Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register


An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya




Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,



Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan

Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490



A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,



Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu



Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC



Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku


This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng

You can download more hausa novels there

Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online

It is free we do not charge for uploading novel

Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services



Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us



Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it



Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT



This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng

For feedback and support

Facebook : https://facebook.com/taskarnovels

Twitter : https://twitter.com/taskarnovels

Telegram : https://t.me/taskarnovels

This Document is compiled by
Shuraihu Usman - 08140419490
YEAR of compilation - 2023;
Published to Taskarnovels.com.ng

1ARZIKI RIGAR ƘAYA (1)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Sarkin Bagadaza, kuma Sarkin Musulunci, Halifa Haruna Rashid na zaune kan karagar mulki ya harɗe, fadawa kuwa sun kewaye shi ana tsakiyar fadanci sai ga wani saurayin bawa ya shigo riƙe da wata hula da masu mulki ke sanyawa. Ita wannan hula ana kiran ta kambin sarauta. Wannan kambi da bawa ya shigo da shi an ƙera shi da jan zinari aka yi masa ado da lu'ulu'u da jauhari da dukkan duwatsu masu daraja, amma ba a rufe saman shi ba. Wannan kambi babu tamkarsa a wannan zamani, kambi ne da kuɗi ba zai iya saye ba.

Bawa ya faɗi gaban Sarki ya yi gaisuwa, sa'annan ya ce, "ya Sarkin Musulunci, Uwargida Zubaidatu ce ta aiko ni gare ka da wannan kambi da ta sa aka ƙera mata. Ga shi an kammala ƙera shi, ta nemi jauharin da za a liƙe saman shi, ta kasa samun wanda ya yi daidai a cikin taskarta, duk wanda aka gwada sai a ga ya yi ƙarami."

Sarki ya dubi barori ya ce a tafi a dubo irin jauharin da Zubaidatu ke buƙata. Barori suka zabura da hanzari suka tafi. Can jimawa sai ga su sun dawo. Suka ce wa Sarki, "Allah ya taimake ka, mun duba taskar Sarki duka, amma ba a samu jauharin da ya yi daidai da wannan hula ba."

Halifa ya fusata ya ce, "ta yaya Sarki kamata, wanda ya mallaki sarakunan duniya duka, ɗan ƙanƙanin abu kamar wannan ya gagare ni mallaka. Kaicon ku! Ku tafi cikin kasuwanni, ku binciki dillalai da tajirai da fatake, maza ku nemo wa uwargida abin buƙatarta."

Barori suka fantsama cikin kasuwannin Bagadaza suna cigiya, har Allah ya gajishe su ba su samu jauhari mai girman da suke buƙata ba. Suka dawo gaban Sarki suka ce, "ya Sarkin Musulunci, wannan abu ya wuyata ga tajiran wannan birni da fataken da ke shigowa. Amma an ba mu labari cewa, ba za a samu wannan jauhari gun kowa ba, sai wurin wani attajiri ɗaya da ke zaune a birnin Basara mai suna Abu Muhammad Kasala."

Yayin da Halifa ya ji wannan zance, sai ya umurci wazirinsa, mai suna Ja'afaru al-Barmaki, da ya rubuta takarda zuwa ga Hakimin Basara, Muhammad al-Zubaidi, ya faɗa masa cewa, maza-maza a zo masa da tajiri Abu Muhammad Kasala zuwa Bagadaza.

Nan take Waziri Ja'afaru ya ɗauki takarda da alƙalami ya rubuta saƙon Sarki zuwa ga Hakimin Basara. Ya buga hatimi kan takarda ya naɗe ta, ya danƙa wa Masrur as-Siyafi, babban haunin Sarki. Wanda shi kuma nan take ya yi shiri tare da 'yan rakiya, suka rankaya sai birnin Basara.

Hakimin Basara ya tarye su da murna, ya shirya musu gara, suka sharɓa. Bayan sun huta sai Masrur ya ce wa Hakimin Basara, "to, ba fa zama muka zo yi ba." Ya zaro takarda, ya karanta wa Hakimi saƙon Sarkin Musulmi. Hakimin Basara ya ce, "na ji, na karɓa." Nan take ya shirya wata tawaga ya haɗa su da Masrur suka nufi gidan tajiri Abu Muhammad.

Da isar su gidan sai suka ƙwanƙwasa ƙofa. Wani bawa ya buɗe ƙyaure ya leƙo. Masrur ya ce masa, "je ka wurin ubangidanka ka faɗa masa cewa, Shugaban Muminai na nemansa zuwa Bagadaza."

Bawa ya koma cikin gida. Jim kaɗan sai ga tajiri ya fito. Ko da ya ga Masrur tare da tawagar Hakimin Basara, sai ya faɗi ya yi gaisuwa, sannan ya ce, "na ji, na kuma karɓa kiran Sarkin Musulmi. Amma ba kwa shigo daga ciki ba, ko ɗan ruwa ku kurɓa kafin na kimtsa mu tafi?"

Masrur ya ce, "ai ba dama, sata lahira! Halifa na can na jiran mu. Don haka babu buƙatar ɓata lokaci. Maza shirya ka fito mu tafi, kafin ran Halifa ya ɓaci."

Tajiri ya ce, "to bari na shiya yanzu mu tafi, amma ku shigo daga ciki ku zauna, kun san an ce shirin zaune ya fi na tsaye. Idan na shirya kuma na samu ɗan guzurin da zan kai wa Halifa, domin zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri-wuri." Ya yi ta lallashin su dai, har suka yarda suka shiga cikin gidan.

Da kutsa kansu cikin turakar farko ta gidan, sai suka ga an daje duka bangayen nan da labulayyen alharini wanda aka yi wa cin baki da ɗanyen jan zinari, aka ƙawata su da duwatsu masu ƙyalƙali da daukar ido. Abu Muhammad ya umurci ɗaya daga cikin bayinsa da ya kai Masrur bayi, ya yi wanka, ya fitar da ƙurar tafiya daga jikinsa.

Bawa ya yi wa Masrur jagora har zuwa ɗakin wanka. Masrur ya ga ɗakin wankan da bai taɓa ganin irinsa ba. Bangayen ɗakin da daɓensa duka na duwatsu ne masu darajar gaske, waɗanda aka cakuɗa da zinariya da azurfa. Ruwan wankan kuma an gauraya su da ruwan wardi.

Bayi suka himmatu wajen yi wa Masrur da 'yan rakiyarsa hidima yayin da suke wanka. Da suka gama wanka, aka ba su tufafi na alfarma, waɗanda aka yi wa ado da kumfar zinari yayin saƙa su, suka sanya.

Bayan Masrur da 'yan rakiyarsa sun kimtsa sai suka nufi inda Abu Muhammad Kasala ke jiransu, suka tarar da shi zaune bisa wani dandamali da aka yi cikin turakarsa. A saman wannan dandamali aka girke wata ƙatuwar kujera mai kama da gado, wadda aka shinfiɗa wa katifu, aka lulluɓe katifun da zannuwan alharini. A saman wannan kujera maigidan yake zaune. Bangon da aka jingina kujerar kuma an lulluɓe shi da labulen hatsaya da alharini da aka saƙa su tare da zinariya, aka kuma lilliƙa masa duwatsun jauharai masu launi daban-daban.

Sa'adda Masrur ya shigo cikin turakar, sai Abu Muhammad ya sauko daga kan kujera, ya tarye shi da fara'a, ya sake yi masa maraba. Ya ja shi suka koma kan kujearar suka zauna wuri guda, sauran mutane kuma suka zauna kan kujerin da ke cikin turakar. Daga nan mai gida ya yi umurni da a fito da abinci da abin sha. Nan da nan bayi da kuyangi suka yi ta jido akussan abinci da gorunan abin sha suna girkewa a gaban baƙin nan.

Masrur ya saki baki yana tu'ajjibin kyawun akussan da aka kawo musu abinci a ciki, su dai ba daga itace aka sassaƙa su ba, ba kuma da dutse aka yi su ba, to ko da ƙashi aka yi su? Oho. Ya ce a ransa, 'na rantse da Allah ban taɓa ganin akussa masu kyau kamar waɗannan ba, waɗanda babu irinsu ko da a fadar Halifa.'

Kowane akushi da irin abincin da ke cikinsa, wani an zuba soyayyen nama, a wani kuma an zuba dafaffe. A wani akushin kuma an zuba farar shinkafa da zuma, wani kuma gurasa ce da miya. Aka dai girke musu abinci iri daban-daban. Suka fara ci suna taɗi, suna annushuwa, ba su farga ba har dare ya ƙwace musu. Da za su koma masauki, Abu Muhammad ya ba kowannensu dinari dubu biyar.

Washegari kuma ya ƙara yi musu kamar yadda ya yi musu jiya. Ya tufatar da su tufafi na alfarma, masu launin kore da ruwan zinari. Ya himmatu ga yi musu hidima. Da Masrur ya ga suna shirin shantakewa, sai ya ce wa Abu Muhammad, "ya kamata ka shirya mu tafi, kada Halifa ya ga mun daɗe, ransa ya ɓaci."

Abu Muhammad Kasala ya amsa masa da cewa, "ya shugabana, yi haƙuri dai ka jinkirta mini, zuwa gobe na gama duk shirin da nake yi, sai mu tafi." Don haka suka sake kwana ɗaya.

Da gari ya waye, Abu Muhammad ya sa bayi suka shirya masa wata alfadararsa da yake hawa. Sirdin da aka ɗaura wa alfadarar da sauran kayan da aka shirya ta da su duka an yi su ne daga zinariya da azurfa da lu'ulu'u, sai ɗaukar ido suke yi cikin rana. Masrur ya dubi alfadarar nan, ya ce cikin ransa, 'zan yi mamaki idan har Halifa bai tuhumi Abu Muhammad yadda ya yi wannan arziki, idan ya je masa da tarin dukiya haka.' Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci.

Za mu ci gaba ranar Laraba mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
29/04/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (2)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Daga nan suka yi sallama da al-Zubaidi, suka fita daga Basara suka fuskanci Bagadaza. A kwana a tashi, ba tare da sun tsaya ko'ina ba, har Allah ya kai su birnin Bagadaza, gidan aminci.

Suka wuce kai tsaye wurin Halifa. Bayan sun yi gaisuwa, Halifa ya umurci Abu Muhammad da ya zauna. Da ya zauna, sai ya sake gayar da Halifa da kyakkyawan lafazi, sa'annan ya ce, "Ya shugaban muminai, na zo maka da wata 'yar tsaraba, idan ka yarda na kawo ta gabanka yanzu."

Halifa ya ba shi dama. Daga nan sai Abu Muhammad ya ɗauko akwati ya buɗe shi, ya fara zaro tsarabar da ya kawo wa Halifa, tsarabar da babu tamkarta. Daga cikin tsarabar akwai wata bishiya da aka yi jikinta da zinariya, rassanta da yaƙutu, ganyayenta da zabarjadi, 'ya'yanta da lu'ulu'u, girman 'ya'yan kamar ƙwayayen tattabara. Halifa ya cika da mamakin ganin wannan itaciya, gayar mamaki.

Abu Muhammad ya kuma jawo wani akwati ya buɗe, ya zaro tanti irin wanda ake kafa wa sarakuna idan sun fita shan iska bayan gari, ko idan an tafi farauta ko yaƙi. Shi wannan tanti an yi rufinsa ne da dardumar da aka saƙa daga alharini da jauharai iri daban-daban, aka ƙawata ta da kwalliyar zinariya da yaƙutu da zabarjadi aka kuma yi zanen surorin tsuntsaye da dabbobi iri-iri, na gida da na daji. Sandunan da ake kafa tantin da su kuwa an yi su ne daga ɗanyen itacen turaren sandal ɗan asalin Hindu, waɗanda da zarar an fito da su waje, wuri zai gume da ƙamshi.

Halifa ya yi mamki matuƙar mamaki da waɗannan abubuwa da ya gani. Abu Muhammad ya duƙar da kai ya ce, "Ya Sarkin Musulunci, ban kawo maka wannan tsaraba don kwaɗayin wani matsayi da za ka naɗa ni ba, ban kuma kawo maka su ba a matsayin rashawa wai don wani laifi da ba aikata. Na kawo maka su ne domin kuwa babu wanda ya dace da waɗannan kaya sai kai. Ni ba kowa ba ne face talaka daga cikin talakawanka. Kuma idan Halifa ya yarda, zan nuna masa wata baiwa da Allah ya hore mini."

Halifa ya ce, "Aikata abin da kake so mu gani."

Abu Muhammad ya ce, "To, madalla."

Ya dubi wani gini da ke cikin fadar, ya motsa leɓɓansa kamar mai karanta wata addu'a, sai mutane suka ga ginin ya zo gabansa ya rusuna. Abu Muhammad ya sake yin wata ishara, sai ginin ya koma inda yake, ya kuma miƙe kamar yadda yake da fari. Daga nan kuma ya yi wata alama da idanunsa, sai aka ga dogayen akwatuna sun bayyana a cikin fadar. Ya yi musu magana, sai mutane suka ji kukan tsuntsaye na fitowa daga cikin akwatunan.

Waɗannan abubuwa sun ƙayatar da Halifa ainun. Ya ce wa Abu Muhammad, "Ya aka yi ka samu duka waɗannan abubuwa? Shin ba kai ne ake kira Kasala ba saboda ragwanci? An fa ce mini mahaifinka wanzami ne, mai yi wa mutane aski a gidan wanka. An kuma ce mini bai bar maka komai ba sa'adda ya mutu."

Abu Muhammad ya ce, "Ya Halifa, abin duk da mutane suka faɗa maka game da ni gaskiya ne, amma saurari labarina ka ji. Akwai abin al'ajabi a cikinsa, wanda da za a rubuta shi da tsinin allura bisa ga kusurwar ido da ya zama abin lura ga masu hankali.

Ka sani cewa, ya Shugaban Muminai, Allah ya ƙara maka lafiya da tsawon kwana. Kamar yadda ka ji mutane sun ba ka labarin ƙuruciyata, to, haka ne. Ko da mahaifina ya mutu bai bar mini kome ba sai zabirar aski domin kuwa shi wanzami ne, kamar yadda ka faɗa.

Lokacin da nake yaro ana kirana da suna Abu Muhammad Kasala saboda tsabar ragwancina, ga kuma son jiki sai ka ce kyanwa. Saboda kasala idan na kwanta barci a cikin inuwa sai rana ta cim mini, ina ji ina gani, ban tashi ba, kome kuɗar da take yi mini ba ni tashi in shiga inuwa sai fa in wani ya zo ya riƙa ni na tashi. Haka na tashi a sangarce har na kai shekara goma sha biyar, lokacin ne kuma mahaifina ya karɓa kiran Ubangiji. Ya mutu bai bar mini kome ba na dukiya, sai zabirarsa ta aski.

Bayan rasuwar mahaifina, sai mahaifiyata ta shiga ɗawainiyar neman aikin da za ta riƙa samo mana abinci, har ta yi gamo da katar ta sami wurin aiki. Sai ya kasance kullum tana zuwa wurin aiki domin samo mana abin kalaci. Ni kuwa kullum ina kwance gida, sai ka ce ruwa, in mimmiƙe abina bisa shinfiɗa ina jiran dawowarta. Idan ma ta dawo ba na iya tashi sai ta kama ni ta zaunar, sai ka ce mara lafiya. Abincin ma sai ta ba ni ga baki sannan zan ci.

Ran nan ina kwance bisa shimfiɗa, sai ga mahaifiyata ta shigo inda nake, riƙe da dirhami biyar na azurfa. Ta ce mini, "Ya ɗana, na ji labarin cewa Dattijo Abu Muzaffar zai tafi fatauci Birnin Sin. Tashi mu tafi wurinsa mu ba shi waɗannan kuɗin, idan ya isa Birnin Sin ya sayo maka wata haja da su, wadda idan aka sayar da ita nan za a sami riba, idan zai koma kuma, mu ƙara ba shi wasu kuɗin tare da ribar ya ƙara sayo mana wata hajar. Wa ya sani ko Ubangiji ya yi mana arziki da waɗannan 'yan kuɗin, domin kuwa shi ne mai arzutta wanda ya so ta inda ba ya tsammani."

Ni kuwa a lokacin na ji daɗin kwanciyar da na yi, ba na son ko motsa ƙafata saboda ragwanci. Yayin da mahaifiyata ta ga haka sai ta yi fushi, ta ce, "Na rantse da Allah, idan ba ka tashi mun tafi wurinsa ba, ba na koma kawo maka abinci ko nama. Ko ruwa ba zan ƙara kawo maka ba, sai dai yunwa ta kashe ka."

Yayin da na ji haka, ya Shugaban Muminai, kuma na tabbata lalle za ta aikata abin da ta faɗa idan ban tashi ba, sai na turɓune fuska, na ce da ita, "To, riƙa ni in tashi."

Ta kama hannuna na miƙe zaune. Na yi miƙa tare da hamma, na ce ta ɗauko mini takalmina. Ta tafi ta ɗauko. Na ce ta saka mini su ga ƙafata, ta saka mini. Daga nan sai na ce, to, ta riƙa ni in miƙe tsaye. Ta riƙa ni na miƙe tsaye, har za ta sake ni, na ce ni sai na dogara ga jikinta zan iya tafiya, idan kuwa ba haka ba faɗuwa zan yi. Haka dai ta yarda na jingina ga jikinta, muka tafi ina jan ƙafafu, jallabiyar da na sanya na taɗiye ni, kamar mai koyon tafiya.

Ko da muka isa bakin teku, mun tarar da har tawagar fatake sun shirya kayansu cikin jirgin ruwa suna shirin tafiya. Dattijo Abu Muzaffar shi ne shugaban tafiyar. Mutumin kirki ne, ga shi da gaskiya da riƙon amana, sa'annan kuma akwai shi da tausayin talakawa. Muka gaishe shi, sa'annan na ce da shi, "Ya baffana, shin kai ne Abu Muzaffar?"

Ya amsa mini, "Ni ne, ya ɗana."

Na karɓi dirhaman nan daga hannun mahaifiyata, na miƙa masa na ce, "Karɓi wannan kuɗin, ka sayo mini wata haja daga ƙasar Sin, ko Allah zai ƙaddara in sami riba daga gare ta idan na sayar da ita a nan."

Dattijo ya juya wajen fatake ya tambaye su, "Kun san wannan saurayi ne?"

Fatake suka amsa, "I, sunansa Abu Muhammad Kasala. Tun da muke ba mu taɓa ganinsa a kan dugadugansa ba, wai kuma har yana tafiya, sai yau. Rabon da mu gan shi ya fito waje ma an daɗe. Kullum yana gida yana sharar barci."

Za mu ci gaba ranar Asabar mai zuwa, in sha Allah.

Bukar Mada
03/05/2023ARZIKI RIGAR ƘAYA (3)

HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA

Dattijo ya juya wajen fatake ya tambaye su, "Kun san wannan saurayi ne?"

Fatake suka amsa, "I, sunansa Abu Muhammad Kasala. Tun da muke ba mu taɓa ganinsa a kan dugadugansa ba, wai kuma har yana tafiya, sai yau. Rabon da mu gan shi ya fito waje ma an daɗe. Kullum yana gida yana sharar barci."

Daga nan sai ya juyo gare ni ya ce, "Ya ɗana ba ni kuɗin, ina roƙon Allah ya albarkace su a cikin wannan tafiya da za mu yi." Ya karɓi kuɗi daga hannuna. Ni da mahaifiyata kuwa sai muka juya zuwa gida.

Dattijo Abu Muzaffar da sauran fatake suka gama shirin da za su yi duka, suka kwance jirgi suka tsunduma cikin teku, suka nufi Birnin Sin. A kwana a tashi har Allah ya saukar da su lafiya. Suka yi ciniki suka gama, suka juyo zuwa gida. Bayan sun yi rabin tafiya sai Abu Muzzafar ya ce, "Af, na kuwa manta da saƙon yaron nan Abu Muhammadu. Babu makawa mu koma zuwa Birnin Sin in sayo masa wata haja da kuɗinsa, wadda zai ci riba da ita idan mun koma gida."

Da sauran fatake suka ji haka, kuma suka ga irin nisan da suka yi da Birnin Sin, ga shi kuma har sun fara jin ƙamshin gida. Sai suka yi ta roƙon Dattijo Abu Muzaffar a kan kada su koma da baya. Abu Muzzafar ya ce musu babu dama, lalle sai sun koma. Fatake suka ce idan ya yarda kowane ɗaya daga cikinsu zai ba da ribar abin da za a samu daga dirhamin nan biyar. Dattijo ya yarda da haka. Fatake suka haɗa kuɗi masu yawa suka ba shi, ya tattara su ya ƙulle wuri guda, sa'annan suka ci gaba da tafiya.

Suka yi ta tafiya har suka iso ga wani tsibiri, suka tarar da birni babba a cikin wannan tsibiri. Suka ɗaure jirginsu bakin gaɓa, suka shiga cikin birni domin sayen kayan ƙarau na zinariya da azurfa da nau'o'in jauhari. Abu Muzaffar ya ga wani mutum da birai da yawa wurinsa. Ya ga wani tsohon biri a cikin biran nan, gashin jikinsa duk ya fara koɗewa saboda tsufa. Idan sauran biran nan suka ga hankalin mutumin nan mai kula da su ba ya wurinsu, sai su rufar wa tsohon birin nan da bugu da yakushi, har sai mutumin ya juyo gare su ya yi musu tsawa. Idan ya ƙara juyawa wani wurin sai biran nan su sake rufe tsohon birin nan da duka.

Yayin da Abu Muzaffar ya ga haka, sai tausayin birin ya kama shi. Ya matsa kusa ga mutumin ya ce, "Ko za ka sayar mini da wannan biri naka?"

Mai biri ya ce, "Nawa za ka saya?"

Abu Muzaffar ya ce, "Ina da dirhami biyar na wani maraya da ya ba ni sallahu, idan ka sallama mini shi haka na biya."

Mutumin ya ce, "Kawo kuɗi. Allah ya sa wannan biri ya amfane ka." Dattijo Abu Muzaffar ya kawo kuɗi ya ba dillalin birai. Bayi suka ja shi, suka kai ga jirgi suka ɗaure.

Bayan sun gama sayayyar da za su yi a cikin wannan birni, sai suka kwance jirgi suka ci gaba da tafiya. A kwana a tashi kuma suka kai ga wani tsibirin. Suka ɗaure jirginsu bakin gaɓa suka taka bisa tudu suka tarar da wani ɗan ƙauye. Suka sami mutanen ƙauyen ba su da wata ɗabi'a sai a yi jinga da su, su yi nutso cikin teku su lalubo ma'adinai irinsu zinariya da azurfa da kuma wuri, su ba wanda ya ɗauki ijara tasu.

Fataken nan kowa ya ɗauki hayar mutum guda ya biya shi, mutanen suka faɗa cikin teku suka yi ƙasa suna lalube. Yayin da birin nan ya ga haka, sai ya kwance ɗaurin da aka yi masa, ya faɗa cikin ruwa tare da masu laluben ma'adinai. Da Abu Muzaffar ya ga haka sai ya yi salati, "Babu tsimi babu dabara face daga Allah Maɗaukakin Sarki. Mun rasa wannan biri bisa ga abin da Allah ya ƙaddara na asarar kuɗin wannan yaro."

Bayan wani ɗan lokaci kaɗan sai masu nutso suka yiwo sama, sai ga birin nan shi ma ya yiwo sama tare da mutane, hannuwansa cike da ma'adinai ya kawo wa Abu Muzaffar. Dattijo ya cika da mamaki, ya ce, "Haƙiƙa akwai abin al'ajabi tattare da wannan dabba.

Daga nan fatake suka hau jirginsu, suka ci gaba da tafiya, har suka iso ga tsibiri na uku. Shi wannan tsibiri ana kiransa da Tsibirin Zannuji. Tsibiri ne na waɗansu baƙaƙen mutane masu cin naman mutum. Yayin da baƙaƙen mutanen nan suka hango jirgin su Abu Muzaffar, sai kowane daya daga cikinsu ya jawo kwale-kwalensa ya nufi jirgin fataken nan yana lasar baki.

Kafin fataken nan su farga har baƙaƙen mutanen nan sun zagaye jirginsu, kowane baƙin mutum ya kama rabonsa daga cikin fataken nan, ya ɗaure ya jefa cikin kwale-kwalensa. Suka juya zuwa cikin tsibirin tare da jirgin fataken, suka ɗaure jirgin a bakin gaɓa. Suka tafi da fataken da suka kama gaban Sarkinsu. Nan take Sarki ya sa aka yanka wasu daga cikinsu aka babbaka masa, ya ce a ɗaure saura a kurkuku. Aka tafi da su, cikin tsananin tashin hankali da firgita, aka ɗaure su.

Yayin da dare ya yi tsaka, sai birin nan ya tafi wurin Abu Muzaffar ya kwance shi. Da sauran fatake suka ga haka sai suka ce wa Abu Muzaffar, "Ka taimake mu ka kuɓutar da mu daga halaka, ya Abu Muzaffar."

Shi kuwa sai ya ce musu, "Ku sani cewa, wannan biri ne ya kuɓutar da ni, da yardar Ubangiji Maɗaukakin Sarki, kuma zan biya shi dinari

Book Chapters
Chapter 1
Chapter 2Chapter 3

1 Comments On HIKAYAR ABU MUHAMMAD KASALA
avatar
musa-abdul

5 days ago

Reply

Littafin yanada matular dadi sosai

Please Login or Register in order to submit comment