Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

sa cikin masifa "yace wallahi tallahi Idan bakiyi hankali ba Sai nayi maki dukan tsiya wawuya kawai mtsss Ya juya zai wuce sai ya ji muryar ta




"Tace tooo Nima wallahi na iya masifa Eehee eeheee tana Murguda baki.



Tsayawa yayi yana kallon ta daga mata gira yayi "yace magana kikeyi ne?.



Aa cewa nayi ko akwai abinci nace.



Dariya tabashi cikin ran sa "yace wannan yarinyar akwai rashin kunya Amman akwai tsoro girgiza kan sa yayi sai ya fita daga cikin gidan.



Dugon nishi tayi "Tace kai Allah ya soni da ya dakeni da wannan shegen hannun na sa mtss.



Haka ta fito daga cikin dakin ta dube dube sai taga babu kowa sai ta dawo falo ta Zauna har bacci ya dauke ta.




Bayan kwan biyu da zuwa su america sai Saheeb ya fito waje gurin mai gadi sai "yace mai gadi ga kudi na ka amso mani lemo Amman kayi sauri kada kade.



To jikin sa na rawa "yace to oga da gudu ya fita daga cikin gidan nan.



Saheeb ya koma gurin swimming pool ya Zauna yana hutawa.



Asiya ce ta fito daga cikin gida tana dube dube sai ta hango sa can kwan ce kamar mai bacci dariya mugunta tayi "Tace yau kam wallahi sai na fita na gano gari kuwa da gudu tafi daga cikin gida tana murnar ganin gari.




Bayan fitar ta sai ga mai gadi yazo da gudu gurin Saheeb "yace oga gashi nan.



Tashi Zaune yayi "yace ok thanks haka ya wuce cikin gida ko da yashiga cikin falo sai ya Zauna har ya kwanta be ga ta fito ba sai yayi shiru yana tunani sannan "yace wai ina yarinyar nan ta shiga ne da sauri ya kira ta ke yarinya ke yarinya Amman shiru da sauri ya meki tsiya ya wuce dakin ta ko da yashiga cikin dakin ta babu kowa.



Gaban Saheeb ya fadi dumm dumm "yace *innalillahi wa inna ilaihir raji un* to wai meyake shin faruwa da ni ne? da gudu ya fito waje yazo gurin mai gadi "yace mai gadi ina kaga tayi ne?.



Wallahi oga ban ga kowa ba.



Tashin hankali kuwa.............




*Hassy soja*ðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠ

*Comment and share*
11/25/20, 1:08 PM - Princess soja ✍ðŸŧ✍ðŸŧ: â™Ĩïļâ™ ïļâ™Ĩïļâ™Ģïļ

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏

â™Ĩïļâ™ ïļâ™Ĩïļâ™Ģïļ
```Love and romantic story```


_Na_


_Hassy soja_



```Wannan labarin nawa salon sa na daban ne ban yarda wani ko wata su canza mani labari ba sai akiyaye```




*MARUBUCIYAR*


_BANI CE BA (ALJANA CE)_

_ASHE YAN UWA NA NE (MU BIYAR)_

_MUFIDA KAWAR ALJANA_

_SUMAIYYAH SUMEE BABY GIRL_

_HAKURI_

_SAI NI YAR DAJI NI KUMA YAR BIRNI CE_

_MUHSEENA DA MUHSEEN_


_AND NOW_

😏 _*ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*_😏


_*BISMILLAHAR RAHAMANI RAHIM DA SUNA NA ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN'KAI*_




_*SADAUKARWA GA MAHAIFIYA TA DA MAHAIFINA ALLAH YA JIKAN MAHAIFINA YAYI MASA RAHAMA MAHAIFIYA TA ALLAH YA KARA MAKI LAFIYA DA NISAN KWANA*_ðŸĪąðŸŧðŸĪąðŸŧ

🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚🔚


PAGE... 8ïļâƒĢ1ïļâƒĢ


*________________*📚


Tashin hankali kuwa da gudu ya fita daga cikin gida Amman bega kowa haka yadawo gida Zauna yana tunani ina tashiga ne gashi ma su baki ne sai maimaita *innalillahi wa inna ilaihir raji un* kawai yake.



Tun Karfe 12:00am began ta ba har lokacin sallah isha,i yayi babu ta babu alamar ta wayar sa ya dauko ya kira daddy lokacin su daddy suna Zaune dakin kiran wayar sa ne yasa ya duba sai ga sunan Saheeb.


Kallon Ammi yayi "yace Saheeb.



Saheeb ko sallama beyi ba "yace daddy wallahi ban ganta ba ban sani inda tashiga ba.



Cikin tashin hankali daddy "yace kamar ya baka ganta ba?.



Tun da safe nake bedar ta ban gan ta ba koma na tambaye mai gadi yace bega kowa ya fita daga cikin gidan nan ba.



Cikin fushi sosai "yace wallahi baka isa ba dole sai kane mu ta duk inda tashiga kaji na fada maka.


Kashe wayar sa yayi yana kallon Ammi can sai ya Zauna yana maimaita *innalillahi wa inna ilaihir raji un*.



Da sauri "Tace daddyn Saheeb lafiya dai ko? Tana kallon sa.



Ajiyar zuciya yayi shiru yayi mata can sai "yace wai Saheeb ya kira ni ya fada mani wai bega Asiya ba.



Kamar ya bega Asiya ba?.


Yana nufin ta bata kenan.



*innalillahi wa inna ilaihir raji un* yaushe wannan Abu ya faru kuma daga zuwa kasar waje sai ta bata to ai dama beyi niyar zuwa da ita ba ne himm! Da sauri ta dauko wayar ta ta kira Saheeb lokacin yana Zaune yana tunani shin wa ma mafarki nake kuma da gaske?.


Karar wayar sa ce yasa ya dago idanuwan sa yana maimaita *innalillahi wa inna ilaihir raji un* kallon wayar sa yayi sai ya ga sunan Ammi da sauri ya dauka "yace Ammi



"Tace Saheeb naji wannan mumunan labari wai baka ga Asiya ba?.



Eh wallahi Ammi na shiga ko ina da ko ina na duba ban gan ta ba kuma mai gadi yace shima dai be ganta ba.



To katashi mana maza maza da sauri kaje ka dubo ta duk inda tashiga kaji na fada maka.


To Ammi insha Allah za, aganta.


To shikenan babu komai sai ta kashi wayar ta tana kallon daddy sai "Tace Amman dai ba aza fadawa maryam ba ko?.



Saboda me kika ce haka?.


Kada hankalin ta ya tashi.


Uhm ya zama dole ta sani kuwa saboda wata rana sai labari yarta.



To shikenan babu damuwa Allah ya sa aganta.



Amin.



Saheeb ne ya fita daga cikin gidan ya duba ko ina ya duba amman be ganta ba haka yadawo gida Zauna cikin tashin hankali sai ya kara tashi ya duba ta bayan gida Amman banza sai ya fashi da kuka.



"Yace wai ina kika shiga ne? *Innalillahi wa inna ilaihir raji un* Allah ka bayana ta haka ya cigaba da tunani inda tashiga Amman babu wata mafita ya je gidan TV gidan raidiyo an sa cigiyata ko Allah zai sa aganta.



*A bangaren Asiya kuwa*



Asiya ce zaune tana kallon dakin "Tace too wai ina ne nan gurin? Koda sace ni akayi ne kuma?.



Aa nice na dauko ki cewar gimbiya jiddah dake Zaune tana kallon ta.



La Ashe ke ce ban sani ba?.



Eh ni ce kawata ai kindawo da zama nan duniyar aljannu saboda Yaya Saheeb yayi hankali sosai ke kuma kiyi karatu da sauran wasu abubuwa kinji ko?.




Eh naji dadin dawowata anan duniyar aljannu yeeeeee yeeeee yeeeeeee.




Kawata Yanxun ba lokacin rawa bane Yanxun lokacin karatu ne kinji?.



Yo ni fa Yanxun yunwa nake ji tana kallon ta.




Gimbiya jiddah tazo gurin ta "Tace too shikenan amman sai kin sha wannan ruwan sannan.



Da sauri ta amsa ruwan ta shanye su duka bata rage ko d'aya ba.



*Bayan wasu kwanaki*



Asiya ta fara hankali wasu abubuwa cikin natsowa take su ta iya karatu ta iya guy sosai sai dai har Yanxun ba ta daina tsiwa ba.



*Abangaren Saheeb kuwa*



Saheeb yana Zaune falo sai yaji kamar muryar Asiya da gudu ya fito ya gani ko da gaske ne Ashe babu kowa shine kawai yake jin haka.



Komawa gida yayi shiga cikin falo sai ya wuce dakin sa ya hadu kayan sa acikin akwati.



*BAYAN WATA BIYAR*




Asiya ce Zaune tana tunani mafarkin Saheeb da tayi "Tace ikon Allah to ko da gaske ne bashi da lafiya?.



Eh da gaske ne bashi da lafiya saboda da ke kuma gida kullum sai sunyi addu, a Allah ya ba yana ki.



Allah sarki wallahi nayi missing din Gogga ta sai ta fashe da kuka.



Haba kawata kuka fa be dace da ke ba zo muje ki ga halin da suke ciki.



Da sauri ta tashi sukaje gurin madubi sai gimbiya jiddah ta "Tace madubi muna son ganin gidan su Asiya.



Ana gama rainki ya dade ko da ya kamo masu sai Asiya ta hango Gaggo da daddy da Ammi Zaune cikin damuwa sosai da sauri Asiya "Tace wallahi inason ganin su ina son su sosai wallahi duk.



To madubi gurin Saheeb muke son gani.



Ana gama rainki yadade sai ya kamo masu Saheeb ne ya fito da Akwati zai sai cikin mota duk ya rame yayi baki da sauri Asiya "Tace Allah sarki yaya Saheeb wallahi kabani tausaye sai ta share hawayen ta "Tace muje ko?.



To shikenan amman gaskiya naji dadin ganinki haka saboda kinyi hankali sosai Amman zuwa sai tayi tsaye tana kallon Asiya "Tace lafiya dai?.




Asiya ta kalle gimbiya jiddah "Tace wallahi inason kumawa gida fa Yanxun yau kwanana nawa ne?.



Dariya sosai gimbiya jiddah tayi "Tace haba haba dai kawata kada ace kin kamu da son Yaya Saheeb.



Wata irin jiyowa tayi "Tace Allah ya sauwake ni wallahi ni tausayen sa kawai nake ba so ba.



To shikenan amman gaskiya muje afadawa mommy ko?.



Me za,a fada mata ne?.


Kin son komawa gida mana.



To shikenan amman ni dai gaskiya kunyar fada mata nake.



Gimbiya jiddah zatayi magana sai ga mommy ta sauko kasa tana kallon su sannan "Tace 'yata lafiya dai ko akwai wata matsala ne?.




Aa mommy.



Ke dai fada mata gaskiya kawai babu wani buye buye.



Buye buye kuma? Name hama?.



Wai meya ke faduwa ne?.



Mommy wai gida take son komawa gurin mijinta.



Masha Allah abu yayi kyau sosai wallahi.



Mommy bafa gurin mijina zani ba fa gurin su Gaggo zanje tana Zaunawa saman kujera.


Ok babu damuwa Amman Yanxun ki ci abinci sannan kiyi wanka kinji ko?.



To mommy insha Allah Yanxun zan ci.


Yauwa 'yata yar albarka kiyi sauri fa.


Da gudu tashiga tolity bayan tayi wanka sai ta fito sai taga breakfast dinta Zaunawa tayi taci ta koshi sosai sannan ta sharuwan madara.



Doguwar riga ce ta sanya kai gaskiya Asiya tayi kyau sosai fito tayi daga cikin dakin gurin su mommy taje "Tace uhm uhm mommy gani.



Wow gaskiya kiyi kyau sosai kawata idan Yaya Saheeb yaga wannan wanka ko Uhm.



Murguda mata baki tayi "Tace yo fa babu ruwa na da shi.



'Yata Zauna kiji wata magana.


Zaunawa saman kujera tayi sannan "Tace mommy na Zauna.



Yauwa 'yata abun da nake son fada maki shine ki rika mijinki sauda kafa kada ki bata masa rai kinji Allah zai baki lada.



Insha Allah.



Yauwa to gimbiya jiddah sai ku wuce.



Lokacin Saheeb har ya iso cikin gida bayan ya fito daga cikin mota Akwati sa ya jawo zai shiga da shi cikin falo yana shiga cikin falo kenan wata farar yarinya ce Zaune saman kujera sai taji kamar muryar Saheeb da sauri ta jiyo tana kallon Saheeb.



Hannun sa ya daga yana nuna Asiya dake Zaune.


Da sauri Asiya "Tace welcome back my baby.



Mutuwar tsaye yayi "yace wai da gaske ne ko dai mafarki ne?.


Matsowa tayi kusa da shi "Tace babu wani mafarki Yaya Saheeb ni ce dai *Asiya sarkin tsiwa yar Gogga*.




Da sauri ya dauko wayar sa ya kira daddy lokacin suna Zaune falo kiran wayar sa ne yasa ya duba sai yaga Saheeb sai ya dauka.



Daddy daddy daddy kuna ina ne?.


Saheeb lafiya kake ne?.



Daddy nadawo gida nan Amman sai naga wani abun mamaki dan Allah kuyi sauri kuzo ku gani.



Too gamuna tafi sai ya kashe wayar sa "yace to ku fa zama be ganmu ba ku tashi muje.



Ammi da Gaggo suke ce muje ina?.



Gidan Saheeb yadawo gida kuma yace muyi sauri.



Da sauri suka wuce daga cikin gidan sai gidan su Saheeb.



Asiya Zaune tana kallon sa shi kuma Saheeb yana nan tsiya ko motsi beyi ba.



Sallamar su daddy yaji ya da gudu yaje gurin su "yace daddy hango can Da sauri su daddy suka kalle Asiya dake tsaye tana kallon su.



Da gudu Asiya taje gurin su Ammi "Tace oyoyo my sweetheart Gaggo oyoyo my Ammi oyoyo my daddy Miss you so much.



Mutuwar tsaye sukayi suna kallon ta Gaggo "Tace wai Asiya ce nake ganin ko mafarki nake ne?.



Babu wani mafarki ni ce dai *Asiya yar Gogga* kuyi hakuri dan Allah please sai ta fashe da kuka.



Da sauri Gaggo ta rungume ta "Tace Allah nagode maka da kadawo mani da 'yata sai ta fashe da kuka.



Da sauri su daddy suka rungume ta suka ce Asiya ina kika shiga ne? Kwana da yawa.



Muna tare da ita cewar gimbiya jiddah dake Zaune tana kallon su.



Da sauri suka saki juna Gaggo "Tace dama kuna tare bamu sani ba?.



Eh hakane ku zauna zan fada maku.



Zaunawa sukayi saman kujera sukayi shiru.



Nice na dauke ta saboda da nakoya ma Saheeb hankali itama tayi hankali to gashi nan lokaci yayi.



Ikon Allah to shikenan babu damuwa Allah yayi maki albarka.



Amin ya Allah.


To alhamdulillah kawata sai wani lokaci idan Allah ya kaimu lafiya dai sai ta bace batt.



Saheeb sai satar kallon Asiya yake itama kallon sa take tana Murguda masa baki.




Murmushi "yace kanwata nayi missing din ki fa.


Ni kuma banyi Miss din ka ba tana harara sa.



Wai ke har Yanxun baki daina fada ba ko.



Ni fa na dai na fada fa.


To ku tashi muje.


Haka suka fito daga cikin gidan.



Saheeb ne yadawo kusa da Asiya ya Zauna ta kashe mata ido "yace dan Allah kanwata kiyi hakuri da abubuwan da suka faru please.



Rike hannun sa tayi "Tace wallahi na yafe maka mijina ina alfahari da kai.



Nima ina alfahari da ke matata uwar 'yayana I love you .


I love you too.


Wai ai ina kika koyi turanci ne?.


A duniyar aljannu mana.


Kina nufin duniyar aljannu kika tafi ne?.


Uhm eh Yanxun dai muje kitchen mu daura girki.


Uhm uhm uhm uhm uhm ni dai ban iya girki ba.


Uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm uhm nima haka ni dai muje.


To haka suka shiga cikin kitchen suka dafa taliya da miyar kwai da kayan ciki.



Bayan sun kamala abinci suka ci suka koshi sosai.



Karfi 11:00pm sai Asiya "Tace bacci zanyi fa.


Muje na baki baby to.



To shikenan babu damuwa.



Bayan suna shiga daki to Allah ya bada 'yaya akan sunna.......



*ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALHAMDULILLAH ALLAH NAGODE MAKA DA BANI IKON KAMALA*
😏 *ASIYA SARKIN TSIWA YAR GAGGO*😏



*ALLAH YA BAMU DALAR DA KE CIKI KURAKURAN DA KE CIKI ALLAH KA YAFE MUNA AMIN YA ALLAH*



*SAI MUN HADU CIKIN SABON NOVEL DIN MAI SUNA*....... 💃ðŸŧ💃ðŸŧ💃ðŸŧ💃ðŸŧ💃ðŸŧ





*Hassy soja*😘ðŸĪŠðŸĪŠðŸĪŠ



*Comment and share*

An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels


Book Chapters
Chapter 1Chapter 2Chapter 3Chapter 4
Chapter 5

1 Comments On ASIYA SARKIN TSIWA YAR GWAGGO
avatar
ali-boukary

12 months ago

Reply

Ina jindadin litafinna allah kara zakin hannu

Please Login or Register in order to submit comment