Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

musu bayanin duk Abinda ya faru tin daga farko har fitowar ta.
"Innalillahi -wa-inna-ilaihir-raji'un.."kawai Baba larai take furtawa,iya tashin hankali kam ya shigeta a yanxu, don gani take kamar yanxu Akan idon ta Abin ke faruwa,sai da tagama jimamin sannan tace
"Sannu kinji,Barka ma da bai miki komai ba," sannan ta d'aga hannu sama tace
"Ya ubangiji ka shirya Wannan bayi naka,Allah mun gode maka,kai ne Abin godiya,Allah ka karemu daga duk wani sharri duniya da lahira"
Duk suka Amsa da Amin,
Khadija da jikin ta yagama yin lakwas da jin baya nin Ameera tace
"Chaiii,wllh bakiji ciki na ba,sai na zagaya"
Wani d'an Murmushi ne ya bayyana kan lips d'in Ameera jin Abinda tace,itama baba larai sai da ta d'an dara sannan tace
"Matsoraciya kawai,abin kad'an sai ya hautsina mata ciki"
Murmushi Ameera ta sake yi kawae,itakuwa Khadija tuni ma ta fice.
Bayan ta dawo ne ta zauna kusa dasu tace
"Mama kamar naji Ance anyi mutuwa?"
"Eh...inna beld'o ce ta rasu,yau kwana hud'u,dama bari nayi sai Anyi bakwai sai na taho kuma sai gaku"
Ameera tace
"Ayyaa Allah sarki,Allah ya jik'an ta"
Baba larai tace "Amin Amin,Ae tasha jinya"
Ameera tace
"Wayyoo..itace Gwagwgwan Ku d'in nan ko Mama?"
"Eyyiii...itace dama ta rage mana,Abokiyar zaman mahaifiyar mu ce"
Khadija tace
"Allah sarki Allah yayi mata rahama,"
Suka Amsa da Amin,sannan baba larai tace
"Idan Anyi Addu'ar bakwai sai mu wuce kawai..."
Zabura Ameera tayi kamar zatayi kuka tace
"Ina zamu wuce?"
Duk ta basu dariya, sannan Khadija tace
"Kano mana,kinji ki da wata tambaya" ta fad'a tana yiwa Ameera hararar wasa,ita kuwa Ameera marairai cewa tayi ta dubi Baba larai tace
"Dan Allah Mama kar mu koma,kashe nifa za suyi,.."
Dariya sosae Khadija tayi tace
"To ba sai a d'aura muku Aure ba kawai.."
Ta fad'a tana kashewa Ameera ido d'aya,
Ameeran kuwa goge k'ollar ta tayi ta dubi Khadija tace
"Ke yanxu sai ki min fatan wannan?,...Mama kinji abinda Khadija tace min koh..?,"
Murmushi Baba larai tayi zuciyarta cike da k'aunar Ameeran tace
"Rabu da shirmen ta Ae ke In Allah ya yarda mijin ki na musamman ne"
Ta fad'a tana shafa kanta,
Kunya ce ta kama Ameeran Dan haka ta sunkuyar da kanta tana Murmushi,
Khadija tace
"Wai! Waya ga mijin Ameera?"
Sai kuma ta tintsire da dariya tana rik'e baki,
Baba Larai ce ta sa tsintsiya ta jefi Khadija tana yi mata dak'uwa tace
"Ungo nan Dije,...Ai zaki ganshin dama"
Ita dae Ameera tana sunkuye tana jin su Amman cikin zuciyar ta cewa take yi
"Ni wama zai Aure ni A yanda nake?..ni fatana Allah ya sada ni da fuskar Mahaifiya ta na ganta ko da once in a lyf ne.."
Baba larai ce ta katse mata tunanin da ta fara yi ta d'ago fuskarta tace
"To...mama Dan Allah muzauna A nan garin karmu koma kanon"
Murmushi kawae Baba larai tayi tace
"Karki damu Ku kwanta da safe mayi zancen"
Kwanciya sukayi daga nan bacci ya d'auke su.
★★★★★★★★★★★★★
*@ 5:00pm*
Harabar _MARHABA EVENT CENTRE_ dake tarauni,jeran gwanen motoci ne Manya-manya na Alfarma sukayi parking a cikin gun,babu Abinda ke tashi agun sai bushe-bushe da sauti mai sanyi,duk inda ka kallah agun furannine different colours an k'awata gun,tindaga sama kuwa rainbow balloon's ne anyiwa ko wacce kusurwa ta gun kwalliya da su ga fitilu red&blue suna on and off,
Mutanen ciki ne suka fara fitowa daga cikin motocin fuskar su kowa ka kalla agun farinciki ne shimfid'e a kan fuskar sa,sunyi kwalliya cikin wani codelaces Ash and red color,Masha Allah sunyi kyau,banda sound d'in cameras babu abinda kake ji,daga can kuma sai ga wata long lexis itama bak'a wuluk,glasses d'in ta masu duhu baka ganin komai,ta shigo cikin gun a guje,gefe itama tasamu tayi parking, nan da nan ya'n Bikin suka nufi gun motar ana gud'a da fesa turaruka,wasu dattijai ne sukazo jikin motar suna jira a bud'e, sai da aka d'auki kusan 20minutes sannan aka bud'e, Masha Allah ganin fitowar Angwaye da Amare da sukayi,sunyi kyau har sun gaji,Abdul da Husna ne A gaba sai Farouq da Fareeda a bayan su,daga baya kuma manya-manyan Abokai da ya'n uwa ne suka take musu baya zuwa cikinhall d'in da Aka tana da don fara gabatar da lunching d'in biki mai tarihi na d'an gidan _Alhaji Abdulfattah mai Nasara_, Bikin daya zagaye kowace Kafa ta media kowa Allah ya sanya Alkhairi yake cewa,Abdul dae fuskar nan laba'asa za'a ce don kai tsaye bazaka iya fahimtar yanayin dayake ciki ba,hadae Akayi taro aka watse daga nan.
Da misalin 10:00pm Aka kai Amare gida jen su dake street d'aya,but different side,bayan sun sha nasihohi daga b'angarori,suma Angwayen haka,mummy tayiwa Abdul fad'a sosae akan ya kula mata da su gaba d'aya,shi dai tinda tafara bai ce komai ba har sai da tagama sannan yace _Insha Allah mummy,_ daga nan ya wuce zuwa gun da Farouq da Sauran Abokan sa suke,daga nan suka tafi suka raka Farouq,
Abdul a harabar gidan yaci burki Dan cewa yayi bazai shiga ba gun yaran nan Dan baiga Abinda zai ce musu ba, tinda ya rako Farouq din kawae shikenan ya wuce bai saurari tsokanar da sauran friends d'in sa suke masa ba,dama shi cewa yayi baya buk'atar rakiyar kowa kar su ja masa raini. _Allah yabada zaman lfy_
11:33pm yagani lokacin da ya shigo cikin main falon gidan,shiru ko ina kamar bashine fal da mutane d'azu ba,kakkashe lights d'in yayi ya haura saman,part d'in sa ya nufa direct,falon sa ya shiga ya Ajiye Leda da keys d'in daya shigo da su,bedroom ya nufa yana shiga ya fad'a toilet yasaki shower mai d'umi, ya dad'e a toilet d'in sannan yafito sanye da bathrub iya gwiwarsa,stool ya janyo ya zauna a gaban mirror yafara tsane ruwan kansa,ya d'ago kenan daga shafa lotion d'in dayayi rubbing a k'afar sa sai yaji kamar Numfashi a kan gadon sa,A hankali ya tashi ya nufi bedside d'in ya kunna lights d'in haske ya gauraye ko ina,ga mamakin sa K'ibd'iyya ya gani kwance ta lullub'e duka jikinta da bargon sa tana ta bacci,Ransa ya d'an b'aci don Shi A plan d'in sa bedroom d'in sa nashi ne for only him don haka ya yaye bargon ya d'an dake ta,da sauri cikin firgita don ita taji zafi ta tashi zaune tana mitsitstsike ido,zama yayi gefen gadon yana kallon ta yace
"What re u doing here...?"
Stammering ta shiga yi tafara k'ok'arin sauka daga kan gadon,
Wani razanannen kallo ya jefa mata yace cikin huskyvoice
"Idan ki ka k'ara one more step frm there.."
Kafin ya k'arasa tace
"Yaa Assignment na nazo ka koyamin ban iya ba kuma Antyn mu yace sai ta daki duk wanda bai yi b..."
Da sauri ya katse ta cikin fad'a yace
"U dey mad!...why can't u wait for me to come?"
Shiru tayi ta sunkuyar da kai k'asa,
Ganin tayi shiru ya sake hasala shi don baya son yayiwa mutum magana yayi masa shiru don haka yakai mata wata cafka yana cewa
"So..I have to repeat my self right..?"
Da sauri ta goce tana girgiza kai tace
"No...I'm sorry"
Tsokiii yaja yace
"Sorry for ur self..useless girl"
K'ibd'iyya ganin ya mik'e tsaye yafara nufo inda take yasa ta fara kuka tare da ja da baya shima yana binta sai da sukaje jikin bango sannan ta runtse ido hawaye na zubowa babu k'ak'k'autawa tana sauraren ta inda zai fara tafkar ta ya kalleta for some minutes ganin yadda ta rufe ido,bin hawayen yayi da kallo yadda suke zuba sai kuma yaji duk ba dad'i,sassauta murya yayi yace
"Oyaa open ur eyes.."
A hankali ta bud'e idon tana kallon sa itama,
"Waya ba ki permission na shigowa part d'ina talkless of entering my bedroom haaa?"
Sai da ta share hawayen sannan tace
"'D'azu ne da aka kawo Anty Husna shine friends d'in ta suke ta disgracing d'ina,shine da Bala ya shigo d'azu mummy ta Aiko sa nace ya bud'e min part d'in na dawo."
Tinda tafara magana ya zuba mata ido har ta gama sannan ya nisa yace
"Are u sure?"
Gyad'a kai tayi tace
"Allah.."
Yace mata
"Okay...but don't Eva and Eva come to my part without my permission, are u clear?"
"Yes"
Ta bashi Amsa yanxu hankalin ta yafara nutsuwa,
Shima ganin haka yasa yace mata
"Jeki falo ki jira ni"
Books d'in ta ta d'auka a kan gadon cox shi sai yanxu ma ya kula sannan ta fice.
Shiryawa yayi cikin wasu pitted cotton pyjamas farare tas masu zanen Rose's masu d'an shara-shara, sunyi masa kyau sosae don sun fito da Ainahin zatinsa na cikakken Giant man of 30yrs,perfume yayi spraying wanda ya had'u da k'amshin bathsoap d'in da yake using,slifas ya zira masu taushi ya fito falon,Azaune kan rug ya hango K'ibd'iyya tana kallon TV,kan 2seater ya zauna yana facing d'in ta,sai da ya d'auki remote ya rage volume d'in sannan ya kalle ta yace
"Ina Assignment d'in?"
Da sauri ta d'auko ta dawo kusa da shi ta nuna masa,sai da sukai kusan 30minutes yana koya mata tana shigarwa sannan suka gama,Murmushi yaga tayi da suka gama ita kad'ai tace
"Thank God..I'm safe"
Cikin ransa yace
"Har yanxu bata san duka"
Kallon sa tayi taga ita yake kallo,d'an diriricewa tayi,ganin haka yasa yace
"Uhuuumm..."
Sosa kai tayi sannan tace
"Yaa yau mummy bata ce tana gaishe ni ba?"
Wayarsa ya d'auka sannan yace
"Tace"
Mik'ewa tayi ta d'au littafin ta tayi hanyar fita,
Da sauri ya tsai da ita yace
"Mik'omin waccan.."
Yayi mata nuni da hannunsa,
Ledar daya Ajiye ce ta mik'o masa,bai karb'a ba yace
"Taku ce,ki kai mata d'aya ki d'au d'aya"
Yana gama fad'a ya mik'e ya nufi bedroom d'in yana cewa
"Ki rufe min k'ofar idan kin fita"
Ta Amsa da "toh Yaya"
_*PINKY CE*_
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
[email protected]
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touch the heart of readers❤_}
#[email protected]
*IG PML WRITERS*
#https//www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
2⃣8⃣
Da sallama Husna ta shigo cikin falon cikin kwalliya mai ban sha'awa tayi kyau sosae cikin wani orange Swiss lace,sai K'amshi ke tashi daga jikin ta,Farouq ne ya fad'ad'a Murmushin sa yana cewa
"Amarya bakya laifi..."
Murmushi tayi tana serving d'in Abincin tana tambayar Farouq Fareeda amman cikin zuciyar ta tsoro ne fal,amman idan ta tino Awannin da suka shafe d'azu su Rukky suna fad'a mata dabarun nan sai ta dake don ta k'uduri Aniyar ko ta yaya sai Abdul ya sota,shi kuwa Abdul tinda ta shigo ransa ya sake b'aci ganin ko veil babu a jikin ta gashi ta tsaya tana surutu da Farouq cikin zuciyar sa yana hango irin hukuncin da zai mata,
Tana gamawa ta fice don gani takeyi idan bata bar gun ba Abdul zai iya disgracing d'in ta don ganin yadda yake watsa mata wani matsiya cin kallo,
Tana fita Farouq yayi Murmushi yace
"Dan Allah kasaki ranka ta fita fa"
Ignoring d'in Farouq yayi yaci gaba da kallon da sukeyi,Farouq sai da yaci ya k'oshi sannan ya tafi,
Shikuwa Abdul daga nan gidan su yatafi don gaishe su.
★★★★★★★★★★★★★
Washe gari da suka tashi bayan sunyi sallar Asuba,fira suka dasa su ukun basu koma ba,Ameera jin ta take kamar Anyi mata bushara,don yanayin garin yayi mata dad'i sosae gashi yau babu Aiki ko tsangwama,wani tattausan Murmushi tayi tana kallon Khadija tace
"Yau nayi Right Nima"
Dariya Khadija tayi tace
"Aikam Dan bakiji yadda nake jina wasai ba Nima"
Duk sukayi dariya,
Baba larai dake gefe tana jin su tace
"Ai ita dama rayuwa indai zakayi hak'uri to komai zai wuce har ya zamto tarihi"
Ameera tace
"Yawwaaa mama kin yadda kenan mu zauna A nan?"
Dariya Baba larai tayi tace
"Ameera kenan,Ai zaman garin nan ko Dan ke bai kamaceni ba,bare kuma Anan d'in ma zamana bashi da wani Amfani"
Cikin rauni Ameera tace
"Yanxu nan kenan sai mun koma?"
Dafa kanta baba larai tayi tace
"Eh..yau d'in nan ma kuwa insha Allah"
Girgiza kai tayi hawaye suka fara bin kuncin ta,
'Dago da kanta mama tayi tana goge mata hawayen tace
"Ameera dole ne nakoma kano Dan Abubuwa da dama, ban so sanar da kuba,amman yazama dole Yanxu na sanar muku,kunga na farko Karatun Ku, na biyu kuma Mahaifinki idan ya dawo nemanki bai sameki ba ya zaiyi?,na uku kuma Wannan d'an uwan nawa da nake fad'a muku ya b'ata tin muna yara jiya an sake samo labarin sa,ance yana nan cikin kanon kinga dole naje na nemeshi don shi kad'ai ne gudan jinina,kuma na cika wasiyyar gwagwgon mu da ta barmin na nemoshi duk inda yake,Wannan shine kawai"
Duk sai jikin su yayi sanyi jin maganganun Baba larai, Khadija ce cikin rashin kuzari tace
"Mama to Allah yasa mu same shin,kema kiga d'an uwanki"
"Amin" tace
Ameera ma tace
"To Amman ya zamuyi da su mama?"
Shiru ta d'an yi sannan tace
"Ba ma unguwar zamu koma ba,dama nayi niyya daga na dawo zan bar gidan,don dama na sami wani gida na kama haya,
Duk murna suka kamayi da jin Albishir d'in barin gidan,
Daga nan tace su tashi su shiga cikin gida a gaggaisa don da Azahar zasu wuce,
Duk suka tashi suka shiga ciki suka gaggaisa kowa sai Masha Allah yake cewa idan yaga Ameera,itakuwa yau zuciyar ta wasai take jinta don kana kallon fuskar ta za kaga Annuri kwance a kan fuskar,haka suka dinga shiga ko ina suna gaishe su sannan suka dawo suka fara shirin komawa kanon dabo.
5:00pm suka sauka a tasha cikin gajiya,wata runfa suka shiga suka zauna sannan Baba larai ta d'au ko wayar ta takoma gefe tafara waya,mintina kad'an sai gata ta dawo gunsu tace musu yanxu za'azo a d'au ke su,
Bai fi 20 mins ba saiga wani mai mota Golf3 yazo yayi parking gunsu,fitowa yayi suka gaisa da Baba larai, tace
" Lawan Ashe ka iso"?,
Yana daukar kayan yana sawa cikin motar yace
"Wllh kuwa Ai dama ina kusa"
Sai da Aka shigar da komai sannan suma suka shiga yaja su suka tafi,zuciyayoyin Ameera da Khadija cike da dokin son ganin gidan da zasu koma,Ameera bata san irin farincikin da take ciki ba,.
Wani farin cikin ne ya lullub'e su ganin bama hanyar unguwar su akayi ba,Unguwar tudun yola suka shiga Baba larai na tayiwa lawan mai mota kwatance har suka iso gidan,gida ne k'arami ba Babba ba mai d'an kyau haka,baisha jiki ba,idon Ameera da Khadija kamar zai fad'o don kallo,mukullin lawan yabawa Baba larai bayan yasauke musu kayan,fatan Alkhairi yayi musu tare da sallama yaja motar ya tafi,
Baba larai ce tasa mukullin ta bud'e gidan,Aikuwa da gudu suna rige-rige suka fad'a wai kar d'aya ta Riga d'aya, Murmushi Baba larai tayi kawae cikin zuciyarta tace
_ko yaushe zasu san sun girma oho?_
Kayan ta fara d'auka tana shigarwa,sukuwa sun shige cikin d'akin sun zube kan kujera suna ta labarin gidan Dan gidan ya birge su sosae, 'D'aki uku ne a gidan ciki da falo Babba sai d'aya da ban madaidaici,gefe kuma band'aki ne da kichin suma,terrazzo ne a tsakar gidan,sai tiles milk a dakunan,gidan dai dai-dai mutum d'aya, sallama tayi ta shiga ta same su kan kujera suna ta santin gidan,itama zama tayi tana cewa
"Kun taho kun barni da kaya ko?"
Dariya sukayi Ameera tace
"Oops wallahi murna nake da canjin rayuwar nan"
Khadija tace
"Wallahi fa"
Babba Larai tace
"Sai mu godewa Allah don shine abin godiya"
Ameera ce ta d'an gyara zama tace
"Mama yanaga to gidan da kayayyakin Amfanin komai?"
Murmushi Baba larai tayi tace
"Ai nan gidan Hajiya kubra k'awata ne tabani Aro"
Khadija tace
"To ita ina take?"
Murmushi tayi tace
"Tatafi saudiyya neman kud'i,"
Dad'i ne ya kama su Ameera tace
"Ashe xanyi rayuwa mai dad'i Nima?"
Baba larai tace
"Ai ba'a futar da rahamar Allah"
Sukace "hakane"
Tashi sukayi sukayo Alwala don rama sallolin da basu yi ba zuciyar su cikin farinciki.
Bayan sun idar ne kuma suka fara shawarar abinda za'a dafa kasancewar magriba tataho,Wannan tace Adafa Wannan, Wannan tace a dafa Wannan, daga k'arshe dae Akabi shawarar Ameera tinda sunzo da doya da kayan miya,inda suka tashi suka d'ora sakwara da miya,
Bayan sunyi sallar ishaa, zaune suke a cikin bedroom d'in d'akin madaidai ci mai d'auke da katifa da sif ta jikin bango,gefe kuma mirror ne da locker,
_mu had'u da daddare may be_
I'm sick,ur prayers re highly needed👏
[1/26, 3:02 PM] maryam Tahir Author Y4: *'YAR ZINA CE👄*
_......Adulterer's Daughter_
*A TRUE LIFE, TOUCHING HRT & LUV STORY*
_BY_
*MARYAM PINKY*
[email protected]
*®REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITER'S*
_{We don just entertain nd educate,we touched the heart of readers❤_}
#[email protected]
*IG PML WRITERS*
#https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
#http://maryamsbello.blogspot.com
*Childhood friend,sec.sch.friend nd naughtiest friend eva ZAINAB BUKOLA SARAKI{Mrs Abdul}*
_This page ix your's badan halinki ba😎_
3⃣0⃣
Yana shiga part d'in bata falo sai plasmar dake ta faman yi ita kad'ai,bedroom d'in ya shiga babu ko sallama can ya hango ta gaban mirror tana d'aura d'ankwali,wani irin takaici ne ya sake kama shi,take yaji zuciyar sa kamar ana zuba masa ruwan dalma,cikin sassarfa ya k'arasa gun wanda yayi dai-dai da d'agowar ta zata tashi don ta kammala d'aurin d'ankwalin,wata irin shak'a yayiwa wuyanta wadda tasa tafara kakarin Amai,bata gama tantance duniyar da take ba taji wani gigitaccen mari wanda yasa taga wasu irin korayen taurari,kuka tasa tana tambayar sa me tayi?,Aikuwa nan da nan zuciyarsa ta sake hasala ya kalleta da rinannun idanun sa da suka juye suka zama ja saboda b'acin rai yace
"So...u don even knw what u do right?"
Cikin azabar shak'ar tace
"Ni ban san me nayi b.."
Bata k'arasa ba taji saukar wani Marin da yafi na d'azu gigita ta tare da cillata kan gado wanda yasa kanta ta bugi da Allon gadon ji kake kum! Sai kuma ta saki wani irin kuka mai cike da wahala,shi kuwa cikin huci yafara cire belt d'in jikin sa yana cewa
"I will teach you lesson right now before the next thing..."
Gadon ya hau ya fara zuba mata belt d'in ajikin ta tako ina,Husna ihu kawai takeyi tana neman taimako shi kuwa banda sauke mata ita babu abinda yakeyi,ganin yana neman illata ta yasa ta mik'e tafara neman gun tsira,Aikuwa shima ya diro daga kan gadon ya bita yana cigaba da labta mata duk ya farfasa mata jiki banda jini babu abinda yake fita ta hancin ta da bakinta gana goshinta inda ta buge shima ya kwaranyo ya wanke mata fuska,falo ta fita da gudu ya Mara mata baya,ganin ba sarki sai Allah sai ta shiga rok'on sa akan yayi hak'uri wallahi ta dena,sauke belt d'in yayi sannan yasa hannu ya ja ta kiiiii har cikin bedroom d'in ya jefata kan gado sannan yazo bakin gadon ya d'ora k'afarsa saitin fuskarta yace
"By Now nasan kinsan me kikayi koh?"
Cikin wahala tace
"A'a..nifa bansan.."
Bata k'arasa ba taji saukar belt d'in a fuskarta,cikin wata irin gigicewa ta furta
"Nasaniiiiiiiiiii"
Ya cigaba da cewa
"Oya tell me waya ce ki kirawo mummy ki sanar da ita"
Husna babu bakin magana don ita kad'ai tasan irin azabar da take ji don haka sai kawae mirgina kanta takeyi,
Ganin tak'i magana yasake shaud'a mata belt d'in yace
"Can't u talk!!!"
Belt d'in ta ratsa ta bata san sanda tace
"Rukky da Fadeela ne" ba
Murmushi yayi a zuciyarsa yace "I know"
Amman a fili sai ya shak'o rigarta ya zaunar ta kan gadon yace
"Tell me me kika cewa mummy"
Aikuwa ta zauna cikin wahala ta sanar mai duk abinda suka yi dasu har wanda bai tambaya don gani takeyi idan bata fad'a ba ya sani zai iya sake dukan ta itakuwa yanxu burin ta kawae ya fita,
Shiru yayi bayan ya gama sauraron ta sannan ya tashi ya jingina da mirrorn yace
"Ke saboda baki da hankali baki da tunani kuma bakisan meke miki ciwo ba shine zaki bi Wannan banzar shawarar tasu,to bari kiji Abinda baki sani ba,Bana son ki bana k'aunar ki bani da wata desire akanki bazan tab'a sonki ba,wato kinga tinda suka ajiye ki ban kulaki ba shine har kika sami bakin kai k'arata gun mummy, to wllh as from today idan kika sake ko kika kuskura kika sake kai k'arata wllh sai na miki wanda yafi Wannan,indai kuna tinanin sex with u zaisa na soki to your brains sun fad'a muku k'arya,...lastly for your information idan kinga zaki iya zama ahaka ki zauna if not kuma fine ga hanya nan,but ki tabbatar baki fad'i laifi na ba,sannan kuma daga yau zan dakatar da maids na gidan nan all,responsibility d'in ya koma kanki like share everywhere including my parts ki tabbatar before I arrive kin gyara ko ina na d'akina da toilet kin fice karki bari na shigo na sameki, mopping, cooking e.t.c (Joseph zai baki sauran details),Kuma ki tabbatar breakfast as early as before 7:00pm is ready including me,and weekend's ki dinga kiran baby kina kuna shiga tare,is that clear??"
Da sauri tace
"Eh.."
Gyad'a kai yayi sannan ya jawo kunnan ta ya murd'e yace
"If I found something rubbish u will see..."
Yanagama fad'a ya take k'afar ta yafice yabar ta,
Yana fita ta kife akan gadon ta bud'e shafin sabon kuka mai cin zuciya cikin zuciyarta tana tsinewa Rukky da Fadeela da haka har bacci ya d'auke ta.
Shi kuwa Abdul yana fita part d'in sa ya shige zuciyarsa wasai yake jin sa kamar ya sauke wani nauyi,bathroom ya shiga yayi taking shower sannan ya fito ya shirya cikin cotton sleeping dress masu dogon hannu milk colour, sallah ya tayar ta shafa'i da wutr sannan ya d'ora da nafilfilu,bayan ya gama ne ya zira flat silifas ya fito ya shiga kitchen,Lipton ya had'o a cup da yankakkun friuts a flate ya fito yana tiriri,A falo ya zauna kan carpet bayan ya janyo k'aramin centre table d'in ya d'ora Lipton d'in akai sannan ya tankwoshe k'afarsa ya fara shan fruits d'in yana kallo peacefully, yayi nisa cikin kallon da shan fruits d'in K'ibd'iyya ta shigo da sallama sanye da hijjabi, A ciki-ciki ya Amsa batare da ya kalle ta ba,
A hankali ta samu waje kusa da shi ta zauna don yanxu ba laifi ta d'an yi nutsuwa,shiru tayi tana kallon da yake yi,turo mata plate d'in yayi alamar taci,d'auka tayi tafara sha shikuma yana kurb'ar Lipton d'in kamar baya son sha,
"Yaya"
Yaji K'ibd'iyya tace
"Batare daya kalle taba yace
"uhummmn.."
Matsowa ta sake yi sannan ta fito da wani littafi _AR-RIJALU WAN-NISA'U HAULAR RASUL_
Tace
"Yaya koya min nazo kayi"
Jiyowa yayi bayan ya rage volume d'in TV ya janyo littafin yana kallo,ganin yayi shiru yasa K'ibd'iyya tace
"Plsss Yaya ka koya min kar Malam Ismael ya dake ni yace duk wanda bai iya ba sai ya Zane shi"
'Dagowa yayi daya ji ta Ambaci duka,bai san sanda yace
"Duka kuma?"
Kyab'e fuska tayi tace
"E,rannan cewa yayi ma ko ni danake ganin Daddy ne ya k'ara sch.d'in wae wallahi sai ya zaneni "
Tsokiii Abdul yayi kawae amman cikin zuciyarsa ya k'udurta duk randa kuwa tace ya dake ta wllh sai ya ci masa mutunci,
Koya mata ya farayi tarihin sayyadina Khadija ne,sai da yayi ta mai-mai ta mata sannan yace tayi ta biyawa, shikuma ya janyo laptop d'in sa yafara research,
"Yaya kasan me?"
Yajiyo ta fad'a,
Girgiza kai yayi kawai alamar A'A,
Tace"malam Ismael d'in nan ko d'an san kai ne,tintini yaka mata mu gama tarihin Nana Khadija amman sai slow yakeyi mana"
Shi dai Abdul bai ce komai ba,tace"Yaya kasan wai me yace ma?"
Girgiza kai ya sake yi
Tace
"Wai baya so mugama saboda sunan Ameera Mustapha ne,kuma wae ba sunan dayake so irin nata saboda wae duk Ajin tafimu hankali da nutsuwa da k'ok'ari yadawo yace ma duka makarantar, shine Aisha lawal tace ita dae ban da ita shine ya zaneta sosae har Abban ta sai da yazo,Amman ba abinda akayi masa saboda shine best teacher,"
Shi dai Abdul Aikin sa yakeyi amman yana saurarenta,
Ta cigaba
"Wae yanxu kuma ita zai Aura,idan ya shigo Ajin komai Khadija, idan kuma akayi laifi ita da sistern ta baya dukan su wai yasan su baza suyi ba,rannan da prefect ta dake ta agun sallah sai da ya kirawo prefect d'in har class d'in mu ya zaneta kuma yace ta tsuguna taba ta hak'uri,ita kuma Ameera munafuka ce sai tayi ta kuka wai ita ta yafe,"
Matsowa ta sakeyi tace
"Kuma yaya kasan ma wacece?"
'Dan ture laptop d'in yayi don da bai d'auki firar K'ibd'iyyan serious ba amman tinda yafara jin abinda take fad'a akan yarinyar yaji wani irin tsanar ta da malam Ismael d'in jin yadda yake wani fifitata,yace
"No.."
Tab'e baki tayi tace
"Su Aisha lawan sunce basu da gida Malam Ismael ne ya kama musu haya gun Maman Khadija take ba babarsu d'aya ba ita bata da iyaye,A school d'in ma 'YAR ZINA ake ce mata bata da..."
Da sauri Abdul ya ce
"Enough Baby banson jin wannan storyn buh remind you be aware of her OK?"
Gyad'a kai tayi tace
"Ni dama bana kula ta.."
Shafa kanta yayi yace
"Good, wata school d'in ma zaki koma"
Mik'ewa yayi ya d'au laptop d'in sa ya kashe TV yace
"Idan kin gama kiyi switch off"
Ta amsa da toh shikuma ya shige bedroom jin kansa na d'an Sara masa,brush ya shiga yayi sannan ya fito ya kashe lights ya bar dim,Addu'a yayi sannan ya kwanta yaja blanket,
Washegari tun Asuba Husna ta tashi ta fara Aikace Aikace duk da tsamin da jikin ta yayi haka ta daure ta ke ta Aikin danma tanayi a gida,6:40 ta shirya komai a central falo kamar yadda joseph yake yi ta gyara ko ina sannan ta koma part din ta bayan ta d'ebi nata,
Abdul kuwa bayan ya shirya kamar kullum

1 Comments On YAR ZINA CE
avatar
abdulkadir-6

1 year ago

Reply

Is a very educated and interesting novel

Please Login or Register in order to submit comment