Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

RUBUTACCEN AL'AMARI


*Na*
*Aysha Aliyu Garkuwa*


πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡?πŸ‡πŸ‡


Hakika ke din zakaran gwajin dafi ce ke zara ce a cikin taurari
Adda amm kasancewarki cikin duniyar marubuta babban alfarma ce ga makaranta ubangiji Allah ya kara daukaki ya dafa miki ya kuma baki ladan abinda kika isar inda kika kuskure kuma Allah ya gafarceki damu gaba daya.

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
Ummul

Hakika mutuwa na da ciwo amma babu abinda mamaci ke buqata da ya wuce adu'armu, damuwa, da saka shi a rai, ko yawan daga hankalinki da makusantanki bashi zai dawo miki da Hamma ba. Ki sani yarda da kaddara me kyau ko mara kyau yana daga cikin imani ki rungumi kaddararki hannu bibbiyu Hamma umar kam ya tafi kuma inshaa Allah tafiyar hutu ce a gareshi tunda kowa ya shaida yayi mutuwar shahada.
Allah ya kara baki hakuri ya jibanci lamuranki ko er kanwata😜

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡

Usman

Hakika kai din jarumine a zahiri da kuma cikin littafin addana ☺ Allah ya kara mala jarumta da hakurin zama da ummul tamu ka sani rarrashi da kwantar mata da hankali shine naka da sannu komi zai wuce inshaa Allah. Allah ya kara muku son juna ameen yayana kuma dan tsoho kakana jauro😜

πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡πŸ‡
*Iyalan shuwa*

Ina kara mika muku ta'aziyata rabbi ya jiqan hamma ya kara baki hakurin rashinshi kyawawan halayensa su bisa amin Allah ya bawa mara lafiyan cikinku lafiya ameen😊






Fatima zaune gaban hajiya sai riritata ake yi hajiyar ce ta gyara zama tace fatima ki saurareni da kyau ban taba kin daya daga cikinku ba ta nunasu su biyun ita da adeeja
Ta cigaba da fadin ku din ya'yana ne ta yaya zan ki ku? Mu biyu Allah ya bawa iyayenmu bamu da yawa muma din sai kuma Allah bai bamu haihuwa da yawa ba har gwara ni nayi hudu shi yasa kika ga na matsu in ganki da ciki shi yasa kika ga na sa an raba auren Khadija saboda ganin mijin na neman kashe mana zuriya eh mana in ya kashe mata mahaifa ai har muma aabin ya shafe mu tunda ya hana zuriyar mu yaduwa ubangiji Allah ya rabaki da cikin nan lafiya kema kuma Allah ya fito miki da miji na gari kije kema ta hayayyfo mana jikoki dariya duk suka yi tace Allah ya muki albarka.


Sai dai me cikin nan ba karamin wahalar da fatima yake ba kaman jira yake yi a san dashi ciwi take yi sosai bata iya yin komi bata iya cin komi duk ta dawo abin tausayi hajiya taso a dawo da ita wajenta amma dake sun hadu da makwabta ma gari dr zakiyya tace kullum zata dinga zuwa dubata sai adeeja ce ta koma gidan dukda bat so ba amma ba yanda za tayi dan woosai take jin kunyan sageer kuma a duk lokacin da ta ganshi sai taji gabanta ya fadi.

Shi yasa bata tana fitowa sai ya tafi aiki fatima na lura da hakan sosai tausayin 'yar uwarta ke ratsata kullum cikin yi mata addua take yi


Sai da cikin ya kai wata bakwai ta dan sami lafiya shima ba sosai ba.

Sageer duk ya birkice inda kuka san shi ke dauke da cikin ko ciwon dole yasa ya ajiye koyarwan da yake yi a ATBU ya zauna zaman jinyarsa dan ba zuwa office dinsa na company dinshi yake yi ba ji yake kan ya dauko ciwon ya maida jikinsa.

Bangaren adeeja ma ba karamin tausayawa er uwarta take yi ba gaba daya ta fice hayyacinta bacci adeeja bata yi kullum tana cikin sallan dare tana rokanwa kanwarta afuwan wannan ciwon da abinda ita adeejan ke ji a zuciyanta.

Hajiya ma bata kwana biyu bata zo dubasu ba gashi dai lafiyan baby kalau amma uwar kullum cikin ciwo take in kaga fatima sai kun tausaya mata amma duk da hkaa ita ke kwantar musu da hankali kullum murmushi ne kwamcw a fuskanta tana nuna musu ba komi su kwantar da hankalinsu zata haihu lafiya.

Kamar ko yaushe hajiya tazo dubata dr zakiyya ma tana gidan dukkansu har sageer din suna palo sun sa fatiman a gaba ta samu taci abinci fir taki dauriya kawai take ti amma wani irin murdawa cikinta ke yi ga kafanta da ya rike shiru tayi dan bata son tayar musu da hankali.

Dr zakiyya ce ta lura da halin da take ciki tace anya fatima ba labour kike yi ba kuwa murmushi tayi wanda kina ganinshi kin san a fatar fuska ne kawai da sauri dr zakiyya tace da sageer dauko mota ka kawo bakin palon nan mu tafi hospital.

Cikin minti biyu ya dawo ya kinkimeta duk da girman cikin dukkansu suka dunguma suka tafi asibitin.


Tun bayan la'asar ake abu daya har asuba fatima ta kasa haihuwa duk tabi ta galabaita dole tasa aka yanke shawaran yi mata aiki.

Turota akayi za a shiga dakin tiyata da ita hannunta ta daga alaman a tsaya adeeja ta yafito ta rike mata hannu murmushi tayi tace ki daina kuka adda ki min addua tunda nake nakudan nan aduan miji na gari nake ta miki sai kuma tayi mirmushi tace kin san me Allah ya karbi adduata dan na san da kyar in fito adda ki daure ki cikawa iyayenmu burinsu ki aure yah sageer ki kulan min da baby na ke kadaice zaki iya rike min babyna a gidan ubanshi kiyi biyayyan da baki yi shi ba a shekarun baya na sani rabon yaranmu yasa kika kasa yin biyayya adda adeeja kiyi shi a wannan karon hawayene ya gangaro mata adeeja ta sa hannu ta goge mata tana wani irin kuka tace ba ki da hankaline inshaa Allahu zaki fito lafiya zafin ciwo ke saki maganganun banza komawa gefe tayi dan bata son jin irin maganganun da take yi hajiya ta yafito tace hajiya ki yafe min duk rashin kunyan da nayi ta mike hajiya na share kwala tace na yafe miki fatima na san yarinta ce lumshe ido tayi ta bude tace hajiya ki min alfarma bayan ba ni ki hada auren yah sageer da adda adeeja hajiya tace fatima zaki fito da yardan Allah ki raini abinda kika haifa murmushi tayi cikin jin ciwo tace hajiya in ban fito ba zaki cika min alkawari? Gyada kai hajiya tayi saboda kukan da yazo mata sageer ne ya karaso hannunta ya rike yace do this for me baby please yanda kika shiga ki fito min lafiya murmushi tayi tace yah hakan ba a hannuna yake ba yana hannun rabbi gyada kai yayo sosai yayi dauriya bai zubar da hawaye ba tace yah sageer ka yafe min duk wani laifi da nayi maka tsawon zaman da muka yi a tare...

Kafin ta dire yace na yafe miki habibty ki daina iein maganganun nan zafa ki fito lafiya murmushi tayi hade da lumshe ido ta bude tace na gode yah sageer in ban fito ba ka min alkawarin zaka auri adda adeeja?

Kafin ya bata ansa nurse ta turata akayi dakin tiyata da ita

Tsawon awanni aka dauka a ciki yayinda yan uwanta ke ta zarya a bakin kofan suna adduan Allah ya fito da ita lafiya.

Dr zakiyya ce ta fito ta jingina da kofan hawaye na zarya a kumatunta da sauri suka karaso wajenta suna tambayanta anyi nasara?

Idonta a lumshi hawaye na gangarowa tace she went into an arrest and her heart beat stopped ta karasa tare da sulalewa ta zauna kara adeeja ta saki lokaci daya suka fadi sumammu ita da sageer...........😭😭😭

πŸ’–RIBAR BIYAYYAπŸ’–












By Sawwama A.












Page 36.








Cikin gaggawa nurses suka kai musu dauki aka shiga dasu wani ward.

Hajiya kam zaman dirshan tayi a wajen ta kasa kwakwaran motsi sai lebenta dake furta innalillah wa'inna ilaihirraju'un Allahuma ajirni fi musibati wa akfilni khairan min ha.

Yayinda zakiyya ma take zaune a jikin kofa tana rera kuka sosai take jin fatima a cikin ranta tana jinta kamar kanwarta salma da suka fito ciki daya cikin 'yan watanin da suka san juna shakuwa mai karfine ya shiga tsakaninsu gashi yanzu mutuwa ta raba su.

Nurse ta fito daga dakin da fatima take ta tsuguna dai dai kunnanta ta rada mata wata magana zumbur ta mike ta shiga dakin jim kadan wata nurse ta fito da yara biyu a nannade kasancewan dama am cire yaran mikawa hajiya hajiya yaranta tayi duk su biyun hajiya ta rungume tana kuka me tsuma zuciya.

Har nurse din ta juyq zata tafi sai ta dawo ta,dafa kafada hajia tace mama kiyi hakuri ki daina kuka tayi jimmm sai tayi kasa da muryanta sosai tace *bugun zuciyan* ta ya dawo sai dai is very weak kiyi mata addua Allah ya tashi kafadunta ba tare da jiran ansan hajiya ba ta mike ta kona dakin.

Hamdala hajiya tayi ta kara rungume yan jikokinta tana kara tsananta addua Allah ya tashi kafadun fatima so take taje ta ga halin da autanta da adeeja suke amma inaaa bata jin zata iya motsawa daga wajen fatima

Tsawon awanni 2 Dr zakiyya ta dauka tare da wani likita cikin dakin kafin suka samu daman shawo kan matsalan amma duk da haka da taimakon oxygen taje numfashi sannan aka turata zuwa wani dakin.



Bude ido tayi tana kallon saman dakin tana kokarin tuno me ya faru a hankali kwakwalwanta ya fara taryo mata abinda ya faru zumbur ta mike ta diro daga kan gadon idonta ne ya sauka kan gadon da sageer yake kwance a hankali ta karasa bakin gadon ta kurawa kyakyawan fuskanshi ido mai kama da nata.

Yatsanta ta saka ta zana karan dogon hancinshi idonta na zubar da kwalla da sauri ta kwabi kanta me nake aikatawa haka ni adeeja fatima bata mutu ba no baza ta mutu ba haka tayi ta sambatu daga karshe ta nufi hanyar fita karo suka ci da zakiyya zata shigo dubata fadawa tayi jikinta tana kuka.

Patting bayanta zakiya tayi tace ya isa haka fatima bata mutu ba ta haifi yaranta biyu du maza dagowa daga jikinta tayi tana dariya tana kuka murmushi zakiya tayi ta shiga ta duba ruwan da aka sawa sageer sannan ta ja hannunta suka nufi dakin da aka kai fatima.

Yah rid suka samu rike da baby daya ita kuma hajiya ke zaune kan sallaya dayan babyn kuma na cikin crib dinshi da sauri adeeja ta karasa ta daukeshi ta rungume shi a jikinta tana jin wani irin nishadi raguwar farin cikinta shine ganin halin da fatima take ciki.

Hajiya tace ja'irar yarinya kin farfado ashe, raguwar wofi kawai dariya duk suka yi adeeja tace haba hajiya dan Allah ai wallahi mun san matsayin mu nida baba karamia wajenki wato ko kizo ki duba mu kina nan makale da mazanki a nan.

Zakiyya tace ai kuwa ashe hajiya na son fatima duk fadan nan nasu nan ma dariya suka yi ban da yah rid da ya murmusa kawai wanda ya sanshi ya san haka yake mutum ne me daurewa wanda bai son wargi cikin dar dar adeeja ta gaishe shi ya amsa a dakila tare da mikewa ya ajiye baby a cikin crib dinshi hajiya kawai yayi wa sallama ya fice matarsa tabi bayanshi tabe baki adeeja tayi ta ajiye babyn ta dau dayan tana cewa hajiya an kira jos kuwa? Hajiya tace ina naga sukunin kiran wani jos ai bana jin akwai wanda ya dauko wayarsa.

Oh toh bari aunty zakiyya ta shigo ta ara min in kira baba. Hajiya tace hakan ma yayi.

Sageer bai farka ba sai magriba a firgice ya farka yana sambatum fatima bata mutu ba i can feel it fatimana tana raye inshaa Allah baza tq mutu yanzu ba zata haihu lafiya ta ba ma babynmu tarbiya alluran bacci aka mishi ya koma.

Washegari da safe yan jos suka iso a lokacin sageer ya farka ya tisa fatima a gaba ko babies din ya kasa dauka tausayawa halin da fatima ake ciki yake har a lokacin oxygen ne ke taimaka mata mama ma na ganinta ta rushe da kuka abin mamaki hajiya ke lallashinta tana tausarta.

Adeeja taji dadin ganin muhd sani yayi kyau yayi bulbul da shi yana samun kulawar kakarsa rungume danta tayi tana me jin dadi.

Sai da fatima tayi kwana uku aka cire mata oxygen.

A kwana na hudu sageer na zaune gaban gadon rike da hannayenta kaman kullum ya zuba mata ido yana mata magiyin ta tashi haka dr zakiyya ce ta shigo tana dubata idanunta ne ya fara far far alamuj zata budesu..........


















*kulli nafsin za'ikatul maut*



Tunda fatima bata mutu ba ko yah rid za a bawa adeeja? πŸ€” *team adeeja*#





SAWWAMA QAWWAMA😘























SAWWAMA QAWWAMA😘
πŸ’–RIBAR BIYAYYAπŸ’–












By Sawwama A.













Page 37.















Dan bude idonta tayi da sauri ta mayar ta rufe saboda hasken da ya kashe mata ido kokarin kara bude idon take amma maganganu take ji a nesa da ita.

Fatima fatima kina jina kin san ni kin ganeni? Dr zakiyya ke jero mata tambayoyi bata amsa ba adeeja ta shigo.

Kaman jiran shigowanta take ta fara samabtu yah sageer ina sonka ab zan juri ganinka da wata macen ba adda adeeja kiyi hakuri mutukar ina raye yah sageer mijina ne kiyi hakuri adda ina son mijina mutukar ina raye baza ki taba mallakansa ba duk da dumbin sonshi da nake hangowa a cikin idonki tabbas in na mutu ke kika fi kowa dacewa da shi da sauri adeeja ta fice a dakin. Ita kuma fatima ta koma bacci.

Kallon dr zakiyya sageer yayi yace meke faruwa da ita ne ? Murmushi tayi tace abinda ke ranta kenan kafin a mata aiki sambatu ne kawai da ta kuma farfadowa zata dawo normal cikin damuwa sageer yace that is when? Murnushi ta kuma yi tace soon kar ka samu damuwa ya gyada mata kai kawai.

Adeeja karkashin wani bishiya ta samu ta zauna tana rizgan kuka meke faruwa da ita ne wannan wani irin bala'i ne ta yaya akayi har tayi saken da fatima ta lura da son da take yiwa mijinta innalillahi wannan abin kunyan da me yayi kama lallai zaman bauchi ya kare a wajenta tunda har fatima ta gane halin da take ciki game da baba karami anya zata iya kara hada ido da fatima kuka take sosai ranta cike da dana sani.

Sai da ta kwashi awa uku tana bacci sannan ta farka wannan karon a cikin hayyacinta ta farka cikinta ta fara shafa taji wayam da sauri tayi kokari mikewa sageer dake fitowa daga toilet ne ya ankara da sauri ya karaso wajenta ya mayar da ita ta kwanta ganin yanda take cije lebe ya san cewan she is in pain zuwa lokacin sauran mutanen dake dakin sun san ta farka

Wayarsa ya ciro a aljuhu ya danna number din dr zakiyya cikin minti biyu ta shigo da yake tana asibitin duddubata tayi sannan tayi murmushi tace komi normal welcome back mommy twins waro kananan idanunta tayi wanda suka kara komawa ciki daya bayan daya take kallon kowa a dakin wanda duk murmushi ne a kwance a fuskarsu idonta ne ya sauka kan cribs din babies dinta

Lumshe ido tayi hawaye ya zubo daga idonta hawayene na farin ciki wai yau itace da yara har biyu saurin bude idonta tayi lokacin da taji duminsu a gefe da gefenta sageer ne a tsugune a kanta yana sakar mata murmushin shin nan me tsada kiss ya manna mata a goshi yace baby ga yaran mu nan da Allah ya bamu kyauta kin gansu nan masu kama dani. Har eyes din? Ta furta a hankali lokaci daya kuma ta kume bakin dan jin wani wari da bakin yake murmushi yayi Ya shafi kanta yaji dadi sosai da yaji maganan ta duk da abinda ta fara furtawa ya bashi dariya wato ita dai da maganan manyan ido shi bai ga aibin idonta ba they arw sexy wani murmushin ya saki yace har eyes din kafin ya tashi, daga tsugunon da yake yace adeeja miko mana silver bowl din nan da ruwa i think your tootbrush is in this drawer ya fadi hakan yana jan drawern ya zaro brush da toothpaste.

Now bari *Saifuddeen da Salahuddeen*😊 su bar mamansu ta huta ya kwashesu ya kai su crib dinsu adeeja ce ta kawo bowl din da ruwa ta ajiye zata taimaka mata ta tashi ya karaso yace no kar ki damu wannan aikina ne gefe ta matsa gabanta na cigaba da faduwa cikin kulawa ya tadata zaune ya kuskure mata baki sannan yasa brush ya brushing mata adeeja na tsaye tana kallonsu cike da sha'awan yanda yake bata kulawa abinda bata taba samu ba a wajen Hameed hana karya daren amarcinsu da safiyar ranan, juuyawa tayi ta fita daga dakin idonta cike da kwalla

Tea ya hado ya kawo mata tasha sannan ya fita ya kirasu hajiya da mama dake waje sannu suka yi mata sannan dr zakiyya ta bata magungunan ta Allah Allah take ta kara jin dumin yaranta kaman sageer ya sani ya dauko daya ya samata a cinyanta yace ga saifuddeen nan rikeshi kuji dumin juna for sometime kafin nan ya ba kaninshi waje shima murmushi tayi ta rungume abunta kallonshi take yaron kyakyawa dashi fari kal ga suma da ya sauko goshinshi kaman diyan larabawa hajiya ce ta matso tana rike da dayan tace fatima kin ga kyautar Allah ko biyu kyautar Allah wanda ba kowa yake bawa ba mikawa sageer dayan tayi ta karbi salahuddeen ko kadan basu da bambanci da juna identical twins ne( yah Allah ka baniπŸ™πŸΎπŸ˜­)kallonsu take tana yiwa Allah tasbihi.


Kwananta biyar da haihuwa aka sallameta taji sauki sosai bakin nan ya bude sai surutu take in hajiya ta shigo ta samu tana zuba zata ce ke gafara can ki rufe mana baki ke da kika kusan lulawa da ragon mijinki a wajen ai babana ban san kai rago bane sai ranan daga kai har khadeeja duk na fiku jarumta ga wata likita ma me ragon zuciya me yiwa patient kuka.

Sai duk wajen anyi dariya dr zakiyya tace ai kam hajiya kin fimu jarumta fatiman ce ta kidima mu fatima tace iyyee ashe dai ana sona hajiya kema fa naji labarin kasa zuwa ki dubo autanki kika yi kina like da kofata yah sageer nafa kwace maka fada.

Haka sukq kasance cikin farin ciki da annushuwa gidan hajiya aka kaita inda sageer ma ya tattaro ya dawi gida abinshi shirye shiryen suna aka fara sosai sosai hajiya ta kira dukka ya'yanta da wanda ta haifa da wanda ba it ta haifa ba(yaran mijinta) tace duk kowa ya dawo ayi suna dashi dan anyi haihuwar da ba a taba gin irinta ba a dangi haihuwar biyu kuma daga autanta ai dole ma ayi gagarumin biki.........














_next page is for my _ _sweet adeeja tunda ni kadai ke sonta_☹











SAWWAMA QAWWAMA😘

























SAWWAMA QAWWAMA😘





















SAWWAMA QAWWAMA😘
πŸ’–RIBAR BIYAYYAπŸ’–














By Sawwama A.












Page 39.











_a year later_

Twins sun girma sunyi wayo sageer ya tsaya akan aikinshi biyu running company dinshi da lecturing sau daya yake zuwa jami'a kuma ya hana fatima komawa school yace ta zauna ta kulan mishi da gida he will do all the struggle ta sha kukanta ta gode amma haka ta hakura ba tare da ta daga mishi hankali ba saboda ita din a ko yaushe me biyayya ce saboda ta san ko yaya akwai ranan da zata ci *ribar biyayya*.


Adeeja hankalinta ya kwanta sosai tana samun kulawa da soyayyar mijinta a gaban kowa bai jin shakkar nuna mata soyayya in yana kasar ko da yaushe suna tare in ko bai nan toh suna makale da waya kuma ya rike muhd sani kaman dan da ya haifa ya sashi a boko da islamiya mai kyau kai in baka sani ba sai ka rantse shine mahaifinshi.

Yanzu haka tana da cikin wata biyar wanda ya sata ta ciko ta kara kyau abinda ga jin dadi a halin yanzu shirin zuwa jos suke su kaiwa iyayensu ziyara daga nan su sada muhd sani da mahaifinshi hameed.



_Hameed_

Hankalinshi a tashe ya shigo gidan yana kwalawa zaliha kira da sauri ta fito tana daura dankwali tace haba abdul wannan kira haka lafiya.. ? Ina fa lafiya ki dauko gyalenki ga Sadiqqa can a mota zamu kaita asibiti wancan lalatacen aka kama yana mata fyade.

Innalillahi shine abinda take furtawa ta dau hijab suka fita.(sadiqqa itace babban yar zaliha da Hameed shekarunta 13)


Zaune suke gaban likita kallonsu yake daya bayan daya cike da tausayin yanda hankalinsu ke tashe akan yarsu.

Gyaran murya yayi yace maganan gaskiya yarinyanku lafiyarta lau a halin yanzu dai.


Hameed ne ya katseshi yace yaz zaka ce lafiyan yarinya kalau bayan turmi da tabarya aka kama ta da mutumin da ake zargin yana da HIV.

Likita ya gyara glass din idonshi yace akan wannan ana kanyin test amma maganan fyade babu shi.

Kallon juna suka yi suka mayar da hamkalinsu kan shi suna shirin magana ya katse su da fadin abinda nake nufi ita wannan yarinyan ta saba da maza ba irin namijin da baza ta dauka ba.

Tsaye hameed ya tashi yace likita ban gane ba ya zaka ce yarinya er shekara 13 zata iya daukan ko wani irin namiji ban gane yaren ba gaskiya.

Watse hannunshi likitan yayi yace mu dai abinda muka gano kenan kuje ku binciki er ku.

A zaune suka sameta akan gadon asibiti ras dinta shaka zaliha tayi mata tace ke dan ubanki wa ya koya miki bin maza ko ki fada min ko in kasheki in kashe banza.

Tsananin shakan da taji yasa ta dinga rokanta da hannunta dan ba bakin magana Hameed yace in ta sakeki zaki fada gyada kai tayi sannan zaliha ta saketa.

Cikin kuka tace mama dan Allah kuyi hakuri mangara hameed ya kai mata yace zaki fada mana abinda muka tambayeki ko kuwa.

Lokacin da mama ke aika an wajen delu mai kayan dadi ne kullum in na bude sai in ga hoton mata da miji tsirara kullum haka nake gani shine kawai ranan na gwada sha nima.

Sunkuyar da kai tayi tace kan nonona yayi ta min kaikayi dama dama bala mai shago kullum yana son kama min nono bana yarda shine da na gaji da jin kaikayin na dau gomata naje siyan cingum kaman kullum hannunsa yasa ya sha kirjina ganin ban hanashi ba ya janyo ni ya rufe shagon yayi ta lailaye min kan nono na da yatsanshi yana kuma tsotsa ni kuma ina jin dadi shikenan kullum in mama ta aikeni sai na diba na sha inje wajen bala ko isiyaku ko madu suyi ta min abubuwa a haka duk suka sanno kuma suke kiran abokanansu ma miyi(wannan ya faru da gaskene iyaye a sa ido a san kuma ne za a dinga aikan yara)

Sulalewa zaliha tayi ta daura hannu aka tana rusan kuka cikin kuka hameed yace zaliha kin cuceni Allah ya isa tsakanina dake kina shaye shayen maganin matan nan kina ce zaki kai adeeja ne baki san ita nata baiwa ce daga Allah ba gashi nan a agrin jaraba kin lalata min tarbiyar yarinya Allah ya isa tsakanina dake kuma ki sani ko me xaki sha bazaki taba kamo adeeja ba jarababbiyar banza ya sa kai ya fice.

Cikin kuka da ihu tace ni da kai wanene jarababbe ba jarabarka ta sani a wannan halin ba gashi yarak ta debo jarabarka a jininka.


Tafe yake yana layi wannan wani irin gararin rayuwane yana isa kofar gidan idonshi suka fada kansu........



















SAWWAMA QAWWAMA😘
πŸ’–RIBAR BIYAYYAπŸ’–













By Sawwama A.











Page 40.










_Final_

Dandazon mutane ya gani a kofar gidanshi sai da gabanshi ya fadi ganin har da police kaman ya juya,sai dai ya dake ganin bai yi komai ba zuciyan shi na dukan tara tara ya isa kofar gidan.

Yaron shi salim dan kimanin shekaru 11 shake a hannun dan sanda sai wani mutum dake gefe yana ta kumfar baki.

Da ganinshi mutane suka fara fadin yawwa ga uban yaron ai gashi nan ji yayi kaman ya saki zawo hannu ya.mikawa dan sandan cikin dakewa suka yi musabaha yace ranka shi dade lafiya.

Kafin dan sandan yayi magana mutumin gefensa ya cefe da fadin danka ne ya satan min boris din babban mota yaje ya siyar.

Hannu Hameed ya aza akai yana kallon yaron da ya sunkuyar da kai hannunshi ya sauke yasa ya dago

Please Login or Register in order to submit comment