Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

da kayan Makaranta mai kalar blue hijabinta kuma fari tas! Shigowar Sultan yasa ta Karaso kusa da shi tana mika masa hannayenta, “Dee ka taimaka ka cire min abin hannun nan kada a Kwace min a Makaranta.�? Kafe ta ya yi da idanu yana tuna wasu abubuwa, sal kuma ya kama tsintsiyar hannun yana kokarin cire mata. Cikin sa’a ya dago kansa ita kanta shi ta kafe da idanu tana kallon sa. Manyan idanunta suka hade da nasa masu yawan lumshewa. Gaba daya suka sakarwa .. kansu murmushi, ‘sannan ya cire mata. “Lazy baby, ki yi sauri ni zan ajiye ku in wuce office.�? Marairaicewa ta yi , “Ayyah Dee, Kila ma kai kayi min baki shi ya sa har yanzu nake Lazy.�? Murmushi ya yi ya dauki jakar makarantarta suka fito. Umma ta dube shi ta riqe baki, “Oh wani sabon gulmar ce kuma yau Za ka rike mata jaka? Kullum da sabon salon iskancin da yarinyar nan take dauke da shi.�? Wucewa tayi . Sultan suka kalli juna da Nasreen sai duk suka basar. Sultan zai tafi kwas wanda za a Kara masa girma, sai dai wannan ne karo na kusan hudu yana soke tafiya kwas dinsa sabod su Nasreen. Amma a yanzu tunda sun girma za su iya yin komai da kansu, yana da buKatar tafiya. Yafi tausayawa Nasreen da ta dora shaKuwar duniyar nan akan Sultan. Haka ya dinga shirye-shirye jikinsa babu Kwari. Nasreen ta shigo dakin ta dube shi ta ce, “Dee in kawo maka Assignment dina ka taya ni dubawa ko nayi dai-dai?�? = Dubanta yake yi kamar yau ya fara ganin ta, “Nasreen kin ga na gaji da yawa, ki bari sai ~ an jima ko?�? Gyada kanta ta yi tana duban yadda yake shirya kaya, “Dee ina za ka je da kayan nan? Na san ba za ka tafi ka bar ni da Umma ba ko? Umma ba ta sonmu ni da Nawfal, ban san me muka yi mata ba. Dee me muka yi mata?�? Shafar gefen sajenta ya yi yana KirKiro murmushi, “Babu abinda kuka yi mata, tana son baku tarbiyya mai kyau ne, Tana sonku kun ji? Ko kin taba ganin inda uwa ta tsani ‘ya�? yanta?�? Nasreen ta yi narai-narai da idanun dake firgita “yan maza ta ce, “Ai ta ce ba ita ta haife mu ba, wai mu a Karkashin gada aka same Sultan da ya ji gabansa ya fadi, ya mike jikinsa har yana kyarma. Kai tsaye falon mahaifinsa ya nufa, wanda yake zaune da Umma. Ya dube su ransa a matuKar bace ya ce, “Umma don girman Allah ki daina cewa yaran nan bake kika haife su ba, har kina gaya masu daga inda suka fito. Yaran nan ba su san komai ba, bai kamata ana yi masu hakan ba.�? Abba ya dube shi cike da mamaki, haka ya dawo da kallonsa gun Hajiya Salma tare da ware ~ idanu, “Salma! Kina nufin duk irin gargadin da nayi maki baki ji ba kenan? Me ya sa za ki dubi yara Kanana kina gaya masu irin wannan maganar?�? Hajiya Salma ta dinga auna wa Sultan harara, ta kuma hada rai ta Ki yin magana. Haka Sultan yasa kai ya fice ransa a bace. Alhaji Lukman ya mike yana dubanta ya fice ya bi bayan Sultan. Sannu ba ta hana zuwa, sai dai a dade ba a je ba. Sultan dai ya bar garin zuwa Enugu, ba tare da wata matsala ba. Haka ya jaddada amanar Nasreen a gurin Mairo ya fi a Kirga. Da zai tafi yaran suka yi masa layi kowannensu ya yi tagumi. Gabadaya ji yake ya karaya. Ya sa hannu ya yafito su duk suka Karaso gabansa yana dubansu. “Nawfal, Nasreen ba za ku yi min dariya ba?�? « , Dukkansu suka fidda murmushi wanda kallo daya za ka yi masu ka fahimci iyakarsa fuska. Shafa kansu ya yi ba tare da ya iya furta komai ba, direba ya ja motar suka fice. Rintse idanunsa ya yi da Karfi yana jin gabansa yana tsananta fadiwa. Ji yake kamar ba zai dawo ya same su da rai ba. Hajiya Salma ta gama leka ko’ina ta tabbatar da babu Abba a gidan, hakan ya sa ta jawo Nasreen da Karfin tsiya ta fesa mata wani abu a cikin idanunta. Yarinyar ta sanya Kara mai Karfi, ta fadi tana shure-shure. Nawfal ya Karaso da gudu ya tallafo ta yana Kwala mata kira. Nasreen tana kuka Nawfal yana kuka, gaba daya an rasa wanda zai lallashi wani Nawfal ya dago ya zuba wa Hajiya idanu, yana jin haushinta da tsanarta a cikin ransa. Ko da yake yaron yana da tabbacin Umma bata kaunarsu. Yana kallon yadda su Haidar suke kwasar dariya. Hafsa ta ce, “Shegiya ba kina taKama da idanunki ba ne? To an nakasa su sai mu ga wani abin yangar.�? Haka suka wuce suka barsu cikin kuka. Ita kuwa Nasreen saboda azaba a take ta suma. Umma ta sake dawowa, ta damki wuyar rigar Nawfal ta ce, “Wallahi kuka sake kuka fadawa waml Wai ni ce nay mata wani abun, sai na kashe ka Nawfal ya gyada kansa yana ci gaba da hayyacinsa saboda kuka. Cikin ikon Allah sai ga Abba ya dawo, kai tsaye ya nufi yaran don ya duba su. Haka yana son ya cika alKawarin da ya daukarwa Sultan zai hada shi da su. Ganinta a kwance bata motsi ya daga hankalinsa. Bai tsaya bin ba’asi ba, ya dauketa sai asibiti. Yana nan tsaye ya kasa zaune saboda tunanin mai ya sami Nasreen haka? Ya fi Karfafa zarginsa akan Hajiya Salma, idan kuwa ita ce, babu shakka zai ya sakinta ta koma gidan su. Kiran wayar Sultan na biyar kenan, yana kasa dauka. Dole yasa wayar a kunne yana cewa, “Sultan ban iso gidan bane. Ka kwantar da hankalinka ina isowa zan hadaka da yaranka.�? Sultan ya cika da mamakin mutumin da ya ce masa yana kusa da gida, yanzu kuma zai ce bat iso ba. “Abba fa ka ce min kana kusa da gida, yanzu kuma ka ce baka iso ba. Abba ko dai da matsala ce?�? Jikin Abba ya yi sanyi, yau ya yi wa dansa karya har ya kama shi, “Ka yi haKuri Sultan babu matsalar komai, har na kusa gida aka sake ~kirana, wani abokin mu bai da lafiya shi ne yanzu na iso asibitin.�? Dole Sultan ya ajiye wayar yana ci gaba da saKe-sake. Lambar mahaifiyarsa ya kira, tana kallo ta Ki dauka gabanta yana fadi kada Nasreen ta farka ta ambaci sunanta. Da kiran Sultan ya yi yawa ta dauka cikin daga murya ta ce, “Wai menene haka kamar kana bi na bashi?””“Umma don Allah ki taimaka ki hada ni . da su Nasreen, Abba ya ce bai iso gida ba.�? “Umma taja dogon tsaki, “To ba zan hada ka da su din ba. Ka ga Sultan? Ka kiyaye ni! Idan ba haka ba, ni na san yadda zan yi da kai. Kada ka sake kirana.�? Kawai sai ta kashe kiran. Wayarsa yabi da kallo yana jin kashe wayar har tsakiyar kansa. Ya kasa jure rashin jin muryar yaran, don haka ne ya ci gaba da jin damuwa da bacinrai. _ Likitocin suka fito suka bukaci Abba da ya biyo su Office. A nan suka yi masa bayanin wani Chemical aka zuba mata a idanun, a sakamakon hakan da wahala ta sake gani da idanunta, sai kuma-_wani ikon Allah. Abba ya yi suman zaune. A yanzu me zai iya gayawa dansa? Dakin da Nasreen take zaune ya shigo yana dubanta, “Nasreen.�? Lalube take yi tana fadin “Na’am Abba. Me ya sa bana ganinka? Abba ina Nawfal? Shi ma ba zan iya ganinsa ba? Abba ka bude min idanuna ina son inganka. Abba idanuna har yanzu Zafi suke yi min.�? Hawaye mai dumi ya biyo idanun Abba. Zuciyarsa ta karye, ba shi da wani Karfin guiwa. Zama ya yi kusa da ita ya kamo ta, ya mayar da ita jikinsa, ‘“Nasreen dina. Wannan Kaddararkice, haka komai za a yi maki insha Allahu sai kin kai labari, domin ke RUBUTACCIYA ce, wanda Allah ya rubuta sai kin sha ruwa a duniyar nan. Ciwo kika ji za ki warke har ma ki fara gani da idanunki kin ji? Yanzu gaya min waye ya watsa maki abu a cikin idanu?�? Nasreen da ta gigice ta hau girgiza kai “Ni ma bansan waye ba Abba: Ka kai ni wajen Dee in nuna masa idanuna, bana ganin kowa sai duhu.�? Wannan karon kalaman bakin Abba sun Kare, dole ya koma kamar kurma. Satinta guda a asibitin, kullum Abba ke kulawa da ita, haka ya Ki yin magana ne yana jiran a sallamota. Nawfal da Mairo mai aiki suke zaman kulawa da ita. Ranar da aka sallame su, suka tattaro suka dawo gida. A bakin Gate suka sami Nawfal kusa da mai gadi ya zauna ya yl shiru, kasancewar a ranar Abba ya hana shi zuwa ya ce ya bari kawai yau za su dawo da Nasreen din. Yana ganinsu ya taso ya Karaso da saurinsa kamar zai kifa. Ganin Nasreen tana lalube yasa Nawfal kafe ta da idanu. Abba ya jawo Nawfal yayi masa dabarar duniyar nan amma ya Ki fadin wanda ya yi wa Nasreen wannan aikin. A tunanin Nawfal da gaske Abba yake yl, yau Nasreen za ta fara gani da idanunta, kafe ta ya yi da idanu, zuciyarsa tana gaya masa Nasreen ta tabbata makauniya.Sai kawai ya hau kuka mai tsanani yana tausayawa ‘yar uwarsa. Abba ya dubi wayarsa yana kallon kiran Sultan, ya dubi yaran ya ce, “Ga Daddynku zai yi magana da ku, idan kun dauka ku tabbatar masa kuna lafiya kun ji? Idan ya san abinda ya faru zai fasa aikinsa ya dawo nan, ku bari har ya gama sai ya dawo sai ya gani. Nasreen ke kuma insha Allahu zamu nemo maki magani ‘har ki warke.”Dukka yaran suka amsa masa. Da kansa ya kira Sultan ya mika wa Nawfal. Muryar Nawfal da yaji yasa ya saki ajiyar zuciya, suka gaisa da yaron yana masa ‘yan tambayoyi. Daga bisani ya ce, a baiwa Nasreen. Cikin Shagwababbiyar muryarta ta ce, “Dee…�? Sai �? kuma_ tayi shiru. Siririyar muryarta ta ci nasarar tsinka masa zuciya, “Nasreen kin ‘yi kuka, Nawfal ma ya yi kuka, gaya min waye ya

*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427**

BOOK 1



CHAPTER 5



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*


*Wannan littafin na kudine idan kina bukata kiyi magana ta wannan number 09068032427*

A JIYA MUN TSAYA

Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.�? Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�?

ZAMU TASHI

Daman ko bai ce ba, Hajiya Salma ba za ta iya tafiya ko nan da can ba. Don haka suka yi Sallama ya fice. Nasreen ta sa sandarta a Kasa tana KoKarin ficewa tun kafin fushinta ya sauka akansu. Nawfal ya rike mata sandar suka fice. Yau Sultan ya dawo garin, yana shaKar iskar garin Kaduna ya ji wata natsuwa tana shigarsa. Yana farin ciki yau zai ga twins dinsa. Mota tana yin parking a lokacin mahaifinsa ya fito zai fice. Farin ciki ya kama mahaifinsa, duk da sai da gabansa ya fadi. Rungume juna suka yi cike da farin ciki, haka yana nan a tsaye yana amsa gaisuwar ma’aikatan gidan. Daga nesa ya hangota fuskar nan dauke da farin ciki, tana rike da

sandarta tana laluben hanya. Nawfal ya Karaso wurinta ya rike mata sandar yana cewa, “Idan na gadama insakar maki sandar inrigaki zuwa inyi masa oyoyo. Nasreen ta yi dariya, ta ce, “Ai nasan ba za ka yi min haka ba.�? Sultan yana magana da mahaifinsa ya kasa Karasa abinda yake fada ya kafeta da ido babu ko kiftawa. Ya rasa wannan wani irin wasan kwaikwayo ne haka? Abbansa yabi inda yake kallo.da kallo, ba tare da ya furta komai ba. Nasreen tana Karasowa ta saki sandar ta ce, “Didina ka kama hannuna intabbatar da kai ne.�? Sultan ya kasa yin motsi sai kallonta kawai yake yi. A zatonsa wasa take yi, amma yanzu ya tabbatar da babu wasa a lamarin nan. Nawfal ya kama hannun Sultan yana cewa, “Didi sannu da zuwa. Na riga wata yarinya rike hannun Didi.�? �? Nasreen ta saki dariya ta ce, “Babu damuwa zan rama watarana.�? A lokacin ta sami daman rike hannunsa kawai ta rungume shi. Hawaye suna sauka daga idanunta zuwa bayansa. Yana jin digar hawayen hakan yasa ya dan rintse idanu ya ware su da Karfin gaske. A lokacin ne Hafsat da Haidar suka fito. “Sannu da zuwa Yaya.�? Su kansu bai amsa masu “ba, hakan yasa suka tsaya suna duban yadda ya yi kamar wanda ya mutu a tsaye. Da gaske ya rasa me zai ce, wacce tambaya ya kamata ya fara yi, kuma idan zai yi din wa zai wa? “Abba Nasreen ta daina gani ne?�? Wannan ‘tambayar ce ta Kwace masa da karfin gaske ta : fizzo kanta ta samu ta fito. Abba ya girgiza kai, “Nasreen bata ganin komai. Kaddara ce ta Ssameta, muna fatan mu samu mu cinye. Ku zo mu shiga ciki.�? Hannunsa daya yasa ya dan shafi bayanta kafin ya dagota daga kwancen da take, yasa hannu ya dauke mata hawayen idanunta, sannan ya riKe hannunta suka shiga ciki Har yanzu jikinsa a sanyaye yake haka ya kasa gazgata abinda ya gani. Dakinsa ya shiga ya kintsa sannan ya fito falon ya iso har gaban mahaifiyarsa ya duka ya gaidata. Ita kanta Hajiya Salma ta sani, kaf cikin ‘ya’yanta babu mai biyayyar Sultan, sai dai wani ra’ayi nata da yasa take jin haushin abinda yake aikatawa. A hargitse ya yi maganar da yasa kowa yake kallonsa, “Abba ashe ba zan iya barin amana a rike min ba? Waye zai aikatawa Nasreen irin wannan mugun abun? Nasreen ta makance amma ba a taba gaya min ba? Ko waye ya aikata mata wannan abun ba zan taba daga masa Kafafu ba.�? Ya ajiye maganar ba yadda ya kamata ba. Nasreen ta Karaso tana lalube har ta iso gabansa, “Dee, wanda ya aikata min hakan ya fi kowa sanin dalilin da yasa ya yi min. Kuma ni na yafe ma wanda ya yi hakan, Kada bakin ciki yasa ka furta wasu kalaman da suka cika yin nauyi. Kayi haKuri kamar yadda Abba ya ce min inkarbi Kaddarata haka kaima ya kamata kayi. Ni bana jin damuwa, ina gode wa Allah a yadda ya �? bar ni. Idan kuma kace za ka dauki mataki bansan wurin wa za ka je daukar matakin ba, domin nima bansan wanda ya aikata min hakan ba.�? Sultan ya dubeta yana jin zuciyarsa tana yi masa wani zafi. Yana kallon manyan idanun nan masu tsari yau sunée a rufe bata gani da su. “Nasreen zan yi bincike zan kuma dauki mataki kamar yadda na fada. Bincike biyu ke gabana kuma Insha Allahu duk sai na aikata su. Duk wanda ya aikata maki hakan babu ko shakka zai iya yin kisan kai.�? Hajiya Salma ta yi maza ta tari numfashinta, domin Sultan gaf yake da zageta, “A’a ya isheni haka. Idan ka tashi yin binciken sai ka hado da ubanka domin shima a gidan ya kwana, ko kuma duk ka kama mu ka rufe har sai ka gama binciken. Idan za ka wuce kaje ka ci abincinka ka wuce, idan kuma tsayawa za ka yi ka samu a gaba kana yi mana tambayoyin rainin hankali Bismillah.�? Sultan ya duKar da kansa-ba tare da ya iya furta komai ba. Abbansa ya dafa shi, “Sultan, ka yi haKuri, kullum da Nasreen nake kwana da ita nake tashi a zuciyata. Na rasa gano wanda ya yi wannan aikin. Ka je kayi bincikenka, nima idan na kama wanda ya aikata min wannan aikin insha Allahu zan tsaya sai naga anhukunta shi, ko wanene kuwa. Haka kaima ka dauki mataki, tunda a lokacin da za ka fara aiki, sai da kayi alkawarin tsayawa akan gaskiyarka, ko da kuwa ni mahaifinka ni ka kama da irin wannan laifin, don Allah ka dauki mataki kada ka ragawa mutum. Idan kayi hakan zan san dana ya tabbata a cikin dan sandan mai amana da gaskiya. Allah ya yi maka albarka. Zan �? bayyana maka matarka da zarar ta kammala Makarantarta, wanda bana jin za ta dauki lokaci, domin tana shekararta ta Karshe ne. Tashi kaje ka ci abincin.�? Sultan ya dan sami natsuwa da kalaman mahaifinsa, kafin ya tashi Nasreen ta fara tashi, tana lalube saura Kiris ta fadi ya Kwala mata kira, “Nasreen! Tsaya.”�? Babu musu ta tsaya ya Karaso ya kama mata sandar suka fice. Hankalin Hajiya Salma idan ya yi dubu to ya tashi, Sai taga kamar da Nasreen ta makancen sai abin yafi sake yin muni, Hankalinta ya Kara tashi ne da Hajiya Ladidi ta tabbatar mata, tunda anyiwa danta aure, to Alhajin ne da kansa zai auri Nasreen din, domin kuwa shi namiji bashi da kunya. Zai reni abu ya kuma aureta. Hauka ne kawai Hajiya Salma ba ta yi ba, domin ita ta kasance mace mai zafin kishi, akan Alhaji Lukman za. ta iya kashe rai. Sultan ya tashi hankalinta Kwarai akan maganar binciken da ya ce, zai yi domin kuwa kallonsa take yi a matsayin mayen ‘yan sanda. A _ dalilin Kwarewarsa yasa ake ta Kara masa girma. Dole ta yi yunkurin daukar mataki akan abubuwan nan tun kafin tana ji tana gani danta ya garkameta a Police Station ‘yan jaridu su sami daman watsata a duniya. Haidar ta aika ya kirawo mata Sultan yana shigowa ta dube shi sosai. “Kana jina? Idan na sake jin ka sami ‘yan aiki kana yi masu bincike ko Kannanka ban yafe maka ba. Nasreen wani Kato ya shigo ya rufe mata baki ba mu ji ba, ya yi mata wannan abin. Kai baka yarda da Kaddara ne? Kai ka sani ko mugayen da suka kashe mahaifiyarta ne suka gane akwai yaran a gidan nan? Ni shi ya sa tun farko ban so rikon su ya zamana a nan ba. Bana son kaje garin tone-tonenka ka jawo mana masifa har cikin gida.�? Sultan ya zubawa mahaifiyarsa idanu kamar mai son gano wani abu. Hankalinta ya Kara tashi ta ce, “Laaahh! Ni kake kallo haka kamar ka sami barauniya? To tashi ka wuce na gama magana. Bai ce komai ba, bai kuma tashin ba. Can ya nisa ya ce, “Umma wai har cikin dakinta aka shiga aka aikata hakan duk baku sani ba? A lokacin kina…�? A zafafe ta ce, “Ina dakin ubanka ne a lokacin. Ingama ce maka ka bar maganar nan amma kuma saboda tsaurin idanu za ka koma yi min tambayoyi? Sultan wai yaushe ka sauya ne? . Zuwan yaran nan rayuwarka sun sauya mun dana. Yauwa Sultan wai wacece matarka? Na yi bincike sosai antabbatar min ba ‘yar gidan Alhaji Mamman ba ce. Anya ya kamata ka amshi auren nan kuwa? Bana son yazo baka yi sa’ar mata ba, dan nuna min ita ko a hoto ne.�? A lokaci guda bayan ta gama masifar ta yi Kasa da muryarta kamar mai rada. Sultan da ya gaji da tsugunnon da yake, ya jawo wata ‘yar kujera ya zauna yana fuskantar mahaifiyarsa, bayan ya dauki dabino | daya ya Sa a bakinsa. “Umma ban santa ba, ban taba ganinta ba, ban san sunanta ba, haka ban san ko ‘yar gidan waye ba. Kasan da ta tafi karatun ma ban san shi ba. Kawai abinda nake buKata addu’a Umma. Idan kika yi min hakan kin gama yi min komai. Kuma insha Ailehu zanyi maku biyayya wajen karbar zabinku.�? Umma ta Harare shi, “Wajen karbar zabin mahaifinka ko kuma zabina? Ni zabin da na ‘baka ka karba ne? Ina son ka bude kunnunwanka da kyau ka ji ni. Ka je ka sami mahaifinka kace sai ya hadaka da matarka ko gaisawa ce ku dinga _ yi. Ya zama dole musan wacece da me za ta shigo gidan. Idan ba ta yi ba, sai ka botsare masa ka saketa kawai ta kama gabanta.�? Muryar Abba suka ji yana magana, “Allah kadai zai iya shiryaki Salma. A duk ranar da shawararki ta yi tasiri a zuciyar danki ina tabbatar maki sai kin yi mugun danasani. Ba zan bayar da hoton ba, bazan kuma hada su ba, har sai lokacin da na gadamar yin hakan. Kai Sultan zo ka wuce.�? Babu musu ya mike ya fice abinsa yana al’ajabin mahaifiyarsa. Ita kuwa hajiya Salma dubansa ta yi ta ce, “Ka dai san babu kyau labe ko? Babu daman inzanta da dana sai ka hau masifa?�? Dubanta ya yi ya ce, “Labe? Waye dan naki? Yaron da kika ware shi a_cikin ‘yan’uwansa kika jawo masu rashin shaKuwa da juna? Ai da wannan kadai idan na bar ki Salma sai Allah ya hukuntaki.�? Bai tsaya saurarenta ba ya sa kai ya fice abinsa. Sultan yana nan ‘tsaye, bayan ya tabbatarwa mai tsaronsa ya wuce kawai ga shi nan zuwa. Yana nan a tsaye yana kallon tsakar gidan. Hafsat ta fito da wani dutse ta ajiye a hanya ta koma ciki. Ba ta kula da shi ba, haka shima bai kula da abinda hakan ke nufi ba, domin kuwa tunaninsa ya yi nisa. Nasreen ta fito tana lalube sai kawai ta ci tuntube da Katon dutsen nan ta fadi a wurin.Sultan ya zaro idanu a lokaci guda kuma Hafsat ta fito daga maboyarta tana kwasar dariya. Zata wuce kenan ta ji anfinciko ta. A razane ta dago tana hada idanu da yayanta ta tsure, “Yaya me nayi?�? Dau! Ya dauke ta da mari, daman kuma hannunsa babu kyau, a take fuskar ta kumbure ~ ta yi jazir, abinka da farar mace. Ya sake daga hannu ya yi ta kwada mata. Sannan ya watsar da ita. A gujen gaske ta yi cikin gida, domin wannan shi ne karo na biyu da ya taba dukanta a duniya, kuma duk akan mutum daya. Karasowa ya yi inda Nasreen din ke zaune ta yi shiru kawal. Yasa hannu ya kamota suka koma inuwa suka zauna. Yana jin dadin Kare mata kallo, baya gajiya da hakan. Ciwon da ta dan ji yake dubawa, bayan ya kama hannunta. A hankah yake shafar ciwon wanda yake sanya mata wata kasala, tana sake lullumshe idanunta, labbanta kamar za ta yi © magana, amman hakan ya gagara. Yanayin da ta shiga yasa mamaki ya kama shi, tambayar kansa yake ko dai ba Nasreen ba ce? Irin yanayin nan masoya kadai ke iya kasancewa a cikinta. Dayan hannunta tasa ta rike hannunsa tana girgiza kai, “Dee.. Na daina jin zafin yanzu.�? Murmushi kawai yaji, kafin kuma muryar Umma ta wargaza masu yanayin da suke ciki. “Sultan! Yanzu akan yarinyar nan za ka yi wa Hafsat irin dukan nan? Ba ka da hankali ne ko mene ne haka?�? Sultan ya yi magana kamar baya son yl, “Umma idan kannena suka yi laifi babu daman in hukunta su kenan?. Haba Umma

Please Login or Register in order to submit comment