Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

datake wankewa sunfi qarfin hannunta duk da kuwa akwai washing machine a gidan Amman saboda MAMA kullum burinta ta quntatawa rayuwarta yasa tace da hannu zatayi,tanayi tana share hawaye dasuke ta zubo mata sakamakon dukan da Maman tayi mata dazu,ba ita tagama ba sai bayan sallar ishaa,
Direct boys quarter ta wuce inda Dan qaramin dakinta yake ita da Baba larai me aikin gidan,tana zuwa tafada kan yololuwar katifar ta data gaji da wahala tana fitar da numfarfashi ga sanyi datakeji,zanin atamfarta ta jawo ta lulluba amman still haqoranta kaf-kaf sukeyi mata,sai da takai minti talatin sannan tafara jin relief,a hankali ta tashi tashiga bandaki domin sauke faralli,tana fitowa tajawo dankwalinta daga cikin kayanta ta shimfida ta tayar da sallah(dama ita bata cire hijjabi)sallah takeyi cike da nutsuwa da iyawa har ta kammala,sai da ta dade tana lazimi sannan tashafa addu'a ta miqe,zama tayi bakin katifar tayi tagumi tana tunanin abinda zataci don yau tin bread din safe da taci bata sake cin komai ba,miqewa tayi taje ta dauko sauran ta debo ruwa a kofin roba sannan ta zauna tafaraci a hankali kamar ba yunwa takeji ba,can sai tayi murmushi komai tatuna oho!,sai da cinye sannan ta maida cup din kan randar dakin sannan ta kulle qofar da glasses tayi switching off na hasken ta kwanta tana karanto Addu'a"bismikallahumma amutu wa'ahyaaa"
_Asuba ta gari_
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE๐Ÿ‘„*
_.....Adulterer's Daughter_
_*A true life,touching hrt nd luv story*_
_BY_
*Maryam Pinky*
*ATTENTION*
_*Assalamu Alaikum masoya littafinnan duk naga qorafinku kuma naji dadi sosae da kuka nunamin kulawarku A kan Wannan littafin Nagode Allah yasaka da Alkhairi,musamman ya'n group JIGAWA HAUSA NOVELS,ZUBY NOVELS, HAUSA NOVELS,DUNIYAR MAKARANTA,DOCUMENT NOVEL,A.S.Y SHOW NOVELS,AREWA NOVELS,da sauransu haqiqa naji dadi da gyararrakinku sai dae mutanen sunyi yawa kuma duk qorafin daya ne wato....ACANZA TITTLE๐Ÿ˜…,na karbi gyaranku da hannu bibiyu Allah yabar zumunci Amman fa Wannan labarin yafaru a gaskene ba qirqirarsa nayi ba kuma yarinyar daya faru akanta wallahi exactly haka aka dinga kiranta da Wannan sunan.....YA'R ZINA nikuma shiyasa ma kawae nayi rubutunsa haka amman Insha Allahu zanbaku numberta domin Correction qofa a bude take nagode Ana tare๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿค๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜๐Ÿ˜˜*
6โƒฃ
*B.U.K Kano,dept of B.A*
A hankali cikin nutsuwa dandazon daliban dazasu kai atleast 500 ke firfitowa daga cikin theatre ta daukan lectures na business Administration na jami'ar bayero dake birnin kano, kowa kagani harkokinsa yakeyi,can sai ga su Asma'u da qawayenta guda biyu suma sunfito hannunsu riqe da handout da bags sanye take da doguwar abaya Ash colour mai farin crystals da zaiba tayi rolling kanta tayi kyau sosae,tafiya suke a hankali ta ya'n matan dasukeji da boko,can gefe suka xauna gun wasu kujeru na qasa,"washhh Allah na!"Asma'u tace tana jingina da jikin bishiya sannan ta lumshe idanunta,Rukky ce tace "wallahi Hussy bake kadai ba,malamin nan ya hada mana zafi da yawa yau"tafada tana yatsine fuska,Fadeela murmushi tayi tadubi Asma'u da har yanxu idanunta ke lumshe kamar me bacci sannan tace"Husna malaminnan naga kamar ya kamufa? Da sauri Asma'u ta bude idonta tana kallon Fadeela kallon u re mad sannan ta kalli Rukky da tace " Ai naga Alama kuma wllh perfect match"Murmushin yaqe Asma'u tayi sannan tace stop that pls infact ma Friend din Yaa Abdul nefa,cikin mamaki duk suka bude baki suna kallonta can Rukky ta dubi Asma'u datayi kamar ba ita tayi maganar ba tace "Ke Husnah re u serious?" Hararta Asma'u tayi tace
"Seriously"
Fadeelah ce tatabe baki tace "No wonder" Asma'u tace "Ashe kin gane"
Rukky ta numfasa tace "Husnah dama har yanxu kuna tare da Man dinnan?" Malalacin murmushi Asma'u tayi Dan sun Sosa mata inda yake mata qaiqayi,fadeela tayi caraf tace"Sunan tare yana Ball da xuciyarta son ransa kinsan me hali baya fasawa"tsokiii Rukky tayi tace "Ae wllh Husna kinyi kuskure da kika bari son Wannan mutumin ya shiga xuciyarki,mutumin da ba'abinda ya ajiye se shegen girman kan tsiya da taqama" Fadeela tayi dariya tace "taqama yake da kyau da kudi naji ance ya siye 4Banks in Kano last 2weeks a NTA news wae" tsokin Rukky takuma jaa tace "Kudinsa na banxaa,Husnah yakamata musami mafita before azo ayi abinnan kokuwa?" Sai yanxu Asma'u tasauke tagumin datayi sannan tadubesu tace"wllh ni kaina narasa yadda zan solving din matsalarnan yanxufa kunga jiya..........anan tabasu lbrn yadda sukai dashi a waya dakuma tambayar da mummy tayi mata"Rukky ce tafara magana bayan sungama sauraron Asma'u tace"Nifa wllh Husna me zai hana kifadawa mummy abinda yake miki kinga ita sae tasami mamansa tace kawae afasa bikin?"dasauri Asma'u ta girgiza kai tace"Inason yaa Abdul dayawa idan ban aure shiba zan iya rasa raina Rukky bakiji yadda nakeji akan sonsa ba kamar zai faso min qirji yafito wllh"tafada tana dafe qirjinta ga hawaye yana zubowa,duk sai suka matso kusa da ita suna bata haquri Dan kuka ya kece mata zuwa yanxu,bubbuga bayanta suke suna encouraging dinta _(They care each other)_ Fadeela tadubi Rukky tace "Nifa inaga tinda tana sonshi ba rabuwa ce Maslahaba,kawae we shall wait 4 d tym,I'm sure he will luv u more when u become couples Husna" HK ne inji Rukky amman cikin zuciyarta tausayin Asma'u takeyi yadda take son maso wani,yauwaa mujira lkcn yanxu lkcn sa ne,amman idan yazo hannunmu he will regret it,dariya duk sukaiwa Fadeela,
"Allah yasa" cewar Asma'u, Fadeela tace "I'm telling u indai muna tare sai kin mallaki Abdul,kin juyashi kamar waina sai yazo yana miki kuka wllh" Qyalqyalewa da dariya Rukky da Asma'u sukai sukace "Allah fadee" Hummnn kudai kuyi shiru kawae ix just a matter of tym sai ya gane kuransa......haka sukayita firarrakinsu irin ta Aminan juna Dan Abotarsu tun primary, secondary gasu yanxu a tertiary ma,basu boyewa juna matsalarsu tare suke solving problems,yanxu haka Bikin Rukky da saurayinta Auwal remain 2month while Fadeela da saurayinta Ahmad remain 8 month,Asma'u ce tukunna yanxu suna level 2 a buk suna karantar Business Administration.
************************
_sorry yau ba yawa_
_6โƒฃ_
6โƒฃ
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE๐Ÿ‘„*
_......Adulterer's Daughter_
_*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*_
_BY_
*MARYAM PINKY*
_*Thix page ix just for u my naughtiest Friend ZAINAB BUKOLA SARAKI,share it wit ur Abdul crush๐Ÿ˜œ,Tnxs 4 ur supportive Role๐Ÿ’‹*_
7โƒฃ
5:47am Agogon dakin ya nuna,juyi tayi tana salati,A hankali ta tashi zaune tana hamma,sai da ta dau 3 minutes a zaune tukunna ta miqe tana tattare hijjabin jikinta sannan tashiga toilet,Tana fitowa ta dauko dankwalinta ta shimfida ta tayar da sallah sai da tayi raka'atul fijr sannan takawo Asuba,zama tayi tana Azkar kamar yadda tasaba,bugun qofar da akeyi ne kamar za'a balla ya dawo da ita daga duniyar baccin data fara,Dan uwarki baxaki zo ki bude ba?,shegiyar yarinya mai zubin yahudawa YA'R ZINA...., shiru tayi zuciyarta na bugun tara-tara ga wani irin tsoro daya ziyarceta,ita Sam ta manta yau ita zatai abin break cox baba larai bata nan,kasa zuwa tayi ta bude qofar duk da har yanxu bata dena jefomata zagin ba,tasan indae ta bude qofar nan sae taci dukan tsiya...jiyowa tayi mamaa tana cewa
"To Dan uwarki,Minti 2 nabaki kifito kiyimana abin karyawa idan kuwa kika bari nadawo baki fitoba,to wllh sai nakusa kasheki shegiyaaa kawae"
Tinda tafara take kuka marar sauti,A hankali ta share hawayenta jin alamar mamaa tatafi,hijjabi ta canxa daga milk zuwa Black sannan ta Zare key din A hankali,ganin bakowa yasa ta sauke ajiyar zuciya sannan tasa gudu sae kitchen,turus ta tsaya a kitchen din tana kallon time table din girkin,siraran yatsunta ta Dora akan time table din tana karantawa:Tea nd bread,egg potatoes,chicken pepe soup,Ajiyar zuciya tayi sannan ta kama aikin gadan gadan,Cikin qwarewa da gwanancewa takeyin aikin kuma cikin nutsuwa,duk da qanqatarta amman sai kace wata cooker,sauri taketayi kar su mamaa su sauko susameta a nan,in less than one nd half hour ta gama jeresu akan tamfatsetsen dining table dake cikin main falo,kitchen din ta koma ta gyara tayi wanke wanke sannan tazo tayi mopping din falon duk cikin sauri takeyin ayyukan,har ta gama batajiyo duriyarsu ba tasan suna can suna bacci,kitchen ta koma tadauki abincinta data zuba a Leda ta rufe ta kwasa da gudu sai boysquarters,tana zuwa ta fada dakin ta rufe bam,sai haki takeyi ta zauna akan katifar tana sauke numfashi,hannunta ta sa qarqashin pillow tajawo wani Dan qaramin littafi _Addu'a'u minal kitabi wassunnah_cikin xuciyarta take karantawa,10:46 data kalli agogon,miqewa tayi tamaida littafin sannan tadauki brush dinta tatafi bandaki,sai da tayi har wanka sannan tafito,ta cikin hijjabin tacanza kayanta zuwa Riga da zani da wani hijjabin Blue black,abinka da farar mace sai tayi kyau fuskarnan ta fito fayau acikin hijjabin,ko oil bata shafa talkless of powder,abincinta ta dauko ta ci kadan tasha ruwa ta ajiye sabida anjima Dan tasan ko ta dafa anjima bata da rabo aciki,zama tayi tazuba tagumi a gun tana tunanin rayuwa,a hankali cikin wata irin murya mai dadin sauraro cike da yarinta take magana _"Ni Ameera to ni menene makomata a duniyar nan?..._da sauri kuma ta toshe bakinta kamar tana gaban wani hawaye sukafara kawowa a idonta a hankali ta furta _Astagfirullah Alhamdulillahi ala kulli Halin_sai kuma tayi shiruuu,sai bugun xuciyarta,a hankali ta tashi tafito qofar dakin ta xauna kan wani Dan stool na clay gefen flowers din gun domin tagaji da zaman dakin,tsintsayen daketa shawagi agun masu ban sha'awa,tayi nisa cikin kallonsu
Tanan zaune taji an ruqunqumeta ta baya kamar zata fadi..."Nayi kewarki YA'R uwa,da sauri *Ameera*ta rungumeta Dan ta ganeme muryar sahibarta a hankali ta furta "Nayi kewarki Nima" duk suka tashi tsaye suna murnar ganin juna,Sai da suka gama murnar sannan suka saki juna,Da gudu Ameera taje ta rungume baba larai tana cewa "Mamaa nayi kewarki" Murmushi baba larai ketayi tana shafa kanta tanacewa"Yar Albarka Nima nayi rashinki"dan qaramin bakinta ta turo gaba sannan tace "Amman mamaa kikatafi kuka barni har sati 1" tafada tana bubbuga qafa,dariya baba larai tayi tashafa kanta tace to ae gamu mundawo kuma bazan kuma tafiya na barkiba kinji koh,hannunta ta miqowa baba larai tana dariya tace "Yawaa mama" da haka suka shiga dakinnasu dama tare suke,Suna shiga suka tarar da Khadija kwance rashe-rashe akan katifa,harara Ameera ta wulla mata sannan tace "Dubi ki Dan Allah kinxo kin wani kwanta,tashi ki matsa baba tazauna" tafada cikin wasa,
Miqa Khadija tasakeyi tana lullumshe ido tace "wash,wllh Ya'r uwa dakinsan gajiyar da nayi dabaki tashe niba" hararar tasake watsamata tace "Humm raguwa kawai" dariya khadeeja tayi tace "Mai da idon Kar su fado,kuma ni dake a sami raguwar" zatayi magana kenan baba larai tafito daga bandaki Dan dama suna shigowa da ta sauke jakarta bandaki ta shige,Ameera ya zaman kadaici?baba larai ta tambayeta tana zama kusa dasu,A sanyaye Ameera tace "Nasha shi kam" baba larai tayi murmushi tace "Ayi ta haquri dai Ameera duk yadda rayuwa taxo kinji yarinyar kirki?" Gyada kanta tayi alamar toh,sannan ta numfasa a hankali ta taso tadawo kusa da baba larai ta kwantar da kanta akan cinyar babaa larai sannan tasa hannayenta duka biyun ta rungume baba larai tace "Amman fa mama sai da Maman sameera tayimin duka" Kasa cewa komai baba larai tayi domin dama tasan za'ayi haka dama amman Dan ta kawar mata da zancen tace
"Ameera kici gaba da haquri" toh mamaa,
Haka suka cigaba da firarsu kamar yadda suka saba su 3,Ameera yar gidance,khadeeja kuwa yar baba larai ce,Aiki taxoyi gidan tun tana goyon Khadija take aiki a gidan har kawo yau,
12:13pm Baba larai firar tasu ta tashi,baba larai ta tashi ta nufi cikin gidan domin sanarwa da Hajiya mamaa dawowarta daga tafiyar datayi zuwa garinsu,sukuma suka shiga gyaran dakin,
*************************
*Aminu Kano int'l airport*
Da misalin qarfe 3:00pm na yammacin ranar Alhamis jirgin Max air yayi landing a Aminu Kano airport daya dauko daga qasar Holland,ciki kuwa harda shahararren Attajiri Dan Attajirin qasar wato *ABDULKARIM ABDULFATTAH MAI NASARA*matashi Dan gayu mai ji da tashen kudi,aji,da kyau,motocine baqaqe wuluk qirar _BW4 Prado's_guda 10,sunyiwa wata mota qirar _Explander_qawanya biyar gaba biyar baya,sai jiniya sukeyi kamar wani president sukaxo dauka,
Jirgin aka bude passengers sukafara firfitowa,farouq ne sanye cikin coat ta cikakken ma'aikacin banki yafito daga cikin jirgin fuskarsa dauke da Murmushi na dawowa qasarsa Nigeria bayan shafe 5yrs a qasar Holland, daga bayansa kuwa Abdulkarim Abdulfattah ne cikin yauqi yake saukowa daga matattakalar benan jirgin,sanye yake cikin coat shima amman black color wadda ta amsheshi,fuskarsa ba walwala kasancewar fuskarsa sanye take cikin bakin glass,hannayensa duka zube suke cikin Aljihu,da sauri Alhaji ABDULFATTAH da securities dinsa suka nufeshi,cikin sassarfa shima Abdulkarim yataho Dan hango mahaifinnasa suna zuwa suka rungume juna cikin tsananin farinciki Alhaji ABDULFATTAH ya furta _"u re highly welcome my luvly son"_qara rungumeshi Abdul yayi sannan cikin husky voice dinsa ya furta _Tnx u My grt Abbah_sakinsa yayi ya rungume farouq shima yayi masa welcome sannan suka dunguma suka nufi gidan su dake unguwar _NassarawaG.R.A Kano_a guje suka fice daga airport din suna jiniya.
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE๐Ÿ‘„*
_.....Adulterer's Daughter_
_*A TRUE LIFE,TOUCHING HRT & LUV STORY*_
_BY_
*MARYAM PINKY*
8โƒฃ
Suna shiga gida Hajiya Amina ce matar Alhaji Abdulfattah da Kibdiyya ne suka fito suka tarbesu,suna parking tinkan su gama Kibdiyya ta ruga a guje Ta rungume Abdoul duk da tsawonnanta iya waist dinsa take,cikin murnar ganin yayannata take fadin "welcom My Yaa Abdul" shima murmushi yaketayi na ganin qanwartasa,cak ya dagata sama sannan ya saita fuskokinsu ya sumbace ta a goshi sannan ya ce "Tnx u my lil sis" Dariya take tayi tana sake rungumeshi sannan itama ta sumbaceshi a goshi,lumshe ido yayi sannan ya sauketa ya dube ta yace "Kinyi nauyi My Angel" turo baki tayi gaba tafara bubbuga qafa sannan takalli su Mummy da Abba dasuke kallon su suna dariya tace "Abba wae nazama likuta?" Murmushi Abba yayi yace "A'a Bakiyi ba"gwalo tayiwa Abdoul daya xuba mata sexy eyes dinsa tace " Mummy ae dai shine ma yazama likuti ko?"dukkansu suka fashe da dariya ban da ita,shafa kanta mommy tayi sannan tace "Yi haquri daughter na,kyaleshi kinji"Abdul ne yadan bata rai sannan ya kalli farouq dayaketa kallon su cike da birgewa sannan yace friend xomu shiga ciki tinda sunbarmu anan suna biyewa shirmen Wannan, Kibdiyya ce ta rufe idonta da hannu bibiyu sannan tace " loll yaa farouq welcome"dariya yayi yace "sai yanxu?" Ai banganka bane sorry,dariya kawae yayi sannan suka nufi cikin gidaa Dan har su Abba sunyi gaba,Abdoul riqe da hannun Kibdiyya suka shiga tanfatsetsen falonnasu daya gaji da haduwa mai cike da kayan alatu,Lokacin da suka shiga har su mummy sun haura upstairs Dan anfara kiran sallar la'asar, farouq ne yakalli Abdoul dayake danna phone dinsa a tsayen yace friend bari kawae na wuce gida nadawo da daddare,batare daya dago ba yace "Okay see u,my regards to Hajiya"ficewa farouq yayi daga falon,
Sai da Abdoul yakuma daukan like 5minutes atsayen yana pressing phone dinsa Kibdiyya na riqe da dayan hannunsa,
Kallonta yayi yasakar mata murmushi, itama murmushi tayi tace " Yaa Abdul muje muyi sallah,shafa kanta yayi sannan ya nufi part dinsa tabi bayansa,
Qaton falo ne mai kyau da tsari dauke da bedroom qato da toilets guda biyu sai dinning table dake falon,kai tsaye bedroom din ya nufa,tsaf yake kamar na mace,yasha gyara,A hankali ya xauna abakin gadon sannan ya sunkuya yana cire takalmansa,A hankali ya furta "baby Koma falo kijirani" noqe kafada tayi....wani razanannen kallo me hautsina kayan cikin mutum ya wulla mata da sexy eyes dinsa masu firgita maxa ba mataba yasa tafice daga bedroom din da gudu tana toshe bakinta sakamakon kukan daya taho mata tana kiran mummyyyy,
Ko a jikinsa shi sai ma tabe baki da tsoki dayaja bayan yarakata da ido,farin towel ya jawo ya daura a waist dinsa bayan ya cire coat din jikinsa,sai da yafara wanka sannan ya dauro Alwala yafito,cikin sauri ya nufi closet dinsa bangaren qananan kaya yaciro farar shirt mai taushi mara hannu da wandonta threequater ya sa sannan ya jawo praymat yatada sallar,bayan ya idar da sallah yayi addu'oi sannan yatashi yakoma kan gadon yadan jingina bayansa da gadon ya lumshe ido yana shaqar ni'imtaccen qamshin turaren _Touchme_dayaketa tashi a dakin,a hankali yafurta _Home,home,sweet home_Murmushi yayi a hankali ya bude idonsa sakamakon jiyo sallamar Umma Rabee me aikinsu a cikin falonsa tana cewa "Oyoyo da baqin turai,ina dannawa yashigane?" Silifas dinsa ya zira yafito falon yana murmushi "Tubarkallah dannawa yazama babban mutum" shafa sumar kansa yayi sannan ya tsuguna har qasa yace "Ina wuni Umma Rabee,munsameku lfy" shafa kansa tayi tace "Lfy lau dana,barka da dawowa gida,Allah yayi muku Albarka" Amin ummah,"Ina Umarun ko yana ciki?",A,a yaje gida,Au toh sannuku sannunku Dama Yanxu na dawo Hajiya take sanar min,murmushi yayi yace"Allah sarki"to nabarka lfy sai kafito,"Okay"yace mata,sannan tafice,Cikin bedroom yakoma sakamakon jiyo kiran sallar magariba da aka fara a massalacin gidannasu,toilet yakoma yasake dauro Alwala sannan ya cire rigar jikinsa ya maida jallabiya coffee color mai kyau wadda ta haska farar fatarshi datake ta shining kamar a tabata jini yafito,turaren _Shams-Al'emraty_ya sa nanda nan yafara futar da sassanyan qamshi sannan yafito yarufe part din ya nufi masallaci,bayan an idar da sallar basu fitoba shida Abbansa saboda mutane masuyi masa sannu da zuwa,sai da sukai sallar ishaaa sannan suka nufi cikin gidan,9:03 sukayi sallama acikin falon,Ba kowa a falon sai mummy tana kallon CCN news dagani su take jira,sannu Alhaji Ashe kuna tare?,Eh..wllh we re yafada yana zama a 2seater dake facing din mummy,murmushi tayi tace "Ni ko welcome ba'abarni nayi ba" murmushi Abba yayi yace "Ae gashi nan" yadau remote yana canza channel, Abdul Kan 3seater da mummy take yaje ya kwanta yadora kansa kan cinyar mummy tare dayin hugging dinta yace "I miss u mummy na" shafa kansa tayi tanajin qaunar tilon dannata a xuciyarta tace"Missed u too son"sallamar farouq ce ta katsesu duka, durqusawa yayi yana gaishe da Abba da mummy,cikin sakin fuska suke amsawa suna tambayarsa Hajiyarsa,"Lfy qlau tana gaisheku"Mummy ce ta kalli Abdul da idonsa ke rufe kamar me bacci tace son ga Farouq, "Okay" kawae yace,Abba cikin xolaya yace "mummy duk murnar ganin dannaki tasa baki bawa kowa Dinner ba" Duk sukasa dariya banda Abdul dayayi kamar bayama falon,sai da suka tsagaita sannan mummy tace "Son wae haka?" Shafa tummy stomach dinsa yayi yana miqewa daga kwanciyar yace "Is true naaa" Okay kutashi muje dining,dukkansu suka miqe suka nufi dinning din,warmers ne manya kala kala da plates da jugs na tangaran a jejjere akai, Abba tafara serving Tuwon Alkama miyar ganye sannan tadubi su Abdul da farouq tace "Yau duk sae kunyi Amai cox dura zanmuku dannasan a can bacin nakirki kukeba"Murmushi farouq yayi yace Chaii mummy, itanma murmushi tayi tace tana xuxxuba musu pounded yam da vegetable soup sai qamshin Aroma ke tashi " Bar kagani"Sai da ta sassaka musu 3-3 sannan ta tutturo musu,shi dae Abdul baice komai ba sae janyo plate dinsa yayi yafara ci, duk suma sukafara ci, sunyi nisa cikin cin abincin bamai magana cox sun kwaso yunwa gashi kuma an sami garar mummy... Abba ne yayi hamdalla Bayan ya kammala yadubi Mummy yace "Allah yayi miki Albarka" murmushi tayi tace "Amin Alhaji" Au...ni kuwa ina Kibdiyya banji taba kotayi bacci?...murmushi mummy tayi tace "Ae Alhaji yau Fushi take,bankuma son me akayi mataba,nayi tambayar duniya amman taqicewa komai sai kuka kawae" Abba ne yace "Ashsha...to taci Abinci?" Inafa tun da la'asarfa,Abdul dayayi shiru yanajinsu,sai yanxu ya tuna da kukan data fita tanayi,Murmushi yayi ya miqe tsam yadauki Abincin yabar gun yanufi upstairs, duk suka bishi da ido,Abba yace "May b ma shiyasata kukan" Da alama kam Dan dama daga part dinsa tafito tana kukan inji mummy,Murmushi Abba yayi yace "Lallashi Yakama shi kuwa"
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:01 PM] maryam Tahir Author Y4: *YA'R ZINA CE๐Ÿ‘„*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
_Shafin na masoyane,Masu qaunata da masu san book dinnan, nagode qwarai da kukafara fahimtata,masu cewa suna nemana Kuma naga saqonku fatan Alkhairi a duk inda kuke๐Ÿ˜˜๐Ÿ‘๐Ÿป,ga numberta_ 07065255269 *For any Advises, comments nd correction*
9โƒฃ
Direct Abdul part din mummy ya wuce,kaitsaye falon ya kunna kai Bakomai sai qarar AC daketayi,in just 5secs ya kalli falon yaga bata cikin,Bedroom yanufa,can quryar gado ya hangota ta takure guri daya Atamfar daxu ce haryanxu a jikinta,jikinsa ne yayi sanyi daya tuna shine yasata kukan cox he knows da tuni batayi bacci ba,Ajiye Abincin yayi akan mudubi sannan A hankali ya haye kan gadon,baccinta take tayi amman sai sauke ajiyar zuciya takeyi,fuskarta duk hawaye sun bushe,qura mata ido yayi kamar yau yafara ganinta,kallonta yafara tinda ga sama(kanta)ya sauko fuskarta,ita ba fara bace kuma ba baqa bace,chocolate color ce,tana gashin gira mai yawa wanda yake qara mata kyau,hancinta baicika tsawo sosaeba,tana ido da lips masu shape din hrt,Idonsa ne ya sauka a kan kirjinta wanda yasa gabansa yayi mummunar faduwa don ganin breast sunfara fito mata Dan ga sunan ma yana ganin yanxu duk da qananane kuma daxu ma daya dauketa dama yaso yaji,tagumi yayi idonsa ya kada jazur yafara tunanin makomar Auren da aka daura musu shida ita shekaru 5-6 dasuka wuce tare da rayuwar Kibdiyyan.........
*Asalin Labarin*
Alhaji Abdulfattah mai Nasara hamshaqin Dan kasuwane kuma Dan boko wanda yaga jiya kuma yaga yau kuma har yanxu ake damawa dasu a qasar,shi Dan asalin jihar jigawane cikin local government din dutse a wani qauye da ake kira SAKWAYA,iyayensa dukkannisu fulanin garinne,su biyu mahaifansu suka Haifa shi da qanwarsa *Fanta*yan garin suke cemata *Larai*Saida iyayensu suka shekara 17bayan haihuwar Alhaji Abdulfattah sannan aka haifi larai saboda haka suke cemasa Mai Nasara,tin bayan haihuwar larai qanwarsa mahaifinsu ya rasu bayan fama da ciwon qafa na shekara biyu,Innarsu ita tacigaba da kula dasu duk da itanma ba Lafiya ce da itaba,Abdulfattah wanda suke kira da Audu bayan yagama secondary school dinsa agarin sai yadawo baya komai sai saida rake,kwatsam wata rana sai kamsilan garinsu yace Gwamnati tana neman wanda suka gama secondary school suka fita da sakamako mai kyau za'aturasu karatu waje, Duk garin su biyu shida Abokinsa Sa'idu suka samu,innace tadinga qarfafa masa gwiwar yaje Allah yanatare da shi Dan shi _MAI NASARA_ ne,bada son ranshi ba haka suka tattara suka nufi tashar garin domin tafiya lokacin sgekarunsa 23,larai kuma 6,innace tadinga yi masa nasiha da ya riqe gaskiya,amana banda shashanci,"Insha Allahu inna"yaketa fada yana sharar qwalla,da gudu qanwarsa larai taxo tanata haki tace "Yaya Yaushe zaka dawo?" Kwallarsa yashare sannan yahade hannayensu su duka har inna sannan yace "zandawo insha Allah" dukkansu kuka sukeyi yadubi inna yace "Inna Dan Allah kidinga rage sa damuwar Inna beldo a ranki kinji,Murmushi tayi tace " toh mai Nasara"da haka sukayi bankwana suna kuka suka tafi,tafiyar da har gobe bai koma garinsu ba tinbayan tahowarsa sakamakon mugun asirin da kishiyar innar wato inna beldo tayi masa na bazai kuma tuna garinba,
_Isarsu Holland 2-05-1970_
Sun Isa Lafiya inda aka kaisu makarantar cikin jami'ar bayan ansama musu Admission shi da Abokinsa sa'idu,sunfara karatu cikin Nasara baruwansu da komai sai karatu gashi gwamnatin na turo musu allowances akan lokaci basu da wata matsala,shekararsu 1 suna karatun fannin kasuwancinsu sunyi kyau sun murje musamman Abdu,yanxu sun sami aboki Dan jakadan nigeria yana sonsu sosae mai suna _MUSTAPHA_shima abinda yake karantawa kenan, lokacin dasuka shiga aji biyu akai juyin mulki gwanatin data daukesu ta sauka,sunyi kuka sosai Dan sunsan karatunsu yaxo qarshe Dan har kudin Accommodation dinsu yaqare yau an tashesu,mustapha Dalha shiya daukesu yakaisu gidan su yayiwa mahaifinsa bayani,ya tausaya musu yakuma dauki nauyin biya musu su cigaba har su kammala,part guda yabasu kusa da na Mustafa sannan yace dukkansu idan sun dawo sucigaba da zuwa kasuwa kasancewarsa hamshaqin Dan kasuwa a qasar,haka rayuwa tacigaba da tafiya cikin nasarori amman ko kadan basa tuna gida,Dan ko zancen komawa Nigeria basuyi,bayan sun kammala karatun,sai duk suka cigaba da zuwa kasuwa inda aketa samun nasibi,kasancewar Alhaji dalha bamai hassada bane yasa duk sunxama suma oga,Anacikin haka Wata ya'r qasar mai suna Angelina ta maqalewa Abdulfattah duk da ba musulma bace,ansha fama sosae har dai ta musulunta zuwa _AMINA_da taimakon Alhaji dalha yashige masa gaba aka daura musu Aure,shima sa'id ba dadewa ya auri _Haajarah_amman YA'R nigeria ce itada iyayenta don haka sai ya tattara yakoma can,Shekarar Abdulfattah da Amina 4 da aure suka haifi dasu kyakyawan gaske Kamar balarabe mai suna _ABDULKAREEM_shima sa'id acan matarsa ta haihu mai suna _Umar farouq_shekarsa 7 Abdulfattah yadauko shi akasasu a mkrnt shida Abdul,kamar yan biyu haka suka kasance gun hajiya Amina,shekararsu 8 hajarah ta sake haihuwar Mace amman ba rai,kwatasam kuma a shekarar SA'ID allah yayi masa rasuwa ,wanda baqaramin gigita Alhaji Abdulfattah tayiba,sanadiyar haka Alhaji Abdulfattah ya tatraro yadawo nigeria yacigaba da Harkokinsa Sai da su Abdul sukakai shekara 17 sannan Alhaji Abdulfattah

1 Comments On YAR ZINA CE
avatar
abdulkadir-6

1 year ago

Reply

Is a very educated and interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment