Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

hali a nuna mata hotonta amma yaki kallonta, don haka ita za ta bar masa gidansa. Haidar ne ya shigo yana duban mahaifiyarsu shi da Hafsat suka Banbare hannunta da Kyar Abba ya samu yana KoKarin ficewa daga gidan yana fadi a ransa zai yi maganinta. Kawai suka ci karo da Alhaji Mu’azzam! Kallon kallo suka aikawa juna sannan Abba ya dawo da baya suka gaisa babu yabo babu fallasa. Alhaji Mu’azzam. ya gyara zaman babbar rigarsa ya ce, “Anya Alhaji Lukman babu abinda ke damunka? Me yasa kake son mayar da kanka Karamin yaro ne? wanda bashi da ra’ayin kansa? Ta ya ya za ka yi wa Sultan aure wanda mu nan da muke dangin mahaifiyarsa bamu sani ba? Ko kana nufin bamu da hakki akansa ne? Akan ‘ya’yan zina kake son Sauya tsarin gidanka? To idan aure babu albarkar uwa auren nan bai dauru ba.�? Abba ya yi saurin bashi amsa, “A fatawarka ba! Amma ni ne uban yaro kuma na aurar da shi ga diyar da ta dace. Zina kuma babu mai tabbacin wane yana aikata zina, sai idan yana da shaidu, kawo shaidun kuma akwai wahala. Ina yiwa kowa kyakkyawan zato. Kowa a duniyar nan yana da tarin matsala akansa, idan baka zina, kana shan giya, idan baka shan giya kana caca, idan baka aikata dukkan laifukan nan kana aikata mummunar laifi wanda yafi muni, wato shirka, hada Allah da wani. Ban ga dalilin da za ka dinga bin diddigin wani dole sai ka gano laifinsa ba. Kowa ya ji da tarin matsalarsa. Hajiya Salma kuma ta bi bayanka zan zo da abinda take buKkata, matar Sultan kuma bata isa ta santa ba, har sai ta tare, bare ta zagaya ta kashe masa auren. Ruwanku ne Hafsat da Haidar subi bayanta, sai dai ku sani irin naku rashin hankalin yafi kama da na uwar da ta haifeku, don haka binta zai fi burgeni fiye da zamanku a nan.�? Ya sa kai ya fice a fusace. Nasreen tasa kuka, wanda ya jawo hankalin Alhaji Mu’azzam kansu. Wani irin faduwar gaba ya tsinci kansa da shi wanda bai taba jin irinsa ba. Bai taba ganin yaran ba, saboda irin tsanar da ya yi masu, sai yau da ya hada idanu da su. Bakinsa ya mutu murus, dole ya nemi wuri ya zauna, yana kallon yadda Hajiya Salma take kuka, Duk wanda ya san meke faruwa zai gane kukan korarta da Alhaji ya yi take yi. “Salma ki yi haKuri ki share hawayenki, ki zauna da ‘ya’yanki, Kada ki yarda akan ‘yar Karamar matsala ki baro dakin mijinki. Ni zan san matakin dauka haka zan lalubo inji wacce yarinya ce ya aura ma danki, Ki kwanter da hankalinki.�?


*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*



CHAPTER 6



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*


A JIYA MUN TSAYA

tsauri. Haka a KarKashin wannan auren da kike son a raba zaki shiga Aljannah. Haka ina son ki zuba ido ki gani, tun aduniya Allah zai saka maki, akan mijinki idan har da gaske yana zaluntarki. Shi Allah baya barin azzalumi. Kada zuciyarki ta yi rauni kawai dan namiji yana cuzguna maki, ki dauka irin taki jarabawar kenan. Idan Allah ya dubi zuciyarki ya tabbatar a wadace take da imani, da son addininsa, sai shi kuma ya saka maki. Kada ki ce wai sai kin ji dadi sannan zaki yabawa addinin musulunci.�? A lokacin kuma aka shigo da Bala mijin Karima. A Kasa yasa ya zauna yana aika masa da mugun kallo mai cike da tsana. “Ka san wannan ko?�? Ya nuna masa Karima da hannu. “Yallabai na santa matata ce, shekarun mu uku da aure da ita.�? Sultan ya dinga jinjina yayi wuri ta fara fuskantar matsala, “Ta ce tana son a raba aurenku, saboda kana dukanta, don haka zan tura ku kotu, daga nan zaka amshi irin naka hukuncin.�?

ZAMU TASHI

Bala ya shiga yayyanka idanu, “Yallabai a yi min afuwa, sharrin shaidan ne ba zan sake dukan ta ba.�? Sultan da zuciyarsa ke zafi, ya dubi Copral Ya ce, “Na tsani mutum ya aikata laifi da gangar yace sharrin shaidanne. Har yaushe musulmin Kwarai zai dinga barin shaidan yana shigowa cikin rayuwarsa, yana wanzar masa da sharri a cikin gidansa? Don Allah dauke min shi ka hukunta min shi har sai ya bani tabbacin shi ne shaidanin.�? Bala ya gigice yana bayar da hakuri hakan yasa Sultan sake watsa idanunsa akansa, “Gaya min sharrinka ne yasa kake dukan matarka, kake yi mata gori akan ta aro addininka ko kuwa har yanzu na shaidan ne?�? : Bala ya ce, “Yallabai sharrina ne kuma nayi kuskure.�? Sultan ya ajiye biro yana dubansu, “Malam Bala musulunci bai yarda miji ya dinga dukar matarsa ba, domin ba ankawo maka ita bane domin ka dinga dukanta ba. Musulunci bai yarda da gori akan komai ba, bare har akai ga gori akan babban abu, wato addini.

Musulunci bai yarda mumini ya dinga tauye hakkin iyalansa ba. Kai hakkin wani ma a waje haramun ne bare akai ga hakkin matarka. Yanzu kasa matarka ta hada mu gaba daya tana yi mana kudin goro, tana kallon malaminka da ya musuluntar da ita a matsayin mugu, tana kallon iyayenka da ‘yan uwanka a matsayin mugaye. Daga Karshe sai ta ji ta tsani musulunci tana neman ta koma wancan addinin da ka sameta a cikinsa. Bayan kai da kaje za ka aureta baka ji lokacin da malaminka ya ce hakkinka ne ka yi mata duka, da gori ba. Malam Bala ka ji tsoron Allah. Ka sani sai Allah ya saka mata, kamun Allah kuma ba.irin kamun mu bane mu hukuma. Kurkun Allah ba irin namu kurkun bane. Ka kiyaye abubuwan nan, za ka fi Karfin gidanka, cin matarka, shanta, rashin lafiyarta kaucewa gaya mata munanan kalamai. Domin kalamai wannan idan kana gaya mata su marasa dadi zaka wayi gari kalamanka su kasheta. Idan kuma kaima jahili ne ba ka san ilimin addinin musulunci ba, ka dauko ‘yar jama’a ka aurota kana yi mata koyarwa irin na jahilai don Allah kaje ka nemi ilimin addinin nan, kada kayi mana asarar mutum daya daga cikin musulunci. Ka �? ka kare hakkin matarka, da mutuncinta. Ina son Copral ka tafi da su, a kawo min malamin da ya daura aurecn da kuma wanda ya musuluntar da ita. “Ni Office dina idan anzo irin wannan case din sai na bi diddigi naji dalilin da yasa ake hakan. Idan mutum ya yi alKawarin gyarawa bai gyara ba, ina da hukunci kala-kala da zai sa mutum ya gyara ba don yana so ba. Bana daukar shirme. Haka bana barin a ci mutuncin mata! Domin ita mace ta wuce komai, sai da ita za ka sami natsuwa, ita ce ta dauki cikinka tana amai, tana kasa barci cikin dare saboda laulayi, a hakan za ta girka maka abinci, ta kai maka ruwan wanka. Tana renon cikinka tana renonka. Idan ta tashi haihuwa, ta kai sati tana naKuda. Wata ko nan take mutuwa, ko shekara ba za a yi ba, za ka Karo wata. Idan ta tsallake ta Haifa, ta shayar ta lura da lafiyarsa. Idan bai da lafiya ta zauna cikin dare tana nemo dabara, kai kuma kana can kana barci. Ta wanke masa kaya ta wanke naka. Mace dai ita ta kawoka duniya ita ta reneka. Shi ne don rashin hankali ka rasa abin wulakantawa sai ‘ya mace? Ka tambaya wane ne Abdullahi Lukman! Bana daukar irin wannan shirman.�? Jikin Bala da Karima ya yi matuar sanyi, hakika D.P.O dinnan na daban ne, yasan hakkin dan adam. Ya dubi Nasreen yaga hawaye shimfide a fuskarta. Hankalinsa ya tashi don haka ya taso ya dawo kusa da ita, yasa yatsa yana dauke hawayen. “Nasreen menene? Waye ya bata maki?�? Fuskarta dauke da murmushi ta ce, “Babu wanda ya bata min. Ina godewa Allah ne da nayi sa’an dan uwan mahaifiya mai sanin ya kamata. Allah kadai yasan wahalar da mahaifiyata tasha kafin ta kawo ni gidan duniya. Allah ka sakawa mahaifiyata. Allah kasa mahaifina bai wulaKanta min ita ba. Daga Karshe Allah ya saka maka da renonmu da kayi tun muna cikin tsumma.�? Sultan ya mike ya dago ta, Zuciyarsa take gaya masa ya rungumeta, Don haka ya mayar da ita Kirjinsa ya rufe da hannayensa, Sannu a hankali natsuwa ta ratsa su, Nasreen ta sake lafewa a Kirjinsa tana sakin ajiyar zuciya. Da kansa ya ga dacewar ya janyeta, ya kamo hannunta suka fice. Mansur da ya gama kallon hotunan Nasreen ya zuKo tabarsa yana fesarwa a fuskar su Hajiya Ladidi. Hajiya Salma ta Kufula don ta tsané rashin tarbiyya, za ta yi magana, Hajiya Ladidi ta matse mata hannu, dole tayi shiru suna ci gaba da kallonsa, “Hajiya wannan yarinyar ta hadu. Soyayyar Karya kuke son in nuna mata, amma a zahirin gaskiya ni sonta nake yi da yaske. Kuma Wallahi! Wallahi!! Sai na aure ta da Karfin tsiya. Wannan ai kalata ce. Hajitya ku bar kudinku wannan da kudina zan aureta.�? Hajiya Salma da Hajiya Ladidi suka yi ‘murmushin jin dadi. Abu kamar wasa soyayyar Nasreen ya mamaye ko ina na zuciyar Mansur, wanda har ya kasa hakuri ya shirya cikin shigar kamala ya je gidan da sunan hira. . A falo Hajiya Salma ta tare shi, ta kuma turo Naareen. Gaba daya ya shagala wajen kallonta, kwafsi daya ne, matsalar idanu, amma shi sannan babu shi a zuciyarsa, babban burinsa ya mallaketa ko ta halin KaKa.””Wanene kai? Me kake nema a wurina?�? Sai da ya shafi sajensa kafin ‘ya ce, “Sunana Mansur. Sonki nake yi, kuma Wallahi sai na aureki.�? “Ni kuma bana sonka, ka tafi tun kafin Abbana ya zo ya sameka anan.”Www.bankinhausanovels.com.ng Mansur ya mike yana tunkarota. A lokacin Abba da Sultan suka sawo kai. Da Karfi Abba ya ce, “Innalillahi wa inna ilaihirraji un.�? Wani irin jiri ya nemi ya kwashe shi ya riKe jikin bango, yana sake watsa idanunsa akan Mansur. Tuni Nasreen ta mike a gigice tana cewa, “Abba Wallahi ban san shi ba, ban taba jin ko muryarsa ba, Umma ce ta ce dole sai na zo, amma ban san shi ba. Ka yarda da ni Abba ba zan yi maka, Karya ba. Ta sake rushewa da kuka.�? _ Shi kuwa Sultan ya rasa dalilin da yake jin zai iya shake Mansur ya mutu har lahira. Don hakane ya wuce Abba ya shake shi, wanda duk Karfi irin na Mansur ya kasa Kwatar kansa daga irin rikon da Sultan ya yi masa. Idanunsa suka firfito waje. Umma da su Hafsat suka rugo a guje sakamakon jin Kakarin Mansur, Umma ce ta Kwace shi, sakamakon marin da ta dauke Sultan da shi, tana wani irin huci, “Sake shi mara mutunci kawai, Ina ruwanka idan saurayi ya zo wurinta? Ko za ka hanata aure ne? lyye Nace aure za ka hana tayi Nine nan nayi masa izini tunda ya ce yana sonta da aure, ai ba jiKata zamu yi mu sha ba, dole za ta yi aure.�? Abba dai yana tsaye Kafafunsa duk sun yi sanyi. Sai yanzu ya sami ikon yin magana, “Kai zo ka fice min daga gida tun kafin ka yi nadamar haukan da kake shirin yi. Idan na sake ganinka a gidana zan yi maka mafi munin wulakanci. Nasreen share hawayenki baki da laifi. Laifin wancan ne, kuma zan dau mataki.�? Ya fada yana nuna Umma da yatsa. Mansur har ya kai bakin Kofa ya waiwayo ya kafe Nasreen da idanu, “Ina nan dawowa in aureki matata. Zan aureki ko da kuwa wannan ne abu na Karshe da zan yi in mutu.�? Sultan ya nufo shi, ya riKe wuyan rigarsa, “Za ka mutu kuwa! Idan wannan bai zama abu na Karshe da za ka yi ka mutu ba, zai zama ganganci na Karshe da za ka yi ka bakunci lahirar. Idan ka san da gaske kai mara kunya ne, anjima ba sai gobe ba, ka sake taka Kafafunka a Kofar gidan nan. Fice!�? Ya tunkuda Kyayarsa zuwa waje. Ya koma kawai ya zauna a kujera ya yi tagumi yana kallon mahaifiyarsa. Abba ya nuna ta da yatsa ya ce, “Ke ce ajalina Salma. Idan na fadi na mutu ke ce sila.�? Hajiya Salma ta ce, “Oh ni kada ka sa min sharrin kisa. Yarinya dai dole za ta yi aure. Kai kuma lafiya kake kallona kamar tsohon maye? Ko dukana nima za ka yi ne?�? Mikewa ya yi kamar zai fita sai ya ji muryar Haidar yana cewa, “Gaskiya Abba ka tsani Umma da yawa, idan ba haka ba, menene a ciki don Nasreen ta yi soyayya? Duk kuka tashi hankalinku kamar kun kama ta da kwarto? Kuma…�? Sultan ya juyo ya watsa masa idanu tare da mika dan yatsansa alamun gargadi. Hakan yasa Haidar hadiye kalamansa, domin bai san cewa bai fita daga falon ba, da babu abinda zai sa shi tofawa. Sultan ya kama hannun Abbansa suka fice kawai. Shi dai Abba a ranar ko barcin kirki bai yi ba, wani tunani ne a cikin zuciyarsa da yake tunanin irin kuskuren da zai iya tafkawa, inhar ya zubawa Umma idanu ta Sauya masa tsarinsa a kan yaran. Haka acan dakin Sultan ya kasa barci, sai tunani fal cikinsa. Dole ya koma dakin Nasreen tana kwance cikin bargo, yasa hannu ya yaye bargon. Abinda ya ganine yasa shi saurin rufeta yana ambaton dukkan addu’ar kariya daga fadawa _ tarkon shaidan. Motsinta ya ji ta tashi ashe ba tayi barci ba, tana KoKarin yaye bargon ta rungume shi, ya dakatar da ita ta ta hanyar rike bargon. Sai a lokacin ta tuna da irin kayan da ke jikinta, don haka ta shiga laluben hijabinta. Shi ya dauko ya taimaka mata tasa. “Nasreen! Me yasa kika fito wajen dan iskan nan? Don Allah Nasreen ki taimakeni inrike amanar da mahaifiyarki ta bani akanku. Na yi mata alKawarin zan iya, ki taimake ni in mutu ba tare da antambayeni yadda na rike amanarku ba. Na kasa barci Nasreen, ina da abubuwan ci gaba da nasa a gabana, amma saboda ku na kasa aikata komai, ina son in aurar da ke, Nawfal ya kama aikinsa, sai insamu nima inKarasa ayyukana. Za ki taimaka min nima burikan nan nawa su cika?�? A gigice take magana, “Wallahi Dee ban san shi ba, ka yarda da ni. Ina dakina Anti Hafsat tazo ta yi min jagora muka je falon. Ya ce yana sona, nace bana sonsa. Ajiyar zuciya ya Kwace masa, yaso a daren ya shiga dakin Hafsat, sai kuma ya canza tunani. “Allah ya yi maki albarka koma ki kwanta kiyi barci.�? Babu musu ta koma ta kwanta, amma kuma bata sakar masa hannun ba, Zuba mata idanu ya yi yana jin wasu abubuwa suna sake canza mazauni a cikin jikinsa. Yana jin_kansa kamar ba shi ba, Dayan hannunsa yasa ya mayar da gashin kanta baya da suke Kokarin | rufe mata fuska. A hankali ya matso sosai ya bata fake a goshi. Wannan lamari yasa Nasreen nutsewa wata duniya. Wanda har bata san lokacin da ya zare hannunsa ya fice daga dakin ba. Dakin Nawfal ya leKa ya same shi zaune akan dadduma yana Sallah. Ibadan yaran yana burge shi, ya sake. gode. wa Allah da, dukkan abubuwan da ya dora su akai babu wanda suka kuskure masa; A hankali yayi maganar da ya ratsa kunnuwan Nawfal. Nawfal kada ka mance ni a cikin addu’arka. Haka, kada ka mance da mahaifiyarka.�? Ya sa kai ya wuce, Dakin Hafsat haka yake yana da yawan leKa Kannansa domin tabbatar da lafiya lau suke kwance. Yana lekawa ya sameta zaune tana waya. Tana ganinsa ta katse wayar tana zare idanu, “Da wa kike waya? Ba zaki bani amsa ba!�? Jikinta na rawa tace “Abokin karatuna ne,�? Sultan ya zaro ido, “Abokin karatunki a wannan daren? Haba Hafsat! A wannan lokacin da ya kamata ace kina ganawa da Mahaliccinki? Ance ki fito da miji ayi maki aure, kin ce baki‘da samari. Amma yanzu gashi kina waya da garjejen Kato ko? Ki kiyaye, ki kama mutuncin kanki, watarana ke uwa ce.�? Juyawa ya yi abinsa ya fice. so Sultan yana Office ya sami kira daga abokansa, sun hadu za su fara meeting. Da sauri ya Karasa dukkan abubuwan da ke gabansa sannan ya kama hanya. Gaba dayan su sun sami isowa shine na Karshe. Tajuddeen Abdulsalam jarumin littafin (Kowa ya kwana laftya), Haisam �? Hayat, Jarumin littafin (Zuciya), Aslaf Mai nasara Jarumin littafin (Sir) Mahbub Muhd Daura, Jarumin littafin (Mafarin lamarin), Ashmaan Ashraf Jarumin littafin (Akaran kaina) Sai kuma Soja, Khamis § Idris Jarumin littafin (Akaran kaina), ga kuma Al-ameen Rabi’u, jinin Sarauta jikan sarki, Jarumin (Akwai_ lokaci). Dukkansu suna zaune kowa da abinda yake yi. Sultan ya basu hannu yana murmushi, “Ga -ni kuma, jarumin Rubutacciyya! Na gaida Karfin Zumuci irin na ‘yar mutan Borno, hakika tayi namijin KoKari da bata barmu mun watse ba, da ba haka ba, Ashmaan shi ne mutum na farko da zai fara datse mana zumuncin nan.�? Dukkansu suka yi murmushi_ sannan Mahbub ya bashi amsa, “Idan Ashmaan bai kashe zumunci ba, ai kai sarkin watsar da zumunci, za ka watsar da komai. Kai dai kawai Allah ya sakawa ‘yar mutan Borno, ita ta riKe mu ta dage lya lyawarta da ba haka ba, da tuni kanmu ya rabu.�? Dukkansu suna ji da kansu, kowa ya ci ya ture. Haka ga -dukkan alamu suna_ cikin kwanctyar hankali suna samun kulawa daga matan su. “Tuzuru bude mana taro da addu’a Kila sanadiyyar hakan ka samu ka shiga daga ciki.�? Aslaf yake tsokanar Sultan. Murmushin ya _ yi sannan ya yi addu’a mai tsawo. Suka shafa. Wannan taron gaba dayansa akan Sultan akayi shi, saboda shi ya gayyato su. Don haka ya fara magana, “Da farko dai andaura min aure. Sai dai bana son doguwar magana, ko Korafi, Abba ne ya daura auren, ban santa ba, ban taba ganinta ba, yanzu haka wai yana jiran ne ta gama karatu ayi bikin tarewa. Ban wani damu ba, domin bani da budurwa, hakan ke nuni da ina da bakin jini Irin na wannan yaran”�? Ya nuna Mahbub da hannu, duk suka yi murmushi. a hakan sai da suka yi korafin meyasa tun a lokacin bai gaya masu ba? Share su ya yi kawai ya ci gaba, “Ina da babban Case a hannuna na kisan kai, Case din akwai buKatar natsuwa da kuma sanya hankali a cikinsa: Mahaifiyar Nasrecn nake son sanin waye ya kasheta tsawon shekaru goma sha shida? Me yasa aka kasheta? Ta bani wani littafi da wasu hotuna, suna cikin wannan files din. Ban taba budewa ba, daman burina inkammala da kulawa da su, sannan insan,abin yi. Duk wanda ya kashe ta babu shakka ya yi kisan nan ne saboda gudun kada ta tona masa asiri, nayi alkawarin idan mahaifina ne mai kisan nan, saina daukar mata fansa, Sai kuma Nasreen da aka watsa wa guba aka makantar min da ita.�? Tajuddeen ya fara magana, ““Wannan case din case ne mai girma, musamman na kisan nan. Haka duk wanda ya yi kisan bai san Nasreen da Nawfal suna nan a raye ba, da sai sun nemi kashe su. Wadannan abubuwan da ke hannunka za su tabbatar mana da komai. Don haka zamu yi lya yin mu muga abinda Allah zai yi. File din kuma za ka iya bani, ko kuma ka ba Mahbub, ko Ashmaan. Sai mu fara bincike. Abinda binciken mu ya bamu sai mu sake dawowa ayi meeting ko ya kuka gani? Dukkansu suka yi na’am da wannan shawarar. Al-ameen ya dube su, “Maganar idanun Nasreen, zan dauki nauyin fita da ita waje, ina da wani aboki da ya Kware da aiki akan irin wannan. Kafin nan zan fara bata kulawa a Asibitina. Dukkansu suka ce basu amince ba, sai kowa ya bada gudumawarsa a kan samun lafiyar Nasreen. Sultan ya rasa bakin magana sai duban su kawai yake yi. Da ace haka abokai suke da hadin kai tabbas da duniyar ma gaba daya ta zama abar sha’awa. Haka aka tashi taron Sultan kuma ya damka komai a hannun Barrister Tajuddeen, ba tare da ya bude ko shafi daya ba. Mahbub ‘yan sandansa suka bude masa mota, haka ma Sultan sauran kuma duk suka ja abinsu suka bace bat! Sultan yana isowa gida, ya watsa ruwa kafin ya iso falo inda mahaifinsa ke zaune. Bayan ya gaishe shi ne, yake gaya masa yadda suka yi da abokansa, daga Karshe ya rufe maganar da fadin za a yi wa Nasreen aiki a idanu, abokan suka dauki nauyi. Wannan magana da Hajiya Salma da ke shirin shigowa falon ta ji, shi ya tashi hankalinta taja da baya ta koma. Ko tambayar mijinta ba tayi_ ba ta dauki gyale. A gidan Hajiya Ladidi taja burki. Tana shiga ta sami Mansur a dakin, da alamu sun gama sheKe ayarsu da Hajiya Ladidi ne ya fito yana gyara .kwalar riga. Yana ganin . Hajiya Salma ya daure fuska, “Yauwa Hajiya ki gaya mata sai na dauki mataki akan dan nan nata sannan zan koma indauke Nasreen. Narantse da Allah sai na dauketa. Amma kafin nan sai na gama gyarawa danki zama.�? Hankalin Hajiya Salma ya tashi ta ce, nan fa daya. Kada ka kuskura ka taba min lafiyar da. Za ka iya yin komai amma banda taba Sultan. Kuma Wallahi idan ka ce za ka taba shi sai kayi danasani, domin kana ganinsa nan ba Karamin tsayayye bane.�? Mansur ya yi Kwafa, “Na fi ki sanin hakan ni da ya shake ni na nemi sheKawa lahira. Amma duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.�? Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.�? Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.�? . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu �? sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata idanun da bana fatan ta sake kallon wasu zuri’ana da su. Don haka nake son ta bar cikin iyalina kowa ya huta. Na mayar da yarinya makauniya, sai take son ta mayar min da miji da da ‘yan jagoranta.�?


*Idan kina bukatar cigaban wannan littafin na RUBUTACCIYA da wasu guda biyu UMM ADIYYA by aziza Idris gombe da MISBAH by SA'ADATU WAZIRI GOMBE kiyiwa wannan number magana ta WhatsApp 09068032427*

🦚RUBUTACCIYA BOOK 1🦚*



CHAPTER 7



*BY FATIMA IBRAHIM GARBA DAN BORNO*



A JIYA MUN TSAYA

duk da hakan sai na koya masa hankali. Yanzu sauri nake yi zan sake dawowa.�? Ya sa kai ya fice. Gabadaya suka zauna Hajiya Salma tana yi mata kallo cike da Kyama, “Hajiya da ‘ya’yanki da_ girmanki kike irin wannan Kazantar? Gaskiya bana son zina ko alama, ina tsananin Kyamatarta.�? Hajiya Ladidi ta tabe baki ta ce, “Ba gara zinan ba, da irin ta’asar da kike yi a gidan mijinki? Malama ki fada abinda ya kawo ki kawai.�? . Hajiya Salma tayi ajiyar zuciya ta natsu �? sosai, “Kin ga wannan shashashan yana son ya kawo mana matsala. Ina ganin abinda ya kamata kawai ki samo wasu daga cikin ‘yan iskanki su dauke yaran nan su kai su can wani gari mai nisa, su jefar da su. Wai Sultan ne yake son fita da Nasreen waje su gyara mata

Please Login or Register in order to submit comment