Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ya bude kofar fita daga cikin gurin sama suka tashi suka wuce sai gidan su Saheeb.



A garin abuje kuwa.



Su Gaggo ne suka shigo cikin falo kowa sai ya Zauna Saheeb ne ya wuce dakin sa Daddy da Ammi da humaeera sai kallon Gaggo suke sai Gaggo ta dago idanuwan ta tana kallon su zata bude baki kenan.



Sai suka ga Asiya ta shigo da gudu ko sallama babu tayo gurin Gaggo.



Gaggo nayi kewarki sosai wallahi.



Da sauri Gaggo "Tace Asiya ki ce ko mafarki nake?.



Haba dai Gaggo wane irin mafarki kuma to ni ce dai *Asiya yar Gaggo*.



Daddy "yace 'yata da ke da waye kuma ina kika shiga ne?.



Zatayi magana kenan sai gimbiya jiddah ta shigo da sallam.



Assalamu Alaikum.



Amin wa Alaikum sallam.



Amman dan Allah kuyi hakuri wallahi muna tare da ita ne lokacin da ni da ta fito daga cikin gida sai na tambaye ta wani guri sai ta nuna man shine naje tare .



Gaggo "Tace haba dai jiddah ko babu komai kina fada kin tafi da ita.



Gimbiya jiddah "Tace la Ashe Gaggo kin gane ne ni.



Daddy Ammi ku kwantar da hankalin ku nice na dauki Asiya ni dai ba mutum bace.



Daga daddy har Ammi da humaeera sai da suka razana saboda tace ita ba mutum bace.



Daddy "yace kamar ya kuna nufin ita aljana ce?.



Eh Yaya Muhammad Abbas ita aljana ce sunanta gimbiya jiddah yar sarkin aljannu ce cewar Gaggo.



Ikon Allah dama akwai aljannu masu zuwa duniyar mutane?.


Sosai ma gashi ko nazo.



Abba na yace zan dinga zuwa ina duba ta sosai.



Saheeb ne kwan ce saman gado yayi d'aya d'aya yana tunani mafarkin sa da wannan yarinyar Amman har Yanxun bega fuskar ta ba "yace wai ko nayi gamo ne?.......




*Masoyya na dan Allah kuyi mani afuwa wallahi mahaifiya ta ce bata da lfy sunyi asibity*🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻🙏🏻




*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏



*MASOYYA NA INA GODIYA SOSAI DA ADDU, OIN KU ALLAH YA SAKA MU DA ALKHAIRI*
💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻💃🏻




_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE... 7️⃣0️⃣&7️⃣1️⃣


*________________*📚



Wai kai ina ruwan ka ne? Mtss ni wallahi ban son shi shigi fa mutum sai shegen girman kan tsiya mtss tana hararar sa.



Asiya wai baki jin magana ko? Wai ma ba Yayan ki bane eeyyye Allah zan bata maki rai fa to?.



Turo baki tayi tana kallon Gaggo "Tace yo baki ga abun da yake mun ba ne?.



To kiyi hakuri mana *Asiya yar Gaggo* kin ga kuma kawun ki nan yana kallon ki ko baki son nama kaza ne?.



Wallahi ina ci kuma da mukaje can ko Gaggo naman kaza har tashi sama yakeyi.




Jar uba wallahi wannan yarinya ta cika shegen surutun tsiya ga karyar tsiya mtss wallahi har zuciyata ta fara tashi saboda bakin bakin ta.



Kawu na wallahi kayi wa wannan yaron magana dan wallahi Allah be san wace ce *Asiya sarkin tsiwa yar Gaggo* ba kuma ni ko himm!.



Saheeb kayi shiru fa ban son jin wata magana anan gurin kaji ko? Kuma ka shirya zuwa sati mai zuwa za,ayi bikin ka da Asiya da na company insha Allah.



Zaro ido Asiya "Tace wai ni ko wata Asiya ce?.




Ke dai kuwa insha Allah zuwa ranar Jumma, at kuwa.





Cikin tashin hankali Saheeb ya kalle daddy da Ammi da Gaggo yaga fuskar su babu alamar damuwa "yace wai da gaske daddy Aure zaka hada mu da wannan kucakar yarinyar?.



Insha Allah kuwa babu maganar wasa anan guri.



Jiri ya fara gani idanuwan sa kuka kake sukayi jaur ko gani bayayi haka ya tashi ya wuce dakin sa yana maimaita maganar.




Ammi ta kalle Asiya "Tace 'yata zo muje daki muyi siri ko?.



Gaggo taji tausayen sa sosai "Tace wai Yaya Muhammad Abbas ba za,a dai na wannan maganar ba?.



Aa maryam na riga na yanke hukunci babu maganar wasa.



Asiya ta zo gurin Ammi "Tace mama wai ina zamuje ne? .




Da humaeera da Ammi da Asiya suka wuce dakin Ammi.




Bayan Ammi ta Zauna sai ta kalle Asiya "Tace 'yata zo ki zauna kusa gare ni.



Asiya ta Zauna tana kallon dakin "Tace Tabb wallahi wan can duniyar ta fi wannan kyau sosai.



Humaeera sai ta bushe da dariya "Tace aradun Allah kin bani dariya sosai fa.



Aradun Allah da gaske nake kuma ni fa Antyn ki ce ta Murguda mata baki.



Naji dai ai dama ke Anty na ce Amman agurin Yaya Saheeb ba.



Tabb Allah ya sauwake ni dan Allah ki daina mani maganar wan can kucakin to.



Yi hakuri anty Asiya to tana kallon ta.



Yauwa 'yata kana ji ko zamuje gurin gyaran jiki da salon kinji ko?.



Menene salun kuma?.



Hhhh salon aka ce fa.


Yo ina ruwa na da wata salu.



Kina cin naman kaza ko?.



Eh wallahi akwai dadi sosai kuwa.



Yauwa to kin ga da ankai ki gidan ki sai ki taci har sai kin koshi sosai.



Da gaske kike.



Eh mana kuma kina son makarantar boko ko?.




Menene bokoko?.



Saheeb ne Zaune yayi tagume sai tunani mafi ta yake Amman har Yanxun babu wata mafita.




Kai dole nayi hakuri da wannan kadarar tashi yayi ya fita daga cikin dakin.




*Bayan kwan ukku*



Asiya Zaune tana kallon TV sai Saheeb ya sauko daga saman bene can ya hango asiya Zaune tana kallon murmushin mugunta yayi "yace eyye lallai ne yarinyar nan da sauri ya zo gurin TV ya kashe kayan kallon.



Cikin masifa "Tace kan uban can to wallahi baka isa ba ina Zaune ina kallo na sai kazo ka kashe mun kaya.



Saheeb tsaye yayi yana mata kallon wulakanci "yace ke ina wasa da ke ne? Wallahi zanyi ⚽ da ke Allah kuwa yarinya sai rashin kunya eeye.



Murguda baki tayi sannan "Tace wai kai ina ruwan ka da ni ne to nayi rashin kunyar tana Murguda masa baki.




Hhhhh gaskiya inason irin wannan soyayyar na fa shiyasa nake son ayi wannan Auren.



Wata uwar harara ta watsa mata "Tace kanwata Allah zamuyi fada dake fa ni wallahi ban son shi shigi fa mtsss ta wuce dakin Gaggo tana ta famar masifa.



Ashe su Ammi da daddy suna kallon su sai dariya suke sosai daddy ya kalle Ammi "yace wallahi shiyasa nake son suyi Aure dan nasan dole wata rana sai sun shirya sosai.



Wallahi kuwa gashi ma har lokacin yazo sauran kwan biyu fa.



Hakane Allah ya nuna mu lafiya.



Amin ya Allah.




*Washe gari*


Gaggo ce zaune tana kallon Asiya da takeyi mata surutu.



Asiya Yau su Shatu da Rabi zasu zo fa.



Da sauri ta kalle "Tace da gaske kike Gaggo? .



Eh mana insha Allah natura Kamal abokin Saheeb.



Tabe baki tayi "Tace uhm to shikenan ni wallahi ban son shi mutum sai shegen girman kan tsiya mtss kai haba gaskiya naji dadin wannan maganar ki Gaggo Allah sarki Shatu da Rabi.




Allah ya shirya ki Asiya wallahi ki gyara halayinki mtss baki da aiki sai fada dama ai halin ku guda.



Yo ni fa ina da hankali na to dan haka sai kidai na fadar wannan maganar too.



Ai shiyasa nake son nayi maki Aure na huta da masifar ki ta tsiya wallahi.



Yo ni fa bani da masifa Gaggo Amman akwai masifafe mai girman kan tsiya mtss.



Ke wallahi tashi ki fita na gaji da bakin surutun ki na tsiya.



Da gudu Asiya ta fito daga cikin daki tana dariyar Gaggo Saheeb ne ta hango Zaune yana char da abokanan sa.



Da gudu tazo ta buge wayar hannu sa sai ta fadi kasa cikin fushi sosai "yace ke baki da hankali ne?.




Eh ai rashin hankalin kenan Murguda masa baki take.



Ya daga hannun sa zai mari ta sai yaji muryar shatu na cewar Rabi kina ganin abun da nake gani kuwa.



kai kai kai wallahi kuwa *Asiya ce yar Gaggo* kuwa.



Da gudu Asiya tazo guri su Shatu rungume juna sai ihu suke Wayyo Allah mu Wayyo dadi Wayyo kwaliyar mu.



Saheeb tsaye yake yana kallon ikon Allah cikin ran sa "yace ikon Allah su kuma wannan fa.



Shatu "Tace kwaliya naga kinyi kyau sosai.



Eh wallahi nima dai abun da nake kallon.




Wallahi Aure za, ayi mani wai.



Suka hada baki suka ce Aure kuma? Ikon Allah aradun Allah bamu sani ba.




Shatu ta dago idanuwan ta tana kallon sa "Tace la Rabi dube balarabe tsaye yana kallon mu.



Da sauri Rabi ta kalle sa "Tace ikon Allah dama larabawa na zuwa nan?.



Kai waye balarabe din?.



Gashi nan a tsaya.



To babu wani balarabe sai dai mai girman kan tsiya mtss dan Allah ku wuce muje cikin daki.



Haka suka wuce suna kallon sa har suka shiga dakin Gaggo.



Saheeb ya Zauna yana kallon sama "yace kai gaskiya dole na kama girma na idan kuma ba haka ba zata raina ni sosai.



Zaune suka dakin Gaggo suna hutawa sai Shatu "Tace uhm uhm wai Gaggo wani balarabe ne muka gani cikin gidan nan.



Oho Saheebu ko ai shine Yayan ta kuma shine angon ta.




Kai kwaliyar mu dama shine zaki Aure baki fada muna ba suna kallon ta.



Wata uwar harara ta watsa mata "Tace baza,a fada munafuka mtss ni fa wallahi kun san halin na to.




Kai kuyi mani shiru ku shirya zuwa anjima zakuje gyaran jiki.



To Allah ya kai mu lafiya



A falo suka Zauna sai dariya hhhh suke gaskiya naji maganar ki akwai dariya sosai.



Wallahi kuwa ai dan mai gari ya shiryu.



Humaeera ce da baby walida suka shigo cikin falon sai "Tace Aa anty na baki kiyi ne?.



Asiya "Tace lah Humaeera Ashe kina zuwa Yau?.



Eh mana gashi nan nazo muje gyaran jiki da salon.



Shatu da Rabi suka ce menene sulan kuma?.



Aa salon nace ba sulan ba fa ku tashi muje gurin mai gyaran jiki.



Da gudu suka fita waje sai gurin mota suka shige cikin mota suka fita daga cikin gidan.




Agaje suka dawo gida kowa ya gaji sosai saman gado suka fada sai bacci ya dauke su.




*WASHE GARI*
*A YAU NE ZA, A DAURA AUREN ASIYA DA SAHEEB*......





*Hassy soja*😘🤪🤪🤪



*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍🏻✍🏻: ♥️♠️♥️♣️

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

♥️♠️♥️♣️
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_🤱🏻🤱🏻




PAGE...7️⃣5️⃣&8️⃣0️⃣


*________________*📚


*WASHE GARI*

*A YAU NE ZA, A DAURA AUREN ASIYA DA SAHEEB*



Gida suke yake da mutane sai murna suke Amman Saheeb kuwa yana dakin sa kwan ce sai rawar Dari yake.



Su Shatu da Rabi da Asiya sai guje guje suke basu kamar ba biki akeyi ba mutane sai dariya sukayi masu.



Ammi ce ta dauke wanka atamfa gaskiya tayi kyau sosai ta fito tana dube dube sai wata mata "Tace uhm Hauwa wani abu kike nema?.



Eh wallahi Saheeb be fito bane?.


Eh gaskiya duk Yau ban gan sa ya fito ba.


Ok babu damuwa bari naje dakin sa.


To wai ina Amaryar take?.



Duba su dakin maryam.


Ok.


Da sauri ta hau saman bene tana shiga dakin sa can ta hango sa kwan ce sai rawar Dari yake da gudu tazo gurin sa "Tace my baby lafiya dai ko meya same ka ne?.



Muryar sa na rawa "yace zazafi ne mai zafi tun jiya nake ji na haka Ammi.



Da sauri ta dauko wayar ta ta kira daddy ta fada masa.


Sai ga daddy ya shigo cikin dakin yana kallon su "Yace Ammin yara ki bari agama dauren Auren tukun na.



To shikenan amman kana ganin babu wata matsala ko?.


Insha Allah dama ai ciwon Aure ne yake yi.


Ciwon Aure kuma?.


Eh saboda nace sai ya Aure ta shikenan fa.


To Allah ya kyauta ai lokacin dauren Auren ya kusa ko?.


Eh.


Ok babu damuwa bari na fada na Humaeera ta wuce da su Asiya gurin kwaliya to.


To shikenan Allah ya kaimu lafiya dai.




Bayan Ammi ta fito daga cikin dakin sa sai ta hango asiya da kawayen ta Zaune suna dariya "Tace aradun Allah kin bani dariya sosai wai da gaske kike ko da wasa shatu.


Yasin da gaske nake baki ga nayi kyau sosai ba.



Asiya 'yata Asiya.


Da sauri ta dube mai kiran ta Ammi ce ta hango tsaye tana kallon su sannan "Tace naam da gudu tazo gurin ta "Tace gani.



Yauwa 'yata yar albarka rike hannun Asiya tayi "Tace muje za, ayi maki kwaliya Yanxun sai ta kalle su Shatu "Tace kuzo nan guri kunji ko.


Da gudu shatu da Rabi suka zo gurin Ammi "Tace too gamu.



Yauwa ku wuce dakin na mai kwaliya tazo zatayi maku Yanxun dai zuwa anjima za, aje gurin bude company insha Allah.



Asiya tashiga cikin dakin ta Zauna mai kwaliya ta tsaya tayi mata kwaliya mai mugun kyau sosai ta "Tace wow gaskiya kiyi kyau sosai sai kace aljana ce.



Asiya ta dago idanuwan ta sai suka hada ido da gimbiya jiddah "Tace ke ce haka kikazo?.



Gimbiya jiddah "Tace Eh nice gaskiya kawata kinyi kyau sosai fa.



Mai kwaliya kuwa mutuwar tsaye tayi tana kallon Asiya "Tace ikon Allah to ke amarya da ke da wa kike magana ne?.



Humaeera "Tace babu ruwan ki da ita kin dai gama yi mata kwaliya ko?.



Eh wallahi na gama mata.


To shikenan zaki iya tafiya tana binta da kallo har ta fita daga Dakin.



Asiya "Tace wai yaushe zaki zo ne?.



Zan zo zuwa anjima Amman akoda yaushe ina tare da ke.



Gimbiya jiddah to shikenan sai kinzo kenan dan Yanxun su daddy suna gurin dauren Auren su.



Ok babu damuwa Humaeera sai munzo ko sai taba ce bat.



A gurin dauren Auren kuwa kowa yazo har da sarkin kano da shugaban kasa duk sunzo dauren Auren.



*ANA DAURE AUREN ASIYA ABDULLAHI DA ANGON TA SAHEEB MUHAMMAD ABBAS AKAN SADAKI DUBU DARI UKKU ALLAH YA BADA ZAMAN LAFIYA*




Amin ya Allah daddy yau yana cikin farin ciki sosai wai yau dan sa yayi Aure ikon Allah haka ya dawo gida cikin farin ciki ya wuce dakin Saheeb.



Lokacin Saheeb yana Zaune yayi shiru sai yaji muryar daddy yana cewar wallahi kuwa Allah ya yarda an daura Gaban Saheeb ya fadi "yace shikenan sai ya rufe idanuwan sa yana maimaita *innalillahi wa inna ilaihir raji un* wannan wane irin masifa ce.



Ashe Daddy yana jin sa "yace babu wata masifa sai alkhairi dan haka Ana daura maku Aure tun da zakaje gurin daurin Auren ba to mu munje mudawo Allah ya baku zaman lafiya mai daurewa ko ka shirya zuwa anjima za, ayi bikin bude war companyn ku insha Allah daga nan sai ya fita daga cikin dakin.



Saheeb ya rasa abun da yake damun sa gashi bani da lafiya ga Aure gaskiya dole na bar Nigeria da sauri ya kira abokin sa ya fada masa ya yankar masa ticket sannan ya kashe wayar sa.




Bayan Karfe 4:00pm

Ammi ce da su Asiya Shatu da Rabi da humaeera da Gaggo da sauran mutane suka shiga motoci suka wuce company su daddy ma haka suka wuce can company.



Anyi bikin bude war companyn sa ita kuma Asiya an bude mata company atamfa da leshi lafiya an gama lafiya kowa cikin farin ciki ya dawo gida.




Bayan an watse sai ga Saheeb ya shigo cikin falo sai ya isko su Ammi da daddy yana zuwa gurin su sai ya Zauna yana kallon Ammi.


Ammi ta lura da kallon da Saheeb yake mata "Tace Saheeb lafiya dai ko? naga kamar akwai magana abakin ka ne?.



Uhm uhm uhm dama dama sai ya fara surar kan sa.


Dama me ka fada mana.



Dama gobe insha Allah zan tafi America ne.


America kuma da kai da waye zaku tafi ne?.



Ni ka d'aya zani.


Daddy "yace ok babu damuwa Amm Ammin yara to sai ki hada ma 'yata kayan ta dan zasu tafi america gurin cin amarci.



Da sauri ya dago idanuwan sa yana maimaita maganar daddy "yace daddy bafa tare zamu ba gara abarta nan gida saboda karatun ta.



Cikin fushi daddy "yace Ai ko sai dai afasa tafiyar nan ko.



Allah ya baku hakuri wallahi ni ba haka nake nufi ba sai ya tashi ya wuce dakin sa.



Ammi "Tace shashan banza kawai muzakayi boko.



Daddy ya bushe da dariya "yace Allah Ammin yara ki bani dariya sosai fa.


Washe gari kowa ya fito breakfast Amman ban da Saheeb yana dakin sa yana gyara kayan sanyawar.



Asiya kiyi sauri fa dan wannan tafiyar bata wasa ba fa.


Turo baki tayi "Tace haba Ni dai wallahi ban koshi ba fa.



Wallahi kin san halin yaya Saheeb baya son jira fa ko?.



Tabe baki tayi "Tace yo ina ruwa na da shi ne lokacin yana saukowa daga saman bene koda ya iso ya durkusa kasa "yace Ammi daddy Gaggo barka mu da safiya dafatan kun tashi lafiya?.



Lafiya Qlau Alhamdulillah Saheebu har ka shirya kenan.


Eh wallahi gashi ma jirgen Karfe 8:00am zai tashi.


To bazakayi breakfast bane?.


Aa sauri nake sai na shiga jirge zan ci wani abu sai ya hada ido da Asiya tana murguda masa baki sai ya dauke kansa.



Ok shikenan Asiya tashi ku tafiyar ku kin ga jirgen ya kusa tashi da yake kayan ta na cikin mota.



Turo masu baki tayi tana kallon su sannan "Tace wai ina zamuje ne Yanxun?.



Kasar waje zakuje da ke da mijin ki mana.


Menene kasa na waje kuma?.



Dan Allah gafara can wallahi zan tafiya na barki sai shegen surutun tsiya mtss.



Gaba d'aya suka fita waje gurin motar su Asiya tashiga cikin mota ta Zauna Saheeb ya shiga ya Zauna ta tada motar suka fita daga cikin gidan nan.



Su Ammi da Gaggo da Humaeera sai bye bye suke masu har motar ta bar unguwar su da sauri Gaggo ta shige cikin gida idanuwan ta sun ciki da hawaye.



Bayan sun iso filin jirge sai suka hada ido Asiya ya watsa mata harara "yace ke mahaukaciya lafiya kina kallona?.




Ni dai ba mahaukaciya ba ce Murguda masa baki tayi.



Ke ni kikeyiwa rashin kunya ko?.



Tabe baki tayi "Tace yo ni ma ai rashin kunya kakeyi mun.



To shikenan amman wallahi tallahi ko himm!.



Fito sukayi daga cikin mota suka wuce cikin filin jirgen suna zuwa ankiran su "Yace to malama sai ki wuce muje ko?.



To wuce muje mana.



Haka suka shiga cikin jirgen saman bayan sun Zauna sai aka rufe jirgen.



Kowa ya Zauna dan Yanxun jirgen zai daga to sai matar ta wuce dakin.




Jirgen na tashi wani irin ihu Asiya tayi "Tace Wayyo Allah na Wayyo Gaggo na mutu shikenan Yaya Saheeb zai kashe ni da sauri ya rufe mata baki mutum sai kallon su suke suna masu dariya.



*A sauka lafiya Asiya da Saheeb*




Sai Karfe 11:00pm suka iso gidan nan kai gaskiya gidan ya hadu ba karya haka suka shiga cikin falo gidan.



Asiya sai hamma kawai take "Tace uhm uhm uhm ni wallahi yunwa nake ji sosai.



Wata uwar harara ya watsa mata "yace dauke ni ki canye nace ki dauke ni ki canye Allah tun sanda na kara jin bakin bakin ki sai na balaki mtsss wawuya kawai sai ya tashi ya wuce dakin sa ya ya kwanta.



Faduwa kasa tayi na shure shure sai ta fashe da kuka "Tace Wayyo Allah na mutuwa zanyi haka ta cigaba da kuka har bacci ya dauke ta.



Bayan tayi bacci sannan ya fito daga cikin dakin sa yana kallon ta "yace kai gaskiya daddy wallahi dai ka cuceni da ka hada ni da wannan yarinyar wallahi mtss haka ya wuce ya amso mata abinci ya ajiye mata saman kujera sai ya jiya yana kallon ta duk taba shi tausaye sai ya wuce dakin sa ya kwanta.



Bayan ya shiga dakin sa cikin dare ta farka da kuka sosai take kuka "Tace Gaggo kina ina ne ko da ta dago idanuwan ta sai ta ga gimbiya jiddah Zaune tana kallon ta "Tace kawata zo ki ci. abinci kinji ya?.



Da sauri tazo kusa da gimbiya jiddah ta Zauna ta bude kular abinci sai ta ga tuwo da miyar kaji haka taci abun ta har ta koshi sosai sannan "Tace kina ganin abun da Yaya Saheeb yake yi mani ko sai ta kara fashewa da kuka.



Haba kawata ki yi shiru mana bani kwana biyu zakiga abun mamaki sosai kinji ko kawata.




To shikenan nagode sosai.



To kwanta kiyi bacci kinji?.



To tana kwantawa sai mai dadi ya dauke ta.


Asuba tagari.




Tun da sanyin safiya ya dauko ruwan sanyi ya watsa mata "yace ke kucakar yarinyar.



Da sauri ta tashi Zaune tana kallon sa da mamaki.



"yace lafiya kikayi ma mutane Zaune ai ba zama ya kawo ki ba yarinya.



To wallahi baka isa ba zata kara magana ya buge mata baki.



Wallahi duk sanda kika kara yi mani rashin kunya sai na balaki kuwa dan Allah gafara can wuce muje gurin flowers ki basu ruwa haka suka fita waje gurin flowers ya tsaya yana kallon ta cikin tsawa "yace wuce ki fara zuba masu ruwa sannan da kin gama ga motoci nan ki wanke su sosai wallahi duk basu fita ba ko himm!.



Cikin masifa "Tace kan uban can to wallahi baka isa ba sai kace yar aikin ka.



Yazo da sauri zai dukan ta da gudu ta wuce dakin ta ta rufe kofar dakin.




Ashe yana da makulin dakin sai ya bude dakin can ya hango ta Zaune tayi tagume tana kallon sama jin tayi Ana bude dakin da sauri ta tashi tsaye tana mamakin sa cikin ran ta "Tace kai to shi yaushe ya shigo cikin dakin ban sani ba?




Daure fuskar sa yayi "yace uwar wa kike ce ma be isa ba?.



Yo ni fa banyi magana ba.



Yaso yayi dariya Amman sai ya daure fuskar

Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On ASIYA SARKIN TSIWA YAR GWAGGO
avatar
ali-boukary

12 months ago

Reply

Ina jindadin litafinna allah kara zakin hannu

Please Login or Register in order to submit comment