Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

matsayin miji da mata. Kada ka mance Nasreen RUBUTACCIYA ce, tun tana cikin mahaifiyarta take haduwa da Kaddara, har yanzu tana rayuwa. Dole duk inda Nasreen take ta dawo domin bata da wani wurin da ya wuce nan gidan. Ka kwantar da hankalinka mu dage da addu’a.�? Lumshe idanunsa ya yi yana tunanin a wani hali suke a yanzu? Wasa-wasa sai da Sultan ya yi kwanaki biyar yana jinyar kansa. Ko da ya dawo gidan ma sai ya koma yi masu yajin magana. A take ya kira su Mahbub ya gaya masu komai, hakan yasa dukkansu suka baro aikin su suka iso wurinsa. Barr Tajuddcen ya fara magana kamar kullum, “Sultan akwai sarkakKiya a_ cikin wannan lamarin. Ta ya ya hakan zai faru? Ta ya ya za a sace Nasreen da dan uwanta? Dole mai wannan aikin yana kusa da kai ne. Nasreen -matarka ce? Daman da ita Abba ya daura maka aure? TirKashi! Abin akwai sarKaKiya.�? Haisam ya karBe da cewa, “Ko dai mahaifinsu ya gano akwai ‘ya’yansa a gidanku ne? Zai yuwu sai kawai ya aiko a sace su.�?
Aslaf ya girgiza kai, “Ni ma tunanin da nake yi kenan, idan ba haka ba waye zai sace su?”�? Mahbub ya girgiza kai, ““A’a mahaifinsu bai san da zaman su ba, bana jin shi ne zai yi wannan aikin. A dai sake bincike.”Ashmaaan ya dago yana duban kowa, har anfidda rai zai yi magana, sannan ya tanka, “Ku natsu sosai ku dubi maganar Mahbub, Idan har mahaifin nasreen yasan suna raye, ba zai bari su kawo wannan shekarun ba, zai aika a yi farautar ransu kamar yadda ya yi na uwarsu. Amsar wanda ya aikata hakan yana wurin Sultan domin kuwa shi ne yasan mutanen da take takun saKa da su.�? Khamis ya dan murmusa ya ce, “Dadina da kai kaifin basira dan mutan Sudan. Maganar gaskiya ba mahaifinsu ba ne ya yi aikin nan, wanda ya aikata laifin nan makusancin Sultan ne, na kurkusa. Sultan kayi sakaci gaskiya. Yaran da suke dauke da abubuwa masu rikitarwa, za kabar su kara zube? Kana da irin matsayin nan a hukumance amma kake barin ~wani lagwanin direba ya jasu zuwa Makaranta? Ai yaran nan tsaro suke bukata. Ka mance na yi irin wannan sakacin aka tafin min da mata? Ka mance Ashmaan ya yi irin wannan gangancin aka kusa kashe masa mata? Daga Karshe me ya biyo baya? Dabararsa ta Kwace shi, da ya dauke matarsa ya turata London. Shi Mahbub da ya fimu dabara, ai hada matarsa ya yi da ‘yan sanda ya kuma sanya doka mai tsanani akanta. Yanzu dai menene abin yi?�? Al-ameen ya ce, “Aikin gama ai ya gama. If not da gidajen daya daga cikin mu ya kawota aka boyeta har a gama bincike, mu zaKulo masu laifukan. Yanzu maganar bincike a kan wadanda suka yi kisa dole a dakata tunda shaidun sun Bace. Kawai mu mayar da hankali wajen nemanta.�? Sultan ya girgiza kai, “Mahaifiyata ce kadai ta tsani Nasreen da dan uwanta tsana mai tsanani. To kaina ya kulle ko ita ce za ta sanya ayi hakan domin nisanta su da mu? Sai kuma wani dan iska da ya taba zuwa wai yana sonta Wai sai ya aure ta. A lokacin bansan andaura mana aure ba, zafin da mahaifina ya dauka ya bani mamaki. Su dai nake zargi.�? Barrister Tajuddeen ya danyi rubutu ya -. dago yana duban Sultan, “Sorry to say Sultan, Umma ita ce asalin suspect! Amma kuma tafi Karfin mu gaskiya. Sai dai mu bi komai a hankali har Allah ya warware mana ‘wannan tashin hankali. Sannan zamu sa malamai suyi ta sauka suna addu’a. Allah ya bayyana maka matarka da dan’uwanta,�?
Gabadaya aka amsa da Amin. Sultan ya dan shafi sajensa ya ce, “Zan bar garin nan. Ba zan iya zama a cikin gidanmu ba, sai in ga kamar zan ga Nasreen. Yarinyar da bata ganin gabanta ya za tayi rayuwa a wurin da babu tattali? Ba zan yi aure ba, zan tsaya in jirata har ta dawo gareni.ba�? Babu wanda ya nemi ya dakatar da shi, domin dukkansu sun dandani dacin soyayya. Haka suka tashi suka yi musabaha sannan duk suka rabu. Sultan yana isowa gida ya same su suna zaune ya gaida su, sannan ya dube su fuskar nan babu fara’a. “Abba nan da wasu lokuta insha Allahu zan koma Abuja da aiki. Sai a taya ni addu’a.”�? Abba ya dube shi da tausayawa ya ce, “Sultan ya zama dole kayi aure. Ba zan zuba ido ka kai wannan shekarun babu mata ba. Ka yi hakuri kada kayi fushi, ka raya sunnar manzo. Kullum matsayi sake zuwar maka yake yi, amma ka kasa haKuri da Kaddararka.�? Shiru ya yi yana sauraren Abbansa. “Abba zan jira ta har ta dawo.�? Shiru dakin ya yi har yaushe za a tsaya jiran dawowar Nasreen? Wa ya san rana? Kyale shi kawai ya yi domin ya samu natsuwa. Umma zata yi magana ya daga mata hannu. Sultan har ya fice zai shiga dakinsa ya dawo da baya yana kallon Kofar dakin Nasreen da babu kowa a ciki. Girgiza kansa kawai ya yi ya wuce., Duk wasu kayayyakinsa da yasan zai iiya nema ya tattara su wuri daya. Hoton da suka dauka su uku ya kafe. da idanu. Shi Nasreen sai kuma Nawfal. Ya jima yana kallon hotunan kafin ya zuba su a cikin kayansa. Cikin gaggawa aka daga shi zuwa Abuja, a lokacin ne kuma ya sauya sabuwar rayuwa.

Da asubahi suka tashi suka gabatar da Sallah,
a lokacinne kuma mai abinci ta 1so tana Kokarin hada murhu. Nasreen da Nawfal suka gaishe ta, Ya jawo hannun Nasreen ya zaunar da ita a gefe guda, ya taya mai abincin hura wuta. Duk ruwan da ake dibo mata shi ya-diba mata, hakan yasa ta fahimci yaron yana da zafin nama, duk da jikinsa yana nuna hutu. Gari yana yin haske mutane suka shiga zuwa siyan abinci, a lokacinne kuma ta zuba masu nasu abincin ya {Karasa inda Nasreen take zaune ta yi tagumi ya janye tagumin yana dubanta, ‘‘Nasreen ki daina damuwa bana so. Ga abincin ki ci, ni zan je inwanke mata kayan miya.�? Tausayin Nawfal ya kama ta, yau kwatakwata bai huta ba. Tana cin abincin tana kuka. Ta rasa ta yadda za a yi ta taimakawa dan uwanta yau yasha wahala sosal. Basu suka samu suka zauna a inuwa ba, har sai da aka kira Magrib. Haka idanuwan mazan nan ya koma kanta. Da zarar suka fahimci makaunlya ce sai su tausaya masu. Haka basu yarda angane a wurin �? suke kwana ba. Sai da dare ya yi sannan ya zagaya ta baya ya ajiye mata ruwan wanka, saboda Amina ta basu aron bokiti da soso. Ya ce, “Nasreen ta shi kije ki yi wanka.�?

Babu musu ta tashi ta zagaya. Yana nan tsaye yana gadinta har ta gama kintsawa, ta mayar da kayan makarantarta…RiKe hannun Nawfal ta yi, tana kuka, “Nawfal kana shan wahala da yawa. Nawfal ba zamu iya wannan rayuwar ba.�? Shima riketa. ya yi “Zamu_ iya Nasreen, ki Karfafa zuciyarki zamu _ iyaWatarana sai labari.�? Da haka ya samu yake Karfafa mata guiwa, Haka suka kwana cikin cizon sauro da cinnakai, gaba daya jikinta sun yi rudu-rudu saboda azabar cizo. Washegari ta ce, “Nawfal ba zamu nemi wani wurin kwanciyar ba? Na gaji da, nan. Sai da ya yi murmushi sannan ya ce, “Allah ya bamu.sana’a mai dan Karfi ko Daki ne mu kama sai mu ga abinda Allah zai yi. Nasreen ta yi na’am da bayanan Dan uwan nata, wanda ya fita nisan tunanin, A kwanaki biyar kadai Nasreen ta fita hayyacinta, shi kuwa Nawfal har ya fara sabawa da wahala da kuma kwanar siminti, Sultan. kullum yana ¢ikin ransa, yasha komawa gefe ya yi kukansa yadda ransa ke so, ya dawo ya share hawayensa. Ana hakanne akayiwa Amina Sata a shago, aka likawa Nawfal wai shi ya saci kudin,: Wannan abu ya yi wa Nasreen ciwo. Amma sai Nawfal ya nuna mata babu kemai jarabawa ce, Haka ta kore su a ~ gaban jama’a ta kunyata su, ta dora masu laifin sata. Suka fice titi Nasreen tana bara ana ba su kudi a nan ne suke samun na cin abinci, Nawfal ya dube ta zaune a gefen titi ya ce, “Nasreen dole mu san abin yi, bara alamun mutuwar zuciya ce da ke addabanmu ‘ya’yan hausa, bana son mu kasance daga cikin su. Gara mu bemi na kanmu Zan dinga zuwa wajen mai garuwan nan yana bani ina siyar masa sai ya bani wani abu. Ni yanzu makwancin mu yafi damuna. . Na gaji da bin kangon nan da muke yi.�? Nasreen ta sharce hawayenta ta ce, “Nawfal ina son ganin Deedi, bansan halin da yake ciki ba, Nawfal mu koma gida don Allah.�? Girgiza kansa ya yi, “Gara mu mutu a nan da mu koma gida. Nasreen Umma tana neman rayuwarki ne, idan ta kashe min ke wa zan gani inji sanyi a raina? Wacce irin rayuwe zanyi ni kadai babu ‘yar uwar haihuwata? Nasreen har yanzu na kasa yafewa Umma da ta makantar min da idanunki. Na kasa ganin farinta. Don haka kiyi haKuri da talaucin mu, mu nemi-na kanmu. Zanje wani gida mai zaure mai kyau inroka mu dinga kwana a ciki kin ji?�? Kanta kawai ta daga ba tare da ta iya furta komai ba. Zazzabi ne mai zafi ya rufeta sai karkarwa take yi. Hankalin Nawfal ya kai matuKa a tashi dole ya fice ya nemo karare ya kunna mata, sannan ya nufi Chemist da ragowar �? kudin hannunsa ya siya mata magani. Wasawasa sai da Nasreen ta koma sai andagata ankwantar. Kullum magana daya take yi masa ya kaita wajen Deedinta kada ta mutu. Shi kuma ya yi alKawarin babu inda za su sake komawa a gidan nan.�? Kasancewarsa mutum mai zuciya. Haka kuma yana da lambar Sultan akansa da ta Abba, amma yaki barin ma tasan da hakan, domin yasan za ta matsa sai an je an kira su, shi kuwa roKon Allah yake yi Allah ya Kara nesanta
Su. Sultan cikin ikon Allah ya dinga samun daukaka da kuma Karin girma akai akai wanda hankalinsa yafi kwanciya da yake nesa da mahaifiyarsa, sai dai Nasreen da take nan daram kamar yau ya fara sonta. Ya Kara kyau da haske, sai “yar rama da ya yi: Baya son magana idan ba ta kama dole ba. Haka baya ziyartar gida aikin kawai yasa a gaba. Katon gidansa babu abinda babu na more rayuwa, haka gidansa cike yake da ‘yan sanda masu kare lafiyarsa. Ya zama aiki yake yi babu ji babu gani, wanda a yanzu ya hau kujerar G Wannan girma ba shi kadai ya shafa ba, hatta iyayensa da ke garin Kaduna sai da abin ya zame masu abin alfahari, a dan shekarunsa ya taka matsayin da ba kowa yake da wannan arzikin ba. Farin jininsa a jini yake, ya zama dan gaban goshi a cikin ‘yan sanda. Ganinsa wahala yake yiwa jama’a haka bai cika zama a gida ba, saboda ayyuka. Da zuwansa ya kawo sauye-sauye na ban mamaki. Ya zuwa yanzu ya gama fahimtar ya rasa Nasreen har abada. Sai dai kuma ya fara samun surutai a gidajen jaridu akan rashin matarsa. Tun abin baya damunsa har ya koma yana daga masa hankali. Babban burinsa. Nasreen ta dawo ta shiga dakinta. Yau a wurin aiki ya kwana, saboda wasu mahimman tattaunawa da suke yi da IG. Yana dawowa gida daya daga cikin ‘yan sandansa ya sanar masa da zuwan iyayensa. Haka kawai ya ji baya farin ciki da zuwansu. Yana shigowa ya ga mahaifinsa yana zaune yana karanta Jarida. Farin cikin ganin mahaifinsa yasa shi murmushi. Frij ya nufa ya fincike hancin Coke ya dora a cikinsa, tare da _ furta, “Alhamdulillahi. Abbana na ji dadin zuwanka.�? A Kasa ya zauna sai ka ce ba shi ba ne idan zai fita yake shan, mur, ana biye da shi kamar wani sarki, Umma ta fito ita da wata yarinya, kallo daya ya yi mata yaji wani irin tsanarta a ransa. Kai da ganinta ka ga mara tarbiyya.
Sama-sama suka gaisa, kafin Abbansa ya dube shi ya ce, “Sultan baka da alamar aure. Baka san hakan tonon asirinka bane? Duniya tana kallon kowane shige da ficenka. Girma ne ya same ka tun kana da Kananun shekarunka. Don haka mahaifiyarka ta samo maka mata har andaura auren da kanmu muka kawo maka. Nasan kai mai biyayya ne, baka taba ce min a’a ba. Me kika ce Hajiya?�? . Sultan. ya .kafe mahaifinsa da idanu, sai yanzu ya kula da wata rama da ya yi abin akwai al’ajabi. Haka ya cika da mamakin yadda mahaifinsa zai amincewa mahaifiyarsa wajen nema masa mata. A sanin da ya yi wa mahaifinsa mutum ne mai Zafi, ba ya son wargi, haka ummansa tana shakkarsa duk kuwa_ irin masifarta. Yau ga shi Abba yana mata magana cike da ladabi. Yau ga Abba yana bin dukkan shawararta. Haka ya nuna alamun tsoronta da yake ji Karara. Sake zuba masu ido ya yi yana son ganin Karshen wasan, Umma ta dubi yarinyar da fuskar nan ta sha kwalliya ta ce, ‘“Kaima Alhaji sai ka bari ingabatar da ita. Wannan dai sunanta Zakiyya, ita ce ‘yar Hajiya Ladidi da na taba yi maka maganarta. Ba ta da matsala za ka ji dadin zama da ita. Bana son Kananan maganganu don haka nake son ka riketa da amana, ka fito da ita duniya ta santa. Ko ya kace Alhaji?�? Abba yana magana kamar jikinsa har rawa yake yi, idan har ba idanunsa ne suke yi masa gizo ba. “Haka ne Hajiya. Ai shi Babana bai taba yi min musu ba. Allah ya yi maka albarka.�? Bai iya amsawa ba, sai idanu da yake bin kowannensu da shi. Suna nan zaune mai aikinsa ya kawo masu abinci, kowa ya zuba yana ci, amma Sultan ya kasa kai koda cokali daya bakinsa. Zama ya yi kawai yana zare safar Kafarsa, ya mike yana fadin zai dan watsa ruwa. Umma ta Kyafta mata idanu Abba sai faman yashe bakinsa yake yi. Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?�? Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.�? Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.�? Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,


*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*



CHAPTER 9



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*




A JIYA MUN TSAYA

Sultan yana shiga yaga mutum ta biyo shi, bai ce mata komai ba, ya rage kayan jikinsa ya shige bandaki. Abin mamaki ita ma ta _ shigo tana dubansa, “Ko dai zan tayaka ne?�? Ya zaro idanunsa yana dubanta, “Za ki taya ni fa kika ce? Wai ke ba amarya ba ce? Don Allah malama fice min a daki ki bari sai na nemeki tukun.�? Haka ta fice jikinta babu Kwari. Tunda Zakiyya ta sake dora idanunta akan Sultan sai ta ji kamar duk duniya babu namiji mai kyansa da tsarinsa. Haka unifoam yana matuKar yi masa kyau. Ko a yanzu din ji take kamar ta rungume shi. Haka dai ta yi hakuri har su Abba suka shirya komawa. Abin mamaki Abba ke rikewa Umma Jakarta. Gabansa ya tsananta faduwa. Hakan ke nuna masa barinsa gidansu gidan ya sake lalacewa ne ya Kazance. Da Kyar ya samu ya jawo Abbansa gefe yana kallonsa da rinannun idanunsa, “Abba meke faruwa ne? Abba me ke damunka haka duk ka rame? Abba Allah ba zai Kyale ni ba idan har na bari wani abu ya same ka.�? Sultan ya Karashe maganarsa kamar zai sawa Abbansa kuka. Abba ya sude bakinsa da ya bushe ya ce, “Sultan ka kwantar da hankalinka babu abinda ke damuna. Sai dai bansan me yasa ba, nake tsoron mahaifiyarku. Yanzu ba na iya yi mata musu. Abubuwa kala-kala babu wanda ba ta yi. Kawai kaci gaba da taya nida addu’a Allah yasa ~ inciye jarabawata. Sai kuma maganar Nasreen,

ZAMU TASHI

Sultan har yanzu babu labarinsu. Wannan ciwon na tabbata da shi zan koma ga Mahaliccina.�? Hawayen da Abba yake Kokarin dannewa sai da suka zubo, ya sa hannu da sauri ya goge kamar mai tsoron wani ya gani. Sultan ya kasa cewa uffan har Abban ya gaji ya juya wurin motarsu da ‘yan, sanda za su jagoranci tafiyar tasu, saboda yanayin hanyar. Hannu kawai ya iya daga masu har suka fice. Cikin sauri-sauri ya shirya cikin

kakinsa ya fito hannunsa dauke da wayoyl. �? Zakiyya ta yi narainarai da idanu tana dubansa, “Ka zauna a gida ma.. Hannu ya daga mata ya wuce abinsa. Abinda bai sani ba, yana fita Zakiyya ta gayyato ma’aikatan jaridu tasa aka dauke ta hotuna, tayi bayani dalla-dalla a matsayinta na matarsa. Ta kuma cewa a daina cewa mijinta bai da mata ita ge matarsa, Kwanan Sultan biyu bai leKa gidansa ba, ita kuwa ko a jikinta. Haka tana sane da ya sallami mai girkin gidansa kasancewarsa namijl, amma ko sau daya ba ta taba Sa tsintsiya ta share ko da falo ba. Haka ruwan fridge ya dinga zuba yana shiga KarKashin kafet din, nan da nan dakin ya dauki wari. Kitchen kuwa wasu abubuwan da ba a sanya a fridge ba, har sun lalace suna wari. Ko a jikinta, ita dai idan ta samu ta ci abinda take son Ci, Za ta nemi wuri a falo ta sa film din batsa tana kallo. Gabadaya Sultan ya mance da Allah ya yi ruwan wata Zakiyya a cikin gidansa. Tunanin halin da mahaifinsa yake ciki ya fi komai daga masa hankali. Kai tsaye ya gane mahaifiyarsa ta yi amfani da bokayen tsubbu domin cimma burinta. Mahaifiyarsa ta yi nisan da ba ta jin kira, �? tayi nisan da take mance girman Aljannah, da kuma abubuwan da ya kamata ta bi domin shigarta Aljannah. Gabansa ne ya fadi da Karfi da ya tuna da Kannansa da ke cikin gidan, yana —tsoron lalacewar tasu tarbiyyar. Ya zama dole ya je idan har abin da matsala ya kwashe su daga gabanta. Yana tsoron bakin da Umma take yi wa ‘ya’yan wasu ya faru akan ‘ya’yanta. Duk yaron da ta gani dan iska ne, nata ne masu kirki. Kowa ta gani mazinaci ne, nata ne masu kare kansu daga sharrin zina, kowa ta gani aron addininta suka yi,
nata ne wadanda suke da asali a cikin addini. Ta ya ya Allah ba zai aiko da jarabawa cikin gidansu ba? Ta ya ya Zakiyya ba za ta zamo matarsa ba? A bayyane ya yi magana, “Ya Allah! Ban kasance mazinaci ba, kada ka jarabceni da rayuwa da mazinaciya. Allah ban taba jayayya da yinka ba, kada ka jarabceni da_laifin mahaifiyata. Allah mahaifina bai ° kasance azzalumi ba, kada ka jarabce shi da macen da za ta zalunce shi. Allah ka warware mana wannan matsalar da ke tunkaro mu, ka kare min Kannena a duk inda suke. Allah ka bayyana min Nasreen da dan uwanta cikin Koshin lafiya.�? Zare rigarsa ya yi ya kama hanyar gidansa jikinsa a sanyaye. Har a lokacin babu dan sandan da ya gaya masa cewa Zakiyya ta gayyato ‘yan jarida. Yana sa Kafafunsa a cikin gidansa hankalinsa ya ninku a tashi. Ransa ya yi mugun baci, ya dubeta rai a Bace ya ce, “Ke ba ki da hankali ne? So kike ki mayar min da gida dafidalin wari? Ko bola kika samu ne? Ki tashi ki gyara gidan nan tun kafin bacin raina ya sauka akanki.�? Jikinta yana rawa_ saboda_tsoron yanayin da taga Sultan, ta wuce kitchen domin dauko tsintsiya. A lokacinne ya bayyana a kitchen din. Ya ma kasa magana saboda azabar warin da ya ziyarci hancinsa. Dole ya sa hannu ya toshe hancinsa. Haka ya koma hankalinsa a tashe. Sultan ya tsani Kazanta fiye da tunanin mutum, dakinsa ya koma ya kwanta yana kallon sama, cikin tunanin da shi kansa bai san ko na menene ba. Nazari yake yi ta yadda za a yi ya iya rayuwa da Zakiyya a matsayin mata. Yana nan kwance bai motsa ba, ta gyara dakunan sama-sama ta je ta sheKa wanka ta antaya maganin da uwarta ta ba ta, sannan ta Kara shiga ruwan zafi, kamar yadda Hajiya Ladidi ta karanta mata, domin aikin da aka yi mata don ta koma budurwa har yanzu tana dan jinsa. Ita kanta yadda aka dinke ta abin yana bata tsoro, haka tana shakkar zai iya ganewa cewar ita ba budurwa ba ce, idan hakan ya faru tana da tabbacin Sultan korar kare zai yi mata. Shi kuwa wanka ya shiga ya fito daure da tawul yana tsane ruwan jikinsa. Ta shigo dakin babu ko sallama, kallo daya ya yi mata ya dauke kansa gabansa yana fadiwa. Babu laifi yarinyar tana da kalar tata kyan, sai rashin kamun kai da ke dawainiya da ita. Jikinsa ta Karaso tasa hannu ta rungume shi. Kamshin maganin da ta yi amfani da shi, ya yi ta dawainiya da shi, don haka ya fara mayar mata da martani, da taimakon tsaftace jikinta da ta yi. Ba shi ya farka ba, sai da asubahi. Ware idanunsa ya yi yana duba irin barnar da ya yi wa ‘yar mutane. Mamakin samunta a budurwa yafi komai tsaya masa a rai, domin yadda yaga bai taya taba, ita ta fara kawo kanta yasan da matsala. Haka wannan budurcin da ya samu ya sanya ya Kara ganinta da girma da mutunci a idanunsa. Gabadaya zanen gadonsu ya lalace da uban jini. Tana nan kwance kamar kayan wanki tana shakar barcinta. Mamaki ya sa ya kafe ta da ido, yaushe za a yi wa mace hakan ta kwantar da hankalinta? A hankali ya zame kansa ya shiga bandaki ya tsaftace jikinsa, kafin ya sa hannu ya tasheta, tana bude idanu ta fara magana cikin magagi, “Bilal ka rabu da ni barci nake ji.�? Sultan ya zaro idanu yana sake dubanta, “Bilal kuma? Waye Bilal?�? Ware idanunta ta yi gabanta ya fadi da Karfi, sai yanzu ta tuna abinda ya faru, don haka ta fara raki, “Wash! Don Allah ka taimaka min ba zan itya tashi ba.�? Sultan dai kallon ta kawai yake yi, haka kuma zai iya makara yin Sallar asuba, don haka yace “Ki yi haKuri Zakiyya zan makara.�? Ya sa kai ya fice abinsa. Yana fita ta mike ta shige bandaki ta gasa jikinta, sannan ta cire zancn gadon ta shimfida masa wani ta sake hayewa gadon tana shaKar barcinta. Babu Sallah bare Salati. Yana dawowa ya dube ta yana tantaman anya ta yi Sallah? Sai kuma ya kau da

Please Login or Register in order to submit comment