sannan ya fito ya mika mata
hannu
ya ce. "Ba ni wannan cittar, shiga ki yi wanka".
Ba ta musa masa ba ta dure cup ta mike ta shige
wankan.kafin ta fito ya tanadar mata shayin
tafarnunwa da zuma ya kai mata har daki
sannan
ya koma mata da madara peak wadda zata
dusashe waurin tafarnuwar. Bayan ta shirya da
kansa ya shasshafa mata man zafi a
makogwaronta zuwa kirjinta, sannan ya rike
hannunta ya yi kokarin kallon kwayar idonta ya
ce. "Don Allah ki zo mu je ki sha hantsi kinji?
Kar
ki daka ta ni ki duba lafiyarki kinji?" Ta kawar
da
kai tana shakar hancin,da sauri ya saki
hannunta
ya yago tissue ya mika mata. Wannan
dawainiyar
da yake mata ce ta hanata yi masa musu wanda
ta ke ji kamar yana mata ne domin saihiyar
kaunar da yake mata tunda babu abin da yake
amfana daga gare ta. Ya daukar musu darduma
da ruwa da filo ya bata rikon ruwan da
tambulan,shi kuma ya dauko mata lemon citta
guda biyu suka tafi. Sun sami sadiya zaune a
daya daga cikinb kujeru da ke rumfar tana
danne
danne waya,Abdullahi ya yi mata sallama tare
da
dan zolayarta amma ta yi fuska. Ya shimfida
dardumar ya sanya filon sannan ya karbi ruwan
hannun fatima yana cewa. "Sannu da
kokari,zama
ban da kwanciya". Ta yi murmushi a kasalce ta
kwanta,ba tare da ta tayar da kanta akan filon
ba. Ya bita da kallo kafin ya yi magana ta riga
shi da taushin murya. "Ka yi hakuri don Allah.
Ya
ji sanyin maganar har cikin ransa,ina ma tare
da
sadiya ko hindatu suke wuni su kwana? Ya
zauna
yana mika mata filom yana cewa. "To na
hakura
sa filon". Ta girgiza kai,ta ce. "Zauna akai ka
karanta min magazine. Kafin ya yi magana sai
ga
hindatu cikin shirin fita.ta yi musu sallama tare
da gaishe da abdullahi,ita kuma fatima ta
gaisheta,Abdullahi ya ce. "Kin ga kuwa hindatu
gaba dayanku ya kamata ace kun je ganin
jariri,fadima muwadda. Matar yaya abdullahi
ce
ta haihu na manta ne ban sanar da ke ba.ya
kamata kuma ki je barka,ko bari zamu yi da
dare
na kai ku gaba daya? Kamar gaske ta ce. "Ai
tunda ba ka sanar da ni akan kari ba ka
makara,Allah ya kai mu suna, hindatu ki shafo
min kan baby...... Ya tare ta. "Idan na ce sai
kun
je sai a yi yaya? "Sai ka aikata abin da bai
kamata ba, ka. Debe ni da mura na je na
shafawa
mutane". Hindatu ta ce. "Ni fa Abu Turab ko
me
ka tsara ba zan fasa fitar nan ba tunda na
shirya,sati biyar fa ban ga waje ba..... Haba kai
har yanzu ba ka tsufa da kulle ba". Ta karasa
da
dariyar zolaya. Shi kuma ya saci kallon fatima
ya
ce. "Kina korafi akan wata daya,me wata uku
ta
ce me?" Fatima ta juya baya tana shakar
hanci,ta
ce. "Kai za a tambaya tunda kake jin zaka iya
maye min gurbin duk wani hali da aboki" "Dan
ma
yana kwatantawa". Inji hindatu cikin
raha.fatima
ta dan yi dariya kawai,shi ma abdullahi haka
yana kallon fatima da ta juya musu baya,ya ce.
"Ita ma dan ba ta sai da turaren wuta a gidan
biki ne shi yasa ba ta matsa min sai ta fita ba"
Ba ta damu da juyowa ba ta ce. "Ka dai samu
dama a kaina kawai,amma nawa uzurin ai ya
zarce na turaren wuta.na kuma zuba maka ido
nan da wata uku masu zuwa in sabuwar
amaryaka zata shigo ka barni na fita". Ya jima
kafin ya samo inda wannan maganar ta
samu,sai
can ya tuna ganinta,dan haka da kyar ya samo
abin cewa. "Ni ban san wata amaraya ba ban da
ke shekaru talatin nan gana ba watanin uku ba"
"Allah ya nuna mana". Inji hindatu da ta so
katse
hirar bayan kishi ya sosa ranta.ta nufi sadiya
tana cewa. "Kin ga sadiya dan Allah rabi
kanwata
zata zo yau mun yi waya da ita yanzu suna bisa
hanya, ni kuma na riga ba shirya ban son fasa
fita,kuma da yake dama hutu zasu zo min sai
kawai na ce su sauka a wajenki. Dama sadiya a
wuya ta ke,neman me taba ta take ta fashe a
kansaa. A wulakance ta ce. "Ni ma fita zan yi".
Abdullahi ya dan kalli sadiya amma bai tanka
ba,
sai fatima da ke jinsu ta ce. "Idan babu
damuwa
ba sai ta zo wajena ba, Allah ya sa matara aure
ce mu samu mai gidan nan ya barni mu sarara".
"To addu'arki ba ta ci ba". Suka hada baki shi
da
hindatu suna yi mata dariya,hindatu ta yi
mata
godiya,shi kuma ya dubi fatima da muryar
rarrashi ya ce. "Bari na kaita titi na samar
mata
taxi". Ta amsa masa. Suka fice aka barta da
sadiya wajen ya yi dif! Kamar babu masu rai a
wajen, wannan ya ba wa fatima damar bacci
mai
nauyi saboda kasalar jiki. $ can hayaniyar
abdullahi da sadiya ta farkar da ita,Abdullahi
da
sadiya ta farkar da ita,Abdullahi na cewa.
1 · Like · React · Report · May 15, 2015
Amierah S-Man
Zuciya d kwanji
8) "Sadiya dama ana tambayata unguwa ranar
da za a yi ta ne da kike neman ki zage ni dan
na
hanaki fita?" A tsiwace ta ce masa. "To da
wanne
KWANJIN zaka ce sai na yi abin da kake so
alhalin kai ka take dukkan adalcin da ya
kamata
ace ka yi min? Ai babu wani dalilin da zai sa ka
ce sai na bi dokarka" Cikin alamar sikewa ya ce.
" Ai dama ke batunki ba ya wuce nan, kullum ke
an bata miki. A'a ba a yi miki adalci ba, komi
aka
yi miki ba a burge ki alhalin ke kin gaza da taki
biyayyar. Ni na rasa wamnan mugun son mulkin
naki wallahi....." A kule ta katse shi da cewa.
"To
idan an yi min makauniya ce da ba zan gani
ba,ko kana tsammanin gara ce ni irin hindatu
wadda za mayar borar gida ta kasa damuwa?

Please Login or Register in order to submit comment